Uncategorized

Tubali Book 2 Page 12 Complete Novel

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

Kamar jira yakeyi kuwa suna shiga cikin dakin, ya sake hannunta tare da turata gefe, Cikin yanayin b’acin rai da murtuk’e fuska yace.  

“Waye shi? Waye wancan  gardin da kika rungume, tell me wayeshi wanni d’an iska ne, da har kike had’a jikinki da nashi? Akanme zaki manna masa ƙirjinki mallakina a ƙirjinsa?”.

Ya k’are maganan cikin masifar tsawa Cikin fushi kuma da b’acin rai.

Jin ya kira Yah Azeez din da d’an iskane kuma, ya sata soma girgiza kanta, lokaci daya kuma cikin muryata da ta raunana sosai tace.

“Shifa ba d’an iska bane.”

“Ohhhh.”

Ya fada yana me kura mata idanu, tare kuma dasa hannayensa ya kama waist d’insa, cikin fushi yace.

“Da kikaje kika rungumesa, ya kwantar dake acikin jikinsa sadakin nawa ya biya aka d’aura muku aure? Waye shaidun ku!?”.

Da sauri ta fara jujjuya mishi kai hawaye na kwaranyo mata sam ta gaza cewa komai.

Shi kuwa Rayyern cikin takaici murya a sark’afe yace.

“Janna da aurena fa ya ruggumeki hakan shine ba iskanci ba kenan da aurena fa a kanki kefa matatace kika manna masa ƙirjinki a nasa Janna hakan dai-dai neeh.” 

Ya kare mgnar tamkar zaiyi kuka.

Saurin girgiza masa kai tayi, kana Cikin yanayin tsoro tsoro tace.

“Allah ba d’an iska bane Yayanah ne.”

“Karya kikeyi taya ya ya zama yayanki, a ina kuma yaushe har kike kiransa yayanki, kina da aure amma saboda rainin na barki kina abinda kikaga dama kinje kina runguman wani k’aton banza! Sabida na barki ko?”.

Ya kare maganan atsawace wanda har saida taji yay’an hanjin ta sun kad’a.

Hakanne kuma yasa cikin raunin da yafi kama da shogob’owa a wurin mai kallonta da sakalci tace.

“K’aton banza kuma?

 shifa ba k’aton banza bane, Allah Yaya nane Yah Azeez ne Babanmu d’aya dashi, shine  yayanmu na biyu fa dama yayi karatunsa anan kuma anan yake aiki, Allah ba karya bane kuma ma ka tambayesa kaji…”

Ta kare maganan da sigar dake bayyana tsananin yarintarta. 

Rayyern kuwa Harara ya watsa mata, cikin kuma tsareta da idanu yace.

“Da Allah rufemin baki ke kina da Yayane.”

Idanunta ta d’an zazzaro tare da kwato numfashinta, murya na rawa tace.

“Mekake nufi ni bani da Yaya kenan? ka tambaya mana kaji Babanmu d’aya dashi.” 

Ta fad’a tana me turo bakinta gaba. 

Shikuwa Rayyern cikin halin ko in kula yace.

“Shutup dama ke kina da Babane? Waye baban naki?”

Saurin d’agowa tayi ta kalleshi, lokaci d’aya kuma taji numfashinta na kokarin k’wacewa, saboda abunda ya fad’a d’in yasa, taji numfashinta na slowdown. 

Cikin yanayin rauni da kuma shagwab’ar dake damunta, kana cikin muryar kukan da yazo mata tace.

“Kamar ya zaka ce bani da Baba, wallahi ni dai inada Babana…”

Ta kare maganan tana me sakar masa kuka.

  Ganin hakanne kuma yasa Rayyern din had’e fuska, tare da gyara tsayuwarsa cikin murtuk’e fuska, da kuma razanannen tsawa yace.

“Kirufemin baki duk uba baya juran ganin ana cutar da d’iyarsa naki da kike zaton mahaifinkine akwai ayar tambaya a kansa na raunin jink’ai na iyaye.”

Da sauri ta rufe bakinta tare da had’iye kukan nata, wanda hakan yasa numfashinta wani irin fusga, har saida taji kanta na juyawa luuuu Kamar zata fad’i. 

Wani irin fusga ta soma yi da kirjinta, dan jawo numfashin nata dake kokarin kwacewa.

Shikuwa Rayyern saboda tsananin b’acin rai ko lura da hakan ma baiyi ba, juyawa yayi afusace ya nufi bedroom din dake cikin falon.

Shikansa ayau din baisan meya b’ata masa rai har haka ba, bai kuma san Meyasa zuciyarsa ke tafarfasa ba ya dai san tun ranar da yaga yadda Junaid na mata dukan mutuwa a gaban wanda take cewa mahaifinta bai kulaba yake da yak’in bai zama uban bad’ini ba kana in ya tuno yadda akayi aurensa da kalaman Barrister Kabir a lokuta ma-ban-ban-ta yakanji kansa na juyawa tabbas yasan akwai wani abu a k’asan tubalin wancan ahlin da take jin iyayenta ne.

Jannart kuwa Ganin ya wuce bedroom ne yasa ta, zama akan d’aya daga cikin kujerun falon, da sauri take maida numfashi, tare da rumtse idanunta.

Rayyern kuwa yana shiga bedroom din kayan dake jikinsa ya rage, tare da wucewa bathroom yayi wanka. 

Bayan ya fito awankanne kuma ya sake maida kayan daya cire din, batare kuma daya sake bi takan al’amuranta ba, ya hau saman bed ya kwanta.

Har yanzu kuwa jin zuciyarsa yakeyi babu dadi, b’acin rai tsantsane kawai ke tafiya masa ya zama dole su kwana a hotel sabida gudun kar har yanzu wancan na bibiyarsu…..

Jannart.

Ahankali take sake matse jikinta waje daya, saboda wani irin masifaffen sanyin da takeji, wanda yake kara sawa numfashinta na seizing. 

D’agowa tayi ta kalli agogon dake sak’ale ajikin bangon d’akin,  wanda yake nuna mata k’arfe d’aya na dare. 

Sake matse jikinta tayi tare da karyar da wuyanta gefe, tana me tunanin yanda zatayi ta kwana acikin falon.

Musamman ga yanda numfashinta keyi yanzun, tamkar wanda zai d’auke gaba d’aya, da alama kuma asthma dinta ne Keson tashi. 

Tana nan ahakane kuma taji ringtone na tashi, acikin aljihun rigarsa dake jikinta, da alama dai wayarsa ya bari acikin aljihun rigar.

Jin ringtone din yaki dai nawa Ne kuma, yasa ta sa hannu ta zaro wayartasa tare da ajiyesu akan table.

Kwata kwata ta kasa Koda kwanciya saboda, da zaran ta kwanta sai taji kamar numfashin nata zai bar jikinta.

After 10mn

Zuwa yanzu gaba d’aya ta fara shidewa saboda, yanda numfashin nata ke fita, yana yin sama da kasa, kirjinta kuwa sai duka yakeyi tamkar zai rabe biyu.

Acan b’angaren Azeez kuwa yawo yasha sosai, Ganin babu alamar zai sake ganinsu ne kuma, yasa shi hakura da neman nasu ya koma gida. 

Saidai duk hankalinsa atashe yake.

Hakan yasa shi soma kiran Daddynsu amma kwata kwata, wayan Dadyn baya shiga.

Duk da cewar yasan yanzun dare ne, amma kwata kwata bazai iya hakura  da abunda ya gani yau din ba, Lallai ya zama dole yakira gida ya sanar musu.

Samun wayar Daddyn nasu da yayi akashe ne kuma, yasa shi kiran wayan Abba Kabir, cikin sa’a kuwa wayar ya shiga. 

Bugu biyu kuwa Barrister Kabir din ya d’auki wayar, tare da  karawa akan kunnensa.

Azeez kuwa jin Abba Kabir ya d’aga wayarne, yasa batare daya jira wani abu ba, cikin tsananin rudani hadi da damuwar dake damunsa yace.

“Abba Naga JANNART.”

Wani irin bugawa Barrister Kabir yaji zuciyarsa tayi, cikin tsananin tashin hankalin daya shiga yace.

“Innalillahi wa’ Ilaihirraju’un Azeez wani irin magana kakeyi ne haka?”

“Magana nakeyi akan Jannart Abba, wallahi yau da idanuna naga Jannart a Mascow, Abba Jannart ba bata tayi ba, na ganta da idanuna kuma itama ta ganni, har na rungumeta kuma munyi magana da ita.”

Yah Azeez din ya fada Cikin confidence.

Abba Kabir din kuwa gumin da suka keto masa ya share, cikin sabon tashin hankalin da yakejin kansa aciki yace.

“Azeez ba Jannart bace, ba Jannart ka gani ba Azeez watakila idanunka gizo sukayi maka, amma ba ita bace.”

Cike da tsananin mamaki Azeez ya murtsuka idanunsa, saboda Jin abunda Abban nasu ya fad’a, lokaci daya kuma ya girgiza kansa, with full confidence yace.

“Abba ba karya nakeyi maka ba, ba kuma gizo idanuna sukeyi minba, Wallahi wallahi Jannart nagani ba wata ba, Abba taya kake tunanin zan kasa gane Jannart aduk inda na ganta, Jannart ce Abba wallahi ita nagani tare da wani saurayi, wani wanda bansan shiba, bana son zuciyata ta zargi Jannart, nasan ba halinta bane bare nayi tunanin ko wani saurayi ta biyo, kuma amma a yanayin dana ganta, batayi kama da irin wanda za’ace an saceta ba, naganta cikin kwanciyar hankali da jin dadi, Abba Ina cikin matuk’ar rud’ani, akan meya kawo Jannart Mascow..”

Shiru Barrister Kabir yayi, still kuma gumi ne ke sake keto masa, ya shiga tashin hankali kwarai. 

Wacce amsa zai bawa Azeez? Shine abunda ke dukan kwakwalwarsa…

Acan b’angaren su Jannart din kuwa,  duk yanda Rayyern yaso bacci ya daukesa abun yaci tura, domin da zaran ya rufe idanunsa, To hoton Jannart da wannan gayenne keyi masa yawo acikin idanunsa.

Doguwar tsuka ya kuma ja alokacin da ya sake jiyo, ringtone din wayarsa akaro na biyar, wanda yake tashi daga can cikin falon.

Ahankali ya zuro da k’afafunsa k’asa, saboda baisan wanene mai kiran nasa da wannan lokacin ba,  bud’e kofar dakin yayi tare da kutsa kansa cikin falon, Ganin wutan falon akunne ne kuma, yasa da mamaki ya karaso cikin falon.

Dai-dai yazo tsakiyar falonne kuma, kunnuwansa suka jiye masa yanda sautin, numfashin Jannart din ke fita, tamkar Wacce zata shid’e, domin da dukkan alama numfashinne ya k’wace mata.

Da sauri ya juyo ya kalleta, tare kuma da maida dubansa ga way’ansa Wacce take ta k’ara.

Screen din wayar ya kalla, ganin kuma sunan Barrister Kabir ne, ke yawo akan wayar yasa shi sake dawo da kallonsa ga Jannart din,  cikin wani irin yanayi yake kallonta.

Saidai kuma ganin kiran wayan na shirin katsewa ne, yasa shi daukar wayar tare da karawa akan kunnensa. 

Daga can b’angaren kuwa Barrister Kabir din, jin Rayyern ya d’aga wayarne yasa cikin tashin hankali yace.

“Rayyern wani ya ganku yau?”

Yanayin yanda Barrister Kabir din yayi, maganar kamar adan tsorace ne kuma yasa Rayyern din gyara tsayuwarsa.

“Eh wani ya ganmu wani wanda bansan ko waye ba, ita kuma harda rungumeshi tayi, bansan dalilin ta nayin hakan ba.”

Rayyern din ya fad’a yana me kura mata idanu, fuskarsa kuwa ahad’e take, daga jin yanayin muryarsa kuma kasan cewa, ransa amatukar bace yake har yanzu.

Abba Kabir kuwa jin abunda Rayyern din ya fad’a ne, yasa shi dan yin shiru, kana kuma asanyaye yace.

“Azeez ne Tabbas Azeez da gaske yake yaga Jannart, nasan Kai baka sanshi ba amma ita ta sanshi, saboda yayanta ne d’an Alhaji Idi Sale Dakata ne.”

Fuska Rayyern din ya dan ya mutsa, still cikin rashin sakewa yace.

“Oh haka ta fad’a but I don’t trust her, cause naga tayi hugging nasa.”

Haka nan yaji yana ta maimaita gayawa Barrister Kabir yaga ta ruggumeshi like yana kai kararta ne garesa.

Ajiyar zuciya Barrister Kabir ya sauke, fahimtar wani abu dake sukar zuciyar Rayyern din da yayi ne kuma yasa shi, Dan tausasa murya kana asanyaye gane azabebben kishine ke cinsa yace.

“I’m sorry Rayyern yayanta ne da gaske kamar yanda ta fada ma, yanzu Ina Jannart din take.”

Kalonsa ya maida ga Jannart din, cikin kuma haushin ta da yakeji yace.

“Gatanan wai fushi takeyi dani dan na hanata ruggumeshi sai wani numfashi takeyi sama-sama.”

Ya fad’i maganan in don’t care manner. 

Abba Kabir kuwa jin hakanne yasa, cikin tashin hankali yace. 

“What Rayyern numfashi sama-sama kuma? Please check her tana da problem fa.”

Abba Kabir din ya fadi haka cikin gaggawa.

Wanda jin hakanne kuma yasa Rayyern kashe wayan, da sauri ya k’arasa kanta, saboda ganin yanda take ta mimmik’ewa.

“Ke.”

Ya fad’a yana me d’an zungurinta da k’afansa.

Ko kallonsa baiga tayi ba balle  yasaka ran zata amsa masa, saidai har yanzu numfashin nata bai daina k’wacewa ba.

Ganin hakanne kuma yasa shi d’an rank’wafowa kanta, idanunsa ya d’an kura mata Ganin abun nata like serious ne ya sashi cewa.

“Hey what’s wrong with you Janna?”

Kanta ta d’an soma girgizawa, Ahankali kuma Cikin sheshshekan numfashi  ta kamo hannunsa wanda ya dafe saman kujera dashi.

D’aura hannun nasa tayi akan chest dinta, cikin wani irin yanayin dake nuna galabaitar ta, murya na rawa tace. 

“Pl…Please Na… Naan zan mutu numfashina, ka taimakeni Naan mutuwa zanyi, numfashina zaibar jikina, help……. help……me”.

Ta karasa maganan cikin shakewar murya, lokaci daya kuma Idanunta suka soma juyewa. 

Idanunsa ya zuba mata cike da mamaki, hadi da kuma tashin hankali yake kallonta.

Murya na dan rawa yace.

“Janna open your eyes and tell me what’s wrong?  Tell me Janna meyeke damunki fad’amin kinji faɗa wa Naan ɗinki?.”

Yayi maganan yana me daura hannunsa akan wuyanta.

Jannart kuwa duk ta fara ficewa a hayyacinta, Yayinda hawaye ke bin gefen fuskarta yana kwarara, tanason gaya masa cewar Asthma dinta ne ya tashi, amma ta kasa saboda numfashinta dake seizing.

“Naaaaaannnnnnnnn Numfashinaaaaaaaaaa…..”

Da k’yar ta fadi hakan afusge, lokaci daya kuma numfashin nata yayi low, take kuma Idanunta suka lumshe.

Cikin hanzari mamaki, tsoro, rawan jiki, da kuma tashin hankali Rayyern din yasanya duka hannayensa ya kama kafad’unta, hankalinsa amatukar tashe yace.

“Janna! Jaannaa!! please open your eyes, Janna are you okay? Janna weckup please..”

Ya kare maganan yana me jijjigata, hankalinsa atashe Ganin bata ko motsa bane, kuma yasa shi d’aukarta tare da rungumota jikinsa.

Tamkar wata Y’ar tsana haka ya d’auketa, Cikin hanzari kasancewar kuma key din motarsa yana cikin falonne, yasa yana dauka baijirayi komai ba, kaitsaye ya nufi hanyar fita daga falon.

Koda ya fito gudu ya fara Yayinda Jannart din ke cikin jikinsa,  kasancewar kuma Acan sama d’akin nasu yake ne, shiyasa dole saiyayi tafiya mai nisa kafun ya sauko.

Hakan kuwa shiyasa duk inda yazo wucewa sai ankalleshi, Yayinda ma’akaitan hotel din ke tambayansa ko lafiya.

“She’s patient.”

Shine kawai abunda yake fad’a musu.

Ahaka har ya sauko kasa, inda yayi parking motarsa.

Ak’agauce yayi  bud’e murfin motar  ya shiga, agefensa ya kwantar da ita.

Tare da yiwa motar key a 360 ya ja motar yayi gaba.

Gudu yake sosai akan titin kasancewar kuma, dare yayi sosai shiasa babu yawan ababen hawa akan titin.

Wannan dalilin yasa cikin mintuna kad’an ya iso harabar babban asibitin, wanda ya kasance shine mafi kusa dasu. 

Yana zuwa kuwa ko gama dai-dai-ta parking din motar baiyi ba, ya fito tare da ita ajikinsa.

Kaitsaye ya nufi cikin asibitin. 

Ganinsa da Doctors sukayi ne kuma, yasa kaitsaye suka kawo gadon marassa lafiya,  aka d’aura Jannart din akai.

Kaitsaye aka wuce da ita emergency, dan bata taimakon gaggawa, kasancewar tuni numfashinta yayi nasa gun.

Dole kuma sai an saka mata oxygen.

Kasancewar kuma Hospital din na d’aya daga cikin, inviglators din da suke koyar dasu abubuwa ne kuma musulmine, yasa aka yiwa Jannart din tarba mai kyau. 

Domin Koda aka tashi shigar da ita Emergency din, tare da Rayyern aka shiga.

Gaba d’aya ya kasa ta b’uka komai, saidai idanu daya zubawa kan fuskarta, wanda aka sakawa Oxygen.

Yayinda sauran Doctors din kuwa, suka shiga checking dinta, saboda akwai hanyoyin da zasubi wajen Ganin hakikanin abunda ke damunta.

Shikuwa Rayyern Ganin hakanne yasa shi zaro wayarsa, tare da fita daga Emergency din.

Numbern Dr. Sulaiman ya kira saidai kwata kwata baya shiga.

Hakanne kuma yasa shi kiran layin Ramadan.

Cikin sa’a bugu biyu kuwa Ramadan din ya d’auki wayar.

“Ramadan.”

Rayyern ya kira sunansa cikin yanayin damuwa, batare daya bari Ramadan din yace wani abu ba kuma yace.

“Please Ramadan Jannart bata da lafiya, kwanaki da aka kawota Hospital namu meyake damunta?”

Yayi mgnar cikin ruɗu sabida bai san tanada matsalar numfashi ba.

“Subahanallah Hamma Rayyern meyake damunta yanzun? Ina take yanzu?”

Ramadan din ya fada cikin tashin hankali.

“Stop Ramadan ka amsamin tambayata.”

Rayyern din ya fada cikin zakuwa.

“I’m sorry Hamma Rayyern bani na kula da issues din nata ba, Dr. Sulaiman ne, kuma bansan meye problem din nata ba, but ka tambayi Dr. Sulaiman?”

“Way’ansa akashe Ramadan are you in Hospital?”

“Yeah.”Ramadan din ya bada amsa, saboda dama yana Cikin Hospital din, kasancewar yau din night duty ne dashi.  

Ajiyar zuciya Rayyern ya sauke, tare kuma da gyara tsayuwarsa cikin gaggawa yace.

“Okay kayi checking folder dinta, date folder 24/2/2020 please Ramadan hurry up.”

“Okay I will.”

Ramadan din ya fada tare da kashe wayan.

Kaitsaye kuma ya tashi ya nufi inda suke ajiyan  folders dinsu. 

Rayyern kuma tsayuwa yayi tare da zubaw fuskar Jannart din idanu, kasancewar daga inda yake tsaye din yana iya hango fuskarta ta jikin wani glass.

Jin wayarsa na kara ne kuma yasa shi, saurin dagawa tare da kara wayar akan kunnensa. 

Ramadan kuwa jin Rayyern din ya d’aga ne, yasa shi cewa.

“Hamma Rayyern banga foldern Jannart ba fa, babu nata kwata kwata saidai ga wani nan, da nagani amma sunan da aka rubutu, shine Jannart Abdulkarim Sale Dakata.”

 

“What Abdulkarim Sale Dakata!!”

Rayyern din ya fad’a cikin mamaki, da kuma wani irin tunani da yaji ya tsaya masa Acikin zuciyarsa.

Saidai kuma ganin babu lokaci ne yasa, shi cewa.

“Meye problem din mai folder din? Sannan shekarunta nawa?”.

“22. Asthma.”

Ramadan ya fad’a yana me jujjuya folder din, dake hannunsa.

Rayyern kuwa jin hakanne yasa shi, kashe wayan tare da juyawa ya nufi cikin emergency room din.

Koda ya shiga kuwa ya samu har sun Gano matsalarta,  Cikin ikon Allah kuma har sun shawo kan matsalar nata.

Domin numfashinta ya dai-dai-ta sun kuma yi mata duk wani abu daya dace. 

Saidai har yanzu basu cire mata oxygen dinba. 

Ahaka aka kaita har zuwa dakin hutu.

Agefenta ya zauna tare da zuba mata ido, 

A hankali ya lumshe idanunsa tare dasa hannunsa bisa hannunta dake gefensa,

Wani irin sassayan numfashi ya fesar lokacin daya haɗe tafin hannunnsu wuri ɗaya.

dai-dai lokacin ne kuma wayarsa ta soma kara, alaman shigowar kira.

Kallon screen din wayar yayi, Ganin kuma sunan Barrister Kabir ne ke yawo akan wayar, yasa shi d’aga kiran.

Yana karawa akan kunnensa Daga can b’angaren Barrister Kabir yace.

“Rayyern ya Jannart din, fatan tana lafiya?”

Shiru Rayyern din ya d’anyi, kamar bazai amsa ba can kuma, cikin dakiya yace.

“Barrister Waye Abdulkarim Sale Dakata?….!

*

TUBALI 52

Wata  iriyar bugawa zuciyar Barrister  Kabir tayi, wanda har saida Rayyern din yaji sautin kakkarfar Ajiyar zuciyan daya sauk’e. 

Ahankali kuma Cikin sanyi dason b’oye babbar damuwarsa yace.

“Barrister Abdulkarim Saleh Dakata yayana ne, sannan kuma k’anin Alhaji Idi Saleh Dakata ne, mu ukun duka acikin mahaifiya d’aya muka fito, haka ma kuma babanmu d’aya, amma Dr. Rayyern me yasa kayi min wannan tambayar?”

Barrister Kabir din ya tambaya, cike kuma dason jin amsar abunda ya tambayan.

Rayyern kuwa jin abunda Barrister Kabir din ya fad’a ne, yasa shi juyawa ahankali ya sauk’e idanunsa akan Jannart dake kwance, Wacce take shak’an numfashi ta Oxygen.

Yanayin yanda take kwance flat ne kuma yasa, Idan ba mutum ya kula da cewar tana shak’an numfashi ta oxygen ba, to direct zakayi tunanin matacciya ce, Dan babu wani abu na jikinta dake motsawa sai zuciyarta. 

Murza tafin hannunta dake cikin nasa yayi tare, da ɗan ɗago hannun nata sama ya manna shi kan tattausan sajensa.Ahankali kuma ya janye kallonsa daga gareta, tare da rumtse idanunsa, cikin dakiya ya gyara tsayuwarsa kana yace.

“I’m sorry to say Barrister ba dangartakar ku dashi nakeson sani ba, inason sanin matsayinsa da kuma alak’arsa da Matata Jannart ne?.”

Wani irin dogon numfashi hadi da ajiyar zuciya, Barrister Kabir ya sauke, lokaci daya kuma duk idanunsa suka ciko da hawaye dan abubuwa biyu da suka zo masa lokacin daya kalmar matata da Rayyern ya kira Jannart da ita shine karsashinsa, son jin alak’anta da Barrister Abdulkareem Saleh Dakata kuwa shine mafi rinjayen rauninsa a rayuwar duniya, haka kuma damuwa mai tarin yawa ta bayyana akan fuskarsa, domin tambayar da Rayyern din yayi masa, ya tono masa wani rauni da kuma mikin dake kwance a zuciyarsa. 

Asanyaye kuma cikin son kawar da maganan yace.

“Rayyern mubar wannan maganan, yanzu ka fad’amin wanni hali Jannart take ciki?”

Ya k’are maganan cikin raunin muryar da tasa, zuciyar Rayyern karaya, saboda ayanda yaji ak’asan muryar Barrister Kabir din, tsananin damuwa ne da kuma wani abu mai kama da fargaba. 

Idanunsa dake alumshe ya d’an bud’e, kana cikin yin k’asa da murya yace.

“Zataji sauki da yardar Allah, saboda na kawota hospital dan yanzu haka ma oxygen ne ahancinta.” 

Still ajiyar zuciya mai karfi Barrister Kabir din ya sauke, cikin tarin yanayin damuwa kuma yace.

“Allah Ya bata lafiya, kayi hakuri Rayyern Dan Allah ka kulamin da amanata, Jannart tana da buk’atar kulawarka ako da yaushe, Jannart marainiyace kada ka manta kuma duk wanda ya kula da maraya , Allah zai kula dashi sannan zaiyi masa Garkuwa aranar tashin Alk’iyama, Dan Allah Rayyern ka kula sosai, saboda tana da cronic asthma, nasan baka san da hakan ba, amma dole saika kiyaye wajen rabata ta’ammali da abu mai sanyi.” 

Idanu Rayyern din ya kuma alumshewa kana ahankali, kuma cikin sanyi yace.

“Insha Allah zan kula da hakan, soon kuma zata samu sauki.”

“Allah yasa haka Rayyern, sannan kayi hakuri da ganinku da Azeez yayi, ya kuma tashi hankalinsa akanku  ne, saboda yana d’aya daga cikin mutanen da suke kamar kashin bayan  farin cikin Jannart, yana nuna tsananin kulawarsa agareta, shiyasa itama Jannart din da ta gansa, ta kasa hakuri har saida taje garesa.”

Kai Rayyern din ya dan jinjina, batare kuma daya sake cewa komai ba, ya maida idanunsa ya lumshe.

Barrister Kabir kuwa ci gaba da cewa yayi.

“Tabbas plan dinmu yaso lalacewa saboda ganinku da Azeez din yayi, amma Allah ya rufa mana asiri, saboda Koda Azeez ya kira wayan Alhaji Idi Sale Dakata, dan sanar dashi cewar yaga Jannart, wayar bata shigaba Wannan dalilin ne kuma, yasa Azeez din ya kirani,  sanin bani da wata hujja ta karya da zan iya fad’a masa, Wacce zai gamsu da ita ne kuma, yasa na sanardashi gaskiya da kuma hakikanin abunda ke faruwa,  saidai na fad’a masa cewar akan matsalar dake tsakaninta da Junaid ne yasa aka b’oyeta.”

Ajiyar zuciya Rayyern din yayi, tare da fesar da wani iska daga bakinsa.

Cikin kuma d’an yanayin rashin gamsuwa yace.

“Amma kana ga fad’a masa hakan bazai zamo matsala, ko sanadin rugujewar komai ba?”

“Bazai zama ba Rayyern, nasan Azeez nasan waye shi bazai tab’a fallasa abunda na fad’a masa ba, duk da na b’oye masa wasu abubuwan, amma nasan shikansa bayason irin cutarwar, da d’an uwansa Junaid ke nunawa ga k’anwar tasu, saboda haka karka damu Azeez zai iyayin komai dan bawa Jannart kariya, musamman ayanzu dana gargad’esa da kar ya fad’awa kowa, ya kumayi min alk’awarin cewa bazai tab’a fad’ad’in ba zuwa gaba kuma zan sanar dashi dukkan abinda bai saniba.”

Again numfashi Rayyern din ya fesar, cikin kuma maida kallonsa ga Jannart din dake kwance yace.

“Shikenan ba damuwa.”

Shima Barrister Kabir din Ajiyar zuciya ya sauke kana anutse, cikin maida hawayen dake kwance acikin idanunsa yace.

“Rayyern akwai lokacin da zaka san waye Abdulkarim Saleh Dakata da alak’arsa da matarka, saidai kuma ba yanzu ba, amma kamar yanda Kaga Azeez haka shima yake, domin duk wani suffa da kamanninsa Azez ne ya d’auka,  domin sometimes Idan Jannart tana tambaya na, akan kamannin Baffan nata Abdulkarim Saleh Dakata, saboda bata sanshi ba nakan ce, ta kalli Azeez domin idan taga Azeez kamar photo copy d’insa ta gani, saboda tsananin kamar da sukeyi….”

Ya k’are maganan cikin wata irin muryar, dake bayyana alaman kuka, wanda hakanne kuma yasa shi, tsagaitawa da maganan.

Rayyern kuwa jin hakanne yasa shi, d’anyin shiru acikin zuciyarsa yana me mamakin abunda, zaisa Barrister Kabir din awannan yanayin, Lallai Tabbas yasan cewa akwai wani abu, da Barrister Kabir din yake b’oyewa, more especially yanzu da yayi masa tambaya, akan Abdulkarim Saleh Dakata, meyene To wannan abun?

Itace tambayar da bashi da amsarta.

Ganin shirun yayi yawa ne kuma yasa shi cewa.

“Allah ya jik’ansa da rahama, yasa can yafi masa nan.”

“Ameen summa Ameen nagode matuk’a Rayyern.”

Barrister Kabir din ya fad’a cikin wani sabon sheshshek’an daya zo masa, Jin da yayi kuka mai sauti na shirin k’wace masa ne kuma, yasa shi ajiye wayan batare kuma daya katse kiran ba.

Araunace ya kifa kansa akan pillown dake hannunsa, cikin tarin damuwa da kuma ciwon da yakeji aransa, ya saki kuka mai tsuma zuciya.

Dai-dai lokacin kuma Aunty Dijat dake tsaka da bacci ta farka, tare da bud’e Idanunta arazane, saboda sautin kukan mijin nata da taji.

Ganinsa da tayi azaune yana kukanne kuma, yasa ta matsowa inda yake tare dasa hannunta ta dafa shoulder d’insa.

Tabbas tasan abunda yakesa mijinta kuka, alokuta daban daban, musamman ma dai Idan tagansa a irin wannan yanayin.

Araunace kuma cikin sanyin da jikinta yayi tace.

“Abban Hafeez.”

Jin muryar matar tasa acikin kunnuwansa ne, yasa shi dagowa ya kalleta lokaci daya kuma, ya maida kansa ya d’ora acinyarta.

Cikin muryarsa dake fitar da Amon kuka yace.

“Dijat zanyi rashi biyu asanadin rashi d’aya, nayi rashi d’aya acikin shekaru 22 da suka wuce,  sannan kuma sanadin wancan rashin, zan sakeyin wani rashin anan kusa, Dijat Ina kukane saboda inason y’an uwana, banason rasa su, amma ya zanyi Dijat nasani dole zamu rabu, k’addara da jarrabawar Ubangiji zata rabamu,  inajin nauyin wannan abun azuciyata kullum.”

Ajiyar zuciya Aunty Dijat din ta sauke, cikin kuma so da tausayin mijinta tace.

“Kayi hakuri Barrister Tabbas kowacce rayuwa da irin k’addararta, amma Insha Allah babu wanda zaka sake rasawa.”

“Dole zan rasa Dijat nina sani lallai dole zan rasa, rashin da nayi shekaru 22 da suka wuce, shi zaisa na sakeyin wani rashin ayanzu. Maraicin Jannart nake dubawa Dijat, Maraicin Jannart maraicine da yake cike da abubuwa masu tarin yawa,  haka kuma maraicine da yake buk’atar tausayawa da jin k’ai,  Ina matuk’ar tausayin Jannart….”

Ya kare maganan still cikin kuka, wanda hakan yasa Aunty Dijat soma shafa bayansa ahankali, kuma cikin lallashi take tausasa sa.

Rayyern kuwa dake Jin duk wani abu dake faruwa acikin wayar, idanunsa ya rumtse da k’arfi, saboda wani irin masifaffen raunin da yaji ya lullub’esa haka nan yaji wani irin tausayin Jannart da Barrister Kabir keta nanata maraicinta.

Tabbas bazai iya jurewa jin abubuwan da suke fad’ad’in ba, wanda hakanne kuma ya sashi zare wayar daga kunnensa, tare da katse k’iran gaba d’aya.

Ahankali kuma cikin dogon tunanin daya fad’a, ya juyawa tare da zubawa Jannart din dake kwance idanu hannunta ya manna kan bakinsa tare da liƙa mata wani sassayan kiss.

Filla filla kuma haka yakejin maganganun Barrister Kabir na dawowa kunnuwansa.

Babu kuma abunda yafi tsaya masa arai, kamar Maraicin Jannart din, da yaji Barrister Kabir din nata ambata.

Asanyaye cikin kuma tsananin tausayinta da yaji ya dirar masa azuciya, ya ronk’ofo jikin.

Lallausan tafin hannunsa ya d’aura akan goshinta, wanda yaga yana ta tsatstsafo da gumi,  ahankali ya share mata gumin, tare kuma dasa Y’ar yatsarsa ya gyara mata, dogon gashinta wanda ya d’an rufe mata gefen fuskar ta.

Still kuma duk abunda yakeyi din idanunsa, nakan kyakkyawar fuskarta wacce tayi fayau, ga kuma zara zaran gashin Idanunta wanda suka baje, suka kuma k’arawa fuskarta ta kyau.

Akaron farko yakejin wani irin matsanancin tausayi, da rauninta na ratsa cikin zuciyarsa.

“Maraicin Jannart nake dubawa, Maraicin Jannart yana matuk’ar buk’atar kulawa, da kuma tausayawa.”

Way’an nan  kalaman sukeyi masa yawo acikin k’wak’walwa, wanda har saida hakan yasa shi jin wani nauyi azuciyarsa. 

Wannan dalilin yasa asanyaye ya d’an sukuyo da kansa gareta, wanda hakan yasa numfashinsa soma sauk’a akan kyakkyawar fuskarta. 

Ahankali kuma cikin tausasa murya yace.

“Allah ya baki lafiya My Janna.”

ya kare maganan nasa da tausayawa.

Ahankali kuma ya jawo kujera ya zauna akusa da ita, cikin dan yanayin sanyi ya kamo hannunta na dama ya rik’e acikin nasa.

Wanda hakan yasa tafukan hannayensu had’ewa awaje d’aya. 

Wani irin d’umin dad’in da yaji ne kuma yasa shi, kwantar da kansa agefenta, tare kuma da d’aukan hannun nata, ya d’aura ak’asan hab’arsa.

Idanunsa ya lumshe  anutse kuma yake shak’an, daddad’an k’amshin turaren dake tashi ajikinta.

Almost 5mn suna nan ahaka, Yayinda Jannart din keta baccinta cikin nutsuwa.

Shikuwa Rayyern ahankali yake d’an yawo da bayan hannun nata akan fuskarsa, har dai ya gangaro zuwa kan lallausan sajensa.

Idanunsa ya kuma lumshewa adai-dai lokacin, da ya kawo hannun nata saitin bakinsa, ba tare da zato ko tsammani ba kuma, saiji yayi ya d’aura mata sassayan kiss akan bayan hannun nata a karo na biyu. 

Jin abunda yayi dinne kuma yasa shi sake lumshe idanunsa, ahankali ya janye hannun nata zuwa kan hab’arsa.

Itakam Jannart duk batasan ma meya keyi ba, saboda baccinta kawai takeyi. 

To shima Rayyern din dai ahaka bacci ya d’aukesa, yana rungume da hannunta, yayinda kansa kuwa ke manne ajikin gadon nata.

Bacci sukeyi sosai saboda dama tuni dare ya raba, musamman ita Jannart wanda akayiwa allurar bacci, saboda ta sanadiyar baccinne numfashi da kuma bugun zuciyarta zasu dai-dai-ta.

*5:00am.*

Ahankali take d’an motsa jikinta, wanda takejin yayi mata nauyi sosai, cikin sanyi da kuma kalasar dake damunta, ta bud’e Idanunta wanda sukafi kama dana y’an maye.

Da sauri tasa hannu ta dafe saman marar ta, da takejin ya cika saboda tsananin fitsarin da takeji,wanda kuma shine ya tasheta daga baccin da takeyi.

Ahankali ta d’an juya Idanunta gefe, inda ta sauke ganinta akansa.

Bacci yakeyi atsanake still kuma hannunta na cikin nasa, wanda ya rik’e gam tare da d’aura kansa akai. 

Idanu ta d’an zuba mishi hade dajan dogon numfashi, saboda har yanzu akwai oxygen akan hancin ta, saidai tuni numfashinta ya dai-dai-ta. 

Ahankali tasa d’ayan hannunta ta tab’a oxygen  din, cikin kuma wani irin yanayin dake nuna bata wani hayyacinta sosai, saboda alluran baccin da bai gama saketa ba.

“Naaaaaannnnn!!!”

Ta kira sunansa cikin sassayan murya, tare dajan dogon numfashi. 

Still kuma Idanunta na ci gaba da rufewa, kamar wata y’ar maye.

“Naaaannn!!!”

Ta sake kiran sunansa asanyaye. 

Rayyern kuwa acan cikin baccin nasa, ya d’anji sautin muryarta sama sama, hakan kuwa shi yasa ya bud’e idanunsa.

Ganin idanunsa abud’e ne kuma, cikin yanayin mayen baccin da baigama sake shiba yace.

“Janna, kin tashi ya jikin naki?”

Idanunta dake bud’ewa da rufewa ta d’an juya, kana asakalce cikin kuma yanayin marassa lafiya tace.

“Da sauki, please Naan kacire min wannan abun numfashina ya dai-dai-ta.”

Tayi maganan tana me nuna oxygen din.

Shikuwa Rayyern jin hakanne yasa shi, d’an rank’wafowa kanta tare dasa hannusa ya dafa saman kirjinta  atsanake yaji numfashin nata na tafiya.

Wanda hakanne kuma yasa shi gangaro da hannun nasa, saman mak’oshinta saboda yanason yaji  bugun zuciyarta. 

Akokarinsa nayin hakanne kuma, lalausan tafin hannunsa ya sauk’a asaman breast dinta, batare daya sani ba.

Wani irin masifeffen abu yaji yana bin dukkan jijiyoyin jikinsa, wanda haka yasa ya

D’an d’ago da sauri  ya kalleta, kana cikin tausasa murya dason shagwab’ata yace da narkewa da shima yayi yace.

“Bugun zuciyarki bai gama dai-dai-ta ba Janna, ki d’anyi hakuri kinji.”

Kai ta d’an jinjina masa kana cikin kasala ta zare oxygen din akan hancinta, ashagwab’e kuma tace.

“Naan zanyi fitsari.”

“To.”

Ya fad’a tare da k’arasa zare mata oxygen din, dai dai ta yunk’ura zata tashi ne kuma, Rayyern din ya saka hannayensa duka ya tallafota,tare da zaunar da ita akan

Saidai kuma yana zaunar da ita, yaga ta tafi luuuuu zata kwanta, alamun tana cikin magagin bacci.

Da sauri ya tallafota ta fad’a jikinsa, idanu ya d’an zuba mata ganin yanda jikinta ke rawa ne kuma, yasa shi rungumeta tsam ajikinta.

Pat-pat haka zuciyarshi take harbawa.

 “Yah salam”.

Ya faɗi a cikin zuciyarsa domin yaune karo na forko da yayi mata irin wannan ruggumar murya a narke can ƙasan maƙoshinsa.

“Janna.”

Ya kira sunanta cikin dan tausasa murya.

Jannart kuwa jinta ajikinsa ne yasa ta sake narkewa, tare da lumshe Idanunta. 

Cike da sabon shagwab’a tace.

“Naan zanyi fitsari.”

“To muje na kaiki toilet tunda naga kaman baccin bai gama sakeki ba.”

D’an k’aramin bakinta ta turo gaba, tare da cewa.

“A’a zan iya zuwa da kaina.”

“Bazaki iya zuwaba Janna muje na kaiki.”Ya fad’a cikin serious, tare da kamo hannunta ta sauko daga kan gadon.

Bisa jagorancinsa kuma suka nufi toilet din dake cikin dakin.

Shiya bud’e mata k’ofar toilet din ta shiga, har ta saka k’afarta acikin toilet din kuma saita dakata, tare da juyowa ta kalleshi da maraitattun idanunta.

Gane abunda take nufi ne kuma yasa shi, d’auke kansa gefe tare da cewa.

“To kiyi fitsarin mana.”

Bakinta ta d’an turo gaba, cike da salon shagwab’a tace.

“a’a nidai ka fita.”

Idanunsa ya d’an jujjuya saboda Jin abunda ta fad’a,  Ahankali kuma yace.

“Ok ashe abun babu dadi kenan.”

Da sauri tayi k’asa da kanta, saboda gane abunda yake nufi.

Shikuwa Rayyern kansa kawai ya girgiza, batare kuma daya sake cewa komai ba, ya juya tare da sakar mata kofar ya fice daga cikin toilet din.

Ganin hakan da tayi ne kuma yasa ta, tsugunnawa tayi fitsarin, Koda ta gama alwala tayi, saboda tasan zuwa yanzu lokacin sallan asuba yayi.

 Bayan ta idar da alwalanne kuma, ta Mike asanyaye ta murda handle din kofar ta fito.

Tana fitowa dinne kuma sukayi karo dashi, saboda dama bai bar jikin kofar ba.

Da sauri tayi baya baya kaman zata fad’i, Ganin hakanne kuma yasa Rayyern din rik’ota, tare da jawota ya zaunar da ita akan gadon.   

Idanunsa ya dan zuba mata, Ganin hakanne kuma yasa ta lumshe nata idanun, tare da bud’e bakinta ahankali tace.

“Naan Zanyi sallah.”

Dan karamin bakin nata dake matsowa ahankali ya kalla, Cikin kulawa yace.

“Janna anan babu sallaya, kuma kinga ko hijab babu, amma kijira bari na duba Dr. Imran tunda shi Musulmi ne, nasan baza’a rasa sallaya ba, amma samun hijab kam zaiyi wuya.”

Kai ta d’an langwab’ar kana ahankali tace.

“To ai mayafina ma zaiyi sallah idan na nad’ashi ya rufe duk gashina, kuma kayana baya nuna jiki.”

Yanayin yanda ta k’are maganan tana lumshe Idanunta ne, kuma yasa shi jinjina kai.

Saidai batare daya sake cewa komai ba, ya shige cikin toilet din dake cikin dakin.

Al’wala ya dauro, bayan ya fito daga toilet dinne kuma, ya dan kalleta tare da cewa.

“Bari naje nayi sallah, Idan na dawo sai kiyi naki sallan.”

Kai ta jinjina masa tare da maida jikinta ta kwanta, akan gado shikuwa Rayyern ficewa daga cikin dakin yayi.

Kaitsaye kuma Dan madaidaicin masallacin dake cikin Hospital din ya nufa.

Koda yaje ya samu har an idar da sallah, hakan yasa shi kad’ai yayi nasa sallan.

Bayan ya idar da sallan ne kuma, direct ya wuce office din Dr. Imran. 

Yana isa bakin office din kuwa, suka hadu da Dr. Imran din.

Cikin mutum tawa sukayi musabaha, kana fuska asake Dr. Imran din yace.

“Ya jikin Madam din, yanzu nake rayawa araina cewar zanje na duba ta.”

Murmushi Rayyern din yayi, tare da cewa.

“Alhamdulillah jikinta yayi sauki sosai, yanzu ma ta tashi wai tanason tayi sallah ne.”

Murmushin Jin dadi Dr. Imran din yayi, kana cikin farinciki yace.

“Masha Allah ai indai ma numfashinta ya dai-dai-ta, to zaku iya tafiya gida babu wani matsala, yanzu muje na duba jikin nata mugani.”

“To.”

Dr. Rayyern din yace tare da juyawa, suka nufi dakin da Jannart din take.

Suna shiga kuwa suka sameta akwance, saidai kuma ganinsu da tayi ne yasa ta tashi zaune. 

“Mrs Rayyern sannu ya jikin naki?”

Dr. Imran ya fad’a yana me kokarin, d’auke oxygen din dake kan gadon.

Jannart kuwa jin sunan da ya kira ta dashi ne, yasa tayi kasa da kanta Ahankali kuma cikin sanyi tace.

“Da sauki sosai.”

“Masha Allah haka akeso ai, Allah ya kara afuwa, yanzu babu wani abu dake yi miki ciwo kenan?”

Kanta ta gyad’a alaman “Eh”

Hakanne kuwa yasa Dr. Imran juyowa ya kalli Rayyern.

“Doctor zaka iya daukanta ku tafi gida babu matsala, saidai kaman yanda kasanine mai asthma dole sai anayi ana kiyayewa, sannan ka tafi da way’annan alluran guda 5 kullum, guda d’add’aya zaka na yi mata.”

Kai Dr Rayyern din ya jinjina tare da karb’an alluran, ya rik’e.

Jannart kuwa jin ance allurai za’ana yi mata ne, yasa ta juyo ta kalleshi, araunace da kuma yanayin tsoro tace.

“Naan allurai za’ana min kuma”.

Ido ya d’an zuba mata tare da gyaɗa mata kai.

Cikin yanayin sanyi tace.

“Abba na ya hana amin  allura kawai abani magani.” 

Idanunsa ya d’an zuba mata Ganin kuma da gaske batason alluranne, yasa shi gyara tsayuwarsa tare da cewa.

“Janna dole ai miki alluran sune zasu taimaka miki ai wajen samun sauki, ko bakyason ki rabu da asthma dinne?”

Still rau-rau tayi da idanu, tare da soma kunkuni acikin zuciyarta, saboda harga Allah ita batason allura dama a dole Dr Lukman keyi mata data samu Abbanta ya hana kuma ta huta.

Dr. Imran kuwa ganin suna magana da wani, yaren da baisani bane yasa shi, sakin murmushi tare da mikawa Rayyern din takardar sallama. 

Rayyern kuwa bayan ya karb’i takardar, hannun Jannart din ya kamo.

Cikin yin k’asa da murya yace.

“Muje ko.”

Babu musu kuwa ta kama hannun nasa, saboda har yanzu jikinta babu kwari, sannan kuma idanunta basu daina rufewa ba saboda bacci.

Ahaka dai suka fito daga cikin Hospital din. 

Inda Dr. Imran ya rakosu har bakin mota.

Saida yaga tashin motarsu kuma, kafun ya koma cikin asibitin nasa. 

Su kuwa su Rayyern Koda suka dau hanya, shagwab’a sosai Jannart din take tayi, tare kuma da wasu irin sambatu wanda shi baisan ma na meye ba.

Saidai duk abunda takeyi yana kallonta, ta gefen idanunsa, yanayin yanda take abubuwan nata ne kuma, yasa shi fahimtar cewa har yanzu alluran da akayi mata dinne bai gama sake ta ba, shine kuma ke sawa tana sambatu, kasancewar bata samu isashshen bacci ba.

Kaitsaye gida suka nufa, suna zuwa kuwa ya yi parking motar, tare da fitowa ya zagayo b’angaren Jannart din ya fito da ita. 

Yana rike da hannunta haka suka nufi cikin gidan.

Koda suka kawo bakin kofar falon, hannunsa ya d’aura akan security door din, tare da danna wasu numbers, almost 4 minute glass din ya nuna masa reguest.

Ganin yadda take layine, yasashi gyara tsayuwar sa tare da manna bayanta da k’irjinsa kana ya d’an zuro kanshi ta kan habarta na dama.

Hannunta ya kamo ahankali ya daura akan glass din,  take kuwa duk na’urorin wajen suka amsa, inda sunanta ya bayyana b’aro b’aro ajikin d’an na’urar. 

Idanunta ta d’an zaro tana Kallon abun. 

Dai-dai lokacin kuma na’urar ta rubuta, Accepted.

Zare hannunta daga kan na’urar yayi, Ahankali kuma yace.

“Sake d’aura hannunki.”

“To.”

Tace tare da d’aura hannun nata, take kuwa saiga kofar ta bud’e. 

Kallonsa tayi da mamaki,  shikuwa Rayyern gefenta ya rab’a tare da wucewa Cikin falon.

Ganin hakanne kuma yasa itama ta rufa masa baya. 

Koda suka shiga falon zama tayi akan kujera, Yayinda shi kuwa ya wuce bedroom dinta, ya d’auko mata hijab da sallaya.

Koda ya dawo anan cikin falon ya shumfud’a mata sallayan, tare kuma da mika mata Hijab din.

Kana ya koma gefe ya zauna, itakuwa Jannart ganin hakanne yasa, Ahankali ta tashi tsaye, tare dasa hijab din ta tada sallah. 

Shikuwa Rayyern wayarsa ya d’auka, yayi musu ordern abinci.

Bayan ya gama order ne kuma ya ajiye wayar, tare da maida kansa ya jingina da jikin kujera, Ahankali yake Kallon fararen tafin k’afarta, kasancewar tana zaman tahiya ne.

Jannart kuwa tana gama tahiyan ta sallame sallan, tare da jingina ta kwanta akan sallayan.

Ahankali kuma ta lullub’e duk jikinta, da hijab din nata, tare da maida Idanunta ta lumshe.

“Ya jikin naki?”

Ya tambaya yana me Kallon kyakkyawar fuskarta.

“Da sauki.”

Ta amsa masa batare da ta bud’e Idanunta ba.

Saboda wani irin bacci takeji yana fusgarta.

Dai-dai lokacin kuma aka soma knocking kofar falon, Ahankali ya  mike tare da k’arasawa ya bud’e kofar falon.

Kamar yanda ya tsammata kuwa abincin da yayi order ne ya iso,  bayan ya k’arbi abincinne kuma ya dawo falon.

Akasalance ta Dan bude Idanunta ta kalleshi, cikin sanyi da kuma kasala tace. 

“Naan zanyi bacci.”

D’an rank’wafowa Kanta yayi ahankali, kuma cikin tausasa murya yace.

“Okay amma tashi kici abinci, Idan nayi miki allura saiki kwanta kinji…”

Bakinta ta turo gaba, tare da Dan yi masa kallon wannan mugunta zaimin mai kama da shagwab’a tace.

“Allura da sanyin safiyan nan, Naan kayi haƙuri dan Allah sai anjima  bayana ma ciwo yake.” 

Ta kare maganan tana me daura hannunta, akan hips dinta.

Rayyern kuwa Ganin hakanne yasa wani, irin sihirtaccen Murmushi kwace masa, ahankali kuma ya zauna akusa da ita. 

“Don’t worry alluran ai ba abaya akeyinta ba, a hannune malama.”

Ya fad’i hakan yana me danne dariyar dake ransa, tare kuma da soma bud’e ledodin restaurant din dake hannunsa. 

Jannart kuwa jin hakanne yasa ta tashi ta zauna, cikin sigar shagwab’a tace.

“Ayyah Naan ni hannun nawa ma ai ciwo yake, duk karkarwa ma yake bazai iya tsayuwa waje daya ba, kuma ni banason allura ya karyemin ajiki.”

Takare maganan tana me d’an yin mui-mui da k’aramin bakinta.

Rayyern kam dariyarta gaba d’aya duk ta kamasa amma saiya danne, saboda tunda yake bai tab’a ganin mai tsoron allura irinta ba.

D’agowa yayi ya kalleta.

“Da wani idanunta kamar na y’an shaye shaye.”

Ya fad’i hakan acikin zuciyarsa.

Azahiri kuwa takeaway din abincin ya turo gabanta, tare da zuba mata narkakkun idanunsa.

Cikin kulawa yace.

“Oya eat idan kuma ba haka ba, To ya zama lallai dole sai anyi miki allurai guda biyu kuma in sossoka miki su da k’arfi.” Da sauri ta zazzaro Idanunta, lokaci daya kuma ta k’wabe fuska tamkar zatayi kuka,  badan taso ba kuwa haka ta dauki spoon ta soma tsakalan abincin. 

Rayyern kuwa Idanu ya zuba mata, tare da harde hannuwansa akirjinsa. 

Ganin hakanne kuma yasa ta d’an tuttura abincin bisa dole badan taso ba.

Bayan ta danci kadan ne kuma ta ture abincin gefe, tare da kwaɓe fuska cikin murya kaman zatayi kuka tace.

“Ni nakoshi.”

“Yauwa to sai allura kuma ko?”

Rayyern din ya fad’a yana me  gyara zamansa, tare da d’auko daya daga cikin alluran. 

Da sauri ta matsa nesa dashi, cikin dan yanayin roko, hawaye har yana fita daga Idanunta tace.

“Please Naan, Dan Allah kar kamin alluran yanzu, ka bari sainayi bacci na tashi kaji, please kaji Naan…”

Ta kare maganan tana me yarfa yan yatsun hanunta, cike da tsananin tsoro. 

Idanu Rayyern din ya zuba mata, aransa yana me matuk’ar mamakin irin yanda Jannart din, take matuk’ar tsoron allura. 

Fahimtar yanda duk take atsorace ne kuma, yasa shi dan tausasa murya.Cikin kulawa yace.

“Kwantar da hankalinku Naji bazanyi miki allura ba, tashi kije ki kwanta.”

Ajiyar zuciya mai karfi ta sauke, saboda Jin abunda ya fad’a d’inne kuma yasa, ta Dan lumshe Idanunta tare kuma da matsowa kusa dashi, murya araunace tace.

“ai bazan iya tashi ba, anan zan kwanta, jikina duk babu karfi.”

“Kinason sanyi ya sake kamaki ne? Ko kinason na miki allura, maza tashi muje daki.”

Ya fad’a yana me mik’a mata hannunsa.

Da sauri ta kama hannun nasa ta Mike tsaye, saidai tana tashi din taji jiri na neman kada ita, wanda hakan yasa da sauri Rayyern din ya tallafota, tare da kwantar da ita ajikinsa. 

Batare kuma daya jirayi wani abu ba, kaitsaye ya nufi bedroom d’insa da ita.

Ita kuwa ganin sun nufi bedroom din nasa ne, yasa ta karya fuska tare da d’agowa ta kallesa.

Ashagwab’e tace.

“Naan dakinka kuma? ka kaini bedroom dina mana….”

“Shiiii ni bazan iya kaiki bedroom dinki ba, kinji nauyinki kuwa saikace na buhun masara, taya yama mai nauyi kaman na doki, zai dauki mai nauyi kaman na buhun masara.”

Ya fad’i maganan yana me matse hannunta dake cikin nasa.

Da sauri ta kalleshi, saboda ta tabbatar abubuwan da tayi masa ne yake ramawa. 

Bakinta ta turo gaba cike da shagwab’a kuma, ta d’an muntsineshi wai ko zaiji zafi ya sauk’eta.

Duk da yajita amma bai kulata ba, ahaka har suka k’araso cikin d’akin nasa.

Suna shiga ya direta abakin gado, tare da komawa ya zauna yana meda numfashi, kamar wanda yayi aikin karfi. 

Wanda kuma yanayin hakanne kawai son rai, bawai Dan tana da nauyi ba, Dan hasalima Koda ya dauketa ji yayi kamar ya daga Y’ar shekara 13 ne. 

Itakuwa Jannart ganin hakanne yasa ta, sake shagwab’ewa tare da zamewa ta kwanta akan gadon.

Kamshi da kuma laushi da taushin gadon nasa ne kuma, suka sa tana kwanciya bacci ya dauketa. 

Yanayin yanda yaji saukan numfashinta, alaman tayi bacci ne kuma yasa shi tashi, ya gyara mata kwanciyarta tare da rufa mata blanket. 

Kaitsaye kuma ya fita daga d’akin.

Inda ya koma falo yaci abinci. 

Bayan ya gama cin abincinne kuma ya sake dawowa dakin, kasancewar yau din weekend ne babu aiki.

Ahankali ya d’an zauna abakin gadon.

Dai-dai lokacin ita kuma ta Dan bud’e Idanunta, cikin magagin baccin da take ciki hadi da shagwab’a tace.

“Naaan ni zan koma dakina.”

“To Malama ki koma dakin naki mana.”

Rayyern din ya fada yana me kallonta, tare da zamewa ya kwanta akan gadon.

Wanda kuma duk abubuwan da takeyi din yasan ba a hayyacinta take ba.

Itakuwa Jannart acikin magagin nata, Ganin ya kwanta akan gadonne yasa ta cewa.

“Ni gaskiya bazan kwanta dakai akan gado daya ba.”

“To ki sauka kasa mana, kona rikeki ne?”

Rayyern din ya fad’a yana me gyara kwanciyarsa. 

Itakuwa Jannart jin hakan yasa ta soma kokarin tashi, ashagwab’e kuma cikin yanayi mai kama da mayen da take ciki ta fad’a Kan…!

Back to top button