Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 10 Complete Hausa Novel

     WACECE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy 

      TEN📍

          Rikicewa Deen yayi yanaji kamar yayi karamin hauka,fadi yake tabbas da zai iya dawo da moment dinsu baya daya dawo dashi ya tsige niqab dinta,infact dayasani sace ta yayi kawai ya huta,ya killaceta har sai ta fadamasa WACECE ITA?,amma how could he be so foolish hartayi fooling dinshi haka?,shi har zuciyarsa ya dauka aljanu ne da ita,ashe he was mistaken kawai ta masa wayo ne,be manta da abunda yaji ba,be manta da laushin jikinta da haryau ya kasa tantance wani irin laushine haka kamar wacce batada kashi a jiki?…. “Ya Salam” Ya fada yana dora hannu akai,sai kuma ya koma street din da suka hadu,still be ganta ba,sai ya cigaba da tafiya a kafa batareda yasan ina ya nufa ba,saida ya shiga duka streets din dake area amma begantaba,takaici ne ya kamasa kawai ya zube a kasa a tsakiyar titi dayake irin isolated area dinnan ne da baka samun mutane sai tsiraru,lumshe ido yayi ya cigaba da tinanin inda ze ganta……… Yana cikin wannan halin yaji phone dinsa na ringing,wayar dayayi abandoning for days,yana ganin ana kiransa amma baya dagawa,yana sane kuma yaki kashewa…… ‘This Woman’ ya gani akan screen din kamar yanda ya mata saving,for the past two months tana kiransa amma baya dagawa,yau kawai yaji yanasan dauka….. Picking call din yayi yasa a hands free….

Cikin muryarta me cike da kamala tace “Assalamu alaikum Saifuddeen”….. Shiru yayi yana me jin wani sanyi a ransa,sai kawai ya amsa sallamar a zuciya…

“How’re you doing?”….

 “Ina lafiya” Ya fada kamar bayasan magana

“Inata kiranka for months kana ignoring calls din,hakan ya dace?” Ta fada da kunan rai,kanaji kasan abun na tabata….. Be kulata ba ya cigaba da sauraranta……

“Where are you now?” Ta tambayesa 

“Gida”… Ya bata amsa a gajarce 

“Baka gida saifudden!, kabar inda kake”…. Kashe wayar kawai yayi jin zata fara rainin hankalin data saba….. Cigaba da kira tayi babu kakkautawa,yana gani kuma yaki dagawa,daya gajima sai ya kashe wayar gabadaya….. 

Cigaba da zama a gurin yayi kamar me neman gafara,ya lumshe ido yana tinanin yanda ze bullowa alamarin daya damesa…….

Kamar ance ya bude ido kawai yaga mutane kusan 20 sun zagayesa ko wanne dauke da bindiga a hannunsa fuskokinsu rufe da mask,kafin ma ya motsa suka fesa masa wani abu dan sunsan tsap zece zeyi kokawa dasu and he can play very smart,a take ko abun da suka fesa masa ya sumar dashi,suka kinkimesa suka sasa a mota sukayi gaba dashi……… Ogan su ne ya dauki waya ya shiga kiran wanda yasasu aikin….. Ana daga wayar yace “Deal done!,ko a kashesa kawai boss?”…. Banji me aka ce a dayan side dinba,ogan su ya sake cewa “Your wish is my command”…….

          

    Dialing number Hajiya fatima(aminyar mahaifiyar eesha) eesha tayi tana Allah Allah ta dauka….. Sake kira tayi nan ma shiru baa dauka ba,kasa hakuri tayi ta shirya ta fita,karasawa gate tayi tana ordering bolt,batafi 5mins da tsayuwa ba blot drivern yazo,shiga tayi dan already tayi plqcing location din hajiya fatimah…….. Ko rufe motar batayiba ta fita,already tayi setting bolt dinta to pay with card so bata da case din tsayawa biyan kudi,karasawa tayi gaban gate din mansion din,knocking tayi me gadi ya bude ya laleko,ganin itace yasa be kira landline for confirmation ba,bude mata yayi ta shiga da sauri……

Da sallama ta shiga main parlour,as usual hotonsa ne ya mata welcome kamar yanda ya saba yiwa kowa welcome saboda daidai center entrance din parlourn ne,har wani lumshe ido tayi tsabar jin dadin ganin sanyin idaniyanta….. “My crush” Ta fada beneath her breath…… Mantawa da abinda ya kawota tayi tashiga bin hotonsa da kallo,tafi 10mins a haka harta farajin takun tafiya,sai a lokacin ta dago da sauri……. 

Karasowa hajiya fatimah tayi tace “Daughter kece a tafe?,welcome”…… 

Murmushi eesha tayi tace “wlh nice Mahmah,tun dazu na shigo fa,na tsaya ina bin hoton yaya da kallo,wai dan Allah yaushe ze dawo”…. 

“Soon,na fadamiki akwai wani course dayakeyi abroad ne,yana gamawa ze dawo”

“Can’t wait wlh,Allah ya dawo dashi lafiya”…

“Ameen,naganki haka by this time,thought you’re supposed to be in class by now?”….

“Yes but….,labari nazo kawo miki”…. 

“Koma menene stop joking with your education,everything can wait okay?”… Mahmah ta fada on a serious note,dan ita haka take she’s so jovial amma da taga yaro zeyi badede ba zata taka masa birki……..

“I’m sorry Mahmah,bazan sake ba Insha Allah”

“Yauwa good girl,ina jinki meya faru?”…

“It’s about that my roommate,the unknown girl,yau ta dawo”…. Ta fada cikin farinciki sosai 

“Kai masha Allah,hankali ya kwanta kenan,toh ya kukayi da ita?”….

Dariya eesha tayi tace “wlh there was a progress a big one”… Nan tashiga bata labarin yanda sukayi da fatima zainab…..

Murmushi Mahmah tayi ganin yanda eesha ke bada labarin with so much joy,sannan tace “I’m so happy for you daughter,ki cigaba dabin tactics din dana baki a sannu zaki gane wacece ita as I said earlier,meanwhile if anything come up call me on phone,karki dinga katse abubuwan ki,okay?”

“Yes mom,kuma na kiraki ma ganin baki dauka bane ya sani zuwa,I couldn’t hold it”….. 

“Ehyah I was charging my phone bansan kin kira ba,now get yourself comfortable”…. Nan ta kira laure ta landline din parlourn domin ta kawowa eesha refreshment…….. 

       

     Tinda ya kamo right hand dinta taji komai ya tsaya mata chak,abunda taji is unexplainable saidai sam ba abu me dadi takeji ba,kirjinta ne ya shiga bugawa kamar ze fado,batasan shi ba amma Allah ya bata wani baiwa,she can be very cunning and still see her way through it,duk wanda taga takasa hurting directly,sai tayi playing smart,baiwar da Allah ya mata kenan,da kuma shi ta masa wayo,ta dauka kukan data saki ze sa ya saki hannunta amma ina sai ya kamo dayan ya zamana yana rike da duka hannayenta,dabara ce ta fado mata ta fara rawar jiki kamar me aljanu,sai kawai taji ya rungumeta,it was a first time hug to her,tinda tazo duniya tin tana jaririya babu wani da namijin daya taba hugging dinta koda ko mahaifinta ne,sai yau,on this very day da wani yayi breaking rules dinta harda fara mata karatu a kunne kamar me aljanun da takeso yayi tinanin kuwa,funny enough saita kasa komai saima wani nitsuwa da taji ya sameta da tinda take a rayuwarta bata tabajin irinta ba,she can’t say she welcome the hug amma tabbas she wasn’t sad about…… Tsayawa tayi tana sauraran husky masculine sweet voice dinsa daya ke mata karatun dashi…… 

Kamar wacce aka tasa daga bacci haka taji,sai a sannan taga shashancin datayi,ace tana tsaye namiji rungume da ita a haka ta kasa taking action saima wani nitsuwa datayi,batayi tinanin sabon wayo datakeso ta masa zeyi working out ba,karatun ta kama cikin daddadar muryarta da dole mutum ya tsaya ya saurara….. Take ko taga ya nitsu ya saki nasa karatun yana sauraran nata,and at that moment she manipulated him………..

     

       Zaune yake a office dinsa,kallo daya zaka masa kasan akwai abunda yake damunsa,har dan rama yayi a wannan kwanakin,he has never been this bothered all his life,ga ayyuka sun balakin masa yawa shiyasa ko fita nan da chan baya iyawa,sai abubuwan suka taru suka masa yawa,gashi kiran duniya yayiwa khaleel amma yaki dagawa,a rana saiya kira khaleel kusan sau 30 amma shiru baa picking,ya rasa waze gayawa damuwarsa yaji sanyi a ransa,Deen dayake tinanin ze iya gayawa shima tin jiya yake kiran wayarsa baya dagawa…. Gabadaya dai abun duniya ya ishe Sameer….

Ganin zaman fa baze fisshesa ba yasa shi mikewa,ture duk wani aiki dake gabansa yayi ya fita… Motarsa ya shiga ya nufi gidan khaleel…….. 

Parking yayi a daidai cottage din khaleel,fita yayi daga motar ya nufi entrance din gidan,dogo ne sosai sameer,bashida jiki sosai amma yana da broad chest,kyakkywane san kowa kin wanda ya rasa,duk kyawunsa amma be kama kafar khaleel ba…..

Yafi 5mins yana knocking amma shiru ba amsa,hakanne yasa ya murda kofar,luckily ko ya sameta a bude…… Shiga yayi yana bin falon da kallo,ganin ba kowa yasashi karasawa sama ya nufi bedroom din khaleel….. Murda kofar kawai yayi ya shiga daidai fitowar khaleel daga wanka,da sauri khaleel ya koma cikin bathroom din a guje thinking fatima zainab ce ta dawo😹…… Mamaki ne ya kama Sameer ya daga murya yace “Man meye na guduwa kamar kaga dodo”……. Jin muryar sameer yasasa fitowa da sauri,yace “kai wallahi na dauka dodon ne”….

Fashewa da dariya sameer yayi yace“Ikon Allah akwai dodo a gidannan dama?,kai amma ka bada maza wallahi,jifa yanda ka zura a guje kamar mace”…

Karasowa inda sameer yake yayi yana fadin “bazaka kane bane wlh,kaidai kawai abar kaza cikin gashinta”… A ranshi ko cewa yake ai koda kudi bawanda zeji wannan labarin,dan shi kansa yasan ya tafka abun kunya……

“Kai ni duk bama wannan ba,I have a very serious case,before then meyasa baka picking calls dina?” Sameer ya tambayi khaleel yana zama bakin gado…..

“Wallahi bansan inda na wurga wayar bane,nima na dan shiga wani serious case ne har na batar da wayar bansani ba,amma dai yanzu Alhamdulillah everything is alright”……

“Ah toh masha Allah,ya kamata dai kayi tracking wayarka kodan hotline dinka dake ciki”

“Hakane,I’ll do that today Insha Allah,wayarma tana gidan nan nasani”…..

“Well let’s get back to issues din daya kawoni”

“Ina jinka” khaleel ya fada yana nodding….

“I saw a green snake in this house”….

Zaro ido khaleel yayi yace “Green snake kuma?”…

“Yes her eyes are so gorgeous,banga fuskarta ba amma nasan tabbas kyawunta me tada fitina ne,meanwhile she’s beautiful and wicked,daga gani kuma fitsararriya ce,can you believe har marina tayi kuma nakasa uttering even a word?,this is why I called her a green snake”…… 

Ai khaleel ji yayi gabansa ya fadi,karde karde,karfa ace Fatima zainab ce Sameer ya rikice haka akanta,amma sai ya daure yace “wai kana nufin a gidannan ka ganta,can you describe her?”

“Told you I only saw her gorgeous eyes,she’s all covered fa,harda hand gloves wlh”

“Kace she’s all covered toh how did you see her eyes?”……

“I mistakenly hit her shades,ashe da rabon zanga those attractive eyes”…..

Wani abu ne ya daki zuciyar khaleel ganin in ya cigaba da biyewa sameer zai tada mishi da ciwo ne kawai,hade rai yayi yace “Enough of all the blabs!,she’s my wifey and she belongs to me alone!,bazan boye maka ba sameer banji dadin haduwarka da wifey ba,na dade ina tattalinta da boyeta gudin kar wani ya ganta,kai kanka ka sani,amma tinda ka ganta zan baka shawara,you have to just assume baka gantaba,and my wife shouldn’t be your serious case,ka fahimta?…..

“Dakata mallam are you threatening me or what?”

“Duk yanda ka dauka kaika san dan babu abinda bazan iyayi a kanta ba wlh,she’s mine or nobody’s,wlh ko bazan sameta ba bazan yarda wani ya sameta ba kaji na fadamaka!” Khaleel ya fada a tsawace 

“Toh wlh baka isa ba tinda kai ba ubana bane da zakana threatening dina haka,kuma idan nace ina sonta you can’t do anything about it,let me even make it clear to you;a da so nake kawai nasan wacece ita amma yanzu sonta nima nake,mu zuba ni dakai muga wanda zeyi winnng game din,just watch and see!”…… Sameer ya fada yana fita daga dakin rai a bace,sauka kasa yayi ya fita daga gidan a fusace,shiga motarsa yayi ya shiga dialing number Deen,dan shi kadai ze gayawa wannan abun zuciyarsa tayi sanyi,yasan kuma Deen zeyi supporting dinsa a wannan game din tinda ba wani shiri sukeyi da khaleel ba……….

Back to top button