Uncategorized

Tubali Book 2 Page 3 Complete Novel

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

Shi kuwa Rayyern idonshi ya lumshe sabida ƙugin yunwa da cikinsa keyi,

ahankali yasa hannunshi ya ɗauki spoon din.

Motsa kunun ya farayi wanda yake masu kallon nono, sai dai ganin yana tururine yasashi fahimtar ba nono bane.

A hankali ya ɗan ja guntun  tsaki.

Sai kuma ya ɗan ɗebo cikin cokalin ya ɗan ɗago sama ya zubawa kunun ido,

sunkuyowa ya ɗan yi harshensa, ya ɗan zaro ya ɗan laso kunun.

Zir haka yaji yawun bakinsa ya tsinko kunsan Dakta da son zaki da gardi.

Da sauri yasa spoon din a bakinsa ya zuƙe kunun.

Idonsa ya lumshe sabida dandanon kwakwa da zaƙin dabino da zuma da gyadar da yaji sun gigita masa harshe.

Gyara zamansa yayi tare da d’ago mug din ya kai bakinshi.

Kasan cewar madara da zumar sun sa zafin kunun ya koma dai-dai misali.

Kafa kanshi yayi yana mai lumshe idonshi ya fara zukan kunun.

Yana mai jin garɗinsa, saboda d’umin kunun ya wadaci hanjin cikinsa.

A hankali ya ɗan janye mug din, yana mai jin dandanon lemun tsamin ya, gyara mishi bakinsa Kunsan bakin mara lfy.

Numfashi ya ɗan fesar tare da juyowa ya kalleta tana aikinta kamar bata Kitchine din.

Kafa kai yayi ya shanye sauran kana ya aje mug din, gyatsa yayi mai sanyi kana ya miƙe ya fita yana jin cikinsa tib-tib.

A falon ya zauna bayan ya kara karfin Ac sabida zufan data karyo masa.

Ita kuwa Jannart tana gama kwashe tuwon ta ida miyar, tuni kuma an fara kiran sallan magriba, tana gamawa ta fito.

Yayinda Ita kuwa Mamy tana can wurin Abba.

Washe gari da safe. 

Kasan cewar asabar ce tuni u Ramadan sun shiga gari.

Rayyern kuwa sai karfe goma saura ya sauko cikin shigar tattausar jallabiya blue mai guntun hannun.

Kai tsaye wurin Abbansa ya wuce, bayan sun gaisa ne kuma ya tafi wurin Baba Mauɗo.

Ya dan jima a nan kafin ya dawo ciki.

A falo ya samu Mamy kwance tana kallon tv tuni sha ɗaya ta gota lokacin, gefenta ya zauna a ƙasa tare da jawo system dinsa da ya ajiye kafin ya wuce.

A hankali yace.

“Mamy me aka dafa?.”

Ba tare da ta kalleshi ba tace.

“Dumame mukayi na tuwon jiya dan bai ciwuba, kasan mu kuma muna son ɗumamen dasu Baba Mauɗo duka.”

Kai ya gyaɗa dan yasan time to time suna ɗumamen duk da shi dai ba ci yakeyi ba.

“Me su Riyyam-nsra sukaci?”.

Ya kuma tambayarta.

“Waya san musu ni dai naji Ramadan yanata kwarwa da mita, wai Riyyam-nsra ya cika musu yaji, ina zaton indomie suka soya da kwai.”

Kai ya ɗan juyo ya kalleta tare da cewa.

“Toh Mamy yunwan da nakeji ni me zan samu?”

Cikin kauda kai tace.

“Tambayi matarka.”

Da mamaki ya kalleta ganin ita bashi take kallo bane ma, yasa shi yin kwaffa tare da jingina kansa.

Dai-dai lokacin kuma Jannart ta fito daga Kitchen din riƙe da roba da markadedden gyada a ciki, ta ɗan sa ruwa da yar ƙaramar muciya alamun matsan mai zatayi.

Ido Mamy ta zuba mata, ita kuwa Jannart zama tayi gefe a ƙasa.

Kana ta kuma kallon Mamy ganin har lau ita take kallo.

Da sauri tayi ƙasa da kanta ganin Mamyn ta meda kallonta ga Rayyern ɗin.

A hankali ta ɗan ɗago ta kalleshi cikin lumshe ido tace.

“Ina kwana?”

A hankali ya ɗago kanshi ya juyo gareta.

Ido cikin ido sukayi,  haka nan ba zato ba tsammani bare niya, kawai sai yaji lips ɗinshi sun furta.

“B…!         “Ba abinda za’a bani kenan Mamy.”

Yayi mgnar yana sunkuyar da kanshi, ita kuwa Mamy murmushin dake son subce mata ta danne tare da cewa.

“Gaka ga matarka nan.

Rayyern ka fita idonafa ka dena damuna, ka tambayeta  ita mana, ya zaka zo ka tsareni da mita kamar ɗan yaye.”

Kanshi ya juyo ya kalleta cikin kwaɓe fuska ya kontar da kai bisa kujerar.

Cikin sanyi yace.

“Shike nan Mamy na barki.”

Miƙewa tsaye Mamy tayi tare da nufar side ɗinta tana cewa.

“Bari ma in bar maka wurin.”

Ita dai Jannart jujjuya yar muciyar takeyi, tana haɗe markadedden gyadan.

Tuni kuma ya fara haduwa ya fara nason mai.

Shi kuwa Rayyern cikin haɗe fuska ya kalleta, kana yayi mgnar can ƙasan maƙoshinsa.

“Ke wai ce miki akayi ni bani da rabone a gidan nan?”.

Juyowa tayi ta ɗan kalleshi a fakaice kana ta meda kanta.

Dan bata jishi ba sosaiba ta dai ji alamun yayi mgn kam.

Shikuwa ganin hakanne yasa shi, jan tsaki tare da dan buɗe murya yace.

“Ba dake nake mgna ba? Kina jina kinyi shiru.”

Da sauri ta ɗago kanta tare da cewa.

“Ban jiba?”

A kufule yace.

“Kada Allah yasa kiji, idan kunu na na jiya yana nan, ai sai ki kawo min tunda ba ke kika dama minba.”

Jin abunda ya fad’a dinne kuma, yasa ta satan kallonsa, ta gefen Idanunta, batare kuma da tace masa komai ba, ta miƙe tsaye da robar a hannunta.

Kaitsaye dining ta nufa ta ajiye robar,

sannan anutse ta wuce cikin Kitchen,

mug ta ɗauƙa da spoon kana ta buɗe fridge, sassayan kunun ta tsiyaya mishi.

Kana tasa madara da zuma ta motsa, sannan ta ɗaura a dan tray.

Anutse ta fito daga cikin kitchine din, hannunta dauke da tray din, ta nufo inda yake.

Isowarta ne kuma yasa shi d’ago kanshi ya kalleta.

Jannart kuwa batare da ta kalleshi ba, ta d’an rusuna agabanshi, tare da ajiye try’n, cikin tafiyarta na nutsuwa kuma ta juya ta tafi.

Shi kuwa Rayyern baki ya taɓe tare da cewa.

“Aniyarku zata koma kanki, wato irin bari ki fara kasheni da yunwa dinan ko, dan kin samu an sake miki ragamar gidan.”

Ya ida mgnar nasa yana kai mug din bakinsa.

A zatonsa mai dumine sai kuma ya jishi mai ɗan karen sanyi harda ɗan kankara, da sauri ya lumshe idonshi dan sai yaji kamar yafi daɗi a hakan, sai yakeji kamar masoyinsa milkybar Chocolate dinsa yakeci, dan wani rin gardi yaji kunun yayi mishi.

Jannart kuwa komawa tayi ta ci gaba da aikinta, dan sosai ta tuka tukunzan nan saida ya haɗe da kyau mansa ya fito.

Tsiyaye man tayi a cikin kaskon mai, kana taja kujera ta zauna, tunkuzan ta fara gutsura tana mulmulasu ƴan ƙanana tana sasu kan tray mai ɗan girma.

Yayinda busan doyan  da ta daura yake ta tururi alamun ya dahu.

Da sauri ta ida gama mulmula tunkuzan.

Kana ta miƙe  ta kaishi cikin store ta ɗaurashi sama tare dasa rariya a kai yadda zaisha iska.

Tana fitowa ta sauke tukunyar ta kwashe doyar cikin, kula biyu manya daya nasu Baba Mauɗo daya nasu sai ƙaramar kuma ta Abba.

Dakakken yajin k’arakon da yasha kayan hadi tasa musu a robobi, kana tasa plates, sannan ta ɗaura wannan man data matse yanzu ta soya, ta sawa kowa.

Ganin kusan ƙarfe ɗaya ne yasa tasa kadan a plate, tare dasa yaji da mai, kana ta fito da salat da dafaffen kwai.

Inda ta barshi a nan ta sameshi ya dukufa kan system ɗin nashi.

A nitse ta wuce shi, shi kuwa yatsun ƙafarta ya ɗan bi da ido har saida ta ɓacewa ganinsa.

Bayan sallan azahar ne duk suna zaune a  Dinning table.

Cikin zuba musu ido yace.

“Wlh za’a kasheku da yaji sai Ulcer tayi muku mugun illa, Ramadan kafa san illan yaji, jiya war haka kake cin danwake har kana kuka dan yaji, amma yanzu kazo kanacin wani abu daban kuma.”

Da sauri Ramadan yace.

“Wato harda kuka nayi jiyanko, to amman dai gsky wannan ba yaji, kuma wlh yamin daɗi yama fi min a soya doyan da kwai.”

Riyyam-nsra ne ya ɗan kalleshi yana sa farar doya da yajin k’arago, da yankekken kwai da ƴar al’basa da man gyaɗan a baki yace.

“Gsky nima yamin daɗi wlh, dan Mammy na yawan yi mana shi.”

Kai ya jinjina tare da cewa.

“Okay aci daɗi lfy.”

Sai lokacin Mamy ta kalleshi a fakaice tace.

“Kai har zaka cewa wani yasan illar wani abu kuma yake ci, kaida kasan ciwonka kuma kake meda zaki abokin rayuwarka.”

Da sauri yace.

“No Mamy ciwo na bashi da alaƙa da zaƙin.”

Kai kawai ta gyaɗa tare da zuba mishi ido irin na tuhuma.

Ganin hakane yasa ya juyawa yayi ya nufi sama…

Haka dai al’amarin zaman gidan yayi ta tafiya.

Cikin kwanakin sosai Rayyern ya samu lfy ya koma kamar da.

A can tashar Arewa kuwa sosai Asiya tayi farin cikin jin lbrin bacewar Jannart daya zo mata da wani nasarar rayuwa.

Tunda gashi aikin da take son din ya dawo hannunta.

A gidan Barrister Kabir kuwa sosai hankalinsa ya kwanta yanzu, ya duƙufa kan fuskantar karar da zai shigar ka’in da na’in, nason tono tsohon zalumcin da aka binne, shekara da shekaru.

Alhaji idi Saleh Dakata kuwa sosai ɓacewar Jannart, ya gigita mishi lamuran rayuwa, wannan yasa ya dade rabonsa dasu Dr.Lukman ma.

Sai dai yau tun safe yake gidan Alhaji Bala Tambari.

Kasan cewar yayi tafiya ne, kusan na wata daya yasa suka jima basu gana ba.

Cikin tsananin takaicin abubuwan da suka faru,Alhaji idi Saleh Dakata ya kalli Alhaji Bala Tambari tare da cewa.

“Toh kaji dai duk abinda ya faru, ni kuwa kaji matakin dana ɗauka, da kuma kalubale da nasarorin dake cikin al’amarin, dole inyi wani abu dan tabbatar da abinda zai kiyaye min ahlina da mutuncina.”

Murmushi Alhaji Bala Tambari yayi kana yace.

“Wannan shirin naka yayi, kaga duk kulafacin mutun da nacinsa bazai cimma manufarka ba, amman inada shawara ta musamman da zan baka, ka bari sai na ɗan huta, zuwa jibi zanzo har gidanka, sai muyi maganan.”

Cikin jin daɗi da dukkan yarda Alhaji idi Saleh Dakata yace.

“Toh ngd matuƙa sai na ganka, ni bari in wuce Tababa Company.”

Daga nan sukayi sallama.

Kasancewar yau ɗin Lahadi ne, ya kama kuma gobe Monday Dr.Rayyern Mai-nasara da PA’nsa zasu tashi zuwa China.

Yau tun safe daya fita bai dawo gidaba.

Shida Abbansa dan suna Mai-nasara campany’n su da aketa kafa injinun kayan aiki.

Suna dudduba duk wata inji ko ƙarfen dakeda matsala.

Bisa jagoranci Engineer  Bello, dan su san me-da-me suke da buƙatar sayan sabo, in yaje China.

Gaba ɗaya wurin masarrafin nasu, suketa dudddubawa yayinda PA ke biye dasu a baya, yana riƙe da woyoyin uban gidan nasa.

Shi kuwa Rayyern rike da system nashi yake.

Yana wasu ƴan rubuce-rubuce da alamu bayanan Engineer bello yake adanawa na abubuwan da suke buƙata.

“Wannan shine babbar matsalar data dakatar da komai, badon shiba da tun tuni an fara sarrafa al’kama zuwa fulawa, kana a medata macaroni indomie, da dai sauransu, ganan Cerelac ma da yayi k’aranci, kuma akwai buk’atar lallai muyisa.”

Engr bello ya faɗa yana nunawa, Dr Rayyern wani ɗan ƙaramin ƙarfen da bai taka kara ya karyaba.

Hannu Rayyern yasa ya amshi ƙarfe

Tare da duba numbers din jiki yace.

“Number 2%”.

Da sauri Engr bello yace.

“Eh to 3% ake bukata dan wannan campany’n ai yafi sauran baki ɗayansu girma da manyan kayan aiki,

na manta ne san da zaka tafi ban cema kada ka sayi kamar na wanda ka saba saya ba”.

Kai Rayyern din ya jinjina tare da cewa.

“Ba matsala a ajiyeshi zaiyi amfani, dan na campany’n Jigawa ya fara samun matsala aturashi can. PA.”

Ya faɗa yana kallon Usman.

Da sauri Usman PA yace.

“Ok Sir”.

Haka dai sukayi ta zazzagayawa.

A gida kuwa Jannart ce tsaye gefen Mamy dake kokarin shiga falonta.

“Mamy zaki shiga ne?”.

“Eh.”

 tace tare da juyowa tana kallonta.

“Toh me zamuyi abincin dare?”

Cikin bada ishashshen matsayi Mamyn tace.

“Ki dafa duk abinda kike son muci.”

Murmushi Jannart din tayi, kana cikin sauri tace.

“Yauwa to Mamy tukekken tuwon shinkafa da miyar kase kuna ci ko?.”

Ɗan jim Mamy tayi kana a hankali tace.

“Ba matsala kiyi, ni dai bansan miyarba amman nasan zan iya ci”.

Da sauri tace.

Toh kana ta fada Kitchine ita kuwa Mamy ta wuce falonta.

Tana shiga Kitchine din.

Ta ɗauko tukunyar yar madaidaiciya number biyu kenan.

*(Tun bayan gamakarantan littafin GARKUWA anata damuna wai yadda ake miyar kase, shiyasa Jannart zatayita daki-daki Hajia ki kula miyar tana da masifar daɗi)*

Lalabe tukunyar tayi kana tasa ruwa fiye da rabin tukunyar kusan cikawa ta ɗaura kan gas bayan ta kunna wutan.

Dai-dai-ta wutan tayi Dai-dai misali.

Kana ta debi kayan miyanta masu ɗan dama tattasai al’basa, tumatur kaɗan duk da tasan basa son yaji ta ɗan ɗebi taruhu kaɗan sabida miyar kase tana raina yaji ainun.

Jajjagesu tayi, kana ta adanasu gefe ta rufe.

Ganin tukunyar ta fara Bararraka ne, yasa ta wuce store.

Wannan tunkuzan data aje ta ɗauko 

Ya ɗan bushe ya kama jikinsa yayi kam.

Haka yasa ta juyeshi a roba,

kana ta buɗe tukunyar ta ɗan ɗebi ruwan zafin ta zuba a ciki, 

Sannan ta ɗauko bushesshen yakwanta, mai kyau ta wonkeshi kana ta sa cikin tukinyar tuni ya fara tafasa,

Sai kuma ta jawo robar tunkuzar da ta zuba tafasasshen ruwan a kai, sauri-sauri ta ɗan motsashi ta lallayeshi mgnin ɗan kura in akwai.

Kana ta watsasu cikin tukunyar tare da rufewa, ta kuma ɗan ƙara wutan.

Yadda zasuyi ta watsal-watsal da kyau gudun cakudewa shiyasa ba’asa tunkuzar sai ruwan ya tafasa da yakuwar a ciki,

Rufewa tayi.

In a take kika mulmula tunƙuzarki ba sai kin lallabeta ba,

Yakuwar anfi son bushesshe dan zaifi ɗan tsami.

Amman in ba busashen zakisa ɗanyen ma ba matsalar komai.

Tukunyar ta buɗe kai ta jinjina ganin, yana ta watsal-watsal mulmulayen tunkuzar nan suna ta jujjuyawa.

Yayinda tuni man jikinsu kuma ya tsastsafo sosai kai kace tasa mai.

Juyawa tayi jikin Fridge.

Soyayyan naman miyan da suke ajiyewa, ta ɗibo mai yawa, tare dasa ƙasusuwan tantakwashi, kana ta zo da plate din kan table ɗin, kara yayyanka naman tayi kanana.

Sannan ta buɗe tukunyar ta watsashi ciki ta rufe.

Watsa-watsa haka yake tafasa, ruwan naman yana tsastsafowa yana gaureyewa.

Tuni kuma tunkuzar ta kame jikinta, ta fara komawa tamkar hanta ga ganyen yakuwan yayi shar gwanin kyau, karamar tukunya ta ɗauka a gefen, man gyaɗan hannu tasa kadan, Kana ta juye kayan miyar nan, ta ɗan soyasu sama-sama kana ta sauƙesu.

Bandan kifi tarwad‘a ta ɗauki guda huɗu cikin kwalin da kifin suke a store.

Baresu tayi kana ta gyarasu ta fito da tsokokin ras.

Guntun ruwan dumin data bari ta juye kan kifin.

Kana ta debo al’basa ta yanka mai yawa, irin ƙananan yankan nan.

Citta  da kanamfari ta ɗan daka.

Kana ta buɗe tukunyar ta saka su.

Lokaci ɗaya suka fara zuba ƙamshi.

Rage wutan tayi Dai-dai misali.

Kana ta kimtsa komai.

Ganin la’asar tayi ta fita ta wuce ɗakinta dan yin salla.

A hankali ta fito daga cikin Bathroom din bayan tayi al’wala.

Miƙewa tayi kan sallayar bayan ta idar da sallan.

Sabida sanin miyar tana buƙatar wuta sosai.

Wuta kuma nitsetstsen wuta, ba wurrururun nan ba, an gane ko?

Mamy kuwa bayan tayi sallan bacci ne ya saceta bisa sallayan.

Ita kuwa Jannart huɗu da kwata dai-dai ta miƙe tsaye.

Ninke sallayar tayi kana ta fito ta nufi Kitchen din.

Shiru gidan alamun babu kowa, hakan ne yasa ta kunna tv, tasharsu ta kunna dai-dai lokacin kuma aka sako tallar cekiyanta da akeyi.

Da sauri ta koma da baya ta zauna bisa kujera.

“Allah sarki Daddy na bawan Allah na sashi a tashin hankali, Allah na tuba, Astagafirullah Allah ka yafe min sa mahaifina da nayi a damuwa, Allah ya isa tsakanina da kai, Yah Junaid tunda sanadin ka ne komai ya faru.”.

Cikin rauni a fili yace.

“Anya kuwa Abba Kabir yayi abinda ya dace kuwa, raba uba da yarsa ?”

Ta ƙare mgnar  hawaye masu zafi na tsilalo mata.

Haka nan bege da kewar mahaifinta ya dawo mata sabo, sosai idonta ke zubda hawaye, haka ta nufi Kitchine din.

Hannunta tasa ta sharce hawayenta sabida idonta bai gani da kyau, saboda ruwan hawayen daya cikasu, wanke hannunta tayi, kana ta juya zuwa kan tukunyar miyar nata.

Buɗewa tayi tare da dauko ludeyi ta ɗan motsashi, tare da ɗaukan mulmullen tunkuza ɗaya ta matseshi ta fasashi, kai ta jinnina ganin ya nuna, yayinda kuma har yanzu hawayen ke tsastsafo mata.

Tunkuzar ta nuna tayi dir-dir da ita ta dahu ta koma tamkar hanta.

Naman nan kuwa gaba ɗaya yayi ligib ya diddige.

Tantakwashin kuwa yayi taushi.

 meda marfin tayi ta rufe, Kana ta matsa gefe.

Su maggi Curry da dai sauran kayan ɗandanon ta ɗibo dai-dai yadda take buƙata ta ajesu a plate.

Kana ta ɗauki tukunyar tuwo number biyar tasa ruwa, kana ta hura wutan ɗaya gefen gas din ta daura tukunyar tuwon.

Yankekken albasan nan ta dauko ta watsa a ciki.

Kana ta ɗauki kifi bandan nan ta saka,

Tare da debo wani tafasheshen nama da ruwan tafashen kadan ta saka

Kana ta rufe su.

Shinkafar tuwon ta debo,

tazo ta ajiye a gefe.

Kana ta buɗe tukunyar miyar ta juye soyayyan kayan miyan nan nata duka aciki.

Sannan tasa duk kayan dandano dana ƙamshi, kana ta meda marfin ta rufe sannan ta ɗan rage wutan.

Ahaha gaba ɗaya gidan ya ɗauki kamshi, yayinda miyar kuwa taketa

Bul-bul mai yana ta tsastsafowa komai yayi dai-dai miyar tayi masifar kyau.

(Tsokaci ba dole sai da nama ko kifi ba, ana iya yinta haka nanma ita ɗaya kuma tana daɗi matuka gaya.

Tana son wuta sosai a wurarenmu fulani masuyinta a tukunyar ƙasa mukan ɗaurata  tun safe ko azahar in zamuci tuwon dare da ita.)

Kai ta jinjina jin yadda miyar ke zuba ƙamshi, sai yanzu ta samu kuma hawayenta ya tsaya.

Shinkafar ta wonke wacce take mudu ɗaya kwanon sha, dan suna da ɗan yawa, gidan duk da ma dai tasan masu cikashi sosai.

So tana son ɗumamen miyar kase tasan kuma ba mamaki su Mamy ma su so.

Duk da shi miyar kase in kana cin tuwo malmala biyu to in itace malmala ɗaya ma zata isheki.

Buɗe tukunyar ta kumayi tare da motsa miyar ganin komai yayi yadda take sone yasa ta meda ta rufe, tare da kashe wannan wutan.

Dai-dai lokacin Mamy ta shigo Kitchen din tana mai cewa.

“Kai-kai Jannart yau me kike dafa mana haka gidan yaketa baza ƙamshi”.

Ta ida mgnar tana buɗe tukunyar miyar da sauri ta shaƙi daddaɗan kamshi tare da cewa.

“Masha Allah, tab lallai yau Ramadan akwai kwasar gara, irin wannan dege-dege haka, gashi dama gwanin son nama”.

Tayi mgnar a zatonta duk namane, 

fahimtar hakanne kuma yasa Jannart ɗan yin murmushi tare da cewa.

“Ato in ya gani kam zaiyi zaton duk nama ne ba kasenba”.

Da sauri Mamy tasa ludeyi tana ɗan juya miyar kana ta juyo ta kalleta tare da cewa.

“Yoh ai nima nayi zaton duk namane”.

Tana mai rage wutan tuwon ganin tsanewane ya rage mishi tace.

“Akwai naman ma kam, miyar tana son nama sosai”.

Murmushi Mamy tayi cikin jin daɗi tace.

“kai masha ALLAH.Yanzu bari in ƙarasa tuwon tunda kinyi mai wuyar, je kiyi wonka ga magriba ta gabato”.

Cikin yanayin gajiya tace 

“Toh Mamy.”

Kana ta fita ta tafi.

Ita kuwa Mamy matso da foodflask guda uku tayi, biyu yan madai-daita daya karami.

Miyar ta zuba da zafinta cikin na miyansu Baba Mauɗo saida ta cika musu kular, kana tasa a ƙaramar na Abba kenan.

Sannan tasa a dayar tasu kenan, kowanne ta zuba namomin da tsokokin kifi bandan kana da kasen da kyau, rufe tukunyar tayi kana ta buɗe ƙasan gas din ta ajiye sauran miyar.

Muciya ta ɗauko ta tuka tuwon da kyau tana tarfa garin fulawa kaɗan, hakan yasa tuwon ya tuku yayi dank’o mai kyau, y’ar kwaryar da suke malmala ta ɗauko ta rinka malmalawa tana sawa a kulolin.

Kwaya biyu ta sawa Abba dan tasan cikin mijinta.

Su Baba Mauɗo kuwa kwaya tara ta saka musu, sannan auran kuma da zasu kai goma sha ta juye a kularsu, kana ta tattare wurin ta wonke duk abinda suka ɓata.

Sannan ta dauki tray’n na Abba ta kai falonsa, sannan ta dawo ta shirya nasu kan Dinning table, Bayan tasa plate  biyar da dan na miyarsu da spoons.

Sai kuma nasu Baba Mauɗo ta aje kular akan Fridge sannan ta hada musu plate da sauran abin buƙata.

Komawa tayi ɗakinta dan yin alwala.

Jannart kuwa tsaye take agaban dreesing mirror’nta.

Da alamun tayi wonkanta da al’wala, wani zazzafan lace ne ta saka mai orange, pink, and yellow color  ɗinnan,

dinkin ayi masifar yi mata kyau.

Gashin kanta take tajewa, tana  gamawa kuwa ta tubkeshi a keyarta, Kana ta ninke ɗan kwalin tayi ɗaurin da shi kaɗai tafi iyawa, sabida ita dama tafi ta’ammali da kananan kaya.

Banda hoda ba abinda ta sawa fuskarta, ko man baki bata saba tabar natural pink lips ɗinta.

Turare ta fesa kana ta gyara ɗaurin.

Yayinda ta tubke gashin a ƙeya hakan ya taimakawa ɗaurin yayi ras.

Hijabi tasa jin an kabbarta sallah a masallatai.

Bayan ta idar da sallan ma bata tashi ba.

Sai da akayi isha’i, tana idarwa ta yafa ɗan siririn mayafi pink color kasan cewar akwai ratsin pink a lace din.

A falon ta samu Mamy ita ɗaya.

Gefenta ta zauna tare da cewa.

“Mamy ke ɗaya?”.

Juyowa tayi ta kalleta cikin kulawa tace.

“Wlh kuwa kinga yau har yanzu Abbanku da Rayyern basu dawo ba.

Gashi su Ramadan ma shiru…”

Ta ƙare mgnar tana kallon himilin gashin Jannart ɗin.

Ita kuwa Jannart cewa tayi.

“Mamy ki kirasu mana to”.

Miƙewa zaune tayi tare da cewa.

“Toh”.

Sai kuma ta ɗora da cewa.

“Jannart ko dai inyi miki kitso ne? Naga tunda kikazo kan a tsefe”.

Da sauri tace.

“Ai kuwa ina son kitso Mamy”.

Murmushi tayi tare da cewa.

“Toh ba matsala bari muci abinci sai inyi miki koda cukune, tunda naga bakya son barinshi a sake, kinga sai ki tubke abinki”.

Kai ta gyaɗa kana ita kuma Mamy wayarta ta ɗauka tare da cewa.

“Bari dai in kira s..”

Bata ida rufe bakinta ba Rayyern ya turo ƙofar ya shigo da sallama, kana PA na biye dashi abaya.

“Masha Allah kinga ɗan halal yaki ambato.”

Mamy ta fada. 

Shikuwa Rayyern din cikin yanayin tarin gajiya da yunwa, ya zauna gefen Mamy tare da fesar da numfashi kana a hankali yace.

“Wash Allah na Mamy na gaji, kishi da yunwa kamar zasu karni.”

Da sauri Mamy ta miƙe tare da cewa.

“Toh Jannart kinji shi, ni nayi can nasan Abbanshi ma a gajiye ya dawo.”

Ta ida mgnar tare da kallon PA kana tace.

“PA kada ma ka zauna a nan ku iso kan Dinning table kawai”.

Ai kuwa murmushi PA yayi tare da biyo bayanta yana cewa.

“Hajia azo a bamu abinci.” 

Yayi mgnar yana kallon Jannart.

Ita kuwa Jannart miƙewa tayi a hankali ta ɗan saci kallonsa cikin sanyi tace.

“In kawo maka nanne?”.

Da alamun tarin gajiya da kuma fitinenneyar yunwar, daya kashe masa jiki ya kad’a kai kawai.

Ganin hakanne kuma ya sata juyawa ta nufi dining area.

“PA ya dai kana tsaye zauna mana”.

Ta fadi haka, saboda ganin Usman PA da tayi a tsaye.

Da alamun sauri yace.

“Kai inaga ni bani abincin zan wuce gida dashi naci ko a mota.”

Cikin mamaki tace.

“Saurin me kakeyi haka?”

Tayi mgnar tana shigewa kitchine.

Wani dan kyakkyawan kula ta dauko mai haɗe da na miya.

Kana ta dawo shi kuwa PA fridge dake gefensa ya buɗe tare da cewa.

“Wlh banyi shiri bane kuma gobe da sassafe zamu wuce Abuja, saboda bayan azahar zamu wuce china.”

Kai Jannart din ta jinjina mishi, tare dasa mishi miyar bayan ta sa mishi tuwo malmala uku.

Amsar kular yayi kana ya sauka da sauri, ya sallami uban gidan nasa ya tafi.

Ita kuwa Jannart tray’n ma dai-dai-ci ta ɗauka, plate ta ajiye akai, kana tasa tuwo malmala biyu, tare dasa wani plate din ta rufeshi, sannan tasa miyar acikin wani dan bowl na glass k’arami mai kyaun gaske, Koda tazo diba masa miyar kuwa, sosai ta sa mishi nama da kifin, bayan ta kammala ne kuma, ta saka murfin bowl din ta rufe, 

kana ta ɗauko goran faro mai sanyi da cup.

A hankali ta ɗauki tray’n tare da  sauƙowa akan steps din.

System ɗinshi ne ke bisa cinyarsa, wanda hakan yasa bai kalleta ba, santer table ɗin baƙin Glass din,ta jawo gabanshi bayan ta aje tray’n a kai.

Batare kuma da tace masa komai ba,  ta juya ta koma cikin Kitchine din.

Wani ɗan roba mai kyau ta ɗauka tasa ruwa a ciki kana ta koma ta ajiye a gefen tray’n.

Dai-dai lokacin ne kuma Mamy ta futo, hannunta riƙe da kum da kifiya.

Kan kujerar dake fuskantar wacce yake kai Mamyn ta zauna tare dace wa.

“Yauwa Jannart kin gama masa ko, to zo mu fara kitson kawai.”

Da sauri Jannart din tace 

“To.” 

kana ta matso gabanta ta zauna a ƙasa bisa carpet din.

Tare da ture ɗan kwalin kanta.

Ita kuwa Mamy dan matsowa tayi gaba kaɗan tasa hannunta.

Ta fara warware gashin Jannart din dake tubke.

“Wai-wai Masha Allah, Jannart gashin naki ya cika santsi anya zan iya kitsashi kuwa ga yawa ga tsawo”.

Mamy ta faɗa lokacin da ta gama warware jelar gashin.

A hankali tace.

“Yana da wuyan kitso kam Mamy, ko zamu bari saida safe.”

A hankali ya ɗago kansa ya kallesu,

Idonshi ya tsaida kan tarin gashinta dake kwance bisa kafadunta.

Fuskarshi ya ɗan ya mutsa kana a hankali yace.

“Mamy kitso kuma anan ga abinci na”.

Ba tare da ta kalleshi ba ta fara tattare gashin dan taga a taje yake.

“Ga can wurin cin abinci kaje can”.

Ta faɗa tana nuna mishi Dinning area.

Cikin gajiya yace.

“Wlh na gaji ne Mamy”.

“Toh zauna kana can muna nan, kuma ba taje kan zamuyi ba, me hadinmu da kai”.

Fuskarshi ya kwaɓe tare da aje system ɗin nashi.

Kana ya gyara zamanshi tare dasa hannunshi cikin roban wonke hannun yana mai cewa.

“Kiyi hakuri bari inci da sauri-sauri sai kuyi”.

Buɗe plate din yayi kana ya buɗe miyar.

Ido ya ɗan zubawa miyar tare da cewa.

“Mamy wannan fa miyar menene”.

Tana mai tsaga tsakiyar suman tace.

“Ka dan-da na mana ita kaji yadda take”.

Shiru yayi kamar ya maida ya rufe.

Toh kuma yunwar dake zakularshi kara kaimi tayi ganin abincin.

Hannunshi yasa bisa tuwon ya ɗan gutsuro ƙarami.

“Gaba ɗaya ni ba son cin tuwo da dare nakeyi ba, sabida sa katon ciki yakeyi”.

Ya faɗa yana mai ɗan yago miyar ya haɗa da gayan tare da yin bismillah.

Ya nufi bakinsa da loman yana mai kallon miyar.

A hankali yasa loman a baki.

Da sauri ya murza harshensa yayi gefe dashi tare ɗaukan gayan da miyar.

Garɗin miyar ne ya sashi jan nannauyan numfashin kana ya lumshe idonshi.

Zamanshi ya gyara tare da kai hannunshi ya gutsuro loma ta biyu.

Yana mai jin wani irin tsinkewa da yawun bakinshi sukayi.

Ga ɗan-danon Nama, kifi, kasen.

Kana ga wani ɗan tsami-tsami mai shegen daɗi more Especially ga bakin mara lfy.

Miyar ya diba da ɗan yawa ya haɗa da gayan kana yasa a baki.

Yan kananan tsokokin naman da kifin, ne da diddigin naman ya tauna cikin jin marmarin cin abincin.

Mamy kuwa ido ta zuba mishi.

Sabida taji yadda Abba yayi ta santin miyar har ya cinyeta tsab.

Har yana cewa gobe ɗumamen zaici, ya shiga wonkane ta fiton.

Sunkuyar da kanta tayi ta fara yiwa Jannart ɗin kitson.

Shi kuwa Rayyern matsowa yayi bakin kujerar da kyau.

Yaci gaba da cin abinci.

“Bari kawai inyi miki manyan ibra zasuyi miki kyau”.

Mamy ta faɗa tana fara kitson.

Dago kanshi yayi ya kallesu.

Yatsun Mamy ya ɗan kalla ganin yadda take sasu cikin tattausar sumar mai ɗan karen sulbi.

Haka nan sai ya gaza ɗauke idonshi kan gashin.

Wuyanta ya ɗan kalla fatar fara ƙal kana wuyan yayi wani rin zane kamar guru-guru haka.

Ta goshinta kuma gashin ne ya kwanta lib-lib Mamy na janshi yana suɓalewa.

A hankali ya rumtse idanunshi sabida sun gaza daina kallon.

A fizge ya sunkuyar da kanshi yaci gaba da cin abincin.

Yayinda idanunshi kuma suka sauka akan.

Tattausan tafin kafafunta da suke a naɗe.

Sosai yaci abincin yana mai kallon himilin gashin.

A hankali yayi wani sassanyan gyatsa, tare da aje goran ruwan daya sha.

Kana ya ɗan ture tray’n gefe tare da ɗaura sawunshi kan table ɗin ya samu yayi balance domin cikinsa yayi masa nauyi.

Dan kab tuwon ya cinye.

A hankali yace.

“Alhamdulillah”.

Sai kuma yayi wani sassanyan gyatsa

Kana ya ɗan kallesu.

“Kai tray’n Kitchen kizo muci gaba”.

Mamy ta faɗa tare da sake kan Jannart.

Ita kuwa miƙewa tayi tare da isowa gareshi ba tare da tasa dankwali ba.

Sunkuyowan da tayi ne kuma yasa gashin tahowa.

Har yana taɓa yatsun ƙafarsa.

Wani irin masifeffen taushi da tsulbin gashin ne yasashi jin tsikar jikin sa mimmiƙewa,

Kauda kanshi yayi tare da miƙewa.

Ya nufi sama.

Ita kuma ta kai tray’n kana ta dawo sukaci gaba.

Suna gamawa su Ramadan na shigowa.

Haka yasa suka wuce Dinning area.

Sosai sukaci abinci fiye da zatonsu sunaci suna zuba santi.

“Kai gsky nima gobe d‘umame zanci Mamy”.

Ramadan ya faɗa yana taunar tattausan sokan nama.

Riyyam-nsra kuwa cewa yayi.

“Ni gsky bazanci dumameba amman a ajiye mana miyar gobe da rana amana tuwo.”

Dariya Mamy tayi tare da cewa.

“Gsky dai miyar tayi daɗi, kamar za’a iya cinta da shinkafa fara ko?”.

Dariya sosai Ramadan yayi tare da cewa.

“Jama’a waiji  yaseen Mamy kema yau kin shiga motar santi”.

Cikin danne dariya Jannart tace.

“Ba wani santi Mamy ana iya cinta da farar shinkafa madadin miyar stew ko mai da yaji”.

Haka dai sukayi ta hira sai kusan karfe goma da rabi suka watse.

Washe gari da Asuba, bayan sun dawo masallacin.

Zaune suke a falon baki ɗayansu.

Yayinda PA ma shigowarsa kenan

A hankali yake takowa yana saukowa.

PA ne ya nufi inda yake yana kallon agogon hannunsa.

Shida da rabi kuma bakwai dai-dai jirginsu zai tashi.

Yana gama saukowa yazo ya zauna kusa da Abba tare da cewa.

“Toh Abba zamu tafi.”

Cikin tsananin kulawa Abba yace.

“Toh Rayyern Allah ya bada sa’a ya kaiku lfy ya dawo daku lfy ya tsareka da sharrin abin ƙi”.

Da “Amin.” suka amsa baki ɗayansu.

Kana ya kalli Mamy.

Mamy ko gane me yake nufi ne yasa tace.

“Allah ya kaiku lfy babana ya dawo daku lfy, PA ka kular min dashi da kyau musamman kan cin abinci.”

Kai Usman PA ya gyaɗa bayan sunce Amin.

Shi kuwa juyowa yayi ya kalli Riyyam-nsra tare da cewa.

“Zan dawo in sameka ko?”

Da sauri ya gyaɗa mishi kai yana mai yin rau-rau da ido yace.

“Yesss Hamma Rayyern zan jiraka sai ka dawo, duk da Mammy tana matsawa in koma”.

Kanshi ya jinjina tare da cewa.

“Toh banda yawon banza, da shashanci, kai kuma Ramadan ka kula da aikinka, kasan ganinka zaisa sauran Doctor’s din karsashi.”

Cikin gamsuwa Ramadan yace.

“Toh Hamma Rayyern Allah ya kiyaye hanya, Insha Allah kuma zan kula.”

“Amin.” Yace yana mai miƙewa tsaye.

PA kuwa tuni ya fita, yayinda Ramadan da Riyyam-nsra suka mara mishi baya.

Kana shima Rayyern ya bisu a baya.

“Rayyern!!”.

Yaji muryar Abbanshi da sauri ya ɗan juyo.

Ƙofar ɗakin Jannart ya nuna mishi tare da cewa.

“Dan Allah ka shiga ka sallameta, na roƙeka da girman Allah.”

Wani irin abu mai nauyi yaji ya danne masa zuciya.

“Ya salam”.

Ya fadi a ransa jin Abban yace ya hadasa da girman Allah wato badon shiba.

Wani rauni, da damuwa ne suka rufesa, sabida ganin da yayi suna gab da sashi a sahun ya’ya marassa biyayya.

A hankali ya juya nufi ƙofar dakin.

Ita kuwa Jannart kasan cewar bakonta (al’ada) ya dawo daren jiya ne, yasa yanzu ta fito daga wonka daga ita sai towel ajikinta, take zaune agaban dreesing mirror’nta.

Rayyern kuwa ahankali ya tura ƙofar falon ya shigo, tare kuma da maida kofar ya rufe.

Ahankali kuma ya tako zuwa tsakiyar falon.

Murya a dakile yace.

“Salamu alaikum.”

Jannart dake zaune kuwa shiru tayi, tare da aje goran man da take shafawa, dan jin kamar mgnar mutum, Jin shiru babu alaman wani motsinne kuma yasa ta cigaba da shafa mai dinta.

Still tana cikin shafa maidin ne kuma tasake jiyo kamar sautin muryar mutum.

Da sauri ta mik’e tsaye tare da nufar kofar fita, ahankali ta bud’e k’ofar  tare da d’an lek’o kanta tace.

“Waye?”

Shiru yayi ba tare daya bata amsaba.

Jannart kuwa hakanne yasa ta sake leƙo da kanta, sai dai bata ganshiba.

Jin kaman da gaske ba kowa acikin falonne kuma yasa ta fito gaba ɗayanta.

Inda tayi taku ɗaya ana biyu ta ganshi tsaye.

Cikin wasu irin fitinannun Suit bakake masu masifar kyau da sheƙi.

Da wani irin sauri ta juya ta koma cikin labule.

Shi kuwa Rayyern dauke kansa yayi gefe, kamar bai ganta ba murya a dakile yace.

“Na tafi.”

Da sauri, kuma cikin muryarta dake rawan fargaban ganinsa da tayi, da kuma ganinta da yayi ahaka tace.

“Allah ya tsare ya kiyaye hanya”.

A takaice yace.

“Amin, idan da zuciya ɗaya kika fada”.

Yana faɗin haka ya juya ya fita.

Jin alamun fitansa ne kuma yasa ta fitowa, daga inda ta boye cikin sauri ta koma cikin bedroom din, tana nanata mgnar sa ta karshe, da taji ya fada.

Shi kuwa yana fita, kai tsaye Airport suka wuce.

Su Ramadan kuwa basu dawo ba, saida sukaga jirginsu ya tashi suka dawo tare dasu Hadi.

Su Rayyern din kuwa a Abuja sukayi breakfast.

Kana sai ƙarfe huɗu dai-dai na yamma jirgin da zai kaisu China ya tashi.

Acan  gidan kuwa Ramadan na dawowa ya tafi aiki, Yayinda Riyyam-nsra kuma kofar gida ya fita wurin Baba Mauɗo.

Su kuwa su Dr.Rayyern Mai-nasara dare ya fara nisa sosai jirginsu ya  sauka a.

 Beijing Capital International Airport China.

Suna fitowa a jirgi.

PA yace.

“Yah Subahanallahi, tsarki ya tabbata ga Ubangijin talikai mai duniya da ƙiyama.”

Rayyern kuwa limshe idanun sa yayi.

Duk da yazo wurin nan a ƙalla sau biyar.

Amman idanunsa kullum a sabo suke ganin Airport ɗin, sabida masifar kyau da tsananin haɗuwa.

Duk da tsakar dare ne kai kace tsakar ranace, sabida yadda wurin yake da masifar kyau da ƙawatuwa.

Ina in an haɗa Airport’s dinmu  na Nigeria da nasu tofa ai namu jujine.

Da dan sassarfa suka fito inda zasu samu taxi.

Bayan sun shigane PA yace ya kaisu hotel mafi kusa da Airport ɗin.

Dan campany’n injinun da suke da akalar kasuwancin yana kusa.

Kai PA ya jinjina cikin takaicin Yaren masu idanun kwadin nan wato China sam basu cika gane turanci ba.

Saida Rayyern yayi masa karin bayani da kyau kana ya gane.

Tafiya mai ɗan nisa kaɗan sukayi sai gasu a wani tamfatsetsen hotel.

China world hotel beijing.

Bayan sun sallameshi ne, suka shiga.

Bayan sun kama daki sun, haura wonka sukayi kana sukayi ramuwar sallan magriba da isha’i, kasancewar sunci abinci a jirgi ba yunwa ba kishi ne, yasa kawai suka kwanta dan yin baccin gajiya, saboda tafiya dai ko ya take tafiya ce.

A nan gida kuwa Riyyam-nsra ne zaune gefen Baba Mauɗo yana masa gugan kayanshi.

Yayinda shi kuma yake can gefe, 

wayarsa dake kusa da Riyyam-nsra ne ta fara ringing.

Juyowa yayi ya kalli Riyyam-nsra tare da cewa.

“Wake kirana?”

Ido Riyyam-nsra ɗin ya zubawa fuskar wayar cike da mamaki, ya juyo ya kalli Baba Mauɗo kana ya Kuma juyowa ya kalli fuskar wayar.

Hakan yasa Baba Mauɗo yun ƙurowa da sauri, cikin rawan jiki ya jawo wayar tasa.

Da sauri kuma ya juyo ya kalli Riyyam-nsra.

Shi kuwa Riyyam-nsra cikin wani irin kallo mai cike da mamaki yace.

“in…!

Riyyam-nsra ya faɗa yana kallon Baba Mauɗo da ya miƙe tsaye, tare da amsa kiran wayar ya liƙa a kunne.

Ba tare daya kalleshi ba, kuma ya fita parlon.

Yana gab da fitan ne kuma Riyyam-nsra ya kuma zura mishi ido jin yana cewa.

“I always pray for wisdom, domin saida hikima zan iya warware zare da abawan da ake sakawa tsawon shekaru dole saida hiki zan warware, in kuma gano bakin zaren, kana inyiwa ahalin GARKUWA daga ruftawa bisa gadar zaren  da magauta ke sakawa.”

Sai kuma ya ɗanyi shiru yana mai jinjina kai.

A ƙalla tsawon daƙiƙu 4 kana cikin yanayin zak’uwa da kaɗuwa yace.

“What are you saying?”

Sai kuma yayi dan jim yana mai gyaɗa kai alamun gamsuwa kana yace.

“You can see me at anytime, saboda mgnar zatafi kyau gani gaka.”

Zare soket ɗin dutsen gugan Riyyam-nsra yayi tare, da juyowa ya fuskanci ƙofar dakin 

Kana kuma ya kasa kunnensa da kyau, Yana mai jiyo muryar Baba Maud’on can ƙasa, dan a hankali yake mgnar alamun baya son wani yaji.

Sai dai mamaki mai tarin yawa ne ya rufe Riyyam-nsra, sabida jin yadda Baba Mauɗo yake sarrafa harshensa da ingantaccen turancin da bai taɓa zaton yanajin koda kawo min wuƙa in yanka kabane sabida yanayin shigarsa harcensa suturarsa.

Kana ya gaza gane ina manufar mgnanganun da yake jiyowa, domin daga kan sunan da ya sawa mai kiran ma ya sashi a tunani sannan kuma a take ya tuno hirar da suka tabayi da Ramadan akan Baba Mauɗon.

Shi kuwa Baba Mauɗo, sosai yake mangantuwa.

Har kusan rabin awa yana mgn kana daga bisani ya katse kiran.

Yana shigowa dakin ya kalli Riyyam-nsra da ya ƙarasa gugan yanzu ya tattare wurin.

Cikin yanayin tsare fuska kada yaron yayi mishi wata tambayar, dan ya sanshi surataccen yarone na ƙarshe fuska a ɗan tsare yace.

“Sannu ko Riyyam-nsra Allah yayi maka al’barka.”

Juyawa Riyyam nsra din yayi ya ɗan kalleshi kana yace.

“Amin Baba Mauɗo.”

Ya ida mgnar yana miƙewa da kayan a hannunsa, cikin ɗan madaidacin wordrobe ya shirya mishi su kana ya juyo yana mai cewa.

“Bari inje inyi wonka.”

“Toh sai ka fito ngd ko”

Cewar Baba Maud’o.

Shikuwa Riyyam kai ya gyaɗa kana ya juya ya fita.

Washe gari da dare suna kwance bisa gado shida Ramadan.

Juyowa yayi ya fuskanci Ramadan da kyau.

Tsaki ya ɗan ja ganin har yanzu Ramadan na ruggume da waya, yayi tsit ya nitsu  alamun yana jin abinda Rayhanarsa ke zanta mishi.

Ganin hakane ya miƙe ya fita.

A falon ya zauna kana ya danddanan wayarsa, ya kira Mammy tana ɗagawa tace.

“Riyyam lfy kuwa?”

Riyyam-nsra kuwa jin muryarta da alamun bacci takeyi ne, yasa ya ɗan kwaɓe fuska kana a hankali yace.

“Mammy kaina yana kullewafa da lamarin ahlin na.

Akwai fa abinda ke ɓoye fa,

ina son Baba Mauɗo kuma, ina ganin wasu abubuwa daga gareshi, shin baki da wani ƙarin bayani a kan makusantan baya ne!? naji ina mamaki amman fa babu mummunan zatoa kanshi.”

Cikin sauƙe numfashi tace.

“Ka haɗani video call dashi.”

Da sauri yace.

“Toh Mammy zan hadaku in ya yarda.”

Har zata katse kiran kuma yace.

“Ina Zayton?”

“Gata tana bacci”.

Mammy Ta fadi a takaice tare da katse kiran.

Da safe zaune suke a Dinning area,

 Jannart na kusa da Mamy suna karyawa.

“Ramadan kayi waya da Rayyern kuwa tunda suka tafi?”.

Mamy ta tambaya.

Tea ya dan kurba kana yace.

“Eh tun ranar da sukaje washe gari, mukayi waya dashi, dazuma kuma muna dawowa masallaci ya kira Abba.”

Kai Mamyn ta gyaɗa tare da cewa.

“Eh haka yace min, Amman ni bai kirani ba yayi kyau ai.”

Riyyam-nsra ne ya ɗan kalli Jannart da tayi kamar bata wurin.

“My Aunty idan kunyi waya kice masa, Allah yasa mutuwa ta manta dani da Mamy, fiye da yanda ya mance damu, tunda mu bazai kiramuba.”

Dariya sukayi baki ɗayansu hatta Jannart, saida ta dara tare da cewa.

“Uhum kishi ko Riyyam-nsra”.

A ranta kuma cewa tayi.

“Waya san dani  nima”.

A zahiri kuwa ido ta zuba Riyyam.

Baki ya tura tare da cewa.

“Ba wani kishi fisabilillahi Mamy ya mana adalci kenan, yaufa kwanansa biyu fa ace bai neme mu ba.”

Dariyar tsokana Ramadan yayi tare da cewa.

“Toh ku kirashi mana.”

Ya ida mgnar yana miƙewa tsaye tare da kallon agogon hannunsa.

Ganin lokaci ya tafine yasa ya nufi waje, shi ma Riyyam-nsra da sauri ya miƙe yana cewa.

“Yauwa Hamma Ramadan muje ka sauƙeni, a gidan Malam Mai-nasara mana, munyi da Nasir zamu hadu a can.”

“Toh taho mu tafi.”

Ramadan yace

Daga nan suka fita.

Suna gab da fita agidanne kuma, Ramadan ya ɗan leƙo ta cikin motar ya kalli Ari, tare da cewa.

“Baba Mauɗo fa?”.

Ari yana mai ida buɗe musu gate din yace.

“Yau tun sassafe ya fita har yanzu bai dawo ba.”

Da sauri Ramadan yace.

“Ina yaje, meyasa Hadi bai kaishi ba?”

Da sauri Hadi dake gefe yace.

“Wllh nace zan kaishi yace, a’a in bari ba dadewa zaiba, toh kuma gashi har yanzu bai dawoba.”

“Yayi breakfast ne kafin ya fita.”

Ramadan ya kuma tambaya.

“A’a baiyiba”.

Ari ya faɗa.

Kai Ramadan din ya gyaɗa tare dajan motar suka fice daga cikin gidan.

Wayarshi ya miƙa wa Riyyam-nsra tare da cewa.

“Kira min shi.”

Toh yace tare da duba number kana ya kira.

Miƙa masa wayar yayi jin an amsa kiran.

“Assalamu alaimun  Barka da safiya Baba Mauɗo.”

“Wa alaikassalam Barka dai Ramadan”.

“Baba ina ka tafine yau shiru ban ganka ba.”

Da sauri Baba Maud’o yace.

“Ah gani nan zuwa nazo nan wurin wani ɗan ƙasarmu ne Niger ne zai je gida Agadaz gobe shine zan aikeshi.”

Yana mai taka motar yace.

“Toh sai ka dawo nima na wuce wurin aiki amman ai da ka gaya min da na kaika.”

“A’a ba komai Allah ya bada sa’a.” Baba Maud’on ya fad’a.

Ramadan kuwa da 

“Amin.” Ya amsa kana ya katse kiran.

Shi kuwa Baba Mauɗo juyowa yayi ya fuskanci mutanen da yake mgnar da Allah ne kadai yasan kan me suke tattaunawa cikin killace kai sukaci gaba da mgn.

A cikin gidan kuwa, tattare wurin Jannart ta fara.

Mamy kuwa miƙewa tayi ta koma side ɗinsu dan sanin Abba na tsumayin ta.

Tana gama kimtsa wurin ta wuce Bedroom ɗinta dan, bacci takeji kasan cewar in tana cikin halin larura  tana yawan jin kasala da bacci.

Bayan Ramadan ya sauke Riyyam agidan Malam Mai-nasara,  bai shigaba ya wuce sabida lokacin ya kure masa.

Zaune suke gaban malam Mai-nasara.

Cikin muryar girma yace.

“Zakariyya ya jikin ya’yan naka?”

Kai Riyyam ya d’aga ya ɗan kallesu tare da cewa.

“Jiki da sauki har yayi tafiya ma, zuwa China.”

Da sauri Uncle Mustapha yace.

“Eh lallai haka akayi ai naje dubasa a asibitinsa, da yake ban san gidan nakuba, nan yake cemin zaiyi tafiya in ya dawo zaizo ya duba ka da jiki Malam.”

“Masha allah. Toh Allah ya dawo dashi lfy.”

Cewar Malam da Amin suka amsa.

Nasir ne ya ɗan miƙe tare da cewa.

“Riyyam mu tafi ko.”

Inna ce ta kalleshi cikin tuhuma tace.

“Ku kam baku da aikin yine kullum sai yawo da latse-latsen waya?”

Da sauri Nasir yace.

“Kinfi kowa sanin karatu nakeyi kuma ina gab da hada degree dina, shi kuma Riyyam-nsra yama gama wannan shekarar, kuma aikine yake nema tukun.”

Ya ida mgnar yana haɗe fuska.

Uncle Mustapha kuwa murmushi yayi hakama Malam.

Sukuwa su Riyyam nsra daga nan rijiyar zaki suka nufa gidansu Nasir ɗin.

A falo suka samu babban ya’yan Nasir.

Yah Marwan kasan cewarsa filot ne kwana biyu yana gida.

Marwan yana da sauƙin kai sosai haka yasa suke sakewa dashi,

Bayan Riyyam ya gaida Marwan da Ummansu ne, suka roƙeshi mota.

Miƙawa Riyyam car key din yayi tare da cewa.

“Ku kula da kanku, banda tuƙin ganganci.”

Da sauri suka amsa tare da miƙewa.

Kana suka fita suna cewa.

“Umma sai mun dawo.”

Murmushi tayi tare da cewa.

“Allah ya kiyaye.”

Amin sukace kana suka fice.

Dr.Rayyern Mai-nasara kuwa a ƙasar masu ƙananan idanu, komai yana tafiya bisa tsari yadda yakeso.

Yau kwanansu tara a garin, ya sayi dukkan abun da yake buƙata na campany’nsa.

Sai kuma Engineer bello ya kirashi ya shaida masa suna son wannan karfen 3%, ya zama biyu suka samu domin aje sefiya.

So hakane yasa tashi da shirin zuwa sayansa cikin ingantacen kamfanin kayan ƙarafunan.

Tsaye yake cikin shirin fita PA na tsaye agefensa.

Kiran Mamy ne ya shigo wayarsa da sauri PA yace.

“Mamy ce.”

Yayi mgnar yana miƙo masa wayar.

Amsa yayi tare da karawa a kunne

“Barka da safiya Mamy.” 

Ya fad’a cikin kulawa.

A dakile tace.

“Barka dai.”

Ba tare da ta bari yayi mgn ba ta daura da cewa.

“Ka kira Jannart kuwa tunda ka tafi?”

Idonshi ya ɗan jujjuya alamun nazari kana a hankali yace.

“Mamy waye kuma hakan?”

Fuska ta kuma tsukewa kamar yana gabanta tace.

“Ok bari in kaiwa Abbanku wayar sai ya gaya maka waye ita.”

Da sauri yace.

“Dan Allah Mamy ki saki ranki kimin bayani, wlh ban fahimci mgnar kiba,

niba sai kin haɗani da Abba ba, ɗazu ma munyi mgna dashi.” 

Murmushi ta ɗanyi a ranta tace.

“Uhum Rayyern halinka sai kai.”

A zahiri kuwa cewa tayi.

“Matarka ce baka saniba yanzu tunda ka tafi sau nawa ka kirata?”

A takaice ba tare da yaja mgnar ba cikin kare kai yace.

“Mamy banda number ta.”

Sai kuma yace.

“Dan Allah Mamy kiyi haƙuri ina zuwa zan kiraki anjima yanzu wani aiki nakeyi.”

Bai jira me zata ceba ya katse kiran wayar, kana ya miƙa wa Usman ita, daga nan suka fito d’aya daga cikin taxi ɗin hotel ɗin, nasu suka shiga kamar koda yaushe.

Kai tsaye Chinese Construction Engineering company suka nufa, 

koda suka shiga basu fitoba sai gab da sallan azahar dinsu.

Suna fitowa sukayi salla kana suka shiga taxi ɗin da suka zo dashi dan yana jiransu, tunda batu ne dai na kuɗi daga nan Rayyern yace ya kaisu halal Restaurant.

Tafiyar mai yar tazara sukayi kana suka tsaya, wani babban wuri inda daga can sama aka rubuta HALAL Restaurant’s da manyan baki.

Kai RAYYERN ya ɗan juya ya kalli gefen hagunshi kana ya juyo damanshi.

Bottega ya faɗa a hankali kana ya ɗan kaikace ya zaro katinshi, ya miƙawa PA tare da cewa.

“Shiga ka saya mana, ni pizza ma ya isheni,kai kuma ka sai abinda kakeso, ka sayawa wannan ma.” 

Ya ida mgnar yana nuna masa Driver’n’sun.

Toh yace, ya amsa kana ya  bude  ya fita.

Jim kaɗan ya dawo riƙe da ledodi.

Kana ya shiga suka tafi.

Bayan kwana biyar ya gama har had’a komai, ya kimtsa kayansa kana ya kaisu Airport, dan yana son kayan su rigasu tasowa.

Yau ta kama satinsu biyu cur da zuwa.

Yau ne kuma jirgin kayansu ya tashi sai dai ta Lagos zai sauƙa.

Daga can kuma ya wuce Kano.

Kasan cewar yau ɗin Lahadi ne, shine a.lissafi kuma sunyi kwana goma sha huɗu.

Tunda safe yayi musu  order’n abinci ta online a Frongji Restaurant, kasan cewar komai nasu da tsari, yasa Delivery available ne ko yaushe.

Kuma free delivery ne, cikin abinda baifi 40 minutes ba sai gashi sun kawo musu har ƙofar dakinsu.

Jin ana buga ƙofar ne yasa.

Ya ɗanyi miƙa daga kwancen da yake, ido ya ɗan rumtse sabida kartawar da yakeji cikinsa nayi masa tun daren jiya.

A hankali ya yunƙura ya taso jin anci gaba da bugawar, ya sani bazai iya cin komai ba, sai dai yayi musu order ne sabida PA.

A hankali ya miƙe tsaye sai dai ya kasa ida miƙewa zat, sabida yadda yaji cikinsa na tsananta ciwon in ya gwada tsayuwar, hannunshi yasa ya dafe cikin, kana ya fara taku a hankali.

PA kuwa dake falon kasan cewar  ya fara yin bacci ne, yasa toh sai yanzu yaji bugun da sauri.

Ya miƙe tare da nufar ƙofar yana buɗe wa.

Ma’akkacin Halal Frongji restaurant, din ya miƙa masa ledodin hannunsa kana ya juya ya fita.

Sabida dama yayi musu transfer’n kuɗin su.

Yana juyowa ne kuma ya hango Rayyern ɗin yana fitowa daga cikin Bedroom din.

Ido ya zuba mishi ganin a ɗan sunkuye yake tafiya, kana yana dafe da cikinsa da hannun damanshi, da  sauri ya nufo gareshi, cikin kulawa da fargaba yace.

“Sir lfy kuwa?” 

Cikin rumtse idanunshi ya zauna bisa kujerar dake gefenshi.

Ba tare daya buɗe idonba murya a hankali yace.

“Usman ƙara gudun AC’nnan”.

Da sauri Usman ya juya, ya ƙara gudun ACn kana ya dawo inda yake.

Cikin kulawa yace.

“Sir cikin ne?”

Lip ɗinsa na ƙasa ya taune,

tare da ƙara rumtse idanunshi kana a hankali ya miƙe kan kujerar,

baya son yin mgn sabida ko numfashin ya fesar sai yaji wani irin masifeffen ciwon cikin ya karu.

Ido P.A ya zuba mishi ganin lokaci ɗaya wata iriyar fitinenneyar zufa ta keto mishi tako wanne hudan gashin jikinsa.

Duk da sanyin garin da kuma na’urar take busawa.

Gaba ɗaya hankalin Usman ya tashi sunkuyowa yayi kansa cikin tsananin tsoron kada dai ciwon cikin nasa ne zai tashi yace.

“Hamma Rayyern ko zamu tafi asibiti ne?”.

Cikin sanyi murya can ƙasa yace.

“P.A kaci abinci”.

Ya ƙare mgnar da ɗan ƙarfi alamun baya son mgnar.

Shi kuwa P.A a hankali ya ɗan ja da baya cikin taraddadi yace.

“Toh tashi muci.”

Da sauri ya buɗe idanunsa da tuni sun gama rinewa sunyi jazir sabida ciwo.

A faɗace yace.

“Dan Allah ka zauna kaci abinci.”

Jin hakane yasa P.A aje ledodin kana shima ya zame ya zauna a wurin.

Shi kuwa Rayyern juyawa yayi ya kwanta a kife.

Tare dasa hannunsa duka biyu ya dafe cikinsa.

“Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani’imanwakil, la’ila ha illa’anta subahanaka innikuntu minazzalumin”.

Waɗannan sune yaketa maimaitawa a hankali, yadda P.A ma bayaji kana ya matse cikin yayi shiru.

Hakan ne yasa hankalin P.A ya ɗan kwanta,

har ya samu yaja abincin ya fara ci.

Yanaci yana juyowa yana ɗan kallonsa.

Haka dai har ya gama ci.

Kana ya tattare wurin.

Sannan ya wuce ɗakin kwanansa ya ɗauko wayarsa, kana ya fito falon.

Dakin Rayyern ɗin ya wuce,

Woyoyinsa ya dauko duka biyu kana yazo ya zauna kusa dashi.

Zuwa lokacin kuma cikin ya ɗan lafa,

hakan yasa Ya buɗe idonshi ya kalleshi a hankali yace.

“Me zakayi da waya?”

Da sauri ya kalleshi tare da cewa.

“Dama zan kira Ramadan ne ko Dr Sulaiman in gaya musu halin da ake ciki.”

Tsareshi da ido yayi, hakan yasa yayi shiru.

Hannun ya miƙa masa ya amshi woyoyin kana a hankali yace.

“Kada ka faɗa musu domin zaka tada musu hankali, kuma in nayi Sa’a haka zai keyi yana lafawa har ya bari, so kada ka gaya musu”.

Cikin yanayin rashin gamsuwa yace.

“Okay Sir”.

Shi kuwa a hankali ya miƙa ya tsaya tsakiyar tamfatsetsen falon na al’farma.

Kana ya nufi ɗakinsa.

Kai tsaye Bathroom ya wuce.

Wonka yayi kana ya fito.

Wasu tattausan riga da wondo yasa Pink panther masu sheƙi.

Kana ya gyara labulayen sannan ya ƙara ac sannan ya kashe wutan ɗakin ya dawo ya kwanta.

A nan gida Nigeria kuwa.

Bayan sallan isha’i Abba ne 

Zaune bisa kujera, Ramadan na gabansh, Yayinda Mamy ke gefensu.

Jannart da Riyyam-nsra kuwa suna can main falon suna kallon  wani India’n Film a zee world.

A Karo na barka tai Ramadan ya kuma gyara zamanshi,

Abba kuwa ido ya zubawa TV kamar yana gane me sukeyi.

Yayinda Mamy kuwa ta zuba musu ido.

Cikin kwaɓe fuska da shogobe fuska Ramadan yace.

“Uhum Abba dama..”

Sai kuma yayi shiru.

“Dama me?”

Abba ya tambaya ba tare da ya kalleshi ba.

Cikin sanyi yace.

“Eh dama gidansu Rayhana ce, sukace in tura”

A fakaice Abba ya kalleshi tare da cewa.

“Ka tura me?”

Kamar zaiyi kuka yace.

“Wai in tura manya na ayi mgnar aure in da gaske nakeyi, dan su gidansu daga yarinya ta gama Secondary School bazataci gaba ba, sai an aurar da ita taci gaba a gidan mijinta, to gashi ita Rayhana har taci gaba sabida, batun Hamma Rayyern baiyi aureba, shine sukace toh ai yanzu dai yayi auren sai ayi batun namun ko?”

Ya ƙare mgnar yana kallon iyayen nasu.

Mamy kam kai ta kauda tana mamakin zalama, irin ta Ramadan sam baya iya ɓoye maitarsa akan san aure.

“Wannan dai anyi jarabebben yaro”

Ta faɗa cikin ranta

Abba kuwa numfashi ya ɗan fesar tare da cewa.

“Toh su sukace ko dai kai kace?”

Da sauri yace.

“Su”

Kallonshi yayi tare da cewa.

“Banbancinka da Rayyern kenan Ramadan, kai kakan ɗan taɓa ƙarya shi kuwa duk ɗacin gsky zai faɗeta, yanzu da shine cewa zaiyi shine ya faɗa”

Da sauri yace.

“Toh Abba nine na faɗan.”

Mamy kam dariyar dake cintane ta dan subuce mata.

Ido ya ɗan zuba mishi kana yace.

“Wato kai dai ayi maka aure kake so ko?”

Da sauri yayi ƙasa da kansa.

“Toh ba damuwa tashi kaje zamuyi mgn da Baba Mauɗo.”

Wayyo Ramadan kamar ya mutu dan daɗi ai da sassarfa ya fito.

A falo ya tsaya kusa da Jannart cikin happy yace.

“My Aunty ki shirya kun kusa kai kayan aure.”

Da sauri Jannnart din tace.

“Kai haba dai iye, lallai kam abin nema ya samu kenan matar ma tsunci ta haifi kogi.”

Riyyam nsra kuwa Jujjuyawa yayi tare da cewa.

“Eh matar falke ta haifi sanda,

kai lallai akwai casu a ƙasar Kano”

Sai kuma suka bishi da ido jin ya kira Rayhana ya fara mgn da ita ya haura sama.

Murmushi Jannart tayi tare da cewa.

“Kai Riyyam wai kai baka gajiya da rawane?”

Dariya mai sauti yayi tare da cewa.

“Nida Hamma Rayyern duka ƙugunmu kamar roba yake Bama gajiya da karairayashi”

Harara ta ɗan cilla mishi tare da cewa.

“Ji sharri”.

Da sauri yace.

“Wallahi kuwa my Aunty”.

Cikin hararan wasa tace.

“A’a wlh kada kayi mishi sharri, wannan kuma da son jiki ma abu kaɗan ya kama raki yaushe zai iya jujjuyawa kamar yadda kake”

Dariyar Mamy da suka jine yasa, Jannart miƙewa da sauri ta nufi ɗakinta cike da kunya.

Ita kuwa Mamy tafiya takeyi tare da cewa.

“Gskyarki dai kare mijinki diyata”

Shima Riyyam dariya yayi tare da cewa.

“Aifa kam tana kareshi.”

Nan dai sukaci gaba da hira.

A can China kuwa gaba ɗaya wunin ranar a daki Rayyern yayi shi.

Koda ruwa bai sa a bakinsa ba,

sabida matsa mishi da cikinsa yayi duk bayan 10mnt sai ya lafa na tsawon 10mnt ɗin kana ya sake tashi.

Salla kwai ke tadashi, shima sai in ya samu ya lafa.

P.A kuwa haka ya wuni zirga-zirga a kansa.

Dare nayi kuwa ciwo yace Assalamu alaikum.

Ya tashi gadan-gadan.

Shi kuwa P.A yayi baccin gajiyan zirga-zirgan, da yayi yau din.

“Ya ilahi ya mujibadda’awati.”

Sune kalaman da bakinshi ke iya furta wa, yayinda gaba ɗaya jikinshi ke wani irin masifeffen karkarwa, 

zuface take keto mishi tako ina tamkar wanda ake watsawa ruwa.

Juyi yakeyi a kan gadon yana mai yin duk wata addu’ar da tazo bakinsa.

“Innalillahi wa innailaihi rajiun”.

Yayi addu’ar cikin wani irin azabebben numfashin, da yake ja tamkar ransa zai bar gangar jikinsa.

Kar-kar haka jikinsa ke rawa, so yake ya jawo wayarshi ya kira asibiti, amman  ina ya kasa hakan sabida ko numfashinsa, in yaja kamar zai suma haka yakeji, cikin ya kulle yayi wani irin tauri da zafi.

A hankali ya mirgino dan matsowa zai jawo wayarsa, cikin akasi ya ture woyoyin duka biyu suka fadi ƙasa daga kan bedside drower.

Dai-dai lokacin kuma yaji cikin nasa yayi wani irin damƙa mai cike da azaba.

Wani irin duhune ya rufewa ganinsa.

A hankali yaji kamar gadon na jujjuyawa dashi…

P.A kuwa yanata baccinsa, sai asuba ya tashi, alwala yayi bayan ya fito yayi sallan asuba.

Sabida ganin kamar ya ɗan makara yasa Rayyern yayi ta tadashi kenan bai tashi ba.

Yana idawar ya fito falo.

Shiru ya tsaya tsakiyar falon.

“Bai tashi ba, ko ya fitane, bari in duba dai?”

Yayi mgnar zuciya yana mai nufar dakin.

A hankali ya dan ƙonƙosa kofar.

Shiru ba alamun mgn haka yasa ya kuma bubbugawa yana mai kiransa still shiru.

Dan tura ƙofar yayi tare da sallama a bakinsa.

Cikin yanayin firgici ya zaro ido tare da nufo kan gadon, sabida hango Rayyern ɗin da yayi a yashe bisa gadon tamkar matacce.

Cikin kidima ya haura gadon tare da ruggumeshi yana jijjigashi da kiran sunanshi da ɗan ƙarfi.

“Sir! Sir!! Sirrrrrr!!!!”.

Ya ida kiran da ƙarfi cikin tsananin tashin hankali, domin gaba d’aya jikinsa ya sake yayi sanyi tamkar wanda ya mutu, sai iya cikinsa ne yake da ɗumi.

“Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani’imanwakil Hamma Rayyern tashi”.

Gaba ɗaya jikinsa rawa da karkarwar yakeyi.

Cikin tsananin tashin hankali ya debo ruwa ya yayyafa mishi amman ina.

Haka yasa ya buɗe ƙofar ɗakin ya fita da gudu.

Sauka kasa yayi.

Jim kaɗan sai gashi ya dawo da ma’aikatan hotel ɗin.

Kana da Driver’n’ taxi.

ID card din Rayyern ya nuna musu.

Tare da Receipt’s din kayayyakin da suka saya da kuma takardun Campany da matsayin nasa companies din da kasan cewarsa likita.

Haka yasa da sauri sukasa hannu suka ciccibeshi suka sauƙo aka sashi a mota, P.A ya shiga tare da jan marfin ya rufe kana Driver’n yaja.

Daga nan kai tsaye

Puhua International Hospital and clinic (PIH) Suka nufa.

A cikin motar kuwa cikin tashin hankali P.A ya kira. Dr  Sulaiman yana ɗagawa yace.

“Dr Usman P.A ke mgna”.

Cikin kaɗuwa Sulaiman yace.

“Yesss na gane meke faruwa ne Usman”.

Murya a karye yayi mishi bayanin abinda ya faru ya ɗaura da cewa.

“Yanzu haka yana sume gamu a hanyar zuwa asibiti, yauwa gashi ma mun iso”

Yayi mgnar ganin sun shiga cikin asibitin.

Suna yin parking nurses Suka nufosu.

Da irin wannan gadajen ganin Ambulance ce kuma da tambarin hotel ɗin a jiki.

Suna isa driver’n na buɗe musu.

Da sauri P.A ya fito yayinda Sulaiman ke ce mishi.

Ina kun isa ka haɗani da Doctor ko nurse, duk wanda ka samu kana kada ka gayawa su Abba sai ya farfaɗo kaji ko Usman”.

Da sauri yace to kana ya fito.

Daurasa sukayi a kan gadon kana suka nufi Emergency room.

Yayinda tuni likitoci suka rufawa Nurses din dake tura gadon baya.

Da sauri P.A ya miƙawa daya daga cikin Nurses din wayarsa.

Ƙarawa a kunne tayi.

Kai take ta jinjinawa jin cikekken bayanin matsalarsa, haka yasa da sauri ta miƙa babban Doctor’nsu wayar.

Sosai Sulaiman yayi mishi duk bayani, wannan yasa suka fara bin matakan bashi taimakon gaggawa.

Bayan ya bawa nurse din wayar ta dawowa P.A da ita.

Wasa-wasa kusan awa uku ba’a fito da shiba,

hankali P.A yayi matuƙar tashi.

Sulaiman kuwa ya kirashi yafi sau goma.

Sosai shima ya karaya jin shiru ba’a fito da shi bane.

Yasa yace.

“P.A kira Ramadan ka gaya masa halin da ake ci, ni gsky abin ya bani tsoro”.

Cikin karaya P.A yace.

“To.” kana ya katse kiran.

Number Ramadan ya kira.

Shi kuwa Ramadan lokacin duk suna falon, sun gama karyawa kenan.

Kasan cewar jiya a asibiti ya kwana shiyasa yau zai wuni a gida duk da Monday ne.

Jin wayarsa na ringing ne ya kalli Jannart, dake kusa da wayar inda ya sakalata a caji.

“Waye ne”. Ya tambaya.

Dan leƙa fuskar wayar tayi tare da cewa.

“P.A ne”

Haka nan sai yaji zuciyarsa ta tsinke.

Mamy ma haka abin yake gareta.

Sai suka zubawa wayar ido gaba dayansu.

Riyyam-nsra ne ya ɗan jujjuya ya kallesu.

Yayinda sai kuma yace.

“Hamma Ramadan ka amsa mana”.

“Miƙo min wayar”.

Yace yana kalloshi

Da sauri ya miƙo masa wayar bayan ya amsa kira na biyu.

“Hello P.A ya akayi ne?” 

Cewar Ramadan.

P.A kuwa Murya a sanyaye yace.

“Ramadan Hamma Rayyern ba lfy ciwon cikinsa ya tash…”

Da sauri duk suka juyo suna kallon Ramadan din daya miƙe tsaye yana cewa.

“Innalillahi wa innailaihi rajiun, hasbunallahiwani’imanwakil,

P.A, ina yake? Wanne hali yake ciki? Kuna ina yanzu? Bashi wayar!”

Gaba daya Ramadan din ya gigice.

Jin abinda yake faɗa ne kuma yasa Mamy miƙewa, jiki na rawa take cewa.

“Menene Ramadan meya faru da Rayyern? Ina yake bani wayar”.

Juyawa yayi cikin yanayi tashin hankali jin P.A na cewa.

“Muna asibitine Ramadan, a sume muka kawoshi tun safe, kuma har yanzu bai farfad’oba, nima kaina ban san halin da yake cikiba”

“Yah ilahi ya mujibadda’awati”.

Ramadan ya faɗa murya na rawa.

Mamy kuwa da sauri ta nufi side ɗinsu tana cewa.

“Abban Rayyern, Rayyern! Rayyern!!!”.

Da sauri Abba ya miƙe ya nufo kofar falon su.

Riyyam-nsra kuwa a main falon.

Gaba ɗaya jikinshi rawa ya fara.

Yayinda Jannart kuwa take binsu da kallo.

Shi kuwa Ramadan bin bayan Mamy yayi yana cewa.

“Abba Hamma Rayyern ciwon cikinsa ya tashi, tun jiya da dare yana sume har yanzu bai farfadoba, Abba ya zamuyi.”

Da sauri duk suka tsaya cirko-cirko a tsakiyar falon.

“Kira min P.A maza bani wayar”

Cewar Abba haka yasa Ramadan sake kiran P.A.

Bayanin da yayiwa Ramadan din shi yayiwa Abba.

Tashin hankalin da ba’a sa masa rana.

Jannart kuwa shiru tayi tana kallon Riyyam-nsra daya kira Mammy a waya yana gaya mata abinda ke faruwa yadaura da cewa.

“Mammy kiyi masa addu’a’n samun lfy kin san addu’arki gareshi bata da hijabi, Mammy yana cikin tsananin hali wuya bakiga yadda ciwon ke wahal dashi ba kamar zai ɗauke mana ransa”.

Ya ƙare mgnar murya na rawa hawaye na zuba.

Ita kam Jannart abubuwan sun raunata-ta.

Domin ganin hawayen Riyyam.

Dan ita haka Allah yayi idonta muddin taga hawaye idon wani to nata zai zubo, dan irin idon GARKUWA ne fareta.

Haka kuma tana da rauni abu kaɗan ke sata hawaye.

Bare kuma wannan al’amarin da tasan yana masifar sasu cikin tsananin tashin hankali.

Sautin muryar Abba tajiyo cikin rauni yana cewa.

“Rukayya ki dena yi mishi kuka, addu’arki yafi buƙata, Ramadan tashi maza dauki E-passport dinmu, Ka fara mana shirin tafiya.”

Ya ƙare mgnar suna fitowa main falon a jere.

Yayinda shima idanunsa sunyi jazir alamun tashin hankali.

Waje ya nufa.

Mamy kuwa zamewa tayi ta zauna bisa kujera hawaye na shatata tace.

“Yah Allah kaji tausayin wannan bawa naka, ka jikanshi ka yaye masa wannan azabar ka bashi lfy.

Ya Allah ka zama gatansa a kasar da ba ta saba bashi da kowa sai kai ya Allah”

Cikin raunin murya da sanyi ido na ciko da hawaye Jannart tace.

“Amin ya Allah, Mamy ki dena kuka kici gaba da yimishi addu’a”.

Riyyam ya kalli Ramadan da ya sauƙo yanzu da E passport a hannunsa.

Da sauri Riyyam yace.

“Hamma Ramadan bazakayi muku booking ta online ba ai yafi sauki.

Ka duba ka gani ina za’afi samun jirgin China da wuri Abuja ko Lagos kaga baka da nitsuwar yin tuƙi”.

Da sauri Jannart tace.

“Eh hakanfa zaifi”.

Hakan kuwa shi yasa Ramadan komawa zaune jiki, a mace ya fara bincike kan sifirin jiragen sama na kasa da kasa.

Cikin sa’a kuwa ya samu akwai jirgin zuwa China ta Abuja nanda kwana biyu.

Haka yasa ya fara hidimar neman visa nan take a wurin yayi komai.

Sabida yanzu duniya ta zama a tafin hannu.

A can harabar gidan kuwa.

Gaba ɗaya hankalin Baba Mauɗo yayi matukar tashi da jin wannan lbrin.

Hadi da Ari ma jikinsu yayi sanyi.

Suna nan Sulaiman ya shigo.

Bayan sun gaisane ya kalli Baba Mauɗo cikin kulawa yace.

“Ba komai fa, ya farfaɗo P.A ya ganshi ma, sai dai sun hanashi shiga dakin da yake”.

Toh abunka da nesa in kaji baka gamsuwa in ba gani kayi ba.

Koda suka shiga cikin gida.

Nan yayi ta kwantar musu da hankali.

Haka dai suka wuni a ranar da zulumi bini-bini su kira P.A.

Washe gari ma hakan suka wuni.

Toh da Yamma Ramadan ya tafi Abuja.

Dan Sulaiman da P.A sunce ba sai Abban yaje ba.

Tafiyar Ramadan yasan gidan ya ƙara zama shiru kamar ba mutane.

P.A kuwa shima har yau bai ganshi ba.

Sai da dare ne da ya sake zuwa asibitin sai gobe da safe yazo.

sunce ya koma masauƙinsu ne a cewarsu ma’aikatansu ke kula da maralafiya.

  

Ranar da Ramadan yazo Abuja da dare washe gari da safe.

Jirginsu ya daga zuwa kasar China.

Gab da magriba jirginsu Ramadan ya sauƙa.

Daga Airport ɗin kai tsaye Puhua International Hospital din yace mai taxi ya wuce dashi.

Cikin sa’a kuwa suna zuwa bakin gate din P.A na fitowa.

Nan ya sallami mai taxi shida PA Suka nufi ciki.

“Kayi sauri P.A ta ina zamu bi? Ya jikin nasa? Yana mgn?”.

Ramadan ya jerowa Usman tambayoyin.

Cikin sanyi Usman yace.

“Ko munje bazasu barka ka ganshi ba, amman sunce gobe da safe zamu ganshi. Sai dai in nuna maka dakin da yake ciki kawai.”

Hakan kuwa akayi duk da kasancewar Ramadan likita basu barshi ya shigaba sabida wai ƙare a gidansa zakine.

Dole suka koma masauƙinsu.

Usman din yayi musu order’n abinci.

Bayan sunyi wonka sunyi sallane.

Suna cin abinci Ramadan ya kira Abba wanda lokacin suna tare da Baba Mauɗo nan ya ɗan ƙarfafa musu guiwa.

Kana ya kira Riyyam yace ya bawa Mamy waya.

Toh sun danji sanyi dai.

Washegari

Ƙarfe takwas dai-dai ta samesu tsaye a bakin dakin da Rayyern ɗin ke ciki.

Wanda yau kwana shi uju kenan a na hudu.

Bayan Doctor ya fitone.

Ya kalli Ramadan tare da cewa ya biyosa Office nasa.

Haka kuwa akayi.

P.A kuma yana tsaye a wurin

Tsawon kusan ,35mnt kafin Ramadan ya dawo jiki a mace.

A hankali yace.

“P.A mu shiga”.

Da sauri P.A ya mara masa baya.

Suna shiga suka hangoshi can kwance kan gado.

Lumshe ido Ramadan yayi sai ga wasu hawaye masu zafi sun zubo mishi.

Sabida tausayin Hamman nashi.

Shi kuwa Rayyern cikin yanayin mamaki yake kallon Ramadan tare da buɗe baki a hankali yace.

“Ramadan yaushe kazo”.

Hawaye na zuba yace.

“Jiya nazo Hamma Rayyern”.

Cikin tausayawa P.A yace.

“Sir ya jikin?”.

A hankali yace.

“Alhamdulillah”.

Ina hawaye Ramadan sun gaza tsayuwa, sabida ganin wani irin masifeffen rama da Hamman nashi yayi.

Cikin nan a ɗakale tamkar babu hanji a ciki.

Ya rame yayi fiyau.

Yayi wani irin sanyi ko mgn a hankali yakeyi.

“Abba ya gaisheka da jiki Baba Mauɗo yace inyi maka sannu in shafa masa kanka, Riyyam yanata kuka.

Mamy ma tanata kuka.

Aunty Jannart tace in gaisheka da jikin”.

Idonshi ya lumshe tare da cewa.

“Ayyah na samu sauƙi ai”.

A raunace.

P.A yace.

“Sir a hakan ne ka samu sauƙin?”.

Kai ya ɗan jinjina dan baida kuzarin komai.

Cikin sanyi yace.

“Visa’n mu ya kusa karewa ko.

Dama kwana ashirin da uku ne ko P.A?”.

Da sauri ya gyaɗa kai.

Cikin sanyi yace.

“Kaifa Ramadan?”.

Yana gyara masa pillow yace.

“Ƙafarka kafata ai”.

Kwanansu biyu a asibitin bayan zuwan Ramadan aka sallamesu.

Nan suka fara shirin dawowa.

Sun dai kashe kudi kam dan yanke kwanakin Ramadan.

Cikin sa’a kuwa suka samu jirgin Lagos.

Haka yasa suna sauƙa suka haɗo da kayansu da ya kai kwana bakwai da isowa.

Ƙarfe takwas na dare suka sauka a Lagos.

Sha ɗaya da rabi kuma jirgi ya debesu zuwa kanon dabo jallabar hausa.

A gida kuwa Abba da Baba Mauɗo.

Hadi da Riyyam mota ɗaya ne suka tafi Airport daukosu.

Jannart kuwa tun bayan sallan isha’i da ta fito.

Bata samu kowa a falonba ta koma dakinta

Ta kwanta tana Game har bacci ya kwasheta.

Sha biyu da rabi dai-dai suka iso gida.

Da sauri Ari ya buɗe musu gate.

Cikin kulawa Baba Mauɗo ya fito tare da matsawa gefe.

Kasan cewar dama a tsakiya sukasa Rayyern ɗin shida Abba.

Tallabeshi yayi sabida ganin kamar jiri na dibansa.

Cikin sanyi yace.

“Baba Maud’o zan iya dai”.

Da kulawa yace.

“A’a Rayyanu kaga yadda ka dawo kuwa cikin sati ɗaya”.

Isowar Ramadan ne yasa ya ɗan matsa yace.

“Ramadan tallabeshi.”

Cikin ƙarfin hali yace.

“Ka barni zan iya”.

Dole tasa aka barshi.

P.A da Riyyam kuma dama sunyi gaba da kaya tuni sun haura sama.

Ganinsu ne yasa Mamy fitowa da sauri.

Dai-dai lokacin su kuma suka iso kan barandar.

A hankali ya zauna bisa kujera tare da sauke nannauyan numfashi dan gajiya.

Cikin tsananin so Mamy ta matsoshi tare da jera mishi sannu.

“Sannu  Babana. Ramadan meyasa bazaka taimaka mishi ba, kasan yadda allurar nan take mishi fa”.

A hankali ya fesar da numfashi tare da miƙewa tsaye yace.

“Mamy ba’amin allurar ba”.

Ya ƙare mgnar yana shigewa ciki.

Abba da Ramadan na biye dashi a baya.

Baba Mauɗo Kuma dasu Hadi sukayi baya.

A hankali ya fara take matakalan yana layi.

Ganin hakane yasa Abba rikoshi ya tallabeshi suka fara takawa

Fuska ya ɗan kwaɓe yana cewa.

“Zan iyafa”.

“Kaci gidanku Rayyern, bana son wannan taurin kan da ƙarfin halin dolen nan”.

Abba ya faɗa suna takawa.

Dole yayi shiru.

Suna shiga kai tsaye ɗakinsa suka shiga.

“Zan kwanta bacci nakeji”.

Ya faɗa yana kwanciya.

“Kada kayi bacci bari in kawo ma abinci”.

Cewar Mamy kai ya jujjuya tare da lumshe ido.

“Ku barshi sabida akwai mgnin dake ɗan sa bacci a magungunanshi.”

Cewar Ramadan.

Haka yasa suka fita suka bar Ramadan.

Abba da Mamy suka sauƙo.

P.A da Riyyam suka kwana dakin Ramadan.

Abba kuwa da Mamy a falonsu suka zauna suka fara tattauna wasu, mahimman abubuwan wanda dagasu sai mahalicci su suka san menene.

Washegari da safe.

Misalin ƙarfe shida Jannart ta fito.

Cikin wani tattausan material mai masifar kyau.

Ɗinkin doguwar riga yabi jikinta ya lafe.

Kasan cewarsa Royal blue, pink, yellow, and green sai ya zama kamar zanen dawisu kana yasa farar fatarta kara fitowa ras hips ɗinta sukayi cib-cib da rigar gwanin kyau.

Ta tubke jelan gashinta daya konta kan wuyanta.

Ɗan sisirin mayafi pink color ta yafa.

Sai ƙamshi take bazawa gwanin daɗi.

A hankali ta turo ƙofar falon.

Da sauri ta rusuna ganin Abba na saukowa daga sama.

“Abba ina kwana?”. 

Cikin kulawa yace.

“Lfya lau Alhamdulillah ya gajiyan aiyuka”.

Alhamdulillah tace kanta a sunkuye.

Kofar fita ya nufa.

Ita kuwa da sauri ta nufi.

Kitchine jin gidan ya kacame da kanshi Mamy nata hidima.

“Barka da safiya Mamy”.

Ta faɗa tana shigowa Kitchen din.

Da sauri Mamy ta juyo tare da cewa.

“Barka dai Jannart kin fito”.

Matsowa tayi tana cewa.

“Eh Mamy kawo in karɓa miki aikin”.

Ta ida mgnar tana son amsar ludayen.

Da sauri Mamy tace.

“A’a bari ma ai na gama ma”.

Toh tace tana ɗan matsawa tare da cewa.

“Mamy ya lbrin mai jiki?”.

Da sauri ta juyo tare da cewa.

“A’a na mancema ai sun iso jiya da dare.

Maza haura yana ɗakinsa jeki dubashi da jikin ko”.

Cikin yin ƙasa da kai tace.

“Ayyah ashe sun dawo”.

”Eh wlh kusan ƙarfe ɗaya suka shigo shiyasa ban gaya miki ba.”

Cewar Mamy.

Ita kuwa Jannart

“Ayyah”. Tace tare da tsayuwa.

Ramadan ne ya leƙo Kitchen din tare da cewa.

“Mamy Hamma Rayyern yace tea yake so. Akai mishi tun ɗazu ya gayawa Abba”.

Da sauri Mamyn tace.

“Toh ban saniba, Abbanku woje yayi da sauri”.

“Toh kawo in kai mishi, inaga ya mantane”.

“A’a bari ga matarsa zata kai mishi”

Mamy ta faɗa tana hada kayan tea ɗin akan tray’n.

Shi kuwa Ramadan juyawa yayi tare da cewa.

“Toh bari inje wurin Abba da P.A zamu wuce kai kayan campany”.

Sai kun dawo tayi musu tana mai mikowa Jannart ɗan madaidicin tray’n datasa komai a kai.

Amsar tray’n tayi cikin sanyi tace.

“Mamy ban san dakin shiba ai”.

Ta faɗa tanajin zuciyarta na harbawa.

Ita kuwa Mamy ba tare da ta kalleta ba tace.

“Kina haurawa sama na gefen dama shine ɗakinsa na hagu na Ramadan.

Kiyi maza ki kai mishi”.

Ta ƙare mgnar tana kallonta hakan ne yasa.

Ta juya a hankali ta fita Kitchen.

Tsakiyar falon ta fito tare da nufan steps din a hankali take daga kafafunta.

Haka nan taji zuciyarta na harbawa da sauri-sauri, lokacin da ta daura ƙafarta kan step din forko.

Tunda tazo gidan yanzu kusan kimanin watanni biyu cur harda kwanaki, ƙafarta bai taɓa taka wurinba.

Bare ta haura saman, da sauri ta juyo jin muryar Mamy na cewa.

“A’a Jannart me kike jira, kiyi maza ki kaimashi.”

Da sauri tace. 

“Toh”.

Kana ta fara tattakawan a hankali.

Shi kuwa Rayyern fitowar shi daga wonka kenan.

Dan Abba ya hada masa ruwan wonka kenan ya fita.

A hankali ya matso gaban gadon shi.

Kayan da yasa Ramadan ya ciro mishi ya kalla.

Wani singlet ne mai faɗin hannu fara ƙal mai masifar taushi.

Daga gefen damanta kan kirjin da al’jihun.

Sai kuma wondonshi wanda bazai wuce masa iya guiwa ba.

A hankali ya ɗan sunkuyo ya zauna sabida yar tafiyar da yayin yaji ya gaji.

A hankali ya ware wondon tare dasa  kafafunsa yana daga zaunen.

Cikin tattaro sauran ƙarfinshi ya yunƙura ya taso.

Tare dasa hannunsa daya ya ware towel din dake daure, a kugunsa ya fadi ƙasa, hakan yasa yatsaya ba komai a jikinsa.

Sai gajeren wondon da yake dai-dai kan guiwarsa, bai jawoshi zuwa sama ya suturce shi ba.

Dai-dai lokacin kuma Jannart ta turo ƙ…!

Back to top button