Uncategorized

Tubali Book 2 Page 6 Complete Novel

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

Ahankali Jannart ta bud’e Idanunta dake lumshe, tare da d’an muskutawa ta gyara zamanta, wanda kuma tayi hakanne saboda ganin, an bud’e k’ofar jirgin, har ma wasu daga cikin mutanen dake cikin  jirgin, sun fara fita. 

Kasancewar a (VIP) very important people SECTION sukene shiyasa kuma ba suyi fitan farko ba.

Ahankali ta zare belt d’in dake d’aure agefen cikinta, tare kuma da mik’ewa tsaye, y’ar k’aramar hand bag d’inta ta d’auka, dai-dai lokacin kuma shima Rayyern d’in ya mik’e tsaye. 

Hakan yasa ya zamana tana gaba shi yana biye da ita abaya.

Tafiya suke Cikin nutsuwa, wanda kuma hakanne ya bashi daman k’arewa shape din bayanta kallo, kasancewar doguwar rigan English wears ne ajikinta, mai d’an santsi da kuma sharara, bak’aramin kyau kuwa rigar tayi mata ba.

Ahankali ya janye idanunsa daga kallonta, tare da gyara zaman face mask din dake fuskarsa. 

Dai-dai lokacin kuma suka kawo bakin, k’ofar fita daga cikin jirgin.

Ahankali Jannart ta sak’o jiki da kuma k’afarta ta dama waje.

Wani irin masifaffen sanyi ne taji ya shigeta, wanda har saida yasa ta manne hannayenta duka akan kirjinta, cikin kuma yanayin mamakin kyaun da garin ke dashi, ta soma jujjuya Idanunta tako ta ina. 

“Yah Allah.”

Ta fad’a adai-dai lokacin da ta sauk’e idanunta, akan tsarin burgewa da akayiwa, babban filin airport din, wanda ayanzun yake tamkar rana, saboda tsananin hasken wuta, daya cika ko’ina nawajen, domin matuk’ar ba sama ka kalla ba, ba zama ka tab’a cewa dare yayi ba.

Idanunta ta d’an lumshe Ahankali, tare da k’ara sanya hannayenta ta matse jikinta.

Acikin yanayin nata na hakane kuma, ta k’arasa sauk’owa daga Kan steps din.

Rayyern dake bayanta kuwa, idanunsa ya zuba mata, lokaci d’aya kuma ganin yanda take ta matse jikinta, yasa shi fahimtar cewa sanyi takeji.

Wanda azahirin gaskiya shi sanyin ma, dad’i yayi masa domin haka yakejin kowani kofar gashin jikinsa na bud’ewa.

Ahankali ya k’arasa sauk’owa daga kan steps din jirgin, dai-dai lokacin kuma sauran Doctors d’insa, way’anda already sun riga da sun sauk’o bisa jagorancin Dr Sulaiman, suka k’araso inda yake.

Hannayensa ya zuba acikin aljihun wandon jeans din dake jikinsa.

Tare da d’an soma takawa ahankali ya matsa, kusa da inda Jannart d’in ke tsaye.

“Muje.”

Ya fad’a cikin yin k’asa da murya, batare kuma da ya jirata ba ya soma tafiya.

Ganin hakanne kuma yasa ta rufa masa baya, kaitsaye suka nufi Cikin airport din, inda ananne zasu d’auki akwatunansu, suna gaba sauran Doctors din na biye dasu abaya.

Sudai mamaki da kuma tarin tambayoyi ne, kwance acikin zuciyarsu, saboda wannan ne karo na farko da suka ga, Ogan nasu da wata Mace agaba d’aya tsawon rayuwarsu, macen ma kuma da basusan wacece ba, kasancewar akwai face mask akan fuskarta, shiyasa har yanzu babu wanda yaga fuskarta, hasali kuma duk acikinsu basu da labarin auren Rayyern din sai Dr Sulaiman kadai ne ya sani, sun kuma san cewar kwata-kwata Dr Rayyern ba ma’abocin ta’ammali da mata bane, baya neman mata, to wacece ita awajensa?

Tambayar dake cin zuciyarsu kenan, wanda kuma basu da amsarta. 

Ab’angaren Jannart kuwa sake matse jikinta takeyi sosai, domin duk yanda tayi tunanin sanyin garin ya wuce nan, wani irin masifaffen sanyi ne, dake ratsa cikin k’ashi da bargo, musamman ga ita da take da asma, gaba d’aya bata son sanyi, saboda had’ari ne ga rayuwarta. 

Koda suka k’arasa cikin wajen kuwa, duk suna tsaye lambobin trolleys dinsu ke fitowa.

Saida kowa ya gama d’aukan nasa ne kuma, Rayyern din ya juyo ya kalli Jannart wanda Idanunta suka sanja launi, ga kuma wani irin sautin numfashi da yaji tana fitarwa. 

Hannunsa ya mik’a Ahankali ya k’arbi trolley nata, juyowa yayi ya kalli d’aya daga cikin Doctors din.

“Sadiq kira mana taxi.”

“To.”

Sadiq din yace, kana cikin girmamawa ya fita zuwa babban compound din, Airport din.

Sud’inma kuma fita sukayi, dai-dai lokacin kuma Sadiq din ya nuna musu wasu taxi guda biyu.

Wanda ya taro musu, kasancewar acikin airport dinma, masu taxi ne kaca-kaca.

K’arasawa jikin taxi din sukayi.

Rayyern ne ya bud’e k’ofar d’aya daga cikin taxi din ya shiga, Ganin hakane kuma yasa Jannart ma bud’ewa ta shiga da sauri, Dan acewarta ayanzu bata buk’atar wani jira har sai anbata izinin shiga,  saboda uban sanyin da takeji, tana k’ara wasu y’an mintuna awaje zai illatata.

Ganin su Rayyern din sun shiga cikin mota ne kuma, yasa sauran Doctors dinma duk suka shiga ragowar taxi din.

Kaitsaye hanyar wani  babban hotel din dake cikin garin suka nufa, bisa umarnin Rayyern.

Mik’awa kan titi da sukayi ne kuma yasa Jannart, kwantar da kanta ajikin kujerar motar, tare kuma da Ware dan siririn mayafin Kanta ta rufa ajikinta.

Atunaninta zama a cikin motar zai rage mata sanyi, saidai kuma taji sab’anin haka,  saboda acikin motar harda AC.

Idanunta ta d’an rumtse tare kuma da sake matse jikinta, cikin zuciyarta tace.

“Kai amma way’annan mutane akwai mayu, duk wannan uban sanyin bai ishesu ba, har sai sun had’a da AC.”

Rayyern dake zaune agefenta kuwa, gaba d’aya duk yana lura da yanayinta, saidai yi yayi kamar ma baisan cewa tana jin sanyin ba. 

Tafiyar mintuna kad’an sukayi kuwa, sai gasu agaban wani had’add’en hotel mai tsananin kyau da tsari  *Brosko hotel Arbat Mascow.*

Idanu Jannart ta d’an zaro ta cikin glass din window’n motar, tare da  Kallon dogon  ginin  beneyan hotel din, da bazata tab’a iya misalta kyawunsa ba. 

“Kijira ni anan.”

Rayyern din ya fad’a adai-dai lokacin daya bud’e murfin motar ya fice. 

Haka ma sauran Doctors din duk sun fito, kaitsaye cikin babban hotel din suka nufa, bayan Rayyern ya sallami sauran masu taxi din.

 Kaitsaye cikin katafaren hotel

Din da kaitsaye za’a iya kiransa da Aljnnar duniya suka nufa.

Komai dake cikin hotel din mai kyau ne, kuma abun burgewa, duk da cewar dare ne amma kuma saboda yawan jama’ar dake ta zirga zirga awajen, da kuma wadataccen hasken da ke wajen, yasa wajen ya zamo tamkar rana.

Kaitsaye reception suka nufa, wanda kuma Rayyern dinne keyi musu jagora, kasancewar garin shi ba bak’onsa bane, sab’anin sauran Doctors din nasa, da babu wanda ya tab’a zuwa acikinsu.

Ayau kuma suka sake tabbatar da cewa, kyawun Mascow din ya wuce tunaninsu.

Koda suka k’arasa reception din Rayyern ne yayi musu duk wani abu daya dace, d’akuna 5 ya kama musu, kowannensu da d’akinsa, kud’i ya kashe sosai, domin duk wani abu daya san zasu buk’ata, saida ya umarta da a basu.

Bayan ya sallamesu ne kuma ya juyo, tare da nufo inda Taxi din nasu take.

Dai-dai lokacin kuwa Jannart take k’ara maida hankalinta, akan had’add’en ginin hotel din Brosko Arbat Mascow din, wanda aka k’awata ko ina d’insa da farin haske, ga kuma wasu irin followers wanda ita arayuwarta, bata tab’a ma ganin irinsu ba,  domin furannine masu kyau da walwali.

Tsirarun mutanen dake wucewa akan titin ta kalla, kowannensu sanye yake da manya manyan kayan sanyi, daga sama kuwa dusan k’ank’ara ne ke d’an sauk’owa.

Duk da hakan kuwa mutanen wajen rayuwarsu suke normal, da dukkan alama sun saba da yanayin nasu.

Ahankali ya bud’e murfin motar ya shigo.

“Go.”

Ya fad’a yana me gyara zamansa akan kujeran, hakanne kuma yasa Jannart din d’ago Kanta ta kalleshi.

Karab kuwa suka had’a idanu dashi, janye Idanunta tayi daga kallonsa, tare da sunkuyar da kanta k’asa.

Shikuwa Rayyern y’atsun hannunta ya kalla, dai-dai lokacin kuwa driver’n taxi din yaja suka tafi. 

Tafiya sosai sukayi  kafun suka iso gaban wani dan madaidacin gida, adai-dai wani babban k’ofa wanda gabansa ke cike da shuke shuken furanni mai taxi din ya tsaya.

Wanda hakanne kuma yasa Jannart d’ago kanta, Ahankali ta soma k’arewa wajen da ta gansu din kallo.

Wajene maitsananin kyaun gaske, wanda yake dauke da had’add’un gidajen, da kusan tsarinsu da yanayinsu ya kasance iri d’aya.

Bud’e murfin motar da taga Rayyern yayi ne kuma yasa ta fitowa itama. 

Idanunta ta lumshe ahankali, saboda sanyin da taji ya sake shiga jikinta, saurin d’an takure jikinta waje d’aya tayi, saboda zama ta iya cewa, sanyin wajen ya banbanta dana wasu wajaje dake cikin garin, kasancewar arean kowani gida kewaye yake da wasu irin shuke shuke masu Bala’in kyau. 

Rayyern kuwa sallaman mai taxi din yayi, bayan ya d’auki trolley d’insa ne kuma, kaitsaye ya nufi jikin wannan  gidan, da Jannart ta kasa d’auke idanunta akansa, domin hakanan take ganin ginin tamkar zane. 

Ganin kuma Rayyern din na kokarin wucewa, ya barta ne yasa cikin sauri, ta d’auki nata jakar itama, tare da nufan inda taga yabi.

Ahankali take bin bayansa, Yayinda shi kuwa yake k’ara kutsa kansa cikin gidan.

Dai-dai sun iso tsakiyar gidanne kuma, idanunta suka sauk’a akan wani, makeken swimming pool, wanda aka k’awatasa da wani irin ruwa, gefe da gefensa kuwa wani wuta ne me fidda kala kalan haske, sosai swimming pool din yayi mata kyau.

Daga can gefen swimming pool din kuwa, wasu jajayen furannine masu kyaun gaske.

Itakam batasan  dame zata tsara had’uwa da kuma kyaun gidan ba.

Atakaice ma ganinta take acikin wata duniya sabuwa. 

Isarsu jikin wata k’ofa ne kuma yasa, Rayyern d’an tsayawa, tare da d’aura Hannunsa na dama akan k’ofar.

Wasu na’urori dake jikin k’ofar ne suka d’auki hoton y’an yatsun hannunsa,  bayan da kamar second 5 kuwa sai ga k’ofar glass din ta kawo haske.

“Wellcome back Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara.”

Wata y’ar siririyar murya ta fad’a, Wacce  ta fito daga cikin d’an wani na’ura mai kaman camera dake jikin k’ofar.

Na’urar na gama fad’in haka kuwa, lokaci d’aya k’ofar ta bud’e.

Idanu Jannart dake tsaye abayansa, ta d’an zazzaro saboda itakam bata tab’a ganin, security door irin haka ba.

Rayyern kuwa tura kansa ciki yayi, batare kuma da ya juyo ya cewa, Jannart din k’ala ba.. 

Jannart dake tsaye kuwa Ganin kofar na kokarin rufewa ne, yasa ta jan trolleynta cikin sauri ta shige.

Ahankali ta jefa k’afarta na dama akan wani masifaffen carpet me shegen laushi.

Da sauri ta kalli k’asanta, saboda yanda taji k’afafunta na kokarin nutsewa acikin carpet din. 

Ajiyar zuciya ta sauk’e tare kuma da d’agowa, ta sauk’e idanunta, acikin babban falon da ta samu kanta.

Falone daya amsa sunansa falo, haka kuma falo ne da aka zubawa dukiya mai tarin yawa acikinsa. 

For the first time da ta somayin k’auyanci arayuwarta, domin zata iya cewa bata tab’a Ganin falo mai kyaun wannan ba.

Komai dake cikin falon na yellow and milk colour ne, more especially cushions din falon, way’anda suke da matuk’ar kyau.

Kasancewar kuma ginin falon nada tsawo ne, yasa aka k’awata jikinsa da wallpaper, brown, milk and golding colour, sai kuma wasu had’add’un cottons masu masifar kyau, kasancewar cottons din farare, shiyasa aka d’an tsara baki bakinsu da brown style.

Atsakiyar falon kuwa, wani d’an madaidaicin carpet ne brown and milk colour, sai kuma brown table da aka d’aura akansa. 

Daga can sama kuwa wani abune mai kaman glass babba, wanda ya d’an sako kansa cikin tsakiyar falon. 

Sai kuma babban tv plasma dake aje akan wani glass mai kyaun gaske.

Daga can gefe kuwa wani d’an abune mai sheki wanda aka killacesa acikin rose,  sai kuma na’urar sanyaya d’aki, da kuma wanda yake saka d’aki d’umi.

Daga can gefe kuwa two bedrooms ne, sai kuma kitchine and dining table. 

Jannart dake tsaye kuwa Idanunta ta zubawa cikin falon bata ko k’yaftawa, Yayinda acikin ranta take mamakin irin tarin dukiyan, da aka kashe wajen k’awata falon.

Rayyern kuwa kaitsaye d’aya daga cikin bedrooms din ya nufa.

Ganin hakanne kuma yasa Jannart, ajiye trolleyn ta cikin d’an yanayin matse jikinta, ta zauna akan d’aya daga cikin kujerun falon, tayi hakanne kuma saboda batasan inane zata sauk’a amatsayin masauki ba.

Shiko Rayyern koda ya shiga kayan dake jikinsa ya rage, cikin gajiyawa kuma kaitsaye ya nufi wani waje, wanda nake da yakinin cewa toilet ne, duk da kuwa yanda aka k’awata wajen da gilasai kala-kala.

Ahankali ya murd’a kofar ya shiga, kamar yanda nayi hasashen kuwa hakanne ya kasance, domin nanne toilet din dake cikin d’akin, saidai kuma ganin yanda aka k’awata toilet din, yasa ni tafiya duniyar mamaki, saboda yanda akayi wajen tamkar wajen shak’atawa.

Tabbas wajen ya had’u sosai, ga wanda bai tab’a zuwa ba kuwa dole ne yayi kauyanci.

Anutse ya sakarwa kansa shower, bayan yayi wankanne kuma ya d’aura da alwala, domin zuwa yanzu kusan k’arfe shabiyun dare ake nema, anan wajen nasu.

Ahankali ya bud’e murfin bathroom din ya fito, rike da towel ahannunsa yana me tsare ruwan jikinsa.

Bayan ya kammala goge duk jikin nasa ne kuma, ya k’arasa tare da bud’e trolleynsa, lotion mai dadin k’amshi ya ciro, tare da shafawa ajikinsa.

Bayan ya gama shafa mai dinne kuma, ya saka wani riga da wandon payjamas ajikinsa,  mik’a ya d’anyi kana Ahankali ya k’arasa, gaban fridge ya d’auki goran ruwa yasha.

Saida yaji ya koshi da ruwan kafun ya rage hasken wutan dake cikin dakin.

Kaitsaye kan had’add’en gadon dake cikin dakin ya nufa.

Da addu’a abakinsa ya kwanta, tare kuma da lumshe idanunsa, saboda wani irin gajiya da yakeji, Sam kwata kwata shiya ma manta da wata Jannart.

Acan falon kuwa Jannart ne ta sake matse jikinta waje d’aya, akaro na barkatai kuma kenan yanzun, da ta d’aga Idanunta ta kalli agogon dake kafe ajikin bango.

Idanunta ne suka d’anyi narai narai, saboda wani irin fitinannen sanyin dake ratsa ta takota Ina, har wani huci numfashinta ke fitarwa,  duk da cewar ta duk’unk’une jikinta waje d’aya, amma hakan baisa ta daina jin sanyin ba. 

Ganin Idan ta tsaya ahakan zata cutune yasa ta bud’e Jakanta, wani babban abayanta mai kauri ta zaro, tare da zurawa ajikinta, sake komawa saman kujeran tayi ta mak’ale.

Idanunta ta d’an lumshe Ahankali, saboda Jin sanyin ya d’an ragu mata.

Akan trow pillows din dake manne ajikin cushion din ta d’aura kanta. 

Ahankali ta soma sauk’e Ajiyar zuciya, tare da had’e Idanunta ta lumshe.

Duk da cewar tana jin gajiya sosai ajikinta, tana kuma buk’atar son tayi wanka da ruwan dumi, amma babu yanda zatayi.

Sam batasan haka sanyin Mascow’n yake ba, domin taso ace wani yanki na daban dake, cikin Russia din suka zo, bawai  Mascow nan ba.   

Da wannan tunanin azuciyarta bacci ya d’auketa.

Still kuma ko acikin baccin nata batayi sake, abun rufawar nata ya fad’i ba.

Rayyern dake kwance akan lallausan gadonsa kuwa, sake gyara kwanciyarsa yayi, tare da lullub’e jikinsa da tattausan bargo.

Idanunsa ya d’an lumshe tare da sauke nunfashi cike da nutsuwa, kwata Kwata zuciyarsa ta kasa tuna masa Jannart daya bari a falo, yana nan ahaka har bacci ya d’aukesa.

5:00 am 

Dai-dai alarm din dake gefen gadon nasa, ya soma fitar da sautin kara.

Wanda hakan yasa ahankali ya bud’e idanunsa tare dayin mik’a, sunan Allah ya fara ambata, kafun daga bisani ya tashi ya zauna. 

Agogo ya kalla, tare da zuro 

k’afafunsa k’asa.

Cikin d’an yanayin dake nuna har yanzu yana tare da, gajiya ya d’an lumshe idanunsa, acikin zuciyarsa kuwa tunanin yanda zai fara zuwa masallaci yake.

Saboda yasan tsakaninsu da masallacin akwai nisa, domin ko amota zaije saiyayi 15mn zai isa, Idan da k’afane kuma mutum sai ya share 30mn ma bai isa ba.

D’an ya mutse fuskarsa yayi, saboda gajiyan da yakeji ajikinsa.

Anutse ya tashi daga kan gadon, direct toilet ya nufa, da ruwan d’umi yayi wanka had’e da d’auro alwala, bayan ya fito Daga toilet dinne kuma, ya sanja kayansa  zuwa riga da wandon SP,  lallausan darduma ya shumfud’a tare da tada sallah.

Adai-dai lokacin ta soma bud’e Idanunta Ahankali, harta gama waresu.

D’an yunkurawa tayi ta tashi, ahankali ta mik’a hannu ta d’auki wayarta dake gefe,  Ganin lokacin sallan asuba yayi ne kuma yasa ta, tashi ta zauna.

Ahankali ta soma k’arewa falon kallo, saidai kuma sam bata ga alaman akwai toilet acikin falon ba, gashi duk jikinta wani iri yakeyi mata, ga masifaffen sanyin dake busawa gashi kuma dole zatayi wonkan taci gaba da salla domin tasan zuwa yanzu ta samu tsarki zataci gaba da ibadunta daga sallan asuban.

Ahankali ta ajiye k’afafunta ak’asa tare da mik’ewa tsaye, kallonsa ta mayar ga kofofin d’akuna guda biyun dake cikin falon.

Idanunta ta d’an tsayar akan k’ofar da taga Rayyern din ya shiga jiya. 

Ahankali ta sake gyara zaman babban abayan dake jikinta, Cikin yanayin takunta mai d’auke da nutsuwa ta soma takawa, kaitsaye ta nufi d’ayar k’ofar dake hannun hagu.

Koda ta k’arasa bakin k’ofar ahankali, ta d’aura hannunta akan handle din k’ofar, tare da d’an murd’awa, cikin sa’a kuwa taji k’ofar ta bud’e.

Ajiyar zuciya mai k’arfi ta sauk’e, tare da d’an tura kanta cikin d’akin.

Extra room ne mai kyau, wanda gaba d’aya aka malale k’asansa da wani lallausan carpet, Daga can gefe guda kuwa gado ne d’an madaidaici, sai kuma wani long mirror dake can gefe da gadon.

Bayan bedside carbinet kuwa, babu komai acikin d’akin.

Ajiyar zuciya ta kuma sauk’ewa, Ganin kuma akwai na urar dumama daki acikin dakinne, yasa ta juyawa ta koma falo, akwatinta ta d’auko tare da dawowa cikin d’akin.

Bayan ta ajiye akwatin nata ne kuma, tanu fi wani k’ofa dake cikin d’akin hannunta riƙe da miskil dahar ta nufi kofar, wanda take da yakinin cewa toilet ne.

Kamar yanda tayi zato kuwa hakanne, toilet ne me kyau sannan kuma akwai komai na amfani aciki.

Ganin da tayi kuma akwai shower mai bada ruwan dumi ne, yasa ta kwab’e kayan jikinta, Anutse ta sakarwa kanta ruwan d’umin bayan ta tabbatar da tsarkinta.

Wani irin dadi da nutsuwa taji alokacin da ruwan ya sauk’a akan fatar jikinta.

Sosai sanyin da takeji din ya ragu, bayan tayi wankan ne kuma tayi amfani da turaren miskin kamar yadda ta saba  kana ta had’a da alwala. 

Wani babban bathrobe ta saka, tare da bud’e kofar bathroom din ta fito.

Cikin d’an hanzari gudun kada sanyi ya dake shiga jikinta, ta jawo akwatinta tare da bud’ewa, ta zaro wata had’add’iyar riga mai kaman na sanyi, duk da kasancewar rigar english wears ce amma tana da kauri sosai,  saidai bata da yawan tsawo domin da kad’an ta wuce mata guiwa, domin rigane irin fashion dinnan. 

Koda tasaka rigar cas tayi mata, musamman da rigar ta kasance irin mai kwala dinnan ne.

Tubke dogon gashinta tayi, tare kuma da d’aukan safa mai kauri da tsawo ta sanya ak’afafunta. 

D’aya daga cikin sallayun da tazo dashi ta shumfud’a, tare da zura wani dogon hijabin daya rufe mata duk jikinta, bayan ta kunna na’urar dake d’uma d’aki ne kuma, ta koma kan sallaya tare datada sallah.

Bayan ta idar da sallan tayi azkhar ne kuma ta koma ta kwanta akan lallausan gadon, tare da jan blanket ta rufe jikinta.

Wani irin ajiyar zuciya mai karfi ta sauk’e, badon komai ba kuwa, saidan nutsuwar da taji ta samu.

Acan b’angaren Rayyern kuwa Koda ya idar da sallah, karatun Alqur’ani yayi, bayan ya idar da karatunne kuma ya soma shirya kansa.

Saboda zuwa lokacin har k’arfe 7 tayi, hasken sararin samaniya ya bayyana ko ina. 

Tsab  ya shirya cikin wani had’add’en suit da yayi matuk’ar amsar jikinsa, takalmin Gucci da kuma Gucci parfume ya fesa ajikinsa.

Sosai yayi kyau yau din, Yayinda suit din ta k’ara fito dashi, amatsayin babban likita, yayi kyau ainun, briefcase da kuma wayoyinsa ya dauka.

Ahankali ya murd’a handle din kofar d’akin ya fito, yana me gyara agogon dake daure atsintsiyar hannunsa.

Wayarsa dake rik’e ahannunsa ne ta soma k’ara, alaman shigowar kira, picking call din yayi tare da kara wayar akan kunnensa, batare kuma da ya gama sauraran, abunda ake fad’a masa acikin wayan ba, cikin d’an yanayin gaggawa yace.

“I’m on my way.”

Yana gama fadin hakan ya zare, wayar daga kan kunnensa,  cikin sauri kuma ya fice daga cikin falon.

Kaitsaye babban titin dake k’ofar gidan ya nufa, tsayawa yayi abakin titin tare da d’an soma lallatsa wayarsa, da alama sak’o yake turawa.

Bayan ya gama tura sak’onne kuma, ya maida wayar tasa cikin aljihun sa.

Almost 10mn kacal wata had’add’iyar mota ta k’araso inda yake, parking motar akayi, cikin sauri kuma baturen dake cikin motar ya fito, aladabce ya mik’awa Rayyern din key din motar.

Cikin muryar turanci baturen yace.

“We’ll come back Sir.”

“Thank you Jonas.”

Rayyern din ya fad’a atak’aice tare kuma da bud’e murfin motar ya shiga,  wanda da dukkan alama dama,  yana da motar Wacce Idan yazo k’asar yake amfani da ita, kasancewar ak’asar yayi karatun Degree d’insa na biyu, wannan dalilin yasa yake zaune a gidan da yake mmkin yadda akayi Abbansu  ya mallakeshi anan k’asar ta Russia. 

Jonas  shine Wanda yake kula da komai na gidan dama duk wani abu nasu, duk da ya manyata.

Koda zuwa ya kamashi, shi yake gayawa ya gyara musu komai.

Jonas din ne ya  rufe masa murfin motar, shi kuwa Rayyern cikin k’warewa yaja  motar yayi gaba.

Ganin Dr. Rayyern din ya tafi ne kuma yasa, Jonas tare taxi ya koma inda ya fito.

Rayyern kuwa kaitsaye babban hospital din, dake cikin garin Mascow ya nufa, kasancewar tuntuni ya bawa sauran Doctors din, umarni akan su had’u acan hospital din, so already ma sunje shi kawai suke jira. 

A hankali ya kusa hancin motarsa cikin farfajiyar.

*HSCT centre Mascow*

Cikin parking  space na hospital din yayi parking, Cikin nutsuwa ya fito, tare da nufan cikin hospital din da tafiyarsa ta k’asaita…!

Yana isa farfajiyar asibitin su Dr. Sulaiman dake jiransa, suka k’araso garesa da sauri,  hannu ya basu suka gaisa, bisa jagorancinsa kuma kaitsaye suka wuce, wani babban sashi na musamman dake Cikin hospital din. 

HSCT centre  Hospital ne me kyaun gaske wanda aka yi masa tsari mai kyau, komai dake cikinsa na musamman ne sabida shine babban asibitin horaswa da sukeji dashi a kasar.

Basu k’ara jaddada kyawun asibitin ba kuwa, saida suka shigo babban dakin ganawan manyan likitoti, wanda aka yi masa tsari na daban kuma na musamman. 

D’akin taron da komansa ya kasance na glass, cike yake da manyan  likitoti way’anda suka zo daga k’asashe sassan daban daban na duniya, kowanne likita kuwa ya amsa sunansa likita, wanda kuma sunzo ne dan k’arawa junansu sani.

Koda suka shiga cikin d’akin taron amutumce suka gaisa da junansu, anutse kuma kowanne ya zauna akan kujerar dake lik’e da sunansa.

Cikin girmama junansu, batare da wani babban cin k’asa ko addini ba suka soma gudanar da abunda ya kawosu.

Sosai suka b’ata lokaci wajen meeting, wanda ya d’aukesu sama da 6hours, domin tun 8:00 am suka shiga, basu fito ba kuma sai 2:00 pm dai-dai.

Nan ma bawai sun kammala bane, breaktime ne suka samu, wanda kuma hakanne ya baya musulman cikinsu daman yin sallah’n azahar. 

Bayan sunyi sallan azahar dinne kuma,  suka wuce wani cafe dake cikin hospital din, abinci mai kyau akayi saving nasu.

Saidai shi Rayyern bai wani ci sosai ba, duk da cewar baiyi breakfast ba yau din, amma hakan baisa yaci abincin sosai ba.

Bayan sun kammala cin abincinne kuma, suka sake komawa meeting din.

Basu suka fito ba sai sallan la’asar.

Koda sukayi salla kuwa, sashin da sabbin na’urorin aikin su suka nufa nan akai ta gwada musu ko wanne da kuma aikinsa 

Basu fito ba har sai 5:30 pm, gaba d’ayansu agajiye suke, duk da cewar dukansu sun samu k’arin haske akan abubuwa da yawa, amma gaba d’aya sun jigata, saboda zaman waje daya babu dadi.

Fitowarsu din kenan kuma, Rayyern ya kalli su Dr. Sulaiman way’anda duk gajiya ya bayyana atattare dasu.

“I hope all yours. understanding the meeting?”

Yayi maganan yana me gyara zaman suit din dake jikinsa da rike jakar laptop nashi wanda shiyasa baya son Usman P.A yayi nesa dashi.

“Yeah we understanding.”

Gaba d’aya suka had’a baki wajen amsa masa.

Kai ya jinjina cike da gamsuwa, dai-dai lokacin kuma taxi din da suka tara suka k’araso. 

Rayyern kuwa juyawa yayi ya nufi motarsa, shi kansa agajiye yake ga kuma wani irin kasala dake saukar masa.

Kusan Atare suka fita daga harabar asibitin, shida su Dr. Sulaiman way’anda suka shiga cikin taxi. 

Suna hawa titi kuwa suka raba hanya, inda su masaukinsu Brosko hotel Arbat l, direct hotel dinsu suka nufa, shikuwa Rayyern hanyar gidansa ya nufa.

Cikin nutsuwa yake driving dinnasa, Dai-dai yazo wajen HALAL Sapiens RESTAURANT ne kuma ya tsaida motar, tare da fitowa ya nufi ciki.

Takeaway na african dishes yayi, sai kuma na salad and Chinese dishes. 

Yayi hakanne kuma saboda sometimes yafiso yana mixing food.

Gaba d’aya acikin tsarinsa ma babu Jannart, domin kuwa kwata-kwata ma ya manta da cewar yazo da MACE.

Bayan ya karb’i takeaway dinnasa ne kuma, kaitsaye ya koma mota tare da nufar gidan nasa.

Koda ya iso gidan acikin compound yayi parking motar,  Ahankali yake tafiya yana me zare suit din dake jikinsa.

Hannunsa ya d’aura ajikin kofar, tana bud’ewa ya tura kansa ciki.

Ahankali ya sauk’e Ajiyar zuciya, tare kuma da ajiye ledan Halal Restaurant din dake hannunsa akan kujera.   

Direct bedroom d’insa ya wuce, yana shiga kuwa ya rage kayan dake jikinsa, tare da wuce bedroom in 20mn yayi wanka.

Bayan ya fito ne kuma ya shirya kansa, cikin wasu Sabin kaya.

Wayarsa ya d’auka kana ya kuma dawowa cikin falon.

Zama yayi akan sofa tare da tank’washe k’afafunsa, Ahankali ya bud’e ledar Halal restaurant din.

Chinese dishes din ya soma ci, Yayinda ya maida hankalinsa gaba d’aya kan laptop din dake gabansa. 

Daga can cikin left side bedroom din kuwa, Jannart ce kwance tayi lub akan gado.

Wanda zuwa yanzu kuma tayi matuk’ar jigata, saboda wani irin yunwa dake damunta, kasancewar rabonta da abinci tun jiya da safe, Domin ko acikin jirgi wani dan cake kawai taci.

Tun tashinta yau din kuwa babu abunda takeci sai ruwa.

Wanda zuwa yanzu har ruwan ya soma murd’arta.

Ga kuma wani shegen sanyi dake damunta.

Hannu tasa ahakali ta dafe Kanta dake d’anyi mata ciwo, her know tasan babu kowa acikin gidan, kasancewar d’azu ta fito, ta kuma gama dube dubenta amma sam bataga alaman bayan ita akwai wani rai agidan ba,  har kitchine din dake cikin falon ta shiga wai ko, zata samu abunda zataci amma babu komai.

Hakan kuwa shi yasa koda tayi sallan la’asar ta dawo daki ta kwanta. 

Duk yanda taso bacci ya dauketa kuwa abun ya kasa, saboda yunwa ya hanata sukuni.

Shikuwa Rayyern baiwani ci abincin sosai ba, ya mik’e tsaye, saboda yaga lokacin sallan magriba tayi.

Direct dakinsa ya koma ya d’auro alwala.

Koda ya fito car key d’insa ya dauka, tare kuma da ficewa daga Cikin gidan gaba d’aya.

Kasancewar yana dan gudu ne kuma yasa, tafiyar 13mn ne ya kaisa babban masallacin.

Yana zuwa kuwa ko mintuna 3 baiyi ba aka shiga sallan magriba.

Bayan sun idar ma haka ya zauna acikin masallacin, har saida akayi sallan Isha. 

Acan gidan kuwa Jannart adaddafe tayi sallan Isha, saboda yunwan da take cinta aciki, bayan ta idar da sallan ne kuma ta sake dawowa falon.

Aikuwa cikin sa’a ta samu sauran abincin da yaci ya rage, zama tayi awajen cikin yunwa, batare kuma da tunanin komai ba ta jawo takeaway d’aya ta soma ci,  sosai taci abincin har saida taji cikinta ya kama, kana ta bi da ruwa.

Tana gama cin abincin kuwa lokaci d’aya, taji wani irin kasala ya sauk’ar mata azabebben sanyin da takeji ya ɗan ragu kaɗan.

Ahankali ta mik’e tsaye tare da wucewa d’akinta, tana shiga kuwa ta fad’a kan gado, tare da jawo blanket ta rufawa jikinta, lokaci daya kuma taji wani irin bacci na fusgarta.  

Shikuwa Rayyern bayan an idar da Sallan isha’n, kaitsaye hanyan gida ya nufo. 

A hankali yayi paking kana ya fito tare da rufe motar, cikin yanayin gajiya, Bacci da kasala ya nufi cikin gidan, 

hannunsa ya ɗaura tsakiyar kofar lokacin ɗaya ta buɗe, cikin lumshe ido ya kutsa kansa cikin falon.

Yana taku cikin alamun bacci, gaban santer table ɗin ya nufa dan ɗaukar System ɗin sa daya bari a wurin.

Da sauri ya ɗan zubawa ledodin kan table ɗin idanu,

“Yah salam”.

Ya faɗi tare dasa hannunsa ya dafe kansa.

Allah ya sani shi ya ma mance da ita gaba ɗaya sai yanzu da yaga ledodin da ya bari an sauya musu tsarin zama ta fado mishi a rai, a fili yace.

“Astagfirrullah ba ga irinta nanba na gayawa Abba yaki fahimtata, ni yaushema na kula da kainama bare wata da aka lika min gashi nan wlh na mance da ita”.

Ya ƙarashe mgnar yana  k’arasa isowa gaban table din.

Yana isa kuwa idanunsa suka sauk’a akan ledan abincin daya bari, ga kuma wani takeaway dake gefe wanda aka bud’e. 

Da dukkan alama kuma yasan itace taci abincin.

Kansa ya d’an girgiza tare da lumshe idanunsa, cikin d’an yanayin gajiya yace.

“Sune suka ja miki Allah ya gani ba laifina bane, na fad’awa Abba cewar ni bazan iya kula da wata mace ba, amma yasaka dole saida nazo da ita, zata takurani nasani, then ba Lallai na iya kulawa da cinta ba, cause nima ban kula da nawa cin ba.”

Ya ƙare mgnar yana mai

D’aga kafad’unsa yayi tare kuma da bud’e hannayensa alaman ko oho, bai sake bi takan takeaway dinba kuma ya wuce zuwa bedroom d’insa.

Yana shiga ya kwanta tare da buɗe laptop d’insa yana dan latsawa, ahaka har bacci ya d’aukesa.

Yayinda ab’angaren Jannart kuwa tuntuni ma, ita baccin ya d’auketa. 

        Washegari.

The same 7:00 am dai-dai ya gama shirya kansa, still cikin wasu tsadaddun suit, saidai colourn ya banbanta dana jiya, Domin yau din ash colour suit ya saka, sai kuma wani babban jacket mai kyau daya d’aura akai, musamman Dan tarewa kansa, masifaffen sanyin da akeyi.  

Fitowa falon yayi cikin shirinsa na office tsab,  zama yayi akan d’aya daga cikin kujerun falon, tare da zaro wayarsa yayi musu ordern abinci.

Laptop d’insa ya bud’e tare da d’an soma tattab’awa, yana nan azaunen kuwa yajiyo k’aran intercom, da’alama kuma order’n abincin da yayi dinne ya iso.

Ahankali ya mike tsaye tare da k’arasawa ya bud’e kofar, kaman yanda yayi hasa she din kuwa hakanne, domin abincin ne aka kawo, karb’a yayi kasancewar kuma free delivery ne, shiyasa shi juyawa ya koma ciki.

Zama yayi tare da bud’e takeaways din, way’anda yaga zai iya ci ya d’an tsakala, batare kuma da yaci sosai ba ya tashi, ya wuce zuwa HSCT centre hospital domin yasan yauma 8:00 am dai-dai zasu shiga meeting.

Fitannasa da kamar 17mn Jannart ta bud’e kofar dakin ta fito,  sanye take cikin wani riga da wandon jeans, da sukayi matukar kama jikinta, kasancewar kayan masu kauri kuma shiyasa, basu wani bayyana surar jikinta sosai ba, uwa uba kuma kaurin nasu ya rage mata kaso 30 acikin d’ari na sanyin da takeji.

Ahankali ta k’araso cikin falon, sauk’e idanunta akan abincin da tayi ne kuma yasa ta sauk’e Ajiyar zuciya, domin kafun yanzu harta fara tunanin wuni da yunwa.

Zama tayi acikin falon tare da kunna TV plasma, Anutse kuma cikin kwanciyar hankali ta soma cin abincin.

Bayan ta kammala ne kuma ta kimtsa falon, tare da dawowa ta kwanta akan wata cushion, din da musamman akayi ta dan shak’atawa. 

Acan b’angaren Rayyern kuwa yauma taron nasu ya dau zafi sosai, Dan yau din  kamar karantar dasu akeyi, akan sikila ta yanda za’a magance ta, da kuma yanda za’a iya sanjawa mai d’auke da cutar jini.  

Sosai kuma duk Doctors din suke enjoying abunda ake koyar dasu. 

          *Nigeria*

Mamy ce zaune acikin falon tayi shiru,  saboda duk haka takejin gidan nasu babu dad’i,  domin hatta Ramadan yanzu ba zama yakeyi ba, gaba daya hankalinsa, ya maidashi akan hospital dinsu, Idan ya fita baya dawowa saida yamma.

Abba da shigowarsa kenan, ganin yanda matar tasa ke cikin damuwa ne yasa shi cewa.

“Ruk’ayya.”

Ya k’ira sunanta atausashe.

Hakan kuwa shiya saka ta juyo ta fuskancesa.

“Tunanin me kikeyi haka?”

Abban ya tambaya yana me k’arasowa cikin falon.

Mamyn kuwa Ajiyar zuciya ta sauk’e, cikin dan yanayin sanyin dake dauke da kewa tace.

“Kewar su Rayyern da Jannart nake, gaba d’aya kwana biyun nan gidan duk babu dadi, ga Ramadan ba zama yake ba,  dama ace Riyyam  bai koma ba, to danasan abun da sauk’i, gaskiya nima yanzu kam na matsu ayi batun auren Ramadan, akawo mana Wacce zata na d’an d’ebe mana kewa.”

Mamyn ta k’are maganan cikin dan damuwa. 

Abba kuwa murmushi yayi tare da zama akusa da ita, Cikin kulawa kuma yace.

“To in bandake da abunki Ruk’ayya gaki ga mijinki kuma wani kewa ne ya rage miki?”

Murmushi itama Mamyn tayi, kana cikin dan sakin fuska tace.

“Hakane amma nima ai inason kusanci da y’ay’ana matsayin  kewar miji da ban ta yarama da ban ina son yarana.”

Ta ida mgnar hawaye na silalo mata da alamun akwai wani babban abin data tuna wanda ke damun rayuwarta.

Kai Abban ya jinjina tare da gyara zamansa cikin tausasawa yace.

“Badamuwa maganar auren Ramadan, yanzu muna jiran cewa daga wajen iyayen yarinyar ne, Insha Allah za’ayi bikinsu nan bada jimawa ba,

Sannan yara kuma keda Allah ya bawa Rayyern, Ramadan, ai saikice Alhamdulillah.”

Uhummm taja wani dogon numfashi tare da zuba mishi ido alamun tuni.

Shi kuwa Abba kai ya jinjina mata, tare kauda zancen da cewa.

 “Amma niko tunda yaronnan Riyyam-nsra ya tafi kunyi magana dashi kuwa?.”

Murmushin Jin dadi Mamyn tayi, cikin farinciki kuma tace.

“Masha Allah,eh munyi magana dashi, washegarin tafiyarsa Ramadan ya k’ira ya kuma bani wayar mun gaisa.”

Kai Abban ya jinjina.

Dai-dai lokacin kuma Ramadan ya turo k’ofar falon ya shigo.

Akusa da Mamyn nasa ya zauna, bayan yayi musu sannu da gida ne kuma, ya sake dagowa ya kalli Mamyn nasa, cikin sanyi yace.

“Mamy kina ta zaune duk gidan babu dadi ko?”

Kai Mamyn ta jinjina masa alaman “Eh.”

Hakan kuwa shiyasa Ahankali ya d’an gyara zamansa, tare da cewa.   

“Ai Mamy na fad’a miki cewar gidannan bazai yi dadi ba, matukar babu su Hamma Rayyern, duk gidan ya rame mun zama abun tausayi.”

Murmushi Mamyn tayi tare da kallonsa, domin ita ta gama sanin ayanzun me yake nufi, wanda kuma yanzu suka gama maganan abunda yakeso din da Abba.

Cikin son kawar da zancen nasa tace.

“Yauwa kiramin Riyyam nsra mana.”

“To.”

Ramadan din yace tare dayin dialing numbern Riyyam, bugu biyu ya d’aga, bayan sun gaisa ne kuma ya bawa Mamyn waya. 

Mamy na amsa Daga can b’angaren Riyyam nsra yace.

“Wallahi I miss you so much Mamy na, nayi missing girkinku keda Aunty Jannart.”

Murmushi Mamy tayi kana cikin danjin dadi tace.

“Muma munyi kewarka Riyyam ya Mammyn ka da kuma Zaytoon?”

“Duk Suna lafiya Mamy yasu Abba, da Hamma Rayyern na, bani da numbernsa na k’asar Mascow.”

Riyyam  din ya tambaya cike da kewa.

Mamy kuwa fuska asake tace masa duk suna lafiya, 

Haka dai suka d’an tab’a hira kafun daga bisani sukayi sallama.

Acan Mascow kuwa, kamar dai jiya yau d’inma sai k’arfe biyar, su Rayyern suka tashi ataron nasu.

Ahanyarsa ta dawowa ne kuma ya biya, Halal Mascow on top restaurant ya saya musu abinci.

Koda ya dawo wanka yayi tare da dawowa, falon ya zauna, tashar CNN yake kallo, Ahankali kuma yake d’an cin abincin dake gabansa, wanda kwata-kwata shi yanzu ba wani dadin abincin yakeji sosai ba.

Bayan ya kammala cin abincinne kuma ya wuce masallaci.

Jannart din kuwa kamar jiya haka yau d’inma ta fito taci abinci, saidai bata wani ci sosai ba, drinks din kawai tasha ta koma ta kwanta. 

Taso yin k’ira amma kuma tasan layinta, bazai yi amfani awannan k’asar ba sabida bata da kati ko asi, shiyasa ta hakura, gashi shi kuma tun ranan da suka zo ba ganinsa ma takeyi ba.

Wannan dalilin yasa kawai ta soma buga game,  tana cikin yin game dinne kuma bacci ya d’auketa. 

*Ethiopia.*

Riyyam-nsra ne zaune akan sofan, dake cikin katafaren falon Mammynsa, daga  can gefensa kuwa Mammyn nasa ce, sai Kuma Zaytoon itama dake gefe.

Kakarsu Didi kuwa kwance take akan kujera.

Riyyam-nsra din ne kuma ya d’ago kansa, tare da jingina da jikin Mammynsa, cikin farinciki da kulawa yace.

“Mammy duk wani abun da muke zato da tunani ya tabbata, Mammy Nigeria tsatson mune, kuma jigonmu ce acan tushen farin cikinmu suke, wallahi Mamy ni harma naji na gaji da k’asar nan, inason komawa k’asata ta Haihuwa kuma k’asar mahaifina.”

Ya k’are maganan cikin wani irin bege me karfi dake fusgarsa.

Zaytoon dake zaune agefensa ne ta d’an langwabar dakai, kana Cikin sanyi tace.

“Har gwara kaima Riyyam kaje kaga k’asar, kaje ka ga abunda ni idanuna suka kasa ganemin kaje ka ƙamshin ƙasarmu ka shaƙi iskar ƙarmu.”

Idanunsa ya d’an lumshe kana cikin son bawa y’ar uwartasa k’arfin guiwa yace.

“Insha Allah kema zakije Zaytoon, auren Hamma Ramadan na tashi, Mamy zata je kema kuma zakiji harma da Didi, nikam naji dadin zama cikin ahalina, nayi farinciki sosai Ina kuma fatan kasancewa dasu har abada.”

Idanu Mammy ta d’an lumshe cikin kuma yanayin sanyi tace.

“Insha Allah Riyyam komai zaiyi dai-dai, watarana komai zai wuce mubi komai ahankali.”

Fuska Riyyam din ya d’an kwab’e, kana cikin salon shagwab’a yace.

“Mamy wani irin ahankali tsawon shekaru fa muna zaune ahaka, ayanzu kuma gaba d’aya komai ya tabbata.”

Gyara zama Mammyn tayi kana cikin kulawa tace.

“Riyyam nima inaji ajikina cewar watarana zanje, zuciyata ta zak’u akan naje din, saidai bansan meye zuwan nawa zai haifar ba Riyyam, duk wani abu da kake tunani ya wuce nan, har yanzu akwai k’ullin da bai gama warwarewa ba, amma nasa araina cewa Insha Allah zanje watarana, saidai kuma akwai buk’atar muyita  addu’a, saboda Allah ya sauk’ak’a mana duk wani tsanani.”

Da “Ameen.” Duk suka amsa, kana daga nan kuma suka ci gaba da hirarsu. 

Ahaka rayuwa taci gaba, aduniyar Rayyern da kuma Jannart, babu wanda yaga d’an uwansa tun zuwansu Mascow’n, wanda ak’alla yau kwanansu shida suna neman na bakwai kenan.

Ko yanzun kuwa Jannart dince ke zaune acikin falon,  zaman nan tayi irin na tankwashe kafafu.

Yayinda take sanye da wani pencil jeans pink colour, da kuma wani t-shirt sai jacket mai nauyi da ta d’aura akan shigar tata.

Ahankali ta dan daga kanta sama, tare da kwantar da kannata ajikin kujera.

Yanayin zaman da tayi dinne kuma yasa, gaba daya duk wani shati na halittar jikinta ya bayyana, more especially breast dinta, wanda ko bra bata saka ba, gashi kuma rigar sanyin nata ya Dan bud’e kad’an.

Idan ka kalleta azahirance zakayi tunanin cewar bacci ne ya d’auketa ahaka, saidai kuma azahirin gaskiya bawai hakan bane, domin gaba daya tunaninta ya tafi ne izuwa Gida.

Ayanzu tunanin halin da Dadynta dasu Abdull suke ciki take, domin tasan koma yaya basa cikin yanayi mai dadi, gashi kuma tunda tazo k’asar batayi waya da Abba Kabir dinta ba ko su Mamy da Ramadan batayi mgn dasuba gaba ɗaya kewarsu ya dabaibayeta. 

Ahankali ya turo k’ofar falon ya shigo, hannunsa rike da ledan restaurant da kuma suit d’insa. 

Shigowarsa cikin falon kuwa shiya saka shi sauk’e idanunsa akanta.

D’an tsayawa yayi yana me kallonta, tun daga k’afafunta dake tankwashe, har zuwa kan lafaffen cikinta, da kuma kirjinta zuwa dogon wuyanta.

Idanunsa ya d’an k’urawa soft neck din nata, wanda yake dauke da dan siririn chain, sosai wuyan nata ke da kyau ga wani layi layi,  Ahankali ya kuma dawo da kallonsa ga kirjinta.

Lokaci daya kuma cikin sauri ya janye, idanunsa daga kallonta.

Ledan dake hannunsa ya ajiye, tare da ci gaba da takowa  ya k’arasa shigowa cikin falon.

Jannart kuwa jin alamun takunsa ne yasa ta saurin d’ago Kanta, karab kuwa Idanunsu suka sark’e acikin na juna.

Wanda hakan yasa taji zuciyarta tayi wani irin bugawa, lokaci d’aya kuma taji wani irin rauni ya lullub’e zuciyarta.

Ahankali tayi k’asa da kanta, tare da da hannu ta gyara zaman rigar sanyin ta.

Cikin wata irin sanyin murya mai dauke da shagwab’a tace.

“Sannu da dawowa.”

Idanunsa ya d’an lumshe 

tare kuma da kawar da kansa, murya akasalance da kuma gajiya yace.

“Uhummm.”

Yanayin yanda ya amsa da Uhummm dinne kuma ya sata lumshe ido, saboda hakanan taji yanayin nasa na kasala, ya tada mata da tsikar jiki.

Ahankali Rayyern din ya soma tafiya, har yakai bakin k’ofarsa kuma saiya juyo, ya kalleta, wani abu yakeson ce mata, amma hakanan sai yaji bakinsa yayi nauyi kana shi kansa bai san me yake son ce matanba, hakan kuwa shiyasa kawai ya wuce daki.

Jannart kuw najin alamun ya shige bedroom ne, yasa Itama ta tashi ta wuce nata dakin, yau ko abincin daren ma bata ci ba.

Shikuwa Rayyern Bayan yayi wankane ya dawo falon, abinci yaci tare da komawa dakinsa ya kwanta.

Washegari kuwa kamar yanda ya saba haka ya fita bayan ya ajiye mata breakfast.

After 2weeks.

Ahaka sukeyin rayuwarsu ita dashi, daga wannan ranan kuwa babu wanda ya sake Ganin d’an uwansa, saidai kullum yana ajiye mata breakfast da kuma dinner, da rana kuwa saidai ta ci ragowar breakfast.

Gaba d’aya duk kad’aici ya dame ta, duk da ta saba da hakan amma yanzu batajin dadin hakan. 

Shikuwa Rayyern gaba daya yanzu ya zama busy, domin course din da sukeyi din ya fara nisawa, shi yasa always he’s busy.

Daya dawo kuma ya gaji sosai, daga ya d’an tab’a system d’insa sai bacci.

Yau din kuma tunda ya fita da safe baidawo ba, domin Koda suka tashi ataron nasu, still meeting ya shiga da wasu manyan Doctors na k’asar.

Koda lokacin sallan magriba yayi, bayan yayi sallan meeting din ya sake komawa haka ma sallan Isha.

Basune suka tashi a meeting dinba kuwa sai 1:00 pm.

Agajiye yake sosai yau din, dan ko dak’yar ya iya biyawa ta restaurant ya saya abinci,  da wasu chocolates d’insa, tun acikin mota kuwa yake cin chocolates din ahaka harya iso gida.

Koda ya dawo gidan kusan 11 ake nema.

Haka ya shigo cikin falon, yana mejin yanayinsa na d’an sanjawa, saboda yanzu Kwata-kwata baya ma shan maganinsa, especially now daya zama busy.

Direct d’akinsa ya wuce, tare da sakarwa kansa ruwa. 

Itakuwa Jannart tana can cikin d’aki, duk yunwa ya isheta saboda duk yau bataci abinci ragowar breakfast din nata ba.

Tafito falon nasu kuma bata ga komai ba, wannan dalilin yasa ta koma ta kwanta, saidai duk yanda taso bacci yaki daukanta.

Ganin hakanne kuma yasa ta sha ruwa, tare da komawa ta kwanta, ahaka wani baccin wahala ya dauketa. 

Ab’angaren Rayyern kuwa yana fitowa daga wanka, kaya ya sakawa jikinsa, batare daya sake bin takan abincin daya kawo ba, ya haura saman gadonsa, bacci ne sosai a idanunsa, shiyasa yana kwanciya bacci ya d’aukesa. 

Washegari.

Saturday.

Bakamar sauran ranakun ba, kasancewar yau din weekend ne yasa, bai fito da wuri ba har sai 9:00pm.

Ahankali ya bud’e k’ofar bedroom din ya fito, maida k’ofar yayi ahankali ya rufe.

 Ya juyo ya fuskanci cikin falon,  idanunsa ya dan waro lokacin da suka suka sauk’a Akan…!

Back to top button