Uncategorized

Tubali Book 2 Page 8 Complete Novel

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

Sassayan numfashin ta fesar kana.

Tasa k’afarta na dama acikin d’akin, wani irin sassanyan kamshi daya daki hancinta ne, ya sata lumshe Idanunta tare da, turo kanta cikin dakin bakinta d’auke da sallama. 

Sako kanta acikin dakin da tayi ne kuma, yasa idanunta sauk’a akanshi, inda yake kwance sanye da boxer ajikinsa, sai kuma laptop d’insa daya saka agaba da alama, wani aiki mai muhimmanci yakeyi.

Da sauri ta juya tare da kawar da kanta gefe, saboda wannan ne karo na farko acikin rayuwarta, da ta fara Ganin namiji haka dagashi sai yar finkilar boxer.

Rayyern kuwa dake kwance jin sallama, da kuma motsinta ne ya sashi jan blanket ya d’an rufe cinyoyinsa, tare kuma da juyowa ya kalleta.

Tsaye take amma ta kawar da kanta gefe, sannan tasa duka hannayenta akan kirjinta, da’alama kuma  sanyin dake cikin dakinne yayi mata yawa.

“Meye?”

Ya fad’a yana me tsareta da idanunsa, saboda tunda suka zo bata tab’a shigowa cikin d’akin nasa ba sai yau.

Tsayuwarta ta d’an gyara tare kuma da juyowa ta fuskancesa, saidai bata yarda ta sake ajiye Idanunta akansa ba.

Cikin sanyin muryarta da akullum, take fitar da wani irin daddad’an sauti tace.

“Dama wayarka ake kira shine na kawo ma.”

Ta k’are maganar tana me d’an matsowa jikin gadon, a hankali saboda mik’a masa wayar. 

“Gashi.”

Ta fad’a adai-dai lokacin da ta iso kusa dashi.

Hannunsa ya mik’a mata, still yana daga kwancen batare daya tashi ba, cikin wata irin murya yace.

“Give me.”

Mik’a masa wayar tayi, kasancewar ta sunkuyar da kanta k’asa ne kuma, yasa ta sauke Idanunta akan, wasu kwantattun gashin dake kwance akan kirjinsa, wanda kuma sudinne suka taho har zuwa, saman cibiyansa, gashi ne masu kyau da laushi, duk da cewar basu da yawa amma sun k’awata, farar fatar jikinsa sosai.

Tsaida idanunta tayi akan saman mararsa, wanda tananne gargasan sukafi yawa, kuma sun kwanta lub lub gwanin ban sha’awa,  Kallon gashin jikin nasa ne kuma yasa, ta kasa sakar masa wayar da take mik’a masa.

Tana son gashin jiki sosai domin abun yana yi mata kyau, musamman awajen Namiji, duk da cewar ta saba kanin na legs din, Ya Junaid kasancewar ya saba zama da gajerun wanduna, amma bata tab’a ganin kyawawan gashi kamar na Rayyern din ba, saboda shi nasa har wasu shining sukeyi. 

Rayyern kuwa dake mik’a mata hannu, Idanunta ya kalla saboda yaga ta kasa sakar masa wayar.

Ganin yanda take Kallon jikinsa ne kuma, ya sa shima ya kalli jikin nasa, saboda atunaninsa ko wani abun ta gani.

Fahimtar da yayi cewar hairs d’insa take kallone, kuma ya sashi dawo da kallonsa gareta, Cikin yanayin gajiyawa da Kallon nata yace.

“Wai duk wannan Kallon kam na menene Malama? ko cinyeni kikeson yi ne, Dan nasan zaki iya ko dai naci miki bashin wani abune kike kallonsa a jikina?.”

Maganan nasa daya fad’a ne yasa tayi saurin yin k’asa, da kanta tare da sakar masa wayar, lokaci daya kuma taji wani irin kunya ya lullub’e ta, saboda Sam bataso hakan ya kasance ba.

Jin ya karbi wayarne kuma yasa ta juyawa, da sauri ta fice daga cikin dakin.

Rayyern kuwa bakinsa ya tab’e, tare da bin bayanta da idanu, kasancewar tana tafiyar nata cikin sauri ne kuma yasa, duk wani gab’a dake jikinta motsawa, musamman big hips dinta way’anda suke da shape na burgewa, duk da cewar rigar bacci ne ajikinta, amma hakan bai hana hips din nata bayyana ba, saboda rigar jikin nata yana da santsi, ga kuma dogon gashin kanta daya sauko har bayanta. 

Saurin kawar da idanunsa daga kan hips din nata, yayi tare da maida kansa ya ajiye akan pillow, akaron farko na rayuwarsa da yaji zuciyarsa na tsananta, bugawa akan wani abu na daban.

Idanunsa ya d’an lumshe tare da sauk’e Ajiyar zuciya.

Wayartasa ya kunna tare da duba mai kiran nasa, Ganin new number ne kuma ya sashi share kiran,  saidai ko minti 1 ba’a rufa ba, wani kiran ya sake shigowa, Ganin kiranne kuma ya sashi d’agawa tare da kara wayar akan kunnensa. 

Daga can b’angaren Riyyam  yace.

“Hello Hamma Rayyern Riyyam-nsra ne.”

Ajiyar zuciya Rayyern din ya sauk’e, saboda Jin muryar Riyyam din, cikin muryarsa dake nuna d’an yanayin kasalan dake tattare dashi yace.

“Riyyam yakake yasu Mammy.”

“Lafiyanmu k’alau Hamma Rayyern, saidai nayi kewarka sosai, Mammy da Zaytoon sunce na gaisheka,  kuma Hamma Rayyern mafa tuntuni nake cewa, Hamma Ramadan ya bani numbern ka, amma sai jiya ya turomin.”

Riyyam nsra din ya fad’I haka cikin tura baki.

Rayyern kuwa sanin halin surutun Riyyam dinne, yasa shi gyara kwanciyarsa tare da cewa.

“Ina Mammy?”

“Ga tanan.”

Riyyam din ya fada yana bawa Mammyn wayan, saboda dama tana gefensa.

“Assalamu Alaikum Rayyern.”

Rayyern dake kwance jin muryar Mammy, ya sashi tashi ya zauna, cikin sakin fuska ya amsa mata sallaman tare kuma da gaisheta. 

Mummy kuwa cikin jin dadin jin muryar Rayyern din tace.

“Ya Mascow da kuma Surukata.”

“Lafiya lau Mammy, itama kuma tana lafiya, Zaytoon fa?”

Rayyern din ya tambaya.

Murmushi Mammy tayi kana cikin jin dadin kulawarsa agaresu tace.

“Zaytoon tana lafiya, saidai kasanta kasa ce sarkin bacci, har tayi bacci da na had’aku kun gaisa, yasu Mamynku da Ramadan, fatan duk suma Suna lafiya.”

“Lafiya lau Mammy, d’azu munyi waya dasu, Ramadan kuma yana can yanata zumudi, saboda an bashi mata, kuma naji anacewa aurensa kafun Azumi.”

Rayyern din ya fad’a yana me gyara zamansa, saboda hakanan Idan yana waya da Mammyn yakejin sakewa. 

Mammy kuwa jin abunda ya fad’ane yasa cikin farinciki tace.

“Masha Allah gaskiya na tayasa murna, Allah Ya sanya alkhairi yasa ayi damu.”

“Ameen Mammy zaku zo biki ko?”

Yayi maganar kamar Wacce tazo masa afuzge, wanda kuma abunda ke cikin zuciyarsa ne ya fito fili, saboda haka kawai yakejin yana son Ganin matar ido da ido.

Daga can b’angaren Mammy kuwa murmushi tayi, cikin kuma danne damuwar dake ranta tace.

“Insha Allah zanzo mana Maud’ona Idan angayyace ni.” 

Murmushi Rayyern din yayi tare da lumshe idanunsa, saboda yana jin dadi aduk lokacin da matar takirasa da suna Maud’o.

Cikin sakin rai yace.

“Mammy zaki zo mana, ai basai an gayyaceki ba saboda kema mai iya gayyatan wasu bakinne daban.”

“Hakane Maud’o Allah ya kaimu lokacin, ya kuma bamu Aron rai da lafiya, bari na barka saboda naga dare yayi, nasan awajenka ma nitsawan daren yafi haka.”

Mammyn ta fad’a cikin sakin rai.

Rayyern kuwa kansa ya jinjina, kamar Mammyn tana gabansa kuwa yace.

“Ameen Mammy saida safe, ki gaishemin da Zaytoon.”

“Zataji Insha Allah.”

Mammyn ta amsa masa, tare da zare wayar akunnenta ta kashe.

Shidinma Rayyern ajiye wayar tasa yayi, tare da komawa ya kwanta, kana ahankali ya lumshe idanunsa. 

Acan b’angaren Jannart kuwa tana komawa, d’akinta kwanciya tayi tare dajan babban blanket ta rufe jikinta.

Lub tayi akan gadon tana mejin kunyan, ka mata da Rayyern din yayi tana Kallon jikinsa.

Hannayenta tasa ta rufe fuskarta.

Dan sai taji tamkar har yanzun tana gabansa ne. 

Tana ahaka bacci b’arawo ya d’auketa. 

            *Washegari*

Yau d’in ba kamar kowacce rana ba, domin tunda ya tashi yayi sallan asuba bai sake komawa bacci ba.

6:30 am dai-dai ya gama shirya kansa cikin wasu, tsadaddun suit masu kalan light orange, suit ne masu masifar kyau da tsada, wanda suka bayyana kyawu da kwarjininsa. 

Black shoe na sau ciki ya saka ak’afafunsa, tare da d’aura agogon WW a hannunsa. 

Yayi kyau matuk’a musamman da ya zamana, sajen dake kwance akan fusuka kawo breakfast din da yayi order. 

Amsar breakfast din yayi ya ajiye, saboda bashi da enough time ne kuma, yasa ko tsayawa ci baiyi ba, haka yasa kai ya fice sai baza kamshi yake. 

Direct Babban JSC MEDICINA CLINIC MASCOW Hospital din ya nufa, domin acanne yau za suyi meeting din nasu, kasancewar kuma abunda zasuyi din nada yawa, shiyasa duk suka fito da wuri. 

10:00 am dai-dai Jannart ta bud’e k’ofar d’akin nata ta fito zuwa falon.

Sanye take cikin wani straight gown mai kauri, Wacce ta kama jikinta ta zauna d’amas, sai kuma hulan sanyi da ta saka ta rufe gashinta dashi,  ak’afarta kuwa wani safa ne, wanda da ‘alama yana tare mata sanyi sosai.

K’arasowa tsakiyar falon da tayi ne kuma, ya sanyata lumshe Idanunta.

Badon komai ba kuwa saidan k’amshin turarensa, da ya mamaye cikin falon,  domin duk da cewar ya jima da fita amma kamshinsa na nan.

Lumsassun Idanunta ta d’an bud’e ahankali, tare da neman waje ta zauna akan d’aya daga cikin kujerun falon.

Ledan abincin daya ajiye mata din ta d’auka, tare da bud’ewa , ga mamakinta kuma yau din,  chips and ketchup ne sai kuma hadin Salad da lemon tsami.

Taji dadin hakan sosai saboda dama ta gaji, da ire iren abincin kasar, wannan dalilin yasa sosai taci abincin bayan ta kammala ne, kuma ta Kai sauran ragowan kitchine, tare da dawowa falon, tv ta kunna cikin sa’a kuwa ta samu wani, tasha suna haska film mai kyau.

Komawa kan tree seater tayi, har za ta kwanta ne kuma sai idanunta, suka sauk’a akan sachet din maganin Rayyern din, dake ajiye akan kujeran.

D’aukan sachet din maganin Tayi, tare da d’an jujjuyasa saboda Ganin da tayi, saura guda biyar ne kawai ya rage maganin ya k’are. 

Bayan ta duba sunan maganin ne kuma ta maidashi ta ajiye, Ahankali ta kwanta akan kujeran tare da mik’e k’afafunta, kana ta maida hankalinta duka akan tv’n. 

Tana nan kwance kuwa bacci ya d’auketa, batare da ta shiryawa hakan ba.

                  *Nigeria.*

Abdull ne ya turo k’ofar babban falon nasu, ya shigo hannunsa rike da jakan makarantarsa.

D’an tsayawa yayi daga bakin kofar yana me Kallon, Momynsa wacce take zaune jigum acikin falon, ta d’aura hannayenta bisa kan k’uncinta.

Kansa ya d’an sunkuyar k’asa, lokaci d’aya kuma yaji hawaye sun cika idanunsa, badon komai ba kuwa saidan sanin damuwar dake, zuciyar kowannensu daga Cikin gidan.

Maida kofar falon yayi ya rufe, tare da karasowa ya zauna ad’an nesa da mahaifiyar tasa.

“Momy.”

Ya kira sunanta murya asanyaye.

Saurin d’agowa Momyn tayi saboda sam bata ji shigowar nasa ba.

“Na’am Abdull ka dawo.” Momyn ta amsa asanyaye.

Idanu Abdull din ya zubawa Momyn nasu kana cikin sanyi yace.

“Nasan akan me kike damuwa Momy, nasani akan b’atan Aunty Jannart ce, nima kuma akwai wannan damuwar acikin zuciyata, kullum dashi nake kwana nake tashi, har yau nakanji wani iri, Idan na tuna cewar wai Aunty Jannart ta b’ata, b’atan da har yau ankasa samota, tayaya hakan zata kasance Momy? Nikam nasani wasu ne kawai suka sace Aunty Jannart, Dan kawai su cutar da ita.”

Idanu Momyn ta tsura masa, saboda itama kullum irin tunanin da takeyi kenan, saidai kuma abubuwa da yawa ayanzu kan kulle mata Kai, Lallai akwai Sark’ak’iya mai nauyi, da kuma k’ulli mai wuyar kuncewa, wanda yake cikin gidan da basu sani ba, sau dayawa zuciyarta kan gaya mata, cewa Lallai akwai wani b’oyayyen abu, da ake b’oyewa.

Wanda kuma ita kanta batasan sai yaushe ne, sirrin b’oyen zai fito fili ba.

Ajiyar zuciya ta d’an sauk’e tare da gyara zamanta, cikin sanyin murya mai d’auke da damuwa tace.

“Abubuwa da yawa suna damuna Abdull, bayan b’atan Jannart da kuma rashin lafiyar Dadynku, har da son sanin wani abu da aka bunne, ay’an kwanakin nan bana iya bacci Abdull, bansan mai yasa ba kwata-kwata bani da nutsuwa, saidai koma meye Ina rok’on Allah da ya kawoshi da sauki.”

“Ameen.”

Abdull din ya amsa, tare da mik’ewa kaitsaye ya wuce d’akinsa, saboda agajiye yake sosai.

Itama Momyn mik’ewa tayi ta koma d’akinta,  saboda tun daren shekaran jiya da kunnuwanta suka jiye, mata wani abu gaba d’aya ta kasa sukuni, duk da ta kasa fahimtar inda kalaman da taji Mijin nata na fad’a awaya suka dosa, saidai Tabbas tasan abune mai d’auke da Sark’ak’iya, wanda acikinsa babu komai sai zallan tashin hankali, rud’ani da kuma bayyanar b’oyayyar gaskiya. 

Barrister Kabir.

Ahankali yake har had’a wasu takardu dake gabansa, zuciyarsa cike take da kwarin guiwa, na samun duka shaidun da yake buk’ata. 

Har had’a takardun yayi awaje d’aya, har dai yazo kan wani file na k’arshe, wanda asaman file din, aka rubuta suna kamar haka, *Barrister ABDULKARIM SALEH DAKATA.*

Ajiyar zuciya Barrister Kabir din ya sauke, tare kuma da d’an jujjuya file din, lokaci d’aya kuma yaji idanunsa, sun cika da k’walla.

Cikin jajircewa da kuma tabbatarwa da kansa yace.

“Insha Allah Koda baka raye gaskiya zatayi halinta, abunda aka b’oye zai fito fili, Ranka bazai tafi a banza ba, Lallai dole kowa zai sani, nan babu jimawa zan tone duk wani abunda suka bunne da izinin ubangiji.”

Ya k’are maganan with full confidence, tare da tashi ya taka kan wata kujera,  takardun dake hannun nasa ya maida, can sama wajen ajiyarsa ta sirri, da duk duniya babu wanda ya sani daga shi sai Allah.

Bayan ya b’oye takardun ne kuma, ya bud’e k’ofar d’akin nasa, ya fita zuwa wajen iyalansa  dake falo.

                *Mascow*

Sai 11:30 pm Dai-dai na k’asar yake shigowa cikin gidan.

Bayan ya gama dai-dai-ta parking ne kuma, Ahankali ya bud’e murfin motar ya fito.

Kallo d’aya zakayi masa kafahimci cewa agajiye yake sosai, saboda tunda suka zo kasar, wannan ne karo na farko daya fara lattin dawowa gida, haka zalika kuma yaune karo na farko da sukayi aiki sosai.

Agajiye yake takunsa, Yayinda yasa hannayensa duka biyu, ya zare suit din dake jikinsa.

Ahankali ya tura k’ofar falon ya shiga.

Babu kowa acikin falon, wanda dama kuma bai tsammaci hakan ba, shiyasa ma kaitsaye ya wuce d’akinsa.

Briefcase da kuma car key d’insa ya ajiye akan bed, Ahankali kuma Cikin nutsuwa ya soma, rage kayan dake jikinsa, takalmi da kuma safar k’afarsa ya cire, kana ya zare duk wani kaya dake jikinsa.

D’aya daga cikin sabin towel d’insa ya d’aura akan kugunsa, duk sanyin da akeyi kuwa hakan bai damesa ba, kaitsaye ya wuce toilet yayi wanka.

Koda ya fito daga wankan kuwa, mai kawai ya shafawa jikinsa, sai wani 3quater daya saka.

Tabbas ya gaji sosai domin har wani rufewa idanunsa keyi, bud’e d’an madaidaicin fridge’n dake cikin d’akin yayi, wani babban packet na chocolate d’insa ya d’auko, tare da dawowa ya kwanta akan gado.

Idanunsa ya lumshe ahankali tare dasa, hannunsa ya d’an shafa saman mararsa, saboda kasala yakeji sosai ajikinsa.

Ahankali kuma yana daga kwancen, ya saka hannunsa ya d’auko chocolate d’aya yakai cikin bakinsa.

Jin zakin chocolate din abakinsa ra d’aune kuma, yasa shi sake lumshe idanunsa, tare kuma da gyara kwanciyarsa, bayan ya sake zuba wasu chocolates din abakinsa. 

Yana taunawa ahaka har bacci ya d’aukesa, da ledan chocolate din ahannunsa tamkar wani k’aramin yaro. 

Jannart kuwa tuntuni dama ta riga da tayi bacci, Dan koda tayi sallan isha, da tazo falon bata samu abinci ba, komawa tayi ta kwanta, kasancewar dama bawai wani yunwa takeji sosai ba. 

Washegari kuwa kamar yanda ya saba, tun kafun ya fita yasa aka kawo masa breakfast, bayan yaci nasa yabar mata nata, kaitsaye ya sake wucewa wajen aiki. 

                     *** ***

After 9days.

Tabbas Rayuwa tafiya take, haka ma kwanaki k’arewa suke, akullum kuma lokaci baya jira.

Koda yaushe haka sukeyin rayuwarsu shida ita,  zasu kwana agida d’aya amma sai su share, sama da sati babu wanda yaga d’an uwansa, musamman Rayyern da ayanzu, yake cikin tsananin busy, Dan Koda ishashshen lokacin kansa ma bashi dashi.

Domin tun awancan ranan da takai masa wayarsa,  bata sake sakashi a Idanunta ba, takan fito ta zauna afalo Idan bayanan.

Sannan aduk sanda ya ajiye mata abinci, takanci kad’an tabar sauran. 

Kasancewar kuma ranar yau ta kama Wednesday ne, ya sata fitowa falon dan akwai wani series film din da takeson kallo. 

Ahankali take tafiya harta k’araso tsakiyar falon, inda ta sauk’e idanunta akan ledodin halal restaurant dake ajiye akan table.

Sam bata wani jin yunwa sosai shiyasa, ko kula abincin ma batayi ba.

Zama tayi akan kujera tare da kunna tv, saidai taga ba’a fara series dinba, hannunta ta mik’a saman kujeran, dan d’aukan remote, karab kuwa idanunta suka sauk’a akan, sachet din maganin Rayyern din, wanda babu komai aciki, da alama ya shanye ragowan.

D’aukan empty sachet din tayi, tare da d’an jujjuyawa aranta tana me mamakin, Kodai ya k’arar da wannan din, har ya fara shan wani ne? 

Sanin halinsa nak’in magani da tayi ne, kuma yasa ta watsar da tunanin gefe, ledan abincin daya ajiye tun na safe ta d’auka takai kitchine. 

Ganin yanda kitchine din ya d’an hargitse ne, kuma yasa ta tsaya gyarawa. 

Tana cikin gyaran ne kuma Idanunta, suka sauk’a akan wani babban roba mai murfi, k’arasawa tayi ta bud’e robar, ga mamakinta kuma sai taga pure honey ne, mai kyau aciki.

Wani irin dadi taji saboda dama tanason honey,  kasancewar ta kammala duk wani abu da zatayi ne kuma, yasa ta d’auki wani d’an plate na glass ta zuba honey din  aciki.

Anutse ta dawo cikin falon, hannunta rik’e da plate din tana lasar zuman da yatsanta na dama.

Zama tayi akan kujera tare da nannad’e k’afafunta, ta ci gaba da lasan zuman, rabin hankalinta kuwa naga tv saboda ansoma haska series film din. 

Acan b’angaren Rayyern kuwa, yau din tun 1:00pm

suka shiga heart surgery, basu suka fito ba kuma sai 3:00 pm.

Tunda suka fito yakejin kansa duk wani iri, kasancewar tun safe yakejin cikinsa na d’anyi masa ciwo, dan ko abinci bai iya samu ya sakawa cikin nasa ba, drinks kawai yasha.

Ahankali ya saka tissue ya goge fuskarsa, saboda wani irin gumi dayaji na fesowa akan goshinsa, duk da sanyin da garin ke dashi.

Still jin cikin nasa nad’an ci gaba da ciwo ne, yasa shi tuna rabonsa da magani yau kwana 3 kenan wunin na hud‘u, gashi kuma magungunan nasa sun k’are bai samu ya sayo wani ba. 

Sulaiman dake gefensa ne ya d’an kalleshi, cikin kuma d’anyi k’asa da murya yace. 

“Rayyern are you okay?”

D’agowa Rayyern d’in yayi, batare daya kalli Sulaiman dinba yace.

“Yea I’m okay.”

D’an Jim Sulaiman din yayi, saboda tun daga cikin hospital din ya fahimci, kamar Rayyern din baya jin dadi.

Saboda ya sake tabbatar da abunda yake zargi ne kuma, ya sashi cewa.

“Rayyern ka tabbata you’re okay.”

Idanu Rayyern din ya d’an lumshe,  kana cikin kosawa yace.

“I’m okay mana Sulaiman, if I’m feeling bad mood, I will tell you, so please leave me alone, cause I’m tired..”

Ya k’are maganan cikin cije l’abbansa, saboda baya son yawan tambayoyi.

Sulaiman kuwa Ganin yanda Rayyern din keyi ne, ya sake yardarwa kansa cewar he’s not okay. 

D’an gyara zamansa yayi tare da fuskantar Rayyern din, cikin tausasawa yace.

“No Rayyern k’arya ba d’abi’arka bace, wallahi zan iya rantsewa baka da lafiya, gashi kana zufa a inda ban tab’ayin zufa ba, Rayyern a Mascow fa muke, garin da ko ina dinsa sanyi ne, kayi tunani Idan mutum yana lafiya zaiyi zufa awannan garin ne a irin wannan lokacin?  Rayyern baka da lafiya, saboda haka tell me what’s wrong with you?” 

Idanu Rayyern din ya lumshe, saboda yasan halin Sulaiman da takura, Idan bai fad’a masa gaskiya ba bazai k’yaleshi ba.

“My stomach has paining.”  

Ya fad’a atak’aice.

Idanu Sulaiman din ya zaro, cike da fargaba hadi da tsoro yace.

“Subahanallah Rayyern, kana shan maganinka kuwa?”

“Eh but two days ban Shaba, saboda sun kare ban samu time na saya ba.” 

Rayyern din ya basa amsa kaitsaye.

Sulaiman kuwa ido ya tsura masa, kana cikin dan yanayin tausayawa yace.

“Haba Rayyern Meyasa kakeson yin wasa da lafiyarka? kasan yanda ciwon nan keyi maka idan ya tashi, please dan Allah kana kiyayewa, kasani bawai kai kad’ai kake da buk’atar lafiyarka ba, su Abba da Mamy suna da buk’atar ka, can you imagine yau ace bakanan, mekake tunanin zai faru? bana fatan haka Rayyern Dan Allah kana kulawa da kanka, yanzu tunda yau mun fito da wuri kaje pharmacy ka saya maganin.” 

Kai Rayyern din ya jinjina kawai, tare da mikewa tsaye, batare daya sake cewa komai ba kaitsaye ya nufi wajen motarsa. 

Ganin hakanne kuma yasa Dr. Sulaiman had’a sauran Doctors dinsu, suka tare taxi dan komawa masaukinsu.

Rayyern kuwa yana shiga cikin motar yayi mata key, kaitsaye wani babban pharmacy dake gefen Hospital din ya nufa,  Koda yaje bai samu maganin nasa ba, saidai sunyi masa kwatancen wani pharmacy, wanda suke da tabbacin cewa zai iya samun maganin idan yaje can.

Agajiye sosai yakejin kansa shiyasa bai iya jurewa, tafiyanba kaitsaye restaurant ya biya ya saya abinci, saboda yunwa yakeji sosai.

Isowarsa gidan kenan yana gama dai-dai-ta parking din, motar ya fito hannunsa rike da ledan abincin da kuma suit d’insa, ya nufi cikin gidan.

Ahaka ya shigo falon da cikinsa ya riga ya d’an d’auki dumi, saboda na’urar d’umama d’aki da Jannart din ta kunna.

Ahankali ya zauna akan kujera, tare da bud’e ledan abincin, take away d’aya ya ciro tare da bud’ewa,  Ahankali ya d’auki spoon tare da Kai loman abincin bakinsa.

Idanunsa ya d’an rumtse tare da ajiye spoon din, kana ya maida jikinsa ya kwantar, Hannunsa na dama ya d’aura akan cikin nasa dake ciwo, domin zuwa yanzu ciwon nata k’ara tsumuwa…!

*Da yar ya iya had’iye abincin dake bakin nasa, batare kuma dajin zai iya ci gaba da cin abincin ba, ya mik’e tsaye tare da wucewa bedroom d’insa.

Bayan ya rage kayan  jikinsa ne kuma ya shiga wanka.

Abu fa kamar wasa duk bayan wasu yan mintuna, yakanji ciwon cikin nasa na k’aruwa, saidai kasancewar sa mai dauriya shiyasa yake iya jurewa. 

Ahankali ya murd’a handle din kofar ya fito, sanye yake da rigar wanka fara k’al, Hannunsa na dama kuwa rik’e yake da towel yana goge ruwan jikinsa.

Ganin da yayi lokacin sallah ya kusa ne kuma, yasa shi sanya wani riga da wando agurguje, saidai rigar irin short sleeve dinnan ne, slippers ya saka ak’afafunsa saboda sauri kuwa, ko wayarsa bai d’auka ba, yana mejin ciwon na tasar masa kadan kadan, haka ya d’auki key din motarsa ya wuce masallaci. 

Jannart kuwa yau din Koda  ta idar da sallan Isha ba ta fito cin abincin ba saida tayi wanka,  inda ta shirya kanta cikin wani riga da wando, like sleeping dress, saidai suna da kauri sosai, sannan jikinsu nada laushi da kuma gashi  tamkar jikin kuliya-mage, sosai kayan ya bi jikinta musamman wandon, daya bayyana shape din hips dinta, sai kuma rigar da ta kasance tana da d’an fad’i, saidai hakan bai hana tudun breast dinta bayyana ba. 

Kamar yanda ta saba kuwa hulan sanyi ta saka akanta, tare da watsa dogon gashinta baya. 

Turaren oud ta shafa ajikinta, cikin d’an hanzari ta fito falon saboda cikinta ya fara yi mata kukan yunwa. 

K’arasowa cikin falon tayi ta zauna, tare da jawo ledan takeaway din gabanta.

Abincin ta tsurawa ido saboda taga kamar ba, alaman anci abincin sosai, da alamar Koda ancisa ma to bai wuce loma d’aya akayi ba. 

D’an Jim tayi kamar meyin nazarin wani abu, sanin bai wani damu da cin abinci sosai bane yafi ta’ammali da kayan zaƙi, yasa ta share tunanin, abincin ta d’anci kad’an kafun ta tashi ta wuce d’aki, saboda yau din ana d’an tab’a sanyi sosai, gashi kuma bacci sosai takeji. 

Rayyern shi kuwa Dr Rayyern.

Tun da ya shiga cikin masallacin bai fito ba, saida aka idar da sallan Isha, bayan ya d’an tab’a karatun Al’Qur’ani ne kuma ya d’auko hanyar dawowa gidan.

Ahankali yake taka k’afafunsa, tare kuma da kutso kansa cikin falon, gaba d’aya bayajin yana yanayi mai dad’i saboda ciwon cikin dake damunsa, duk da cewa ciwon nasa bai tsananta ba, amma dai yanayi masa kad’an kad’an,  kaitsaye d’akinsa ya wuce batare da ya lura da ko Jannart din taci abincin ba,  yana shiga kuwa ya fad’a kan gadonsa, tare dayin rigingine kana yaja blanket ya rufe jikinsa.

Cikin nutsuwa yake ambaton sunan Allah abakinsa, hade da lumshe kyawawan idanunsa da suka d’anyi ja,  yana ahaka cikin ikon Allah bacci ya d’aukesa. 

Washegari.

Kamar yanda ya saba tashi akowacce rana haka ma yau din ya tashi, saidai kuma tun tashinsa yaji cikin nasa na ci gaba da yi masa ciwo. 

Duk da yana jin ciwon kuwa haka ya shirya kansa, cikin riga  da wandon suit, sai kuma wani babban jacket daya d’aura akai. 

Yana fitowa kuwa aka kawo breakfast, saidai ko ci baiyi ba haka ya tafi, saboda duk yana jin bakinsa babu dadi.

Jannart kuwa yau din bacci tasha sosai, Dan bata tashi ba sai k’arfe 10, bayan tayi wanka ne kuma ta fita zuwa falon.

Abincin ta d’auka taci, saidai bata wani ci sosai ba ta ture shi gefe, anan cikin falon ta kwanta, tare da d’aukan wayanta ta soma buga game.  

Rayyern kuwa Koda ya shiga wajen meeting dinsu, gaba daya ya kasa nutsuwa, domin tun yana maida attension d’insa garesu, har dai abun ya soma fin karfinsa. 

Fahimtar hakan da Dr. Sulaiman yayi ne kuma yasa shi, d’anyin k’asa da murya  cikin kulawa yace. 

“Gaskiya Dr. Rayyern ya kamata mufita mu nemo maganinka, domin naga har yanzu kamar you’re not okay.”

Idanu Rayyern din ya d’an rumtse, batare kuma da yace komai ba, ya jawo system d’insa ya soma latsawa.

shi dai kam Dr. Sulaiman yasan halin kafiyar Rayyern din Sarai, shiyasa ma baisake bi ta kansa ba, d’aya daga cikin manyan Doctors din da sukeyi musu, invigilators Dr. Sulaiman din ya samu, tare da gaya musu matsalan Rayyern din.

Wani magani d’aya daga cikin manyan Doctors din, ya rubuta tare da bawa Dr. Sulaiman yace ya nemo ya bawa Rayyern din yasha. 

Sanin halin ciwon Rayyern din Idan ya tashi ne kuma, yasa babu wani b’ata lokaci Dr. Sulaiman ya fita zuwa sayo maganin.

Sosai kuwa maganin ya basa wahalan samu, Dan saida ya zagaye pharmacy har biyu amma babu, cikin sa’a kuwa a pharmacy na uku ya samu maganin.

Bayan ya dawo ne kuma ya bawa Rayyern din yasha.

Ahankali ya jingina bayansa da jikin kujera, tare da lumshe idanunsa, numfashi kawai yake sauk’ewa akai akai, Yayinda zuciyarsa kuwa ke bugawa da k’arfi.

Yana nan zaune ahaka har tsawon 30mn cikin, taimakon Allah kuwa ahankali yakejin ciwon nasa na lafawa. 

3:30pm dai-dai yauma suka tashi daga meeting din nasu,  inda suka tsaya wani d’an tattaunawa kuma wanda ya d’aukesu tsawon 30mn.

4 dai-dai amfanin maganin daya sha din ya k’are,  Aikuwa ko mintuna biyu ba’a cika ba, yaji cikin nasa ya dawo da ciwo.

Ciwo kuma gadan gadan ba kaman yanda, ya tashi masa da safe ba.

Hakan yasa duk bayanan da sauran Doctors din keyi, baya fahimta. 

Ahankali ya janye jikinsa baya, tare kuma da d’aukan car key d’insa.

Batare kuma daya tsaya sauraran wani abu ba, ya nufi inda ya ajiye motarsa.

Dr Nura dake ya dan zuba mishi ido ne.

Ya ɗan nunawa. Dr Sulaiman dake kula da duk wani motsinsa shi

Ganin ya juya ya fitane, ya biyosa saidai kafun ma ya iso, tuni Rayyern ya cilla motar tasa kan titi.

D’an Jim Dr. Sulaiman din yayi , acikin ransa yana me fatan Allah yasa kada ciwon Rayyern din ya tashi.

Rayyern kuwa tunda ya cilla motar tasa kan  titi, ya daina fahimtar wasu abubuwan, murza steering motar kawai yakeyi, batare da yana tantance abunda yakeyi ba, saboda zuwa yanzu ciwon nasa ya tsananta sosai.

Wani irin gudun da yakeyi ne kuma, yasa cikin mintuna kad’an ya iso bakin k’ofar gidan nasa.

Yanayin yanda yakejin ciwon nasa ne kuma yasa, ko tsayawa saya musu abinci yau din baiyi ba.

Bayan ya dai-dai-ta parking ne kuma ya bud’e murfin motar ya fito, Cikin yanayin tafiyar dake nuna galabaitarsa, kaitsaye ya wuce cikin falon.

Yana shiga  ya fad’a akan kujera, tare dasa hannayensa duka biyu ya rik’e cikinsa, idanunsa ya rumtse da k’arfi.

Domin har cikin jijiyoyin jikinsa yakejin rad’ad’in ciwon cikin. 

Wani irin numfashi yake fitarwa, mai d’auke da tsananin wahalan da yakeji,  saboda zafin ciwon da yakejin ne, yasa shi soma jujjuya kansa Ahankali, yake sakin nishi wanda yake fita daga bakinsa. 

Jannart kuwa dake  kwance a d’aki tana game, kwata-kwata bata ma ji koda motsinsa ba, saboda  dama takan gane cewar ya dawo ne, ta hanyar k’aran motarsa.

Almost 1hour.

Ahankali ya bud’e idanunsa wanda yakejin sunyi masa nauyi, tare da soma sauk’e Ajiyar zuciya akai akai, lokaci d’aya kuma ya d’anji jikinsa na sakewa.

Anutse ya d’an d’ago kansa ya kalli agogon dake falon.

“6:19 pm Dai-dai da ya ganine, ya sashi yunk’urawa cikin k’arfin hali ya mik’e tsaye.

“Alhamdulillah.”

Ya fad’a k’asa k’asa saboda yanda yaji ciwon ya d‘an lafa masa.

Asanyaye ya nufi bedroom d’insa, Koda ya shiga kayan jikinsa ya cire, tare da shiga toilet yayi wanka had’i da d’auro alwala.

Duk way’annan abubuwan yanayinsu ne cikin rashin k’arfin jiki, da kuma tsananin dauriya saboda duk jikinsa babu karfi. 

Fitowarsa daga wankan kenan ya saka wani, farin dogon wando da kuma farin riga, kasancewar bashi jin karfi ajikinsa sosai ne kuma yasa, ko gama mak’ala bottom din rigar baiyi ba, haka ya juya ya fita.

Adaddafe yake tafiya har ya iso waje, motarsa ya shiga tare da kunnata, kaitsaye ya nufi masallaci.

Yana zuwa kuwa ana shiga Sallah.

Hakkan yasa da d’an hanzari yazo yabi jam’i.

Bayan an idar da sallan magriban ne kuma, ya d’an matsar da jikinsa gefe tare da jingina bayansa ajikin bango.   

Idanunsa ya lumshe tare da soma ambaton sunan Allah acikin zuciyarsa.

Sannu ahankali yakejin ciwon na taso masa, tamkar wanda ake yakutsa marar nasa haka yake ji. 

Yana nan azaune kuma har aka kira sallan isha, Ganin anan kokarin tsaida sahu ne kuma, ya sashi mik’ewa shima ya gyara tsayuwarsa.

Komai nasa acikin k’arfin Hali yakeyi, saboda ciwon na k’ara taso masa akowanni second, hakan yasa Sallan kawai yakeyi amma ba tare da wani ishashshen nutsuwa ba, dai-dai sunkai Sujjadar raka’a ta uku ne kuma,   yaji gaba d’aya duniyar na soma juya masa, Yayinda gaba d’aya jikinsa ya d’auki karkarwa, saboda wani irin matsanancin ciwo da yakeji, sosai yakejin ciwon wanda har hakan ya sashi kasa d’agowa daga sujjadan da yayi, har tsawon minti d’aya kafun ya iya d’agowa.

Adaddafe dai haka ya jure har aka idar da sallan, a sujjadarsa ta k’arshe ne kuma ya lumshe idanunsa, tare da mik’a neman taimakonsa wajen Allah.

Ana idar da sallan ya fice daga cikin jam’in, Cikin yanayin dauriya da cije baki, ya fice daga cikin masallacin, tare da nufan wajen da ya ajiye motarsa. 

Acikin zuciyarsa kuwa addu’a yakeyi, ahaka ya shiga cikin motar tasa, ya nufo gida.

Kwata kwata ba acikin nutsuwarsa yake ba, wannan dalilin yasa shi yin wrong driving, ahaka har ya dawo gida.

Da k’yar ya iya shigar da motarsa cikin gidan, ko gama dai-dai-ta parking din motar baiyi ba ya fito, yana sako k’afarsa waje kuwa yaji ciwon cikin nasa na ci gaba da k’aruwa. 

Ahankali yake taka k’afansa da yakejin kamar ba zasu iya jurewa d’aukan nauyinsa ba,   Saboda ayanzu ciwon ya tashi masa gadan gadan, har takai ga ko bud’e idanunsa ya kasa yi, jikinsa yayinda gaba d‘aya jikinsa ke rawa  sosai tamkar wanda aka jonawa shocking wani irin masifeffen zogi da raɗaɗin ciwon yakeji, ahaka ya nufi cikin gidan ido a rumtse dan in ya buɗesu ma jiri ke dibarsa duhu na rufe ganinsa.  

       *Jannart*

Ahankali ta zare hijab din dake jikinta, tare da mik’ewa tsaye.

Yauma sanye take cikin riga da wando na bacci, the same irin shigar daren jiya tayi, saidai kalan kayan na yau ya banbanta dana jiyan, saboda yau kayan nata pink colour ne, suna da matukar laushi kuma sosai, Yayinda suka bi jikinta suka kwanta.

Ahankali tasa hannunta ta d’an shafa cikinta dake kukan yunwa, saboda yau tun safe bata sake saka wani abu acikinta ba. 

Sanin da tayi cewar zuwa yanzu baikai ga dawowa, amasallaci bane yasa kaitsaye ahaka ba tare da tasa wani mayafi ba ta nufi falon.

Dai-dai lokacin shi kuma Rayyern ya shigo, cikin juyawan kai da tsananin azabar ciwo, ya fad’a saman doguwar kujera, batare dako takalman dake k’afansa ya cire ba.

Hannayensa duka biyu ya d’aura akan cikinsa, tare da rumtse idanunsa da k’arfi yayinda gaba daya jikinsa ya debi karkarwa wani irin taune lips ɗinshi duka tamkar zai tsinkesu wata iriyar fitinenneyar zufa ce mai tattare da tsananin azaba da yanke rai da rayuwa yake tsastsafo mishi tako wanne hudan gashin jikinsa.

Cikin azaba yake fitar da numfashin wahala. 

Ahankali ta bud’e k’ofar d’akin ta fito, hannunta rik’e da wayarta, sako kanta cikin falon da tayi, yayi dai-dai da sakin wani irin nishi da yayi.

“Hayhhhhhhhhh”.

Wanda hakan yasa cikin sauri ta d’ago Kanta ta kalli inda yake kwance.

Wani irin mummunan harbawa taji zuciyarta tayi, wanda hakan yasa ta tsura masa idanunta, cike da tsoro take Kallon yanda gaba d’aya jikinsa ke rawa.

ad’an tsorace ta shiga takowa cikin falon, har ta k’araso inda yake kwancen,  idanunsa dake arumtse ta kalla, kana  ta dawo da kallonta ga jajayene labb’an bakinsa, wa y’anda sukayi ja sosai, sai b’ari kuma sukeyi tamkar wanda yake fama da zazzafan zazzab’i.

Ahankali ta d’an sunkuyo da kanta garesa, cikin tsananin fargaba da kuma tsoron abunda zai faru ta k’ira shi da wani sunan da taji bakinta ya ambata kawai.

“Naan! Naan!!”

Sam baya cikin hayyacin da zai iya amsa mata, duk da yaji sautin muryarta acikin kunnuwansa kuma ya fahimci shi din take kira da da sunan Naan din, amma azaba da kuma zafin ciwon da yakeji ya wuce tunaninsa ayau din. 

Jannart kuwa ganin bai amsa ta ba, ga kuma yanda jikinsa ke ta karkarwa yasa, ta sunkuyowa tare da matsowa kusa dashi sosai, Ahankali ta d’aura hannunta akan forehead d’insa, wanda jijiyoyin kansa suka bayyana rad’o rad’o.

Jin da tayi jikinsa babu zafi ko kad’an ne, yasa ta Kallon hannayensa daya daura akan cikinsa ya damƙe mararshi.

Duk jijiyoyin jikinsa sun mimmik’e, Yayinda  fuskarsa tayi ja sosai.

Ahankali ta sake matsowa kusa dashi, lokaci d’aya kuma Idanunta suka ciko da hawaye. 

Saboda ta fahimci cewar acikin biyu d’aya ne ya faru, ko ciwon cikinsa ne ya tashi, ko kuma ciwon kansa wani irin masifeffen raunine ya rufeta lokaci ɗaya ta tuno yadda hankalin ahlinsa ke mamummunan tashi in sun ganshi cikin makamancin wannan yanayin.

“Hamma Naan ka amsa mana meke damunka?.”

Ta fad’i hakan araunace tare dasa, hannayenta ta zare masa takalman dake k’afarsa. 

Tana mai jin hawaye na silalo mata cikin rawan murya mai cike da rauni tace.

“Innalillahi 

Naan me yake damunka? Kanka ne yake ciwo? ko cikinka? Dan Allah Hamma Naanu ka fad’amin kaji, please kaga duk jikinka rawa yakeyi.”

Jannart din ta fadi haka cikin yanayin tashin hankali, da kuma tsoro hadi da fargaban kada ciwon cikin nasa ne ya tashi. 

Saboda taga yana dafe da cikinsa dayin murkususu, ga kuma wani irin numfarfashin  da nishin yake sakewa akai-akai. 

Ganin yanda yake ta had’a zufa ne kuma, yasa ta matsowa gab dashi, har hucin numfashinsa na dukan fuskarta. 

Zip din dan Jacket din dake jikinsa ta zuge k’asa, tare dasa hannayenta duka biyu akan kirjinsa,  wani irin rauni da tsananin tausayinsa takeji, d’aura hannunta da tayi akan kirjinsa ne kuma, ya sata jiyo yanda zuciyarsa ke bugawa da k’arfi-k’arfi.

Wannan dalilin yasa araunace ta fashe da kuka, cikin kukan nata ne kuma ta soma kokarin zare masa jacket din dake jikinsa.

D’an  matsowa tayi garesa sosai.

Hannunta tasa ta tallaboshi da iya ƙarfinga ta d’an d’agosa daga kwancen tayi, tare da zama abakin kujeran, Ahankali ta d’aura kansa akan cinyarta, cikin sakin sheshshek’an kuka tace. 

“Dan Allah  Naan ka bud’e idanunka, ka kalleni kada wani abu ya sameka, ka bud’e idanunka dan Allah…”

Ta k’are maganan tana kuka sosai, tare da d’an jijjigasa saboda, zuwa yanzu ta tsorata sosai da yanda taji numfashinsa, na kokarin d’aukewa, ga kuma yanda jikinsa ke ci gaba da rawa, zufa kuwa ya keto masa takota Ina.   

Ganin kukan bazai kaita bane kuma, yasa ta tashi kaitsaye ta nufi d’akinsa, Dan nema masa magani.

Saidai Koda ta shiga cikin d’akin, neman duniya tayi amma bata ga Koda kwayan magani ba, hakan yasa ta d’auko wayarsa ta fito.

Ganin abunda yakeyi dinne kuma yasa ta, sake rudewa atsorace ta taho kansa.

Saidai kafun ma ta k’araso har ya tafi k’asa zai fad’o daga kan kujeran, yanata jujjuya jikinsa hannayensa ko na dafe da cikinsa.

Wani sabon kuka ne ya sake kwance mata, cikin matsanancin tausayinsa da takeji, ta k’araso wajen, tare da durk’usawa ta zauna.

Hannayenta duka biyu tasa ta d’ago kansa zuwa kan cinyarta.

Arud’e take fad’in kalmar innalillahi wa’inna Ilaihirraju’un Hasbunallahiwani’imanwakil Naan! Naan!! Hamma Naanu!!!. 

Shikuwa Rayyern da ya gama fita ahayyacinsa, jinsa acikin jikinta ne yasa shi sake matse jikinsa waje d’aya, tare da tura kansa acikinta,  hannunsa na dama kuwa d’aurasa yayi akan cikin nata, duk ya zauce ya fita a hayyacinsa.

Wani irin numfarfashin azaba kawai yake fitarwa, duk da cewar yanajin duk abubuwan da take fad’a, amma bazai taba iya mayar mata da martani ba, saboda baya ko tantama yana bude bakinsa, gaba d’aya numfashinsa zai d’auke. 

Jannart dake kuka kuwa Ganin yanda yake ta shigewa cikin jikinta ne, yasa ahankali ta d’aura hannunta akan cikinsa,  rashin sanin abunda zatayi masa dinne kuma, yasa asanyaye ta soma shafa cikin nasa, tare da d’an dannawa kad’an kad’an.

Hakan da tayi d’inne kuma yasa shi jin, tamkar tana danne masa ciwon ne,  amatuk’ar wahalce ya d’aura hannunsa akan nata, tare da sake tura hannun nata akan cikinsa, har yakai ga tana tab’o kan mararsa. 

Kasancewar baya cikin hayyacinsa, shiyasa duk baisan me yakeyi ba,   Haka ita Jannart dinma bata da wani nutsuwa, kuka kawai takeyi tare da sake ci gaba da danna masa cikin.

Almost 10mn suka d’auka ahaka, saidai har yanzu babu wani abu daya sanja, saima jikinsa dake k’ara sak’ewa, domin hatta numfashi yanzun da k’yar yake furgosa. 

Ganin hakanne kuma yasa Jannart din k’ara rud’ewa, wayarsa dake hannunta ta kunna, cikin rashin sanin abunyi ta dannawa numbern Ramadan kira.

Adai-dai lokacin kuwa Ramadan din zaune, yake acikin falon sama yana aiki a laptop d’insa,  Yana nan zaune kuma kiran wayan ya shigo, Ganin sunan Hamma Rayyern d’insa ne kuma ya sashi d’aga wayar da sauri, tare da cewa.

“Hello Hamma Rayyern.”

Idanu Jannart din ta rumtse, kana cikin tsananin rauni murya na rawa tace.

“Ramadan,  Hamma Hamma ciwon cikinsa ya tashi, ya zanyi Ramadan tsoro nakeji. 

Dan Allah 

Ramadan ya zanyi…..”

Ta fad’i maganar cikin matsanancin kukan da ya riga yaci k’arfin ta.

Ramadan dake zaune kuwa jin abunda Jannart din ta fad’a ne, ya sashi tashi da sauri cikin tsananin tashin hankali yace.

“Innalillahi wa’inna Ilaihirraju’un, Jikin Hamm Rayyern ya tashi? Subahanallah Aunty Jannart yanzu kuna ina? ina Hamma Rayyern di yake? ciwon ya tashi sosai ko? kin basa magani?”

Ramadan din ya had’e mata duka tambayoyin, cikin tashin hankalin daya samu kansa aciki.   

“Muna gida Ramadan, kuma na duba ko ina babu maganinsa ya shanye, bansan yanda zanyi ba Ramadan, numfashinsa d’aukewa yake.”  

Jannart ta basa amsa murya adisashe.

Saboda kukan da tayi.

Ramadan kuwa jin yanda Jannart din ke kuka ne, yasa shi d’an dai-dai-ta nutsuwarsa a matsayin sa namiji, cikin tausasa murya yace.

“Calm down Aunty Jannart, Insha Allah Hamma Rayyern he’s will be fine, bari na k’ira Dr. Sulaiman nasan zaizo ya basa taimako, ki daina kuka Insha Allah zai samu lafiya.”

Ya kare maganan cikin lallashi.

Wanda hakan yasa Jannart din jinjina kai, tare da zare wayan akan kunnenta ta ajiye agefe.

Ramadan kuwa yana kashe wayan, Dr. Sulaiman ya kira, arude yake fad’a masa halin da Rayyern din ke ciki.      

Jin hakanne kuma yasa Dr. Sulaiman tare taxi, Kai tsaye ya nufi gidan Rayyern din.

After 20mn.

Gaba d’aya Idanunta alumshe suke, saidai babu abunda suke fitarwa sai hawaye. 

Har yanzu kuma Rayyern din kwance yake akan cinyarta, Yayinda ya mak’alk’aleta k’am, kansa da fuskarsa kuwa duk suna kan cikinta,  wannan yasa duk wani numfashin azaba, da yake fitarwa akan cikinta yake sauk’a. 

Har yanzu kuma jikinsa bai daina karkarwa ba, ga zufa dake feso masa tako ta ina. 

Wani irin rik’o yayiwa Jannart d’in, tare da sake matse hannunta dake saman cikinsa,  ahankali take yawo da hannun nata, tare da d’an mammatsa cikin nasa.

Wanda zuwa yanzu ya fara jin dadin hakan da takeyi masa, musamman yanda tausassan d’umin tafin hannunta, ke sauk’a  akan mararsa.

Ahankali batare da ta sani ba kuma, hawayenta ke sauk’a acikin gashin kansa. 

Duk da cewar baya cikin nutsuwarsa, amma hakan bai hanashi jin dumin hawayen nata acikin kansa ba da shessheƙan kukanta.

Wani irin fitinannen numfashi yaja, alokacin da yaji ta d’aura hannunta akan, faffad’an k’irjinsa wanda yake bud’e, kasancewar ta cire masa aninayen rigar tasa. 

Ahankali ta tallabe habarsa cikin tafin hannunta.

Tare da d’an bubbugawa a hankali murya a sanyaye take kiranshi.

“Naan! Nasn!! Naan!!! Ka bude ido ka kada ka rufesu, gaya min dame zan taimaka maka, Naan ka bude idonka”. Take mgnar a raunace tana ci gaba da dan marin kumatunsa a hankali hankali, kana ta zuba idanunta kan kyakkyawar fuskarsa asanyaye takeyi masa komai, saboda har yanzu hawayen idanunta sun kasa tsayuwa.

So yake ya buɗe ido ya kalleta amman ya kasa.

   Suna zaune ahakan ne kuma, yaji wani irin fitinanne kuma gigitaccen ciwo na taso masa, ciwon daya fi wanda ya taso masa abaya, ciwon daya sa shi jin duniyar na kifewa dashi.

Haka kuma ciwon da azabarsa yasa shi kasa tantance duniyar da yake, cikin wani irin azaban dake sukan naman jikinsa, ya soma fitar da wani irin numfashi mai kama da nishi, lokaci daya kuma duk jikinsa ya soma sakewa. 

Sautin gurnanin numfashinsa da taji acikin kunnuwanta ne, kuma ya sata bud’e Idanunta amatuk’ar tsorace ta zuba masa idanu.

Baza ta tab’a iya jurewa ganinsa ahaka ba, wannan dalilin ya sakata sakin sabon kuka mai tsuma zuciya.

“A’a, A’a Naan Dan Allah karka rufe idanunka, karka tafi ka barni awannan duniyar da Bani da kowa sai kai,  bansan kowa ba acikinta, Yah Allah ka taimakeni ka rufamin asiri Yah Allah ka taimaki bawanka ka sauk’a k’a masa wannan ciwon.”

Ta k’are maganan cikin matsanancin kuka tare da silalo da hawaye, kana ta sunkuyowa garesa, dai-dai lokacin kuwa idanunsa suka rufe rub. 

Hannayenta duka biyu ta bud’e tare da rungumesa akan kirjinta, ta sake sakin wani sabon kuka, kuka kuma irin wanda bata tab’ayi ba arayuwarta.

Dai-dai lokacinne kuma  Dr. Sulaiman ya turo kofar falon ya shigo.

Ita kuwa Jannart dake tsananin kuka kuwa, ko d’ago Kanta batayi ba,  acikin kukan nata ne kuma ta sake rungume Rayyern din ak’irjinta. 

Azauce take fad’in. 

“Please Naan!! Please open your eyes please Naan don’t leave me please…..”

Ta kai k’arshen maganan tana me jijjigasa, Ahankali kuma takai yatsunta daidai saitin hancinsa.

Abunda taji ne kuma yasa ta waro Idanunta, amatuk’ar tsorace, cikin gigita da kuma tashin hankali, irin wanda bata tab’a samun kanta aciki ba, agaba d’aya rayuwarta.

Idanunta dake zubar da hawaye ta zubawa Rayyern din, tare da soma girgiza kanta da sauri, cikin firgici da kuma mugun bugun zuciyar dake dukan k’irjinta, muryar na rawa tace.

“Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un…!

Back to top button