Health

Wasu Daga Cikin Itacen Da Ake Sarrafawa Masu Matukar Amfani Ga Lafiyar Dan Adan

Sassaƙe na nufin yin amfani da fatanya ko magirbi ko dai wani abin wajen ciro ɓawo ko jikin wata bishiya domin a sarrafa ta a yi magani misalan kaɗan daga cikinsu sun haɗa da:

 

SASSAKEN KIRYA

Ana Amfani da sassaƙen ƙirya ana jiƙa shi da ruwa a sha yana maganin ciwon jiki.

 

Karanta>>> Ina Mata Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah

 

SASSAKEN TAURA

Ana amfani da sassaƙen taura a jiƙa a sha yana maganin (Tamama) jin-kashi wanda yara ke fama da shi.

 

SASSAKEN MARKE

Ana jiƙa sassaƙen marke a ruwa a ba mata masu ciki wata huɗu idan yana yi musu ciwo domin samun lafiyar cikinsu da jaririn da suke ɗauke da shi. Bayana haka ana shanya sassaƙen marke ya bushe a daka a haɗa da irin gero idan za a shuka domin samun kyakkyawan sakamako, sannan kuma baya burtuntuna, har ila yau ana haɗa sassaƙen marked a jar-kanwa a sha maganin tari.

Karanta>>> Hanyoyin Da Ya Kamata Matan Aure Subi Domin Kara Inganta Zaman Aurensu: Malama Juwairiyya

 

SASSAKEN SHIRINYA

Ana jiƙa sassaƙen shirinya da ruwa a rinƙa ba yara suna sha maganin mafarkin yara. Kinkiba.

 

SASSAKEN TUMFAFIYA

Ana kankare sassaƙen tumfafiya a haɗa da nono a sha maganin shawara.

 

Karanta>>> Sirrin Gyaran Nono Kashi Na Daya.

 

SASSAKEN BAKIN MAKARHO

Ana sassaƙar baƙin-maƙarho a jiƙa da ruwa har tsawon kwana uku, a rinƙa sha maganin basir mai tsiro.

 

SASSAKEN MARKE

Ana sassaƙo bishiyar marke a dafa idan ya huce sai a ɗiba a haɗa da lemon tsami a rinƙa sha yana maganin tari.

 

Karanta>>> Maganin Amosani, Karyewar Gashi Da Kuma Zubewarshi Kyauta

 

 

Sassaƙen Farar Ɗorawa da Sassaƙen Mangwaro:

Ana amfani da sassaƙen farar ɗorawa da sassaƙen mangwaron a jiƙa da jar-kanwa a sha maganin basir.

 

SASSAKEN KWANARYA

Ana dafawa da nonon saniya a riƙa sha yana maganin shawara, bayan an sha ana yin amai, ana warkewa sarai.

Karanta>>> Dalilan Dake Sawa Nonuwa Suke Zama Kanana

 

SASSAKEN GAWO

Ana jiƙa sassaƙen gawo da ruwa a sha yana maganin taurin kai, musamman ‘yan tauri ko ‘yan daba.

 

Sassaƙen Goba da Mangwaro da Lemon Tsami:

Ana amfani da su wajen maganin ciki, ana shanya su, su bushe sannan a daka a rinƙa jiƙawa ana sha yana maganin ciwon ciki.

 

Karanta>>> Amfanin  Zobo Ga Lafiyar Jikinmu 

Karanta>>> Tsumin Matan Aure  Don Inganta Auratayya

Karanta>>> Tasirin Da Tazargade Ke Yi Ga Lafiyar Mata

 

SASSAKEN ARARRABI

Ana jiƙa sassaƙen Ararraɓi a rinƙa sha yana maganin tau-tau, bayan haka ana shanyawa ya bushe a daka a rinƙa barbaɗawa a kan tau-tau ɗin.

 

SAIWOWI

 

Saiwoyi na nufin wasu jijiyoyi ne ƙananan da manya waɗanda su ke riƙe da bishiya ko tsirrai. A koda yaushe saiwoyi kan kasance ne a ƙarƙashin ƙasa amma a wani lokacin sukan fito waje ma’ana su kan turo ƙasa. A ɓangaren magungunan Hausawa na gargajiya su ma ba a barsu a baya ba, domin kuwa suna bayar da gudunmawa ta musamman wajen warkar ko kwantar da cuta a jikin Ɗan-Adam ko dabba. Wasu daga cikin saiwoyin da ake haɗa magungunan Hausawa na gargajiya sun haɗa:

Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam

 

SAIWAR KUKA

Ana haƙo saiwar kuka wadda ta ratsa kan hanya, ana haɗa maganin kwarce da kuma maganin soyayya. Akan haɗa abinci da ita a ba yarinya ta ci, maganin mallakar zuciyarta domin soyayya.

 

SAIWAR TAFASHIYA

Mata masu ciki na amfani da saiwar tafashiya, su jiƙa su sha domin samun lafiya cikinsu.

Karanta>>> Amfanin  Zobo Ga Lafiyar Jiki Da Kuma Illolinsa

 

SAIWAR GAUDE

Ana haƙo saiwar Gauɗe a jiƙa a rinƙa sha, yana maganin ƙarfin jiki.

 

SAIWAR RAWAYA

Ana jiƙa saiwar rawaya a sha, ko kuma a shanya ta bushe a daka a rinƙa soyawa da ƙwai ana ci yana maganin shawara.

 

Karanta>>> Hanyoyin Da Zaku Bi Domin Karin Kiba Ba Tare Da Kunsha Maganin ba

 

SAIWAR BAKIN GAGAI

Ana jiƙa saiwar baƙin gagai da kayana ƙanshi a riƙa sha maganin ƙarfin maza.

 

SAIWAR SABARA

Ana ɗebo ko haƙo saiwar sabara da saiwar lemon tsami da ganyen tsamiya a haɗa a daka, sannan a jiƙa rinƙa sha, yana magann tamama (shawara) kamar yankan wuƙa.

 

Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata

 

SAIWAR JEMA

Ana haƙon saiwar jema a wanke a zuba a randa ko ruwan sha, tana maganin mayu.

 

SAIWAR DAYI

Ana haɗa saiwar dayi da farin goro a tauna sannan a haɗiye ruwan, tana maganin farin jinni. Bugu da ƙari idan aka tauna saiwar dayi ita kaɗai aka haɗiye ruwan maganin sammu (Makaru).

 

SAIWAR TAFASA

Ana haƙo saiwar tafasa a dafa da jar kanwa tana maganin ciwon nono

 

Karanta>>> Illolin Kwanciyar Ruf Da Ciki Ga Lafiyar Mu

 

SAIWAR ZOGALA

 

Ana haƙo saiwar zogala a haɗa da saiwar bini da zugu da lemon tsami da kuma barkono a jiƙa a sha, yana maganin sanyi mai kumbura jiki.

 

SAIWAR KUKA.

Ana haƙo saiwar kuka ta ɓangaren gabas sai a jiƙa a sha tana maganin ƙarfin maza ….

 

Karanta>>> Ko Kunsan Amfanin Shan Kunun Aya Lokacin Shan Ruwan Azumin Watan Ramadan Kuwa?

Back to top button