Uncategorized

Tubali Book 3 Page 5 Complete Novel

 

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

Ya salam kusan gaba ɗaya falon ɗibkewa da kuka sukayi.

Shi kuwa Rayyern kukan yakeyi har yana jin kamar kanshi zai buga, cikin tsananin tashin hankali ya tallabo kanta ganin yadda take kuka tuni idanunta sun kumbura sunyi jazir.

Hancinta yayi ja, numfashin ta sai korar juna yakeyi, hakan ne yasa ya jawota jikinsa ya ruggumeta da samun dai-dai ton numfashin ta.

Cikin tsananin tashin hankali Baba Mauɗo ya fara maimaita.

“innalillahi wa innailaihi raji’un Hasbunallahiwani’imanwakil”.

Hakan yasa suma kan suka fara maimaita hakan.

Wanda a take Allah ya fara sauƙo musu da sassauci cikin zuƙatansu.

Sai kuma duk suka fara sauƙe ajiyan zuciya amman banda Jannart da har yanzu maimaita innalillahi wa innailaihi raji’un takeyi tana kuma mai ci gaba da kuka.

Cikin sauƙe ajiyan zuciya Barrister Kabeer yace.

“Ki gafarceni Jannart ki dena kuka, na yi iya iyawata dan ganin komai ya tafi dai-dai.”

Shi kuwa Rayyern cikin sanyi yace.

“Barrister batar tayi kuka! Idan batayi kukaba a yau sai yaushe zatayi kuka, inama ace labarinki yazo kamar namu Janna ace iyayenki na raye, amman kash haka bata kasance ba.

Kiyi kukan rashinsu da kuma ɓoye miki da akayi, amman kada kiyi kukan maraici.

Nayi miki al’ƙawari zan cike miki dukkan gurbinsu.

Zan sama miki farin ciki.

Mammyn na zata zama madadin Mamanki Baba Mauɗo zai zama Madadin babanki.

Kisa a ranki Zaiton da Riyyam-nsra sune ƙanneki.

Ga Hafeez da Hafiza ga Abba Kabir ɗinki.”

Shiru Abba da Barrister Kabeer sukayi suna mai kallonsu da sauraron kalamansa.

Baba Mauɗo kuwa da Mammy kai suka jinjina mata alamun eh hakane.

Ramadan da Riyyam-nsra ba cikin tsananin tausayinta sukace.

“My Aunty kiyi haƙuri, ki dena kuka in Sha Allah bazamu sake barin kiyi kukaba”.

Shessheƙan kukan ta fara ja da ƙarfi.

Sai dai ina abin yaci tura.

Haka yasa Rayyarn kuma ruggume ta, Allah ya sani ya mance ma a cikin mutane suke, yana kuka yace.

“Janna ki kalleni in Sha Allah zan zame miki Nagartaccen miji mai jinƙai, tausayi, kulawa, sadakarwa, zan zame miki bongo abin jingina, kuma garkuwa ga duk wata cutarwa da izinin Allah.”

Kai kawai ta fara gyaɗa masa yana kwato numfashin ta, amman ina, cak numfashin ya tsaya ta lafe jikinsa a sume.

Cikin tashin hankali ya ɗan janye jikinsa, tare da jera mata kira.

Ramadan ne ya miƙa da sauri yana cewa.

“Ya salam Hamma Rayyern suma tayi fa”.

Gaba ɗaya hankainsu ya tashi, hakan ne yasa duk sukayi kanta.

Mammy ce tasa hannu ta amsheta daga jikinsa sabida ganin yadda gaba ɗaya jikinsa yake karkarwa, ya kasayin komai.

Aunty Dijat ce ta miƙa da sauri ruwa ta kuma ɗauki wa mai sanyi.

Tana miƙa musu, cikin sauri Mamy ta yayyafa mata a fuska an kuwa yi Sa’a ta farfaɗo da wani sabon kuka.

Ruggume ta Mammy tayi tana mai ɗan shafa bayanta da tausar zuciyarta da sanyaya kalamai.

Jin kiran sallan mangarib da akayi ne yasa, kab mazan sauƙe numfarfashi tare da miƙewa, suka firfita haraban gidan al’wala sukayi kana kab suka nufi masallaci.

Matan kuwa, cikin sanyi Mammy ta miƙa tare da kamo hannun Jannart daketa shessheƙa ta miƙar da  ita.

Mamy ce ta nuna mata ɗakin.

Sai kuma Aunty Dijat da Zaiton subabi bayanta.

Cikin sanyi da lallashi Mammy ta kalleta lokacin da suka shiga cikin ɗakin cikin tausasawa tace.

“Jannart kiyi haƙuri kinji ki dena kuka, ki shiga bathroom ki watsa ruwan sanyi, zakiji sanyi a zuciyarka.

Sannan kiyi al’wala kizo kiyi salla, a karo na forko a rayuwarki, ki ɗaga hannunki, kiyiwa iyayenki addu’a shine abinda mahaifiyarki ta roƙa, kuma shine zai sasu farin ciki ba kukanki ba.

Kana kiyi sujjada ki godewa Allah da ya hana magautanka samun nasara a kanki ya rayaki har kika san gsky”.

Cikin sanyi ta gyaɗa mata kai.

Ganin haka yasa ta tallabeta suka shiga bathroom din.

Kana ta fito tare da ja mata ƙofar.

Su kuwa su Aunty Dijat da Zaiton main falon suka koma, a bathroom ɗin ciki sukayi al’wala, kana Mammy ma nan ta fito, al’walan.

Mamy kuwa sallayu ta shisshin fiɗa musu, kana duk suka kabbarta sallah.

Acan masallacin cikin gidan kuwa suna idar da salla, Baba Mauɗo yayi ta jerowa su Barrister Abdulkareem addu’o’in neman musu gafara da samun ni’imantaccen makwanci.

Ana shafawa Rayyern ya sulale ya fito ya nufi cikin gida.

Ido ya ɗan zuba musu ganin duk suna cikin falon, ganin bai ganta bane yasashi.

Wuce ɗakinta.

Jiyo shessheƙan kukanta a bathroom ne yasashi kutsa kai ciki.

Cikin bathtub dake cike da ruwa ya hangota tana zaune cikin sa babu komai a jikinta sai, kuka takeyi har jikinta na rawa.

Da sauri ya iso inda take, ita kuwa jin motsin mutum ne yasata ɗago kanta, ganin shine yasata, yin saurin matsowa bakin bathtub ɗin, hannunta tasa ta riƙe sawunsa tana daga ciki.

Kanta ta manna kan sawunsa, cikin tsananin rauni da kuka tace.

“Naan Zuciyata, ta ƙuntata, ruhina ya girgiza a sanadin rashin muradin zuciyata Naan bani da kowa duniya”.

Da sauri ya zauna bakin bathtub ɗin kanta ya manna da cinyarsa cikin sanyi yace.

“Kina dani  Jannart, ki dena cewa haka, kina dami, kuma zamu samar da zuriya maigaɗi, zanyi miki ciki ki haifa mana yara da yawa, gani ga yaranmu ga Mammy ga Mamy ga  Abba ga Baba Mauɗo gasu Abba Kabeer ga Zaiton kinaji Aunty Dijat da Mamy har sunayi mana kallon mai ciki, da ace haka zai tabbata da nayi farin ciki”.

Cikin sanyi ta fara sauƙe ajiyan zuciya jin yadda yake ɗan watsa mata ruwan sanyin a jikinta.

Ganin tayi shirune, yasa ya tasheta, ya zubda ruwan bathrobe ya zira mata, kana yasa tayi al’wala kana suka fito.

Shi ya taimaka mata ta, shirya kana yasa mata hijjabi.

Ta kabbarta sallah.

Shi kuwa falon ya fito.

Nan ya samu su Mammy na zaune, da alamun jira sukeyi isha tayi suyi salla kafin su tashi.

Shi juyowa yayi ya kalli Ramadan daya leƙo tare da cewa.

“Hamma Rayyern Abba yace kazo, muyi salla isha ta ƙarato”.

To yace kana yabi bayansa, so yake yayi sallan ya rabu da kowa yazo ya kula da Jannansa.

Bayan an idar da salla ne.

Mamy ta kai musu abinci falon Jannart.

Kana Mammy kuwa ta shiga ta fito da ita.

Su Abba kuwa a babban falon suka shigo baki ɗayansu, a nan inda Mamy da Zaiton suka jera musu abinci suka zauna.

Gaba ɗayansu babu wanda ya ci wani abincin kirki.

Ita kam ma Jannart kuka ta sawa Mammy data matsa mata taci, abinci sai Mamy ce ta tsoyayo kunu tare da miƙawa Mammy tace.

“Ai inaga gaba ɗaya ma cikin yanata cin abinci, dan tunda suka dawo in Banda kunu batasha sa wani abu a bakintaba sai ɗazune ma ta ɗanci a logoi alogoi.”

Cike da tsananin tarin farin ciki Mammy tace.

“Masha Allah! Masha Allah!! Masha Allah!!! Alhamdulillah! Allah ya inƙanta ya rabaku lfy”.

Sunkuyar da kai tayi tana mai tsiyayar da hawaye, ita kuwa Mammy miƙa mata cup ɗin tayi.

Amsa tayi tana mai zubda hawaye, sun sa mata son haihuwa musamman yadda Naan yake nuna mata in cikine zaiyi farin ciki da yadda ya nuna mata da haihuwa ne kawai zasu faɗaɗa ahlinsu.

A hankali ta kurbi kunun sabida  yadda  Aunty Dijat ke haɗata da Allah tasha

kurɓa takeyi hawayen na zubar mata.

Su kuma haka suka ɗan tsastsakali abincin sama-sama.

Acan falo ma haka mazanma basu wani ci abincin kirkiba.

Rayyern ya fara tashi ya haura sama sabida so yake yaje ya watsa ruwa.

Kafin nan sun watse a falon.

Ai kuwa tayarsa keda wuya.

Barrister Kabeer ya miƙe tare da cewa.

“To mu zamu tafi Hafeez kaje maza kace Mamanka da Aunty Jannart su fito mu tafi”.

Kai Ramadan da Riyyam-nsra suka ɗago tare da zuba mishi idanu tare da cewa.

“Barrister da Aunty Jannart Kuma?”.

Da sauri Baba Mauɗo ya ɗaga musu hannu tare da cewa.

“Wayasa bakinku”.

Yayi mgnar da alamun shima Abba da Barrister Kabeer sun sanar dashi yadda auren ya kasance.

Dr Sajo da Alhaji Bala Tambari kuwa kai  suka jinjina  tare da haɗa baki wurin cewa.

“Gsky ni ban goyi bayan raba yarannan cikin wannan yanayin da suke cikiba”.

Abban Rayyern ne ya ɗan jujjuya musu kai tare da cewa.

“Dan Allah kada kuce komai”.

Hakane yasa sukayi shiru.

Kana suka miƙe tare da yin sallama dasu suka tafi.

Dai-dai lokacin kuma Aunty Dijat da Jannart da Hafiza da Hafeez suka fito.

Wanda a tunaninsu Mamy Barrister Kabeer ya kiratane dan yayi mata nasiha shiyasa basu san me ake ciki ba.

Suna fitowa Barrister Kabeer yasa su Hafeez a gaba,

Abban Rayyern kuwa cikin tausasawa yace.

“Jannart kije wurin Abbanki akwai mgnar da zakuyi, gobe da safe zanzo”.

Cikin sanyi tace.

“Toh Abba”. Kana tabi bayan Aunty Dijat, ta rasa wanne irin yanayi takeji.

Su kuwa su Baba Mauɗo rakasu sukayi har waje.

A tare Dr Sajo da Alhaji Bala Tambari, da Barrister Kabeer suka fita gidan.

Suna fita Abba da Baba Mauɗo kuwa, suka wuce ɗakin Baba Mauɗo suka zauna.

Su Mamy kuwa jin shiru-shiru ne yasa suka, fito falo.

Ganin basa nanne yasa suka tambaya ina Jannart cikin sauri Riyyam-nsra yace.

“Uhumm su Abba sun sa, tabi Barrister Kabeer.”

Cike da mamaki

Sukace.

“Meyasa”. Kai suka jinjina musu alamun suma basu saniba.

Kai Mamy ta jinjina tare da zama a ƙasa gaban Mammy tace.

“Uhummm tabbas akwai wata matsala dan tun jiya naga alamun hakan amman ni kaina bansan menene ba, amman in sha Allah zan bincika mana a daren nan”.

Ita kuwa Mammy cikin sanyi tace.

“Toh ko dai ɗan naki yayi wani laifin ne”.

Kai Mamy ta jinjina kana ta juyo ta kalli Ramadan tare da cewa.

“Kaima ina zaton akwai matsala a lamarin aurenka nan da kyar in ba ɗaga bikin akayi ba”.

Cikin wani irin zabura Ramadan ya zazzaro idanu waje tare da cewa.

“Innalillahi wa innailaihi raji’un dan Allah Mamy kada ki sake faɗan haka wlh zan iya suma”.

Cikin tsare fuska Mammy tace.

“Tafi daga nan ba kunya”.

Jin hakane yasa ma kawai ya haura sama, yayinda Riyyam-nsra yabo bayansa.

Ɗakin Ramadan ɗin suka shiga, yana mai kiran Raihanansa.

A can side ɗin Baba Mauɗo kuwa, cikin sanyi Abba yace.

“Daga yau zan dawo kwana nan Alhaji wanda akayi a bayama rashin sani ne”.

Cikin dariya Baba Mauɗo yace.

“Ni tashi ka barmin ɗakina, kaje kaji da rigimar Ramadan in yaji an ɗaga auremsa.

Kafin gobe kuma muga iya tsaurin ido da rashin kunyar Rayyanu”.

Kamar da wasa fa ma, amman ina fir.

Abba yaƙi komawa cikin gida. Saida Baba Mauɗo ya ɓata fuska yayi da gaske kafin Abba ya mike ya nufi cikin gidan

Jannart kuwa suna shiga cikin mota, Aunty Dijat ta ɗan kalleta jin yadda hannunta ɗaya taɓata yayi zafi.

Cikin kula tace.

“Jannart Zazzaɓi ko?”.

Kai ta jujjuya mata alamun itama bata saniba.

A haka dai suka isa gida.

Suna shiga Su Hafeez suka kwanta bisa kujeru, shi kuwa Barrister Kabeer, zama yayi tare da cewa.

“Dijat ki shiga kitchen ki ɗan dafa mata ko indomie ne taci”.

Jin haka yasa tana ajiye mayafinta ta shiga kitchen.

Ita kuwa Jannart kwanciya tayi bisa kujerar dake gefen Barrister Kabeer dan zazzaɓin takeji sosai.

Shi kuwa cikin nitsuwa yaci gaba da tausar zuciyarta.

Rayyern kuwa cikin sanyi yake tako steps din yana mai sauƙe ajiyan zuciya na kukan da yayi tayi,

Yayinda jikinsa kuma keta baza ƙamshi na musamman.

A hankali ya iso ɗan tsaya tsakiyar falon.

Kai ya ɗan sunkuyar ganin yadda Mamy da Mammy suka zuba mishi idanu.

Cikin sanyi yace.

“Mammy bakuyi bacciba”.

Kai ta jinjina masa, Mamy kuwa cikin sanyi tace.

“Ai yau kam kwanan zaune zamuyi, na yaushe gamo”.

Kai ya ɗan jinjina kana cikin wasiyya ya nufi kitchen.

Fridge ya buɗe Chocolate nasa ya ɗan ɗiba, kana yana fitowa ya nufi falon Jannart ɗin.

Su kuwa da  ido suka rakasa.

A can gidan Barrister Kabeer kuwa, da sauri Jannart ta tashi zaune lokacin da Aunty Dijat ta ajiye mata plate ɗin indomie da kwai a gabanta, tururin su ya bugeta.

A gigice ta nufi Bathroom dake cikin falon, tana maiyi wani irin masifeffen kakari da yunƙurin amai,

Da sassarfa Aunty Dijat tabi bayanta.

Yayinda shi kuwa Barrister Kabeer cike da mamaki yake cewa.

“Subahallahi lfy kuwa”.

Ina babu mai bashi amsa, haka yasa ya rufa musu baya.

Tuni su Hafeez kuwa sunyi bacci.

Ita kuwa Jannart amai take cikin tsananin azaba, ga wani irin fitinennen zazzabin da takeji kamar zai kasheta.

Amai ɗin takeyi a gigice,

Wani irin duhune da jiri suka rufeta a tare,

haka yasa ta fita hayyacinta, sabida abubuwan sunyi mata yawa a wunin yauwa.

Da sauri Barrister Kabeer ya tallabeta tare da ɗagota cak, cikin kiɗima ya juya ya nufi waje yana cewa.

“Subahanallahi Dijat zauna da yara bari in kaita adibiti”.

Cikin tashin hankali Aunty Dijat tace.

“Ya ilahi Abban Hafeez muje tare”.

Yadda yaga har yanzu tana kakarin amai ɗin ne yasashi ƙara gudu.

Bayan mota yasata, kana ya shiga gaba da yana  labubo car key ɗin a aljihunsa.

Kafinma Aunty Dijat ta idosu har yaja motar.

Mai gadi kuma ya buɗe mishi gate yaja ya tafi.

Dole Aunty Dijat ta koma cikin gida.

Asibitin Dr Sajo ya wuce da ita, cikin Sa’a kuwa ya samu Dr Sajon dama asibitin ya nufa ba gidaba.

Amsarta akayi cikin gaggawa tare da bata taimakon gaggawan da suka samu aman nata ya tsaya,

Sannan aka farayi mata dukkan gwaje-gwaje da suka dace.

Da ɗan saurinsa ya fito falon yana cewa.

“Mamy ina take ne?”.

Cikin kauda kai Mamy tace.

“Waye ɗin?”.

Da sauri yace.

“Jannart mana, na duba bata falo a bedroom nasu Zaiton kawai na samu tana bacci har bathroom na duba bata nan, Mamy ina take?”.

Da sauri duk suka juyo suka kalli ƙofar falon jin muryar Abba na cewa.

“Wa’adin ne ai ya cika, ba dama wata takwas ko shekara ɗaya kayi yarjejeniya da Barrister Kabeer cewa zaka sakar masa yarsaba, dan baka sonta ba kuma zaka taɓa sontaba dan haka yanzu sai ka rubuta takardar sakinta ka bani in kai mishi dan shi kam ya tafi da ƴarsa”.

Kamar sauƙar aradu haka yaji kalaman Abba.

Lokacin ɗaya suka ɗunguza mishi lissafi da nitsuwa, cikin yanayin diriricewa yace.

“Ni kuma?”.

Ido Abba ya zuba mishi, tare da tsareshi dasu.

Cikin tsananin kiɗima yaji wata zufa ta keto masa, murya a sarƙafe yace.

“Abba”.

Da sauri Abba ya daka masa tsawar da tashi zamewa ya zauna ƙasa da ɓas, hannunsa duka biyu yasa ya dafe kansa.

Shi kuwa Abba gefen Mammy yaje ya zauna, a ƙasa kusa da matarsa, sunkuyar da kai yayi a matsayinsa na karami a kanta, cikin nitsuwa ya kora mata dukkan bayanan da Barrister Kabeer yayi masa.

Ita kanta Mamy jikinta yayi sanyi.

Mammy kuwa Kai kawai ta jinjina ta miƙa ta wuce ɗaki inda Zaiton take ba tare da tayi mgn ba.

Shima Abba miƙewa yayi ya tafi.

Yana mai cewa Mamy ta biyoshi.

Haka ta miƙe ta bishi.

Ya zama sunyiwa Dr Rayyern watsiyar dila.

Wani irin tashin hankali yakeji mai gigitarwa.

Cikin fargaba ya miƙe da sauri ya haura sama.

Wayarsa ya ɗauka ya fara dannawa Barrister Kabeer Kira, sai dai wayar na shiga ba’a ɗagawa.

Sabida ya bar wayar a falon inda ya tashi.

A can asibiti kuwa cikin sauƙe numfashi Dr Sajo ya kalli Barrister Kabeer dake zaune a gabansa cikin murmushi yace.

“Congrat Barrister ka kusa samun jika nan da watanni takwas masu zuwa, dan Jannart nada cikene kimanin kwana ashirin da biyar zuwa wata ɗaya”.

Cikin wani irin mamaki da tarin al’ajabi Barrister Kabeer ya miƙe tsaye.

A gidan Barrister Kabeer kuwa, da sauri Aunty Dijat ta amsa kiran Rayyern daketa shiga wayar Barrister.

Shi kuwa Rayyern yana jin an ɗaga yace.

“Why! Why!! Whyyyyyyyyyy!? Barrister meyasa zakayi min haka”.

Da sauri Aunty Dijat tace.

“Rayyern ba shi bane,.”

Cikin sauri yace.

“Ina yake”.

“Ya  tafi Asibitin SAJOS HOSPITAL din Dr Sajo ya kai Jannart bata da lfy, sai amai takeyi kamar zata suma”.

Cikin tsananin tashin hankali ya katse kiran.

Tare da zaran car key ɗinsa.

 Gudu-gudu yake sauƙowa har yana taka steps din bibbiyu.

Babu kowa a falon haka yasa ya fita.

Shiga motar yayi yana danna Ari horn a gigice hakane yasa ya wangale masa gate.

Kai tsaye SAJOS HOSPITAL ɗin ya wuce.

Yana isa yayi parking kana ya kusa kai cikin asibitin.

Kasan cewar lokacin sha biyu tayi, shiyasa babu zirga-zirgan mutane.

Kai tsaye ya wuce Office din Dr Sajo bisa jagorancin wata Nurse.

Suma isa wurin tace masa.

“Nanne”.

Kai ya jinjina mata kana ya kutsa kansa ciki.

Cike da tashin hankali ya  kalli Barrister Kabeer dake ɗagowa daga sujjadar da yaji.

Yana ganinsa yace.

“Barrister ina matata?”.

Cikin tsare  fuska Barrister yace.

“Matarka adaba ai yanzu kam ɗiyatace, duk da kaci amanata ka karya alƙawarin da kayi min ka rabata da budurcinta”.

Cikin mamaki yace.

“Wallahi ni banyi mata komaiba ban rabata da budurcinta ba,  amman ina son mamata dan Allah mu janye wanne sharadin amman wallahi tallahi billahil azeem ni ban kusancetaba ban keta budurcinta ba”.

Cikin tsananin tashin hankali da tsoro Dr Sajo ya miƙa tsaye tare da cewa.

“Innalillahi wa innailaihi raji’un Rayyern me kake faɗa haka kamar tatsuniya bayan Jannart har ciki take dashi na wata ɗaya sannan kake ratsewa kaga ga shaidar gwajin da mukayi mata”.

Ya ƙare mgnar yana juyo masa takardar sikainin da sukayi mata.

Cikin wani irin yanayi mai wuyar ganewa ya fara jinjina kansa tare da cewa.

“Wallahi na rantse da girman zatin ubangijin ban kusancetaba ban rabata da budurcinta”.

Cikin tsananin tashin, hankali, tsoro, kiɗima, gigita, Barrister Kabeer yace.

“Kai dan Allah ka dena raina min hankali da rantsewu to cikin na uban nawaye kenan?”.

Cikin zubda hawaye ya fara jujjuya kai murya a raunace cikin gaskata wa yace.

“Na rantse da Allah da Manzonsa da kujerar al’arshi ban kusancetaba kuma cikin naw…!

Tubali Book 3 Page 1

Tubali Book 3 Page 2

Tubali Book 3 Page 3

Tubali Book 3 Page 4

Tubali Book 3 Page 5

Ciki kuma nawane kuma halatta ce”.

Cikin zafin  Barrister ya kuma daka mishi tsawa a hargitse yace.

“Kai tafi daga nan, ko a garin gaɓa-gaɓa ayi haka, yoh in ba mahaukaci ba wa zai ji wannan tatsuniyar taka ya yarda.

Kaida bakinka kace kayi min alƙawarin bazaka kusanceta ba, sannan kaje kayiwa yarinya ciki yanzu kazo kana wani cewa wai kai baka rabata da budurcinta ba, kuma ciki nakane”.

Cikin haƙiƙanin gsky Rayyern yace.

“Haba Barrister ni yarone koni mahaukacine da zanyi ta rantse maka a kan ƙarya.

Da Allah fa na rantse maka, wlh wlh wlh ban kusancetaba, ban rabata da budurcinta ba, kana ciki kuma nawane, domin ni nasan wacece Jannart nasan matata tana nan a cikekkiyar budurwa, kana amintacciya ce a gareni. Batun wani tsohon alƙawarin kuma ai yarintace tasa nayishi a bayan ma”

Toh fa mgna ta ɗau zafi.

Kowa ya kafe a kan gskyarsa.

Shi kuwa Dr Sajo komawa yayi ya zauna yana sauƙe numfashi domin yafi yarda da Rayyern sai dai ya bashi dariya da kalmar wai yarintace to acikin watanni takwas ɗin kenan ya girma.

Shi kuwa Barrister cikin asalin takaici da baƙin ciki yace.

“Rayyern yarinta ko”.

Da sauri ya gyaɗa masa kai alamar eh.

Shi kuwa Barrister cigaba yayi da ceea.

“To yanzu ka girma kenan.

baka kyauta minba, tunda kasan sharaɗinmu meyasa dakaji ka girman zaka meda min yata bazawara da sai ka barni in aura mata ɗan uwanta Azeez nasan shi yana sonta”.

A haukace Rayyern yace.

“Kai Barrister kace duk abinda kaga dama, ai koda na kusanceta matatace halaliyata sadaki na biya.

Kuma da aurena a kanta kake wani cewa zaka aura mata wani.

To mugani muga yadda za’ayi a aura mata wani

Magwaji ya gwoda ya mugani”.

Cikin fesar da numfashi Barrister yace.

“Ka manta sharaɗinmu ne da alkawarin daka ɗaukarmin”.

A fusace yace.

“Sharaɗin banza sharaɗin wofi, ni babu ruwana da wani makareren sharaɗi Mata matatace ciki kuma nawane, kuma wlh duk abinda ya samu matata da cikina za’a ga bala’i mai kai da ƙafa da fiffige  yaseen ina son matata”.

Cikin sanyi Dr Sajo ya kamo hannun Rayyern dake wani rawa da karkarwa ya ajiyeshi bisa kujera.

Kana ya kamo hannun Barrister shina ya ajiyeshi.

Kallon kallo sukeyiwa juna.

Cikin nitsuwa Dr Sajo yace.

“Dr Rayyern mesa kace ciki nakane? Bayan kuma ka rantse baka kusancetaba”.

Cikin tarin fargabar ƙudurin daya gano Abbansa da Barrister Kabeer suke dashi yace.

“Dr  in shi ba likita bane bai san cewa a duniya babu wani abu daya kai sperm sauri ba, to ka gaya mishi yasan da haka.

Jannart dai matatace kana cikin shaidun ɗaurin aurenmu.

Na sani nayi masa alƙawarin bazan rabata da budurcinta ba a wancan lokaci da nakega zan iya rayuwa babu mace.

To amman ai banyi mishi alƙawarin bazanyi wasa da ita, inji ɗumin jikinta ba,

Wallahi ban kusancetaba tana nan da budurcinta ko daren shekaran jiya na tabbatar da haka.

So amman lokuta da dama muna kasancewa tare da ita a matsayin mata da miji.

Ɗaki ɗaya gado ɗaya filo ɗaya, manne da juna.

A lukuta ma bambanta na samu nitsuwa a jikinta, wanda nakeda ilimin irin wannan kan iya samar da ciki.

Domin kai ka sani ciki saurin shiga ne dashi. Banyi kokonton cikintaba.

Na kuma yi imani cikin nawane halattacce, domin haƙiƙa sperm na kan iya wucewa jikinta da gudurin kasheta bamgiji.

Kuma Alhamdulillah wannan ma ya isheka ishara Barrister, nasan nayi kuskuren furuci a baya, amman haka ba yana nufin ni Rayyern wai zan saki matata bane”.

Murmushi mai cike da mamakin tsaurin idon  Rayyern. Dr Sajo yayi tare da jinjina kai tabbas mgnar sa gsky ne a duniya  sperp yana cikin abubuwan da sukeda masifar sauri.

Kana a duk sanda na miji ya kamo, yana kawowane da kwayayen haihuwa dubu, masu tsinin baki, yayinda na mace ɗaya ne.

Na macen zaiyi ta fafutuka har ya samu yayi karo da a bokin rayuwa su haɗu su liƙe, su zama ciki.

Tabbas wannan amintaccen bincikene da likitocin duniya suka yarda dashi.

Yana kuma faruwa a lokuta da dama, har a kan balagazzun ƴan mata masu buɗawa ƙazaman samarinsu ƙafa wai da nufin ai wasa kawai zasuyi baza’a shigaba.

Daga wannan wasan kuwa ubangiji keyin ikonsa, sai kaji ciki ya samu.

*Hattara gareku yan mata, dama zaurawa wlh ciki yana samuwa a haka, kuji tsoron Allah*

Cikin sanyi ya kalli Barrister Kabeer da yake murtuƙe da fuska kana a hankali yace.

“Barrister wlh kamar yadda ya gaya maka, ciki na shiga a wannan yanayi, muddin dai yayi inzali a kanta, har ta kai ga yana jin ɗuminta, kuma haka ba yana nufin ya ratsa budurcinta bane, ka yarda dani wlh tallahi haka na faruwa da iginin ubangiji”.

Wani dogon numfashi Barrister Kabeer ya sauƙe da ƙarfi tare da lumshe idanunsa.

Shi kuwa Rayyern a hankali ya sassauta murya cikin nitsuwarsa data fara dawowa yace.

“Dan Allah Barrister ina Jannart take, ina buƙatar kusa dani”.

Cikin haɗe fuska Barrister ya miƙe tsaye tare da cewa.

“Yarinyar da kace baka sonta ka tssneta bazaka kuma taɓa sontaba, ta yaya, zan bar marainiyar Allah a hannunka bayan nasan ba sonta kakeyi ba, ai wannan bazai taɓa yiwuwa ba”.

Yana faɗin haka ya fice 

Shi kuwa Rayyern hannu biyu yasa ya dafe kansa tare da cewa.

“Innalillahi wa innailaihi raji’un, dan Dr ka taimaka min, wlh Barrister zai azabtar damu, yasa Abba nama yana fushi dani, dan Allah ka taimaka min a matsayinka na waliyin aurenta gareni”.

Cikin sauƙe numfashi Dr Sajo yace.

“Nayi ƙoƙarin hakan tun kafin ka sani, to amman Barrister Kabeer da Abbanka sunƙi su saurareni, amman yanzu kayi haƙuri ka koma gida, muga abinda gobe zatayi”.

Da sauri yace.

“Dr ya zanyi in koma gida bayan Jannart bata tare dani, kuma batada lfy, ta yaya zan samu nitsuwa”.

Ya ƙare mgnar kamar zaiyi kuka.

Shi kuwa Dr Sajo cikin son kwantar masa da hankaki yace.

“Rayyern kabi mgnata ka koma gida, kaje kaji da iyayenka, ni kuwa nayi maka alƙawarin zan ji da Barrister Kabeer, ko dan cikin nan da Allah ya samar dashi a tsakaninku”.

Ina Rayyern fa ya kasa fahimtar Yaren.

Haka ya tasa Dr Sajo a gaba da magiya.

Karshe dai sukaje dakin da aka kwantar da Jannart amman sai suka samu Barrister Kabeer ya kulle ƙofar ya kuma ƙi buɗe wa.

Ranan haka dai Rayyern ya kwana kamar zautacce.

Ramadan kuwa, tunda ya kira Raihana ta shaida masa, tabbas Abbanta ya ɗaga aurensu.

Kuka yayi ta mata tamkar ɗan yaye, ita kanta taji ciwon abin to amman yaya zatayi mahaifinta ne, dole itan ta aro jarumta tana bashi haƙuri.

Riyyam-nsra kuwa falo ya fito yayi ta sana’asa ta bauɗewa Kekkyawar tarbiyya da akayi masa.

Mammy kuwa, da Zaiton baccinsu sukayi cike da farincin haɗuwar ahlinsu.

Mamy kuwa tunda Abba ya gaya mata abinda ke faruwa na sharaɗin auren Rayyern da Jannart, cikin sanyi tace.

“Amman dai yanzu duk wanda yaga Rayyern yasan yana son matarsa kuma suna zaman lfy, na sani lallai yayi kuskure amman kada a tsananta masa”.

Cikin tsuke fuska Abba yace.

“Da yake ba ke akayiwa cin fuskar bako”.

Da sauri ta jujjuya kai, kana a hankali kuma tace.

“Sannan kuma gsky ni kaina banji daɗin ɗaga auren Ramadan da akayi ba, kuma ma wai meyasa aka ɗaga fisabililahi fa?”.

Zamanshi ya gyara yana kallonta yace.

“Surkin nasa ya bani gamsassun hujjojinsa kan batun a ɗaga aure.

Domin ya lura da rawan kan Ramadan.

Yace tabbas kada muyi gamgancin yi musu auren nan a irin ya wannan lokaci da kwanaki goma kacal ne suka rage a ɗauki azumin watan Ramadan.

Yace iyaye da yawa suna wannan gangancin da sakaci a aurar da yara gab da Ramadan, suzo tun kafin su gama marmarin juna da sauƙe jarabar kuruciyarsu a kama azumi.

Sanadin wannan sai azo ma’aurantan suyi ta kusantar juna a cikin darare da rana duk da sunsan azumine, sai bayan salla ayi ta aikawa malamai tambaya ana cewa sabon aurene sunyi ta karya azuminsu.

To da za’ace iyaye su lura da wannan in dai azumi yazo sauran wata ɗaya ko kwana arba’in to a haƙura da auren a kaishi bayan salla domin kiyaye darajar watan.

Ya ƙara da cewa, yaga kan Ramadan yana rawa, zai iya yin komai, yace ya gansa daren jiya har sha ɗaya da rabi yana gidan sa.

Na kuwa gamsu dan wallahi Ramadan jarabebben yarone, marar haƙuri kinga idanun nan sa irin na Rayyern na fahimci duk jarabbabun yarane masu ɗan karen fitina, mace bazata samu sauƙi a wurinsu ba, kawai dai shi Rayyern ya iya takunsa ne.

Shi kuwa wancan ɗan jaririn Riyyam-nsra ɗin in dai ba dandatsen taure zamuyi mishiba, na fahimci tabbas zai iya aikata komai”.

Ya kare mgnar yana kwanciya tare da cewa.

“Bacci zanyi kin gamsu da hujjar mahaifin Raihana ko”.

Kai ta gyaɗa masa tare da kwanciya gefensa, ganin har ƙarfe biyu da rabi na dare.

Ana fitowa sallan Adusa.

Rayyern ya nufi ɗakin da Dr Sajo ya nuna masa daren jiya cewa, nan aka kwantar da Jannart.

Sai dai yana zuwa ya samu, babu kowa a ɗakin koda yaje Office ɗin Dr Sajo nanma sai ya samu a rufe.

Daya tambaya sai akace masa ai daga masallaci gida ya wuce.

Jiki a saɓule yaje ya shiga motarsa cikin sanyin jiki ya nufi gida.

A falo ya samesu gaba ɗayansu tea suke sha kamar kullum amman yau harda Baba Mauɗo kana dasu Mammy da Zaiton.

Amman banda Ramadan da yake durƙushe gaban Abba fuskarsa a kumbure,

Jiki a saɓule ya zauna gefen Mamy dake kallonsa cikin tausayawa duk ya rame a dare ɗaya.

“Mamy Mammy ina kwana”.

Cikin kulawa Mamy ta amsa, yayinda Mammy kuwa ta amsa a daƙile, sai kuma ya kalli Abba da Baba Mauɗo da ko inda yake basu kallaba, cikin sanyi ya gaidasu, a fakaice suka amsa masa,

Riyyam-nsra da Zaiton ne suka gaidasa.

Cikin sanyi ya amsa, kana ya juyo ya kalli Ramadan dake cewa.

“Dan Allah kuyi karoƙesu kada auren nan dan Allah Abba Baba Mauɗo ku taimaka min kugafa dun an gama komai sai ana gobe ɗaurin aure kuma ace an ɗaga.”

Cikin tsuke fuska Baba Mauɗo yace.

“Toh mu dai munyi iya yinmu, sarki mai gaggawa sai dai in kaine zakaje ka basu haƙurin”.

Da sauri ya kuma juyowa ya kalli Abba dake cewa.

“Ni ka tashi a gabana kasan bana son yawan magiyar banza da wofi”.

Miƙewa yayi tare da sakin kuka kamar yaro ya haura sama yana cewa.

“Na shiga ukuna”.

Abin nasama dariya ya basu.

Bayan sun gama shan tea ɗinne Baba Mauɗo ya fita.

Abba kuma yayi ciki.

Mammy ɗaki ta koma.

Ganin hakane yasa Rayyarn longoɓar da kai, cikin sanyi yace.

“Mamy kijifa wai rabani da Janna zasuyi, Mamy ki bawa Abba haƙuri dan Allah.

Kai ta jinjina masa tare da cewa.

“Kayi hakuri zomuje wurinsa.”

To yace kana yabi bayanta.

Shiru yayi gaban Abba ya kasa cewa komai.

Shi kuwa Abba kai ya kauda tare da cewa.

“Tunda baka da abincewa, tashi ka tafi, ka shirya dai ƙarfe takwas dai-dai zamuje gidan Kakanku Malam Mainasara.”

Da sauri ya gyara zamanshi tare dayin kasa da kansa kana murya a sanyaye yace.

“Dan Allah kayi haƙuri, wlh bata da lfy tana buƙatar kulawata”.

Da sauri ya dakatar dashi tare da cewa.

“Ficemin daga nan”. Dole ya tashi ya fita.

Daga nan side ɗin Baba Mauɗo ya nufa.

Ita kuwa Mamy cikin nuna tana fushi da mijin nata kan matakin da suka ɗauka kan Rayyern ɗin ta fito kitchen ta fara aiki.

Ganin haka Zaiton ta shigo ta fara tayata.

 

Shi kuwa Rayyern cikin sanyi ya zauna gaban Baba Mauɗo daya tsaresa da ido, cikin sanyi yace.

“Yah kai mahaifina ka taimaka wa zuciyata datake fuskantar abubuwa biyu lokacin ɗaya, farin cikin bayyanarku da warwarewar ko wanne ƙullin da kuma fargabar rabani da Jannart.

Dan Girman Allah Baba Mauɗo kayiwa Abba mgn ku  dawo min datata, ko dan cikin da ke tsakaninmu.”

Cike da mamaki da kuma tarin farin ciki Baba Mauɗo yace.

“Ciki?”. Yayi tambayar a daƙile da danne farin cikinsa, shi kuwa Rayyern da sauri ya gyaɗa masa kai.

Sai kuma yayi saurin ɗago kansa tare da cewa.

“Ƴar tasu da kace bakaso, bazaka kuma taɓa sontaba, kayiwa ciki dan zalumci ka rabata da budurcinta, duk da yarjejeniyar da kukayi da ƙanin mahaifinta?”.

Da sauri ya fara jujjuya kai tare da cewa.

“Baba Mauɗo ni ina son matata”.

Cikin danne murmushin sa, yace.

“Sai kaje ka gayawa Barrister ai tunda dashi kuka sharaɗin bada niba, maza bani wuri ka shirya zamuje gidanmu”.

Cike da ƙuna ya fita.

Acan wurin Barrister Kabeer kuwa, kasan cewar anyiwa Jannart duk abinda ya dace, kuma Alhamdulillah ta warware, haka yasa, ya ɗauketa suka koma gida.

Yayinda Aunty Dijat kuwa take bata kulawa ta musamman.

Suna zaune a falon ta ganshi ya foto da tarin tsoffin takardun da yake ta ɓoyewa, duk kwana biyu ya shiga silin ya dubasu kamar ɓarawo.

Cikin sanyi yace.

“Jannart kiyi haƙuri tun jiya anje an kaiwa Daddynki sammaci tare da takardar bada umarnin tsaresa, shida  su Alhaji Abdu Tababa da kuma Dr Lukman, da sauransu.

Kuma duk an kamasu, suna tsare, domin nafi son ranar monday ayi komai a gama.

Waɗannan sune tarin shiduna tsoffi da sabbin.

Sannan kuma a ranar za’a saki Junaid sabida zamansa a can yayi  nitsuwa ta haƙiƙa da tuba ma gsky.

Sannan Yah Azeez dinkima zai dawo a satin nan.

Kana Abdul da Mom sai randa Azeez ya dawo in yayi musu bayani zasu zo ki gansu.

Waɗanan kuma takardun kadarorin mahaifinki ne, domin na mahaifinsu Rayyern kam na bawa Alhaji Bala Tambari tun tuni ya kai mushi duk nima a lokacin ban san cewa Baba Mauɗo bane”.

Cikin zubda hawaye ta ajiye cup ɗin tea ɗin da take sha, murya na rawa tace.

“Abba yanzu kashe Daddy na za’ayi”.

Shima hawayen yake tsiyayarwa kana a hankali ya kauda kai tare da cewa 

“Nima Jannart wannan kukan shi nake tayi tsawon shekaru, bana son rasa ɗan uwana duk da mugune ina sonsa, amman kuma sonsa bazai sa in karesaba”.

Daga nan kuma sukayi ta kuka, da kyar Aunty Dijat ta iya lallashinsu.

Ƙarfe takwas dai-dai duk suka fito cikin harabar gidan.

Suna cikin shiga ta musamman Baba Mauɗo yayi wani irin masifeffen kyau kamanninsa da Rayyern da Riyyam-nsra suka kara fitowa fili.

Ramadan da Zaiton da Mammy kuwa suma kamarsu ta ƙara fitowa.

Mamy da Abba ma sunyi matukar kyau.

Cikin motoci suka shiga.

Mammy da Riyyam-nsra suna bayan motar Rayyern, Baba Mauɗo kuwa yana gama kusa dashi.

Mamy kuwa da Zaiton suna bayan motar Ramadan.

Abba kuwa na gaba kusa da Ramadan ɗin.

A haka suka nufi gidan Baba Mauɗo.

A can cikin gidan Malam Mai Nasara kuwa, kusan duk a cike a falonsa.

Kamar yadda suka saba duk ƙarshen wata sunayin zama na musamman to yau ranar zaman tasune.

Ganin Rayyern ne a gaban mota yasa Mai gadin buɗe masa gate.

Haka yasa suka kutsa kai cikin gidan.

A hankali suka fara fitowa daga cikin motocin.

Wani irin sassayan numfashi Baba Mauɗo ya shaƙa lokacin daya sauƙe ƙafarsa a tsakiyar farfajiyar gidan.

A hankali Rayyern ya koma bayansa, ya tsaya ta gefen Mammy hakama Ramadan kana Riyyam-nsra da Zaiton.

Abba da Mammy kuwa matsowa sukayi kusa, dasu.

Shi kuwa Baba Mauɗo cikin wani irin raunin begen iyayensa da tsawon shekara biyu ɗaya dawo hayyacinsa kullum sai yazo ƙofar gidan.

A hankali ya farayin taku yana nufar ƙofar falon Mahaifin nasu da ya hango tarin takalma.

Cikin wani kaɗuwa, duk mutanen cikin falon suka juyo suka zubawa ƙofar falon idanu, sabida jiyo Muryar Baba Mauɗo da yayi sallama.

Da sauri wasu daga cikinsu suka miƙe suka nufi ƙofar falon a lokacin da yayi sallama ta uku.

Kusan a tare suka dawo cikin tsananin rawan jiki da kaɗuwa.

Lokacin da sukayi arba da fuskar babban yayansu. Da Aicha da zaratan samarin da daga ganin sun ganesu.

Cikin tsananin kaɗuwa Uncle Mustapha yace.

“Laa hailahaillahu Muhammadu Rasulullahi sallahu alaihi Wasallama, Yaya Basiru”.

Jin wannan furucin nasane yasa Malam Mai Nasara sakin wani irin tattausan murmushin tare da cewa.

“Allah ya nuna min hakan a mafarki”.

Shi kuwa Baba Mauɗo da sauri ya kusa kansa cikin.

Falon yayinda su Rayyern ke biye dashi a baya.

Wannan shine kyautar Allah.

Faɗin farin cikin sake wannan zuriya a wannan rana a wannan lokaci bazai faɗuba.

Kan kace kobo duk waɗanda basu zo Bama aka kirasu.

Waɗanda basa ƙasar kuwa kab aka kirasu video call.

Shi kam Malam Mai Nasara, shafa kan Baba Mauɗo yakeyi yana zubda hawaye tare da shafa kansu Rayyern baki ɗaya cikin sanyi yace.

“Tun ganin forko da nayi muku naji a jikina cewa ku jinane.”

Cikin sunkuyar da kai Abba ya jinjina kai tare da basu dukkan labarin abinda ya faru.

Ya ƙare da cewa.

“Amman ni kaina bansa shi bane, sai jiya”.

Mammy kuwa sai murmushi takeyi jin yadda Malam ke sa mata al’barka cikin tsananin jin daɗin yace.

“Dama ban cire rai a kankuba.”

Haba ɗaya sun gigice, da farin ciki, kasan cewar dama in zasuyi taron ƙarshen watan, dukkansu sukan zo da abinci na musamman, to wannane yasa duk anan a falon akayi walima mai cike da farin ciki.

Har zuwa azahar, bayan sunyi sallan azahar sun dawone.

Duk ana cike a falon.

A hankali Rayyern ya rarrafa ya isa gaban kakan nasa, kanshi ya ɗaura kan cinyarsa.

Kana murya a raunace yace.

“Malam Ahlinka ya cika, kowa ya cika da farin ciki, amman ni nawa farin cikin rageggene”.

Cikin tsananin so da kulawa duk suka kalleshi cikin so mai tarin yawa tsohon yace.

“Gaya min jikana, kuma likitana, menene cikon farin cikin naka, faɗi zan sama maka shi da izinin ubangiji”.

Da sauri Baba Mauɗo ya kalli Abba shima Abba kallonsa yayi.

Shi kuwa Rayyern cikin narke murya da mayen zazzafar soyayyar da baisan yaushe tayi masa kamun kazar kukaba yace.

“Matata, Malam Matata Jannart itace cikin farin cikina. Babana da Abba na da Baffan ta, suna hukuntani ta hanyar azabtar dani da rabamu a kan wani kuskure da nayi a baya, inasonta kuma itama tana sona Malam dan Allah da Manzonsa Malam ka tayani bawa su Abbana hakuri.

Sannan muje da kai ka bawa Barrister haƙuri ya bani matata”.

Mamy kam dasu Abba ido suka zuba masa, cike da mamakin Rayyern ɗin.

Shi kuwa Malam cikin jin daɗi da son jikan nasa yace.

“To bari ni in baku hakuri a madadinsa”.

Da sauri Abba da Baba Mauɗo suka haɗa baki wurin cewa.

“Ka gafarcemu Malam yadda kace haka za’ayi”.

Cikin sakin murmushi yace.

“Toh muna yin sallan la’asar zanje in ɗauko masa matarsa.”

Haka kuwa akayi bayan an idar da sallan la’asar basu shiga gida Bama.

Malam da ƙanin Baba Mauɗo mai binsa Alhaji Bello sabon kuɗi, da kuma Baba Mauɗo da Abba, da Rayyern ɗin suka tafi gidan Barrister bisa jagorancin Abba.

Cikin sassarfa Mai gadin Barrister, ya shiga cikin gidan tare da sanarwa Barrister cewa yayi baƙi kuma harda Malam Mai Nasara.

Jin hakane yasa Barrister dake tare da Dr Sajo a falonsa fitowa da sauri.

Cikin tsananin girmamawa ya isa gaban Malam Mai Nasara da kuma su Baba Mauɗo.

“Lale-lale Malam da kanka ai da kayi ƙirana ma zanzo.

Kai sannu da zuwa malam ku iso daga ciki.”

Ya ƙare mgnar yana  yanayi musu jagora.

Bayan sun Zazzauna ne, Barrister da kansa ya kawo musu abubuwan sha, kana da sauri ya shiga falon Aunty Dijat yana cewa.

“Dijat maza a dama min fura da nono mai sanyi, yau Malam Mai Nasara ne da kansa  ya kawo mana ziyara, da alamu ƙarata Rayyen ya kai dan naga sai tura baki yakeyi”.

Cikin sauri tace to tare da miƙewa.

Shi kuwa juyawa  ya nufi falonsa yana cewa.

“In an dama Jannart ta kawo”.

To ta kuma cewa, ita kuwa Jannart ido kawai ta binsu dashi, sai yanzu ta gane akwai wata manufar tahowa da ita.

Shi kuwa Barrister a gaban dottijon ya zauna tare da gaidasa.

Kana suka gaisa da sauran baki ɗaya.

Suna cikin gaisawar Jannart ta shigo riƙe da wani ɗan madaidacin kwaraya mai zane, da damu fura da nono mai sanyi.

Cikin sakin murmushi Baba Mauɗo da Abba suke amsa gaisuwarta tare da Alhaji Bello sabon kuɗi.

A hankali ta zauna gaban Malam Mai Nasara tare da miƙa masa ƙwarya da tana mai cewa.

“Barka da zuwa Malam”.

Ta ƙare mgnar tana kallon Rayyern daya ɗaura tafin hannunsa kan nata hannun dake gefensa yana mai murza yatsarsa a kai.

A hankali ta kalli Malam dace cewa.

“A’a masha Allah, wannan kam ba yar jaridar nan bace ta Arewa da kika taɓa yinmin tambayo”. Cikin nitsuwa tace.

“Eh”. Tana mai ƙoƙarin miƙewa,sai kuma ta koma ta zauna jin Malam yace.

“A’a zauna”.

 

Gyara zama yayi tare da cewa.

“To Barrister biko nazo yiwa jikna da kuma bada haƙuri. Duk da bansan meya aikata ba”.

Da sauri ya kwaɓe fuskarsa cikin sanyi yace.

“Dan Allah Barrister kada ka faɗi komai, bana so taji, abinda na sani da shine ina son Matata wlh ni wannan alƙawarin tun randa mukayishi a inda mukayishi nama mance dashi, ina son Matata.

Itace cikon dukkan farin cikina, kuma itama tana sona.

Ko ba haka Janna ki gaya musu muna son juna kada su rabamu, ko dan cikina da yake jikinki, ina sonki ina son abinda zaki haifa min”.

Ya ƙare mgnar da iya gskyarsa tare da ɗago hannunta ya manna da sajensa.

Ita kuwa Jannart cike da kunya tayi ƙasa da kanta, tana mai mamakin kalamansa.

“Ya Salam wai  da gaske ciki nake dashi”.

Sai kuma ta ɗan saki sassayan numfashi.

Abba ne ya gyara zama tare da cewa.

“To sakar mata hannu mara kunya”.

Da sauri ya sake hannun tare dayin rau-rau da idanunsa”.

Cikin sanyi Barrister yace.

“Ke Jannart shiga ciki”.

Aiko da sauri ta mike tayi ciki.

Shi kuwa cikin sanyi yace.

“To Alhamdulillah Rayyern yanzu dai ka gane cewa na miji baya jin cikekkiyar dadin rayuwa sai da mace ko?”.

Da sauri yace.

“Eh na yarda”.

Dariya sukayi baki ɗaya, kana Barrister yace.

“Babu komai, kazo ka ɗauki matarka da daddere, kaci darajar Malam dan da so nayi sai na gara sosai”.

Cikin tsananin jin daɗin yace.

“Alhamdulillah amman kuma, wace garawace tafi wannan?”.

Shiru yayi sabi daƙuwar da Baba Mauɗo tayi masa.

Haka dai akayi ɗan raha kana Barrister ya musu bayanin kama su Alhaji Idi Sale Dakata da akayi.

Ganin magriba ta ƙaratone yasa, suka fito dan tafiya.

Amman ina Rayyen yaki domin yace ƙafarsa kafar matarsa.

Haka yasa dole suka tafi suka barshi a nan.

Tare sukayi sallan magriba da isha.

Suna dawowa ya kira, Hadi akan ya kawo masa mota.

Cikin tsaresa da idanu Barrister Kabeer yace.

“Ni naso ka barmin ita mu ƙara kwana”.

Cikin sauri yace.

“Kayi haƙuri Barrister wlh bazan iyaba”.

A cikin ransa kuwa cewa yakeyi.

“Uhumm Barrister ai ka ingizani, wallahi tallahi daren yau zan tabbatar da Jannart a matsayin matata, zan rabata da budurcinta da kake ramin ihu a kai. Zan meda ita muhallin rayuwata wurin jin daɗi na.”

Shi kuwa Barrister Kabeer murmushi kawai yayi tumo yadda ya haukace masa a Office ɗin Dr Sajo.

Ƙarfe tara dai-dai, suka bar  ƙofar gidan Barrister Kabeer.

Yayinda take gefensa.

Tuƙi  yakeyi cike da jin daɗi sunzo dai-dai wani babban Shopping Mall Jannart tayi wani irin…!

Alhamdulillah duk da dai bawai na jini ƙalau bane, amman ni kaina a matse nake damu gama shiyasa na kwakwarta, amman ba editing.

Back to top button