Uncategorized

Tubali Book 1 Page 14 Complete Novel

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

Mamy ta kirsa da d’an k’arfi, wanda hakan yasa shi dawowa daga duniyar tunanin daya fad’a.

D’ago da kansa yayi Ahankali ya kalli Mamy’n, da ta tsare shi da ido.

“Mamy yaushe kika shigo?”

Ya tambaya da dan mamaki akan fuskarsa.

“Tayaya zaka san lokacin dana shigo, bayan kanason takurawa rayuwarka, dason sawa kanka damuwa akan abunda kasan ya zama wajibi akanka.”

Mamyn ta fad’a.

Longoɓar da kansa  yayi, kamar zaice wani abu kuma saiyayi shiru.

Mamy kuwa Ajiyar zuciya ta sauk’e, had’e da cewa.

“Idan akwai magananin zazzab’i awajenka, ko paracetamol ne ka bani, Jannart ce jikinta duk ya d’au zafi.”

Jin abunda Mamyn ta fad’a ne kuma yasashi d’ago kansa ahankali ya kalleta, fuska ya  kwab’e kana cikin muryarsa mai kama da shagwab’a yace.

“Ni kam Mamy bani da wani magannin zazzab’i.”

Harara Mamyn ta watsa mishi tare da gyara tsayuwarta tace.

“Taya zaka cemin babu bayan bakaje ka duba ba.”

Sake langwabar da kansa yayi, still yace.

“Mamy nasan fa babunne, kuma yanzu ni bana ajiye magani, saidai ko ki tambayi Ramadan.”

“Katashi Kai kaje ka karb’omin maganin awajen Ramadan.” 

Mamyn ta fad’a adake.

Jin hakanne kuma yasa shi mik’ewa jiki asanyaye, ya nufi dakin su Ramadan.

Yana zuwa kuwa ya samu Ramadan da Riyyam-nsra kowannensu na rike da waya ahannu.

Ko Kallon kirki baiyi musu ba, ya tsaya tare da d’age kansa sama, kana yace.

“Ramadan bani paracetamol.” 

Da mamaki Ramadan  yake kallonsa, kamar zaiyi magana kuma saiya fasa, kaitsaye ya bud’e wani Dan box maganin zazzab’i ya ciro ya mik’awa Rayyern din.

Yana karb’a kuwa ya fice, inda ya samu Mamy abakin k’ofa ya mik’a mata.

Amsan maganin Mamy tayi, batare da tace masa komai ba kuma ta juya ta sauk’a k’asa.

Shikuwa d’akinsa ya koma, zuciyarsa cike da takaici.

 Domin shi sai yanzu ne ma yakejin haushin yarinyar da aketa kira da Jannart din.

Mamy kuwa kaitsaye kitchine ta nufa, bayan ta d’auki abincinne kuma ta wuce sashin Jannart.

Jannart kuwa dai-dai lokacin ta fito daga wanka, bayan tayi wankanne kuma  ta sake maida doguwar rigar da ta cire. 

Tana tsaka da maida hijab dinta ne kuma, Mamy ta shigo hannunta dauke da cup da kuma plate din indomei.

Akan wani Dan stull Mamy ta ajiye cup da plate din, tare da duban Jannart din Cikin kulawa tace.

“Yauwa Jannart kinfito ko, ga abinci nan kici, sai kisha magani saboda naji jikinki akwai zafin zazzab’i.” 

Kai Jannart din ta Dan sunkuyar kasa, kana aladabce tace.

“Mamy nakoshi.”

“A’a kam Jannart, saboda kefa na shiga kitchine na dafa abincin nan, saboda haka ki zauna kici, kada kiyimin gardama kinji, koso kikeyi na barki haka, Allah ya kama mu kefa amanace awajen mu, zo maza ki zauna kici.”

Mamyn ta fad’i haka cikin matukar kulawa.

Wanda hakanne kuma yasa Jannart din karasowa, ta zauna akan lallausan sofan dake malale agaban gadon. 

Abincin Mamy ta ajiye mata, Ahankali kuma ta soma tsakuran abincin tana kaiwa bakinta.

Kasancewar kuma da gaske bata wani jin yunwa sosai ne, yasa bata wani ci abincin sosai ba, saidai tea din da Tasha har fiye da rabin kofin.

Dan matsar da plate din abincin tayi gefe, tare da yiwa Mamy alama akan ta koshi.

Hakanne ko yasa Mamy b’are maganin ta bata tasha.

“Ki kwanta to ki huta, Dan Allah karki sakeyin kuka kinji Jannart, kinga shine ya haddasa miki wannan zazzab’in.”

Mamy ta fadi haka tana me daukan plate da cup din abincin.

“To Mamy.” Jannart din ta fad’a, tana me mikewa tsaye ta haura saman gadon ta kwanta.

Murmushi Mamy tayi saboda a iya yaudin kawai ta yada da hankali,da kuma  biyayyar da yarinyar take dashi.

Cikin kula tace.

“A’a Jannart tashi kiyi addu’a kinji, kada bacci ya daukeki batare da kinyi addu’a ba.”

Aikuwa da d’an hanzari Jannart din ta tashi zaune, hannayenta ta hade waje guda,  falaq,suratul nass, da kuma suratul Iqlas, k’afa uku uku, kursiyu da amarasulu sai kuma Hasbiyallahu la’ilaha illahuwa, alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim, k’afa 7, sai kuma suratul Khafirun kafa uku shima.

Bayan ta shafa ne kuma ta koma ta kwanta.

Mamy kuwa cike da farincikin samun ya kuma surkuwa ta gari, ta ragewa Jannart gaba daya hasken wutan dake dakin.

Bayan sunyiwa juna saida safe ne kuma Mamyn ta juya ta fita.

Bayan ta maida plate and cup din kitchine ne kuma, kaitsaye Mamyn dakin Abba ta nufa.

Koda taje Zaune ta sameshi akan gado.

Zama ita dinma tayi agefensa, kana cikin tausasa murya tace.

“Tabbas Rayyern ya samu mata, yayi dace da yarinyar arziki mai ladabi da biyayya”.

Cikin jin daɗi Abba ya juyi ya fuskanceta yana mai jinjina kai alamun gamsuwa.

Ita kuwa Mamy cikin girmamawa tace.

“Toh amma Alhaji meyasa ka umarceni dana kaita wancan dakin, bayan ganan sashin Rayyern.”

Murmushi Abba yayi, tare da maida kallonsa gareta yace.

“Nace ki kaita wancan part dinne Saboda, sai anyi gyara a b’angaren Rayyern kafun ta koma can.

Kadafa ki manta fa amaryace, Koda cewar auren ba dan shiri bane, amma yana da kyau a inganta mata komai nata”.

Da sauri tace.

“Eh gsky hakane kam”.

Ɗan gyara zamanshi yayi tare da cewa.

 “Sannan kuma baki ga dan naki bahagon yaro bane, kwata-kwata na kasa gane inda ya dosa, Sam bai fahimci abunda muke nuna masa ba, atakaicema gani yake kamar takurasa mukeson yi.

Bayan haka kuma ganan Ramadan shima yana saman.

To dole yanzu zai dawo k’asa, kafun adai-dai-ta komai ta koma side din nasu.”

Kai Mamy ta jinjina cike da gamsuwa.

Kasancewar ta gaji ne kuma yasa ta zame ta kwanta gefensa.

Acan b’angaren Rayyern kuwa, akwance kawai yake amma duk zuciyarsa babu dadi.

Ak’alla saida ya kwashe sama da 50mn kafun bacci b’arawo ya iya satan shi.

Jannart kuwa tun fitan Mamy ta lumshe idanunta.

 Yayinda tunani kala-kala ke yawo aciki kwakwalwarta, akaro na farko kenan tun tashinta izuwa yanzu, da zata kwana awani gida sab’anin nasu dan ko gidan Barrister Kabir Daddy bai taɓa barin ta ta kwana ba sai kuma asibiti.

Tunani ne fal zuciyarta, saidai kuma kamar yanda tayiwa Mamy al’ƙawari, batayi kuka ba, da taimakon maganin zazzabin da tasha ne kuma bacci ya dauketa.

Yayinda acan gidan Alhaji Idi Sale Dakata kuwa, kowa ya kwana sharbar bacci batare da tunanin Jannart bata cikin gidan ba, Domin wasu daga cikin mutanen gidan har da gwartin su, saidai banda Junaid Wanda ya taso sad’ab sad’ab ya nufi d’akin Jannart din, saboda gaba daya ya kasa bacci.

 Daya rufe idanunsa Surar Jannart dinne keyi masa gizo, shiyasa yazo domin rage zafin abunda ke damunsa.

Koda ya karasa kofar dakin nata, kaitsaye ya tura kansa ciki.

Saidai kuma rashin ganinta da baiyi acikin dakinba, yasa shi cije labbansa, lokaci daya kuma ya raya cewar ko tana toilet Murmushin mugunta yayi, tare da nufan toilet din kaitsaye.

Tura kofar yayi batare daya jira komai ba kuma ya soma zare belt din wandonsa, saboda ya gama targetting yana ganinta zai Afka mata, amma kuma saidai meye?

Wayam haka yaga toilet din, ba alaman ma anshigesa tsawon sama da 1hour.

Tsuka yaja tare da fitowa, yana kwafa haka ya fice daga cikin dakin, cike da takaicin rasa damar da yayi.

Badan ransa yaso ba haka ya koma sashinsa ya kwanta a tunaninsa ko tana dakin Mom. 

        *Washegari*

8:00 am dai-dai Mom ta gama kammala musu breakfast, wanda kuma har zuwa tsawon wannan lokacin ba taga Jannart ta fito ba.

Hakanne kuwa yasa bayan ta gama setting dining table, kaitsaye tatafi izuwa dakin Jannart din.

Koda ta isa bakin kofar knocking ta fara yi, har na tsawon mintuna 2 kuwa bataji ko motsin za’a bud’e kofar ba, hakan yasa Ahankali ta tura kofar d’akin,  tare da kutsa kanta ciki.

“Jannart! Jannart!!” Momyn ta kira sunan Jannart din, saboda rashin ganinta da tayi adakin.

Jin shiru ne kuma yasa Momyn juyawa ta fita, saboda atunaninta ko Jannart din tana cikin toilet ne.

Kaitsaye dining table ta dawo, tana zuwa kuwa, Daddy da Abdull suma suka fito suka zauna.

Momyn ce tayi saving dinsu,  tana cikin saving dinnasu ne kuma, Junaid ya shigo cikin falon, yana fito, daga shi kuma sai t shirt da gajeren Wando.

K’arasowa dining table din yayi, batare daya gaisar da kowanne daga cikinsu ba, cikin iskancinsa irin na wasu masifaffun sojoji yace.

“Ina Jannart?” 

D’agowa duk sukayi suka kalleshi.

Sanin halin rashin mutumcinsa ne kuma yasa Mom tace.

“Yanzu na dawo daga dakinta banganta ba, tun safe kuma bata sauko ba, amma Ina tunanin ko tana toilet ne.”

“Bawani bata gidan nanne ma gaba d’aya, y’ar iskar yarinya, jiya ma da dare ai naje dakinta amma bansa meta ba, wallahi Idan na kamata sainaci Uwarta.”

Baki Momy ta tab’e, tare da kallonsa cikin yanayin mamaki tace.

“To kai meya kaika dakinta da dare?.”

“Oho bansani ba, munafurci kawai.”

Junaid din ya fad’a kaitsaye, babu wani shakka ko shayi.

Duk da Abba yana jinsa kuwa, haka yayi shiru bai tanka masa ba, saima Kallon Momyn da yayi, yace.

“Kije ki duba toilet din, ko me ta keyi kice mata ta bari, injini tazo mu yi breakfast.”

“To.” Momyn tace, tare da juyawa tasake nufan dakin Jannart din.

Tana zuwa ta tura kofar, but still Jannart bata ciki, da d’an mamaki Momy ta karasa jikin kofar toilet din, tare da kasa kumnenta.

Waiko zataji karar ruwa, saidai bataji komai ba, hakan yasa Momyn ta tura kofar tana me kiran sunan Jannart.

Saidai meye, idanunta ba abunda suka gane mata, domin kuwa Jannart bata cikin toilet din. 

Mamaki ne ya kama Momyn, saboda Sam bata taba tunanin Jannart bata cikin toilet din ba.

Juyawa tayi cikin sauri ya dawo falo.

“Alhaji Jannart fa batanan, na duba bata dakinta kuma bata bayan gida.” 

Cak Alhaji Idi Sale Dakata yatsaida duk wani abu da yakeyi, cikin yanayin mamaki had’i da razana yace.

“Bangane mekike cewa ba, wannan wani irin maganar banza ce, tayaya zakice bata dakinta kuma bata bayan gida, wannan gashi anan dinma batanan, To ko tana dakinki ne?”

Kai Momy ta girgiza da sauri, tare da cewa.

“A’a wallahi bata dakina, tun Safe ma banga sauk’owarta ba, zaiyi wahala ace ma tana dakina.”

“Kije ki duba ta yanzu.”

Dadyn ya fada cikin bacin rai.

Hakan yasa da sauri Momyn ta juya zuwa dakinta,  kamar yanda ta zata kuwa hakanne, domin Jannart bata cikin dakinta.

Dawowa falon ta sakeyi, tare da Kallon Daddyn tace.

“Alhaji Jannart fa bata dakina.”

Idanu Daddyn ya zazzaro waje,  Abdull kuwa da mamamki yace.

“Ha’a To Ina Aunty Jannart ta shiga ita da yawo ma bayinsa takeyi ba, amma bari na duba compound ko Garden ko tafita shan iska.”

Yana gama fadin hakan ya mik’e ya fita.

Kaitsaye garden dinsu ya nufa amma baiganta ba, hakan yasa ya dawo, fuskarsa dauke da damuwa yace.

“Daddy banganta ba.”

Kwafa Junaid yayi, tare dasa hannayensa a aljihun wandonsa, cikin bakar muguntan dake cinsa yace.

“Nifa Tunjiya na fada muku banganta ba, maybe yawon iskancinta ma ta tafi, dama ai ta saba tafiya kwanan gida.

Rijiyace kowanni dan iska yana iya zuwa ya zira gugansa yaja ruwa son ransa.”

Idanu Momy ta rumtse saboda har acikin zuciyarta bataji dadin bakar maganar da Junaid din ya fada akan Jannart d’in ba.

 Daddy kuwa Wayarsa ya zaro daga cikin aljihun rigarsa, tare da lalub’o numbern  Jannart din ya danna mata kira.

The first time akace masa wayan nata, is switch off, da Mamaki Daddy ya sake dialing airtel number dinta, still switch off,  wani irin bugawa yaji kirjinsa yayi, cikin sauri yace.

“Junaid je maza ka duba side dina, watakila ko taje gaisheni ne.”

Juyawa Junaid din yayi, Inda kaitsaye ya nufi side din Daddyn, Koda ya karasa baiganta ba, har cikin bedroom na Dad din ya shiga amma babu ko alamarta.

Dawowa yayi yana ta kwafa, yace baiganta ba.

Mik’ewa tsaye Daddy yayi, cikin tsananin tashin hankali ya nufi kofar fita daga falon, batare kuma daya lura ba har tuntub’e yake.  

Kaitsaye compound din gidan ya fito, tun daga nesa kuma ya soma k’walla kira.

“Ado! Ado!!” 

Baba Ado dake bakin gate wurin Ashiru ne, Jin irin kiran da Alhajin keyi masa ne kuma yasashi tahowa da sauri.

Kallonsa Alhaji Idi Sale Dakata’n yayi, kana cikin dan daga murya yace.

“Jannart ta fita ne?”

Kai Baba Ado ya girgiza kana cikin girmamawa yace.

“A’a Alhaji Jannart bata fita ba, kwata kwata tunsafe Ina zaune anan banga wani ma daya fita acikin gidan nan ba.”

Shiru Daddyn yayi, na yan wasu mintuna, kamar kuma Wanda aka tsikara yasoma k’wala k’iran Guards.

Su kuwa k’attin banzan ma sai yanzu suka tashi daga nannauyan baccin daya daukesu. 

Jin kiran da Ogan nasu keyi musu ne kuma, yasa cikin  sauri duk suka k’araso.

Kallonsu Daddyn yayi tsab cikin hade fuska yace.

“Ina Jannart, dawa ta fita acikin ku?.”

Kai suka girgiza dukansu,  kana suka had’a baki wajen cewa.

“A’a bamuga Jannart ba, mu yanzu ma tashinmu wata kila tana cikin gida.”

“Wani irin cikin gida kuma, bayan babu Inda ban duba batanan, maza ku zagaye duka gidan nan ko zaku ganta.”

Dadyn ya fada cikin bacin rai.

Nan take kuwa guard din suka  bazu ako ina dake cikin gidan, amma ko alamar Jannart basu gani ba.

Hankalin Daddy yayi masifar tashi, musamman daya sake kiran wayanta yaji akashe.

Haka ya dawo falon afujajan, Yayinda Momy kuwa ta kasa zaune ta kasa tsaye, saboda abune kaman wasa amma yana neman Zamowa gaskiya. 

Kallon Daddyn tayi, tare da Daukar wayarta tace.

“Bari na kira Barrister Kabir.”

Dialing number’n Barrister Kabir din tayi, bugu hudu kuwa Barrister Kabir ya dauka.

Bayan sun gaisa da Momynne kuma, cikin tashin hankali tace.

“Barrister bamuga Jannart bafa, munnemeta sama da kasa acikin gidan nan amma bamu sameta ba, munkira wayarta kuma akashe, Kodai tazo wajenka ne?”

Daga can b’angaren Barrister Kabir ya mik’e tsaye tare da daga muryarsa cikin nuna tashin hankali yace.

“What!! Wannan Wace irin magana ce, Ba’a ga Jannart ba, annemeta anrasa? Ita kudi ce da za’ace annemeta anratsa? Ko kuma ita din wayar hannu ce da za’ace an nemeta anrasa.”

Ya k’are maganar cikin yanayin tsawan, dake nuni da bazai iya tolerating nonsense akan Jannart ba.

Momy kuwa cikin tashin hankali tace.

“Wallahi Barrister bamuganta ba, body guards dinta da masu gadi duk sunce basu ganta ba.”

“Gani nan zuwa.” Barrister Kabir din ya fada agigice.

Tare da kashe wayar.

Bayan ya kashe wayartasa ne kuma ya saki wani irin murmushi tare da juyowa ya kalli Aunty Dijat dake zaune.

“Sakarkaru sai yanzu suka lura da cewar Jannart bata gidan, hmmm da sannu munafukan boye zasu fito fili, kowa kuma zai girbi abunda ya Shuka.”

Dariya Aunty Dijat tayi.

Yayinda shikuwa ya dauki key din motarsa ya fice.

Kaitsaye gidansu Jannart din ya nufa.

Yana isa gidan kuwa ko gama dai-dai-ta parking baiyi ba, ya fito.

Inda  Daddy kuwa ke tsaye, gaba daya hankalinsa atashe yake sai safa da marwa yake, Yayinda kuma yake ta balbale guard din da fad’a, tankar zai hausu da duka, sai cewa yake, su je su nemo Jannart duk inda ta shiga ta fita. 

Barrister Kabir kuwa agigice ya karaso, hankalinsa amatuk’ar tashe yace.

“Yaya ina Jannart? Waya dauke mana Jannart? Ina kuka kaita?.”

Kai Alhaji Idi Sale Dakata ya girgiza, cikin tsananin damuwar da yake ciki yace.

“Bansani ba Kabir, bansan Ina Jannart tayi ba, munduba ko ina amma babu ita babu alamanta.” 

Hannu Barrister Kabir ya daura akai, lokaci daya kuma ya jujjuya idanunsa sukayi jajur, ahaukace ya soma neman Jannart din, tare kuma da soma zagaye cikin gidan yana leka har cikin followers, sunan Jannart din kawai yake kira da iyaka karfinsa.

Daddy kuwa bala’i da tashin hankali ne ke cinsa, cikin zafin nama kuma ya kalli Ashiru.

Afusace yace.

“Ashiru Ina Jannart waya bude mata kofa ta fita, ka fadamin nace ko kuma yanzu nasa bindiga na harbe kanka.”

Yakare maganar atsawace tare dasa hannu kuma ya dauke Ashirun da lafiyayyen Mari.

Kai Ashiru ya girgiza, cikin shanye zafin marin yace.

“Alhaji banganta ba, tun jiya gidannan akulle yake, gaba daya jiyama kowa ya sani bataje aiki ba, tunjiya bata fito ba, ga guards dinta nan suma shaidane.”

Sake hasala Daddyn yayi, Wanda hakan yasa ya sake gallawa Ashiru mari, tare da juyowa ya soma balbale Body guards din.

Cikin fushi yake cewa.

“Aikin banza k’attin banza kawai, angaya muku ahaka kawai na daukeku aiki ne, sokaye kun kwanta bacci sai kace matattu, yan iska kusan duk inda zaku ku nemomin y’ata.”

Barrister Kabir kuwa, zuwa yanzu har muryarsa ta Dishe, saboda yanda yake ta k’wala kiran Jannart.  

Gaba daya lokaci daya jikinsa har karkarwa yakeyi, hankalinsa ya matukar tashi, inda yake reaction tankar da gasken gaske shima baisan inda Jannart din take ba.

Cikin kuma tashin hankalin daya nuna yana ciki ne kaitsaye ya nufi dakin Jannart din.

Yana shiga kuwa ya soma wargaza komai dake cikin d’akin,  ananne fa kuma idanunsa suka sauka akan wayarta.

Da sauri ya dauki wayar dake kashe ya kunna,  batare ma daya jira wayar ta karasa kawowaba ya dawo cikin falon, inda dukansu ke tsaye, cikin kuwa harda Junaid dake zukan shisha. 

Wayar nata na kawowa Barrister Kabir ya shiga cikin dialing call dinta.

Aikuwa last sunan wanda tayi waya dashi Ne ya bayyana.

“Yah Junaid”

Idanu Barrister Kabir din ya zazzaro cikin matukar hasala, kuwa ya karasa cikin falon, batare da wata wata ba, ya Ware yatsunsa biyar ya zabgawa Junaid zazzafan Mari.

Tare kuma da juyawa afuce ya nunawa Dady screen din wayar Jannart din.

Cikin tsananin fushi yace

“Ba gashi ba, shine last mutum din da tayi magana dashi awaya, koma meye shi yasan inda take, Ina ya kaita? Yaya ka tambayeshi Ina ya kaita nace!!!!!!”.

Barrister Kabir din ya fada amatuk’ar tsawa ce, tsawan kuma daya saka hantar cikinsu kadawa.

Shi kuwa Barrister Kabir kuwa cikin fushi Ya…!

 Ya shak’o wuyan Junaid din, ransa amatukar b’ace, cikin kuma son d’and’anawa  Junaid din thesame azabar da yake ganawa Jannart yace.

“Ina kakai Jannart! Kafadamin Ina kakaita, kasan inda take tabbas, ba kuma abunda bak’ar zuciyarka bazata iya sawa ka aikata ba, kafadamin Ina ka kai mana Jannart!!!?”

Barrister Kabir din ya k’are maganan cikin tsawa sosai.

Tare da sake makure wuyan Junaid.

Junaid kuwa idanunsa ya Dan zaro cike  da mamaki yace.

“Wai Abba mekakeson fad’ane? Ni ban San inda Jannart take ba, ba kuma nina d’auketa ba, na d’auketa ma nakaita Ina, watakila tanacan ta tafi yawon banz……”

Wani irin wawan mari Barrister Kabir din ya zabgawa Junaid din akan fuskar sa, cikin tsananin b’acin rai da hasala, ya kuma sake zabga masa wani marin,  wanda har saida hakan yasa fuskarJunaid din tayi jajur mgnar da yake son fitarwa kan Jannart ta makale,  idanunsa ya zazzaro lokaci daya tare da somayin huci.

Barrister Kabir kuwa ji yake Kamar ya rufe Junaid din da duka, ransa yakai kololuwa wajen b’aci da irin mugayen furucin da Junaid din ka jefar Jannart dasu.

 Cikin fad’a sosai ya juyo ga Daddy dake tsaye yace.

“Yaya ka fad’awa Junaid na bashi nanda anjima yaje duk inda ya kaita ya daukota, ni nasani shine ya sace ta, domin kuwa shine last mutumin daya kirata awaya.

Uban meya gaya mata a wayan? 

sannan meye dalilinsa na kiranta awaya?

 Shi ya sace ta, saboda ya cika banzan burinsa na dabbanci akanta, komai zaiyi kuma bakayi masa magana, gashi nan kaga illar da hakan ya jawo ko Yaya?, gashi nan ya saceta ya rabamu da ita, ya kaita inda zai cutar da ita.

Yaya kana mance Jannart marainiyace amma ya maida cutar da ita tamkar abinci da ruwan shansa, Allah ya  wadaran hali irin naka Junaid.”

Barrister Kabir din ya kare maganar cikin muryar kukan daya zo masa”.

Momy da Abdull dake tsaye agefe kuwa, gaba dayansu kuka suka saka, saboda.

 Sunsan cewa tabbas Junaid din zai iya aikata hakan, ballema jiyan Momy da kunnuwanta taji yana cewa saiya cika burinsa akan Jannart din.

Daddy kuwa ransa Idan yakai dubu to  yayi masifar b’aci, akaron farko kuma cikin fushi, ya dawo da kallonsa ga Junaid, tare kuma da ta sowa ya nufi kan Junaid din.

“Ina kakaita Junaid, Ina kakai min Jannart?

 Ka fad’amin Ina kakaita? Junaid me zakayi da ita.”  Daddyn ya tambayesa atsawace.

Abunda Bai tab’ayiwa Junaid din ba kenan, musamman akan Jannart.

Ganin hakanne kuma yasa Junaid din soma girgiza kansa, cikin mamakin tuhuman da sukeyi Mishi yace.

“Wallahi Allah Daddy bani na dauketa ba, bansan inda take ba, bani na sace ta ba.”

Cikin nuna ɓacin rai a fili Barrister Kabir dake tsaye.

Cikin rufe idaunsa da kuma mance alak’ae dake tsakaninsu yace.

“Nabaka nan da awa 2 Junaid, Lallai-Lallai kanemomin Jannart, duk inda ka kaita, kaje ka daukota Idan kaki kuma nida kai bibbiyu, wallahi-wallahi saikayi dana sanin sace marainiyar Allah da kayi.”

Sake dawo da kallonsa ga Daddy yayi,  kana cikin tafasar zuciyar dake bayyana zai iya aikata komai akan b’atan Jannart din yace.

“Yaya kasa baki kasake tuna masa, awa 2 na basa ya fito da ita daga inda ya b’oyeta,  sannan yanzu zan.

 Kaiwa y’an sanda report, bayan haka kuma zan zagaya  cikin duk wani asibiti da nasan yana cikin garin nan, dole ayau asamo inda Jannart  take.”

Yana gama fad’an haka ya juya kaitsaye ya nufi hanyar fita daga gidan.

Koda yazo bakin gate harara ya watsawa Ashiru, kana cikin takaici yace.

“Shashasha kana nan tsaye abakin gate Koda yaushe, amma ka kasa sanin fita da shigan mutane sakaran banza kawai.”

Ya Kai karshen maganan nasa yana me bankad’e Ashiru’n, Cikin pretending yasakai ya fice daga Cikin gidan.

Daddy kuwa zuwa yanzu saboda tsananin bakinciki, da takaici da kuma Tarin bacin rai, jikinsa har rawa ya somayi yayinda yake jin, tamkar yasaka hannayensa aka ya kurma ihu, saboda b’atan Jannart din.

Sanin bashi da wata makamane kuma yasa shi, soma balbale guards din, Jannart din.

Cikin fushi hadi da bala’in dake cinsa yace.

“Bantab’a nadaman ajiyeku

Acikin gidana ba sai yau, k’attin banza k’attin wofi kafuran arnan da basa sallah, tayaya ma za’ace yarinyar da nake biyanku mak’udan kud’i duk wata akanta, za’a nemeta  a rasa, ashema k’attin wofi dana banza na tara, lusarai way’anda basu da aiki sai ci da kwanciya, ku fita ku barmin gidana yanzu basai anjima ba, dukka na sallameku, kada na sake.

 Ganin Koda mummunar fuskar daya daga cikinku ne, ku fitamin agida.”

Daddyn ya kare maganan cikin bacin rai.

Dan har yanajin tamkar ya rufe guards din da duka.

Sukuwa k’attin banzan, sun matukar ji haushin zagin da Alhajin yayi musu, aso da niyarsu kuma shine su tanka masa, amma kuma saidai tuna cewar zai iyasa a dauresu ne, yasa basu tanka masa ba, sad’ab-sad’ab haka suka kwashe komatsansu suka fice daga cikin gidan. 

Junaid kuwa zaman dirshan yayi, yana Mejin wani irin tafasar zuciya, saboda alluran nasa ta motsa, sosai matukan da Barrister Kabir ya sharara masa suka tsaya masa arai.

Lallai Barrister Kabir din yayi sa’a, kasancewar shi kanin mahaifinsa, domin yau da ace wanine daban Yayi masa hakan ba Barrister din ba, yayi rantsuwa bindiga zaisa ya harbe mutum.

Acan b’angaren Barrister Kabir din kuwa, yana fita daga cikin gidan, motarsa da yayi parking awaje ya shiga, bayan yayiwa motar key ne kuma, ya saki wani irin Murmushi, mai kama da dariya.

Hakika irin wannan firgicin ya jima yanaso ya gani, akan fuskar Yayan nasa akan Jannart dama shima  Junaid, wannan tsoron shiyake matukar so yaga yayi tasiri acikin zuciyarsu

“Tu kunnma Alhaji Idi Sale Dakata, wannan kadan daga cikin bangon littafin tashin hankalin da zaka fad’ane anan gaba.”

Barrister Kabir din ya fad’a abayyane, kana zuciyarsa cike da nishadi ya nufi gidan Dr Sajo domin dama duk abunda yakeyi dazun, pretending ne kawai ba komai ba.

Koda ya isa gidan Dr. Sajon kuwa, ya samu Doctorn na nan kasancewar yau din weekend babu aiki.

Har cikin falon Dr Sajon kuwa ya shiga, bisa jagorancin wani Dan matashin saurayi wanda zai iya kai sa’an Rayyern.

wanda kuma yake dan Dr Sajon ne. 

Yana shiga cikin falon ya durk’usa guiwowinsa ak’asa, tare da kai goshinsa k’asa, yayiwa Allah Sujjada, wani irin farinciki yakeji acikin zuciyarsa, bayan ya d’ago daga sujjadan ne kuma ya kalli Dr. Sajo dake kallonsa yana murmushi, cikin matukar farinciki yace.

“Alhamdulillah Allah abun godiya, doctor shawararmu tayi, komai da muka tsara ya tafi yanda ya kamata, Insha Allahu yanzu kwata-kwata ma hankalinsu bazai tab’a zuwa kaina ba.”

Murmushi Dr  Sajon ya faɗada lokaci daya kuma farinciki ya bayyana akan fuskarsa.

Barrister Kabir kuwa ci gaba yayi da cewa.

“Junaid ya daure kansa da kansa, da zaluncin da yakeyi wa Jannart tsawon shekaru.

 yanzu shikansa Yaya Idi bai isa yayi wani tunani akan abunda ya shafeni ba, Alhamdulillah Allah.”

 

Still murmushi mai kama da dariya Dr Sajon yayi, cikin kuma jin dadin labarin da Barrister Kabir din yazo masa dashi yace.

“Masha Allah Barrister Kabir, wannan abu yayi dadi, haka mukeso yanzu kaga mun dauke hankalinsu daga kan komai, zasu tsaya wa abu daya ne kawai, inda kaikuma zaka ci gaba da bincike, da kuma kara Adana hujjojinka, sannan Jannart kuma tana killace a gidan mijinta, Alhamdulillah Wannan shine matakin nasara na farko da muka fara hawa.”

Kai Barrister Kabir din ya jinjina, kana cikin gamsuwa yace.

“Insha Allah, da sannu duk wani kulli zai warware, gaskiya kuma zatayi halinta, yanzu sunacan hankalinsu duk atashe, musamman shi Yaya.”

Dariya Dr Sajo yayi, tare da gyara zamansa, cikin ya bawa shirin nasu yace.

“Aikinmu yayi kyau gaskiya, Allah kuma ya dafa mana.”

“Ameen summa Ameen.”

Barrister Kabir din ya amsa, zuciyarsa wasai babu wani alaman damuwa.

Hira suka d’an tab’a kad’n da Dr Sajon, kafun daga bisani Barrister Kabir din ya tashi ya tafi.

Acan gidansu Rayyern kuwa, kusan atare suka jero wajen shigowa cikin gidan.

Wanda kuma dawowarsu kenan daga sallan asuba.

Abba, da kuma Dr.  Rayyern ne agaba, sai Ramadan da Riyyam-nsra dake take musu baya.

Ahaka suka k’araso cikin babban falon dake k’asa, tare da neman waje kowannensu ya zauna.

Mamy kuwa sanin zaman shan coffee al’adar mazan gidanne, yasa tun kafun su dawo daga masallacin ta gama had’a musu coffee wanda yaji kayan k’amshi.

Ganin shigowarsu Cikin falonne kuma yasa,  Mamy daukan coffee din tare da tahowa cikin falon.

Zama tayi a tsakiyarsu

Kana ta fara tsiyayawa kowannensu a mug ta mik’a musu.

Riyyam-nsra ne ya Karb’i Mug din coffee din da Mamyn ke mik’o masa, tare da tank’washe k’afafunsa, cikin yanayin jin dadi yace.

“Mamy ngd. Da wannan al’farmar, da na samu.

Wanda yake sawa nake ga kamar ina gaban Mammy na dan itama haka takeyi min

da zaran nadawo amasallaci sai  ta bamu abun tab’awa.

 wannan yana d’aya daga cikin abunda yasa naji zaman gidannan yafi min na hotel.” 

Dariya Mamy da Ramadan sukayi, domin hatta Abba ma saida ya dan murmusa.

Shikuwa Rayyern gaba daya ma ya dauke wuta, Yayinda ya Kawar da kansa gefe, ahankali yake sipping coffee din, ko gefen dasu Riyyam din suke kuwa bai kalla ba.

Mamy kuwa bayan ta kammala had’a musu komai ne, ta mike tare da komawa kitchine, mug din coffee din da ta had’ashi musamman dan Jannart ta d’auka,  Koda ta fito daga cikin kitchine din, batare da ta tankawa su Ramadan da Riyyam dake hira ba.

 kaitsaye ta  wuce dakin Jannart.

Ahankali ta murd’a handle din kofar falon ta shiga, kamar kuma yanda ta tsammata hakanne ya kasance, saboda babu kowa acikin falon.

Kaitsaye kofar bedroom din ta nufa, Koda taje tsayawa tayi abakin kofar tare, da d’an k’wank’wasawa kana cikin kulawa takira sunanta.

“Jannart.”

A can cikin Bedroom kuwa.

Jannart dake zaune akan sallayan jin muryar Mamyn na kiran sunanta ne yasa ta, amsawa aladabce.

Mamy kuwa dake tsaye, jin Jannart din ta amsa ne, yasa ta tura kofar dakin ahankali ta shiga, bakinta dauke da sallama.” 

Ganin Jannart din da tayi akan sallayane kuma, yasa kata sakin Murmushi, cikin kulawa tace.

“Masha Allah Jannart kin tashi ashe.”

Kai Jannart din ta jinjina alaman Eh, lokaci daya kuma tayi kasa da kanta, cikin sassanyar muryarta dake bayyana zallan ladabinta tace.

“Mamy inakwana.”

Yalwataccen murmushi Mamyn tayi, tare da cewa.

“Lafiya lau Jannart, fatan kema kintashi lafiya ya jikinki?”

Cikin jin daɗi tace.

“Da sauki sosai.”

Jannart din ta bata amsa tana medan wasa da yatsun hannunta.

“Masha Allah, haka akeso Allah ya kara sauki”.

“Amin Mamy ngd”.

Jannart ta kuma faɗa.

Ita kuwa Mamy murmushin jin daɗi tayi tare da cewa.

 “Ga coffee nan mai zafi maza ki shanye shi.

zakiji d’umi  cikinki zai ware.”

Mamyn ta fad’a tana me ajiye mata mug din Coffee din.

“Toh Mamy Nagode.”

Still Jannart din ta fada tana mekokarin gyara zamanta.

Mamy kuwa murmushi tayi tare da cewa.

“Ba komai Jannart, ki saki jikinki, Idan kinsha coffee din kuma zaki iya komawa bacci, ki dai samu ki huta kinji ko.”

Kai Jannart din ta jinjina, inda Mamyn kuwa cike da kauna, hadi da yaba hankalin yarinyar ta juya ta fita.

Ganin fitar Mamyn ne kuma yasa, Jannart daukan coffee din ahankali ta soma sha, saboda dadin da coffee din yayi ne kuma yasa harta shanye feye da rabinshi, batare da ta farga ba cin cikinta yayi dumine kuma yasa aje sauran.

Alhamdulillah kuma ta danji karfi ajikinta.

Mamy kuwa tana fita daga dakin Jannart din, direct kitchine ta sake wucewa.

Dan soma shirin aikin breakfast.

Yayinda kuma har yanzu Ramadan da Riyyam ke zaune acikin falon suna tad’i. 

Kasancewar tuntuni Rayyern ya tashi ya haura sama, Koda yaje dakin nasa ma kuma kwanciyaya yayi, saboda gaba daya Daren jiya baiwani samu isashshen bacci ba.

Cikin sa’a kuwa Yana kwanciya bacci ya d’aukesa. 

7:30 pm dai-dai.

Mamyn ta kammala had’a duk wani abu da takeyi.

Ita da Riyyam ne kuma suka jere duk abincin akan dining table, Yayinda Abba da kuma Ramadan ke zaune acikin falon.

“Bismillah komai ya zama ready, Ina Rayyern bai sauk’o ba ko.”

Mamy ta fad’a adai-dai lokacin da take ajiye plate plates na cin abincin.

Jin abunda ta fad’ane kuma yasa Abba dake zaune yana karatun Alqur’ani juyowa ya kalleta,  cikin tausasa harshe yace.

“Masha Allah, amma nikam daga yau na daina cin abinci acikin ku.

 ana shiryamin nawa Acan dining table dina”

Murmushi Mamy tayi, cikin gamsuwa da kuma fahimta mijin nata tace.

“To shikenan Ranka ya dad’e Insha Allah, naka shirin ma na musamman zanna maka.”

Yar dariya sukayi, Yayinda Riyyam-nsra kuwa Kallon Abban yayi, cikin nishadi  Yace.

“Abba Kai bazakayi irin na turawa bane.”

Murmushi Abban yayi, tare da girgiza kansa yace.

“To ni ai ba bature bane Riyyam.”

Kai Riyyam ya jinjina aransa yana mejin dadi, saboda akaron farko kenan da yaga Abban yayi masa murmushi, tabbas yaji dadin abun. 

Mamy kuwa cewa tayi, Ramadan da Riyyam duk su taso suzo suci abinci.

Aikuwa dama kaman jira suke, zama sukayi akan dining table din, Yayinda Mamy da kanta tayi saving dinsu, kana Itama tayi saving din kanta.

Abba kuwa har yanzu yana nan zaune acikin falon.

Suna cikin cin abincinne kuma Mamy ta d’an d’ago Kai ta kalli Abban.

Cikin tausasa muryarta irin na mata masu ladabi ga mazajensu tace.

“Yauwa Alhaji, yarinyar nan Jannart kaga irin yanayin yanda tazo gidannan, komai anyisa ne asace a boye.

Hakan yasa batazo da suturun sawa ba, sai nake ganin maizai hana, Indai babu matsala a fita aje asamomata suturun sawa.”

Kai Abban ya jinjina cike da gamsuwar abunda Mamyn ta fad’a yace.

“Tabbas ya kamata kam asamomata kayan sawa,  tun dai ayanzu kam duk wani hakkinta ci da shanta da sutura jinya yana wuyan Mijinta ne, saboda haka ku tambayesa ya bada kudi, Idan yaso sai kije kiyi mata duk wata sayayya da ta dace.” 

Kai Mamy ta jinjina, cikin kuma yin kasa da murya da alaman ladabi tace.

“Mijinta kuwa?”

“K’warai kuwa shid’in dai, ai yanzu duk wani nauyinta ya rataya ne akan wuyansa ne.

Hakkinsa ne dole kuma shi zai sauke dan haka ya fara da wurima.”

Kai Mamyn ta jinjina, kana a gamsashe tace.

“To shikenan Insha Allah zanyi masa magana.” 

Daga haka kuwa babu wanda ya sake cewa komai, suka ci gaba da cin abincinsu.

Bayan sun kammala ne cin abincinnasu ne kuma suka dawo  cikin falon.

Mamy kuwa Ganin lokaci ya danja sosai ne, yasa ta kalli Ramadan, kana cikin kulawa tace.

“Ramadan jeka kiramin Hammanku, gashi har kusan goma ko breakfast bai sauk’o yayi ba.”

“To.” Ramadan yace tare kuma da mik’ewa ya haura sama, Koda ya k’arasa d’akin Rayyern d’in, samunsa yayi acikin blanket yana ta bacci.

Batare daya tashesa ba kuma ya juyo, tare da dawowa falon.

Tun kafun ya zauna kuma ya kalli Mamyn tare da cewa.

“Mamy Hamma Rayyern fa bacci yakeyi, ni kuma gaskiya tsoron tashinsa nake kada na tashesa kuma ya hauni da fad’a.”

D’an Jim Mamyn tayi, tare da mik’ewa tsaye tace.

“Shikenan badamuwa bari na fad’awa Abban ku.”

Kaitsaye falon Abban ta wuce.

Koda taje zaune tasa meshi, zama tayi ad’an gefensa kana cikin tausasa Murya tace.

“Natura Ramadan ya kira Rayyern, amma yace bacci yake har yanzu bai tashi ba, ka kumasan Rayyern kwata kwata baya so atashesa Idan yana bacci kasan matsalar ciwon kansa.”

Kai Abban ya girgiza bayan ya tankwashe kafafunsa ne kuma ya d’ago da kansa ya kalli Mamyn, cikin bada umarni kuma yace.

“Yau dai kam atashesa daga baccin da yakeyi, saboda yana da kyau yasan cewar yanzu bawai lokacin kansa kawai yake dashi ba.

Yana da lokaci wata, maza ki tura Ramadan ya taso sa.”

Kai Mamyn ta jinjina, cikin Dan ladabtar da murya tace.

“Ramadan yace yana jin tsoron tashin sa, kada Yayi masa fad’a”

“To ke kije ki tasosa.”

Abban ya fad’a kaitsaye.

Jin hakanne kuma yasa Mamy yin shiru, saboda tasani Sam Rayyern bayaso Idan yana bacci azo atashesa any how, musamman kuma kasancewar yana da matsalan ciwon Kai,  shiyasa Mamyn ma take gudun yin duk wani abu dazai takurasa, domin tun yana karaminsa, Idan yana bacci bata  cika son tashinsa, saidai idan ya gaji ya tashi dan kansa. 

Fahimtar hakanne kuma yasa Abba mik’ewa tsaye, tare da cewa.

“To ni bari naje na tasosa da kaina.”

Hakan kuwa akayi inda kaitsaye ya nufi sama, nan sashin Rayyern din.

Yana zuwa kuwa ya tura kofar dakin ya shiga.

Still Rayyern din bacci yake.

 Yayinda ya lullub’e duka jikinsa da blanket.

Karasa shigowa dakin Abba yayi,

Idanu ya ɗan zuwa fuskar Rayyern ɗin yana mai tuno wata kamanceceniya.

Numfashi ya ɗan fesar tare kuma da matsowa ya daura hannunsa dai-dai kan wuyan Rayyern din, Jin da yayi jikin Rayyern d’in babu alaman zafi ne, yasa shi soma kiran sunansa a nitse.

“Rayyern! Rayyern!! Rayyern!!!.”

Abban ya kira sunansa sau uku cikin kuma yanayin Dan daga murya. 

Take kuma sauti da Amon muryar Abban ya ratsa kunnuwansa, wanda hakan ya  sashi soma bud’e lumsasssun idanunsa ahankali, lokaci daya kuma jijiyoyin kansa suka amsa.

Saidai Ganin Abban nasa da yayi atsaye ne yasashi karasa bude idanunsa. 

Abba kuwa gyara tsayuwarsa yayi, tare da cewa.

“Katashi daga wannan baccin da kakeyi kaje kaci abinci, sam baka karya ba, sannan kuma ka kawo kudi za’aje a iyawa matarka sayayya.”

Jin an ambaci mata ne kuma yasa shi shagwab’e fuska, tare da karyar da wuyansa gefe, cikin zallar yanayin shagwab’a yace.

“Abba kudi kuma, ni fa banida kudi.”

Tsareshi da ido Abban yayi, kana cikin tsare gida yace.

“Ka kawo kudi za’ayiwa matarka sayayya nace, ko kamanta cewar yanzu duk wani  ci da sha da tufatarwar ta yana wuyanka ne?”

Bakinsa ya d’an tura gaba, kana cikin lumshe ido, ya mirgina gefe tare da saka hannunsa akan bedside drawer, ya d’auko Atm card d’insa, mikawa Abban atm card din yayi, still yana ta tura baki tamkar wani karamin yaro.

Abba kuwa karb’an atm card din yayi, batare daya sake cewa Rayyern din komai ba ya juya ya fice sabida yasan Ramadan yasan pin number sa.

Yana fita kuwa Rayyern ya sake langwab’ar da kansa, cikin wani irin takaicin yarinyar da aka tashesa daga baccin da yakeyi ta sanadiyarta,  kwana daya kawai tak da tayi agidannasu, yau gashi har an fara takura rayuwarsa da shiga sabgar sa a kanta.

Abba kuwa Koda ya sauko kasa, atm card din ya bawa Mamy tare da cewa.

“Kisaya mata duk wani abu da kikasan zata buk’ata, maganan suturun sawa kuma ki saya mata isassu, komai da komai ahada a saya mata.”

“To Insha Allah, zan saya mata duk wani abu daya dace.”

Ramadan dake gefe ne kuma  yace. 

“Mamy nida Riyyam zamuyi miki rakiya, ko Riyyam.”

Ya ƙare mgnar yana kallon Riyyam-nsra.

Kai Riyyam ya jinjina cikin sauri, hade da cewa.

“Eh Mamy zamu rakaki, Ado Bayero Mall zamuje ko Jifatu, ko kuma  Mudassir and Brothers?” 

Murmushi Mamy tayi, tare da cewa.

“Shoprite dindai zamu fara zuwa, saboda nasan akwai komai da komai, Idan akazo b’angaren dogin riguna kuma, sai muje Jifatu, yanzu dai bari naje na shirya saina zo mutafi.”

“To.”

Suka amsa mata.

Ramadan kuma juyowa yayi ya kalli Riyyam-nsra tare da cewa.

“Wai ni kam yaushe kasan Kano haka!?.”

Kai ya shafa tare da cewa.

“Nida jihata ƙasata!”.

Kiran wayarshi da akayi ne yasa baibi ta kan furucin Riyyam-nsra ba.

Yayinda ita kuwa Mamy kaitsaye bedroom dinta ta wuce, bayan tayi wankane kuma ta shirya kanta acikin, wani tsadadden leshi, tare da yafa mayafinta cikin kamala ta fito.

Kaitsaye kuma d’akin Jannart din ta nufa.

Koda ta shiga falon, yanzun ma bata iske Jannart dinba shiyasa kaitsaye ta wuce cikin d’akin.

A dai-dai lokacin kuwa Jannart din, zaune take abakin gado, hannunta rike da wani dan littafi na turanci tana karantawa, wanda kuma yana daya daga cikin, yan abubuwan da ta taho dashi.

Ganin Mamy da tayi ne kuma, yasa tayi saurin sunkuyar da kanta k’asa, Mamy kuwa murmushi tayi, kana cikin kulawa tace. 

“Jannart nida Ramadan da Riyyam zamuje kasuwa, sannan Abbanku ma zasu fita yanzu saboda naji dazu suna magana da Baba Maud’o akan cewar zasuje wani waje.”

Cikin girmama tace.

“Toh Mamy sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya”.

Amin Mamy kana ta daura da cewa.

“Yanzu ki fad’amin me dame kikeso asayo miki Idan munje.”

Kai Jannart din ta dan sunkuyar k’asa, cikin sanyin murya, had’i da tsantsar ladabinta ga Mamyn tace.

“Mamy duk abunda kika sayamin yayi.”

Kai Mamyn ta jinjina cike da gamsuwa kuma tace.

“Masha Allah! To bari muje saimun dawo ko. Idan zaman dakin ya isheki, zaki iya fitowa falonki kisha iska, ko kallo kiyi nasan zai d’ebe miki kewa kafin mu dawo”.

“To Mamy, amman sai yaushe zaku dawo ne?”.

Jannart din ta tambaya, cikin tausasa murya.

Murmushi Mamyn tayi, again kuma itama cikin kulawa tace.

“Jannart kinsan yanayin kasuwa, Idan ka shigesa sai abunda Allah yayi, kana lisssafin zaka dawo da wurwuri, kuma sai kaga ba haka abun yake ba.”

Kai Jannart din ta jinjina, inda Mamy kuwa ta cigaba da cewa.

“Ni kaina bansan yaushe zamu dawo ba, saboda iya yanayin cikowan jama’a,n da muka samu, iya jimawan mu, amma dai Ina da yakinin bazamu wuce azahar ba.”

“Mamy har azahar.”

Jannart din ta tambaya fuska a karye.

“Eh mana Jannart, domin ya danganta da irin abubuwan da zamu saya, kuma kinga yanzu ma ana neman wajen karfe sha d’aya bamu tafiba.”

Kai Jannart din ta jinjina tare da gyara zamanta, tace.

“To Mamy saikun dawo Allah ya tsare.”

Da “Ameen.”

Mamyn ta amsa, harta juya zata fitane kuma idanunta suka Sauk’a, akan breakfast din da ta kawowa Jannart din, wanda ko tab’ashi batayi ba.

Kallonta Mamyn tayi, kana cikin kulawa tace.

“Jannart Meyasa baki ci abincin dana kawo miki ba?.”

Kai Jannart din ta dan sunkuyar kasa, kana murya  asanyaye tace.

“Mamy banajin yunwa sosai ne, amma zanci zuwa anjima.”

“A’akam, banyarda da hakan ba, sam ban lamunci zama da yunwa ba sauk’o maza kici abinci kinji.”

Mamyn ta fad’a tana me kamo hannunta, ta zaunar da ita akan sofa, tare da matso mata kwanon abincin gabanta, cikin kulawa kuma tace.

“Kici abinci kinji, kada ki zauna da yunwa, domin yunwa tana illatar da lafiya, ko ke dinma irin Mijin naki ne, baku damu da abinci ba sai kayan kwalama.”

Shiru Jannart din tayi, kana Cikin matukar kunya, ta sadda kanta kasa, domin aduk sanda taji ance mijinta, wani irin abu ne takeji mai nauyi ya tsaya akan kirjinta to waye mijin? Ya yake? Me halinsa?.

Wadanan sune tambayoyin da takewa kanta tun jiya.

  Mamy kuwa zuba mata abincin acikin plate tayi, tare da cewa.

“Idan kina buk’atar wani abu kafun mudawo, akwai kitchine anan cikin falon mu.

 Taso ma muje na nuna miki.”

Mamyn ta fad’a tana me kamo, hannunta babu musu kuwa Jannart din ta mik’e, tare dabin bayan Mamyn suka fito, har cikin babban falon.

“Kinga wannan shine kitchine dinmu, wacccan kofan kuma anan part dina dana Abbansu Rayyern yake akwai  kofar shiga da fita ta cikin falonmu wanda ba sai anbi ta nan ba.”

Mamyn ta fad’a tana meyi mata nuni da kitchine da kuma sashin su ita da Abba.

Kai Jannart din ta jinjina cike da gamsuwa.

“Can kuma dakunan k’asane irin Part ɗin dake sama ne. sai kuma sama inda anan bedroom na Rayyern, da kuma Ramadan suke, sai kuma extra part guda d’aya da yake can ta woje.

Sai nasu Baba Mauɗo, sai wanda kike ciki.

A can saman Mai gidanki yake.”

Mamyn ta k’are maganan tana meyi mata nuni da saman.

Jannart kuwa, kanta tad’an sadda k’asa, tare kuma da soma wasa da y’an yatsun hannunta, kana cikin sanyin murya tace.

“Mamy To meza’a girka yau d’in, kafun kudawo zan girka tunda dama ina zaune ne kawai babu abunda nakeyi.”   

Murmushi Mamy tayi, tare da girgiza Kanta, kana cikin tsananin kulawa tace.

“A’a ki huta kinji Januart, bana son ki shiga kitchine daga yanzu.

Idan na dawo, zan girka abincin karki damu, ai bazamu wani jima sosai ba”

Dan juya  kanta, tayi, saboda zuwan su Ramadan da kuma Riyyam kallonsu ta ɗanyi kana ta juyo ta kalli Mamy,  atsanake cikin yanayin dake nuna biyayyarta tace.

“Da gaske Allah Mamy zanyi girkin, kinga zaku   dawo a gajiye.”

Riyyam-nsra da yake karasowa wajennasu ne yayi saurin cab’e zancen da cewa.

“Please mana Mamy kibar My Aunty  tayi mana girki yau, nasan abincinta dole zaiyi dadi.”

  Jin muryar Riyyam-nsra dinne kuma yasa Jannart ɗin.

 Dan dago da kanta, ta kallesu dai dai lokacinne kuma Ramadan ma

Ya karaso wajen.

Fuskarsa dauke da murmushi kuma yake Kallon matar Hamman nasa.

Cikin sakin fuska da kuma walwala yace.

“Good morning my beautiful Aunty, ya kwanan bak’unta.”

Murmushi ta ɗanyi kana ta ɗan kalleshi. 

Tare da cewa tace.

“Morning.”

Riyyam ne yayi saurin matsowa kusa da ita, tare da danyin kasa da muryarsa, cikin kulawa yace.

“Aha My Aunty kin tunani ko?”.

cikin ɗan sakin fuska ta gyaɗa mishi kai, alamun ta tunoshi haduwarsu a airport,

Cikin yanayin rawan kansa yace.

“Aunty Jannart ni sunana Riyyam-nsra, tiktokers nasan kinsani ko?”.

Murmushi tayi tare da gyaɗa kai, ganin yadda ya tsareta da ido.

Kuma tabbas ta tunoshi haɗuwarsu a airport.

Shima murmushi yayi tare da cewa.

“Yauwa shi kuma wannan Hamma Ramadan sunansa, kuma yaya nane, akwai kuma babban yayanmu  Hamma Rayyern.”

“Please kiyi mana abinci maidadi kinji, wanda zaisa kunnuwanmu su motsa.”

Ba iya Mamy da Ramadan ba harta ita saida ta saki murmushi mai hade da dan dariya.

Mamy kuwa Ganin lokaci na k’ure musu ne yasa, tace.

“Jannart rabu da shirmen Riyyam, koma daki kije kici abincinki.

Maganan girki kuma tunda kin dage sai kinyi, ki dafa mana abu mai sauki kawai.”

Kai Jannart din ta jinjina, sannan cikin zazzakar muryarta tace.

“Mamy ku dawo lafiya.”

Da “Ameen” duk sauka amsa, inda Mamy ta had’a kan Ramadan da Riyyam sukayi waje. 

Itakuwa Jannart d’akinta ta koma, duk da cewar bata wani jin yunwa amma haka ta zauna ta d’an ci abincin, bayan ta kammala ne kuma ta d’aura da, lemon strawberry da Mamyn ta had’o mata dashi.

Gyatsa mai sanyi tayi tare da cewa.

“Alhamdulillah”.

Kana ta yunƙura 

A nitse ta mik’e tsaye tare da d’aukan plates din da taci abincin ta fita dashi.

A hankali ta buɗe ƙofar falon nata.

Kana ta sako kanta.

Cikin Babban falon.

Numfashi ta dan fesar sabida wani irin masifeffen sanyin AC’n da suke busowa duka biyu.

A hankali take takowa har ta iso tsakiyar falon.

“Masha Allah, Mamy ba dai tsabta ba”.

Ta faɗi haka tana jujjuya kai tana kallon komai doke cikin falon.

Tsab-tsab sai ƙamshi da sanyi daya wadaci falon.

A hankali ta juyo ta nufi Dinning area.

Tray’n dake hannunta ta ajiye kam table ɗin.

Kana ta juya a nitse.

Ta dawo tsakiyar falon.

Gaban tv ta nufa.

Sabida shiru da gidan yayi sai taji kamar tana tsoron gidan.

TV’n ta kunna cikin sa’a kuma kan tashar Sunnan TV yake.

Inda aka saka sautin muryar Malam Sulaiman.

Rage sautin tayi dai-dai misali.

Kana a hankali ta juya ta nufi Dinning area.

Tray’n data ajiye ta ɗauka a hankali ta nufi Kitchen kaitsaye.

“Wow. Masha Allah”.

Ta kuma faɗa tana mai bin tsarin Kitchen da kallo komai tsab-tsab.

Kai tsabta rahmace.

Ta kuma cewa tana mai 

nannad’e hannun rigarta.

 Tare kuma da k’arasawa gaban sink, plates din da taci abincin ta wanke, bayan ta kammala wanke wanken ne kuma.

Ta ɗan tsaya jim a tsakiyar Kitchen din.

Cikin sanyin murya tace.

“Toh me zan dafa?”.

Tayi mgnar alamun tambayar kai da kai.

Kanta ta ɗan jinjina kana matso gaban Fridge guda biyu dake cikin Kitchen din.

A hankali  ta bud’e babban deep freezer

Kai ta jinjina tare da ƙara matsowa.

 Gaba daya cikinsa shak’e yake da kayan Miya, hadi da kuma naman, Rago, Saniya, da kuma naman kaji, sai kifayen da tuni sun daskare ma acikin fridgen. 

 Naman kaza ta d’ebo d’an da-dai.

bayan ta wanke naman ne kuma ta zubashi acikin tukunya tare da kunna gas ta d’aurashi akai, al’basa ta ɗauka wanda ta gani a jere cikin wani da karfe.

Mai yawa ta yanka kana ta watsa a cikin naman.

 Kana ta ɗan kalli gefenta inda wasu robobi farare masu marafe pink color ke jere, da kayan bukatu kamarsu. k’amshi, da dandano.

 garlic, kanumfari da kuma maggi Corry ta saka. 

Kana ta meda marfin ta rufe.

Sai kuma taja kujera ɗaya dake gaban ɗan ƙaramin table ɗin dake tsakiyar Kitchen din ta zauna tana mai tunanin to me zata dafa musu.

Lokaci ɗaya.

Gidan ya cika da ƙamshin tafashen.

A hankali ta ɗan juyo ta kalli tukunyar daketa fidda tururi mai masifar ƙamshi.

Ganin naman na dahuwa  ne kuma yasa ta mike ta sake bud’e fridge din, inda ta ibo.

 Pease, green beans, carrot, green pepper, red chilies, cabbage, cucumber, onion, and liver,  tsayuwa tayi na musamman inda ta yanka kowannensu, awaje na musamman, saidai Banda carrot wanda tayi greeting d’insa. 

Bayan ta kammala duk wayannan dinne kuma, kazan na gama dahuwa.

Ta sauƙeshi kana ta ɗauki kaskon suya ta doro tare da zuba mai.

Kana ta fara  soya shi sama sama.

Tana gama ta ajiyeshi gefe.

Kana ta ɗauko kayan miyanta duk abin buƙata

 tare fara aikinta a nitse ta hada masa pepper onion chicken soup.

Gaba ɗaya kwamshin ya ƙara de ko ina.

Tana kammala had’a kazartata kuwa ta d’aura shinkafa kasancewar, fried rice and coleslaw takeson yi.

Da ɗan hanzarin taci gaba da aikinta yanayi tana ɗan jujjuyawa da waige-wauge na bakunta da kaɗaici.

 Cikin abunda bai wuce awa ɗaya da rabi ba kuwa ta kammala,  had’a abincin acikin babban food flask.

Bayan ta gama da abincinne kuma ta dawo b’angaren drinks.

 Shaka mai dadin gaske ta had’a musu, sai kuma pineapple and orange juice.

Cikin abunda bai wuce 50mn ba ta gama haɗa abubuwan shan, gidansu Rayyern din gaba d’aya ya kacame da k’amshin daddad’an girkinta. 

Ganin akwai sauran lokaci ne kuma yasa ta, had’a fan cake ta somayi.

Acan b’angaren Rayyern kuwa, sai yanzu yake tashi daga kwanciyar da yayi, ahankali ya zuro da k’afafunsa k’asa, tare kuma da mik’ewa, kaitsaye ya nufi bathroom saboda yanason sakarwa kansa ruwa.

Ajiyar zuciya ya sauk’e a dai-dai lokacin da yaji saukar ruwan shower ajikinsa, lokaci daya kuma ya lumshe idanunsa, tare da soma gogawa jikinsa sabulu.

Cikin  nutsuwa yayi wankasa, tare da d’auro alwala.

Yana fitowa daga cikin toilet din kuwa, k’arar fitar motar Abba, wanda suka fita da Baba Maud’o ya daki kunnensa.

Wanda ya fita da Baba Mauɗo.

D’an langawab’ar da kansa gefe yayi, tare dasa hannu ya shafa lafaffen cikinsa, kasancewar sai ayanzu ne ma yake tuna cewar rabonsa da abinci tun daren jiya,  sosai kuma zuwa yanzu yakejin yunwa na k’wak’ulan cikinsa.

Anutse ya shafawa jikinsa mai, bayan ya kammala  shafa mai dinne kuma, ya  karasa gaban Sif din kayansa.

Wani had’add’en rika da wando, masu masifar taushi pink color masu digon fari-fari.

 ya ciro tare da sakawa ajikinsa, kasancewar kuma rigar irin mai aninaye a gaban nanne, yasa faffadan chest d’insa bayyana.

Body spray ya shafa ajikinsa, tare kuma da d’aukan watch d’insa ya makala.

Masha Allah bak’aramin kyau shigar riga da wandon tayi masa ba, musamman ma yanda kawataccen sajensa keta shining ya kwanta lib.

Wayarsa ya d’auka, tare da k’arasawa, jikin dan karamin fridgen dake cikin dakin nasa ya bud’e,  fuskarsa ya d’an ya mutsa, saboda yanda yaga fridge din babu komai naci acikinsa, chocolates dinsa duk sun kare, sai drinks kawai da sukayi saura.

Maida murfin fridgen yayi ya rufe, kaitsaye kuma ya nufi cikin falon nasu dake sama, saidai still shima babu komai acikinsa, sai kayan shaye shaye.

Kansa ya d’an girgiza saboda yunwa sosai yakeji.

Batare da tunanin wani abu ba kuwa, ya nufi falon k’asa, inda ahankali yake sauk’owa daga kan matattakalan falon,  Yayinda k’amshin sa ke dada mamaye ko ina.

Saidai kuma jin da yayi ko ina shiru babu motsin mutanene yasashi soma rarraba idanunsa ba amun kowa a gidan.

Sai wani ɗan karen kamshin da yake shige masa hanci.

K’arasa sauk’owa daga kan steps din yayi, tare da k’arasowa tsakiyan falon ya tsaya, hannayensa duka biyu ya d’aura akan k’ugunsa, tare kuma da karyar da wuya ya d’an langwab’ar da kansa gefe, cike da alamun  shagwab’a.

Acan cikin kitchine kuwa Jannart ce tsaye, tana k’arasa had’a fan cake din da takeyi.

Tana aikinta a sake.

sabida doguwar rigarta ne ajikinta, sai kuma dan kwalin rigar da ta daura akanta, wanda hakanne kuma  yasa dogon gashinta ya baje akan gadon bayanta kuma a zatonta babu kowa a gidan sai masu gadi.

Aikinta take cike da nutsuwa, Yayinda karatun al’q’uranin da ta kunna acikin falon ke kawowa kunnuwanta ziyara har Cikin Kitchen din shiyasa tsoronta ya kau. 

Rayyern kuwa daya gama k’arewa falon kallo, Ganin babu motsin kowa acikinsa ne, yasa kaitsaye ya nufi dining table, inda yaga manyan food flask a ajiye.

Acan b’angaren Barrister Kabir kuwa, Koda yabar gidan Dr. Sajo, kaitsaye wajen saida wayoyi ya nufa.

Iphone 11promax ya saya, tare kuma da sabon SIM, wanda  akayiwa register a matsayin nashi.

Daga shagon sayan wayan kuma, kaitsaye gida ya nufa.

Koda ya isa gidan nasa, anan falo ya samu Aunty Dijat zaune, yayinda Hafeeza ke kwance akan cinyarta  tanayi mata tsifa.

Hafeez kuwa yana can gefe, ya duk’ufa akan homework d’in da aka bashi a school. 

Shigowar Barrister dinne kuma yasa, duk yaran tashi Aguje sukaje suka rungume Babansu.

Aunty Dijat kuwa murmushi ta  sake, had’e da Kallon mijin nata cikin kulawa tace.

“Sannu da dawowa Abban Hafeez.”

Kai Barrister Kabir din ya jinjina mata, alaman amsawa, tare da neman waje agefenta ya zauna.

Mintin daya kawowa su Hafeez ya basu, tare da zaro Sabuwar wayan daya sayo ya soma kokarin saka sim.

Kallonsa Aunty Dijat tayi, cikin d’an yanayin mamaki kuma tace.

“Abban Hafeez wannan Wayarfa ta waye?”

Murmushi Barrister Kabir din yayi, tare da cewa.

“Wayar Jannart ce dana sai mata, saboda yanzu babu waya a hannunta, bakuma zataji dadin zama ba waya ba gaskiya.”

Murmushi Aunty Dijat din tayi, cikin yabawa da wayar tace.

“Masha Allah gaskiya wayar tayi kyau.” 

Kansa ya jinjina alaman godiya, batare daya sake cewa komai ba kuma ya mike kaitsaye ya wuce dakinsa. 

Rayyern kuwa ahankali yake taka k’afafunsa, cike da shagwab’a, had’i kuma da yunwar dake k’wak’ulan cikinsa, ya nufi hanyar kitchine din. 

Hannunsa dafe da cikinsa, cikin kuma kasalalliyar murya ya fara kiran sunan Mamy.

“Mamy! Mamy!!.”

Sai kuma ya ɗan sa hannunsa ya shafa cikinsa murya can ƙasa yaci gaba da cewa.

“Mamyna yunwa, please ki bani abinci..”

Ya Kai karshen maganan nasa, yana me gab da saka kansa acikin kitchine din.

Jannart dake tsaye cikin Kitchen din kuwa jin muryar mutum, akurkusa ne yasa ta saurin juyowa cike da tsoro.

Dai-dai lokacinne kuma ya sako kansa cikin kitchine din.

Ido hud’u da sukayi ne kuma yasa Zuciyar Jannart wani irin bugawa, take taji wani abu ya daki kirjinta, wanda har hakan yasa tayi saurin sadda kanta k’asa, tare da kama yatsunta ta had’esu waje d’aya.

Cike da…!

Back to top button