Uncategorized

Tubali Book 2 Page 7 Complete Novel

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

Abincin daya kawo jiya da daddaren, idanunsa ya d’an zubawa ledodin, wanda da dukkan alamu babu wanda ya tab’a su, Dan suna nan kamar yanda ya ajiye su.

numfashi ya d’an fesar tare da soma takowa, ya k’araso tsakiyar falon, inda abincin ke ajiye. 

Isowarsa wajenne kuma ya sake tabbatar masa da cewar, tabbas babu alamun an tab’a ledodin.

Bakinsa ya d’an tab’e tare kuma da komawa ya zauna, akan d’aya daga Cikin kujerun falon, idanunsa ya d’an lumshe Ahankali, dai-dai lokacin kuma daga can waje aka soma knocking kofar falon.

Ahankali ya d’an bud’e idanunsa, tare da mik’ewa tsaye, saboda already dama yayi musu order’n breakfast, to yanzun ma yasan breakfast din nasu ne ya iso.

K’arasawa yayi ya bud’e k’ofar tare, da karb’an ledodin breakfast din. 

Kana ya dawo ya zauna akan sofa.

Duk da cewar baya wani jin yunwa sosai, amma hakan baisa shi kincin abincin ba, bud’e ledan yayi ya somaci, saidai bai wani ci sosai ba ya ture abincin gefe.

Yanda yaji duk baya wani jin dadin cikinsa ne kuma, yasa shi mik’ewa ya koma d’aki,  sachet din maganinsa ya d’auko, tare kuma da dawowa falon ya zauna.

K’wayoyin maganin da sukayi saura ya zubawa ido, wanda kwata kwata basu wuce guda 16 ba, kasancewar akowacce rana mutum zaisha guda d’add’aya ne.  

To Yanzu dai way’anda suka rage masan, basu wuce na 2weeks ba, banda ma yayi wasa da shan maganin yasan da yanzu basu Kai haka yawa ba.

B’alle maganin yayi ya saka abakinsa, tare da Korawa da ruwa marar sanyi.

Bayan yasha maganin ne kuma ya mik’e tsaye, babban agogon Bangon dake sak’ale acikin d’akin ya kalla, wanda yake nuna masa 12:pm dai-dai kenan na rana. 

Ajiyar zuciya ya d’an sauk’e tare da d’aukar wayarsa, hadi da car key d’insa, domin duk da cewar yau din weekend ne, amma suna da test da zasuyi akan, yanda ake dashen k’oda, wanda kuma yau dinne firstly da zasu fara, gwaji akan abunda aka koya musu. 

Kaitsaye ya fice daga cikin falon, direct wajen da ya ajiye motarsa ya nufa, Ahankali ya d’aga kansa yana me Kallon yanayin garin, duk da kasancewar yanzun rana ne, amma sudai awajensu tamkar safiya ne, saboda gaba d’aya yanayin garin babu rana, sai wani irin sanyi mai ratsa cikin k’ashi da bargo, ga kuma dusan k’ank’ara da yake sauk’owa daga sama. 

Snow kawai tako ta ina. 

Yana shiga cikin motar kuwa yayi mata key, tare da cillata kan titi, kaitsaye ya nufi wani babban asibiti.

*JSC MEDICINA CLINIC MASCOW,* domin acanne zasu yi karatun nasu na yau. 

Jin k’aran tashin motar ne, yasa ta bud’e Idanunta dake lumshe.

Ahankali takai dubanta ga jikin window’n dakin nata,  wani irin sassanyar numfashi ta fesar, tare kuma da d’an yunk’urawa ta tashi ta zauna, Allah ya sani tana matukar shiga takura, azaman da takeyi ita d’aya acikin gidan, tana buk’atar waya sosai, amma bata da yanda zatayi, saboda tasani layinta ba kudi, shi kuwa gaba d’aga ya shareta, akullum yanayin abu tamkar baisan da zamanta acikin gidan ba.

Gashi tun da suka zo ko fita bata tab’a yi ba ko dan harabar gidan.

D’an k’aramin tsuka taja, saboda gaba daya ta gaji da kwanciyar da takeyi.

Ahankali ta sauk’o daga kan gadon, tare da zubo da k’afafunta k’asa.  

Kallon kanta tayi, saboda sanye take da wani dogon wando mai kauri, wanda ya kama jikinta sosai, sai kuma wani top long sleeve, shid’inma dai mai kauri ne sosai, still kuma sai wata riga jacket da ta d’aura akan shigar nata, kanta kuwa sanye yake da hulan sanyi.

D’an kwab’e fuska tayi, domin duk da irin shigar da tayi din, bai hanata jin sanyin da akeyi ba, Sam har yanzu bata saba da sanyin garin ba.

Wayarta dake kan bedside ta d’auka, sanin da tayi cewar Rayyern din ya fita ne, yasa kaitsaye ta nufo falon. 

Koda ta fito kuwa tv ta kunna, saidai gaba d’aya babu wasu channels, sai zallan na turawa, ba haka ta soba amma dole ta hakura, zama tayi tare da bud’e ledodin breakfast din da taga ya ajiye.

Chinese dishes ne, da kuma African dishes, kamar dai yanda ya saba yi musu order akoda yaushe. 

Fuskarta ta d’an kwab’e tare kuma da turo d’an k’aramin bakinta gaba.

Cikin shagwab’a tace.

“Ni gaskiya I’m tired da way’annan foodies din, always abu d’aya ni nagaji, Nigerian dishes nakeson ci, me zanyi da Chinese dishes niba 

mai kananan idanu ba.”

Ta k’are maganar cikin tura baki tamkar Rayyern din yana gabanta. 

Haka dai ta d’an tsakali abincin taci, domin kwata kwata bata iyacin chinese dishes din. 

Bayan ta kammala cin abincinne kuma, ta haye saman kujera ta kwanta. 

           *Kano Nigeria*

Abba da Mamy ne ke zaune, acikin katafaren falon nasu, inda Abban ke zaune akan sofa, Mamy kuwa na durk’ushe agabansa tana had’a masa coffee. 

Abban ne ya d’ago kansa ya kalli Mamyn, kana cikin kulawa yace.

“Ni kuwa Ruƙayyah ya labarin y’arki Jannart, tunda suka tafi  kun gaisa da ita kuwa?.”

D’agowa Mamyn tayi ta kalli Abban, domin dama kamar ya Sosa mata inda yakeyi mata k’aik’ayine.

Numfashi ta d’an fesar, cikin kuma rashin jin dadin abunda zata fadad’in tace.

“A’a ba muyi waya da ita ba har yau, kwata-kwata bansan me yake damun Rayyern ba, domin duk sanda zamuyi waya dashi, Idan nace ya bawa Jannart din wayan, sai yace min baya gida, To amma kuma nasan bazaimin k’arya ba, saboda dama ba zamanne ya kaishi ba, kasan Rayyern da sabgogi.”

Kai Abban ya jinjina, tare da gyara zamansa, cikin sanin halin Rayyern din yace.

“Ni ai banma tambayesa itaba, saboda nasan dole wani uzurin zai kawo, amma yanzu ke kinyarda da uzurin da yake baki, na cewar ko yaushe baya gida?  ai tunda yana da lokacin da zai iya dawowa gida yayi bacci yayi wonka ya sauya kaya, To yana da lokacin zama ya bata wayar ku gaisa,  bansan Meyasa Rayyern yake haka ba, da gasken gaske na fahimci cewar, zama da Mace ne bazai iya ba, saboda baisa abun acikin zuciyarsa ba shiyasa, amma babu komai na zuba masa ido, awannan karon zanga iya gudun ruwansa a gari irin Mascow mai yanayi na musamman da kuma mace kamar Jannart da kuma keɓantaccen wuri zan bishi da ido inga iyakar yaudar da zuciyarsa ke masa na cewa zai iya rayuwa ba mace.”

Ajiyar zuciya Mamy dake gefe ta sauk’e, cikin nazartar maganganun mijin nata kuma murmushi tayi tare da  cewa.

“Tabbas nima dai sau dayawa ina mamakin yanda yake cewa baya gida, amma da fari na yarda da maganganunsa, saboda kasan Rayyern bai cikayin k’arya ba, Dan banace baya k’arya ba kwata kwata arayuwarsa, saboda babu wani d’an Adam d’in da baya k’arya a dai wannan ƙarni namu, saidai na wani yafi na wani amman dan nasan karya ba dabiarsa bace,  amma gaskiya nidai kam jikina yayi sanyi, kada fa Rayyern yaje ya ajiye y’ar mutane ne, kawai ya fita harkarta.” 

K’wafa Abban yayi tare da d’aukan kofin coffee din nasa, cikin yarda da hukuncin da zuciyarsa ke yanke masa yace.

“Hmmmm zanyi magananinsa kuwa Idan har hakan ta kasance, saboda matarsa ce ko da ace bayasonta kuwa akwai, hakkinta da ya rataya awuyansa, amma ki barni dashi kawai.”

Abban ya k’are maganan yana me Kai kofin bakinsa. 

Mamy kuwa shiru tayi, saboda tasan idan abun da tayi yakini gaskiya ne, to kuwa Rayyern bai kyauta ba.

Ganin da tayi kuma Abban ya ci gaba da shan coffee dinne, yasa ta tashi ta wuce kitchine Dan k’arasa had’a abincin dare, domin bata son Ramadan ya dawo ya samu bata gama had’a abincin ba, kasancewar yanzu duk hankalinsa, ya koma kan hospital dinsu, tun safe Idan ya fita sai bayan magrib yake dawowa, hatta yau Weekend ma bai zauna ba.

             *Moscow.*

Gaba d’aya cikin d’akin da suke gwaji din, ya d’auki shiru babu abunda kakeji kuwa, sai k’aran na’urori da kuma sanyin, AC dake tashi duk da sanyin dake garin kuwa, amma yanayin aikin da sukeyi din yana tsananin buk’atar sanyi. 

Yanayin test din nasu kuwa ya  kasu kashi biyu ne, domin kanana daga cikin Doctors din suna gwada aikinne, akan robot ma’ana wasu halittun da aka kirkira ma tsakaita kuwa, akan halintun kananan dabbobi sukeyi nasu gwajin.

Yayinda manya manyan Doctors din, da suka amsa sunansu masu experience ke gwada, aikin akan mutane majinyata way’anda, suke fama da lalurar kidney.

Acikinsu kuwa harda Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, wanda ya bada gaba d’aya attension d’insa, akan wanda yakeyiwa aikin,  agefensa kuwa Dr. Sulaiman ne da kuma Dr. Nick Michel, wanda shima Babban Dr. ne ak’asar France.

Saidai duk da k’warewansa idanu ya zubawa, Rayyern alokacin da yake aikin dashen k‘odan.

Saboda su iya nasu mik’o masa kayan aiki ne.

Adai-dai lokacin da Rayyern ya kammala, dasa k’odan bayan ya d’inke cikin mutumin dake kwance, ne ya sauk’e wani irin nannauyar Ajiyar zuciya, tare kuma dasa hannu ya dafe saitin zuciyarsa.

“Yah Rabbi”

Ya k’ira sunan Allah abayyane, 

Cike da gamsuwa hadi da samun k’arfin guiwa, da yarda akan cewar Allah’n ne maiyi, shine kuma mai bada sa’a akoda yaushe shike rayawa ya kuma kashe. 

Kashe wutan theater room din da yake ciki yayi, da kansa kuma ya turo gadon da mutumin ke kwance har zuwa wani extra room, wanda acikinsa ne za’a jere way’anda akayiwa surgeryn, saboda a tabbatar da lafiyarsu. 

Kusan Atare Doctors din suka kammala aikin nasu. 

Yayinda zuciyoyinsu ke cike da alhinin, yanda way’anda sukayiwa aikin zasu tashi. 

Dukansu kuwa Fatansu shine, patients din su tashi lafiya batare da wata sabuwar matsala ba. 

Almost 1hour suna zaune cikin zullumi, saboda har yanzu babu d’aya daga cikin majinyatan da ya farka.

Ak’a’idan aikin nasu kuwa, wanda patient d’insa ya fara farkawa batare kuma da wata matsala ba shine yazo first. 

Cikin sa’a kuwa Patient din Dr. Rayyern Muhammad Mainasara ne ya fara bud’e idanunsa.

Inda kuma ya tashi garau batare da juyewan, brain ko haddasuwan wata matsalan ba, Dan Koda ya bud’e idanunsa acikin hayyacinsa yake sai yan kananun surutan da suke dole, bayan ƙaƙkanin lokaci kuma ya zama dai-dai.

Wani irin farinciki na ya cika zuciyar Rayyern, lokaci d’aya kuma ya shiga godewa Allah, saboda yasan bayin kansa bane, kowacce Nasararsa daga Allah ne.

Gaba daya Doctors din sun Taya Rayyern farinciki, tare kuma da mamakin k’warewarsa, musamman Envigelators da suka kasance consultant’s ne, saboda basu tab’a tunanin wani

Daga cikin Doctors din zai k’ware da sauri akan abun har haka ba, musamman ma shi da yake d’an Nigeria, basu tab’a tunanin shi zaiyyi wining ba. 

Domin faruwar hakan alamace dake, nuna musu babban nasararsa, shine kuma zai karb’i award na ban girma, tare kuma da certificate din da zai nunawa duniya, cewar shi babban likita ne, amintacce kuma yardajje akowacce k’asa. 

Tabbas Rayyern yaji dadin hakan azuciyarsa, domin ko babu komai zai kankaro mutumcin k’asar sa.

Alhamdulillah Sauran 

Patients dinma, da akayiwa operations din sun bud’e idanunsu, cikin sa’a kuwa kowanne da hayyacinsa ya dawo hakama nasu Dr Sadiq da sukayi gwajin su kan ƙananun dabbobi suma na Dr Sadiq ya tashi lfy bisa alamu gaba zai taka matakin da Rayyern ya taka a yau.

Sosai Doctors din sukayi kokari, harma way’anda suka gwada nasu akan mutum mutumi. 

3:00 pm Dai-dai suka kammala, duk wani abunda zasuyi, Ganin garin nata k’ara gumewa da snow ne kuma, yasa duk suka watse, kaitsaye Rayyern ya nufo gida.

Saidai kuma kafun ya k’araso saida ya tsaya, amasallaci yayi Sallan La’asar, kana ya biya Halal restaurant yayi musu takeaway, na Arab dishes kafun ya nufo gidan kaitsaye. 

Gaba d’aya yau din jin zuciyarsa yake wasai, badon komai ba kuwa saidan wannan nasarar daya samu.

Shigowa cikin falon yayi, tare da neman waje ya zauna, bayan ya zare jacket din dake jikinsa, kasancewar duk ta b’aci da dusan k’ank’ara dake dan sauka. 

Kallon d’an table din dake cikin falon yayi, rashin Ganin ledodin daya bari awajen ne kuma, yasa shi gane cewar Jannart din ta fito, domin ta hakanne kawai yake gane fitowarta, ko rashin fitowarta, kasancewar Idan ta fito takan kwashe ledodin takai kitchine.

Ledan daya shigo dashi din, ya d’auko tare da d’aukan chicken kebab ya soma ci, bai wani ci sosai ba ya ajiye, sai kuma pizza da drinks din daya d’ansha.

Bayan ya kammala ne kuma kaitsaye ya wuce bedroom d’insa, saboda yana so ya d’an watsa ruwa. 

Koda ya shiga bedroom din kayan jikinsa ya rage, tare da fad’awa bedroom ya sakarwa kansa ruwa.

Bayan ya fito awankanne kuma ya shirya, kansa cikin wasu Sabin riga da wando, tare da d’aura wata jibgegiyar rigar sanyi akai.

Still kuma car key d’insa ya d’auka, direct ya fice daga Cikin gidan. 

Daga gidannasa kuwa kaitsaye wani babban  shagon saida kaya ya nufa.

Mall Yevropeyskiy ya wuce kai tsaye dan yafi kusa da inda yake.

kayan sawa da kuma sweaters Chocolate’s

masu yawan gaske ya saya.

Har ya juya zai tafi ne kuma, idanunsa suka sauk’a akan wasu, womenswears masu azabar  kyau, wanda dukansu kaya ne da zasu tare sanyi.

Domin irin jibga jingan rigunan nanne da y’an k’asar suke sawa.

K’arasawa wajen clothes din yayi, tare kuma dasa hannunsa ya zaro wasu manyan jacket masu kyau, guda biyu ya ciro jacket din, sai kuma wasu wanduna masu kyau, way’anda ya ibosu sama da guda biyar haka nan yake kallonsu yana murmushin, a hankali ya lumshe idanunsa da alamun yana so  tuno wani abune.

Zuba su yayi acikin basket din dake hannunsa, kaitsaye kuma ya nufi wajen biyan kudi.

Koda akayi masa bill bai damu da yawan kudin ba, haka ya mik’a musu atm card d’insa suka cire.

Daga mall din kuwa, kaitsaye wajen sport ya nufa, saboda yana son dan motsa kafafunsa. 

Acan gida kuwa Jannart tunda ta k’ule d’aki bata sake fitowa ba, ko da kwanciyar ma ya isheta bacci ne ya d’auketa, ba ita ta tashi ba kuwa sai dab Sallan Magriba, bayan tayi Sallah ne kuma, ta d’auko wani book dinta, ta soma karantawa. 

Tana nan azaune har aka kira Sallah’n Isha, tana idar da Sallan kuwa ta haye kan gado, saboda sanyin garin ya sake yawaita.

Rayyern kuwa tunda ya fita bai dawo ba sai yanzun.

Ahankali ya bud’e murfin motar ya fito, tare da Kwaso manya manyan ledodin kayan daya saya, kaitsaye ya nufi cikin gidan.

Yana shiga cikin falon kuwa, idanunsa suka sauk’a akan, ledan abincin daya sayo d’azun, babu alaman an tab’asa.

Kauda kansa gefe yayi, for the first time kuma kenan daya d’aga, idanunsa ya kalli kofar dakin nata haka nan yaji kamar ba dadi.

Bakinsa ya d’an tab’e kana kaitsaye ya wuce dakinsa.

Yana shiga ya dire ledodin dake hannunsa, tare da wucewa toilet yayi wanka, bayan ya fito ne kuma ya shirya kansa, cikin wasu kayan bacci masu nauyi. 

Hayewa saman gadonsa yayi, tare da kunna laptop d’insa, ya soma receiving sakonnin da ake turo masa, kaitsaye sakon maganer’n Companynsa ya fara dubawa, inda yake shaida masa yanda abubuwan companyn suke tafiya, da kuma yanda manyan y’an kasuwa, ke zuba hannun jari acikin companyn, komai dai yana tafiya normal.

Domin Koda ya duba details na companyn, ya ga abun na tafiya akan dai-dai.

Iya sakon da yasan suna da muhimmanci yayi replying, sauran sak’onnin kuwa ko duba su, baiyi ba ya kashe laptop din nasa. 

Idanunsa ya d’an lumshe, dai-dai lokacin kuwa wayarsa dake gefe ta soma k’ara.

Ganin sunan Ramadan na yawo akan screen, din wayar ne kuma ya sashi d’agawa, tare da kara wayar akan kunnensa.

“Good Evening Hamma Rayyern, I hope you’re okay.”

Daga can b’angaren Ramadan din ya tambaya.

Idanunsa ya d’an lumshe tare kuma da gyara kwanciyarsa, Cikin kulawa yace.

“I’m Okay Ramadan, you? Ina Mamy da Abba?”

Murmushi Ramadan yayi tare da cewa.

“Same to you Hamma, Mamy da Abba kuma suna lafiya, Ina Aunty Jannart?”

Idanunsa ya d’an lumshe, kana cikin yin kasa da murya yace.

“Tayi bacci.”

Kai Ramadan ya jinjina, Jin kamar Hamman nasa agajiye yake ne kuma, yasa shi danne dariyarsa,  domin shi wani tunani na daban zuciyarsa ta basa.

“Okay Hamma gud night, but please ka gaishemin da Aunty Jannart Idan ta tashi.”

“To.”

Rayyern din ya fad’a agajarce, domin bayason Ramadan ya sake yi masa wata tambayar, daga haka sukayi sallama. 

Ahankali ya zare wayar daga kan kunnensa, tare da mik’ewa tsaye, ya k’arasa gaban fridge din dake cikin dakin.

Koda ya bud’e fridge din dan siririn tsaki yaja, saboda ganin da yayi babu ruwa aciki.

Gashi kuma yana buk’atar ruwa, saboda tunowa da yayi baisha maganinsa ba.

Kaitsaye ya nufi kofar fita daga cikin d’akin.

Dai-dai lokacin kuwa Jannart, da fitowarta daga, d’akinta kenan ta nufi kitchine, saboda Itama ruwan take da buk’ata.

Saidai kuma ganin duhu da tayi afalonne yasa ta, d’an tsayawa tare da soma laluben inda makunnin wutan falon yake.

Dai-dai lokacin kuwa Rayyern din ya fito, ko kad’an kuwa duhun bai tsorata shi ba, kasancewar yasan kan gidan shiyasa, baya wani buk’atar haske kaitsaye, ya nufi kitchine din.

Dai-dai ya kawo tsakiyar falon ne kuma, itama Jannart din ta iso wajen, wanda Jin motsin mutum da tayi, ya saka duk ta tsorita, juyowan da zatayi ne kuma sukayi karo, inda take kafad’ansa ya bugi hab’arta.

Wani irin k’ara ta saka tare da saurin, sanya hannayenta ta kama hab’ar nata.

Rayyern kuwa d’an ware idanunsa yayi, saboda bai tab’a kawowa aransa cewar tana cikin falon ba.

Jin yanda tayi k’ara ne kuma yasa shi, matsawa cikin sauri ya kunna, wani dan blue din hasken wuta dake cikin falon.

Idanunsa ya sauk’e akanta, wanda har yanzu tana rik’e da hab’ar nata, ta kuma rumtse Idanunta, da alama ya bugeta sosai.

Ahankali ya soma k’arewa shigar dake jikinta kallo, wata doguwar riga ce mai kauri, sai kuma hulan sanyin dake kanta, Yayinda dogon gashin kanta ya sauk’o kan kafad’unta. 

Duk da cewar hasken daya kunna din, bayi da karfi sosai, amma hakan bai hanashi kallon yanda fuskarta, tayi fayau ba, ga kuma shatin nipples dinta da suka bayyana, kasancewar gaban rigar nata akwai tsagu ne, kuma yasa yake iya ganin tsakiyan kirjinta, ma’ana tsakiyan breast dinta. 

Idanunsa ya mayar kan fuskarta,  tare da soma takowa ahankali ya shiga matsowa inda take. 

Dai-dai yazo kusa da ita ne kuma ya tsaya cak, kyawawan hannayenta ya kalla, akaron farko a iya tsawon rayuwarsu, ya sake matsowa kusa da ita sosai, har hakan ya bawa hucin nufashinsa dama sauk’a akan kirjinta.

“Meye?”

Ya fad’a da wata irin husky voice, din dake bayyana baccin da yakeji.

Jannart kuwa dake tsaye, Jin muryarsa da tayi akusa da ita ne, yasa ta saurin bud’e Idanunta da suka cika da k’walla, ta sauk’esu akansa.

Shek’in ruwan hawayen da idanun nata keyi ne, ya sashi jefa nasa idanun acikin nata, still cikin wata irin muryar daya kusan sata rud’ewa yace.

“Meye? Kinada damuwa ne? Me kikeso, uhummmm tell meeee.”

Yaja ƙarshen mgnar cikin kasalalliyar murya a tausashe

Hawayen dake cikin idanun nata ne suka gangaro, lokaci d’aya kuma tayi k’asa da kanta, tare da  had’e yatsun hannunta waje d’aya.

Shi kuwa Rayyern a hankali ya m..

Motsa kafafunshi ya danyi baya kaɗan domin ji da yayi bugun zuciyarsa na tsananta.

“Ruwa zan sha.”

Ta fad’a cikin wata muryar shagwab’a. 

Idanunsa ya d’an lumshe saboda wani fitinannen, kamshinta daya bugi hancinsa.

D’an matsawa gefe yayi, batare kuma daya ce mata komai ba, ya rab’a ta gefenta, wanda har hakan yasa jikinsa d’an gogan nata jikin,  kaitsaye kitchine din ya wuce.

Yana shiga kuwa ya bud’e murfin fridge, goran ruwa guda biyu ya d’auko, kana ya dawo cikin falon, Tana nan tsaye ayanda ya barta, saidai ta kuma rik’e hab’arta. 

K’arasowa wajen nata yayi, tare da mik’o mata goran ruwan, cikin silent voice yace.

“Take it, then go to sleep now, ko na jimiki ciwo ne?”

Yanayin yanda yayi maganan nasa ne cikin tauyawa da tausasawa, yasa duk taji tsikar jikinta na mimmik’ewa, Ahankali ta girgiza masa Kai, kana cikin sanyin murya tace.

“Zafi nakeji.”

Ta k’are maganar tana me nuna masa gefen lips dinta, da ya d’anyi ja.

Idanunsa ya d’an tsurawa Lips din nata, saboda yanda yaga Suna shek’i, d’an kawar da idanun nasa kuma yayi Ahankali,  kana cikin sanyi yace.

“Babu ciwo awajen, zuwa anjima zai daina zafi sannu ko sorry ban san dake a wurin bane.”

Yayi maganan yana me Kallon wuyanta.

 Ita kuwa Jannart jin abunda ya fad’ane ya sata karb’an bottle water’n, da yake mik’o mata tare da juyawa, cikin sanyi ta nufi bedroom dinta.

Da idanunsa ya bita, har saida ya ga ta shiga cikin bedroom dinta, kafun ya juya shima ya nufi nasa bedroom din. 

Yana shiga ya sawa kofar key,  maganinsa ya b’alla yasha, kana ya koma ya kwanta.

Koda ya lumshe idanunsa still k’amshin turaren nata yakeji, acikin hancinsa,  dan gyara kwanciyarsa yayi, batare kuma daya baya wani tunani daman shigowa, cikin kwakwalwarsa ba bacci ya d’aukesa.

Haka itama Jannart tana shan ruwan, kwanciya tayi cikin mintuna kad’an kuwa bacci ya dauketa. 

Acan b’angaren Ramadan kuwa Koda suka gama waya, da Hamman nasa Whatsapp dinsa ya shiga, Ganin Riyyam  da yayi a online ne, kuma yasa suka fara chat, ananne kuma ya turawa Riyyam  din numbern Rayyern, Wacce yake amfani da ita anan Mascow din. 

       Washegari.

Yau ya kama Sunday, tunda Rayyern ya bar gidan kuwa bai dawo ba,  domin can cikin garin ya shiga, Saboda akwai wasu Frnd’s d’insa da sukayi karatu tare, yaje sun danyi wani taro.

Jannart kuwa yauma ad’aki ta wuni, saboda duk kwana biyun da ciwon Mara take wuni shiyasa fitan ma, bai wani dameta ba duda bata jin hakan don al’adarta zata zo tayi mmkin hakan daya fara mata yanzu. 

                *** 

After five days ago.

Ahaka sukeyin rayuwarsu ta yau da kullum, komai na tafiyawa Rayyern yanda yake so, saidai zuwa yanzu gaba daya abubuwa sunyi masa yawa.

Haka ma Ab’angaren Jannart rayuwarta take ita d’aya, tun daga daren ranar kuwa bata sake saka Rayyern din a Idanunta ba.

Iyaka ya ajiye mata abinci tazo taci. 

Da hakanne kuma kowannensu yake sanin, lafiyar d’an uwansa ta haka suke sanin zaman juna.

Acan gida Nigeria kuwa, abubuwa duk suna tafiya yanda ya kamata, musamman a company babu wani mishkilan da ake samu dan Rayyern yana aikinsa da kyau ta yanar gizo-gizo kana ga amintattun ma’aikata, haka asibitin ma Ramadan yana iyaka kokarinsa sosai.

Ko yanzu dawowansu daga masallaci kenan, shida Abban nasa.

Bayan sun shigo cikin falon ne kuma, Ramadan din ya nufi sama.

“Ramadan.”

Abba ya k’ira sunansa.  

Jin kiran Abban ne kuma yasa  Ramadan juyowa, tare da dawowa ya zauna acikin falon.

Kallonsa Abban yayi kana Cikin sakin fuska yace.

“Karna manta ban Gaya maka ba, dazu iyayen Rayhanna sun kirani, sun kuma shaidamin cewar, sun baka auren yarsu, kamar yanda muka buk’ata, sannan kuma sun bamu lokaci, amma Idan son samu ne ayi bikin kafun watan Ramadan yazo.”

Idanu Ramadan ya dago ya kalli Abban nasa, cikin tsananin jin dadi da farinciki yace.

“Alhamdulillah Allah Nagode ma.”

Yayi maganar cikin manta cewar, agaban Mamy da kuma Abban yake.

Mamy dake gefe kuwa murmushi tayi, saboda ta sani dama Ramadan din yana son aure. 

Ramadan kuwa cikin zumudi ya kalli Abban nasa, tare da cewa.

“To Abba yanzu yaushe za’akai kudin sa rana da kayan lefe?”

Kallonsa Abban yayi, baice komai ba saidai aransa yana mamakin, yanda Ramadan din ke tsananin son Aure. 

Ramadan kuwa Ganin irin Kallon da, Abban keyi masa ne ya sashi mikewa da sauri, cikin kunya ya haura sama.

Ganin hakanne kuma yasa Abba yin dariya, kana ya mik’e ya wuce part d’insa, inda yabar Mamyn zaune itama tana dariya. 

Tana nan zaune kuwa Ramadan din ya sauko, cikin shirinsa tsab, inda yayi kyau acikin riga da wandon jumpern  dake jikinsa.

Kallonsa Mamy tayi, gaba daya farincikinsa abayyane yake, fuskarta dauke da murmushi tace.

“To yau kuma sai ina?”

Murmushi yayi, tare da Dan matsowa cikin yin kasa da murya yace.

“Ayyah Mamy am zanje gidansu Swe….” saurin gimtse bakinsa yayi, saboda ya kusa yin b’aran b’arama.

Mamy kuwa dariya tayi saboda Sarai, ta fahimci abunda yake nufi.

Kanta kawai ta girgiza, shikuwa cikin sauri ya juya ya nufi waje.

Yana shiga mota Ari ya bud’e masa gate, kaitsaye ya cilla hancin motar tasa waje, direct kuwa gidansu Rayhannan sa ya nufa, yana mejin wani irin shauk’i acikin zuciyarsa.

Koda ya isa gidan nasu tarba na mutumci ya samu daga wajen mahaifiyar Rayhannan,   bayan Rayhannan ta fito ne kuma ya tsura mata idanu, baya ko k’yaftawa, kasancewar ta mai kunya ne kuma yasa ta sadda kanta k’asa.

Asanyaye tace.

“Please ka daina kallona hakanan.”

Murmushi yayi tare da gyara zamansa, cikin jin dadi yace.

“Tayaya zaki hana mutun kallon Matarsa? Ke dinfa yanzu gab kike da zama tawa.”

 

Murmushi tayi tare dasa hannu ta rufe fuskarta.

Haka dai suka sha hirarsu kafun daga bisani yayi mata sallama ya tafi.

Daga gidansu Rayhannan  kuwa gida ya dawo.

Yana zuwa kuwa ya samu Baba Maud’o zaune abakin gate.

Da sauri ya k’araso wajen Baba Maud’on, cikin sakin fuska da dokin da har yanzu bai gama sake shiba yace.

“Baba Maud’o an bani Rayhanna, d’azun Abba yake fadamin.”

Murmushi Baba Maud’o yayi tare kuma da Kallon Rayyern din, jikin taya shi murna yace.

“K’warai kuwa Ramadan nasani, Abbanku ya fad’amin na tayaka murna sosai.”

Murmushi mai kama da Dariya Ramadan din yayi, tare da juyowa ya fuskanci Baba Maud’o, kana ransa asake yace.

“Baba Maud’o na kasa b’oye farinciki na, hankalina ya kwanta, yanzu bani da wani sauran fargaba,  kana min addu’a please Baba Maud’o, Allah yasa albarka acikin had’innan.”

Murmushi Baba Maud’o yayi wanda har saida sautin ta, ya fito fili cikin sakin fuska yace.

“Insha Allah Ramadan, addu’a kuma kullum inayinta, Allah yasa matarka ce ya kuma kawar da duk wani fitina.” 

“Ameen Ameen.”

Ramadan din ya amsa, tare da mikewa kaitsaye ya nufi cikin gidan nasu, kasancewar dare yayi kuma bacci yakeji. 

Washegari.

       *Mascow*

Ahankali yake driving motar da yanayinsa, dake bayyana tsananin gajiyar da yake d’auke da ita da yunwa.

Kaitsaye gida ya nufa, dai-dai ya hau wani titi ne kuma, wayarsa dake gefe ta soma kara alamun shigowar kira,  share wayar yayi, kamar bazai d’aga ba kuma sai ya d’auki wayar, Ganin sunan Abbansa ne kuma ya sashi d’aga wayar da sauri.

Tare dayin Sallama.

Daga can b’angaren Abba ya amsa.

Shikuwa Rayyern din cikin sanyi yace.

“Abba yasu Mamy da Baba Maud’o.”

Abba dake zaune afalo gyara zama yayi, tare da cewa.

“Duk Suna lafiya, Mamynka tace agaisheka, ya Jannart take?”

sake gyara zaman wayar akan kunnensa yayi, kana cikin nutsuwa yace.

“Lafiyanta Qalau.”

Kai Abban ya jinjina tare da cewa.

“Masha Allah To bata wayan mugaisa.”

Jin abunda Abban ya fad’ane kuma yasa shi, danna Horn din motarsa, cikin dan ladabtar da murya yace.

“Abba bana gida, amma yanzu nake kokarin komawa.”

Daga can b’angaren kuwa jin Karan Horn din mota ne, yasa Abban yarda da abunda Rayyern din yace, cikin jaddadawa yace.

“Shikenan babu damuwa, Idan ka koma saika had’ani da ita.”

“To Abba Allah Yasa kada na manta.”

Jin abunda Rayyern din ya fad’ane kuma, yasa Abban yin shiru, Cikin d’an yanayin bacin rai yace.

“Rayyern!”

Da sauri ya amsa da

“Na’am Abba.” domin jin yadda Abban ya kirashi ba wasa

“Rayyyern!!”

Abban ya kuma kiranshi a dake.

“Na’am Abba.”

Still Rayyern din ya sake amsawa cikin fargaban umarnin da za’a bashi ko fada

Abban kuwa ransa ab’ace yace.

“Rayyern ni kake cewa, Allah yasa kada ka manta hadani da matarka?”.

Da sauri ya jujjuya kansa tamkar yana gaban Abban.

Shi kuwa Abba cikin dakile murya yaci gaba da cewa.

“Bansan Wacce irin rayuwa kakeso kayi da yarinyar nan ba, Wacce irin rayuwace haka Rayyern, Jannart matarka ce fa, wallahi wallahi Allah saiya tambayeka, akan hakkinta, baka kyautawa Rayuwarta Rayyern, akan ka afarayin aiki da kasuwanci da karatune? ko kaine kawai ma’aikaci a duka duniyar nan? Meye ka d’auki kanka da bazaka kula da matarka ba? kasani ko yau ka mutu Allah zai kama ka, da rashin sauke nauyinta dake kanka, kuma kasani ban baka ita ka tafi da ita don kayi ta wofantar da ita ba,  tayaya zakana irin wannan sakacin, kullum Kai baka gida, baka da lokacinta kenan?”.

Lips d’insa ya d’an taune, cikin sanyin murya yace.

“Abba kayi hakuri…”

“Nayi hakuri dame Rayyern?”.

Cikin girmamawa yace.

“Abba kayi haƙuri akan komai ma na tuba”.

Cikin fada Abban yace. “Bani zaka bawa hakuri ba kasan Wacce zaka bawa hakuri, yarinya tana zaune ak’ark’ashinka amma baka San abunda ya dace ba, tunda ta tafi batayi waya da kowa ba, ka kulleta awaje daya, sannan yanzu Ina maka magana, kana cewa wai Allah yasa kada ka manta,  shikenan yayi maka kyau Allah yasa ka manta ɗin!!!”.

Abban ya fadi maganan atsawace, kuma cikin fushi lokaci daya kuma ya katse kiran.

Da sauri Rayyern yabi wayar da kallo, lokaci daya kuma yaji duk zuciyarsa babu dadi, ajiye wayar agefensa yayi, domin dai-dai lokacin ya iso gida.

Yana gama dai-dai-ta parking, ya bud’e murfin motar ya fito.

Hannunsa rik’e da waya da kuma, ledodin takeaway din da yayi musu ya nufi cikin falon gidan. 

Yana shiga kuwa ya zauna akan daya daga cikin kujerun falon.

Wayarsa ya dauka ya sake dialing numbern Abban.

Har saida wayan ta kusa katsewa kuwa, kafun Abban ya d’auka.

Jin Abban ya d’auki wayarne kuma yasashi, kwantar da murya cikin sanyi yace.

“Dan Allah Abba kayi hakuri, zanyi yanda kake buk’ata.”

Daga can b’angaren Abba azafafe yace.

“Hakurin me kake bani ne  Rayyern?.”

Rayyern din kuwa sanin halin Abban nasu, Idan har yayi fushi ne yasa shi, sake yin k’asa da murya cikin tausasa harshe yace.

“Naji Abba kayi hakuri Dan Allah! In sha Allah zan kiyaye zanyi yadda kukeso”.

Idanunta ta bud’e da sauri, saboda jin muryarsa da tayi, da dukkan alama kuma tasan waya yakeyi.

Saurin tashi daga kwancen da  take tayi, tare da Kai dubanta ga kofar dakin nata.

Duk yau zaman gidan bayayi mata dadi, saboda kadaici, ga kuma wani irin masifaffen kewa daya cika zuciyarta, tana matuk’ar son tayi magana da Abba Kabir dinta, wannan dalilin yasa ta yanke cewar, Idan ya shigo yau din zata rok’esa aron waya. 

Da sauri ta zuro da k’afafunta k’asa, batare kuma da ta damu da shigar riga da wandon dake jikinta ba, kaitsaye ta nufi falon, kanta sanye da hulan sanyi, sai kuma wani bedroom shoe mai kyau.

Riga da wandon dake jikin nata kuwa, bak’aramin bayyana shape dinta sukayi ba, duk da cewar Suna da kauri, amma sunyi mata kyau sosai, Dan saita fito kamar irin y’an matan turawa dinnan, domin saboda tsabar zaman waje d’aya, har wani yellow da ja skin dinta yayi tsabar fari.

Ahankali ta bud’e kofar dakin ta fito.

Tana fitowa kuwa yana sauke idanunsa akanta.

Saurin yin kasa da kanta tayi, tare da karasowa cikin falon.

Shikuwa tun fitowarta ya kasa d’auke idanunsa, daga kallonta saidai fuskarnan tasa  babu alaman Murmushi.

Ahankali ta zauna akan carpet, tare da nannad’e k’afafunta.

Rayyern din kuwa Ganin ta zauna ak’asan san ne, yasa shi gyara zamansa, tare da kwantar da murya cikin ladabi yace.

“Abba gatanan na shigo cikin gidan.”

Yana gama fadin hakan ya mik’a mata wayan.

 

Ai kuwa kaman jira take har hannayenta, na rawa  wajen amsar wayar. 

Tana karawa akan kunnenta, tayi Sallama.

Abban ne ya amsa mata, cikin kulawa da kuma sakin rai yace.

“Jannart ya kike ya gida, fatan komai da komai lafiya.”

Ajiyar zuciya ta sauke cikin tsananin jin dadi, tace.

“Lafiya k’alau Abba yasu Mamy, Ramadan da Baba Maud’o.”

“Duk Suna lafiya, gama Mamyn naku anan kusa bari na bata.”

Cikin jin dadi Jannart din ta jinjina kai, Jin Mamy ta karb’i wayanne kuma yasa ta karyar da wuya, cikin muryar shagwab’a tace.

“Ina wuni Mamy.”

“Lafiya kalau Jannart dinmu, wallahi munyi kewarki sosai, fatan dai kina nan lafiya.”

Mamyn ta tambayeta cike da kulawa, hadi kuma dajin dadin samun Jannart din.

“Nima nayi kewarku sosai Mamy, nayi kewarku sosai da sosai garin ba dadi sam Mamy, Ina Ramadan?”

“Ramadan yana can wajen aiki, kullum saiya tambayeki.”

Mamyn ta fad’a tana nazartar kalmar Garin ba dadi sam da Jannart ɗin ta fadi, shadar zaman doya da manja sukeyi kenan.

Jannart kuwa Kai ta kwantar kana cikin sanyi, tace.

“Ayya Mamy kice ina gaishe sa, Idan kunyi waya da Riyyam nsra ma kice ina gaishesa.”

“To Jannart Insha Allah zasuji, amma Ina dai babu wata matsala kam?”

Kai Jannart din ta d’an sunkuyar, cikin tausasa murya tace.

“Eh Mamy babu komai.”

“Masha Allah haka akeso ai, amma dai kina kulawa da sanyi, Dan naji ance sanyin garin daban yake dana kowacce k’asa.”

“To Mamy.”

Jannart din ta amsa,  daga hakane kuma sukayi sallama da Mamyn, sosai Jannart taji dadin wayar da sukeyin, musamman taji zuciyarta tayi sanyi.

Acikin kaso 50 na damuwarta duka sun kau, dama matsalarta kewa ne kawai.

Ahankali ta zare wayar akan kunnenta, tare da mik’o masa.

Idanunsa dake alumshe ya bud’e tare kuma dasa hannu ya karb’i wayar.

Itakuwa Jannart maida kanta k’asa tayi, tare da sauke idanunta akan yatsun k’afarsa, wanda taga yana d’an motsa su Ahankali.

Idanu tad’an zubawa yatsun nasa, bakinta kuwa Ahankali yake motsi da alama, wani abu take son fad’a.

Rayyern dake zaune asamanta kuwa, Akasalance ya Kai dubansa gareta, karab kuwa idanunsa suka sauk’a akan saman kirjinta,  kasancewar rigar da ta saka din mai d’an fad’in wuya ne, shi yasa saman kyawawan breast dinta suka bayyana.

Janye idanunsa gefe yayi, tare da maida kansa ya kwantar ajikin kujera.

Itakuwa Jannart d’agowa tayi ta kalleshi, Ahankali ta d’an had’e hannayenta waje d’aya.

Cikin daddad’an murya da kuma sanyin yanayi, mai kama da rok’o tace. 

“Ummmm… Dan Allah kakiramin Abbana!!!”

Ta k’are maganan cikin seizing voice, lokaci daya kuma Idanunta suka kawo ruwa.

Yanayin yanda yaji sauti da Amon muryar nata ne, kuma ya saka shi bud’e idanunsa, tare da Kallon cute face dinta.  

Ahankali ya mik’o mata wayar,   ba tare kuma daya ce komai ba, ya maida kansa.

Itakuwa Jannart cikin jin dadi ta mik’e tsaye, da wayartasa ahannunta kaitsaye ta nufi dakinta.

Tana shiga kuwa tayi dialing numbern Abba Kabir. 

Cikin sa’a kuwa bugu biyu wayar ta shiga. 

Rayyern kuwa Ganin ta shiga daki ne, ya sashi tashi shima ya wuce nasa d’akin, bayan yayi al’wala ne kuma ya wuce masallaci.

Jannart Kuwa tanajin Abba Kabir ya d’aga kiran, ta kara wayar akan kunnenta, lokaci daya taji tamkar zatayi kuka, cike da matsanancin kewa, batare da ta iya amsa sallaman da yayi mata ba tace.

“Nayi kewarka sosai Abbana.”

Daga can b’angaren Abba Kabir kuwa, Jin muryar Jannart d’insa ya sashi lumshe ido, shima cike da tsananin kewa hadi da jin dadin, kiransa da tayi yace.

“Muma haka Jannart dina, munyi kewarki sosai, ya Mascow din, fatan duk kuma nan lafiya.”

“Lafiya K’alau Abbana, yasu Aunty Dijat dasu Hafeez, Allah nayi kewarsu sosai, har ma da Daddy na.”

Ta kare maganan cikin shagwab’a.

“Duk suna nan lafiya Jannart, suma kuma sunyi kewarki, Ina Rayyern din?”

Abba Kabir din ya tambaya, Dan waigawa bayanta tayi, kamar Wacce takesa ran ganinsa sai kuma tace.

“Yana lafiya Abba.”

Kai Abba Kabir din ya jinjina,  cike da jin dadin jin muryoyin juna, haka suka sha  hirarsu,  bayan sun kammala wayar ne kuma ta tashi tayi Sallah.

Shikuwa Rayyern bashi ya dawo gidan ba, saida yayi sallan Isha, Koda ya shigo cikin falon, zama yayi akan sofa tare da d’aukan, abincin daya shigo dashi ya danci kad’an.  

Bayan ya kammala cin abincinne kuma ya mik’e tsaye, direct dakinsa ya wuce, yana shiga ya soma rage kayan dake jikinsa.

Wani fari kal din towel ya d’aura akan waist d’insa, tare da nufar toilet kaitsaye.

Duk da cewar yana jin gajiya sosai ajikinsa, amma hakan bai hanashi yin wanka anutse ba, yana fitowa daga wankan direct gaban dressing mirror d’insa ya nufa.

Wani d’an k’aramin towel ya d’auka, tare da soma goge jikinsa dake jik’e da ruwa, sosai gargasan jikin nasa suka kwanta lub,  ga wani hasken fatarsa daya sake bayyana.

Body lotion kawai ya shafa ajikin nasa, sai kuma turarensa mai dadin kamshi, bayan ya gama shafa mai dinne kuma, ya saka wani wandon boxer ajikinsa.

Duk da sanyin da ake yi kuwa, haka ya nufi kan gadonsa ya kwanta, batare da ya saka riga ko rufe kyakkyawar surar jikinsa ba.

Kwanciyar rub da ciki yayi tare da jawo laptop dinsa, ya soma dannawa. 

Acan b’angaren Jannart kuwa, Koda ta idar da sallan nata, kwanciya tayi akan gado, zuciyarta cike da nishadi, saboda duk wani damuwan dake zuciyarta ya kau, yau tayi waya da Abbanta da kuma su Mamy, taji komai yayi mata wasai.

Gyara kwanciyarta tayi, juyawan da zatayi ne kuma Idanunta suka sauk’a, akan wayar Rayyern da ta ajiye akan bedside drawer dinta wayar na kawo haske alamun kira. 

Da sauri ta d’an dafe goshinta, saboda ita gaba daya ma ta manta da batun wayar. 

Sanin da tayi cewar zai buk’aci wayarne, kuma yasa ta tashi daga kwancen, wasu takalman ta saka tare da miƙa hannu zata jawo wayar.

Garin hakane ta amsa kiran.

Juyo fuskar wayar tayi da niyar taga wake kira sai taga ashema ta amsa kiran.

Sabon number ne, da sauri ta kalli rubutun dake ƙasan number Ethiopia ta faɗa cikin nazari, alamun daga can kiran yake.

Kiran na gab da sinkewa ta amsa da addu’ar ko Riyyam-nsra ne,

Da sauri ta kara wayar a kunne jin muryar Riyyam-nsra yana cewa.

“Asssalamu alaikum, Hamma Rayyern”.

Cikin sakin fuska da jin daɗin tace.

“Wa alaikassalam Riyyim”.

“Lahh My Aunty”.

Riyyam-nsra ya faɗi cikin jin daɗi da so da mutuntaka.

“Na’am Riyyam-nsra yasu Mammy da Zaytoon.”

“Duk suna lfy, mu Aunty nayi kewarku, kullum ina son in kiraku bani da number ku Hamma  Radaman ɗan wulaƙanci sai yau ya turo min”.

Hanyar fita ta nufa tare da cewa.

“Allah sarki autan Mammy i miss u so much wlh”.

Cikin jin daɗi yace.

“wlh na fiku kewa gaba ɗaya yanzu Ethiopia ta daina min daɗi ma yaseen”.

Ya ƙare mgnar yana shiga falon Mammynsa.

Ita kuwa Jannart

 murd’a handle din kofar tayi ta buɗe kana ta fito kaitsaye ta nufi dakinsa. 

Suna masu ci gaba da mgn da Riyyam-nsra.

Ahankali ta murd’a handle din k’ofar d’akin nasa, tare dasa K’afarta ciki.

Cikin wani irin yanayi t…!

Back to top button