Uncategorized

Tubali Book 2 Page 11 Complete Novel

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

Idanu shima Rayyern din ya zuba mata, Ahankali kuma ya d’an nisa tare da gyara zamansa, atsanake yace.

“You’ll cooking why? Ko bakyason abincin restaurant din da nake kawo miki ne?”

Yayi tambayar Cikin kulawa, still kuma yana me kallonta.

Itakuwa Jannart Ganin irin Kallon da yakeyi mata ne, yasa tayi k’asa da kanta,  asanyaye tace.

“A’a kawai dai inason na fara girki ne.”

“Okay shima girkin yana cikin aikin da yasa Abba ce mu taho tarene?.”

Kai ta ɗan ɗago ta kalleshi ganin yadda ya tsareta da idone yasata yin ƙasa da kai.

“Abba yace mu taho tarene dan ki kula sani, so in Kuma na liƙa miki aikin girgi ai baki da lokacin kula dani, in dai da gaske kike kula da nidin zakiyi”.

Yayi mgnar cikin kauda kai dan shi kanshi mmkin kansa yake a kwanakin nan.

Ita kuwa Jannart a hankali tace.

“Toh ai shima kula da kaine”.

Da sauri yace.

“Toh shi na yafe ki bari sai mun koma gida, a nan dai cewa akayi ki kuladani da gadina ko”.

Ya ida mgnar murmushi ya tsubce mishi.

Ita kuwa  shiru, tai

“Kin ganeko?”.

Ya fada atakaice tare kuma da tashi, kaitsaye ya nufi bedroom d’insa, saboda dama bai shigo cikin gidan ba, saida yayi sallan Isha.

Da idanu ta bishi har saida taga shigewarsa, cikin dakin kafun ta tashi tare dakai plate and takeaways din kitchine, itakam yoghurt kawai tasha, tare da wuce wa dakinta ta soma buga game. 

Yana shiga bedroom nasa,

 ya rage kayan jikinsa kana nufi saman gadonsa ya kwanta. 

Idanunsa ya dan lumshe saboda wani irin daddad’an kamshi, daya bugi hancinsa, wanda yake tashi ajikin bedsheet din. 

Sake gyara kwanciyarsa yayi, tare da jawo laptop d’insa ya soma duba, sakonnin da suka shigo email dinsa.

Yana kwance ahaka kuwa bacci ya daukesa.

Yayinda a b’angaren Jannart ma hakanne ya kasance, domin tana tsaka da latsa waya, bacci mai nauyi ya dauketa.

Batare dako kofar d’akinta ta rufe ba.

Washegari.

Kamar yanda suka saba haka yau dinma, da sassafe kafun gari ya gama yin haske yayi musu ordern abincin.

Koda ya gama shiryawa kuma, abincin ya d’anci kadan, batare kuma daya jira fitowar Jannart d’in ba, ya wuce Azimut hotel Olympic Mascow inda zasuyi meeting.

Yayinda Jannart kuwa sai bayan ya tafin ta iya fitowa taci nata abincin.

*After 3days*

Ahaka suka ci gaba da rayuwa, Yayinda take iya kokarin ta wajen  kulawa dashi, domin aduk sanda ya dawo takan fito ta bashi abinci yaci, sannan kuma akan Idanunta yake shan magungunan sa kana ta gyara masa ɗaki, a hankali wata iriyar sassayar shaƙuwa ta ɗan fara ratsa zuƙatansu. 

Tun daga wancan ranan da sukayi maganan kayan abinci kuwa, bai sake dago mata maganar ba, har zuwa yau din kuma bai kawo kayan provision dinba.

Itama kuma ganin yayi shiru shiyasa bata sake ce masa komai agame da hakan ba, duk abunda ya kamata kuwa tana yi mishi.

Domin kullum bayan ya fita takan shiga ta gyara masa d’akinsa, tare da wanke masa toilet.

Saidai kuma dare nayi kowannensu yake kama gabansa.

Bata shiga d’akin nasa da dare ne kuma, gudun kada ya sake koranta kamar yanda yayi mata a wancan ranan duk da tana ganin sauye-sauye sa yawa daga garesa.

Ranar yau ta kasance Tuesday, kuma yaune zasu fara gwaji akan heart surgery, wannan dalilin yasa gaba d’aya, Doctors din a ankare suke.

Kowa ya shirya tsab tare da fatan samun nasara.

Kamar yanda ya saba kuma ordern abinci yayi musu, bayan ankawo yaci nasa ne kuma, ya d’auki briefcase d’insa ya wuce Hospital.

Koda ya karasa Hospital din already ya samu duka Doctors din, kasancewar shi kawai dama ake jira, shiyasa yana zuwa suka shiga theater room dan fara aikin. 

Acan gida kuwa Jannart kwata kwata, ko fitowa yau din batayi ba, bacci tasha ta koshi, Koda ta tashi daga baccin kuwa game ta d’anyi awayanta, kana daga bisani bacci b’arawo ya sake d’aukarta.

Atak’aice dai haka ta k’are wunin ranan, batare da ta fito taci abincin da Rayyern din ya ajiye mata ba.

Asashin su Rayyern kuwa komai ya tafi musu yanda suke so, domin kuwa har sunyi surgery din, kuma komai yayi kyau, inda kowannensu ya fito da kyakkyawan result. 

Bayan sun kammala duk wani abun da zasuyi ne kuma, kaitsaye ya nufo hanyar dawowa gida, saboda yau din duk agajiye yake jin kansa.

Kafun ya karaso gidanne kuma ya tsaya, a wani restaurant ya saya musu abinci.

Koda ya karaso gidan bayan ya gama dai-dai-ta parking din motarsa, anutse yake tafiya har ya k’araso cikin falon,  yana shigowa kuwa ya soma kokarin zare, suit din dake jikinsa, yana acikin hakanne kuma idanunsa suka sauka akan takeaway din daya ajiye mata tun safe, Wanda kwata kwata babu alaman an tab’ashi.

Idanunsa ya d’an kankance cike kuma da mamaki yake Kallon takeaway din. 

Ahaka har ya karasa shigowa cikin falon.

Saboda ya tabbatar da abunda yake zargi ne kuma, ya sashi bud’e takeaway din, Aikuwa abincin yana nan babu alaman ko cokali daya anyi.

Ajiyar zuciya ya d’an sauk’e tare kuma da juyawa, ya kalli kofar dakinta dake kulle.

Ahankali kuma ya janye idanunsa daga Kallon dakin, ledan dake hannunsa ya ajiye, Kaitsaye kuma ya wuce bedroom d’insa.

Yana shiga ya soma rage kayan jikinsa, tare da wucewa toilet yayi wanka hadi da dauro alwala, kasancewar ankusa kiran sallan magriba.

Yana fitowa awankan kuwa mai kawai ya shafa, sai turare wanda shafasa ya zame masa d’abi’a.

Anutse ya zura wata army green jallabiya ajikinsa, wayarsa da kuma key din motarsa ya dauka, kaitsaye kuma ya fice daga falon, bayan ya saka wasu slippers a kafafunsa.

Koda ya fito falon zama yayi Ganin akwai dan sauran lokaci ne kuma, yasa shi zama ya d’anci abincin kad’an. 

Bayan ya kammala ne kuma ya shiga, kitchine ya kuskure bakinsa,  batare da wani jinkiri ba kuma, ya juya kaitsaye ya fice daga cikin falon.

Cikin sa’a kuwa yana zuwa masallacin ana shiga sallan, hakan yasa da hanzari ya shiga jam’i.

Bayan sun idar da sallan kamar yanda ya saba, zama yayi a masallacin har saida suka sallame sallan Isha, Kafun ya kama hanyar dawowa gida.

Again Yana shigowa falon takeaway din abincin daya ajiye ya kalla, saidai ganin bataci abincin ba kamar yanda ya ajiye haka yazo ya samu,  ya sashi d’ago kansa fuskarsa d’auke da  yanayin mamaki yake Kallon kofar dakinta.

Inda yake jiyo sautin muryarta na tashi, wanda da’alama kuma waya takeyi.

Ahankali ya dan matsa kusa da kofar nata, dai-dai lokacin kuwa yaji sautin muryarta na fadin.

“Okay My Aunty Insha Allah zan kiyaye, eh zan bashi number Hajia Rabi’ah wata ƙil zai yarda ya amso min su.”

Ajiyar zuciya ya dan sauke, saboda Jin muryar nata ya tabbatar masa da cewar tana lafiya.

Kasancewar babu abunda zaiyi acikin falonne kuma, yasa shi juyawa ya wuce bedroom d’insa.

Yana shiga kuwa ya zare jallabiyan dake jikinsa, tare da komawa ya kwanta akan gadonsa, had’e da lullub’awa jikinsa blanket, kana ya jawo system d’insa ya soma latsawa. 

Yana nan ahaka har bacci ya daukesa.

Jannart kuwa har dare ya raba bata fito taci abincin ba, tun tana buga game awayarta kuwa, har bacci b’arawo ya dauketa. 

Washegari.

Yau dinma tun kafun ya fita yayi musu order.

Kamar yanda ta saba ay’an kwanakin kuma, ita da kanta ta zuba masa abincin a plate yaci.

Saidai ita bai ga alaman zata ci ba, Dan komawa can gefe tayi ta zauna.

Ahaka harya kammala cin abincinsa ya tafi.

Ita kuwa Jannart Ganin ya tafi ne, yasa ta tattare wajen daya ci abincin.

Batare kuma da ita taci ba ta koma d’aki tayi kwanciyarta dan fruits take dan ci in taji yunwa kasancewar akwaisu a Fridge. 

*some hours ago*

Ahankali ya daura hannayensa akan waist d’insa, tare kuma da fesar da wani irin numfashi.

Abincin safe da kuma na daren daya ajiye mata, wanda duk bata ci ba ya kuma kallo,  Cikin yanayin tsananin mamakin kwana biyu da ta dauka, bata saka abinci acikinta ba, ya dago ya kalli kofar dakinta.

Yayinda acikin ransa yake tambayar kansa, abunda zai hanata cin abinci har na tsawon 2days.

Wani tunani da yazo cikin ransa ne kuma, yasa shi juyawa ya nufi bedroom d’insa.

Jannart dake dakinta kuwa, tana sane bawai kuma tana kin cin, abincin bane saboda wani abu na daban, kawai dai tana yin hakanne saboda tana son, ya tuna da maganan kayan provision dinsu, ba ya ga haka kuma, ta gaji da cin kalan abubuwan da yake kawo mata din, shiyasa yanzun kawai take shan fruit.

Rayyern kuwa Koda ya shiga dakinsa, kwanciya yayi  tare da lumshe idanunsa.

Ahankali yake sauke ajiyar zuciya, Yayinda acikin ransa yakejin, rashin Jin dadin cin abincin da Jannart din batayi ba.

Wani abu daya sake tunawa ne kuma, yasa shi tab’e bakinsa tare da d’age kafad’unsa, cikin halin ko in kula yace.

“Wannan damuwarta ne, bataji yunwa bane.”

Daga can wani b’angare na zuciyarsa kuwa, sai yaji kaman abunda ya fada din ba dai-dai bane, domin har abada bazai tab’a manta irin yanda tayi kuka sosai akansa ba, ta tsaya dashi alokacin da yake halin buk’atar taimako, ta kula dashi sosai more especially akan lafiyarsa ya lura tunda yayi ciwo take bashi kula ta musamman mai cike da tausayawa ta kula dashi fiye da yadda Abbanshi, da Mamy da Ramadan kan kula dashi in ciwonsa ya tashi.

Yanaji ajikinsa bai kyautu yayi mata haka ba, kodan abubuwan da tayi masa.

Ahankali ya fesar da wani irin numfashi, tare da mikewa atsanake ya karasa gaban drawern sa.

Wani riga da wando ya ciro, tare da saka kayan ajikinsa, kaitsaye ya nufi hanyar fita daga dakin. 

*Nigeria.*

Alhaji Idi Sale Dakata ne ke zaune, acikin tamfatsetsen falonsa, Yayinda Abba Kabir ke zaune acan gefensa.

Zugum haka suka zauna kowannensu da irin abunda, yake sak’awa acikin zuciyarsa.

Dai-dai lokacin kuma Momy ta shigo, ta iskesu acikin irin yanayin, Dan jim tayi tana me nazartarsu, domin da dukkan alamu ta fahimci cewar, wani magana suka tattauna atsakaninsu, wanda hakan yasa duk sukayi jigum. 

Ganin mood din nasu ne kuma, yasa Momyn juyawa ta koma, batare da ta ce kala ba, saboda ma ta lura kwata kwata su Abba Kabir din basu ganta ba.

Acan Mascow kuwa Jannart ne ke kwance, Yayinda wayanta ke sakale akan kunnenta, tana waya da Riyyam nsra, wanda ya hadata da Mammy da kuma Zaytoon suka gaisa.

Rayyern kuwa Koda ya fito daga cikin dakin nasa, sosai yayi kyau cikin shigar dake jikinsa.

Inda ya daura babban jacket akan shigar tasa, saboda wani irin matsanancin sanyi da akeyi.

Dan jim yayi tare da Kallon ƙofar nata, acikin zuciyarsa yake tunanin me zai fada mata, sanin bashi da wani abun cewa ne kuma, yasa shi nufar dakin nata kai tsaye.

Ahankali ya tura kofar dakin ya shiga, bakinsa dauke da sallama. 

Jin alamun bud’e kofar dakinne kuma, yasa Jannart dake zaune saurin juyowa suka had’a idanu dashi. 

 Wayar dake kunnenta ta zare, tare da tashi ta zauna tana me fuskantar shi.  

Cikin kuma Dan yanayin mamakin ganinsa acikin dakin tace.

“Naan.”

Idanunsa ya zuba mata, saboda ganin yanda duk saman breast dinta ya bayyana, kasancewar wuyan rigar dake jikinta ya zame batare da tasan hakan ba.

Ahankali ya karasa shigowa cikin dakin, tare da karasawa gaban dressing mirrorn ta, inda yaga wani cup ajiye agefe.

Lek’a Cikin kofin yayi wanda yake dauke da zuma.

Juyowa yayi ya kalleta, hakan ne kuwa yasa da sauri tayi kasa da kanta tana murza yatsun hannunta.

“Meye kike wani sunkuyar dakai, sai kace kinga Dodo.”

Kanta ta girgiza masa alaman “A’a.”

Still batare kuma da ta dago Kanta ta kalleshi ba.

Shikuwa Rayyern idanunsa ya cigaba da tsura mata, Ahankali kuma ya matso kusa da ita, tare dasa hannunsa acikin aljihun wandon sa, cikin tsareta da idanu yace.

“Meyasa bakya cin abinci, tell me mekike ci Janna?”

Kanta ta girgiza masa alaman “Babu.”

Still kuma bata dago ta kalleshi ba, haka kuma bata motsa labb’an bakinta ba.

Shikuwa Rayyern Ganin hakan ne yasa shi, bata fuska cikin tsare gida yace.

“Almost 2days baki ci abinci ba, meyasa ahaka kikeson kina rayuwa, bakisan cewar rashin cin abinci, yana haifar da Ulcer ba?”.

Saurin dan satan kallonsa tayi, saboda Jin abunda ya fada din, kasancewar tasan halinsa shine ma gwani wajen Kin cin abinci. 

 Amma wai yanzu da bakinsa yake fadin hakan.

Fuska tadan kwabe ashagwab’e kuma cikin narkar da murya tace.

“Nifa banason abincin ne, bayamin dadi kuma nace maka ka saya mana kayan provision amma kaki..”

Ta kare maganan tana me tura bakinta gaba.

Wanda hakan yasa shi dan lumshe idanunsa, ahankali yace.

“To kenan idan bake kika dafa abincin ba, bazaki ci ba?”

Sake kwabe fuska tayi, still a raunace tace.

“Ni fa yanzu ma yunwa nakeji sosai, kuma ni banason wancan abincin.”

Idanunsa yadan zuba mata, Cikin yanayin nazartar ta yace.

“Okay wani kalan abinci kikeso?”

“Nigerian Dishes nakeso, ba irin way’anda kake kawowa ba.”

Ta fada tana me karyar da wuyanta gefe.

“Nigerian dishes? a Mascow dinne zaki samu Nigerian dishes? like bakisan awacce k’asa kike ba ko?”

Yayi maganan yana me kallonta, Domin har yanzu idanunsa na gane masa saman breast dinta dake waje da nimples ɗin ta da suke tsaye cas. 

Jannart kuwa Jin abunda ya fad’a dinne, yasa ta kwab’e fuska tare da yin rau rau da Idanunta.

“Alright Oya taso mu tafi.”

Rayyern din ya fad’a, yana me duba agogon dake daure  atsintsiyar hannunta. 

Itakuwa jin abunda yace dinne yasa ta tashi ta tsaya.

Kallonta ya somayi daga sama har kasa, inda take sanya da dogon wandon pencil jeans, sai kuma t-shirt mai fadin wuya, akanta kuwa hulan sanyi ne, sai kuma kafarta da ta sawa safa.

D’an soma Kallon dakin yayi, inda ya sauke idanunsa, akan wani shararan riga mai kaman abaya dake gefen gadonta.

Daukan rigan yayi tare da mika mata.

“Idan kinsa ki sameni a falo.”

Ya fadi haka yana me juyawa ya fice daga dakin. 

Jannart kuwa jin hakanne yasa ta saka riga mai kaman abayan, tare da daukan wani karamin vail ta yane kanta dashi. 

Cikin dan sauri ta saka wasu takalma sau ciki akafanta,  wayarta ta dauka batare kuma da b’ata lokaci ba, ta rufa masa baya. 

Koda ta fito falon hanyan waje taga ya nufa, wanda hakan yasa ta d’an tsayawa cikin sanyi tace. 

“Naan Ina zamuje?”

“Restaurant.”

Ya fada atakaice batare kuma daya juyo ya kalleta ba.

Itakuwa jin hakanne yasa ta gyara mayafin jikinta, cike dajin dadin fitar da zatayi a karo na forko tunda suka zo, ta rufa masa baya, Dan hakanan sai taji wani farinciki, saboda tun da suka zo Mascow din bata fita ba ko sau daya. 

Koda suka karaso wajen motar tasa, cikin zumudi ta bud’e murfin motar ta shiga.

Shi kansa Rayyern ya lura da irin farincikin da take ciki, wanda hakan yasa shi jin wani irin abu a Cikin zuciyarsa.

Yana shiga cikin motar ya tada ita kaitsaye suka fice daga Cikin gidan. 

Suna hawa kan titi ne kuma karamar wayar tasa dake hannunta ta soma kara,  Ganin sunan Riyyam-nsra na yawo akan screen din wayar ne kuma, yasa ta d’agawa tare da kara wayar akan kunnenta.

Daga can b’angaren Riyyam-nsra din yace.

“My Aunty dazu muna waya dake kika katse lafiya kuwa?”.

Murmushi tayi cikin kuma kasa boye farin cikinta tace.

“Sorry Riyyam Hamma ne yake kirana zamu fita shiyasa na katse.”

Murmushi Riyyam-nsra din yayi, cikin jin dadi yace.

“Ahh Lallai To sai kun dawo.”

Yana gama fadin haka ya kashe wayan.

Ita kuwa Jannart juyowa tayi ta ɗan kalleshi a hankali tace.

“Naan”.

Shima ɗin juyowan yayi ya ɗan kalleta, tare da cewa.

“Na’am Janna”.

Cikin yanayin sanyi tace.

“Uhum dama akwai sakon da aka iko min ne daga Nigeria”.

Da sauri yace.

“Saƙon me kuma A wurin waye?”.

Gyara zama tayi tare da cewa.

“Magungunan sanyine da turaruka Aunty na ta aiko min, sabida ciwona kuma da yanayin sanyin garin”.

A nitse yace.

“Toh zamu amsoshi”.

Wayarta ɗago tare da cewa.

“Sai dai in kira Aunty  Rabi’atu sai kuyi mgn ta gaya maka inda take, muje ko”.

Kai gyaɗa mata, yana mai kallon titin,

ita kuwa da sauri ta kira Hajia Rabi’ah kana ta bashi waya,

a mutunce suka gaisa kana tayi mishi kwatancen masauƙin.

Miƙa mata wayar yayi tare da cewa.

“Mu fara zuwa can dan muna kusa da inda suken.”.

Haka kuwa akayi tafiyar 13mnt sukayi suka riski gidan.

Mutunce aka tarbesu.

ganin kamar sauri sukeyine yasa ta ɗauko kayan ta bata, kana ta rakosu har wurin mota.

A sit ɗin baya ta ajiye katon ɗin tare da shiga gaba, kana yaja mota suka tafi.

Tafi kaɗan  suka iso wani babban wajen shak’atawa Victory park wuri mai masifar kyau da kayan k’awa.

Parking motar yayi ya fita, jim kadan kuma sai gashi ya dawo hannayensa rike da robobin ice cream. 

 

Gyara zamansa yayi, tare da ɗan juyowa ya kalli fuskarta mai kewaye da yanayin ta na sanyin rauni,

Mik’a mata yayi tare da cewa.

“Kina sha?!”.

Da sauri ta gyaɗa mishi kanta,

Tare da miƙo hannunta ta kama rubar, a hankali ya d’an kauda idanunsa tare da sa yatsunshi kan nata ya manna a jikin robar mai masifar sanyi.

“Sheyyyhhhhh”.

Taja wani irin dogon sauti sabida masifar sanyin da taji yana ratsa yatsunta.

Shi kuwa Rayyern wani irin yar-yar haka yaji tsikar jikinsa na zubawa sabida sautin da taja ya gigita masa kwanya,

“Ahshhhhy Naan sanyi”.

Ta faɗa cikin wata iriyar sassayar murya”.

Juyo da kanshi yayi ya fuskanceta tare da jingina kan nasa jikin kujera.

A hankali ya turo harshensa waje kad’an ya d’am laso lips ɗinshi, still bai sake mata hannunba, 

Cikin wata iriyar fitinenneyar murya yace.

“Kin cika raki sanyi nefa ba zafiba”.

Yayi mgnar yana tsareta da narkakkun idanunsa.

Rau-rau tayi tare da kwaɓe fuska.

Ƙara matse hannunta yayi.

“Ahsssshyyy Naan zafeeeeeh!”.

Ta kuma sakin ƙara da ɗan ƙarfi.

Bakinshi ya ɗan tura tare da cewa.

“Raki ki koyi juriya da kame bakin nan da iface-iface kada wata rana kiyi abin kunya,”.ya ƙare mgnar tare da

Sake hannun nata  kana ya sa hannun kan siterin motar, sannan ya kifa kansa bisa tafukan hannunsa yayi shiru yana maijin wani irin masifeffen abu akanta ji yake tamkar ya ruggume ta ko zaiji sanyin abin.

Itama shiru tayi tana hurawa yatsunta dumin bakinta,

Shi kuwa Rayyern wasu tagwayen numfarfashin yake sauƙewa a hankali,

Kusan 56 second suka d’auka a haka

Kana ya gyara zamanshi Tare kuma da tada motar  suka kara gaba.

Itakuwa Jannart duk da tasan bata wani shan sanyi sosai, amma tana matukar son ice cream sosai.

Ga kuma yunwan da takeji, shiyasa batare da wani tsawaita tunani ba akan illar da zai iya mata ta soma shan ice cream din tanasha tana lumshe ido, shi kuwa Rayyern a fakaice yake kallonta.

Ahaka har suka isa wani  babban wurin cin abinci Russian pub restaurant wurine da akeji dashi a ƙasar wanda mutanen k’asashe ma banbanta ke zuwa shiyasa mafi akasari akwai abincin kasashe daban-daban ɗan wuri  yafi kowanne girma acikin garin na Mascow.

Suna isa kuwa ya bud’e murfin motar ya fito, Ganin hakanne kuma yasa Jannart din fitowa itama. 

Kaitsaye suka nufi cikin restaurant  din. 

Koda suka je Ab’angaren daya kasance na musamman suka zauna.     

Daya daga cikin Waiters na restaurant din  ne ya kawo musu menu.

Rayyern kuwa Kasancewar baya bukatar abincin ne, yasa shi mikawa Jannart din menu. 

Duk da cewar bata ga Nigerian dishes acikin jadawalin abincin ba, amma ta zab’i abunda take Ganin zata iya ci.

 

Take kuwa aka kawo mata abunda ta buk’a din.

Nan aka jera mata abubuwan da ta zaɓa,

Shi kuwa Rayyern gyara zamanshi yayi tare da d’an fesar da numfashin cikin zuba mata narkakkun idanunsa yace.

“Kici”.

Jin abinda yacene, da kuma yunwar dake zaƙularta yasa ta sa hannu ta dauki spoon tare da gyara zama kana ta fara ci. 

Yanayi tana kallon can woje kasan cewar akwai glasss mai ruwan garai-garai.

Kana iya ganin waje.

Rayyern kuwa Ganin ta soma cin abincin ne, yasa shi mikewa.

“Naan!”.

Tace ganin ya juya zai tafi,

Juyowa yayi ya dan kalleta,

Kanshi ya jinjina ganin kallon tambayar ina zakaje takeyi masane yasashi cewa.

“Kici ina zuwa zan d’an shiga cikin Mall d’in nanne”.

Kai ta gyaɗa mishi cikin gamsuwa.

Shi kuwa  kaitsaye ya nufi mall din dake cikin restaurant din.

Jannart kuwa da idanu ta bisa, kana kuma taci gaba da cin abincinta yanayi tana d’an lallatsa wayarta.

Dai-dai lokacinne kuma Azeez ya shigo cikin restaurant din, yana shigowa Cikin wajen daya kasance VIP ya

Zauma kujerar dage can gefenta wanda shima da glasss a tsakaninsu,

Bayan an kawo mishi abinda yake buƙata ne kuma ya ɗan fara ci,

Loma biyu ana uku ya ɗan ɗago kansa dan jin alamun akwai mutun gefensa, ai kuwa idanunsa sauka akan ta.

Cikin wani irin tsananin mamaki, kaɗuwa, al’ajabi  ya zaro Idanunsa waje cike da tsananin mamaki hadi da firgici ya mik’e tsaye, jiki na rawa ya ya soma nufo inda take zaune.

Saboda yana son ya tabbatar da cewa, idanunsa bawai gizo sukeyi masa ba.

Aikuwa isowar sa wajen ya tabbatar masa da cewar, bawai gizo idanunsa keyi masa ba.

Wannan dalilin yasa cikin tashin hankali da kuma firgici da tarin mamaki yace.

“JANNART.”

Da sauri Jannart din ta juyo saboda Jin muryar ɗan uwanta Yah Azeez d’in tayi acikin kunnuwanta. 

Aikuwa tamkar ba zata haka taga Yayan nata tsaye akanta.

  Da wani irin sauri ta Mike tsaye baki na rawa tace.

“Laah Yah Azeez”.

 batare da ta jirayi komai ba kuma ta fad’a jikinsa.

Tare da rungume sa kam kam cike da tsananin Jin dadi kuma tace. 

“Yah Azeez.”

Rungume ta sosai Yah Azeez din yayi sabida ganin abin yake tamkar a mafarki shiyasa ya ruggumeta gam dan ya tabbar ido biyune.

Dai-dai lokacin kuma Rayyern ya fito daga mall din,  fitowar tasa kuwa tayi dai-dai da rungumetada Azeez din yayi. 

Atake kuwa idanunsa ya sauka akansu cikin wani irin….!

Idanun nasa ya zazzaro waje cikin kuma yanayin tsantsar mamaki, yake Kallon Jannart din wanda take rungume akirjin wani Namiji wanda baimasan dashi ba. 

Lokaci daya kuma cikin few second yaji wasu irin abubuwa na yawo acikin brain d’insa, zuciyarsa kuwa wani irin zafi takeyi tamkar Wacce aka hurawa wuta.

Ransa yakai kololuwar b’aci musamman tunawa da yayi, cewar akwai igiyar aurensa akanta wani irin abu mai masifar ɗaci yaji ya tokari ƙahon zuciyarsa.

Jannart kuwa da tsananin farinciki ya cika zuciyarta, sake rungume Yayan nata tayi, Yayinda takejin wani irin nutsuwa da dadi acikin zuciyarta.

Yah Azeez din kuwa ahankali ya tallab’o kanta, muryarsa adan raunace, da kuma tsananin mamakin ganinta ak’asar da yayi yace.

“Jannart kece? I can believe inajin har yanzu kaman mafarki nakeyi.”

Sake rungumeshi sosai Jannart din tayi, cike da matsanancin farincikin da take ciki kuma tace.

“Nice Yah Azeez bawai mafarki kakeyi ba, nayi kewarku sosai, Nayi kewarka Yah Azeez.”

Ta kare maganan cikin rawan murya, tare da jin wasu irin hawaye na kokarin, cika Idanunta.

Yah Azeez kuwa Ganin hakanne yasa shi, tallafo hab’arta tare da Kallon fuskarta, bakinsa dauke da tarin tambayoyi yace.

“Jannart Meya kawoki Mascow? Jannart ke dawaye kukazo? Meyasa kikabar gida Jannart Meyasa? Kowa yana cewa kin b’ata hankalin su Daddy duk atashe yake akanki? Jannart wa ya kawoki k’asarnan???”

Yah Azeez din yayi mata duka tambayoyin, cikin tsananin damuwa da kuma wani tarin fargaba, saboda bayason ya yarda da abunda zuciyarsa ke fada masa, cewar Jannart din guduwa tayi ko ta biyo saurayine.

Dai-dai lokacin kuma Rayyern dake tsaye, wanda zuwa yanzu ya gama cika fam, zuciyarsa tafasa take sosai, Yayinda ransa kuwa yayi masifar b’aci idanunsa har rufewa sukeyi, ahasale kuma cikin takaici ya soma takowa zuwa inda suke. 

Jannart kuwa jin tambayoyin da Yah Azeez din keyi mata ne, yasa ta dago idanunsa da suka cika da k’walla ta kalleshi,  bud’e bakinta da niyar yin magana da tayi, yayi dai-dai da isowar Rayyern wajen.

Ransa amatukar b’ace yasa hannunsa d’aya ya damko Jannart din, tare da janye ta ajikin Azeez, ahasale kuma cikin fad’a, da b’acin rai ya saka hannunsa d’aya akan kirjin Azeez ya turesa gefe.

Cikin bayyana tsananin b’acin ransa, ya watsawa Azeez din wani irin mugun kallon da yasa hantar cikin Azeez kad’awa.

Taune lip d’insa na k’asa yayi tare da nuna masa yatsa afad’ace yace.

“You’re very stupid man, waye kai da zaka zo ka rike min matata haka? I say Who are you?” 

Ya k’are mgnar da karfi cike da hautsinewar tunani.

Idanu Yah Azeez ya zubawa Rayyern din, wanda yafi yi masa kama balarabe, saidai jin yayi Hausa ne yasa shi kankance idanunsa, shima ransa ad’an b’ace yace.

“Bakai zaka tambayeni ni waye ba, ni zan tambayeka ko kai waye, akan meye zaka zo ka tureni haka? Kasan ko ita din wacece awajena, waye kai meye kai sannan akan meya zaka janye ta daga gareni, meye alak’arka da ita da har kake cewa matarka wanne ubanne ya aura maka ita!?”.

Wani irin buguwa Jannart taji zuciyarta tayi, saboda ita sai ayanzu ne ma take tunawa, da cewar babu wanda yasan inda take.

A matuk’ar tsorace ta dawo da kallonta ga Yah Azeez, wanda yake jifahta da Kallon tuhuma, Yayinda shi kuwa Rayyern gaba daya ma yanayin fuskarsa ta sanja, idanunsan nan sunyi jajur, haka ma fuskarsa dake bayyana alamun bacin rai. 

Wani irin tsorone taji ya kamata, wanda hakan yasa ta rumtse Idanunta.

Rayyern kuwa wani irin hautsinennen kallo ya watsawa Azeez, din Cikin yanayin bacin rai kuma yaja wani irin dogon tsuka, tare da bangaje Azeez din.

“Tamyata kakeyi akan matata mallakina dana biya sadaki aka ɗauka mana aure da cikakkun shaidu kamar yadda musulunci ya tsara, akan matata sirrina kake cemin haka Stupid kawai.”

Ya fad’a in don’t care manner.

Batare dako Kallon Azeez din ya sake ba, ya damke hannun Jannart, tare da janta cikin zafin Rai suka nufi hanyar fita daga restaurant din. 

Ganin hakanne kuma yasa Azeez rufa musu baya, cikin tsananin mamaki da rudu yake cewa.

“Hey you stop, ina zaka kaita meye hadinka da ita, da har kakeson guduwa da ita?!!!!”

Yah Azeez din ya fad’a da d’an k’arfi, adai-dai lokacin suka fito daga restaurant din.

Jannart kuwa Ganin idanun Rayyern din sun rufe da b’acin rai ne, yasa ta soma dan jujjuya kanta,  cikin muryarta dake fitar da sautin kuka take cewa.

“Naan please leave me, Dan Allah ka tsaya kaji please Naan ka tsaya nayi maka bayani pleaseeeeeee….”

Ta kare maganan cikin tsananin damuwa, tare kuma da dan waiwayawa tana Kallon Yah Azeez dake biyosu.

Sam Rayyern kam kamar ba dashi ma Jannart din take ba, kwata kwata yaki sauraranta, hasalima ji yake tamkar ya fara buga wasan, kwallo da ita awajen tsabar takaici.

Dai-dai lokacin suka iso bakin motarsa, gefen me zaman banza ya bud’e, batare da tunanin ko zataji ciwo ba, ransa amatukar bace ya cillata cikin motar, tare da maida murfin motar ya rufe gib.

Cikin fusata ya juyo ya shige cikin motar shima, tare da yi mata key ahasale ya cillata kan titi.

Ganin hakanne kuma yasa ran Aziz sake b’aci, afusace shima ya tafi da gudu ya shiga tasa motar Dan rufa musu baya, saidai kafun ma ya tada nasa motar har sun hau kan titi. 

Tuni kuma wasu motoci sunsha gabansa, wanda hakan yasa motar su Rayyern din yi masa nisa, kasancewar kuma dare ne shiyasa cinkoson ta d’anyi yawa, saidai duk da haka bai dauke idanunsa daga kan, motar Rayyern dinba saboda bayaso su b’ace masa.

Rayyern kuwa wani irin gudu yake shararawa akan titin, tamkar wanda zai tashi sama,  wanda kuma daga gani kasan zuciyarsa cike take da bacin rai.

Hakanne kuma yasa ko Kallon Jannart din baiyi ba, wanda taji ciwo a hannunta sanadiyar wurgata acikin motar da yayi.

Jannart kuwa gaba daya duk ta rud’e, Yayinda hawaye ke gangara akan fuskarta.

Cikin tsananin damuwa da kuma magiya take cewa.

“PLEASE Naan dan Allah ka tsaya, kaji D’an uwa………”

“Shut up, ki rufemin baki ko na tattaki acikin motar nan zaki tsaya da aurena a kanki kina ruggume ko wani Tom and Jerry d’in!!!  In ruggumar kikeso ki gaya min Mana in ruggumeki ko na hanaki ruggumeni ne!!!!”.

Ya katseta ta hanyar fadin haka atsawace.

Tsawar da ya haifar mata da kad’awan yayan hanji, da kuma wani irin fad’uwar gaba, saboda tunda take dashi yaune kawai, taji yayi irin wannan tsawan, ga kuma wata irin murya da yayi mata magana dashi, mai saka mutum firgicewa. 

Numfashinta dake kokarin k’wacewa, saboda tsawan da yayi mata din ta fusgo, lokaci daya kuma taji wani irin matsanancin kuka, na taso mata.

Hakanne kuma yasa ta manna kanta da jikin glass din window’n motar, asanyaye ta saki wani marayan kuka, wanda  ita kanta batasan kukan na meye bane, na tsoron Rayyern dinne ko kuma na jimamin ganin Yah Azeez dinta ne, itama bata sani ba. 

Kasancewar kuma glass din windown b’angaren da take zaune, yana d’an sauk’e ne yasa duk wani snow da akeyi, yake busata Yayinda dusan kankara keta saukowa ajikinta. 

Rayyern kuwa duk da yana iya jiyo sautin tashin kukanta, amma haka yayi banza da ita, saima gudu daya ci gaba dayi tamkar wanda zai tashi sama.

Suna ahaka dinne kuma taga ya kama wata hanya ta daban, ba hanyar da suka biyo ba, domin duk da bata tab’a fitowa ba tunda suka zo, amma tasan inda suke bi yanzun ba hanyar gidansu bane.

Yah Azeez da har yanzu ke biye dasu kuwa, gaba daya awahalce yake tukin, saboda yanda motoci sukayi yawa agabansa, kasancewar tuni su Rayyern din sunyi masa nisa. 

Rayyern dake driving kuwa fahimtar Azeez din na biyosu ne, yasa shi shiga wata kwana mai yawan go slow, tafiya sukayi na tsawon 30mn kafun suka iso, gaban wani makeken  hotel d’in izmailovo alfa hotel, wanda aka k’awatasa da furanni masu matuk’ar kyau. 

Parking motar Rayyern yayi, batare daya jira wani abu ba kuma ya bud’e murfin motar ya fito.

Kaitsaye b’angaren da Jannart din ke zaune ya nufo, bud’e murfin motar yayi, tare da finciko hannunta ya fito da ita daga cikin motar. 

Ransa ab’ace yake sosai shiyasa bai damu, dako dusan k’ank’aran dake saukowa yana sauka akansu ba.

Musamman ita Jannart da bawani kayan kirki bane ajikinta, wanda tun acikin motan dusan k’ank’aran ya bata mata jiki. 

Kaitsaye wani park dake cikin hotel din suka nufa, suna isa wajen kuwa Rayyern din ya rike hannunta gam, tare da sunkuyawa ya durk’usar da, ita ak’asan wasu shuken shuken flowers suka zauna bisa kujera. 

Batare kuma daya damu da irin yanda dusan k’ank’aran ke dukansu,

Still har yanzu kuma yana rike da hannunta.

Saidai yanzun tafin hannayensu ne ke had’e. 

Dai-dai lokacin kuwa Yah Azeez ya shigo cikin hotel din, ganin motar mutumin dake tare da Jannart din da yayi a fake ne, kuma yasa shi saurin yin parking nasa motar shima, cikin hanxari  kuma ya fito tare da nufan cikin hotel din Kaitsaye, saboda shi atunaninsa sun shiga cikin hotel dinne.

Rayyern kuwa da yake Kallon Azeez din, ganin ya shiga cikin hotel dinne, yasa shi yin kwafa tare da sake jawo Jannart din, kaitsaye ya nufi wajen motarsa. 

Bayan sun shiga ne kuma yaja motar suka kara gaba.

Idanunta ta rumtse da karfi, tare kuma da matse jikinta waje daya, sosai jikinta yake karkarawa wanda hakan yasa numfashinta wani irin fusga sabida abubuwan sun had’e mata ga sanyin da tasha, ga na garin ga tsoro hakan yasa numfashin ya fara sauya salon fira. 

Har yakai ga sautin fitan numfashin nata, na ratsa cikin kunnuwansa. 

Juyowa yayi ya dan kalleta, tare kuma da watsa mata Harara, cikin  zafin zuciya ya cigaba da tuk’a motar, yana shara gudu tamkar mai tashi sama. 

Acan hotel kuwa Yah Azeez Kaitsaye receiption na hotel din ya nufa, saidai koda ya tambaya ko akwai mutanen da suka shigo yanzu, ce masa akayi babu.

Wannan dalilin yasa asanyaye ya fito daga cikin hotel din, yana fitowa kuwa idanunsa suka sauka, akan wajen daya bar motar Rayyern din.

Ganin babu motar awajenne kuma yasa shi dafe kansa, cikin takaici yace.

“Oh My God I lost them, who be this guy? Waye shi meye hadinsa da Jannart, nasani Jannart ba mutumiyar banza bace, saboda haka babu yanda za’ayi ace, tana da alak’a da mutumin da baisan koshi waye ba.”

Tsuka yaja tare dasa hannu ya  buga sterring motarsa, cike da takaicin rasa su da yayi yace. 

“Ina fatan sake ganinki Jannart, wancan guy din kuwa ko waye shi, saina koya masa hankali, koma meye ne ya faru asanadiyarka ne Junaid, saboda Kai da kuma banzan halinka ne, Jannart take cikin duk wannan yanayin, huuhhhhhhh.”

Ya fesar da wani irin numfashi mai zafi.

Asanyaye kuma cikin takaici ya koma cikin motarsa ya zauna.

Acan b’angaren Jannart kuwa zuwa yanzu, karfin hali kawai takeyi wajen kwato numfashinta, saboda wani irin sanyin da takeji, yana ratsa har cikin k’ashi da b’argonta.

Wannan dalilin yasa ta kankame jikinta waje daya.

Dai-dai lokacin kuma Rayyern din yayi parking motar, acikin wasu jerin motoci dake gaban wani had’add’en garden d’in Hermitage garden Mascow, wanda aka wadatasa da yalwan haske tako ta ina. 

Ahankali ya zare sit belt din dake jikinsa, tare kuma da juyawa ya kalli bayansa,  Ganin kuma babu wata mota dake bin bayansu ne, yasa shi bude murfin motar ya fito.

Still zagayawa gefenta yayi ya fito da ita, duk da cewar yanajin irin karkarwar da hannunta daya rike keyi, amma haka ya share tare da hade fuskar sa domin shi kansa bai san iya azabar fushin da ke ransaba wanda bai san na menene ba, ko kallonta kuwa baiyi ba sabida wani irin zafi da tafasa da zuciyarshi keyi ko gyabta idonsa yayi ganinta yake ruggume jikin Azeez, kaitsaye ya nufi cikin Garden din.

Suna shiga cikin kuwa ya sake hannunta, tare da nufan wani privet sit ya zauna.

Ahankali kuma ya juya yana me watsa mata Harara, saboda wani takaicin da yakeji,  abanza ta jawo masa b’uya tamkar  wani marar gaskiya ko b’arawo.

Jannart kuwa da duk jikinta ke karkarwa, Ganin irin Kallon da Rayyern din ke watsa mata ne, yasa ta kame jikinta waje d’aya, tare da rumtse Idanunta, saboda wani irin sanyi da takeji.

A kujeran dake facing nasa ta zauna, tare da sake kankame jikinta waje daya, hakanan ta samu kanta da wani irin tsoronsa, wanda ita kanta batasan kona meye ba.

D’aya daga cikin waiter na wajenne ya k’araso, tare da Dan rusunawa ya tambayesu me za’a kawo musu.

“Coffee.”

Rayyern ya bashi amsa atak’aice, Yayinda kasa kasa kuma yake hararan Jannart din, wanda daga inda yake din yana iya jiyo yanda, numfashinta ke fusga tamkar Wacce zata wacce tayi tsare.

Bakinsa ya d’an tab’e tare da kawar da kansa gefe, domin acan cikin zuciyarsa har yanzu, wani irin b’acin rai yakeji.

Cikin abunda bai wuce 5mn ba, waiter din ya kawo musu coffee two cup, wanda yake ta faman tururi saboda zafin da yake dashi.

 

D’an d’ago Kanta tayi ahankali ta saci kallonshi, Ganin kuma ba ita yake kallo bane yasa ta, d’aukan coffee din da sauri ta Kai bakinta.

Idanunta ta d’an lumshe tare da sauke ajiyar zuciya, domin duk da cewar coffee din akwai zafi sosai, amma hakan bai hanata kaiwa cikin bakinta ba.

Saidai kuma saboda tsananin sanyin da akeyi, yasa zafin Coffee din bai kona mata baki ba, madadin haka saima wani irin nutsuwa da taji yana saukar mata, Yayinda dumin Coffee din ke dumama mata hanjin cikinta.

Jin dadin hakanne kuma yasa ta shanye coffee din lokaci guda, domin dama bawai wani yawa ne dashi ba.

Ajiye cup din nata tayi ahankali tare kuma da turo dan karamin bakinta gaba, cikin rauni da kuma yanayin tsoronsa dake damunta, ta turo d’an k’aramin bakinta gaba. 

Still Ahankali kuma ta soma motsa labb’an bakinta, wanda da’alama wani abu takeson fad’a, amma kuma ta kasa saidai Kallon Rayyern din da takeyi kasa kasa.

Rayyern kuwa duk abunda takeyi yana lura da ita sarai, bawai kuma Dan idanunsa basa kanta bane, shi yake nufin baya kallonta, a’a kawai dai da idanun zuciyarsa yake kallonta, kuma duk hankalinsa yana kanta ne.

Jannart ko Ganin da gaske idanunsa ba’a kanta suke bane, yasa ta jawo d’ayan kofin Coffee din, wanda aka ajiye dominsa, batare da wani tunani ba ta kafa kofin abakinta, bata ciresa ba kuwa saida ta shanye coffee din tas.

Sai alokacinne kuma ya juyo ya kalleta, da sauri ta ajiye kofin dake hannunta, gudun kada yayi mata masifa ne kuma, yasa tayu rau-rau da ido tare da narke fuska.

Sai kuwa ta rumtse Idanunta, like masifan Idan yayi mata akan idanunta zai sauk’a.

Rayyern kuwa Ganin hakanne yasa shi, had’e fuska cikin muryar dakiya yace.

“Da kika shanye naki Coffee din, kika dawo kan nawa baki nayi? Kin iya shan abuna kice kina so in ruggumeki ne bazaki iya bako”.

Kanta tad’an girgiza Ahankali kuma Cikin yanayin tsoron kada, ya sake daka mata tsawa irin yanda yayi mata d’azu ta girgiza masa Kai alaman “A’a.”

Shikuwa harara ya watsa mata tare, da d’agawa waiter hannu kana yayi masa alama, akan ak’aro musu wani Coffee din.

Ita dai Jannart jin baiyi mata tsawan bane, yasa asanyaye ta bud’e Idanunta, tare da hade yan yatsunta waje daya, ta soma murzasu dan saboda sanyi, har ji take tamkar ba ahannunta suke ba.

Kamar yanda Rayyern din ya buk’ata kuwa, wani Coffee din aka sake kawo musu.

Tura mata kofi daya yayi gabanta, Yayinda shi kuma ya d’auki nasa ya soma sipping ahankali.

Jannart dake masifar jin sanyi kuwa, batajin zata iya sipping coffee din da kad’an kad’an, hakan yasa ta sake Kai cup din bakinta, bata ciresa ba kuma saida ta shanye duka Coffe din.

Wanda daga zamanta zuwa yanzu tasha 3cup kenan.

Har yanzu kuwa jarababben sanyin da takeji, yaki barinta saima kara shiga jikinta da yakeyi, kasancewar Cafe din da suke ciki, duk akewaye yake da shuke shuke, da yake cikin  garden yake haka wajen yake da shuke-shuke, wannan dalilin yasa wajen yake da sanyi sosai. 

Shiyasa har yanzu jikin Jannart din yaki daina b’ari, haka take ta karkarwa tamkar Wacce aka jonawa Shocking. 

Rayyern ahankali ya ajiye cup din dake hannunsa, tare kuma da d’ago kansa ya kalleta.

Rawar sanyi takeyi sosai, domin hatta hakwaranta suma karkarwan sanyi sukeyi, kayan dake jikinta ya dan soma karewa kallo, wanda gaba daya duk dusan kankara ya b’atasu, musamman Y’ar abayan dake saman kayan nata, hatta gashin kanta ma dusan k’ank’arane.

Kawar da kansa gefe yayi, tare da mikewa tsaye ya sake had’e fuskarsa sosai, rigar sweater’n dake jikinsa ya zare.

Tare da takowa ahankali ya dawo bayanta, cikin tsare gida da hade fuska, ya yafa mata  sweater din nasa ajikinta.

Wanda yasan hakan zai taimaka mata wajen rage sanyin.

Dai-dai ya juyo ne kuma idanunsa suka sauk’a, akan motar Azeez wanda tazo ta gilma ta wajen, ya hango motar ne kuma saboda duka wajen glass ne, wanda yake ciki zai iya hango komai dake waje.

“Oh my God wannan wanni irin mayene? Meyasa yake ta bibiyarmu? Why why???”

Ya k’are maganan cikin wani sabon b’acin rai, da kuma haushin ta da yakeji saboda itace ta jawo komai, domin da tun farko taci abincin daya kawo mata din, da yanzu basu fito har Suna wasan tsere da wani daban ba.

Ahasale ya sake kamo hannunta, batare kuma da ya bari ta gama mikewa tsaye ba, ya soma janta bayan ya ajiye kudin Coffee din da suka sha, akan table din kaitsaye suka fice daga wajen. 

Ita dai Jannart binsa kawai takeyi tamkar rak’umi da akala.

Suna shiga cikin mota kuwa yayi reverse, tare dayin yanke yabi wata hanyar na daban, wanda kuma yayi hakanne saboda, gudun kada su sake had’uwa da Azeez, wanda shi kwata kwata baisan waye shiba. 

Tafiya kad’an sukayi ba wani mai tsawo ba, suka iso gaban wani makeken hotel.

 Mascow Marriott Grand hotel, wanda kuma da dukkan alama hotel ne na musamman, da ko acikin garin ba kowane ke zuwa ba dan hotel ne daya amsa sunansa. 

Bud’e murfin motar yayi tare da fitowa, Ganin hakanne kuma yasa Jannart dake, duk’unk’une cikin sweaternsa, bud’e  murfin motar itama ta fito.

Ganin da yayi tana d’an waige waige ne kuma, yasa shi kama hannunta da karfi.

Haka suka nufi cikin hotel din yana gaba tana biye dashi abaya.

Koda suka k’arasa receiption d’aki ya kama musu, parlor and 1bedroom.

Bayan an basu key dinne kuma suka wuce sama.

 Suna shiga cikin y

Back to top button