Uncategorized

Tubali Book 2 Page 5 Complete Novel

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

Tare da fuskantarsu dukansu, cikin dan nisawa yace.

“Gaba d’aya matsalarmu a kullum akan Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara ne, wanda kuma ni kaina bani da iko, ko wani matsayi da zan iya dakatar dashi akan abunda ya saka agaba, saboda duk wani k’a’ida da dokokin da akebi ya bisu, Idan kuma har nace zan wargaza masa tsari.

 To tabbas zai iya Kai k’arata wajen na sama dani, hakan kuma zai iya sawa na rasa aikina, yaron ya wuce duk yanda muke tunani, kowacce hanya da zamu b’ullo masa ya sani, kansa yana ja sosai, babban abunda na lura dashi kuma shine, kwata kwata baya tsoron magautansa yaron yana nan Tamkar a  haifeshi ne domin daukan fansa!!!.”

Numfashi mai nauyi duk suka ja, musamman Alhaji Idi Sale Dakata wanda gaba daya abubuwa suka had’e masa. 

Ga zafin b’atan Jannart ga kuma, na wannan shegen yaron Dr. Rayyern.

Barrister Kabir kuwa, kalaman Alhaji Bala Tambari na karshe yaketa nanatawa a zuciyarshi don son fahimtar wani abin.

Haka dai taron nasu ya watse gaba d’aya zuciyar Alhaji Idi, da kuma na Dr. Lukman Alhaji Abdu Tababa babu dadi, kowannensu kuma saboda Rayyern.

Dr. Lukman din, da kuma Alhaji Abdu Tababa ne suka had’a hanya wajen tafiya, haka ma Alhaji Bala Tambari shima tafiya yayi. 

Hakan yasa falon ya rage daga, Daddy sai Barrister Kabir.

Juyowa Alhaji Idi Sale Dakata’n yayi? Ya fuskanci Barrister Kabir, cikin kuma nuna halin damuwa yace.

“Kabir ayanzu babu abunda yake damuna, kamar b’acewar Jannart, har yanzu babu wani labari,  kwata kwata ayanzu ma ba batun companyn Rayyern Mai-nasara bane ke damuna,  matsalar b’acewar Jannart itace ke damuna hukuma suna iya yinsu abin yaci tura.”

Afakaice kuma ta k’asan idanu, Barrister Kabir ya kalli Yayan nasa, tare da d’an ya mutsa fuskarsa.

Wanda kuma daga wajen Alhaji Idi Sale Dakata’n ma hakan yake, domin kuwa bayan yayi maganar shima, ta k’asan idanu, ya kalli K’anin nasa, tare da sakin wani Shu’umin murmushin, da shi kad’ai yasan ma’anar yinsa. 

Barrister Kabir kuwa, mur yasha tare da saka fuskar tsare gida, irin tasu ta lawyoyi, saboda shima akwai wani abu daya gano amatsayinsa na lawyer.

Shi yanayiwa Barrister Kabir kallon biri, shi kuwa Barrister Kabir yanayiwa yayan nasa kallon Ayaba.

Koda suka fito daga d’akin taron Alhaji Idi Sale Dakata’n, main falon gidan suka dawo,  inda suka samu Momy ta gama had’a abinci.  

Sama sama haka Barrister Kabir yaci abincin, bayan sun kammala ne kuma yayiwa Yayan nasa sallama, kaitsaye kuma daga gidan Alhaji Idi Sale Dakata’n, gidansa ya nufa. 

Koda ya isa gidan afalo ya samu Dijat. 

Hira kadan suka tab’a kana kaitsaye ya wuce bedroom d’insa.

Key ya sawa kofar bedroom din, tare da komawa ya zauna, bayan ya d’auko wasu  takardu.

Anutse yake wargaza takardun, tare da Ware wasu daga ciki yana duddubawa. 

D’ago wata takarda da yayi ne kuma, ya sashi tsurawa rubutu, da kuma hoton passport din dake jiki idanu.  

                  *** *** 

Almost 4weeks kenan yanzu da, dawowar Rayyern daga China, Alhamdulillah kuma jikinsa ya warware.

Bisa taimakon Ramadan da kuma Jannart, way’anda suke kula da shan maganinsa. 

Hakan yasa ciwon cikin nasa yayi sauki, ya kuma gama samun karfin jikinsa, duk da cewar time to time ya kanji, ciwon cikin na tashi masa, amma da yasha magani yake jin sauki. 

Ahankali yake sauk’owa daga kan matattakalan falon, inda yayi kyau cikin shigar Ash colour suit dake jikinsa.

Yayinda hannunsa ke rik’e da briefcase, da alama kuma aiki zaije.

Ya dawo asalin Rayyern d’insa, big man wanda bai wani cika son wasa ba, wani Rama da yawan kasalan da yakeji ada, duk sun kama gabansu.

Mamy dake tsaye akan dining table, jin alaman takun takalmansa ne yasa, ta d’ago kanta ta kalleshi.

Ganin yanda yayi kyau ne kuma, yasa Mamyn sakin murmushi, Cikin kulawa tace.

“Babana yadai, yau na ganka cikin shiri haka fita zakayi ne?”

Kansa ya jinjina, adaidai lokacin da yake gama sauk’owa daga kan steps din yace.

“Eh Mamy yau zanje company.”

Murmushin dake kan fuskar Mamy ne ya fad’ad’a, cikin jin dadi tace.

“Ah Lallai Masha Allah Babana ya samu sauk’i, amma Ina fatan kanajin karfin jikinka sosai.”

Idanunsa ya d’an lumshe tare da jinjina mata kai alaman. “Eh.”

“To kayi breakfast tukun kafun ka tafi.”

Mamyn ta fad’a tana me nuna masa kujera, tare dayi masa alama akan ya zauna.

Fuskarsa ya d’an shagwab’e, kamar zaice a’a kuma saiya zauna.

Dai-dai lokacin kuwa Jannart ta shigo cikin falon, sanye take da riga da wando ajikinta, saidai wandon irin mai fad’in nan ne, haka ma rigar Wacce take da igiyan d’aurewa, hakan ne kuma yasa lafaffen cikinta bayyana, saboda yanda ta d’aureshi da igiyan, haka ma shape din cikin nata ya bayyana sosai.

Kasancewar kuma kayan nada  kalan baki, shiyasa ta yafa siririn mayafi daga kanta zuwa wuyanta. 

Sassanyan kamshi take bazawa, shigowarta cikin falonne kuma yasa shi sauk’e idanunsa akanta.

Mamy kuwa Ganin Jannart dinne yasa Cikin kulawa tace.

“Yauwa Jannart yi saving din mijinki mana, yana sauri zai tafi wajen aiki ne.”

Kai Jannart din ta d’an sunkuyar k’asa, cikin yanayin nutsuwa tace.

“To Mamy.”

Kaitsaye dining table din da yake zaune ta nufa, saidai koda wasa bata bari sun had’a idanu ba.

Koda ta k’arasa inda yake, plate ta d’auka tare da bud’e food flask, cikin sanyin muryar dake bayyana nutsuwarta tace.

“Ina kwana.”

“Lafiya.”

Ya amsa mata atak’aice, tare da zubawa kyawawan fararen yatsunta idanu. 

Abincin ta zuba masa, bayan ta kammala ne kuma ta turo masa plate din gabansa.     

Tare da saka masa apple juice din da ta had’a, acikin wani d’an glass cup.

Ahankali ya soma cin abincin, tare kuma da dan lullumshe idanunsa, saboda yanda yake jin kamshinta na shiga hancinsa. 

Jannart kuwa Ganin ya fara cin Abincin ne, yasa ta wucewa kaitsaye ta nufi sama, Dan d’auko maganinsa.

Ahankali ta tura kofar d’akin ta shiga.

Lumshe Idanunta tayi saboda, wani irin kamshi daya bugeta.

Ga kuma sanyin ac dake busa ko ina.

Dan bud’e Idanunta tayi, tare da soma bin ko ina dake cikin dakin da kallo, komai nasa need babu alaman datti, duk da cewar ya kwana acikin dakin, amma saida ya gyara komai kafun ya fita.

Hakanan kawai ta samu kanta da sakin murmushi, kaitsaye kuma cikin nutsuwa, ta wuce ta dauko magungunan nasa. 

Koda ta sauk’o k’asa harya kammala cin abincin nasa, saidai juice dinne da bai gama shaba, wanda kuma yake sipping d’insa ahankali.  

K’arasowa kan dining table din tayi, Anutse ta b’are magungunan tare kuma da zuba su acikin tafin hannunta.

Kallonsa ta d’anyi, tare da mik’a masa magungunan, alaman ya karb’a.

D’ago idanunsa yayi ya kalleta, cikin yanayinsa daya saba yi mata magana yace.

“Ni yaro ne, da har sai kin b’aremin magani, ni bazan iya dakai na bane akace miki? Sai kiyi ta wani ɗuɗɗuramin magunguna babu ko tausayi”

Idanunta ta d’an janye daga kallonsa, saboda ayanzu babu wani abu nasa da bata sani ba, saikayi masa abu sau goma, amma baya tab’a gani yanzu zai gwatsaleta ta fahimci zarginta yakeyi ma shi.

K’wayoyin idanunta tad’an juya ahankali, sau d’aya kuma cikin sigar lallashi tace.

“Okay I’m sorry take it.”

Hararanta ya d’anyi ta k’asan idanunsa,  sanin Mamy na cikin falonne kuma yasa shi, bud’e tafukan hannunsa, Anutse ta zuba masa maganin ahannunsa, gudun kada hannunta da nasa su had’e, tayi hakanne kuma saboda, ita kadai tasan me takeji, aduk sanda ta tuna lokacin da fatar hannunsa ya tab’a nata.

Rayyern kuwa bayan yasha Maganin ne ya mik’e tsaye, tare da d’aukan briefcase d’insa, cikin sauri yace.

“Mamy na tafi saina dawo.”

“A dawo lafiya Allah ya bada sa’a.”

Mamyn ta bashi amsa, Cikin kulawa.

Da  “Ameen.”

Ya amsa kana ya sakai ya fice daga cikin falon.

Ganin hakanne kuma yasa Jannart dawowa, kusa da Mamyn ta zauna.

Shikuwa Rayyern yana fita kaitsaye company ya wuce,

Koda yaje kuwa ya samu ma’aikatan nata aiki, kowa na aikinsa kamar yanda ya dace. 

Gaba d’aya ma’aikatan sun bada himmansu wajen yin aikin  tsakani da Allah.

Domin har anfara har had’a cattoon’s din abubuwa, wanda kowanne kwali d’auke yake da sunan tambarin. 

MAI-NASARA. 

Komai Yayi masa sosai, hakanne ma yasa shi jinjina kansa, kaitsaye kuma ya wuce office d’insa dake nan cikin companyn.

Wasu d’an aikace aikace yayi, bayan ya kammala ne kuma ya fito, kaitsaye hospital d’insa ya wuce.

Bashi ne ya dawo gidan ba kuwa sai k’arfe 10:00 pm dai dai. 

Hakan ya faru ne kuma saboda tsayawa da yayi, yiwa wata operation, baya ga haka kuma, ya tarawa kansa aiki sosai, wannan dalilin yasa shi tsayawa, ya d’an rage ayyukan.

K’asa k’asa ya danna Horn din motar tasa, cikin abunda bai wuce mintuna 2 ba kuwa, aka wangale masa gate din gidan.

Anutse ya tura hancin motar ciki, bayan yayi parking motar ne kuma ya fito.

Tare da Kallon Baba Maud’o wanda shine ya bud’e masa gate din.  

“Baba Maud’o da kanka, ai daka bari na fito na bud’e, sam banaso naga kana wahalar da kanka, saudayawa Idan naga kana wannan aikin sai naji duk babu dadi, please Baba Maud’o ka bari.”

Rayyern din ya fad’i haka ga Baba Maud’o cikin tausasa harshe.

Baba Maud’o kuwa Murmushi yayi tare da d’an gyara tsayuwarsa, kana Cikin kulawa yace.

“Haba Rayyern meye na damuwa kuma, bayan kasan hakan aikina ne, kuma gashi Ari yayi bacci shiyasa.”

Fuska Rayyern din ya d’an kwab’e, hade da karyar da wuyansa yace.

“Ni dai Baba Maud’o da gaske banason hakan, banajin dadi Idan naga kana bud’e gate inajin wani nauyi a zuciyata.”

Murmushi Baba Maud’o yayi, tare da komawa wajen zamansa ya zauna.

Ganin hakanne kuma yasa Rayyern d’in ma, matsawa ya zauna akusa da Baba Maud’on.

“D’azu Barrister Kabir yazo dubaka da jiki, amma baisame ka ba, saidai yace agaisheka.”

Baba Maud’o ya fad’a yana me Kallon Rayyern din. 

  

 Shikuwa Rayyern Ajiyar zuciya ya sauk’e, tare da d’an mammatsa hannunsa.

Cikin kuma taushin murya  yace.

“Ina amsawa, bari na shiga ciki Baba Maud’o, yau duk na gaji aikin office ya gajiyar dani.”

“To Rayyern Mukwana lafiya.”

Da “Ameen.”

Rayyern din ya amsa, tare da wucewa ciki kaitsaye.

Koda ya shiga main falon nasu babu kowa, hatta su Ramadan da Riyyam nsra duk suna daki. 

Kaitsaye kuma shima d’akin nasa ya nufa.

Yana shiga kuwa ya soma rage kayan jikinsa. 

Bayan ya shiga toilet yayi wanka ne kuma, ya shirya kansa cikin lallausun kayan bacci.

Bayan yasha Nutri milk ne kuma ya koma kan gado ya kwanta.  

Kasancewar agajiye yake ne kuma, yasa yana kwanciya bacci ya d’aukesa. 

Washegari. 

Arewa24 tv station.

Aunty Fauziya ce ke tafe cikin d’an sauri, saidai kallo d’aya zaka yiwa Fuskarta, ka fahimci cewa   tana cikin yanayin damuwa.

Fitowarta  kenan kuma daga dakin yad’a labaransu, sukayi Karo da Salman.

Kallonta Salman din yayi, Ganin damuwa afuskarta ne kuma yasa shi d’an tsayawa, Cikin kulawa yace.

“Aunty yadai naganki haka, wani abu ya faru ne?”

Kai ta d’an girgiza, cike da damuwa tace.

“Salman b’acewar Jannart ke damuna, tayaya za ‘ace mace kamar Jannart ta b’ace b’at kamar kud’i? hankalina yana tashi sosai Salman, ka duba dai irin jami’an tsoron da Babanta ya bawa cikiyar nemo ta, ga kuma mu da kullum sai munsa cikiyarta, amma har yau babu wani wanda yace ya ganta, abun yana min ciwo Salman, ga mahaifinta asanadin haka ko lafiyar kirki bashi dashi, kwanan nan naji har India aka fita dashi,  duk kuma akan lamarin b’acewar Jannart, Ina cikin damuwa akan hakan.”    

Ajiyar zuciya Salman ya sauk’e.

Dai-dai lokacin kuwa Asiya tazo ta wucesu, saiwani karairaya takeyi tamkar zata b’alle.

Ganin hakanne kuma yasa Aunty Fauziyan wucewa office dinta, take kuwa Salman ya rufa mata baya.

Koda suka isa cikin office din zama, duk sukayi, ananne kuma Salman ya d’ago ya kalli Aunty Fauziyar.

Cikin sanyi ya d’an gyara zamansa tare da cewa.

“Gaskiya da banyi niyan fad’awa kowa ba saboda sirrine, saidai ke naga gaba d’aya hankanlin atashe yake, akan b’atan Jannart, amma Dan Allah duk wata magana da zan fad’a miki inason ta zama sirri.”

Nisawa Aunty Fauziya’n ta d’anyi, tare kuma da fuskantar sa tace.

“Kafad’i duk abunda kakeson fad’a Salman, Insha Allah bazan gayawa kowa ba, kasanni kasan koni wacece zan rik’e duk wani sirri.”

Kai Salman din ya jinjina, tare da dan gyara zamansa kana yace.

“K’warai nasan hakan Aunty Fauziya, nasan ke ta musamman ce shiyasa ma na yanke shawarar sanar dake, danki cire wannan damuwar dake zuciyarki, agaskiya Jannart ba b’ata tayi ba.”

Idanu Aunty Fauziyan ta tsura masa cike da mamakin, Jin abunda ke fitowa daga bakinsa tace.

“Kamar yaya Salman ka warwaremin maganar ta yanda zan fahimta.” 

“Jannart ba wai b’acewa tayi ba, K’anin Babanta Barrister Kabir shi yayi mata aure, batare da sanin kowa ba, yace kuma yayi hakanne saboda wani dalili nasa maik’arfi, wanda kuma acewarsa hakanne kad’ai zai tseratar da rayuwarta, daga fad’awa koman magauta masu farautar rayuwarta.”

Wani irin gauron Ajiyar zuciya Aunty Fauziyan ta sauke, duk da cewar taji mamakin maganan k’warai, amma kuma taji sanyi acikin zuciyarta.

Numfashi ta d’anja tare da Kallon Salman din, cikin sanyin yanayi tace.

“To wannan al’amarin da d’aure kai yake gaskiya,  amma kuma shi yaron da aka aura mata d’in tana sonshi ne, ko kuma shi yana sonta?” 

Kai Salman din ya girgiza, kana asanyaye yace.

“Agaskiya kuma wannan ne bansani ba Aunty.”

D’anjim Aunty Fauziyan tayi, na y’an wasu dak’ik’u kuma tace.

“Kayi hakuri Salman, agaskiya ada nayi tunanin duk abunda zaka fadamin zan rufeshi, amma kuma sai gashi yanzu, naji ajikina tamkar akwai wata rawa da zan iya takawa, akan wannan al’amarin,  lalle dole zan san yadda  zanyi naga Jannart, muje wajen MD.”

Ta k’are maganan tana me mik’ewa tsaye.

Hakan yasa Salman rufa mata baya, kaitsaye suka nufi ofishin MD.

Koda sukaje Aunty Fauziyan ce ta kawo masa maganan Jannart, tare da nuna b’uk’atar ta nason Ganin Jannart din.

Jin buk’atar tasu ce kuma yasa MD jinjina kansa, cikin kokonton hakan yace.

“Agaskiya inajin kamar hakan bazaiyiwu ba Fauziya, saboda maganan nan sirrice da ba’aso kowa ya sani, nima kaina ba’a gayamin Dan matsayina ko wani abuba, a’a kawai dai angaya minne saboda, kada Jannart din ta rasa aikinta anan gaba,  haka ma Kai Salman kasan dalilin da yasa aka gaya maka,  saidai ba damuwa bari mu jarraba, zan k’ira Barrister Kabir din muji.”

Ya k’are maganan yana d’aukan wayarsa.

Aunty Fauziya kuwa murmushi tayi, tare dayi masa godiya.

Shikuwa MD’n kiran numbern Barrister Kabir yayi, cikin sa’a kuwa ya samu Barrister Kabir din ya d’aga wayan. 

Bayan sun gaisa ne kuma yake shigar da buk’atar Aunty Fauziyan awajen Barrister’n.

D’an Jim Barrister Kabir yayi, cikin d’an nazari kuma yace.

“To shikenan MD, amma kana ga kayarda da matar kuwa, kana ga sirrinmu bazai fita awajenta ba.”

Yayi mgnar murya a sake dan yanzu ko mgnar ta fita yana da ɗan yaƙini fito na fito da magautanta sai dai baida cikekkun hujja.

“Sosai kuwa Barrister, saboda Fauziya D Sulaiman macece mai amana, karanci, tausayi, da  saukin kai, kuma akwai rawar da zata iya takawa, musamman Kodan wajen bawa, Jannart din shawarwari ma.”

MD din ya fad’a.

Jin hakanne kuma yasa Barrister Kabir cewa.

“Badamuwa bari na turo muku numbern, amma ko Salman ban yarda a bashi numbern ba, ita matar kawai za’a bawa.”

“To Insha Allah.”

MD din ya fad’a. 

Nan ya katse wayar, da kaman minti d’aya kuwa sai ga, text na numbern Jannart din ya shigo cikin wayar MD.  

Take kuwa MD ya tura mata numbern.

Godiya Aunty Fauziyan tayi masa, cikin jin dadi kuma ta juya ta tafi.

Haka dai Rayuwa ta ci gaba, inda yau ansamu k’arin kwanaki, akan wata d’ayan daya shud’e.

Alhamdulillah kuma abubuwa duk, suna tafiya yanda ya kamata, musamman a b’angaren Rayyern, wanda ayanzu kusan kullum Idan ya fita, baya dawowa sai dare,  saboda yakanje asibiti da company, shiyasa gaba d’aya ma ko isashshen zama baya samu.

Ab’angaren Jannart kuwa rayuwarta take normal, saboda ayanzu ta gama sabo da duk y’an gidan, Masha Allah komai yana tafiya mata daidai sai dai time to time tana tuno gidansu har tayi kwalla.

Acan tashar tasu kuwa, yau din Aunty Fauziyan ce zaune, acikin office dinta, wayarta ce kuma ke rike ahannunta. 

Gaba daya ta shiga cikin nazarin kiran wayan Jannart, saboda yanda take kokonto akan ta kira ne ko a’a.

Ayau dai kam ta yanke shawarar kiran wayan Jannart din.

Acan gidansu Rayyern kuwa, yau Nasir yazo, hakan yasa suka had’u shida Riyyam nsra da kuma Ramadan.

Gaba d’ayansu afalon saman suka zauna, haka duk suka cika musu gidan da sowa, saboda Kallon wasan k’wallo da sukeyi.

Wanda kuma sun samu freedom din nasu ne, saboda ganin Rayyern baya nan.

Ciye ciye kuwa ba kalan wanda ba suyi ba, bayan pizza da shawarman da sukaci, hatta sweet saida suka sha, anan kuma cikin falon suka zubar da ledodin musamman Nasir shima dan masifan son zaƙine,  haka kuma duk wasu pillows dake jikin kujerun falon, saida suka watsar dasu sukayi musu d’add’aya. 

Bayan sun gama abunda za suyi ne kuma suka fice, batare da sun gyara falon ba.

Rayyern kuwa yaudin ad’an gajiye ya dawo gidan.

Wanda hakanne ma yasa bainemi su Mamy ba, kaitsaye ya wuce saman.

Saidai yana shiga, abunda ya gani ya sashi d’an zaro idanunsa.

“What is this?”

Ya fad’a yana me Kallon yanda falon nasu ya haukace. 

Saurin Ajiye briefcase d’insa yayi, tare da juyawa cikin sauri ya koma, domin yasan hakan ba aikin kowa bane, saina su Ramadan da Riyyam-nsra.

“Mamy Mamy!!”

 

Da k’arfi yake d’an k’wala k’iran sunan Mamyn, yana me saukowa daga kan steps din.

Mamy kuwa jin kiran da Rayyern din keyi mata ne, yasa ta d’an lek’owa daga kitchine tare da cewa.

“Lafiya kuwa Rayyern?”

Fuskarsa ya d’an kwab’e tare dasa hannu, ya kama waist d’insa, cike kuma da takaici yace.

“Mamy Ina su Ramadan, kinga yanda suka yi min kaca kaca da falo kuwa? sunb’ata min komai, sunyi ciye ciye sunbar duk wani datti awajen, Mamy wallahi ki kirasu suzo su share.”

Ajiyar zuciya Mamyn ta sauk’e, tare kuma da komawa ta zauna, tana me cewa.

“Nifa banmasan da yaushe suka fita ba, nasan dai d’azun sunanan harma da Nasir, amma yanzu kam da ‘alama basa ma cikin gidannan.”

Fuskarsa ya sake kwab’ewa, still cikin kame k’ugu yace.

“Gaskiya ni Mamy azo agyaramin, sun b’ata komai ko wajen da mutum zaibi mai tsabta babu.”

Murmushi Mamy tayi saboda sanin halin rigima, irin nasa da tayi ne kuma yasa, ta kalli Jannart da yanzu fitowarta, cikin dan tausasawa tace.

“Dan Allah Jannart jeki gyara masa falon, nikam aiki nakeyi a kitchine, Idan ba haka ba wannan da kike gani bazai barmu ba, ya tamana kwarnafi kenan kaman mu muka b’ata.”

“To.”

Jannart din tace tare da sunkuyar da kanta k’asa, kana anutse ta haura saman.

Shikuwa Rayyern sauka falon kasan yayi ya zauna.

Koda ta haura kuwa Anutse ta soma tattare falon, cikin mintuna kad’an kuma ta kammala, air freshener ta fesa tare da jawo kofar ta rufe.

Kana anutse ta sauk’o k’asa.

Tun fara sauk’owanta daga kan steps kuwa ya tsurawa, kyawawan k’afafunta ido, musamman yanda ta d’an tattare sket dinta, hakan yasa yake iya hango kyawawan singalalinta. 

Itakuwa Jannart Anutse ta k’arasa sauk’owa k’asan.

“Yunwa nakeji.”

Ya fad’a still bai d’auke idanunsa daga kan kafarta ba dan yana tsoron kallon samanta gani yake zata tsole mishi ido da waɗannan abubuwan nata saukinta  ɗaya bata rabuwa da mayafi.

 

Kai kawai ta jinjina masa, alaman to, kana cikin nutsuwa ta nufi kitchine. 

 Fried rice and coleslaw da kuma tamarin juice ta kawo masa, Anutse ta ajiye abincin agabansa, daidai lokacin kuma wayarta dake aje gefensa, ya soma tsuwa alaman shigowar kira. 

Saurin d’agowa tayi tare dakai dubanta, ga screen din wayar, Ganin new number’n dake kiranta ne kuma, yasa duk ta cika da mamaki, Ahankali kuma ta dawo da kallonta garesa,  wanda shidin ma kuma idanu ya zuba mata.

Sake Kallon wayartata tayi, cike da mamaki.

Shikuwa Rayyern fuska ya tab’e, cikin kuma halin ko inkula yace.

“Kima daina wani pretending ki daga, ki fada musu cewar na warke, domin basu samu yanda suke soba, ban mutu ba.”

Idanunta ta d’an zuba mishi, cike da mamakin kalaman nasa, da yakeyi wanda akullum bata fahimta, batasan me hakan yake nufi ba, shin wai baiyarda da ita bane ko kuwa, yana ga kamar cutar dashi zatayi.

Kanta kawai ta girgiza tare da d’aukan wayan nata, Ahankali ta sakala wayar akan kunnenta, saidai batayi gangancin fara magana ba.

Daga can b’angaren Aunty Fauziya kuwa, Jin an d’aga wayar ne yasa ta yin sallama.

Aikuwa take Jannart ta d’auko muryar, lokaci guda cikin mamaki da farinciki tace.

“Laa My Aunty  kece?”

“Eh nice Jannart, ya kike ya kwana biyu.”

Aunty Fauziyan ta tambaya tana murmushi.

Cike dajin dadi Jannart din tace.

“Lafiya kalau my Aunty, wallahi nayi kewarki a ina kika samu number na.”

“Nima haka Jannart, numbern ki kuma Abbanki ne ya bani.”

Aunty Fauziyan ta fad’a cikin kulawa,  tare kuma da cewa.

“Fatan kuna lafiya ya maigidanki?”

D’an juyowa Jannart din tayi ta kalleshi, wanda kuma shidinma kuma ita yake kallo. 

Saurin juyar da kanta tayi, kana cikin sanyi yace.

“Lafiyanshi k’alau.” 

“Masha Allah, Kodai yana kusa ne naji muryarki k’asa k’asa.

“Uhummm.”

Jannart din ta amsa tana dan Murmushi.

Jin hakanne kuma yasa Aunty Fauziyan cewa.

“Shikenan Jannart muyi waya anjima, yanzu bari na barki kiji dashi.”

Tana gama fadin hakan kuwa ta katse kiran. 

Jannart kuwa batare da ta sake juyowa ta kalleshi ba kaitsaye ta wuce d’akinta. 

Shikuwa Rayyern bayan ya gama cin abincin ne ya tashi ya haura sama.

To ahaka dai rayuwa taci gaba da tafiyar musu, bayan 5 weeks kuma abubuwa duk sun sanja, yanayin gari da kuma weather ya juya izuwa, yanayin zafi, domin zuwa yanzu har anfara iska da kuma hadari dake nuna shigar yanayin farko-forkon damuna.

Kamar yadda yayi kwanaki shida baya, yau din ma tun bayan sallan la’asar, misalin biyar saura.

 Gaba ɗaya garin ya game da hadari, bak’ikk’irin daga gefen gabas kowa ya daga ido ya kalli hadarin sai ya razana, sabida yadda yayi gangami yayi duhu.  saidai kuma cikin dan wani lokaci hadarin ya fara komawa ja, da dukkan alamu kuma, iskane mai k’arfi yake kokarin tashi irin na forkon damuna. 

A cikin compound din gidan nasu kuwa, Abba ne da Baba Mauɗo ke zaune, suna nan zaunen ne kuma suka hango Rayyern wanda ya fito, Cikin nutsuwa yake tafiya.

Yana mai daga kanshi yana kallon saman gidan nasu tare da zazzagaye kowani lungu da sak’o na gidan. 

Baba Mauɗo kuwa binshi da ido yake yana wani irin murmushi mai cike da jin daɗin.

Idanu Abban ya dan lumshe tare da jingine kanshi da jikin bango.

Cikin yanayin nazarta yace.

“Hmmm  gado ba karambani ba, komai na daga cikin d’abi’ar mahaifinshi bai bari ba.”

Shikuwa Rayyern dake ta faman zazzagaye gidan,  yanayin hakanne saboda sunnah ce da Manzon Allah (S.A.W) ya keyi, Idan yaga hadari Yakan zazzagaye gidansa, Dan dudduba abubuwa abinda ke bukatar gyara ya gyara na killacewa a killace.

Yana cikin zagayen ne kuma wayarsa dake cikin aljihunsa ta soma kara.

Koda ya duba, ganin sunan sunan Dr. Sulaiman ne ya sashi d’agawa. 

Bayan sun gaisane kuma Dr. Sulaiman din yace.

“Dr batun tafiya Mascow fa, komai ya riga daya Kankama, Insha Allah nanda 2 to 3 weeks masu tafiya zasu tafi.”

“Okay.”

Kawai Rayyern din yace atakaice tare kuma da katse kiran.

Sabida iskar ta fara saukowa,

Ci gaba yayi da zagaye wajen, harta side din su Baba Maud’o kuwa saida yaje ya duba, Ganin komai normal ne yasashi dawowa cikin gida.

Wanda zuwa lokacin kuwa iskan ya taso gadan gadan.

Lokacinne kuma Abban shima ya shigo, tare da neman waje ya zauna.

Baba Mauɗo Kuma ya shiga side ɗinsu

Rayyern din kuwa windows din dake abude ya rurrufe.

Yayinda Abba kuwa ya zuba masa ido, adai-dai lokacin kuwa shi kadai yasan me yake rayawa acikin zuciyarsa da kuma abinda yake tinawa 

Rayyern kuwa Bayan ya gama rurrufe ko inane, idanunsa suka sauk’a akan k’ofar falon Jannart, da iska ke bud’eshi yana rufewa shi gib da karfi.

Juyawa yayi kamar zai haura sama kuma sai ya fasa ganin Abba nata kallon shi sai kuma ya kalli wannan kofar.

Anutse ya nufi kofar tata, Koda ya isa hannunsa yasa ya tura k’ofar, tare kuma dasa kansa acikin falon, yayi hakanne kuma saboda nan ne kadai falon daya rage da bai duba ba.

Ahankali ya sauk’e idanunsa akan Jannart Wacce ke zaune akan kujera.

Sanye take cikin wata riga Marar nauyi, wanda tayi mata kyau sosai,  ga kuma gashin kanta dake watse dan ko d’ankwali bata dashi.

Idanunta da hankalinta kuwa, duk yana ga tv inda take Kallon wani cartoon mai abin dariya.

Idanunsa ya d’an janye daga kallonta, had’e dajan d’an guntun tsaki, kaitsaye kuma ya wuce dan rurrufe windunan falon.

Sautin tsakin nasa ne kuma yasa Hankalin Jannart dawowa kansa, da sauri ta juyo, ganinsa da tayi ne kuma yasa ta, saurin tashi ta gyara zamanta.

Saidai kuma gaba daya babu mayafi akusa da ita, hakan yasa ta d’an takure jikinta waje daya.

Shikuwa Rayyern ci gaba da rufe windows din yayi har ya juya ya fuskanci tsakiyar falon.

Sai kuma ya ɗan juyo kansa ya kalli bayanshi ganin yadda labuyen suka a harde alamun iskane ya hardesu, ba tare daya juya ba.

 Ahankali kuma ya dan Mika tsawonsa,  dan son gyara labulen daya hard’e asama sabida iskar sosai ya daga hannunsa sabida windows din sunada tsawo sosai.

Hakan kuwa shi yasa rigarsa ta d’age ta ɗanyi sama.

Daga cibiyarsa zuwa kasa suka bayyana,

Dai-dai lokacin kuwa Jannart ta sauk’e Idanunta akan shatin, saman mararsa kasan cibiyarsa da kuma black boxer  din dake jikinsa.

Wanda ya kara haska farar fatarsa.

Idanunta ta zubawa wajen, bata ko k’yaftawa, saboda yanda shatin marar tasa ya bayyana sosai, ga kuma hasken da wajen ke dashi kana ga wani tattausan gargasa dake kwance daga ƙasan cibiyar tasa har zuwa ƙasa sosai inda robar boxes dinsa ke manne da jikinsa har ana iya ɗan hango saman mararsa kana asalin dogon wondon kuma yayi ƙasa sosai kan mazauna sa wanda haka yasa shatin surar jikinsa bayyana.

Wani irin rawa takejin jikinta da idanunta sunayi.

Yayinda gaba ɗaya tsikar jikinta ke mimmiƙewa tsaye.

Wani irin harbawa zuciyarta keyi mai tafe da tsoron abinda idonta bai taɓa katari dashiba.

Rayyern kuwa kanshi na sama, baima san tana kallonshi ba.

Saida ya gama warware labulen.

ahankali ya d’an sauk’e hannunsa sama, tare da juyowa ya sauk’e idanunsa akanta da sauri ya sunkuyo ya kalli setin inda take kallo a jikinsa.

Fuskarsa ya tsuke tare da tab’ewa kana ya watsa mata wata Zazzafar hararanta cikin takaici yace.

“Meye? Mayya kawai cinyeni zakiyi ne?”

Da sauri ta kauda idanunta tayi daga garesa, tare da mikewa tsaye ta d’auki wayarta yayinda wata azabebbiyar kunya ta rufeta. 

Ahankali ta dan Raba zata wuce zuwa daki.

Shikuwa Rayyern cikin tsautsayi, labulen da yake gyarawan ya ture  wani goran ruwa dake gefe, hakan kuwa shi yasa ruwan ya malale awajen.

Juyawa shidinma yayi da niyar fita, dai-dai lokacin kuma Jannart ta iso sukayi gab da gab, batare da sun Ankara ba kuwa, saiji yayi gaba daya tsantsi ya debe sa  Suuuuuu haka ya tafi idanunsa ya zaro, tare kuma da fad’awa kan Jannart, wani irin masifeffen tsorone da fargaba ya rufeta wanda yasata rumtse idanunta jin sun tafi suuuu sun f…

Jannart suuu suka tafi, cikin tsoron  kaiwa k’asa Jannart ta sanya hannayenta akan damatsan sa, tare da rikesa k’am, kana ta rumtse Idanunta da masifan karfi.

Aikuwa duk da yin hakan da tayi bai hanasu kaiwa k’asa ba, cikin abunda bai wuce 1second ba gaba d’aya duk suka zube awajen saidai shi ya koma kasa ita a sama.

“Auchhhhh!!”

Rayyern ya fad’a da k’arfi tare da rumtse idanunsa.

Wanda ya fadi hakanne  kuma saboda buguwan da yayi, ga kuma Jannart da ta fad’o saman k’irjinsa wacce tsoro yasa ta maƙalƙale masa.

Jannart din ma wani siririyar k’ara ta saka, musamman da kirjinta ya bugu ajikin nasa kirjin sosai taji tsayayyun breast ɗinta sun bugi kirjinsa. 

Atare duk suka rumtse idanunsu, saboda zafin fad’uwar da sukayi ne kuma, yasa duk kowannensu ya kasa yin k’wakk’waran motsi.

Still Har yanzu kuwa hannayen Jannart nakan dantsen hannunsa, tayi masa wani irin rik’o dake bayyana tsoronta. 

Yanayin yanda suka kasance ahaka dinne kuma yasa, d’an kunnen Jannart din mak’alewa da gaban rigarsa, Ahankali ta d’an d’aga kanta, saidai jin rigar tasa ya kama d’an kunnenta ne yasa ta kasa d’agowan,  saboda wani zafi da taji. 

Dai-dai lokacin kuwa gaba d’aya duk wani haske dake cikin d’akin ya d’auke, saboda d’auke wuta da akayi sabida iskar data turbude garin Kano baki ɗaya, ga kuma yanayin garin kwata kwata babu wadataccen haske yayi duhu.

Shi kuwa Rayyern al’amarin ya magaga ya zarta zatonsa ya kama hanyar wata fitinenneyar duniyar da bai san sa ita,

Sabida yadda yake jin wasu irin masifaffun abubuwa suna tsikarinsa sabida yadda yaji sauƙan Cabɓullenta bisa nasa ƙirjin.

Wani irin maraitaccen numfashin yaja can ƙasan maƙoshinsa tare cusa kanshi tsakanin wuyanta da kafaɗarta wani numfashin ya kuma sha sabida sassayan ƙamshinta da ya zuƙa.

Idanu Jannart ta d’an rumtse, cikin gajiya da kuma zafin da take d’anji ajikinta, ta d’an sake matsar da kanta saman kirjinsa, wanda kuma burinta shine ta samu ta zare d’an kunnenta daga jikin rigarsa.

Hakan da tayi d’inne kuma ya bata daman jiyo bugun zuciyarsa, wanda take tafiya da sauri sauri dib-dab-dib-dab.

Idanunta ta d’an lumshe tare da soma d’an jujjuya kannata, dake kwance saman kirjinsa, saboda ta kosa dan kunnen nata ya fita.

Shikuwa Rayyern dake kwance ak’asanta, hannunsa d’aya yasa ya kama gefen ba yansa, tare kuma da lumshe idanunsa, Ahankali k’amshin dake fita ajikinta, da kuma wanda ke fita acikin gashinta ke ratsa cikin hancinsa.

Sosai yake iya jiyo bugun zuciyarta daga cikin kirjinsa.

Idanunsa ya kuma rumtsewa adai-dai lokacin da yaji tana murza kanta akan chest d’insa.

Lokaci d’aya kuma yaji wani irin abu nabin kowani sashi na jikinsa.

Yaarrr yarrrrr haka tsikar jikinsa ke zubawa, Yayinda duk wani kofan gashi na jikinsa, ke bubbud’ewa.

Tun da yake aduniyarsa bai tab’ajin hakan ba, bai kuma san menene hakan ba, sai ayanzu da yaji yanda d’umin numfashin Jannart d’in, ke dukan wuyansa, ga kuma yanayin yanda yaji tana juya kanta akan kirjinsa, da wani irin salo.

Bugu da k’ari for the first time daya tab’a kasancewa da Mace haka, tunda yake aduniya hakan bai tab’a faruwa dashi ba sai yau, bai tab’ayin kusanci da Mace sosai haka ba bai tab’a sanin ya ake fuskanta ba in anyi kusanci da juna.

Idanunsa ya d’an sake rumtsewa, tare kuma dasa hakorinsa ya ciji jajayen labb’ansa.

Kwata kwata bazai iya jurewa kasantuwarsu ahaka ba, domin shi kam awajensa hakan bak’on lamari ne, da bayajin k’wak’walwarsa zata iya d’auka saboda abubuwan masu yawa ke ɗaurewa da kwancewa a sasan jikinsa.

D’an yun k’urawa yayi da niyar tashi, amma sai yaji ya kasa, saboda Jannart din dake kansa, da kuma bayansa wanda ya d’an rik’e.

“Wayyo Allah, ke ki tashi akaina mana, ko doki kika samu ne?” 

Ya k’are maganan da wata irin fitinenniyar murya yana me taune lips d’insa.

Jannart dake kwance akansa kuwa, Jin abunda ya fad’a d’inne kuma yasa ta turo d’an k’aramin bakinta, gaba Cikin yanayin shagwab’a tace.

“Ni bazan iya tashi ba, d’an kunnena ya mak’ale ajikin shirt dinka, Idan na tashi da k’arfi kuma kunnena zai yage.” 

“To ya yage din mana sai meye, nidai da halla malama tashi akaina, da nauyinki zanji Koda zafin fad’uwan da nayi, Dan mugunta ma ai ke ya kamata ki fad’a k’asa ba niba.” 

Ya fad’a yana me yunk’urin tashi zaune.

Hakanne kuma yasa Jannart din sakin wani k’ara tare da manna kanta da ƙirjinsa da kyau kana ta kara rumtse damatsan hannunsa, saboda d’agowan da yaso yi ya sa tajin kunnenta zafi sosai.

“Auchhh kunnena.”

Ta fad’a cikin wata irin shagwab’abbiya kuma kasalalliyar muryar, daya sashi komawa ya kwanta lib.

Hakan ko yasa ta ɗan ɗago, sai kuma tayi maza ta sake fad’awa jikinsa, saidai awannan karon atausashe kirjinta ya fad’a kan nasa.

Wani irin shocking yaji  tun daga k’asan k’afarsa, har zuwa tsakiyar madigan kansa wanda hakan yasa Rayyarn nasa wani irin masifeffen harbawar daya sashi furta.

“Aushhhhhyyyyyohhhhh”.

Yaja sautin da karfi dan abin yazo masa a bazata.

Taushi da kuma tudun tagwayen abu biyu masu kamar audugan da yaji 

Akan kirjinsa ne,  yasa shi rumtse idanunsa da sauri, tare kuma da dunk’ule hannayensa.

Lokaci d’aya kuma numfashinsa ya soma wani irin fusga,  Yayinda zuciyarsa kuwa ta shiga bugawa a millions.

“Yah Salam  wayyoooooooo Allah na ni mema ya shigo dani wannan jarabebben d’akinne? Why Rayyern Why?” 

Ya fad’i hakan azuciyarsa, yana mejin tamkar yasanya hannayensa ya tureta, ko hakan zai sa ya daina jin abubuwanda yakeji na game dukkan sasan jikinsa gaba ɗaya, wanda kwata kwata arayuwarsa baima sansa ba to amman kuma haka nan sai yaji ya kasa baya son tureta, sai yakeji tamkar su tabbata a haka.

Jin sautin  bugun zuciyartasa ne kuma, yasa Jannart d’an d’agowa, saidai bata wani Kallon fuskarsa da kyau saboda duhu.

“Meyasa zuciyarsa ke bugawa fast fast haka?”

Tayiwa kanta tambayar, dai-dai lokacin kuma Cikin ikon Allah ta samu ta zare d’an kunnenta daga jikin rigar tasa.

Hakanne kuma ya bata daman d’ago Kanta, tare da mirginawa cikin sauri ta sauk’a ajikinsa. 

Jin ta sauk’a daga jikinsa ne kuma, yasa shi sauk’e wani irin ajiyar zuciya tare da mikewa tsaye cikin sauri wani irin haushin sauƙan nata daga jikinsa ne ya rufesa har kamar ya saki kuka. 

“Mcheeeww mutun sai nauyi kamar dutse.”

Ya fad’a abayyane yana me shafa bayan rigarsa, dake Jik’e da ruwan. 

Jannart kuwa duk da cewar baya ganinta, sosai baki ta murgud’a masa, tare da d’aukan wayarta tamik’e tsaye.

Kaitsaye d’akinta ta wuce, domin shima Rayyern din yana tashi, baijirayi komai ba ya nufi hanyar fita daga cikin dakin.

Ahankali yake tafiya yana d’an ciccije bakinsa, har ya gama fitowa daga part din Jannart din.

Dai-dai ya fito falonne kuma idanunsa, suka sauk’a akan Abba dake zaune bisa kujera.

Hakanan yaji kirjinsa ya buga, lokaci d’aya kuma yaji wani irin masifeffen kunya Abban nashi ya kamashi, akaro na farko kuma kenan yanzun, agaba d’aya rayuwarsa da yaji kunyan Abban nasa ta kamasa.

Tamkar wani marar gaskiya haka yayi k’asa da kansa, kana cikin sanyi ya taho sad’ab sad’ab ya haura sama sam ya kasa ya mishi mgn, sai yakeji tamkar Abba yaga abinda ya faru.

Da kallon mamaki Abba yabi bayan Rayyern din, musamman da yaga yanda bayan rigar Rayyern din, ke jik’e da ruwa, wanda kuma shi a iya saninsa, ko digon yayyafi ba’ayiba balle ko yace shiya jik’a Rayyern din.

Ajiyar zuciya kawai Abban ya sauk’e, tare da mik’ewa shima yayi b’angaren sa.

 Rayyern kuwa yana haurawa sama, rigar dake jikin nasa ya cire.

Tare da sanjata izuwa wata, Ahankali ya d’an zauna abakin gadonsa tare da jawo Laptop d’insa ya soma hidimar tafiyarsu Mascow. 

Saidai gaba daya ya kasa daina jin k’amshin Jannart din acikin hancinsa. 

D’an rumtse idanunsa yayi, tare kuma da bud’esu alokaci guda, cikin d’an yanayin k’osawa yace.

“Fitinanniya.”

Acan b’angaren Jannart kuwa Koda ta shiga d’akinta, kwanciya tayi lub akan gado, tare da d’aukan wayarta ta soma buga game.  

Duk yanda taso maida hankalinta akan game din kuwa abun yaki, domin hakanan takejin k’amshin jikin Rayyern din, ya kasa barinta tayi sukuni, duk da cewar baya wajen amma mayen kamshinsa yana wajen. 

Fuskarta ta d’an ya mutse, tare da shagwab’e murya, cikin kasa da murya tace. 

“Ai duk shiya jawo muka fad’i, da wani k’amshinsa awajen.”

Yanayin yanda tak’are maganan tana murgud’a baki, Idan ka gani zakayi tunanin agabansa take. 

Almost 40minute kuwa ana tsula iska kana hadarin gaba d’aya ya washe, dai-dai lokacin kuma aka soma kiraye kirayen sallan magriba.  

Atare duk mazan gidan suka wuce masallaci, Abba, Rayyern Ramadan da kuma Riyyam-nsra. 

Acan suka iske Baba Maud’o ma, wanda shi yakan riga ma kowa dake gidan tafiya masallaci.

Koda sukayi sallan magriban kuwa, basu fito daga masallacin ba har saida suka sallame sallan Isha.  

Koda suka dawo gida, anan kan dining table suka zauna, Yayinda Abba kuwa ya wuce sashinsa kaitsaye.

Mamy ne takai masa abincinsa, Ramadan da Riyyam-nsra kuwa Jannart ce tayi saving d’insu.

Ubangayyan kuwa bai hawo kan dining table d’in ba, anan cikin falon ya zauna, batare kuma daya ce akawo masa nasa abincin ba.

Itakuwa Jannart tana sane dashi, amma saita share batare da ta tambayesa ko yana buk’atar abinci ba, ta nemi waje ta zauna, tare da soma tsakalan abincin da ta zubawa kanta. 

Rayyern dake zaune kuwa Ganin Mamy ta fito daga b’angaren Abba ne, yasa shi mik’ewa tsaye.

“Babana kai bazakaci abincin bane?”

Mamy ta tambaya da kulawa.

Fuskarsa ya d’an yamutsa, cikin kuma halinsa na rashin son yawan mgn daya tashi masa yau din yace.

“Ba’a bani ba”.

Yanayin yadda yayi mgnar yana kuma kallon Jannart ƙasa-ƙasa ne yasa, Mamy yin murmushi tare da cewa.

“To bari a kawo maka”.

Cikin kauda kai yace.

“No Mamy ni nakoshi.”

“Amma Babana kafasan baka jima da tashi daga ciwo ba, Meyasa bazaka maida hankalinka wajen cin abinci akan lokaci ba?”

Mamyn ta fad’i haka cike da nuna masa, tsananin soyayyar da takeyi masa. 

D’an marairaice fuskarsa yayi,  hakan yasa yayi tamkar k’aramin yaro.

“Seriously Mamy nak’oshi ne, kuma anjima zansha tea, yanzu bari naje wajen Abba.”

Ya k’are maganar yana me nufan sashin, Abban kaitsaye.

Mamy kuwa da Idanu ta bishi har saida ya shige part din Abban, kafun ta janye idanunta tare da dawowa kan dining table din ta zauna. 

Ahankali Rayyern ya tura k’ofar d’akin Abban ya shiga bakinsa d’auke da sallama.

Abba dake zaune akan carpet, yana cin abinci ne ya d’ago kansa, tare da amsawa Rayyern din sallaman, fuska asake yace.

“Rayyern shigo mana.”

Abban ya fad’a cikin kulawa. 

K’arasowa cikin falon Rayyern din yayi, tare da matsowa ya rusuna agaban Abban nasa, cikin girmamawa had’i da ladabi yace.

“Abba barka da warhaka.”

Kai Abban ya jinjina, tare da d’aukan d’aya daga cikin spoons d’in dake, kan tray din abincinsa ya mik’awa Rayyern din.

“Muci abinci.”

Abban ya fad’a cike da kulawa.

Kansa ya d’an rausayar gefe, tare dasa hannu ya shafa cikinsa, cikin sanyi yace.

“Abba nak’oshi.”

Kallonsa Abban yayi kamar zaice wani abu kuma saiya fasa, saboda dama yasan halin Rayyern cin abinci akai-akai bawai ya wani damesa bane sai daifa idan ya ritsa abinda yakeso ba sauki. 

Rayyern kuwa d’an gyara zamansa yayi, tare da fuskantar Abban nasa, cikin muryar dake nuna girmamawa yace.

“Abba dama akan maganan tafiyarmu Mascow ne”.

D’an zuba mishi ido Abba yayi kana ya dauki cup ruwa ya dan sha kana ya aje tare da cewa.

“Uhum ina jinka”.

Gyara zamansa ya danyi tare da ci gaba da cewa.

“Yanzu mun kammala komai ranar tafiyan nata matsowa, kuma Ina d’aya daga cikin way’anda zasu tafi, saboda ni nema zanyiwa sauran Doctor’s din jagora,  da nayi tunanin bazanje ba, amma kuma sai naga zuwan yana da muhimmanci, saboda akwai babban likita daya daga cikin malamaina nacan, daya nunamin dacewar zuwan nawa, tunda duk way’anda zasuje din ak’ark’ashin kulawana suke, To ya kamata na kasance tare dasu.”

D’an dakatawa da cin abincin Abba yayi, tare kuma da d’ago kansa ya kalli Rayyern din, cikin gamsuwa yace.

“Masha Allah, ashe har tafiyar tayi kusa, zuwa nanda yaushe ne zaku tafi?”

“Nan da sati biyu Insha Allah.”

Kai Abba ya jinjina tare da cewa.

“Allah ya kaimu, amma naji ku biyar zaku tafi, saidai ka manta masauk’inmu da yake can, wajen zaman mutum biyu ne kawai sai inga kamar zaku takuru a ɗan gidan tunda ba wani babba bane.”

Kai Rayyern din ya jinjina tare kuma da gyara zamansa, cikin kwantar da murya yace.

“Eh Abba, su sauran staffs din namu, hotel zamu kama musu, nida Usman P.A ne kawai zamu zauna, anan gidan.”

Kallonsa Abba yayi cikin dan yanayin mamaki yace. 

“Kaida Usman P.A kuma?”

“Eh Abba, dashi zamu tafi saboda nasan zai d’an ragemin wasu ayyukan.”

Rayyern din ya fad’a atausashe, daga cikin zuciyarsa kuwa yana tsoron kada Abban, nasa ya shigo da wata buk’atar.

Abba kuwa kansa ya girgiza, tare da cewa.

“A’a kam bada Usman P.A zaka tafi ba, da matarka zaka tafi.”

Azabure Rayyern din ya d’ago kai, tare da zaro idanunsa ya kalli Abban, cikin yanayin kad’uwa yace.

“What Abba….”

D’aga masa hannu Abban yayi alaman dakatarwa, cikin nuna masa gaskiya da kuma hakikanin tabbacin maganansa yace.

“Na maimaita da matarka zaka tafi Rayyern, ba kuma zan sanja magana ba, saboda banason irin abunda ya faru dakai a China ya sake faruwa,   Ina da tabbacin cewa matarka zatafi kula dakai, fiye da Usman P.A, domin shi ba ad’aki d’aya zaku dinga kwana ba, kaga bai zama lallai yasan awani hali kake ciki ba a cikin dararen zamanku a can,  amma matarka fa tana tare dakai akoda yaushe, Dan haka za tafi kowa, sanin wanne hali kake ciki.”

D’an numfasawa Abban yayi, kana cikin kulawa yaci gaba da cewa.

“Lafiyarka tafi mana komai Rayyern, akoda yaushe bama son duk wani abu na cutarwa dazai sameka, saboda haka bazamu tab’a barinka ka kasance awata duniya, Kai kad’ai babu wani mai baka kulawa ba.”

Fuska Rayyern din ya kwab’e, lokaci d’aya kuma yaji komai duk ya daina yi masa dad’i, bakinsa ya bud’e ahankali da niyar yin magana.

Saurin dakatar dashi Abban yayi,  cikin tsare gida yace.

“Kada kace komai Rayyern domin wannan Umarni nane, bawai shawara ba.”

Abban ya fad’i haka cikin tsare gida, tare kuma da jajjadada umarninsa. 

    K’asa Rayyern din yayi da kansa, tare kuma da d’an marairaice fuska cikin sanyi yace.

“Kayi hakuri Abba bawai Ina ja da umarninka bane, amma Barrister Kabir yace baya son kowa yasan cewar tana nan gidan, Koda kuwa zuwa nan da compound d’in gidan ne.” 

“Nasan da hakan, shiyasa ma tafiyar da zakuyin babu wanda zaisan kun tafi tare, tunda bawai da kowa da kowa muke mu’amala ba sannan kuma tafiyarku tare kamar wani matakin tsaretane.”

Abban ya fad’a yana me gyara zama danci gaba dacin abincinsa.

Rayyern kuwa badon yaso ba, haka ya mik’e tare da yiwa Abban sallama, kaitsaye ya fice daga cikin falon. 

Direct main falo d’insu ya nufo.

Dai-dai lokacin kuwa Mamy da Jannart d’in ke zaune,  inda Mamyn ke kan sofa, sai Jannart dake zaune ak’asa tana latsa wayarta.

K’arasowarsa cikin falonne kuma, ya sanyashi kama k’ugu, tare da Kallon gefen da Jannart d’in take, k’asa k’asa ya watsa mata wani kalon da bai san manufarsa ba.

Cikin kuma yanayin shagwab’a ya kalli Mamynsa, tare da karyar da wuya, asanyaye yace.

“Mamy inason muyi magana.”

Jin abunda ya fad’a d’inne kuma yasa, Mamy d’agowa ta kalleshi.

“Magana kuma Rayyern, to inajinka.”

Mamyn ta fad’a tana me maida hankalinta garesa.

“No Mamy dake kawai nakeson magana.”

Ya fad’i hakan cikin gatse da kuma gayya, tare kuma da sake hararan Jannart k’asa k’asa, wanda ita batama san yanayi ba.

Mamy kuwa jin abunda ya fad’a d’inne yasa ta, Kallon Jannart dake zaune, ganin kuma gaba d’aya hankalin Jannart din ba akansu yake bane, yasa Mamyn mik’ewa, cikin nutsuwa tace.

“To mu haura sama.”

Ai kuwa kaman jira dama yake tuni ya shige gaba, Mamyn na biye dashi a baya.

Suna shiga cikin falon nasu kuwa ya juyo, tare da Kallon Mamyn nasa, cikin son isar mata da k’orafi yace. 

“Eyyah Mamy kiji Abba fa, wai  da wancan yarinyar yakeson naje Mascow, Mamy takurani  zatayi Allah, ni kuma Mamy banason takura, yanzu meye laifi Idan na tafi da Usman P.A?.”

Murmushi Mamy tayi, tare da kallonsa Cikin kulawa tace.

“To meye abun damuwa acikin wannan Rayyern, ka tafi da ita mana, kuma kasan baka isa tsallake umarnin mahaifinku ba, Lallai dole abunda yace shi za’ayi, kuma nima bani da wani ja akan hakan.”

Fuskarsa ya shagwab’e tare da karyar da wuyansa gefe,  cikin sanyi da rashin samun k’arfin guiwa yace.

“To yanzu Mamy Dan Allah kiyi wani abu mana.”

“Ni babu abunda zan iya Rayyern, kasan waye Abban ku Idan yayi magana baya tab’a sanjawa, nima kuma Ina goyan bayan hakan, saboda hujjar daya kawo hujja ce mai kyau.”

Mamyn ta fad’i hakan cike da son jaddada masa yiwuwar hakan.

Shikuwa Rayyern gane akan maganar tasu babu wani sauyi ne, ya sashi juyawa tare da neman waje ya zauna.

Mamy kuwa kanta kawai ta girgiza, tare da juyawa ta fice daga falon.

Kaitsaye falon k’asa ta nufa, anan. Ta iske Ramadan da kuma Riyyam-nsra wanda yanzu shigowansu, kasancewar bayan sunci abincin daren sunfita wajen su Baba Maud’o.

 

Ganin sunata hira ne kuma yasa Mamyn wucesu,  kaitsaye ta nufi b’angaren Abba.

Su kuwa su Ramadan sun jima suna hira, kafun daga bisani Jannart ta wuce d’akinta, Ganin hakanne kuma yasa suma duk suka watse.

D’aki suka koma inda kowannensu ya rungumi wayarsa,   Musamman Riyyam-nsra da ya sakeyin wata sabuwar budurwa, y’ar k’asar Nigeria kuma y’ar nan cikin garin kano, wanda ta nace masa akan cewar tana son su had’u.

Shikuwa Ganin yanda take tura masa wasu part, daga cikin body dinta ne yasa shi, bata duk wani attension d’insa.

Saidai kuma gaba d’aya ya kasa, sanin wani karya zaiyi, Dan samu ya fita ko zuwa hotel ne su had’u da yarinyar dan sam Rayyern ya saka masa takunkumi. 

Acan b’angaren Jannart kuwa, tana shiga d’akinta kwanciya tayi,  kasancewar ta gaji ne kuma yasa cikin mintuna kad’an bacci ya d’auketa.

               Washegari

 kamar kullum ita ta taya Mamy duk wasu aikace akace, bayan sun kammala breakfast bayan taci nata ne, kuma ta koma daki ta kwanta.

Ab’angaren Rayyern kuwa tun  6 ya wuce hospital, saboda akwai wasu patient da yake son dubawa. 

Bayan kuma Rayyern din ya tafi ne kuma, Ramadan shima ya mara masa baya, saidai yau harda Riyyam-nsra suka tafi hospital din, saboda shi yace bayason zaman gida. 

Ganin duk gidan yayi shiru ne kuma, yasa Mamy da Jannart watsewa afalon suma.

 Rayyern kuwa bashi ya dawo gidan ba, sai bayan oppsallan magriba.

Bayan sunyi sallan Isha ne kuma duk suka shigo gida.

Bayan sun kammala Diner ne kuma, suka dawo cikin falon suka zauna.

Jannart ce ta fito daga cikin d’akinta, inda  take cikin wani had’add’en doguwar riga navy blue, wanda yayi mata matukar kyau.

Musamman da ta yafa d’an siririn farin mayafi akanta.

Fitowan nata kuwa, yayi daidai da shigowar Rayyern cikin falon, karab kuwa ya sauk’e idanunsa akanta.

Duk da cewar ba akusa suke ba, amma hakan bai hanasa.

 Ganin k’yallin da fuskarta keyi ba, still ga kuma bakinta, da yake fitar da shining na pink lipstick din da ta saka.

Janye idanunsa yayi daga kallonta, tare da k’arasowa cikin falon ya zauna.

Ita kuwa Jannart batare ma da ta lura dashi ba, kaitsaye kitchine ta wuce.

Koda taje ta samu sandwich d’in da take gasawa ya gasu. 

Kashe oven din tayi, tare da d’aukan wani bowl, bayan ta saka poil paper aciki ne kuma, ta juye duka sandwich din.

D’aukan bowl d’in tayi ahannunta, tare da nufowa falon cikin takun ta na nutsuwa.

D’an tsayawa tayi ta d’auki tissue paper, kana ta k’arasa isowa cikin falon. 

Da Murmushi Mamy ta kalleta, kana fuska asake tace.

“Jannart sarkin aiki, sannu duk kin cika mana gidan namu da k’amshin sandwich din naki.”

Murmushi Jannart din tayi, tare kuma da matsowa ta ajiye bowl d’in sandwich din agaban Mamy.

Cikin kuma d’an yanayin alk’unya tace.

“Bismillah Mamy kici sandwich din.”

“Haba My Aunty Mamy kawai, tun d’azu fa muke zaman jiran sandwich din, da k’amshinsa ya cika ko ina dake cikin falon nan, Allah tun kafun ki kammala yawuna yake ta tsinkewa.”

Ramadan ya fad’a yana me matsowa, kusa da bowl din, tare da yagan tissue ya d’auko sandwich din guda d’aya.

Janart kuwa Murmushi tayi, tare da neman waje ta zauna akan sofa. 

Ramadan kuwa Koda yakai sandwich din bakinsa idanu, ya lumshe, tare da jinjina kai, bakinsa cike da sandwich din wanda yaji rid’i yace.

“Gaskiya Aunty Jannart you’re the best, komai kin iya domin ban tab’a cin sandwich mai dadin wannan ba da  Allah waya koya miki girki haka?.”

Murmushi Jannart tayi tare da cewa.

“Malamai na nada yawa, Mom Aunty Dijat da kuma AYSHA ALIYU GARKUWA marubuciyar littafin GARKUWA dan na koyi abubuwa da yawa a ciki littafin sai kuma shirin Akoshi da rufi na tasharmu”.

Yana mai haɗiye na bakinsa yace.

“Kai Allah yayi musu al’barka ya jikansu suda iyayensu al’farma Annabi da al’ƙur’ani, ai mu sun mana gata Allah kawo Raihana ki koya mata komai”.

Dariya sosai Riyyam-nsra, Jannart, Mamy sukayi suna masu cewa Amin.

Riyyam nsra dake zaune ne ya taso cikin dariya da sauri, tare da cewa.

“Nima ai baza’ayi banda niba wanga santi.”

Ya kare maganan yana me daukan sandwich din yakai bakinsa. 

Idanu ya lumshe tare da jinjina kansa, saboda yanda yaji dadin sandwich dinma harya zarce yanda Ramadan ke fadi.

Rayyern kuwa tab’e bakinsa yayi, tare da kawar da kansa gefe.

Riyyam-nsra kuwa sake gyara zama yayi, tare da ninke k’afafunsa, d’ago da kansa yayi ya kalli Mamy da kuma Rayyern, lokaci d’aya kuma sai yaji duk jikinsa yayi sanyi, wanda hakan yasa asanyaye yace.

“Mamy, Hamma Rayyern this week dinnan fa zan koma Ethiopia”.

Cikin abinda ba gaza one second ba duk suka katse dariyarsu tare da zuba mishi ido cikin tsareshi da ido Rayyern yace.

“Meyasa? Yaushe ka tsara tafiyar?”.

Kanshi ya jingina jikin kujera cikin sanyi yace.

 “Saboda Mammy ta matsa akan na dawo, tun last week take min maganan dawowa na to daga nan na fara shirin tafiyar, kuma nima nayi kewarsu sosai, sannan kuma na gama aikin da nazoyi ak’asar nan, yanzu babu wani abu daya ragemin sai komawa”.

Cike da tsananin mamaki Ramadan, ya d’ago da kansa ya kalli Riyyam-nsra din.

Murya araunace yace.

“Koma wa Ethiopia kuma Riyyam? sannan kuma this week why ka bari sai end of the month mana.”

Murmushi Riyyam-nsra din yayi, tare da kwantar da kanshi, cikin sanyi yace.

“Dole zan koma Hamma Ramadan ko shekarane ai zaizo dole in koma, saboda yanzu bani da wani reason na zaman k’asar nan, dama daliline ya kawoni.”

Idanu Rayyern dake zaune ya zubawa Riyyam din, Cikin yanayin nazarta yace.

“Wani aiki ne ya kawo ka, then wani reason?”

Murmushi mai kama dana waskewa Riyyam-nsra din yayi, kana cikin samun madafa yace.

“No Hamma Rayyern ba wani babban aiki bane fa, d’an k’aramin aiki ne kuma ma harna gamashi,  dama kawai inada passion nazu wa Nigeria ne kan TIKTOK nema fa.”

Idanu Rayyern ya zuba masa batare daya sake cewa komai ba.

Mamy kuwa cikin dan yanayin damuwa tace.

“Haba Riyyam tafiya hakanan lokaci d’aya, ba zato ba tsammani ka bari mana kad’an k’ara kwanaki.” 

Murmushi Riyyam din yayi, tare kuma dasa hannu ya shafa sumar kansa, cikin dan sakewa yace.

“Mamy Mammy ta matsa akan saina dawo, baya ga haka ma najima a k’asarnan almost 4to5 month fa.” 

Shiru duk sukayi cike da jimamin tafiyar Riyyam din.

Musamman Ramadan da yakejin zaiyi kewar Riyyam din sosai, haka ma Jannart Domin ba kad’anba Riyyam-nsra din ke d’ebe mata kewa, domin akullum tana ganinsa kaman Abdull d’insu ne, baya ga haka kuma Riyyam din yana da shiga zuciya.

Rayyern kuwa mik’ewa yayi tsam ya nufi sama, saboda yagaji sosai a hospital baya ga haka, kuma yau dinma yaje company saidai ba new company dinsu yaje ba, yaje company dinsu wanda ake sarrafa auduga ne.

Koda ya haura saman kwanciyarsa yayi.

Acan falo kuwa basu yi wani hira sosai ba, duk suka watse kowa ya koma d’akinsa.

Almost 3days.

Kenan yau wanda acikin kwanaki ukun kuma, komai yana tafiya dai-dai musamman ab’angaren  new Company, din da su Rayyern din suke son budewa.

Dan zuwa yanzu ankammala komai da komai, har an fara sarrafa kayan provision. 

Kowanne store dake cikin company din kuwa, an cika sa da sarafeffen kayan provisions kala daban daban. 

Komai na dafawa sun sarrafa shi.

Alhamdulillahi kuma ranar Friday aka tsaida amatsayin, ranar da za’a bud’e companyn.

Kasancewar kuma yau alhamis, shiyasa ake ta shirin bude companyn gobe, wannan yasa gaba d’aya Rayyern bai samu ya zauna ba.

Hasalima Koda ya fita bashi ya dawo gida ba, sai k’arfe 10 dai-dai.

Wannan yasa agajiye yayi bacci.

 

Washegari ranar jumma’a.

Kusan gaba d’ayansu Atare suka tafi masallacin jumma’a, bayan sun Idar da sallah ne kuma, Abba ke sake shaidawa Baba Maud’o cewar yaune, zasu bud’e sabon kamfanin nasu.

Sosai Baba Maud’o yayi farinciki, tare kuma da fatan Allah ya sanya al’khairi, ya kad’e duk wata fitina, ya kuma sanya musu riba mai albarka.

Da. “Ameen Ameen.” 

Abba ya amsa.

Bayan sun dawo daga masallacin ne kuma, suka soma shiri dan zuwa bud’e companyn.

Ganin yanda suke ta hada

hada ne kuma yasa, Jannart dake gefen Mamy matsowa kusa da Mamy cikin sigar rok’o tace.

“Ayyah Mamy dan Allah nima zanje in ba matsala.”

Murmushi Mamy tayi tare da juyowa ta kalleta cikin sakin fuska tace.

“To Jannart ai zaki iya zuwa, amma bari na tambayi Abbanku naji me zaice tunda kin san a tsare kike.”

Kai Jannart din ta jinjina, cike kuma dajin dadi ta cigaba, da juya pepper chicken din da takeyi tare da cewa.

“Toh Mamy a gaya mishi Allah yasa a barni”.

Amin 

Mamy tace tana fita Kitchen din.

 direct sashin Abba ta wuce, Koda taje ta sameshi yana shiryawa.

Zama tayi abakin gadonsa, cikin tausasa murya da kuma bashi girma amatsayinsa na Mijinta tace.

“Dama magana nazo muyi.”

Aje hular hannunsa yayi tare da cewa.

“Ina jinki”.

Cikin zuba mishi ido tace.

“Jannart ce ta sameni wai tanason zuwa bikin bud’e companyn, shine nace bari nazo naji ta bakin ka.”

Kai Abban ya dan jinjina cikin gamsuwa yace.

“To ai ba abundamuwa bane, zata iya binmu saimu tafi tare ko, kice mata ta shirya.”

Dan Murmushi Mamyn tayi, saidai kuma cikin jimami tace.

“Amma Alhaji kamanta cewar zamanta awajenmu sirrine.”

D’an Jim Abban yayi na wasu mintuna kana yace.

“Babu damuwa, zata iyayin shigar da babu wanda zai ganeta, misali ko irin shigar larabawa haka da suke rufe fuska, kinga Idan tayi haka babu wanda zai shaida ta ko!?.”

“Hakane To bari naje na sanar mata.”

Mamyn ta fad’a tana me mik’ewa tsaye.

A kitchen din ta samu Jannart, Cikin kulawa kuma tace mata taje ta shirya, saidai amma tayi shigar da bakowane zai ganeta ba. 

Cikin jindadi Jannart din tace.

“To.”

Kasancewar ta kammala aikin da takeyi dinne kuma, yasa kaitsaye ta wuce d’akinta Dan shiryawa. 

Acan b’angaren su Ramadan kuwa tsab suka shirya, cikin shigar manyan kaya, shida Riyyam-nsra kayansu iri d’aya Getzner ce orange color mai masifar maiƙo da kyau kalar kayan ya ƙara haska fatarsu saida sukayi wani yellow-yellow.

Bayan sun gama shiryawanne kuma duk suka fito falo.

Dai-dai lokacin kuma Rayyern ya fito daga cikin dakinsa, yayi kyau sosai cikin shigar suit din dake jikinsa Pink guava mai dan ɗigon maroon.

Wanirin sheƙi yakeyi suit din rigar cikin itama maroon hakama net din sa.

Kana ga takalmam toms maroon suma masu masifar kyau da sheki.

Ga kuma wani had’add’en  agogon daya saka.

Sosai yayi kyau masifar kyau sajen shin nan ya kwanta lib-lib sai sheƙi sukeyi yan siraran lips ɗinsa jajaye suma suna sheki, 

Tattausan sumar kanshi tana kwance lib sai ƙamshi da sheƙi sukeyi.

Wayarsa ce riƙe a hannunsa.

Yana takowa da dan sassarfa,

cikar haiba da kuma kwarjininsa duk sun bayyana.

“Wow Masha  Hamma Rayyern kayi masifar kyau”.

Cewar Ramadan yayinda tuni Riyyam-nsra kuma yaketa daukansu hoto.

Haka suka rankayo zuwa falo, yana gaba Suna biye dashi abaya.

Koda suka sauk’o k’asa afalo suka samu Mamy.

Sai kuma Abba, Dr. Sulaiman, da kuma Usman P.A, duk sun shirya sauk’owan su Rayyern din kawai suke jira.

“Abba mutafi time yana kurewa.”

Rayyern din ya fad’a yana me duba agogon hannunsa. 

 Kai Abba Ya jinjina, tare da Kallon Mamy Cikin kulawa yace.

“Kira Jannart.”

“To” Mamyn tace, saidai batakai ga mikewa ba, Jannart din ta bud’e kofar falon ta ta fito.

Sanye take da doguwar riga maroon colour, Wacce aka k’awata jikinta da adon fararen duwatsu shuwariski.

Rigar irin abaya masu fad’innan ne, da tayiwa jikinta matukar kyau,  sai kuma babban mayafin da ta saka akanta, wanda kuma ta nad’ashi har akan fuskarta, kamar dai yanda larabawa keyi, hakan kuwa shiyasa idanunta kawai ake iya gani.

Bak’aramin kyau tayi ba, domin tafito ne a balarabiya sak, tayi kyau ainun. 

Wanda har hakan yasa akaron farko, Rayyern ya kasa d’auke idanunsa daga kanta.

Duk da yaji bakincikin cewar da ita zasu tafi, amma ya yaba da shigar jikin nata ainun.

“Masha Allah Jannart kinyi kyau.”

Mamy ta fad’a cikin yabawa shigar dake jikin Jannart din, saboda shigane na musulunci, da  kuma shigane daya boye asalin kamanninta.

Atare duk suka rankaya suka fita, zuwa compound din gidan, inda tsala tsalan motoci suke jiransu. 

Wata black Range Rover Rayyern ya shiga, haka ma Abba da Baba Maud’o.

Su Ramadan da Riyyam-nsra kuwa motocinsu daban, Yayinda Mamy da Jannart ma suka shiga nasu motar.

Haka Usman P.A da Dr Sulaiman.

Convoy motocin nasu sukayi, ahaka har suka isa cikin babban kamfanin. Daya amsa sunansa kamfani.

Jama’a da kuma yan jaridune cike awajen, bayan su Rayyern din sun isone kuma, wajen ya dinke da sowa.

Haka dai suka karasa wajen zama na musamman suka zauna, sosai Jannart ta yaba da tsarin kamfanin. Domin tayi imani ko kamfanin Dadynta bai kai wannan ba.

Taro akayi mai tsabta bayan kowa yaci yasha ne kuma, aka bude companyn.

Yan Jarida kam sun samu abunda sukeso, musamman da suka ga yanda Rayyern yasa, wasu daga cikin ma’aikatan kamfanin, suka cika motoci da kayan provision, inda ya bada umarnin, akai kowacce mota ta abinci, gidan yari, da gidan Marayu, sauran motocin kuma yace rabawa gajiyayyu.

Ai kuwa hakan da yayi ya daki zuciyar mutane da yawa, hakan yasa yan jarida suka kara kaimi wajen shooting.

Alhamdulillah anyi taro lafiya, inda taron ya samu halartar manyan baki, yan kasuwa shareholders mata da maza suke ta zuwa, kowa yanaso ya zuba hannun jarinsa a kamfanin.

Bayan duk Jama’an dake wajen sun watse ne kuma, suka tattara duk suka koma gida. 

Zuwa lokacin kuwa har dare ya soma yi, wannan yasa agajiye dukansu suka koma gida.

  Washegari Saturday still a busy suka tashi, musamman Rayyern.

Yayinda Riyyam-nsra kuwa keta shirye shiryen, komawarsa Ethiopia.

Saboda ranan Monday Insha Allah zai tafi.

Acikin yan kwanakin kuma duk cikin hidima suke, saboda mutane daban daban da suke zuwa gidan su Rayyern din Taya murna yayinda shi kuwa Rayyern yanzu bai samun zuwa asibiti ma, a Company yake wuni kullum sabida yana son dai-dai ta komai ta yadda in ya tafi ta online zaci gaba da aiyukansa wasu kuwa ya mikasu ga MD. 

Kasancewar yau Lahadi ne kuma yasa, Riyyam-nsra shiryawa yaje gidansu Naseer.

Hira sukayi sosai da Naseer din kafun daga bisani yayiwa, Umman Naseer din sallama, daga nan kuma gidan Malam Mai-nasara suka wuce.

Bayan sunyi masa sallama ne kuma, suka dawo nan gidan su Rayyern din. 

Hira suka sha sosai, duk da cewar zuciyarsu babu dadi, saboda sunsan zasu yi kewar Riyyam din sosai.

Washegari Monday kuwa, k’arfe 8 dai-dai jirgin su Riyyam din zai tashi.

Duk yau din haka suka tashi babu dadi, saboda shakuwar dake tsakaninsu more Especially Ramadan da yayi zugum,

dan har wani ciwon kai yakeji, saboda tafiyar Riyyam-nsra din.

Haka ma Jannart.

K’arfe 7:50 am dai-dai kuwa Abba, Baba Maud’o, Rayyern da kuma Ramadan suka rakashi airport,  cike da kewarsa, kyautttuka kuwa babu irin wanda basu bashi ba, domin Rayyern ma ba k’aramin kud’i yayiwa Riyyam-nsra din transfer ba.

Jannart kuwa har snacks tayi masa, tare da basa kyautan wani Apple Watch dinta mai kyau. 

Sosai yayi musu godiya da irin karamcin da suka nuna masa, Koda yazo shiga jirgi,

Ruggume Ramadan yayi sai ga hawaye shar-shar a idanunsa

Cikin rawar murya yace.

“Hamma Ramadan azanzo aurenka”.

Cikin rawan murya Ramadan yace.

“Zanyi kewarka Riyyam-nsra inaji ba dadi tamkar zan rabu da rabin jikina nakeji”.

Da sauri Baba Mauɗo ya juya musu baya yana maijin wasu irin zafafan hawaye na tsastsafo mishi.

A hakan yaji Riyyam-nsra ya ruggumeshi ta baya kawai sai yaji hawayen sun silalo mishi.

“Allah sarki Baba Mauɗona zanyi kewarka”.

Ina ya kasa mgn domin in yayi mgn zasu gane yana kuka.

Cikin rauni Rayyern ya ɗan kamo hannunsa tare da cewa.

“Toh Riyyam-nsra mu zauna kawai mana”.

Da sauri ya sharce hawayen sa tare da juyawa gaban Abba ya ruggumeshi yana cewa.

“Mammay na nake son gani da kai mata sakonta amman in sha Allah nan kusa zan dawo”.

Daga nan ya juya ya nufi wurin shiga jirgin

Yana  zubda k’walla tare da daga musu hannu, aransa  yakejin zaiyi kewarsu sosai.

Saidai kuma yasani cewa.

Lallai watarana zai dawo, zai dawo ya zauna acikinsu, zama kuma na musamman bawai irin wanda sukayi ayanzun ba.

K’’arfe 8 dai-dai jirgin su Riyyam-nsra din ya d’aga, zuwa k’asar Ethiopia. 

Haka su Rayyern din suka dawo gida, jikinsu  asanyaye.

Ramadan ne ya zauna akusa da Jannart, cikin sanyi yace.

“Wallahi duk gidannan babu dadi, Riyyam shi ke samu duk wani farinciki, gashi yanzu ya tafi, again kuma Hamma Rayyern ma nanda one week zai tafi, gaskiya nima tafiya zanyi.” 

Cikin.sanyi Jannar tace.

“Gsky dole muji gidan ba daɗi,

To ba gani ba ga Mamy, ka daina fushi.”

Longoɓar da kai Ramadan din yayi, tare da mikewa tsaye, Cikin yanayin jin yuwa  yace.

“Muje ki bani abinci My Aunty.” 

Mamy dake kallonsu ne tayi murmushi, cike da k’aunar y’ay’annata tace.

“To Ramadan kamanta da cewar, Rayyern da Jannart zai tafi? ai zama mu kad’ai kam ya kama mu.”

Jin abunda Mamyn ta fad’ane kuma, yasa Jannart saurin juyowa ta kalli Mamyn,  domin kwata kwata ita bata masan da zancen ba.

Ramadan kuwa fuska ya sake kwab’ewa Cikin yanayin damuwa yace.

“Gaskiya Mamy nima zan tafi London shak’atawa, ko ki gayawa Abba Dan Allah yaje, gidansu Rayhanna mana, atambayamin aure, gidan ya rame da yawa, please Mamy.” 

Ya k’are maganan yana me had’e hannayensa, alaman rok’o.

Murmushi Mamy tayi, kana cikin kulawa tace.

“To me kakeci na baka na zuba Ramadan, ai komai ya kusa, tunda har ankai kudin, nagani inaso, kuma iyayen Rayhannan sunce zasu tuntub’i Abbanku.”

Idanu Ramadan din ya dan zazzaro cikin, mamaki hadi da tsananin jin dadi yace.

“Wow Mamy yaushe akayi haka bansani ba, Dan Allah su Abba sunje.”

Murmushi Mamyn tayi tare da jinjina masa Kai tace.

“Eh su Abbanku sunje shekaran jiya, shine kuma yace kada na fad’a maka, da alama surprising dinka yakeson yi yanzuma subutar bakine.”

“Masha Allah Alhamdulillah, thank you Mamayna, soon nima zanyi aure wow.”

Ramadan din ya fadi haka cikin tsananin jin dadin daya rage masa kewar Riyyam-nsra.

Mamy da Jannart kuwa murmushi sukayi. 

Haka dai suka d’an tab’a hira, kafun daga bisani suka watse.

Jannart kam gaba daya jin cewa da ita, za’a tafi Mascow yasa jikinta yin sanyi.

Wanda hakanne ma yasa ta d’aukar waya, ta kira Abba Kabir.

Bugu biyu kuwa ya d’auka bayan sun gaisa ne, kuma ta gyara zama kaman Abban yana gabanta tace.

“Abba kaji wai  dani zai tafi Mascow, d’azu Mamy take fad’a.”

Daga can b’angaren Abba Kabir yayi murmushi, Cikin kuma jin dadi yace.

“Waye ɗin”.

Cike da kunya tace.

“Shi Doctor din”.

Murmushi mai sauti Barrister Kabir yayi tare da cewa.

“Masha Allah Jannart, ai babu damuwa zaku iya zuwa, Allah Ubangiji ya tsare ya kuma kareku aduk inda kuke, yaushe ne zaku tafin?”

Fuskarta ta d’an shagwabe Cikin yanayin sanyi, tace.

“Abba basu fadamin ranar ba, amma nasan zasu fada ma Idan lokaci yayi.”

“To shikenan Jannart.”

Abba Kabir din ya fad’a, daga haka kuma hira kadan sukayi sannan sukayi sallama. 

Washegari kuwa Abba da kasan ya kira Barrister Kabir ya sanar masa batun tafiyar. 

Wanda kuma yau ya kama saura kwana biyu tafiyar tasu, sosai kuma suke ta shirye shirye tuni Rayyern ya tsara ayukan campany’nsa yadda ya dace.  

Ana Gobe zasu tafi dinne kuma, Abba Kabir yazo sukayi sallama da Jannart din.

Washegari.

1:pm dai-dai jirginsu zai t

Yashi zuwa Mascow, hakan yasa tunda safe suka kammala shirinsu.

Cike da yakinin kewarsu, Mamy Abba da kuma Ramadan suka rakasu airport.

Karfe takwas jirginsu ya tashi zuwa, Abuja.

Bayan sun isa Abujan ne kuma, da kammanin awanni biyu jirginsu na zuwa Mascow ya d’aga zuwa sararin samaniya.

Ko acikin jirgin kuwa kujeransu na hade dana juna, tunda suka kama hanya kuwa, Jannart ta kwantar da kanta akan kujera tare da lumshe idonta dan bacci dake fuzgarta,

haka ma Rayyern shidinma lub yayi, Ahankali yake sauke ajiyar zuciya, tare kuma da ajiye idanunsa akan, yatsun hannunta wanda suke shinning. 

Tafiya sukayi mai Nisan zango k’arfe.

8: 30 na daren garin, jirginsu ya sauk’e ababban airport din dake cikin garin na Mascow…!

Back to top button