Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 17 Complete Novel

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

    SEVENTEEN📍

        “Nace ka fadamin ina ka kaishi!!!”….

Fatima zainab ta fada a tsawace….. 

Ajiyar zuciya ya sauke ganin idan be bita a hankali ba komai ze iya lalacewa,gwara ya lallabata su rabu lafiya, Afterall bashi ya dauki wanda sukayi accident din tare ba, kishine kawai yasasa fadin hakan, kuma koma wa take magana akai ze nemosa sannan ya tabbatar ya kashesa dagaske!…..

        “Relax love, bari in fadamiki iya abinda nasani”..

Ya fada yana kallon lumsassun idanuwanta masu kaifi…..

       “Actually bansan ku biyu kukayi accident din ba saida nazo likitoci suke fadamin, dana tambayi ina dayan yake sukace iyayansa sun tafi dashi, wallahil azeem abinda nasani kenan”……

Gyada kai tayi har zuciyarta ta yarda da abinda ya fada dan mutum ce ita me saurin sensing in mutum karya yake ko gaskiya yake fadi, sannan hankalinta ya kwanta tinda iyayensa ne suka tafi dashi dole zasu basa kulawa me kyau……

Batareda tace komai ba ta masa nuni dayaja motar su tafi zuciyarta sake da kudirin dake ranta, sam bata manta da mama ba da abinda  tayi niyar yiwa mama,kuma ya kamata a ce ta fara taking action tin yanzu……

         “Kaini office din daddy”…..

Ta fada bayan tagama lissafin daddy na office a wannan lokacin, zatafi san haka kuma dan tasan mama ta sakankance by now, zuwanta gidan kuma zesa ta iya gane shirinta so gwara kawai ta samesa a office a sirrince…….

Daso samu ne ya tambayeta me zatayi a office din daddy, amma ina ya riga ya bata rawarsa da tsalle tinda ya bari sabani ya shiga tsakaninsu, sai yaji yana shakkarta yau….. 

Daidai ‘Khaleel ventures and co’ yayi parking, ta fita batareda tabi ta kansa ba….. 

Harta nufi hanyar shiga company din saita dawo da sauri, luckily ta sameshi a inda tabarsa ko motsawa beyi ba……

       “Ai dama nasan zaki dawo”….

Ya fada yana smiling sannan ya miko mata niqab, batace komai ba ta karba ta daura sannan tashige ciki…… 

Direct office din daddy ta nufa, secretary dinsa tabita da kallo ganin ta nufa office din manager without permission, taso ta dakatar da ita sai taga ta mata kwarjini, tanaji tana gani tashige office din batareda ta hanata ba, addu’ar ta daya Allah yasa karta janyo mata matsala……

Da sallama ciki ciki ta murda handle din tashiga tana dage niqab dinta…..

Daddy dake zaune ya mike da sauri ganin wacce akace ta mutu tazo office dinsa, toh kodai fatalwa ce?…. A kidime cikin rawar jiki yace…..

        “Wa innahu sulaimanu wa innahu bismillahir rahmani raheem, ku kuke ganinmu bamu muke ganinku ba, Wayyo Allah ba ance kin mutu ba?”……

Wata muguwar dariya ta saki data kara ruda daddy yaji kamar ya saki fitsari tace…..

       “Ban riga na mutu ba amma ina shirin mutuwa idan baka biyamin bukatar danazo dashi ba!”…..

Daddy dafe cikinsa dayaji ya murda yayi, cikin zaro ido yace…., 

      “Innalillahi wa inna ilahi raji’un,mutum ko aljan, dan Allah kiyi hakuri ki kyaleni, mekike so?”….

Daidaita nitsuwarta tayi tana tinanin wanda ya fadama daddy ta mutu? Gashi yanzu ya ganta ya dauka fatalwa ce, dole ta mishi bayani yanzu dan yasamu nitsuwar daze fahimci abunda tazo dashi sosai…….

       “Relax daddy! Banfa mutuba, ina part din momma sanda mama ta kona part dina”……

Girgiza kai daddy yayi cikin rashin yarda yace….

      “Are you sure?”……

      “Yes tambayi abdul!”…..

Bece komai ba ya dauki wayarsa ya fara dialing number abdul daya manta when last sukayi waya dalili kuma shine yake ignoring calls din abdul, yanzu ko dole ya kirasa tinda yana bukatar tabbaci akan wannan al’amari, bayan haka ma yanata so ya kirasa guilty conscience ya hanasa……

Saida wayar ta kusa tsinkewa sannan abdul ya daga bayan yagama mamakin kiran da daddy ke masa yau……

         “Son how’re you?”….

Daga daya barin abdul da har lokacin be dena mamaki ba yace….

        “I’m good! Ina wuni”….

      “Alhamdulillah son, kazo part dina yau da daddare I want to see you, meanwhile I want to ask you a question now”…….

         “Okay, Go on”…..

         “Ba ance hafsah ta kona Fatima zainab ba?”….

          “No bata cikin part din a lokacin, bata kone ba!”…….

Wani ajiyar zuciya daddy ya sauke kana ya kashe wayar…. Sai yaji kamar anmasa albishir da gidan aljanna, ashe shiyasa befara facing consequences din mutuwarta ba? Wato dai tana raye!… Sai kuma yaji haushin kansa na rashin tambayar abdul, to inama abdul din yake? Yaga baze iya wahala ba yabi uwarsa!…..

         “I’m so happy that you’re alive daughter, ni kadai nasan irin tashin hankalin dana shiga, yanzu haka hafsah na police station, maganar nan da nake miki gobe zamu shiga court akan case din!”……

Mamaki ne ya kamata ganin yanda daddy yayi taking abun so far,ita tananan tanawa mama shiri ashe har ana chan ana hukuntata bata saniba, well Allah ne ya kamata akan ramin muguntar data gina gashi ta rufta da ita batareda wacce tayiwa tashiga ciki ba… Amma fa dukda haka bazata hakura akan kudirinta ba, dole sai ta nunawa mama iya karta sosai,.. 

        “Can I proceed with my request?”….

Fatima zainab ta fada batareda tayi magana akan case din mama ba, tinda dai yaga she’s alive ruwansa ne ya fito da mama, ruwansa ne ta cigaba da zama achan, ita bashi bane a gabanta ba…….

        “Sure! Inajinki daughter”…..

Daddy ya fada yana danne danne a wayarsa, message yake kokarin turawa abokinsa daya kasance DPO akan zezo ya dauki mama anjima, idan yazo ze masa bayani kawai so yake a fara filing bail dinta….. 

         “Inaso ka aureni!”……. 

Ta fada kai tsaye……

 Sakin wayar dake hannunsa yayi yana tinanin kunnensa ne beji daidai ba,yace…..

           “Kikace me?!!!!”….

            “Yes you heard me! Aure nakeso muyi!”….

Ta kuma fada batareda taji ko dar ba…

            “No, you must be joking daughter, khaleel din fa? Ya zaayi tsofai tsofai dana in auri kamarki, this is a joke!”……..

Daddy ya fada with an unbelievable look….

Marairaicewa tayi tace…..

        “Forget all that, dan Allah daddy ka taimaka ka aureni koda na dan wani lokaci ne”…..

Sakin baki yayi yana kallonta ganin dagaske take, hardasu dan Allah kuma? A iya saninsa da ita in zaayi mata abu ayi in baza’ayi ba she always got alternative, da wuya kaganta tana roko, curiously yace mata….

         “Why do you want me to marry you?!”….

         “Just like that! Daddy in baka aureni ba zanshiga damuwa, zan iya rasa raina idan baka aureni ba”…….

Shirune ya biyo baya na tsawon minti goma kowa da abinda yake sakawa aransa….. 

Sosai daddy yashiga tinanin mafita akan al’amarin, inya billa tachan sai yaga abin be tafi yanda yakeso ba, ganinfa dole yana bukatar shawara yasashi fadin… 

   “I’ll think about it”……

          For the fifth time tace….

        “Did you commit the crime?!”..:..

Deen dayake zaune a wani VIP cell dayake ciki shikadai ya dago ya kalli mami yana girgiza kai…

       “Tell me what transpired before the accident?”..

Kamar bazaice komai ba sai kuma yace…..

     “I was kidnapped!”…..

      “When?” Ta fada surprisingly….

      “Ranar da kika kirani kikace in bar inda nake, nace miki ai ina gida”…..

Ya fada ko a jikinsa….

        Harara ta watsa masa sannan tace…

    “Wanda beji maganar mahaifiyarsa ba ina zega daidai a rayuwarsa?, yanzu kalli abunda ka janyowa kanka dako ubanka baze wani taimakeka akai ba!”……..

Shiru yayi bece komai ba….

     “At what time exactly were you kidnapped?”

Ta sake fadin hakan ganin yayi shiru…..

      “Few minutes after I answered your call, I can’t say the time exactly”…

Batace komai ba ta daga wayarta tayi dialing wata number……

Baa dade ba aka kawo mata abinda tayi requesting, wayar Deen aka kawo mata kamar yanda ta bukata akan zatayi investigation dashi…..

Mika masa wayar tayi tace…..

      “Check your call log, I want to know the exact time!”……. 

Taso ta duba a tata wayar saidai kash Iphone ce, ita kuma Iphone  dauke past calls take musamman ita data kasance me yawan making calls saboda yanayin aikinta, shi kuma inda Allah ya taimaka Samsung yake using…… 

Karban wayarshi data kasance kirar ‘Samsung Galaxy Z Fold4New’ yayi, sannan ya shiga call log dinsa, scrolling down yayi har yazo gurin call din da yayi da ita, shiga kan call din yayi sannan ya mika mata wayar……

Karba tayi ta duba time din, har zata basa wayarsa idonta yakai kan sunan dayayi mata saving, da sauri ta dago ta kalleshi tace….

       “You must be very stupid, nice ‘this woman’?!”…

Zaro ido Deen yayi, shap yamanta haka yamata saving gashi yanzu ya mika mata ta gani…..

Kafin yace me ya nemata ya rasa a wajan, sai a lokacin wani danasani ya kamasa, betaba ganin illar yanda yayi saving sunanta ba sai a lokacin, sosai yaji wani iri ranar, yaji kuma ashirye yake ya bata hakuri gashi kuma tariga tabar wajan, shikuma bashida damar fita…. Kwanciya yayi a kan gadon yana tinanin yanda ze shawo kanta, yasan mutum dayace kadai zata iya shawo masa kanta gashi bata kasar….. 

          Zuciyarta fess tabar office din daddy, dan tariga ta kudirta aranta ko yanaso ko bayaso saiya aureta, har lissafin yanda zamansu da mama a matsayin kishoyi ze kasance tayi, kwata kwata taki bawa zuciyarta damar tinanin halin da khaleel ze shiga, ba abinda ya shafeta da momma dama…….

Yananan inda tabarsa kamar tace masa ya jirata, shiga motar tayi tace masa ya kaita gidan daddy, dan so take tayi maza ta dau abinda zata dauka tabar gidan kafin a saki mama dan bataso su hadu sai ranar da zata kawo mata kayan fadar kishiya, tariga tasan yanda zatayi da daddy ya barta ta kawo kayan….

Kicibus sukayi dasu khaleel a compound din gidan, ita tashigo su kuma sun fito zasu tafi masallaci….. 

Batace musu komai ba tashige ciki, da sauri khaleel ya bita ciki….

Sameer daya makale kamar gunki ya bisu da kallo, ko baa fadamasa ba yasan wifey din khaleel ce, aiko bazaiyi sake ba wannan karan, bibiyarta ze farayi a sirrince har yasamu burinsa ya cika…..

Smirking yayi jin wani shegen tinani ya fadomasa….

          Driving take rai a bace, ace dan da ka haifa yayi saving sunanka da wani ‘this woman’?, me hakan yake nufi? Batada mahimmanci a rayuwarsa kenan? 

Ita sai yanzu tagane Deen kamar playing dinsu yake daga ita har uban nasa, kullum sai tadinga ganin kamar ubansa ne ya janyesa shiyasa baya zuwa wajanta kwata kwata, ashe haka ubannasa shima yake tinanin ita ta janyeshi? Zatako kyaleshi har sai yagane kurunsa, sai ya tabbatar da bata da amfani a rayuwarsa, saita tabbatar masa da this woman ce ita……

Wayarta ce ta fara ringing, special ringtone din dataji ne yasata dauka da sauri……

         “Really?, okay ganinan, ina kusa dama”..

Mami ta fada tanajin kamar anyaye mata duk wata damuwarta ganin wacce ta kira…..

Nnamdi Azikiwe International Airport ta nufa tana dan kara speed din motar….. 

Hugging juna sukayi kamar wasu yara ko wacce na farin cikin ganin yar’uwarta……

        “Bansan haka nayi missing dinki ba saida naganki”….

Cewar mami da murmushi ya kasa barin fuskarta….

        “Wallahi nima haka yaya, ya Allah I never thought zanshigo Nigeria anytime soon, but anything for my saif”……

Dan bata rai mami tayi tace….

      “Dana sani na fadamiki duk wani case da akayi dashi, ashe da tuni kinzo, why’re you telling me this just now!”……

       “Sorry yaya, ai wannan ya kai azo, yanzu ya ake ciki da case din? Ina Saif din yake? And where is the girl they had accident together?”…….

 Tuno da yanda suka rabu da Deen yasa mami fadin.

      “Hmmm ki rabu da senseless son dinnan naki, the girl is still in the hospital, ya kamata muje mu dubata ma, mukarasa mota ko?”…..

Haka kuwa akayi sukasa aka daukan musu luggage dinta akasa musu a mota, shiga sukayi mami taja motar… Suka cigaba da hirarsu ta yaushe gamo…..

       “Yauwa what do you want to tell me da kikace sai nazo?”…..

Jamila ta fada abun ya tsaya mata a rai….

         “Hmmm it’s about yarinyar da sukayi accident tare da Saifuddeen, zamuje ki ganta ai, zakiga abinda nake fada”…….

        “Okay Allah ya kaimu”….. 

Ta fada tanajin kamar su tafi gurin yarinyar a lokacin…..

          “What are you doing about the case, ni nasan Saif baze iya kisa ba!”….

          “Na cire hannuna akan case din!!”….

          “Bangane kin cire hannunki ba?, kinsan me kike fada kuwa? Mubarshi a kasheshi akan abinda nidake munsan be aikata ba?”……

Haderai mami tayi tace…..

          “You heard me right! Na cire hannuna, ubansa ya dauko masa lawyer, in kuma an kashesa Allah ya jikansa!!!”……

 ~Unique Barakancy~

Back to top button