Uncategorized

Tubali Book 2 Page 13 Complete Novel

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

END OF BOOK 2

Ta faɗa kanshi. Da sauri yaja sassayan numfashi tare da rumtse idanunsa.

Hannunsa na dama yasa ya tallabe da sauri dan tana gab da suɓucewa tayi ƙasa.

Kan ƙirjinta ya maidata tare da sauƙe numfashi kana ya ruggume ta tsam-tsam a jikinsa, yana mai jin ɗumin numfashinta a wuyansa,

Yayinda tudun Caɓɓullenta suke tsukar ƙirjinsa wanda hakan yasa tsikar jikinsa mimmiƙewa.

Cikin yanayin gigin bacci da mayen allurar da rashin sanin indama take tace.

“A’a nidai gaskiya saidai mu kwanta ahaka, muyi kaida k’afa, kuma karka yi wayo ka motsa.”

Takare maganan tana turo  bakinta gaba, tare kuma da gyara kwanciyarta a jikinsa da kyau,

“Oushhhhh, Jannnaaa”. Ya faɗa da narkekkiyar murya sabida yadda take mutsu-mutsun a jikinsa yasashi jin D dinsa tayi wani irin masifeffen harbawa wanda hakan yasashi ruggume t da ƙarfi tamkar zai maida ita cikin jikinsa,

har saida yaji taushin breast ɗinta suna ratsa kirjinsa.

Yayinda ita kuwa Jannart taji zafin matso mata tsayayyun Caɓɓullenta da basu taɓa fuskantar hakanba,

Cikin yanayin maganin baccin tace.

“Wahyyy Nono na zafi”.

Juya kansa yayi da kai tare dasa hannunsa ɗaya da yake tsuma a tsakiyarsu, murya can ƙasan maƙoshi a narke yace.

“Janna nawa nefa”.

Ya ƙare mgnar yana shafo ƙirjinta,

Cikin muryar maye tace.

“A’a wlh nono ne”.

Matseta da ƙarfin da yayine  yasa yin zillo tare da, zamewa daga jikinsa ta zauna gefensa baki ta tura tare da zuba mishi ido.

Shi kuwa Rayyern da sauri ya miƙa hannunsa zai kamota,  ya faɗin.

“Ai na sayesu tunda na biya sadaki”.

Da sauri ta kaucewa kamun da zaiyi mata, ta konta gefenshi, inda  kanta ta wurin sawunsa nasa kan ta wurin sawunta sabida bata da ƙarfin da zata iya gudu.

A rigingine ta kwanta ta kalli sama, wanda hakan ya bawa kirjinta daman bayyana. 

Cikin mayen bacci da allura tace.

“Uhhm, ni dai ka barmin abina”.

Rayyern kuwa jin abunda ta fad’ad’in ne yasa shi, bud’e idanunsa ahankali ya d’an kalleta.

Saidai tudun breast dinta basu bari ya ga full face nata ba.

Azahirin gaskiya shi maganganun nata ma, dariya suke basa saboda kallo d’aya zakayi mata, ka gane cewar abuge take sai dai gaba ɗaya tsikar jikinsa a tashe take jin maganganun nata yake tamkar dan motsa mishi sha’awarta takeyinsu. 

D’an janye idanunsa daga Kallon nata yayi, tare kuma da tashi ya dan jingina bayansa da jikin saman gadon sabida wani irin muƙa da D dinsa keyi, ƙamarsa ɗaya ya ɗaura kan ɗaya, ya dannesa wai ko zai ji sauƙi.

Da sauri kuma ya jawo laptop d’insa dake gefen gadon, inda ya d’aura akan cinyarsa, wai  duk dan ya danneta ya hanata fitowa kwaɗayin.

Kawai sai ya fara lallatsa system ɗin wai ko zai samu hankalinsa ya bar kanta, dan

Akwai aikin da ya kamata ace ya kammala tukunna.

Cikin Sa’a kuma ya fara yin control ɗin abin duniyan.

Anutse yake duba laptop din nasa.

Jannart kuwa Acan cikin baccin nata, cike da karfin allurar da kuma raunin ciwo.

“Naaaan.”

Takira sunansa da wata irin muryar dake bayyana mayen baccinta.

yanayin yanda yaji sautin muryar nata ne kuma, yasa shi lumshe idanunsa saboda wani irin abu da yaji acikin jikinsa.

“Ummm.”

Ya amsa mata murya asanyaye, batare kuma daya bud’e idanunsa ba.

“Naaaaan..”

Ta sake kiran sunan nasa, saidai awannan karon taja harafin dake karshen sunan nasa, cikin yanayi na d’an kasala.

“Ummm Janna!”

Ya fad’a shima asanyaye tare da bud’e idanunsa, ya sauk’esu akanta. 

Sanin da yayi kuma cewar tana cikin mayen bacci, shiyasa bai tambayesa meye ba’asin kiran sunan nasa da tayi ba.

Saidai zubawa kyawawan Lips dinta idanu da yayi, kasancewar kuma d’akin ya d’au shiru sosai ne, yasa shi jiyo sautin numfarfashin, da take fitarwa slowly kana a hankali tace. 

“Naan nono yana ƙaiƙayi sosa meeeeeeen”.

Wani irin masifeffen harbawa yaji Naan ɗinsa tayi, yarrr-yarrr haka yaji tsikar jikinsa na miƙewa.

Da sauri ya sunkuyo kanta,

Sai kuma yaga taja wani narkekken numfashi tare da ci gaba da baccinta.

“Ya Salam Janna zaki kasheni”.

Ya faɗa saman lips ɗinshi.

D’auke kansa daga Kallon nata yayi tare da kife kansa bisa guiwowinsa a ƙalla 5 minute kafin ya sauƙe numfashi tare da maida hankalinsa ga aikin da yakeyi.

Saidai ba’aje ko inaba ya fara jin kansa acikin wata sabuwar duniya ta daban,  badon komai ba kuma saidan numfashinta, da yakejin yana sauk’a atsakiyar tafin k’afansa da kuma kalamanta na mayi da tayi ta masa.  

Hakan yasa sosai tsikar jikinsa suka soma tashi, Ganin bazai iya aikin bane kuma yasa, ahankali ya rufe laptop d’in nasa, tare da ajiyesa akan bedside drawer. 

A d’an kasalance ya zame hade da kwantar da bayansa akan gadon.

Cikin sanyi ya kuma lumshe idanunsa.

Tare da soma shak’an daddad’an kamshin jikinta dake tashi acikin dakin. 

Bazaice bayajin dadin yanda d’umin numfashin nata ke dukan k’afansa ba,  musamman yanda ayanzun yaji wani abu mai kama da nutsuwa, na shiga cikin jikinsa.

Duk da yanda yakejin wani irin acikin jikinsa kuwa, bayajin zai iya janye k’afarsa, saboda daga wani sashi na jikinsa, yana jin dadin hakan.

Sunanan ahaka kuwa wani bacci mai d’an nauyi ya fusgesa.

Almost 40mn da kwanciyar nasu ne kuma, Jannart din ta soma fitar da wani irin numfashi.

Wanda kuma hakan bai rasa nasa ba, da rufe jikinta da blanket d’insa da tayi, wanda yake da matuk’ar kamshi.

So kamshin da ta shak’a d’inne Yayi mata yawa, hakan yasa numfashinta soma yankewa.

Acikin baccin nata ne kuma, jin numfashinta na kokarin kwacewa yasa, ta soma kiran sunansa batare da ta bud’e Idanunta ba.

“Naan! Naan!….”

Take fad’a cikin sarkewar murya.

Shikuwa Rayyern acikin baccin nasa, ya jiyo sautin muryarta wanda hakan yasa shi bud’e, idanunsa ahankali kuma ya mik’e zaune.

Ganin bata bude Idanunta bane kuma, yasa shi sanya hannunsa ya d’anja yatsun k’afarta.

Cikin wata irin sassanyar murya yace.

“Janna na meye ne?”

“Numfashina ne zai d’auke.”

Ta fad’a ad’an wahalce tare kuma da bud’e bakinta, tana shak’an numfashin tanan. 

Rayyern kuwa idanunsa ya d’an zuba mata, na y’an wasu mintuna. 

Kana ahankali ya dan matsa tare da jawo, magungunanta dake gefen gadon. 

 

D’aya daga cikin alluran ya d’auko, tare da zuk’an ruwan alluran acikin sirinji. 

Bayan ya kammala komai ne kuma, ya juyo ya kalleta.

Dai-dai lokacin kuma tasa hannayenta ta rik’e wuyanta, again batare da ta bud’e Idanunta ba tace.

“Naan da gaske numfashina zai sake d’aukewa, wayyo Allah nikamma mutuwa zanyi.”

Ta k’are maganan cikin rawar murya.

Ganin hakanne kuma yasa Rayyern din matsowa kusa da ita, ahankali yasa hannunsa ya shafa gefen fuskarta, cikin tausasa murya da kuma lallashi yace.

“Noo bazaki mutu a Janna in kin mutu da waye Naan dinki zai rayu.

Tashi ko zanyi miki allura, daga haka bazaki sakejin d’aukewar numfashi ba.”

Fuskarta ta shagwab’e, saboda Jin abunda ya fad’a cikin kuma kasala, da turjiya tace.

“Allura kuma Naan? .”

Idanunsa ya zuba mata, Ganin da gaske take bata son alluran, ga kuma yanda numfashinta ke d’aukewa ne, yasa shi sanya hannayensa duka biyu, ya tada ita zaune.

 Ta da’itan da yayi ne kuma yasa tayi saurin bude Idanunta, tare da narkar da kanta ashagwab’e tace.

“Please Naan karkayi min allura, Allah nasan numfashin ma zai dai-dai-ta da kanshi duvet d’inka ne keda kamshi sosai in na yayeshi zanji sauk’i.”

Ta kare maganan tana me d’an yayyafa yatsun hannunta, Rayyern kuwa sanin batason alluran ne yasa shi, matsowa kusa da ita tare da kamo hannunta, Cikin kulawa yace.

“Calm down Jannart, dole fa sainayi miki alluran, Idan kuma baki tsayaba kinsan zata iya karyewa a jikinki.”

Idanunta ta rumtse da k’arfi tare kuma da soma jan jikinta baya, wanda  da alamu so takeyi ta gudu.

Fahimtar hakan da yayi dinne kuma yasa shi, fusgota tare da jawota ta fad’a jikinsa. 

Batare da tunanin komai ba kuma, ya rungume ta tsam ajikinsa. 

Hade da kama d’ayan hannun nata, ya rik’e da kyau, kana ya dai-dai-ta zaman alluran dake hannunsa. 

Jannart kam Idanunta ta kuma rumtsewa, tare da manna kanta akan shoulder d’insa, cikin rauni da magagin baccin  had’i da, yanayin korafi  daya k’wace mata murya can k’asa-k’asa tace.

“Nidai ka sakeni, ka k’yaleni banason alluran, kuma babu ruwana dakai, tunda mukazo kakeyimin abubuwa kala kala, kace min bani da Baba, still kuma kace wai bani da Yaya, shine yanzu kuma kazo zakayi tamin allura bayan kuma nacema Abbana ya hana sabida allurar k’ara ciwon takeyi, nidai ka sakeni.”

Ta k’are maganan cikin kuka, like yarinya Y’ar 10years ko k’asa da haka. 

Rayyern kuwa duk da yaji abunda take fad’a d’in, bai saurareta ba, saima sake rik’eta da kyau da yayi, atsanake ya soka mata alluran akan dantsen hannunta.

Razanannen k’ara ta saka masa, adaidai lokacin da taji zafi da kuma radad’in alluran na ratsa cikin jikinta. 

Shi kuwa Rayyern cikin wata iriyar fitinenneyar murya yace.

“Bazan sakeki ba Janna har gaban abadan bazan sakeki ba”.

Lokaci d’aya kuma ta saka masa kuka, tare da soma d’an bugun kirjinsa da d’ayan hannunta dan dama hannun Rayyern nada zafin allura sosai.

Cikin kuka kuma take cewa.

“Wayyo Allah zafi! zafi!! zafi!!! Naan banaso ka cire Naan ka zare minshi a hankali dan Allah.”

Duk da cewar yanajin kukan nata wani iri kalamanta kuma sunfi kama da masu motsa fileengs, acikin kunnuwansa amma haka ya daure, saida ya kammala shigar da ruwan alluran jikinta, kafun ya zare alluran.

Jin bata daina kukan bane kuma yasa shi, d’aura yatsun hannunsa adai-dai inda yayi mata alluran, Cikin kulawa da kuma sigar lallashi, ya soma shafa dai-dai wajen da yayi mata alluran.

Hakan da yakeyi mata dinne kuma, yasa ta jin tamkar sosa mata wajen yakeyi, wanda kuma hakan ya d’anyi mata dad’i. 

Atsanake kuma cikin sanyi ta manna kanta, akan kirjinsa tare kuma da lumshe Idanunta, anutse take sauraran bugun zuciyarsa. 

Saidai har yanzu Cikin yanayin shagwab’a take sakin sheshshek’an kuka, kana kuma cikin rawar muryar, dake bayyana har yanzu a buge take  tace.

“Ni bazan sake zuwa dakin nan ba, kuma ma kaji ka sani ni ina da Babana, karka sake cewa bani da baba, kuma bazan sake yarda kamin alluranka mai zafi ba.”

   

shikuwa Rayyern jin hakanne yasa shi, lumshe Idanunsa tare da sake jawo blanket ya rufa mata daga shoulders dinta zuwa k’asanta.

Murya asanyaye kuma cikin yanayi mai kama da rad’a yace.

“Allura mai zafi ko ai bazaki tsira da itaba yarinya uwar raki kawai”.

Ya k’are mgnar yana ruggume ta tsam a jikinsa, tare da fesar da sassayan numfashin murya a narke kamar cikin rad’a yace.

“Janna waye ne Abdulkarim Saleh Dakata?”

Jin tambayan da yayi mata d’inne kuma, yasa k’ara ta mannewa jikinsa sabida k’arfin alluran, still asanyaye tace.

“Baffana ne k’anin Dadyna mamansu da Babansu d’aya, amma ya rasu tunda jimawa.”

Ta fad’a tana meyin rau-rau da Idanunta wanda suke tsiyayar hawaye.

Rayyern kuwa ahankali ya d’aura hannayensa akan bayanta, tare da sake shigar da ita cikin jikinsa ya zab’i ya tambayeta yanzune da take cikin yanayi mayen bacci yasan zata iya gaya mishi komai koda ko bata son fad’an tunda gashi tana sake mishi wasu zantuka masu nauyima a kyauta.

Again cikin tausasa murya yace.

“Ayyah Allah Yajikansa da rahama yasa ya huta.”

“Amin.”

Ta amsa tana mai lumshe ido.

Yayinda takejin kasala da kuma bacci na dad’a sauk’o mata. 

Rayyern ko ahankali ya d’aura hab’arsa akanta, Cikin nutsuwa ya lumshe idanunsa, saboda daddad’an kamshin gashinta daya shak’a, ahankali kuma ya k’ira sunanta.

“Janna”

“Uhummm.”

Ta amsa masa tana me sake dai-dai-ta kunnenta, adai-dai saitin bugun zuciyarsa da takejin tana bada sauti dib-dab.

“Kinayiwa Baffan naki addu’a kuwa kullum Idan kinyi sallah?”

Rayyern din ya tambaya, yana me yawo da yatsun hannunsa akan dantsen hannunta. 

Shiru ta d’anyi kana asanyaye tace.

“Ummm inayi.”

“k’arya kikeyi nasani bakya yi, Idan kuma kina yi to kiyi rantsuwa da Allah.”

Rayyern din ya fad’a kaitsaye, saboda sam baiji ajikinsa cewar tanayi dinba.  

Jin abunda yace dinne kuma yasa Jannart din, b’oye fuskanta  cike da magagin bacci tace.

“To ai sai wataran wataran nakeyi.”

Murmushin gefen baki ya d’anyi, tare da sake lumshe idanunsa, saboda already yasan batayi, wannan dalilin yasa tanayi masa k’arya ya gane.

Ajiyar zuciya ya d’an sauk’e Cikin kulawa da tsananin rauni da tausayinta da tauye zamowarta ɗiya mai tunawa da iyayen da aka ɓoye mata asalinsu  cikin tausasa murya yace.

“Ok naji amma kinayi mishi addu’a akullum kinji, yana da y’ay’a ne?”

Kanta ta girgiza masa batare kuma da ta d’ago ta kallesa ba tace.

“A’a bashi da y’ay’a rana d’aya ya rasu da matarsa ita a wurin haihuwa ta rasu.”

Kansa ya d’an jinjina kana cikin nazartar wani abu yace.

Haka nan yaji wasu irin zafafan hawaye suna tsastsafo masa.

“To Meyasa ke bazaki zame musu madadin Y’a ba, ta hanyar yi musu addu’a, Zaije ya iskesu har cikin kabarinsu.”

Cikin sanyin jiki tace.

“Zannayi insha Allah, amma waya baka labarinsu?”

Ta fad’i hakan tana me d’ago Kanta ta kalleshi.

“Ba bani labarinsu akayiba.”

Ya fad’i hakan atak’aice.

Jin hakanne kuma yasa Jannart din sake kallonsa, asanyaye tace.

“nasan ai baka sansu ba, Abba Kabir dinane ya baka labarinsu?”

Kansa ya girgiza alaman a’a, Cikin nutsuwa da kuma sanyin murya yace.

“Ko d’aya, amma kinsan sunan matar tasa ne?”

Kanta ta jinjina alaman eh, kana kuma cikin yin kasa da Kai tace.

“Nasan dai Abba Kabir yana kiranta da suna Aunty Zee, inaga Zainab shine sunanta na gaskiya, kuma Abba Kabir yana cewa tana da kirki sosai, kirkinta wai yafi na kowacce Mace a Family dinmu wai haƙurina irin natane.”

Bakinta dake motsi ya kalla kana ya d’an jinjina kansa, 

Cikin wani irin raunin da ya samu kansa aciki, hadi da karyewar zuciya ya sake hugging dinta, ahankali yace.

“Kinyi al’kawari zakina yi musu addu’a ko?”

“Eh.” Ta fada tane me lumshe gajiyayyun Idanunta, wanda basu da maraba dana y’an shaye shaye.

Rayyern kuwa gyara zamansa yayi, tare da sanya hannayensa duka ya d’agota, wanda hakan yasa suka zamana suna facing d’in juna. 

Idanunta dake ta lumshewa ya kalla da kyau, fahimtar da yayi cewar ta fara tafiya wata duniyar ne kuma, yasa shi d’an zamewa gefe wanda hakan ya bata daman kwanciya. 

Gyara mata blanket din dake jikinta yayi, ahankali kuma cikin kulawa ya haura can saman gadon shima ya kwanta.

Ita bacci ya fara d’auka kafun daga bisani, shima bacci ya daukesa.

3:00pm.

Bud’e idanunsa yayi ahankali kuma yake ambaton sunan Allah, tare dayin mik’a ya tashi ya zauna.

Jannart din dake kwance tana bacci ya kalla,  ganin yanda take ta sakin Ajiyar zuciya ne kuma, yasa shi sauka daga kan gadon, kaitsaye ya wuce bathroom.

Yana shiga kuwa ya sakarwa kansa ruwa, bayan yayi wankanne kuma ya had’a da al’wala.

Yana cikin wakanne kuma Jannart ta bud’e Idanunta, saboda tun tashinsa dama itama ta farka.

Jin motsinsa acikin toilet ne kuma yasa ta, yunkurawa ahankali ta zauna akan gadon.

Rayyern kuwa ahankali ya turo kofar bathroom din ya fito, jikinsa sanye da rigar wanka.

Yana gama fitowa kuwa ya sauke idanunsa akan gadon,  Ganin Jannart din da yayi zaune atsakiyar gadon ne, kuma yasa shi yin mamaki saboda bai kawo aransa cewar, zuwa yanzu zata tashi daga baccin ba. 

Idanunsa ya d’an zuba mata, ahankali kuma yana me goge jik’akk’en kansa da towel yace.

“Akwai ruwan zafi a bath kije kiyi wanka, Idan kinfito sai kiyi lunch, oya weck up.”

Ya fad’a yana me karasawa gaban dressing mirror. 

Jannart kuwa kasancewar bata wani jin karfin jikinta sosai, shiyasa bata musa masa ba. 

Ahankali ta sauko daga kan gadon, tare da wucewa toilet, 

Tana shiga kuwa ta cire kayan jikinta. 

Hade da shigowa cikin bathtub din wankan ta kwanta.

Saboda kamshi da kuma dumin ruwanne, yasa ta soma sauke ajiyar zuciya akai akai.

Tana nan ahaka har wajen mintuna 10, kafun tayi wanka tare dayin al’wala. 

Bayan ta kammala ne kuma ta rasa, ta yanda zata maida kayan da ta cire, saboda tun jiya da safe sune a jikinta.

Ganin bathrobe d’insa da tayi akan karfen shower ne, kuma yasa ta d’auka tare da zurawa ajikinta, take kuwa ya sauko mata har sama da guiwowinta.

Ahankali ta bud’e kofar toilet din ta fito,  dai-dai lokacin shi kuma tuni ya gama kimtsa Kansa, cikin wasu had’add’en riga da wando.

Jin motsin fitowarta ne kuma yasa shi, dago kansa ya kalleta.

Gani yayi ta nufi hanyar fita daga dakin nasa, saidai bai tanka mata ba, har saida ta fice kuwa kafun ya d’auke idanunsa daga kallonta.

Ad’an k’agauce ya shumfud’a sallaya, tare da tada sallan azahar, Dan da d’an saura kafun akira sallan la’asar. 

Bayan ya idar da sallan ne kuma ya zauna, akan sallayan Yana nan zaune kuma har aka kira sallan la’asar din, hakan yasa batare daya jinkirta ba, ya tashi yayi sallah.

Bayan ya idar da sallan ne kuma yayi musu, ordern abinci. 

Acan b’angaren Jannart kuwa Koda ta shiga bedroom dinta, kaya ta saka ajikinta wani doguwar riga, irin marar nauyin nan ta saka, kasancewar kuma bata saka bra bane, yasa tsayayyun breast dinta bayyana, hatta nipples dinta kuwa ana iya Ganin shatinsa. 

Dogon hijab ta saka kana ta tada sallah, azahar tayi bayan ta idar ne kuma tayi la’asar. 

Azahar da kuma addu’o’i tayi kana ta Mike tsaye, bayan ta zare hijab din dake jikinta.

Kaitsaye ta nufi gaban mirror, dai-dai lokacin kuma Rayyern din ya bud’e kofar dakin ya shigo.

Jin motsinsa ne kuma yasa ta juyowa da sauri. 

Ganinsa da tayi dinne kuma yasa ta Dan soma takowa, wanda hakan ya bashi daman sauke ganinsa, akan tsayayyun breast dinta, wanda suka tsaya cur kaman zasu tsole idanunsa.

   Saurin janye idanunsa daga kallonta yayi, tare da d’an yin kasa da kansa, hakanan yaji tsikar jikinsa na mimmikewa rumtse idanunshi yayi da k’arfi. 

Jannart kuwa batare da ta fahimci abunda idanunsa suka kalla ba, ad’an shagwab’e tace.

“Naan lafiya?”

A hankali ya d’an kalleta ido a narke yace.

“Pleess Janna ki dena tsolemin idanu”.

Da sauri ta kalleshi tare da cewa.

“Na tsole maka ido kuma!?”.

Tamkar yaro k’arami haka ya gyad’a mata kai tamkar zaiyi kuka,

Ciki da mamaki tace.

“Toh ni kuma yaushe na tsole maka ido kuma da me!?”.

A hankali ya zubawa k’irjinta idanu,

ganin inda yake lallone yasa itama ta kalli wurin da sauri ta kuma kallonsa sai taga kuma ya longoɓar da kansa bisa kafaɗarsa murya a narke ido shanye yace.

“Muje kici abinci.”

Ya fad’a cikin yin k’asa da murya, batare kuma daya sake kallonta ba, saboda duk kallo daya da zaiyiwa kirjin nata, sai yaji duk tsikar jikinsa ya tashi zuwa yanzu ya fahimci akwai wani abu na musamman a jikin  fitinenneyar yarinyar nan. 

 

Batare daya sake ce mata komai ba, kuma ya juya ya fita, yana fita din kuma ta rufa masa baya, kasancewar ita dinma yunwa takeji. 

Koda suka fito falon, kaitsaye kitchine ya wuce ya d’auko plate, Yayinda ita kuwa Jannart din ta zauna akan daya daga cikin kujerun falon.  

Abincin ya zuba mata acikin plate, tare da turo mata gabanta. 

“Kici.”

Ya fada anutse tare da ajiye mata fork din dake hannunsa.

D’an kallonsa tayi ashagwab’e, kamar zata ce wani abu kuma saita fasa, spoon ta d’auka tare dasaka abincin a bakinta taso ma ci.

Saida yaga ta danci da yawa kafun ya d’ago idanunsa ya kalleta.

“Ya jikin naki.”

Ya fad’a adai-dai lokacin da yake Kallon yanda d’an karamin bakinta ke motsawa. 

“Da sauki sosai.”

Ta bashi amsa, tana me ture plate din abincin daga gabanta, saboda ji da tayi ta koshi.  

Shikuwa Rayyern Ganin hakanne yasa shi, b’allan magani ya bata.

Fuska ab’ace kamar Wacce zatayi kuka haka ta karb’i magungunan tasha.

Bayan tasha maganinne kuma ta zame ta kwanta, akan kujera 3seater.

Yayinda Rayyern kuwa ragowar abincin nata ya dauka ya soma ci.

Anutse take karewa kyakkyawar halittarsa kallo, domin kuwa komai nasa gwanin burgewa ne, musamman yalwataccen sajen dake kwance akan fuskarsa.

Idanunta ta lumshe tare da soma sakin Ajiyar zuciya. 

*Nigeria.*

Ramadan da kuma Mamy ne ke zaune acikin babban falon gidan nasu, kasancewar yanzu dawo wansa daga wajen aiki ne kuma, yasa Mamyn Zubo masa abinci.

Har yakai loman farko na abincin bakinsa ne kuma, ya juyo ya kalli Mamyn kana cikin tausasa murya yace.

“Mamy Jannart fa bata da lafiya, jiya da dare hamma Rayyern ke gaya min, wai asthma dinta ne ya tashi har Hospital ma sukaje.”

Da sauri Mamy ta d’ago ta kallesa, cikin damuwa da jin abunda ya fad’ad’in tace.

“Subahanallah Jannart bata da lafiya, kuma shine Ramadan ka sani amma baka fadamin ba sai yanzu?”

“Kiyi hakuri Mamy wallahi jiya wajajen karfe 12 na dare Hamma Rayyern yake sanarmin, kasancewar naga dare yayi sosai ne kuma yasa ban  kira na sanar daku ba, amma yau da safe ma munyi waya, kuma Hamma Rayyern yace jikin nata da sauki, har an sallamosu ma.”  

Ramadan din ya fada cikin son kwantarwa da Mamyn hankali.

“Allah sarki Jannart baiwar Allah, dama tana da asthma ashe bamu da labari, maza kiramin su naji yaya jikin nata yanzu.”

Mamy ta fad’i haka cikin alhini da kuma tsananin tausayawa ya Jannart din. 

Ramadan kuwa atake yayi dialing numbern Rayyern din, wanda kuma yasan ayanzu Jannart dinne ke using dashi.

Cikin sa’a kuwa kiran ya shiga.

Adai-dai lokacin kuwa Rayyern dinne, zaune afalo wanda ya tankwashe kafafunsa,  Yayinda Jannart kuwa ke gefensa, tana ta wasa da wani chain dake hannunta.

Jin alamun shigowar kira a Y’ar k’aramar wayan dake gefenta ne kuma, yasa ta d’an yunkurowa ta tashi, tare dakai dubanta ga screen din wayar.

Sunan Ramadan da tagani b’aro b’aro akan screen din wayarne, kuma yasa ta d’agawa tare da kara wayar akan kunnenta.

“Ramadan.”

Ta kira sunan Ramadan din cikin sakin fuska.

Ramadan kuwa jin itace akan layin yasa shi, Dan sakin murmushi Cikin kulawa yace.

“My Aunty ya jikin naki? Allah yasa kin warware kinyi karfi sosai ta yanda zaki iya wasan tsere.”

Murmushi mai hade da dariya tayi, wanda hakan yasa Rayyern dago kansa ya kalleta.

Itakuwa cikin sakin fuska tace.

“Eh mana naji sauki sosai Ramadan, yasu Mamy da Abba.”

“Duk Suna lafiya ga Mamy din nan ma zaku gaisa.”

Ya fadi haka yana me mikawa Mamy wayan.

Mamy ko da sauri ta amsa tare da kara wayar akan kunnenta, Cikin kulawa tace.

“Jannart ya jikin naki, ashe wai bakiji dadi ba.”

“Mamy jikina da sauki sosai, nama warware.”

Jannart din ta fad’a cikin tausasa murya.

“Ayyah sannu Jannart Allah Ya kara sauki, yasa zakkan jiki ne ashe kina da asthma kwata kwata ai bamu sani ba, sannu ko asthma bata da dadi Idan ta tashi.”

Mamyn ta fad’a Cikin kulawa.

Jannart din kuwa da “Amin.”

Ta amsa kana, sukayi sallama da Mamyn. 

Mikawa Ramadan din wayar Mamy tayi, shikuwa kasancewar ya kammala cin abincin nasa ne, yasa shi mikewa tsaye. 

“Ramadan.”

Mamy ta kira sunansa cikin kulawa, wanda hakan yasa shi juyowa ya kalleta, tare kuma da d’an rusunawa yace.

“Na’am Mamy.”

Gyara zama Mamyn ta d’anyi, kana Cikin kulawa da kuma tausasa murya tace.

“Abbanku yace na fad’a maka sunkai sadaki gidansu Rayhanna jiya, yace yayi hakanne kuma saboda yaga Kai hankalin ka, yafi karkata akan batun had’a lefe.”

Da sauri Ramadan din ya karaso gaban Mamyn, cikin wani irin tsananin farinciki dajin dadi yace.

“Alhamdulillah Mamy na, Abba ya kaimin sadaki wayyo Allah na nawa aka kai?”

Ya tambaya cikin zumudi da kuma tarin farincikinsa, wanda ya kasa b’uya. 

Mamy kuwa Ganin hakanne yasa ta girgiza kanta, fuskarta dauke da murmushi tace.

“Nima bansani ba saidai kaje ka tambayeshi, tunda naga alamun ba kunya ne dakai ba.”

Dariya Ramadan din yayi, kana cikin tsananin farinciki ya juya da hanzari ya haye sama.

Yana shiga bedroom d’insa kuwa, kiran Riyyam nsra na shigowa. 

Da sauri ya d’aga wayan ko gaisuwar da Riyyam din keyi masa kuwa bai amsa ba, cikin zumudi yace.

“Riyyam Alhamdulillah nakusa aure, ka shirya zuwa biki nanda 2month, jiya su Abba sunkaimin sadaki.”

“Yehhhhh zata fashe zamusha biki, wayyo Allah Nigeria zan dawo cikinki soon, congratulation Hamma Ramadan, naji dadi sosai tun yanzu ma zan fara shirye shiryen biki.”

Dariya sosai Ramadan yayi, cike da farinciki kuma haka suka ci gaba da  hiransu. 

Acan Mascow kuwa Jannart tana kashe wayan, komawa tayi ta kwanta, tare kuma da lumshe Idanunta saboda wani Dan bacci da takeji.

Rayyern kuwa dake zaune wayarsa ya ciro, tare da dannawa lamban Baba Maud’o kira.

Bugu biyu kuwa Baba Maud’on ya d’aga.

Bayan sun gaisa ne kuma Baba  Maud’on yake tambayarsa ya Jannart.

Ahankali ya d’an juyo ya kalleta, Ganin Idanunta alumshe ne kuma yasa shi dan tausasa murya kana yace.

“Gata nan Baba Maud’o amma itama bata ji dad’i ba, ashe tana da asthma to shine jiya da muka fita asthman nata ya tashi.”

“Subahanallah Allah ya kara sauki, yasa zakkan  jikine, bani ita nayi mata sannu da jiki.”

Baba Maud’on ya fad’a cikin kulawa.

Rayyern kuwa atake ya mik’awa Jannart din wayan.

Da sauri ta amsa tare da karawa akan kunnenta, cikin sakin fuska da kuma girmamawa tace.

“Ina kwana Baba Maud’o.”

“Lafiya kalau ɗiya ta Jannart ya jikin naki?”

Baba Maud’o ya tambaya Cikin kulawa.

“Da sauki sosai Baba, nama warware yanzu babu abunda yake damuna.”

“Masha Allah haka akeso ai, To Allah ya kara lafiya Jannart.”

“Amin nagode sosai Baba Maud’o Allah ya saka da alkhairi.”

Ta fad’i hakan cikin tausasa murya.

Daga haka kuma sukayi sallama da Baba Maud’on, ta mikawa Rayyern din wayarsa. 

Ganin irin Kallon da yakeyi mata ne kuma, yasa ta maida Idanunta ta lumshe.

Tare kuma dajin wani irin sanyi acikin zuciyarta. 

Rayyern kuwa laptop d’insa ya dauka yasoma latsawa, Suna nan ahaka kuma har lokacin sallan Magriba yayi.

Bayan ya sake dan tsakalan abincin da yayi musu order ne kuma ya wuce

Bedroom d’insa ya tare da yin al’wala, kana yazo ya tafi masallaci. 

Yayinda ita kuwa Jannart tuni ta shiga nata dakin itama tayi al’wala tare da tada sallah.

Kamar Koda yaushe kuwa baidawo Cikin gidan ba, saida akayi sallan isha.

Kasancewar ana sanyi sosai ne kuma, yasa bai wani jima awajen ba ya dawo.

Ganin bata falonne kuma yasa shi wucewa bedroom d’insa,  wanka yayi tare kuma da kimtsa kansa cikin wasu kayan bacci masu taushin gaske. 

Harya d’an kwanta kuma saiya tuna da cewar, Jannart din bata sha magani ta na dare ba.

Hakan yasa shi saukowa daga kan gadon, kaitsaye ya nufi falo, inda ya ajiye maganin ya nufa, bayan ya dauka ne kuma ya nufi d’akinta kaitsaye hannunsa rike da flat din pepper soup.

Ahankali ya turo k’ofar dakin ya shiga bakinsa dauke da sallama.

Dai-dai lokacin kuwa Jannart din tsaye, take agaban mirror tana shafawa jikinta turare, Yayinda take  sanye da wani riga da wando na bacci.

Wanda kwata kwata tsayin wandon baiwuce guiwarta ba, sai kuma rigar da ta kasance Y’ar fingil, Wacce ta bayyana har saman mararta, da kuma breast dinta way’anda ba kullum ake sa musu bra ba.

Da sauri ya rumtse idanunsa tare da dafe kansa.

“Ya Salam wannan yarinyar zata juyamin tunani.”

Ya fad’a acikin zuciyarsa tare da cije lips d’insa, saboda wani irin abu da yaji yana tasomai tun daga kansa, har zuwa karkashin kafansa, Yayinda daga gefe guda kuwa yakejin wani abu na sukan Rayyern d’insa.

Jannart kuwa juyowa tayi ta kalleshi, saidai ganin hannunsa dauke da magunguna ne yasa ta, b’ata fuska tare da Dan karyar da wuyanta gefe, akasalance tace.

“Naan nifa banajin yunwa, kuma bana son magani, please ka bari saida safe kaji.”

Narkakkun idanunsa da suka soma sanja kala ya zuba mata, Yayinda yakejin Brain d’insa na kokarin hautsunewa. 

Ahankali kuma Cikin muryarsa da ta Dan shak’e yace.

“Kici abincin kadan sai kisha magani.”

Yakare maganan yana me karasa shigowa cikin dakin, tare da mika mata plate din abincin.

Haka badan taso ba ta danci abincin, bayan ta danci kadan ne kuma ya bata magungunan, idanunta rau rau haka tasha maganin.

Shikuwa Rayyern jingine jikinsa Yayinda gefen gadonta, tare da lumshe idanunsa.

Jannart din kuwa jin pepper soup din yayi mata dadi sosai ne, yasa ta maida hankali wajen cinsa.

Saida taci sosai kuma kafun ta ture abincin gefe.

Jin shiru babu motsin Rayyern dinne kuma yasa ta juyowa, ta kalli b’angaren da yake.

“Naan.”

Takira sunansa ashagwab’e. 

Saidai kuma jin shiru bai amsa ta bane,yasa ta Dan matsowa kusa dashi.

Ahankali kuma cikin sanyi

Ta sake cewa.

“Naan bacci kayi?”

Ta fadi maganan tana me Kallon, jajayen lips d’insa dake sheki, hadi da kwantattun gashin giransa. 

Wani irin masifaffen kyau taga yayi mata, wanda hakan yasa ta sake matsowa kusa dashi, har ya zamana suna jin numfashin juna.

Kasancewar atunaninta bacci yakeyi ne, yasa ahankali ta d’aura yatsanta adai-dai kan eyebrow d’insa, cike da shaukin hakan ta soma shafawa.

Tare kuma da d’an gangarowa zuwa kan, dogon hancin sa.

“Naan ka tashi kaji, kada kayi bacci anan ka tashi.”

Tayi maganan in a silent sound wanda hakan, yasa daddadan kamshin dake fita abakinta sauka akan fuskarsa. 

ahankali kuma batare da tunanin wani abu ba, ta sauko da hannunta, zuwa kan labbansa wanda suke matuk’ar burgeta.

Ahankali take shafa lips din nasa, tare da rausayar da kanta gefe.

Ganin yaki bude idanun nasa ne kuma, yasa ta turo dan karamin bakinta gaba.

Ashagwab’e kuma cikin kasala tace.

“Nidai gaskiya ka tashi min akan gado na, ai kaima kana da daki kaje can ka kwanta mana.”

Ta kare maganan cikin wani yanayin, da yasa tsikar jikinsa mimmikewa.

Musamman saboda abunda takeyi masa din, tuni ya jefasa acikin wata duniya na daban.

Dan har ji yake jijiyoyin jikinsa na harbawa.

Ahankali still batare daya bud’e idanunsa ba, yasanya hannayensa duka biyu ya janyota jikinsa. 

Tare da matseta akirjinsa har saida tayi kara. 

“Wai ke baki iya zama da kaya bane? Sai kiyi ta tsole min idanu da waɗannan abubuwan”.

Ya tambaya cikin wata irin muryarsa, Wacce take Acan kasan makoshi.

“Kamar yaya yanzu ba kaya bane ajikina.”Jannart din ta fada tana me turo bakinta gaba. Tare da soma yunkurin kwace kanta.

Hakan da takeyi din kuma shiya yasan, ya kara jin kansa awani irin yanayi.

A hankali yace.

“Koda yake kince sunayi miki ƙaiƙayi ko, yau dai bari na sosa miki su”.

Ya ƙare mgnar murya a fitine

Wanda hakan yasa ahankali ya zamar da ita gefensa, tare da mirginawa yayi mata rumfa da kirjinsa.

“Ahhhhhh.”

Ta fada ashagwabe tare da turo masa Dan karamin bakinta.

Shikuwa Rayyern Ahankali ya dan bud’e idanunsa wanda suka yi ja, cikin wani irin yanayin da yake ciki kuma, yaja wani irin sexual breath tare kuma da sauke, rikitattun  idanunsa masu dauke da tsananin sha’awa akan…….

Back to top button