Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 7 Complete Novel

   WACECE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

~Unique Barakancy~

      SEVEN📍

       Tinda aka shiga da Deen emergency likitoci ke kansa,taimakon gaggawa suka bashi ganin yana internal bleeding,iya taimako sun bashi sannan kuma suna expecting farkawarshi anytime soon,amma shiru ba labari,tini Dad da Mom sunzo abuja,Dad sai fada yake akan yayi warning dinshi akan dawowa abuja,amma dake kunnen kashi ne dashi be jiba,toh zeyi maganinshi very soon,ze mishi abinda dole ya zauna guri daya…. Mom dai lallaba dad take tayi,tana kuma bashi shawaran yanda zasu shawo kan abun…… Ansamu komai ya daidaita har anfita dashi daga emergency amma kume be farka ba,mom da dad na zaune a aminity din da aka dawo dashi…….. A hankali Deen ya fara bude idonsa,sai yaji kansa ya sara masa,kokari yayi ya bude ido yana tinanin ina ne nan,chan kuma sai ya tino yarinyar da yake bi a mota,kalle kalle ya dingayi ta ina ze hangota,ganin ya farka dad yayi maza ya kira doctors,taruwa sukayi a kansa daga su dad har doctors din,binsu da kallo daya bayan daya yayi,mamaki ya shigayi ganin mom da dad a tare dashi,a hankali cikin muryar marasa lafiya ya kallesu yace “dan Allah ku fadamin WACECE ITA?”…… Kasa gane me yake magana akai sukayi,sai kawai aka mishi allurar bacci,nan da nan ya koma bacci kuwa………

           Khaleel binta yayi da kallo yana mamakin yanda ta shanye duka,wani farinciki na kara mamaye zuciyarsa,yau hakarsa zata cimma ruwa,dariya yake a zuciyarsa yana tinanin first night dinsu ze tabbata tin baa daura aure ba,ciki siyasa irin tasu ta yan duniya yace “wifey are you okay” ganin sai jujjuya kai take…… Gyada Kai kawai tayi alamar she’s fine,cije lebe yayi ya matso kusa da ita yace “toh ko zakije ki kwanta ki huta”…… Girgiza kai tayi sannan cikin muryarta data chanja tace “no need”……, Wani killer smile yayi jin yadda muryarta ya chanja sannan ya sunkuyo daidai fuskarta yana bin lips dinta da kallo,kokarin hade lips dinsu yayi sai yaga taja baya tana ware idanunta sosai akansa…..  Saida yaji gabansa ya fadi ganin irin kallon da take masa,a da idan tana mishi irin wannan kallon sai ya diririce amma yanzu ko a jikinsa sanin cewa bata hayyacinta…… Sake yunkurin kissing dinta yayi ta kuma jan baya…… Kamar a mafarki yaji ta kwashe da wata muguwar dariya,ta kalli cikin idanuwanshi tace “Why do you have to drug me when I can willingly comply?”….. Shiru yayi yama rasa me zece jin furucinta…

Fatimah zainab ko ita kadai tasan meke going a mind dinta,an dade baa mata abunda ya tabata ba from someone she atleast cherish,she’s so disappointed,of all people wai khaleel,wannan shine betrayal of the highest order,tinda tasha first cup tayi sensing wani abu,saboda koma wani kalan drug ne it adds sweetness to the yoghurt,tanan kuma tayi detecting something is wrong,domin ta tabbatar da hakan,yasa tashanye tass,tabbas this is one of her mission coming here,gashi khaleel is making it easy for her…….Katse tinaninta yayi bayan yayi summoning courage yace “ I never thought you can give it to me easily,pls forgive me wifey,I just can’t control myself tonight,Allah ne kadai yasan me nakeji akanki”……  

Dauke kai tayi tana mamakin rashin kunyarsa,wato har yanada gout din dazai fadamata haka?,zatako shayar dashi ruwan mamaki,mamakin da har ya mutu baze manta ba,he must pay for it,amma zatabi komai a sannu…….. “Where is the stuff you diluted to my yoghurt?”…. Ta fada murya chan kasa….. Kallon rashin fahimta ya bita dashi….  Gyada kai tayi tace “You have to take the drug as well,because your normal self can’t support what I’m feeling,we need to be even before anything occur!”……. Jiki na rawa ya mike fuskarsa dauke da murmushin jindadi,batare da ya bata answer ba,ya shiga dakin daya dauko wanchan,bude drawer yayi yaga ba komai,sai a lokacin ya tina ashe guda daya ne a ciki,dukan wall din dakin yayi da hannunshi yana danasanin juye mata duka,sai kuma ya fara dudduba sauran drawers din,har yayi give up,fortunately saiga wani a last drawern daya bude,tsallen murna yayi ya dauka ya fita daga dakin,ya wuce kitchen direct,bude fridge yayi ya dau yoghurt ya fito….. Zaune ya sameta still yanda ya barta,zama yayi a kujerar dake kallon nata,ya juye duka quantity din drug din a cikin yoghurt,ya kafa kai ya shanye tana binshi da kallon kasan ido…………

Murmushi tayi ganin idonshi harya fara chanjawa,har effect din maganin ya fara aiki akansa,toh abinka da wanda yake a bukace dama…..

Dago kai yayi ya kalleta da jajayen idanunsa murya a shake yace “Shall we?”….. Daga masa kai kawai tayi tana murmushi…… 

Tashi tayi ta fara cire handgloves dinta,bin hannayenta yayi da kallo kamar ya cinyesu,ga wani bakin lalle a hannun me shegen kyau,lallen da yake tinanin tattoo ne,dan duk sanda Allah ya nufeshi da ganin  hannunta sai yaga lallen kuma same design yake gani,koda yaushe a sabonshi yake kuma,shiyasa kawai ya yanke cewa tattoo ne……. Kokarin cire hijab dinta tayi yaji kansa yayi wani mugun sarawa,sai ya alaka hakan da abinda yasha….. Sama tayi da hijab din tana gab da cirewa yayi saurin rintse ido…. Karasa cirewa tayi tana binshi da wani shu’umin kallo…… Ganin ya rufe ido tace “Yadai? open your eyes mana!”….. Shiru yayi yanajin wani abu na mishi yawo a jiki,effect din abunda yasha na kara tasiri a jikinsa,amma kuma sai ya kasa bude ido ya kalli surar da yake mararin kallo a koda yaushe……. 

Socks dinta ta cire ta karaso inda yake,shafa fuskarshi tayi ya janye hannunta da sauri jin wani irin abu da be tabaji ba,sake kai hannunta kan kirjinshi tayi,a sukwane ya kuma ture hannun…..  Hade rai tayi tace “Meye haka?”…. Da wata kalan murya yace “karki kara tabani!”…… Dage girarta daya tayi tace “Aiko dole in tabaka,ba haka kake so ba?”………….“Nidai dan Allah karki kara tabani”

“Toh bude idonka!”

“Bazan iyaba,bazan iya kallonki a haka ba”

“I’m not naked bude idonka,wannan maganin yanada karfi khaleel,I’m losing my control!” Ta fada tana fashewa da dariya…..

Jin dariyar da tayi yasa khaleel ya tsure,yaji wani tsoro ya kamashi,wannan shi ake cewa anga samu anga rashi,yana tsananin bukatarta a wannan lokacin amma inta tabasa sai yaji kamar an dora masa gaurashi a jiki……..

Jin hannayenta kawai yayi a gashin kansa,ai besan sanda ya tureta ba ya haye sama a guje,itama ta bishi a guje dariya na taso mata tana dannewa…….. 

Kumm! Yaji ya bige da bango kasancewar haryanzu idonsa a rufe yake,be gama tance inda yake ba yaji alamunta a gefensa,da sauri ya tsuguna still idonsa a rufe yace “Dan Allah dan annabi kiyi hakuri,ki kyaleni,wlh na hakura”…….

Tabe baki tayi tace “Wlh bazan hakura ba,ka gama sani cikin wannan hali kuma kace in hakura?,aiko dai saika biyamin bukatata!”….. 

Dafe goshinsa  yayi wanda yayi kullutu kasancewar bugewar da yayi,cikin muryar tashin hankali yace“toh ai kinga dai nima ina cikin yanayin amma nace na hakura,toh dan Allah kema ki hakura,duk mu hakura gaba daya”……. 

Koh kulashi batayi ba tayi dariyar mugunta ta sake sunkuyowa kanshi,jin haka yasa ya tashi a haukace ya nufi hanyar bedroom dinshi a guje,kafarsa ta bige da flower vase amma ko zafi be jiba ya shige,rufe kofa yake kokarinyi yaji ta banko,a guje ya shige toilet ya rufe kofar da sauri yana godewa Allah daya bashi ikon tserewa toilet,yanzu da ba toilet a dakin ya zeyi?🤣… 

Toh ina ze iya da wannan masifa,yana zaman zamanshi ya debo ruwan dafa kansa,a yau ya yadda fatimah zainab tafi karfinshi,Ashe tatsuniya yaketa gayawa kanshi da yake cewa dan shi aka halicceta?……,jin tana buga kofa yaji wani gumi na karyo masa,sai gashi yana kuka wiwi yana bata hakuri daga cikin toilet din,Itako dagewa tayi saiya bude yasan yadda zeyi da ita haka kawai ya bata abu tasha kuma sai ya gudu ya barta a cikin yanayi?.…. Inaaa!

Bubbuga kofar ta farayi da karfi,sai ga shi yana sakin fitsari shaaa a wando,gabadaya yaji ya nemi banzan feelings din ya rasa,ashe komai ma samun guri yake?….. Cikin muryar kuka yace“Ki tausayamin ki min rai,kiyi hakuri ki yafemin,nasan ban kyauta ba,amma dan Annabi kiyi hakuri”….. 

Bata kulashi ba tace “Ko ka bude kofar yanzu,kona ballata!”……. Jin haka kawai ya zube kasa sumamme…………

     Unique Barakancy ce😁

Back to top button