Uncategorized

Tubali Book 1 Part 8 Hausa Novel Complete

 

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

Kai Abba ke jinjina masa cikin tarin gamsuwa kana a nitse yaci gaba da cewa.
“Kuma mun samu al’kama aciki sosai kusan buhu dari bakwai”.
Gyara zama Abba yayi tare da cewa.
“Ita al’kamar ba duk stores din hawa na biyu ita bane, bazatayi yawa ba?”.
A hankali ya ɗan kalli Abba tare da cewa.
“A’a bazatayi yawaba Abba sabida abubuwan buƙatunta da yawa, ita za’a sarrafa ayi fulawa kana a juyata ayi Sufageti da makaroni da indomie sannan za’a barta ita ɗaya ma.
Kuma yanzu anfi ta’ammali da irin abincin kana zamu fidda buhunan don buƙatun cikin gida kamar su hidimar ababen biki da masu ƙananan sana’o’in duk suna buƙatar fulawar”.
Gyara zama Abba yayi fahimtar yana tare da gajiya  da yunwa ne yasa shi cewa.
“Je kaci abinci kayi wonka zamu ƙarasa mgnar gobe da yamma”.
Kai ya gyaɗa kana ya miƙe ya fito.
Kai tsaye side ɗin sa ya wuce.
Wonka yayi mai rai da lfy ya shafa mai.
 Kana ya zaro.
Wasu tattausan yadin voyel mai masifar taushi  mai gidan dara-dara baƙi ne mai sheƙi ya saka.
Wanda yayi masifar mishi kyau farar fatarshi ta ƙara bayyana a ciki matuƙa gaya.
Wasu tattausan toms yasa Nevy blue masu masifar kyau kana ya kafa hular zanna bukar itama Nevy blue mai ratsin Black da royal blue.
Sajenshi ya konta lib sai sheƙi yakeyi tamkar yadin jikinsa fararen ƙananan kayan dake jikinsa suka ƙara haska kalar kayan inda ana iya ganinsu kaɗan ta dara-daran wani sassayan turarensa ya fesa.
Kana ya zari wayarsa ya zura a al’jihunsa kana ya nufo falon.
Cikin zumuɗi Riyyam-nsra yace.
“Wow Masha Allah, Hamma Rayyern dama haka kayan hausa fulani keyi maka kyau tubar kalla kai duk kayan da kasa sai sunyi maka kyau”.
Ya ƙare mgnar yana ƙoƙarin ɗaukarsa hoto.
Da sauri yasa hannunshi ya shafa ƙeyarsa lokacin da Rayyern ya ɗan ɗaka mishi mari cikin tura baki yace.
“Dan Allah ɗaya kawai”.
Bai kulashi ba.
Sai juya da yayi ya fuskanci Mamynshi,
hannunshi ya ɗaura kan cikinsa yana shafawa tare da kallon Mamy kana ya longobar da kai.
Murmushi Mamy tayi tare da miƙewa ta nufi Dinning table saninsa yasa ba sai yayi mgna ba take fahimtarsa.
Bayanta yabi yana kallon Ramadan tare da cewa.
“Me kakeyi a gida”.
Cikin tsoron kada ya korasa asibiti yace.
“Na gaji ne Hamma Rayyern kuma Dr Imran da Yah Sulaiman da Dr iley duk suna can”.
“Shine kuma yanzu Sulaiman yake cewa inje ana buƙata ta?”.
Kai ya ɗan shafa tare da fara inda-inda.
Shi kuwa tsaresa da ido yayi tare da nazartarshi kana a hankali yace.
“Kada ka zama maƙaryaci!”.
Da sauri yace to.
Wayarsa ce ta kuma ringing ganin Sulaiman ne yasashi miƙewa tare da buɗe Fridge Chocolate masu yawa ya ɗiba daskararru kana ya zaro goran ruwa da sauri haka yasa bai san wanda ya daskare ya ɗaukoba.
Cike da mamaki Mamy ta bishi da ido jin yana cewa.
“Mamy sai na dawo ana nemana a asibiti, Mamy abu mai ruwa-ruwa nake so in na dawo”.
Kai Riyyam-nsra ya jujjuya kana a hankali yace.
“Allah sarki Hamma Rayyern sam baya samun hutu, lokacin cin abinci ma rasawa yakeyi bawan Allah.
Dan Allah Hamma Ramadan muje ka tayashi”.
Kwaffa Ramadan yayi tare da dungure mishi ƙeya kana yace.
“Dan Allah Barshi shi baida wani uzuri sai aiki ni kuwa  ina fama da uzurin soyayya.
 taso mu tafi kaga Auntynka yaro”.
Ai kuwa da sauri ya miƙe.
Shi kuwa Dr  Rayyern Mai-nasara yana fitowa Hadi da PA suka miƙe.
Da sauri yace.
“Noh Hadi bari. PA mu tafi”.
Da sauri PA yace “Toh”. kana yabi bayansa.
Yana shiga motar yaja.
Hadi kuma ya buɗe musu gate, suka fita.
Saida suka fita sun hau titin da zai kaisu Mai-nasara Hospital ne ya ɗan miƙawa PA goran ruwan alamun ya buɗe mishi. 
Amsa PA yayi tare da cewa.
“A daskare yake fa”.
Hannu yasa ya amshi gorar ya ɗan jijjiga tare da jan tsaki sam rabinsa duk a daskare yake.
Aje goron yayi kana ya ɓalle ledan Chocolate ɗinsa ya fara taunawa da yawa-yawa sabida azabebbiyar  yunwar da yakeji.
A nitse ya zurawa motoci uku dake bayansu idanu.
Binshi sukeyi gadan-gadan kamar masu niyar takashi.
Da sauri  yayi kwana ya shiga hannun damansa.
Ga mmkinsa sai gashi sun biyoshi a guje har na gaban na gab da buga mishi motarsa.
Cikin ransa yace.
“Okay!!!” sai kuma ya juya hagu da gudu.
Cikin nitsuwa yace.
“PA ko zaka sauƙa!”
Da sauri PA yace.
“A’a muje in ba matsala, naga motocin nan binmu sukeyi fa, ba halin tsayuwa”.
Kai ya gyaɗa mishi kana ya juya akalar motarsa dan canza hanya.
Sabida sanin ana buƙatarsa a asibiti in ba don hakaba zai tsaya yaji dasu.
So amman ganin duk inda yayi suna biye dashi kamar inuwa ne yasashi juya akalar motarsa kai tsaye titin da zai kaishi Jan bulo ya nufa.
Ganin haka ne kuma yasa motocin nan uku suka tsagaita da binshi.
Gaba ɗaya ransa ya hatsala ya tafasa sabida yadda suka sashi dole ya fasa zuwa inda akeda buƙatarsa da neman taimakonsa ya nufi inda baya son zuwa.
Wani irin masifeffen tsaki yaja tare da taka motarsa ƙirar B.M.W. fara kal mai masifar kyau da sheƙi.
Takata yakeyi a fusace.
Kai tsaye layin gidan Alhaji Idi Saleh Dakata ya shiga.
A hasale yake danna horn babu k’ak’k’autawa wanda hakan yasa mai gadin buɗe masa gate ɗin jiki na rawa.
Yana buɗewa kuwa ya kutsa kai.
A can gidan Barrister Kabir kuwa.
Cikin tsoro Jannart ta kalli wayarta inda ta samu miss call 17. 
13 daga ciki na Yah Junaid ne biyu na Daddy ɗaya kuma Salman ɗaya Hajia Rabi’ah.
Murya na rawa tace.
“My Aunty  zan tafi kawai kinga har yanzu Abba bai dawoba ga Daddy ma nan yanata  kirana ga kiran Yah Junaid goma sha”.
Ganin yadda jikinta ke rawane yasa cikin sanyi tace.
“Toh gsky kam harda kiran Daddy kam kije, in ya dawo zaije yaji ko lfy”.
Ledan da take miƙa mata ta amsa tare da cewa.
“Nah shiga uku kinga yanzuma ga Yah Junaid yana kira”.
Ta ƙare mgnar tana nufar woje, Dijat na biye da ita a baya.
Tana fita sakarkarun suka muƙe da sauri ta shiga mota jiki na rawa Baba Ado yaja jin yadda take ce mishi.
“Baba Ado mu tafi mu tafi, awa uku Daddy ya bani gashi har biyar nayi.”
Ajiyar zuciya Dijat ta sauƙe lokacin da suka fita.
Jiki a mace ta koma cikin gida.
Su kuwa a 360 suka nufi gidan.
Cike da Mamaki Usman yake kallon Dr Rayyern Mai-nasara daya fita cikin motar fuska a murtuƙe yacewa mai gadin.
“Ina Ubangidan naku?”.
Cike da mamaki mai gadin ya kalleshi kana ya juyo ya kalli ƙofar babban falon Alhaji idi Saleh Dakata wanda daga nan bakin gate ana iya hangoshi.
Baya buƙatan ƙarin bayani sabida yadda mai gadi yayi ya tabbatar masa ogan nasu na ciki.
Kana kuma ga tarin takalma alamun da mutane a cikin.
Cikin wani irin taku mai cike da haiba ya nufi falon.
Yana zuwa yasa yatsunshi biyu ya ɗan bugi ƙofar.
Da sauri duk suka juyo suka kalli ƙofar Junaidu dake baƙin kofarne yasa hannunshi ya buɗe dai-dai lokacin kuma shima ya turo ƙofar.
Ganin  Dr Rayyern Mai-nasara na kutso kai cikin falon ne yasa Junaid matsowa tare da cewa.
“Kai lfy ina zaka je waye kai!?”.
Ya ƙare mgnar yana tsare gaban Dr Rayyern Mai-nasara din.
Wani irin kallon daya hautsina hanjin cikin Junaidu.
Rayyern ɗin ya watsa mishi,  tare dasa hannunsa ya dafe gefen kafaɗun Junaid da yatsu biyu kana ya tureshi da ƙarfi, har saida ya bugi gini kana yace.
“Matsa yaro ba wurinka nazoba wurin tsohonka nazo”.
Ya ƙare mgnar yana nufan cikin falon gadan-gadan.
Wani irin kallon mamaki shakka mai haɗe da tsoro Alhaji idi Saleh Dakata, da Alhaji Abdu Tababa, da Dr Lukman suke mishi kamar idanunsa zasu faɗo ƙasa.
Da karfi ya jawo kujerar dake gefenshi kana yasa ƙafarshi ya tureta guuuu ta tafi har gaban Daddyn Jannart cikin rashin tsoro ya zauna bisa kujerar tare da jawota ya motso shi da kyau suna fuskantar juna cikin kakkausar murya yace.
“Meh hakan! Me kake nemana kana tura waɗan can karnu kan naka nemana, gani gabanka, ka gaya min me kake buƙatar inyi maka da kake sawa ana bibiyata.
Nace me kake son inyi maka!!!”.
Ya ƙare mgnar da masifar ƙarfi tare da buga santer table ɗin dake gabansa har saida cups ɗin saman suka kwanta suka gangara ƙasa.
Kana hakan yasa duk suka kame jikinsu da zazzaro idanunsu.
Da sauri Alhaji Idi Saleh Dakata ya ɗagawa Junaidu hannu dan ganin ya yunkuro zai kama Rayyern.
Shiru sukayi baki ɗayansu, shi kuwa Rayyern cikin tafasan zuciya yace.
“Da ka barshi ya isoni ai.”
Yayi mgnar yana tsare Daddy da idanu.
“Mitssssss”. Yaja wani dogon tsaki tare da cewa.
“Ina da aiki mai mahimmanci ka sani na baroshi nazo nan dan inji uzurinka sannan kayi shiru kana zaro min jajayen idanu kamar na (DUJI)  to wlh hawainiyarka ta kiyayi Ramata.
Kada kasa in juyo kanka na wuni ɗaya wlh zaman kasar Kano zaifi karfinka.
Ya za’ayi ina girmama furfurarka kana kaucewa, to muddin baka kiyayeni ba tabbas zaka rasa gemun naka gaba ɗaya.”
Da sauri ya juyo ya watsawa Dr Lukman wani kallon da yasa shi jin zufa tun daka cikin naman jikinsa dan masifar tsoron da idanun Dr Rayyern Mai-nasara din ya bashi.
Cikin sauri yayi ƙasa da kanshi tare da cewa.
“Yaro man kaza lallai ka bimu a hankali dan wlh in kace zaka ja damu to wlh.
Ko na’urar jin bugun zuciya ka dena riƙewa.”
Wani irin gigitaccen tsawa ya dakawa Dr Lukman har saida ya miƙe tsaye dan firgita.
Da yatsa ya nuna shi kana ya jujjuyata sannan yace.
“Mu zuba Ni da kai magwaji ya gwada ya gani”.
Sai kuma ya kalli Alhaji Idi da Alhaji Abdu Tababa da suka zuro mayun idanunsu suka kafesa da ido suna masu nazarin wanne irin kisa ya kamata su yiwa yaron nan ne mai shegen taurin kai ko wani irin illa mafi muni za suyi masa rayuwarsa.
Cikin gargadi ya nunasu da yatsa kana yace.
“Wlh idan kuna cin ƙasa, to ku kiyayi ta curi.
ina mai tabbatar muku in baku kiyayeni ba zaku shiga uku.
Tun wuri ka gayawa waɗan can karnukan naka su dena bina, in kuwa ba hakaba zaka rubta rami.
Kada ku mance na gaya muku.
Idan nace zan taka mutun bashi da GARKUWA a kaina zan takashi domin tsakanina daku faɗane tsakanin gsky da ƙarya.”
Gaba ɗaya jikinsu tsuma yakeyi.
Yayinda Junaidu kuma zufar tsoro ta keto mishi.
Dai-dai lokacin kuma motocinsu Jannart suka shigo gidan.
Da sauri ya juya ya fita sabida hango sun da yayi kasan cewar ƙofar a buɗe take.
Yana isa wurin Jannart na fitowa kasan cewar ta bayanta yazo bata san ya isoba.
Wani ƙauuuuu taji lokacin daya yarfa mata wani irin masifeffen mari ta bayanta kuma kan kunneta.
Wani irin dummmm taji ya biyo bayan kauuu ɗin cikin gigita ta juyo…
Dai-dai lokacin kuma Barrister Kabir ke tsaye gaban Dijat dake mishi bayanin abinda yasa Jannart ta tafi.
Ta kara da cewa.
“Ɗan Allah Abban Hafiz ka bita, kaga meke faruwa kada Junaidu ya mata wani abu”.
Cikin sauri Barrister Kabir yace.
“Zai matama maza ku koma ciki bari inje”.
Ya faɗi mgnar yana komawa cikin motarsa.
Ita kuma taja hannun Hafiza tayi gaba Hafiz na biye dasu a baya.
Shi kuwa Barrister Kabir cikin gudu yake tuƙib ya nufi gidan yayan nasa.
A gidansu Jannart kuwa.
A falon Daddy cikin wani irin masifeffen hatsala Dr Rayyern Mai-nasara ya juya zai fita.
Har yaje bakin ƙofar sai kuma ya tsaya tare da juyowa ya kallesu kana yace.
“Wallahi Ni nan Muhammad Rayyern wargine dai-dai da ƙugun ko wanne mugun tsohon ɗan riba”.
Yana faɗin haka ya sako kai ya fito.
Dai-dai lokacin kuma Junaid yayiwa Jannart wani irin shaƙa mai ƙarfi kana ya wurgata ƙasa.
Hakan yasa ta saki wani irin raunataccen kuka mai masifar wahala tare da yunƙurawa ta kuma tasowa.
Tana mai yarfa hannun tare da ja baya gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi.
Wani irin gigitaccen mari ya kuma zuba mata kan kunneta wanda yasa ta buga wani irin tsalle tare da ihun wahala a tare.
Dai-dai lokacin kuma Rayyern ya iso parking lot ɗin.
Da sauri ya juyo ya kalli gefen da yaji ihun sabida karadin ihun ya cika masa kunne da ƙarfi har saida yaji kansa ya sara.
Siraran idanunshi ya zubawa fuskar yarinyar tabbas ya ganeta.
Kai ya rausayar ya juya tare da taɓe bakinsa alamun.
Oho yama kasheki in yaso kunfi kusa ai.
Barrister Kabir kuwa gudu yakeyi sosai sabida kiran Jannart da yayi har sau uku bata amsaba ya tabbatar masa ba lfy ba.
Shi kuwa Junaidu cikin tsananin mugunta da son huce haushinsa ya kuma shaƙo wuyanta.
Wanda yasata yin wani irin kakari tare da zazzaro idanunta woje.
*Dan girman Allah da Manzonsa da darajar iyayenki kada ki fitar min da littafina dan kin biya kudin karantawa bawai yana nufin kin mallakeshi bane, na roƙeki da isar zatin ubangiji daya bamu rai da lfy, don soyayyar manzon tsira dan mutuncin iyayenki kasa ki karantamin littafina in baki biyaba, tun forko kunsa littafina na kuɗine, kada ku tauye hakkina kuji tausayin maraicina*
Wanda kuma su Baba Ado da Ashiru mai gadi kab suka rumtse idanunsu da ƙarfi sabida ganin yana son kashe baiwar Allah.
Wani irin kallo Rayyern yayiwa Usman P.A dake cewa.
“Innalillahi zai kashe tafa”.
“Toh me ruwanka ba gidansu ɗaya ba”.
Dr Rayyern ɗin ya fad’a,
Waɗannan ƙattin samudawan kuwa suma cirko-cirko sukayi to ya zasuyi.
Ɗan uwanta ne wa zai hanashi in ba mahaifinsu ba.
Su kuwa su Alhaji Abdu suna jin ihunta amman basu fitoba hakama Daddy.
Mom kuwa dake wonka sauri-sauri takeyi dan ta samu ta fito.
Abdul kuwa gefe ya tsaya yana zubda hawaye.
Wani irin gigitaccen duka  fa Junaid ya fara yi mata tamkar zai ɗauke ranta.
P.A kam tuni shima hawayen tausayin yarinyar ya cika masa idanu.
Shi kuwa Dr Rayyern Mai-nasara cikin yanayin halinsa na babu ruwansa da shiga harkar da bata shafeshi ba,
yayiwa motar key kana ya tada ya juya akalarta zuwa bakin gate.
Hon ya danna amman ina Ashiru mai gadi baima san yanayi ba.
Cikin jan tsaki ya kuma danna horn still Ashiru baima san yanayi ba.
Shi kuwa Junaid cikin huce haushinsa ya daddage ya yarfa mata wani irin marin.
Da yasa ta saki ihu da ƙarfi.
“Wayyo wayyo Allah na Wayyo Mom Wayyo Abba  Yah Junaid zai kasheni Daddy”.
Bata ida rufe bakinta ba ya kuma zabga mata wani marin azabebben mari.
Wanda yasa jinin haɓo ɓallo mata ta hancinta.
Da k’arfi Dr Rayyern ya rumtse ƙwayar idanunsa, kana ya bud’esu a hankali.
Dai-dai lokacin kuma Abba ya iso bakin gate ɗin, ganin yanata dannan hon ba’a buɗe mishi bane yasashi.
Buɗe mota ya fito.yana fitowa yana jin ihunta.
Haka yasa ya kutsa kanshi da gudu cikin gidan ta ƙaramar kofar.
Dr Rayyern kuwa kashe motar yayi ganin ba’a buɗe mishi gate ba.
A hankali ya meda bayanshi ya jingina da jikin kujerar kana yasa hannunshi ya dafe saman marfin motar sabida yayi ƙasa da glasss ɗin.
Tallabe kanshi yayi da tafin hannunsa kana a hankali yace.
“Bari muga ƙarshen Game ɗinnan ko P.A”.
Cikin tausayi P.A yace.
“Sir zai kasheta fa”.
Ganin kallon da ya mishi da idanunsa da suka time zuwa launi jane ne kuma yasa yayi shiru.
Kana ya zuba musu ido ta cikin mirror motarsan sabida zuwa yanzu sun dawo bayanshi kusa da motarshi ƙanƙance idanunsa yayi tare da zubasu kan madubin yana kallon duk yadda Junaid ke mata.
Isowarsu bakin motar tasa ne kuma, yasa Junaid damk’o tarin sumar kanta, wanda gaba ki daya ya watse akan gadon bayanta, saboda tsananin wahalan daya bata,  irin damk’an da yayiwa fashion nata ne kuma yasa ta sakin wani irin azababben ihu, batare da ko gama rufe bakinta tayi ba, ya bugata da jikin motar.
Wanda hakan yasa   Ta fad’a kan motar, atake kuwa jinin dake zuba daga hanci da bakinta ya tsananta ya fara zurarowa har kan motarsa. 
Da ƙarfi ya rumtse idanunshi tare da kame jikinsa.
Da yaji zuciyarshi tana wani irin masifeffen harbawa da wani irin masifeffen tsalle kamar zata fito woje.
Dai-dai lokacinne kuma Abba Kabir ya shigo cikin gidan hankalinsa amatukar ta she.
Ashe kuwa baimaga komai ba a tashin hankali ba, saida yaga yanda Junaid din ya buga Jannart ajikin mota. 
Wanda hakan yasa ko ihu mai karfi ta kasa fitarwa, ga kuma jinin dake ci gaba da fita ta hancinta ba ƙaƙƙautawa.
Cikin wani irin tashin hankali kiɗima maitsanani Abba Kabir ya nufosu a guje.
Shi kuwa Dr Rayyern Mai-nasara wani irin masifeffen tsuma yaji naman jikinshi nayi gaba ɗaya babbar yatsarshi da Jannart ta fasa mishi had’uwarsu ta forko sai wani irin karkarwa takeyi.
Abba kuwa yana gudun nufosu yana.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun. Junaid! Junaid!! Junaid!!! Baka da hankali ne kasheta zakayi ne. Kai wanne irin azzalumi ne!?”.
Ya ida mgnar yana isa inda suke.
Batare da wani jinkiri ba kuwa ya d’auke Junaid da wani irin gigitaccen Marin da yasa Junaid yayi tagal-tagal ya koma baya,
Cikin tsananin fusata da makatar  ido da zuciya yasa hannunshi duka biyu, ya hankaɗeshi, saida ya faɗi ƙasa.
Abu da ɗan giya dama ba ƙarfi ba.
 
Jikinsa na rawa kana kuma Ransa amatukar bace yace.
“Baka da hankali ne Junaid wannan wani irin dabbanci ne, ko kasheta kakeson yi?”
Abba din ya fada amatuk’ar tsawace.
Tare kuma da sunkuyowa  kan Jannart dake kwance akan motar Dr Rayyern jini na ci gaba da fita ta hanci da bakinta.
“Jannart! Jannart!! Jannart!!!”.
Ya kirata da azaban ƙarfi cikin tarin ruɗani.
Wanda sautin kiranta da yayine yasa Dr Rayyern Mai-nasara buɗe kwayar idanunshi da suka sauya launi daga fari zuwa jazir.
Idon ya zuba musu ta cikin madubin yana ganin yadda Barrister Kabir yake jijjigata a gigice yana mai cewa.
“Jannart Bud’e idanunki nine Abbanki ne yazo bud’e idanunki Jannart!!!” 
Barrister Kabir din ya fada da muryarsa wacce tayi rauni sosai, kana kuma yana me dan jijjigata tuni ya gama gigicewa gaba ɗaya jikinshi rawa yakeyi rauni mai tarin yawa ya rufeshi.
Duk wanda ya ganshi yasan yana cikin tashin hankali. 
A dai-dai lokacin ne kuma Rayyern ya bud’e murfin motar tasa ya fito, wanda ya fito ne kuma saboda yiwa Junaid warning, akan  jinin daya shafa masa  ajikin sabuwar motar sa. 
Kana kuma ya sashi ya wonke mishi jinin daya zuba mishi jikin motarsa, in ba wani salon sharri bane yake neman sa dashi.
Barrister Kabir kuwa dake dukufe akan Jannart jin motsin mutum da yayi abayansa ne yasashi saurin juyawa, inda idanunsa suka sauka akan Dr Rayyern Bashi Muhammad Mai Nasara din koda yana cikin gigita ya gane waye ne shi. 
Aikuwa azabure ya mike tsaye, batare kuma da wani dogon tunani ba ya kamo hannun Rayyern d’in, cikin muyarsa dake rawa yace.
“Dan Allah Dr. Rayyern ka taimakamin, kalli Jannart jini take ta zubarwa, Dan Allah Kataimaka kada ta rasa rayuwarta.
Dan Allah ka ceceta ka ceci tsohuwar gsky itace hujja ɗaya gareni…”
Yanayin yanda yaji maganar mutumin dake rik’e da hannunsa ne, yasa akaron farko yakai dubansa, ga Jannart d’in dake kwance, kan motarsa jini na zuba mata ta hanci da baki.
Idanunsa ya d’an k’ank’ance saboda, yanda yaga numfashinta na sama da k’asa.
Lallai Tabbas yasan cewa Idan bai taimaka mata ba, To zata iya fad’awa cikin wata matsalar daban kana ya lura wannan mutumin mutum ne mai daraja da Kekkyawar zuciya, a hankali ya kuma kalli yadda hancinta keta zubda jinin haɓo.
Da sauri ya Juya.
  tare da kutsa kansa acikin motarsa, cikin sauri ya d’auki wannan bottle water din nasa mai matukar sanyi. 
Sabida muryar Barrister Kabir da yaji yana kuka da kiranta.
Da sauri ya juyo ya
K’arasowa kan Jannart din wacce.
Yanzu Barrister Kabir ya ɗagota daga kan motar ya tallabeta a jikinsa yana kiran Daddy.
“Yaya! Yayah Idi !!!”.
Da sauri ya ƙara so gabansa tare da murɗa marfin gorar faron mai masifar sanyin nan.
Kanta da Abba ke tallabe dashi ya saita tare da  d’an sunkuyowa ya soma zirara  mata ruwa mai bala’in sanyi a tsakiyar akanta.
 Yayi hakanne kuma saboda bata taimakon gaggawa sabida  yasan idan ya zuba mata ruwan sanyi akanta, Lallai jinin dake fita a hancin nata zai tsaya.
A dai-dai lokacin da yake tsaka da zuba mata ruwanne kuma, Alhaji Idi Sale Dakata, da kuma aminansa da suke cikin babban falonsa suka fito zuwa tsakar gidan, ganin abunda ke faruwane kuma yasa suka nufo kansu gadan-gadan.
Jannart dake kwance akasa kanta bisa cinyar ƙanin mahaifin nata kuwa sanyin ruwan da Rayyern din ke zuba mata ne yasa ta, jan wani irin dogon numfashi, lokacin ɗaya kuma jinin dake zuban ya tsaya.
*Kiyiwa Allah da Manzonsa kada ki fitar min da littafina,  in kin San kin sayane dan ki fitarmin da littafina ki gaya min in meda miki kuɗin dan girman Ubangiji ɗayae haliccemu, kada ki karantamin littafina in baki biyaba ganan account na 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU,  sai ki turo shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276 ko kuma ki sayi katin MTN ki copy number’s din ki turo min ta WhatsApp*
Ganin jinin ya tsaya ne kuma yasa.
Dr Rayyern Mai-nasara juyawa sauran ruwan ya zuba a jikin motarsa inda junin yake ya gangara yayi ƙasa.
Kana ya juya ya shiga motarsa tare dayi mata key da danna horn.
Cikin sa’a kuwa Mai gadin ya fara kiciniyar buɗe mishi gate yanayi yana sharce hawayen tausayin Jannart.
Ita kuwa Jannart Lokaci ɗaya kuma gaba daya jikinta ya d’auki karkarwa,  take ta soma fitar da wani irin numfashi mai kaman sheshshek’a alamun kuma athsman ɗinta yana tasowa.
Idanu duk suka zuba mata, Yayinda Abba kuwa ya tsaida idanunshi kan ƙirjinta.
Inda yake Kallon yanda bugun zuciyarta ke tayin k’asa.
Adai-dai lokacin da bugun zuciyar nata ya tsaya cak ne, kuma Idanunta suka soma kakkafewa, lokaci d’aya ta saki wani irin nishi’n daya saka Abba firgici.
Dai-dai lokacin kuma  k’irjin Dr Rayyern Mai-nasara yayi wani irin masifeffen harbawa.  
Take kuwa numfashinta ya d’auke D’ibbbbbb
Cikin tsananin tashin hankali, da kuma tsananin rud’ewa, Barrister Kabir  ya sanya hannayensa duka biyu ya tallafo Jannart d’in.
“Jannart! Jannart!! dan Allah bud’e idanunki Jannart!!! innalillahi wa inna Ilaihirraju’un! Yaya Idi Jannart ta suma, bata numfashi!!!”
Barrister Kabir  din ya fad’a yana me.
Kallon Yayan nasa, wato Alhaji Idi Saleh dakata, cikin matsanancin tashin hankali.
Shima kuwa Alhaji Idi Saleh Dakata’n tashin hankali ne, kwance akan fuskarsa, cikin yanayin  rud’ewan da yayi, ya kalli Dr Lukman dake tsaye, tare da cewa.
“Dr. Lukman ka duba mana ita dan Allah.”
Jin hakanne kuwa yasa Dr Lukman dake tsaye, d’an matsowa kusa dasu,
dan duba Jannart din, wacce ita yanzu bata masan duk wata Waina da ake toyawa acikin gidanba.
Idanu Barrister Kabir ya d’ago tare da watsawa, Dr Lukman din muguwar harara, cikin kuma yanayin fushi da tsananin b’acin rai yace.
“Kada kayi kuskuren tab’a min y’a.
Domin kuwa na jima da sanin muguwar cutar da kakeyi mata ta karkashin k’asa.”
Cak Dr.Lukman din ya tsaya, tare da matsawa gefe batare kuma daya karaso wajen ba, saboda jin abunda Barrister Kabir din ya fad’a. 
Barrister kuwa sungumar Jannart din yayi, kaitsaye kuma cikin sauri ya nufi hanyar fita daga cikin gidan.
Da hanzari kuwa maigadi ya bud’e masa dan madaidicin kofar dake jikin gate din gidan ya fice. 
Koda ya fito kuwa murfin motarsa na gidan baya ya bude, tare da tura Jannart din ciki ya kwantar da ita.
Batare kuma daya jira komai ba, ya zagaya ya shiga b’angaren driver, ahanzarce ya tada motar, tare kuma da cillata kan titi, kaitsaye yabi bayan motar Dr Rayyern Mai-nasara dake ta sharara gudu, akan shumfud’add’en titin kofar gidan daya mike santa yana mai jin jijiyoyin kansa na tsananta harbawa sabida ihu da hayaniyar da akayi tayi a kanshi .
Shi kuwa Barrister biye dashi yake a hamzarce.
Wanda kuma yayi hakanne saboda sanin matsayin Rayyern da yayi, na likita zai iya taimaka musu.
Yayinda ab’angaren Rayyern kuwa tuk’in motar yake, yana maijin wani irin b’acin rai acikin ransa, badan komai ba kuwa saidan b’ata masa rai da lokaci da akayi agidan Alhaji Idi Salte Dakata, Tabbas yasan cewar.
 Koda ace yaje asibitin nasa yanzu, babu wani abu da zai iya aikatawa, Domin yafi kowa sanin kansa Idan ransa na b’ace baya tab’a iyayin komai, koda ma kuma ace yayi din bisa dole, to abun bazai zama hundred percent yanda yake so ba ga kuma alamun ciwon kansa da yake ji.
Y’ar k’aramar tsuka yaja, tare kuma da d’an buga kan steering motar tasa, kaitsaye ya sanja akalar tafiyar tasa, inda ya saki hanyar asibitin nasu daya kama, direct ya shari kwana tare da hawa kan titin da zai sa dashi da gidansu. 
Ganin hakanne kuma yasa P.A d’agowa ya kalleshi, kamar zaice wani abu kuma saiya fasa, saboda yasan halin maigidan nasa, da yawan lokuta bayason adameshi da yawan magana. 
Barrister Kabir dake bayan su Rayyern din kuwa, shima gudu yake shararawa, still kuma har yanzu yana mebin ba yansu, sai-dai duk bayan mintuna kad’an yana juyawa ya kalli Jannart dake kwance flat agidan baya, babu alaman numfashi ko d’igo ajikinta. 
Wanda hakan kuwa shi yake k’ara sanya Barrister Kabir din acikin tashin hankali. 
Tafiyar da bata wuce ta 30mn ba sukayi, isowarsu wajen wani jection ne kuma yasa, Usman P.A d’an d’ago kai ya kalli Rayyern din.
Sake Kallon bayansu Usman P.A din yayi, still kuma ganin motar da tun d’azu yake ankare da ita, na binsu abayane , yasa shi d’an muskutawa cikin kuma yanayin mamaki yace.
“Sir kaman fa binmu wannan motar dake bayanmu takeyi.” 
Idanu Rayyern din ya d’aga, tare da maida kallonsa ga madubin motar wanda yake haska musu duk abunda ke bayansu.
Tabbas shima ya lura da motar, saidai kuma bai d’auki hakan amatsayin wani serious abuba,  batare kuma daya tankawa Usman P.A ba, kaitsaye ya hau kan titin daya shigar dasu layin gidansu. 
Suna isa bakin gate din tamfatsetsen gidan nasu ne kuma, barrister Kabir ya taka wani irin birki. 
Wanda kuma hakan yayi dai-dai da tsayawar motar Rayyern din shima, cikin kuma zafin nama da zafin ciwon kan sa yakeji ya bud’e murfin motar ya fito, saboda duk atunaninsa Alhaji Idi Sale Dakata ne, bai daddara da gargadin daya yi masa ba, ya sake turo masa wasu mutanen dan su bibiyeshi.
Fitowarsa daga cikin tasa motar ne, kuma yasa Barrister Kabir fitowa shima cikin hanzari, kuma ya nufo Dr. Rayyern d’in.
Muryarsa na rawa yace.
“Dan Allah Dr. Rayyern ka taimakamin, kada Jannart ta rasa ranta, Dan Allah ka taimakawa rayuwarta, wlh itace kaɗai babbar *HUJJATA,* ita kad’ai ce Hujjar da zan nuna anan gaba, please ka taimaka min!!” 
Barrister Kabir din ya fad’i haka cikin tsananin tashin hankali, da kuma muryarsa wacce take fitar da sautin kuka.
Dr. Rayyern din kuwa Jin amo da kuma sautin, muryar Barrister Kabir din dake fita cikin kuka ne, da kuma amo mai shiga kunne, yasa shi rumtse I danunsa, tare dasa hannunsa na dama ya dafe kansa, dake wani irin sarawa, dan lokaci daya yaji kaman ana buga masa gudu ma a tsakiyar kannasa, abu na farko da bayaso arayuwarsa shine, yi masa magana cikin sigar kuka da kuma d’aga murya,  sannan kuma aduk sanda wani ya buk’aci taimako afujajan awajensa, ya kanji zuciyarsa ta karye. 
Balle kuma Barrister Kabir din da yake ta had’ashi da sunan Allah. 
*Inama ace makaranta zasu kasance kamar Dr Rayyern in an had’asu da Allah zasuyi abu ko zasu bari, dan Allah da Manzonsa da darajar iyayenku idan Free PAGE ya kare kada ku fitarmin da littafina, in kinsan kin sayane dan ki fitar dan Allah ki gaya min in meda miki kuɗinki Dan girman Allah da tsarki littafinmu akwai karami. Group 500 ne kacal 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276 ko ki sayi katin MTN ki copy edin ki turo min ta WhatsApp*
“Usman!”
Rayyern din ya kira sunan Usman P.A da wata irin murya.
Jin amo da kuma sautin muryar Rayyern din cikin wani irin yanayi na dabanne kuma yasa, cikin sauri Usman ya fito, tare da k’arasowa yana Kallon Ogan nasa. 
“Ka kaishi hospital Usman kacewa Sulaiman ya duba patient din, please kuje Usman kutafi daga nan please…..” 
Rayyern din ya fad’i hakan, cikin wani irin yanayi marar dadi dayakejin kansa aciki, tare kuma dasa hannayensa duka biyu ya kama kansa.
Usman kuwa fahimtar halin da Ogan nasa ke cike ne yasa shi, saurin kallon Barrister Kabir.
Ahanzarce yace. 
“Muje na rakaku hospital dinsa akwai Doctor’s zasu dubata in sha Allah zata samu lfy.”
Ko jiran abunda Barrister Kabir din zaice kuwa baiyi ba, ya bud’e murfin motar barrister din, nan b’angaren mai zaman banza ya zauna.
Ganin hakanne kuma yasa Abba Kabir din shima komawa cikin motar, a 360 ya murzawa motar key tare da cillata kan titi, kaitsaye suka nufi asibitin Mai-nasara Hospital, saboda dama Barrister Kabir  din yasan asibitin. 
Ganin sun miki hanyar asibitinne kuma yasa Usman P.A ciro wayarsa ya dannawa Dr Sulaiman Kira.
Bugu biyu kuwa Sulaiman ya dauki wayar, bayan sun gaisa ne kuma Usman P.A ke fad’awa Sulaiman din cewa.
“Gamunan a hanyan Mai-nasara Hospital zamu kawo emergency patient, bisa umarnin Dr Rayyern.” 
Da “to.”
Kawai Dr. Sulaiman ya amsa, Yayinda shi kuwa Usman P.A ya katse kiran.
Rayyern kuwa da har yanzu ke tsaye abakin, motar tasa hannayensa duka biyu yasa ya cigaba da rike kansa dake sarawa. 
Jin da yayi cewar bazai iya jurewa tsayuwar bane, yasa shi nufar gate din gidannasu, koda ya isa jikin gate din, hannunsa ya daura akan y’ar karamar kofar dake jikin gate din, tare da tura ta ciki.
Baba Maud’o dake zaune abakin kofar dan Part ɗin sa, yana me sauraran radio ne ya d’ago kansa, saboda ji da yayi an tab’a kofar shigowa gate din. 
Aikuwa yana d’aga kansa ya sauke idanunsa akan Rayyern, da har yanzu yake dafe da kansa da hannuwansa duka biyu.
“Rayyern!!!” 
Baba Maud’o ya kira sunansa, cikin yanayi na  mamaki da kuma zallar damuwa. 
Batare kuma daya bari Rayyern din ya amsa masa ba, ya d’aura da cewa.
“Subahanallah Rayyern maiya sameka? Lafiya kuwa? Meke damunka? Bugewa kayi akan naka ne? Ko kuwa wani abune ya same ka?”
Baba Maud’o yayi masa duka tambayoyin cikin bayyana tsananin damuwarsa. 
Shikuwa Rayyern da ayanzu, yakejin idanunsa sun fara yi masa nauyi, kai kawai ya iya girgizawa Baba Maud’on, batare kuma daya iya cewa komai ba, kaitsaye ya wuce cikin gidannasu. 
Hakan da yayi dinne kuwa yasa Baba Maud’o, Jin wani iri acikin zuciyarsa, take kuma damuwa maitsananin yawa ta bayyana akan fuskarsa, saboda ya sani ba karamin abubane zai sa Rayyern din dawowa acikin irin wannan yanayin, Lallai akwai abunda yake damunshi. 
“To kodai awajen aikin nasa ne aka bata masa rai? Kodai kuma ciwon kansa ne?”
Baba Maud’o yayiwa kansa tambayar da bashi da mai amsa masa ita, sai Rayyern din.
Ganin da yayi zancen zuciya bazai kaishi bane kuma, yasa shi dan bud’e kofar gidan ya lek’a waje, ganin motar Rayyern din da yayi fake akofar gate dinne kuma yasashi saurin fitowa, tare da leka cikin motar,  ganin akwai key ajikin motar ne kuma yasa, da kansa ya wangale makeken gate din, tare da dawowa ya shiga cikin motar, da kansa ya shigo da motar ciki, saboda a lokacin shi kad’aine ya rage agidan, Hadi driver da kuma sauran masu bawa flowers ruwa duk basanan. 
*Dan Allah da Manzonsa idan free PAGE sun kare kada ku fitar min da littafi, ina rokon nanne da yakinin duk Musulmin kirki mai cikar imani da sanin darajar Allah da Manzonsa da darajar iyayensa nasan bazai fitarmin da shi ba, ko ya karanta na watan*
Rayyern kuwa Ahankali yake tafiya, yana me d’an jujjuya kai tare kuma da rumtse idanunsa, da yakejin sunyi masa matukar nauyi.
Isowarshi jikin kofar da zata sadashi da babban falon gidanne kuma, yasa shi d’aura hannunsa akan handle din kofar.
Dai-dai lokacin kuwa Abba da Mamy ne ke zaune acikin falon da alamun tattauna abu mai mahimmanci sukeyi.
Inda Abba ya d’ago kansa ya kalli Mamy, cikin yanayin  yin ƙasa da murya da alamun tsawatarwa yace.
“Kinsan abunda yake bunne, wanda kuma har yanzu bamu shirya tono shi ba. Meyasa kikeson ki bada kofa da abubuwa da yawa zasu iya wakana ba tare da mun shirya musuba.
Wannan sirrin mai karfi ne da cikar rauni, Tono shi kuma dai-dai yake da tsayawar bugun zuciyar wasu mutanen, musamman Rayye……”
Sauran maganan dake bakin Abban ne kuwa, suka mak’ale, asakamakon jin motsin bud’e kofar falon da akayi, 
Wanda hakan yasa cikin sauri duk suka maida kallonsu ga bakin k’ofar.
Ganin Rayyern din da sukayi dafe da kai ne kuma, yasa duk suka mimmik’e,  
“Rayyern lafiya kuwa?”
Abba ya tambaya hankalinsa atashe.
Kai Rayyern din ya d’an girgiza musu, batare daya ce komai ba, kuma ya k’arasa shigowa cikin falon, tare da nufan kan 3 seater, din leather cushion dake Cikin falon ya kwanta.
Still kuma hannayensa ya sake maidawa duka biyu ya rik’e kansa.
Al’amarin daya sanya hankalin su Abba da Mamy matukar tashi kenan.
 Da sauri Abba ya k’arasa inda Rayyern din ke kwance, hannunsa ya d’aura akan Rayyern din, cikin muryar dake bayyana zallan damuwarsa da farga yace.
“Rayyern me yake damunka, kodai ciwon kanka ne ya tashi!?”
Kai Rayyern din ya jinjina alaman “Eh.” Saboda ayanzu yakai wani stage da bayajin zai iyayin wata magana.
Zazzafan numfashi Abba da Mamyn suka sauƙe, cike kuma da alhinin tashin ciwon kannasa, Abba ya zaro waya dan kiran Ramadan.
Yayinda Mamy kuwa ta matso kusa da Rayyern d’in, anutse ta zauna tare da soma shafa masa tarin sumar dake kansa. 
A dai-dai wannan lokacin kuwa, Ramadan ne ke zaune acikin wani had’add’en lambu, dake cikin wani katafaren gida, yayinda ya k’urawa wata fara kyakkyawar matashiyar budurwar dake zaune  agefensa  idanu.
duk da cewar kuma  ak’alla budurwar dake zaune agefen nashi, ba zata wuce 20 years ba, amma tana da cikar halitta mai kyau, da ganinta kuma kasan cewa yar manyan mutane ne,  Rayhanna kenan kyakkyawar matashiyar budurwar mai alkunya.
Yayinda ad’an gefe da Rayhannan kuwa Riyyam-nsra ne zaune, yanata yiwa Hamman nasa tsiya.
Cikin kuma ya bawa da zab’in Ramadan d’in yace.
“Gaskiya Hamma Ramadan ka iya zab’en kyakkyawar budurwa, tamkar daga saudiya aka sassak’ota.” 
Murmushin Jin dadi Ramadan yayi, tare da sanya hannunsa na dama ya dafa kafad’an Riyyam din,  again kuma cikin kasa dauke idanunsa daga kan Rayhanna’n nasan yace.
“Angaya maka cewar ni na wasa ne, ai kwata kwata bana sanya, ko da ka d’auka cewar ni irin suma  Hamma Rayyern ne waliyai.”
Dariya Riyyam nsra ya saka, Yayinda ita kuma Rayhanna ta sanya mayafinta ta rufe fuskarta, wanda tayi hakanne kuma saboda Sam bazata iya jurewa, irin Kallon da Ramadan din keyi mata ba, Domin kallone da yake bayyana tsananin kauna da soyayyarsa agareta. 
Baki Ramadan din ya bud’e da niyar cewa wani abu, amma kuma sai k’aran wayansa dake tashi, acikin aljihun rigarsa, ya hanashi furta komai.
Zaro wayartasa yayi, ganin sunan Abba na yawo akan screen din wayar ne, kuma yasa shi d’agawa da sauri.
Daga can b’angaren kuwa Abba dake tsaye agefen Rayyern ne yace.
“Ramadan, Rayyern! Rayyern ciwon kansa ya tashi!” 
Idanu Ramadan din ya dan zazzaro tare kuma da, mik’ewa tsaye cikin tashin hankalin daya samu kansa aciki yace.
“Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un, Abba maiya samu Hamma Rayyern din, yaushe kuma ciwon kan nasa ya tashi?”
Ya tambayi Abban  cikin tashin hankali, gami da tsananin damuwa.
“Bansani ba Ramadan, Domin yanzu dawowanshi gida, yanzu haka gashinan a kwance sai faman rike kan na yakeyi.
Maza Ramadan kabar duk abunda kakeyi ka dawo gida, sannan ka biya ta pharmacy ka had’o masa magunguna.” 
Abban ya fad’i hakan, cikin muryar dake bayyana cewa, kwarai yana cikin damuwa. 
Ramadan kuwa idanunsa da suka ciko da k’walla, saboda tausayin dan uwannasa yad’an lumshe, kana cikin muryarsa da tayi rauni sosai yace.
“Shikenan Abba ganinan zuwa.”
Yana gama fadan hakanne kuma Abba ya katse kiran.
Riyyam-nsra da tun d’azun shima ya mik’e tsaye hankalinsa atashe matuka, yace.
“Hamma Ramadan mai yasamu Hamma Rayyern? Dan Allah karkacemin wani abu na cutarwa ne ya sameshi.” 
Idanu Ramadan din ya bud’e, cikin yanayin sanyi yace.
“Ba abunda ya sameshi Riyyam, kawai dai ciwon kansa ne ya tashi, wanda dama kuma yana dashi, saidai bai cika tashi ba, harsai da dalili, Idan ciwon kannan ya tashi Riyyam, Hamma Rayyern yana shan wahala, saidai duk da haka gwara ciwon kan, akan matsanancin ciwon cikin da yake tashi mishi, awasu mabanbanta lokuta.”
D’an rank’wafowa yayi ya kalli Rayhanna, da itama gaba daya damuwa ta bayyana akan fuskarta, saboda tasan matsayin Dr Rayyern din awajen Ramadan, tasan yanda Ramadan ya dauki Rayyern, da kuma yanda yake girmama duk wani abu daya shafesa, haka kuma tasan yanda Ramadan din ke daukan duk wata matsala ko damuwar yayansa, Domin sauda yawan lokaci Ramadan din, kan fad’a mata cewar Hamma Rayyern dinshi, shine duk wani Garkuwa’rsa, shine kuma wanda ya tsaya masa akan jindadi da farincikinsa. 
“Hanna zantafi, Hamma Rayyern bashi da lafiya, zamuyi waya later.” 
Ramadan din ya fada murya asanyaye.
Mik’ewa tsaye Rayhanan tayi, tare da cewa.
“Shikenan badamuwa, Allah Ubangiji ya bashi lafiya, yasa zakkan jikine.”
Da “Ameen.” Ya amsa, har wajen da motarsa kirar Benz ke fake kuma Rayhanan ta rakosu, inda tayiwa Riyyam-nsra sallama.
Saida taga ficewarsu daga cikin compound d’in gidan nasu, kuwa kafun ta koma ciki.
Duk zuciyarta babu dadi, saboda duk wata damuwa da tagani akan fuskar Ramadan to ta shafeta. 
Ramadan kuwa suna ficewa daga cikin gidansu Rayhannan, wani irin gudu ya soma shararawa akan titi, wanda hakan yasa cikin mintuna kadan suka iso, babban pharmacy dinsu.
Ko gama dai-dai-ta parking din motar baiyi ba, haka ya fito ya shiga cikin pharmacy din, duk wasu magunguna da yasan Rayyern din zai buk’ata ya had’a, tare da fitowa agurguje yaja motar suka nufo gida kaitsaye.
Isowarsu bakin gate din gidanne kuma yasa, Ramadan soma danna horn.
Wannan yasa cikin sauri Baba Maud’o dake zaune abakin gate din, yayi jigum, yazo ya bud’e musu, gaba d’aya bayajin dadi acikin zuciyarsa, saboda sai ayanzunne ma yake tunawa da cewar, halan ciwon kai din Rayyern dinne ya tashi, saboda aduk cikin gidan babu wanda baisan da cewar, Rayyern na fama da ciwon kai dana ciki ba. 
Ramadan kuwa yana shigowa cikin gidan yayi parking motar, cikin sauri kuma shida Riyyam suka fito, kowannensu fuskarsa dauke da matsanancin damuwa suka shige cikin gidan.
Tunkafun su karasa shiga cikin babban falon gidan kuma, Ramadan ya soma b’abb’alle magungunan da zai bawa Rayyern din. 
Wanda hakan yasa suna shiga cikin falon, direct Riyyam-nsra ya k’arasa gaban deep freezer, tare da dauko bottle water marar sanyi kasan cewar ba’a jima da sasuba.
Koda ya dawo goran ruwan ya mik’awa, Ramadan wanda zuwa lokacin harya gama b’are magungunan, inda da kansa ya tallafo Hamman nasa, tare da  zuba masa magungunan, kana ya had’a masa da ruwan faro. 
Atake kuwa Rayyern ya had’iye magungunan, saidai kuma cikin radadin ciwon kan nasa da yakeji, ya sake komawa ya kwanta, Yayinda sannu Ahankali yake ci gaba da d’an jujjuyawa kan nasa.
Idanu duk suka zuba masa, kana cike da tsananin tausayawa sukeyi mishi sannu, Riyyam-nsra kuwa zama yayi dab’as ak’asa, idanunsa da suka cicciko da hawaye ya zubawa Hamma Rayyern d’in, acikin ransa kuwa yana me addu’a, da fatan Allah Ya bawa hamma Rayyern dinnasu lafiya. 
Rayyern kuwa dake kwance kannasa ya sake rikewa, tare da lumshe idanunsa, wanda sukayi jazur,  saboda tsabar wahalan da yakeji kuwa, hatta jijiyoyin dake kwance akan goshinsa saida suka fito rud’u rud’u.
*Dan girman Allah masu sayan littattafai dan  su fitar su watsashi kuyi hakuri kada ku saya littafina  dan Allah nace in kin saya kuma ki gaya min in meda miki kuɗinki*
Bayan kaman mintuna 15 dashan maganin nasa ne kuma, ya soma  sauke wani irin wahalalliyar ajiyar zuciya.
Yayinda sannu ahankali yakejin relief nad’an saukar masa. 
In a 20mn kuwa batare da zato ko tsammani ba, bacci mai nauyi ya daukesa.
Jin yanda numfashinsa ke fita da d’an fusga ne kuma, yasa su Abba gane cewar yayi bacci,  ajiyar zuciya suka sauk’e dukansu,  Yayinda Abba kuwa ya d’an rankwafa tare da gyarawa Rayyern din kwanciya. 
Bayan ya koma ya zauna akan kujera ne kuma yasa hannunshi duka biyu yayi tagumi cikin alamun tarin fargaba, tashin hankali, so, da tarin tausayin d’an nasa .
Ido Ramadan ya ɗan zuba mishi kana a hankali yace.
“Abba ba komai fa in sha Allah zai samu lfy”.
Numfashi ya ɗan sauƙe a hankali kana  murya asanyaye  yace.
“Hakika yanzu aduniya babu wani abu da yake, damuna da kuma matuk’ar d’agamin hankali sama da ciwon Rayyern.
 Ciwon Rayyern yana damuna, musamman ciwon cikinsa da Idan ya tashi masa, yakeyin kamar zai rabamu dashi, Tabbas Ina matuk’ar tsoron ranan da ciwon nasa zai tashi, Ina fargaban hakan akoda yaushe, Ina mai kuma addu’a da fatan, Allah ya yayemishi wannan ciwon kai da ciwon cikin, Domin kuwa aduk sanda d’aya daga cikinsu ya tashi, shi kad’ai yasan wani irin zafi da yakeji tunda har yake fidda shi hayyacinsa.” 
Abban ya kai k’arshen maganan nasa, cikin raunatacciyar murya, Yayinda idanunsa kuma suka cicciko da hawaye.  
Ganin hawaye a idanun Abban ne kuma, yasa Mamy, Ramadan, Riyyam duk sukaji jikinsu yayi sanyi, take kuma idanun Mamayn ma duk suka cicciko da hawaye, kasancewar ta Mace ne kuma, yasa ta kasa controlling hawayen nata, harsaida suka sauk’o kan fuskarta, batare kuma da ta bari kowa yaga hawayen nata ba, ta share da sauri. 
Dai-dai lokacin kuwa Baba Maud’o dake tsaye abakin k’ofar shigowa falon, ya d’an d’aga muryarsa wajen yin sallama. 
Jin muryar Baba Maud’o dinne kuma yasa, Ramadan mikewa ya k’arasa tare da bud’e kofar, Cikin kulawa yace.
“Baba Maud’o bismillah ka shigo mana.”
Kai Baba Maud’on ya girgiza, tare da cewa.
“A’a basai na shigo ba Ramadan, dama nazo ne na tambaya naji ya jikin Rayyanu.” 
Ajiyar zuciya Ramadan ya sauk’e, cikin kuma son kwantarwa da Baba Maud’on hankali yace.
“Jikinsa da sauki sosai Baba Maud’o, yasha magani kuma yanzu haka ma bacci yake, Insha Allah kuma Idan ya tashi daga baccin, zai ji saukin ciwon kan.”
Kai Baba Maud’on ya jinjina, cike kuma da gamsuwa yace.
“Masha Allah! Allah Ubangiji ya k’ara masa lafiya da Nisan kwana mai amfani.”
Da “Ameen.” Ramadan ya amsa, ganin Baba Maud’on ya juya ya tafi ne kuma, yasa shima komawa cikin falon.
Baba Maud’o kuwa Koda ya nufi dakinsa dake cikin gidan, hannayensa yasanya ahankali ya share hawayen da suka gangaro daga Cikin idanunsa, wanda kuma yayi imani cewa, da ace bai bar wajen Ramadan din da wuri ba, To da akan idanun Ramadan hawayen nasa zasu zubo..

Back to top button