Uncategorized

Tubali book 1 Chapter 7 complete hausa novel

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

Yayinda acikin ranta take fata da kuma burin ganin auren d’an nata, Tabbas tana matuk’ar son ace mata Rayyern dinnata yayi aure, domin  kuwa ko babu komai zai samu macen da zata kula dashi, Wanda zata jib’anci duk wani al’amuransa, kama daga ci da sha zuwa farin cikinsa kula mishi da tsabtan muhalinsa ko Ramadan ma ya huta. 

Sai-dai kuma amma ya zata yi, tunda duk sun fahimci cewar ba son auren yake ba, baya shiga harkar mata, balle harsu saka ran cewar watarana zai samu wacce zata yi mishi.

Ido ta zuwa Ramadan wanda kiran wayarsa da akayi yasa ya miƙe ya nufi Dinning area, bisa kujera ya zauna.

Bisa alamu duk.

Raihana ce ta kirashi budurwarshi.

Rayyern kuwa yana isa cikin bedroom din, kayan jikinsa ya rage tare da shigewa cikin bathroom ya sakarwa kansa ruwa. 

Idanunsa ya lumshe adai-dai lokacin da yaji Sauk’an Sassayan ruwan showern akan fatar jikinsa. 

Haka yakejin wani irin nutsuwa na musamman na sauk’ar masa.

Ahankali kuma yakejin duk tarin gajiyar da yayi yana sauka.

Atsanake ya kammala wankan nasa, inda ya fito daga shi sai towel dake daure a kugunsa, ad’ayan hannun nasa kuwa mini towel ne Wanda yake tsane jikinsa dashi.

Bayan ya kammala ne kuma ya Shafawa jikinsa wani had’add’en mai, tare da men spray mai dadin kamshi. 

Sabin riga da wandon da ya ciro daga cikin drawer d’insa ya sa.

A hankali ya fito dan sauƙa ƙasa, coffee yake so ya ɗan sha.

Yana fita falo kuwa ya samu Abba da Ramadan a tsakiyar falon da alamun mgnar Aure Ramadan yakeyiwa Abba.

Shi kuwa Abba idanu kawai ya zubawa Ramadan yana kallonsa, ya sani a zatonsu bai damu da mgnar auren Rayyern bane.

Shi kuwa yasan sunada babban buri da manufa da shi yakeso yaga Rayyern ya cimmawa, so ganin bai damu da harkar mata bane yasa ya zuba mishi ido, tunda shi nuna musu yake baima san me akeyi da maceba shi kanshi yasan aiyukan daya ɗaurawa Rayyern sun mishi yawa sunfi ƙarfin shekarunsa kawai ƙarfin hali ne da ƙwazo da jarunta yasa yake iya leading komai yadda ya kamata, amman ya rasa lokacin kansa, yana son ya sashi ya saki aikin asibitin ya fuskanci kasuwanci su, to kuma yasan likitancin shine burinsa badon hakaba ai da sai ya bawa Ramadan sashin asibitin duk da dai yanzuma shi bai cika zuwaba. 

A hankali ya ƙara so kusa dasu.

Ganin haka ne yasa suma 

suka miƙe suka karasa kan dining table danyin dinner. 

Shidai Rayyern kamar kullum baiwani ci abincin kirki ba, ya tashi tare dayi musu sallama ya wuce side d’insa.

Yana shiga kuwa ya murzawa kofar tasa key.

Toilet ya koma ya sake dauro alwala, bayan ya fito ne kuma ya sanja kayan jikinsa izuwa payjamas mararsa nauyi.

Wata yar jaka da yake ajiyan chocolate d’insa ya dauko, tare da bud’e cikin jakan ya dauki babban ledan chocolate na milka & oreo, bayan ya Bare ledan ne kuma yasa chocolate din abakinsa, tare dayin switchoff na wutan dakin ya kwanta. 

D’an mirginawa yayi, kana ya dauki wayarsa dake aje akan gadon.

Sak’onnin Email da ake turo masa ya shiga dubawa atsanake, time to time kuma yake  lumshe ido saboda yanda yake jin dadi da kuma zakin chocolate din na game bakinsa. 

Ya dauki sama da 30minute kuwa yana duba sakonnin, inda yake replies na wasu sakonnin da suka zama dole, sauran sakonnin kuwa da basu da buƙatar amsa sharewa yayi tare da kashe datansa ya ajiye wayar. 

Yana gama shanye chocolate din nasa kuwa, ya daura kansa akan pillow tare da jawo blanket ya rufawa jikinsa. 

Addu’an kwanciya bacci yayi, kamar kuma yanda ya saba yi akowacce rana, haka yau dinma Yana me ambaton sunan Allah bacci ya daukesa.

              10:30 pm.

Jannart.

Sake had’e jikinta waje d’aya tayi, tare da rungume dan k’aramin pillown dake Manne akirjinta.

Ak’alla yanzu kusan mintuna 20 kenan da takeson bacci ya dauketa amma ya kasa, duk yanda takai ga rumtse Idanunta kuwa, To wasu kalan tunani ne ke bijurowa cikin k’wak’walwarta. 

Yayinda ƙamshin turaren dake fita ajikinta Yana me Ratsa cikin hancinta ya hana ta sakat.

Akasalance kuma cikin yanayin shagwab’a takai hannun ta dake kamshin turaren zuwa kan hancinta,  Sam batasan taya akayi kamshin dake jikin al’kyabban nasa ya kama jikinta ba har hakaba.

Gashi asanadiyar kamshin gaba daya ta kasa bacci, Wanda kuma batasan dalilin hakan ba.

Ajikinta takejin wani iri aduk sanda kamshin turaren nasa ya daki hancinta, har wanka tayi wai ko zata daina jin kamshin amma babu wani abu daya sanja.

“Oh Allah wannan wani irin jarababben kamshi ne haka daya kasa barin jikina?, Wani irin kamshi ne da shakansa ke haifar min da bugan zuciya, Yah Allah nidai kasa nayi bacci yanzu, Dan wallahi nagaji, daga saka al-kyabba kawai sai kamshin mai al’kyabban ya manne min.” 

Ta kai karshen maganan tana me sake kankame jikinta waje daya. 

Tare kuma da rumtse Idanunta da karfi, acewarta wai ko bacci zaizo ya dauketa.

Domin ita kanta ta kasa tantance hakikanin abunda kamshin ke bata, nutsuwa ne ko akasin haka.

Sai-dai koma meye tayi imani cewar kamshin nada matukar daɗi shaƙa da sanyaya rai .

Haka kuwa ta dinga juyi akan gadon nata, har sai wajajen 11 pm kafun bacci ya dauketa. 

         *Washegari.*

Kamar yanda ya saba kowacce rana, haka yau dinma ta kasance masa.

Saidai kuma kwalliyar tasa tayau ta banbanta dana sauran ranaku. 

Saboda kalan suit din nasa nayau Maroon ne, sai kuma milk colour long sleeve wacce ta kasance aciki.

Yayinda ya saka wa kafansa wasu tsadaddun takalma masu matukar kyau da daukar hankali. 

Yayi kyau matuka, musamman ga fuskarsa, Domin kuwa Lallausan bakin sajensa ya kwanta lub, haka ma gargasan saman idanu dana giran sa masu daukar hankali.

Agogon rolex daya daura akan tsintsiyar hannunsa ne kuma ya k’ara bayyana kyaun adon nasa.

Hakika Rayyern kyakkyawan matashi ne Wanda ya hada abubuwan so dana burgewa, komai nasa na dabanne, shiyasa abune mawuyaci Namiji ko Mace suyi mishi kallo daya su dauke kai.

Ahankali yake saukowa daga kan steps din falon, Yayinda gaba daya Rabin hankalinsa ke ga agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa yana Kallon lokaci.

Abba Mamy da kuma Ramadan da suke zaune akan dining table ne duk suka d’ago suka kalleshi. 

Abban ne kuma ya danyi gyaran murya, tare da cewa.

“Rayyern agogo sarkin aiki ka fito.”

Jin abunda Abban ya fad’a ne kuma yasa shi ɗan lumshe ido tare da longobar da kai bisa kafarsa.

Cikin kuma yanayin dake bayyana tsananin kaunar iyayen nasa yace.

“Abba Mamy barkanku da safiya.”

“Yauwa barka dai Rayyern ka fito ko, dama yanzu nake da shirin kiranka, Domin tun dazu na gama breakfast kuma naga yau baka sauko da wuri ba, yanzu fa wajen 8 ake nema.” 

Cewar Mamy dake kokarin hadawa Ramadan tea.

“Eyyah Mamy yau ba hospital zanje ba shiyasa ban sauko da wuri ba, inason naje na duba aikin company’n mu da ake ginawa ne, tun jiya engines din da nayi order a us suka iso, To yau inaso naje naga ya yanayin aikin yake tafiya, Domin na fiso daga ansa engines din abude company’n saboda mutane su amfana tunda an gama komai na gini haɗa enginer’s ɗin ne kawai ya rage kuma yau za’a fara.” 

D’an tsagaitawa da maganan nasa yayi, tare dajan kujera ya zauna.

Cikin sanyi kuma yaci gaba da cewa.

“Mamy da yawan matasa acikin Nigeria’n nan sunyi karatu, amma suna fama da matsalan rashin samun aikinyi, hakan kuwa shi yake sa wasunsu su shiga aikata abunda bai dace ba, yana da kyau ka inganta rayuwar na kasa dakai, da kuma mutanen dake neman taimako, wannan dalilin yasa zan d’ebi ma’aikata da yawa na zuba su acikin company’n saboda su samu hanyar da zasu na cin abinci da kuma biyan buk’atunsu ko Abbana?.”

Kai Abba da Mamy harma da Ramadan suka jinjina, cike kuma da tsananin gamsuwa Abba yace.

“Duk wani tunaninka dai-dai ne Rayyern, wannan yasa akoda yaushe nake alfahari dakai, Allah ya dafa muku akan duk wani abu da kukeso ku cimma kaida d’an uwanka.”

Da “Ameen.” Suka amsa su dukansu.

Nanfa Mamy ta had’a masa tea da soyayyen k’wai hadi plaintain yaci.

Bayan ya kammala ne kuma yayiwa iyayen nasa sallama, inda shida Ramadan suka fito atare.

Bayan sun shiga motocinsu ne kuma Baba Maud’o ya taso zai bud’e musu gate.

Da sauri Rayyern ya kira Hadi yace ya buɗe musu gate.

Toh yace kana ya buɗe musu.

nanfa kowa yayi hanyarsa, inda Ramadan ya nufi hospital dinnasu, shi kuwa Rayyern kaitsaye ya wuce inda ake ginin new company d’in. 

   Adai-dai lokacin daya mik’i titi ne kuma ya maida hankalinsa ga tukin da yakeyi.

Hakanan kuma yaji ajikinsa tamkar akwai wani abu dake faruwa.

Kansa yad’an d’aga Ahankali ya kalli mirror.

Karab kuwa idanunsa suka Sauk’a akan motar dake biye dashi abaya.

Idanunsa yadan kankance tare da maida kallonsa ga numbern dake jikin motar.

Wani irin murmushi yayi, a lokacin daya gane cewar motar da take bibiyarsa daren jiyane ta biyosa yau ma.

Kansa yadan jinjina, still ba tare da tsoro ko fargaban komai ba ya ci gaba da tukin, saidai lokaci zuwa lokaci yakan dago kansa ya kalli motar dake bibiyartasa ta cikin mirror. 

Adai-dai wannan lokacin kuwa a gidan su Jannart gaba dayansu zaune suke akan babban dining area’n da aka kawatasa da abubuwan burgewa. 

Dady Momy Abdull da kuma Jannart ne kecin abinci, Yayinda shi kuwa Junaid gaba daya hankalinsa ya maidashi ne ga Jannart.

Da yake watsa mata wani irin kallo, mai kama da na kiyayya da kuma tsananin jin haushi. 

Ita kuwa Jannart lura da tayi, da irin Kallon da Yayan nata ke watsa mata ne yasa ta kasa koda d’ago kanta.

Badan kuma tanajin yunwa ba haka take ta tura abincin acikin cikinta.

Junaid kuwa tsaida idanunsa da yayi akan  d’an karamin bakinta dake tauna abinci ne, yasashi sakin kwafa. 

Tare da cije labbansa, kana acikin zuciyarsa yace.

“Wallahi nayi rantsuwa duk ranan dana kama yarinyar nan ahanuna, bazan kyaleta ba sainaga bata numfashi, ko mutuwa zata yi kuwa bandamu ba saina sauke duk wani abunda nakeji, shegiyar yarinya mai kama da aljanu, kullum wutar sha’awarta take huramin ajikina, wutar kuma da har yau na kasa kasheta.”

Hmmm ya sake yin k’wafa tare da watsa mata hararan, daya sa hanjin cikinta kad’awa. 

Saurin kawar da kanta gefe tayi, tare da ajiye spoon din dake hannunta. 

Hakanne kuwa yasa Dady dake ankare da ita, d’agowa ya kalleta tare da cewa.

“Jannart kwana biyunnan me yake damunki ne wai, ina lure dake ko abincin kirki kin daina ci.” 

Jin tambayar da Dadyn yayi mata ne, kuma yasa tadan sunkuyar da idanunta kasa, tare da soma wasa da yatsun hannunta, cikin sanyin daya zamar mata sabo tace.

“Babu abunda yake damuna Dady, kawai dai Ina kewar gidan Abba Kabir ne.

Dan Allah Dady kabarni naje, nayi maka alk’awarin bazan jima ba zan dawo, Dan Allah…” 

Ta k’are maganar tana me karyar da wuyanta gefe.

Yayinda lokaci daya kuma Idanunta suka cicciko da hawaye. 

Shiru Daddyn nasu yayi baice komai ba ak’alla har na tsawon mintuna 5. 

Hakanne kuwa yasa zuciyar Jannart karyewa, saboda tasan abune mai sauki Daddyn ya hana ta zuwa, tunda dama bayan office daya yarje mata zuwa, bai sake yarje mata zuwa ko ina ba. 

Komai zatayi dole saida izininsa, hatta shopping Idan zatayi dole saida amincewarsa zata je. 

“Shikenan kije amma kada ki jima, kwata kwata 3hours na baki, Sannan kuma kafarki kafar su Sunday, ban amince ki taka k’afarki a wani waje ba Idan babu su.” 

Dadyn ya fad’a cikin kakkausar murya. 

“Nagode Daddy kuma Insha  Allah, zan kiyaye.”

Ta fad’i hakan cikin farinciki, saboda bata tab’a kawo aranta cewar zai barta ba. 

Batare kuma da ta jira komai ba ta mike tsaye, tare da nufan dakinta kaitsaye. 

Inda Junaid ya bita da Kallon takaici kasa-kasa, Domin Sam baiso Daddyn nasu ya bata izinin fita ba.

Yaso ace ta zauna agida yaudin, ta yanda zai sake kai Mata Hari, da kuma dana mata tarkon da ba zata tab’a iya tsallakewa ba. 

Acan b’angaren Rayyern kuwa, duk da yasan cewar ana biye dashi amma tukinsa yake cikin nutsuwa. 

Ahaka har ya kawo bakin babban katafaren company’n nasa.

Wanda asamansa aka rubuta.

*MAI-NASARA NIG LTD* 

An kuma yi rubutunne da manyan haruffa, Wanda komin Nisan inda mutum yake zai iya karantashi.

K’aran horn din motar daya danna ne kuma yasa masu gadin babban companyn su biyu suka had’a karfinsu wajen bud’e babban gate din mai matukar girma. 

Cikin k’warewa ya tura hancin motar tasa cikin companyn, Yayinda yake Kallon motar dake biye dashi abaya, Wanda shigansa Cikin company’n ya sata juyawa ta koma. 

Wani irin murmushi dake d’auke da ma’anoni daban daban yayi, bayan ya gama daidaita parking ne kuma, ya bud’e murfin motar ya fito.

Inda atsanake ya soma karewa babban company’n nasu kallo.

Company ne mai girman gaske, Wanda Idan mutum yace zai zagaye duka cikinsa, sai ya share sama da awa biyar yana yawo bai isa karshen saba, Domin kuwa hawa hawa har bakwai akayiwa babban ginin company’n, ko wani hawa kuwa girmansa ya zarce tunanin mutum. 

Haka kuma company ne da aka k’awatasa da ginin zamani, had’i da shuke shuken flowers masu kyau da burgewa. 

Tabbas anyiwa company’n tsari mai kyau, da burgewa, Domin duk da girmansa, saida aka k’awata ko ina da abubuwan more rayuwa na zamani. 

Ahankali yake taka k’afafunsa tare da nufar Cikin company’n yana mai son danne tunanin son sanin menene Tubalin dukiyar mahaifin nasu tabbas bakwai zarginsa yakeba amman yana son sanin tubalin dukiyar, sai dai yasa a ransa tabbas ya kusa tambayan Abbansu.

Ganinsa da ma’aikatan wajen suka yi ne kuma, yasa suka dinga rusunawa suna gaishe sa.

Inda shi kuma ya dinga amsa musu fuskarsa asake, saidai ba wai sakewa irin Wanda zata saka wasu daga cikinsu su rainashi ko suga zallar saukin kansa ba.

Sakewace irin Wanda take bayyana, basu matsayinsu da yayi amatsayinsu na y’an Adam. 

Domin ko Allah Da kansa yace ya karrama y’an Adam.

Duk inda ya wuce kuwa kansa yake jinjinawa, saboda yanda yaga ma’aikatan dake saka engines din na saka komai akan tsari mai inƙanci.

Kaitsaye babban katafaren office d’insa dake can sama ya nufa bayan ya gama duba wuraren da ake kafa na’urorin sarrafa shinka yayinda Engineer dake jagoranci aikin ke biye dashi a baya.

Yana nunnuna mishi komai kai tsaye Office nashi ya nufa.

Wanda already anriga da Anyi setling komai dake cikinsa, ank’awatasa da abubuwa masu kyau da burgewa Office din babbane mai yalwan kayan ƙawa. 

Koda ya shiga cikin office din suit din dake jikinsa ya zare, tare da zama akan hamshakiyar kujerar da musamman take mallakinsa. 

Wayarsa dake cikin al’jihunsa ya zaro. 

Tare da kunnata kaitsaye ya saka numbern wannan motar da acikin kwana biyun take bibiyarsu. 

Bayansa ya jingina da jikin kujeran, tare kuma da Dan lumshe Idanunsa.

“Road Safety.” 

Ya fad’a cikin sanin makamar inda daya nufa.

               *Jannart.*

Tsaye take agaban dressing mirror dinta, Wanda gabansa ke cike da tarin kayan kwalliya.

Yanayin yanda take sanye da towel ajikinta ne kuma,  yake bayyana cewar fitowarta daga wanka kenan. 

Atsanake take shafawa lallausan fatar jikinta mai, Yayinda zuciyarta ke cike da nishadi da kuma zumudin fitar da zatayi yau din.

Kasancewar tayi missing din gidan Abba Kabir din sosai.

Bayan ta gama shafa mai din ajikinta ne kuma, ta murza powder akan fuskarta, hade da gogawa red lips dinta shining lipgloss.

Sai kuma kajol da mascara da ta saka, Wanda suka kara fitar da kyaun fuskarta.

 Batare kuma da ta sake goga wani abun akan fuskarta ba, ta k’arasa gaban wardrobe dinta, 

Inda ta zaro wani had’add’en doguwar rigar material, wanda yasha dinkin fitted gown Wanda yana ɗaya daga cikin kayan da Barrister Kabir ke dinka mata, da Mom. 

Koda ta sanya rigar ajikinta, kuwa ba karamin kyau yayi mata ba.

D’an kunnen gold marar nauyi tasa akunnenta, tare da daukan wani siririn mayafi ta yafa akanta. 

Bayan ta zura half cover shoe akafarta ne kuma ta dauki wani baby hand bag Wanda yayi shige da kalan kayanta ta rik’e 

Agogon dake sak’ale ajikin Bangon dakin ta kalla, ganin da tayi kuma lokaci na tafiya ne, yasa agurguje ta dauki wayarta ta fice daga cikin dakin. 

Koda ta sauk’o afalon k’asa ta samu Momy.

Ganin yanda Jannart din tayi kyaune kuma yasa Momyn sakin murmushi, cikin nuna kulawa tace.

“A’a Jannart yau wacce rana ansaka kayan hausawa.” 

Murmushi Jannart din tayi, tare da karasowa inda Momyn ke zaune, ashagwab’e tace.

“Momy kayan baimin kyau ba ko?.”

Dariya Momyn tayi had’e da cewa.

“Ya miki kyau mana sosai Jannart, ai yama fi miki kyau akan kowanni kaya.” 

Murmushin daya bayyana fararen hakwaranta tayi, cikin yanayin dake bayyana jin dadinta tace.

“Nagode sosae Momy na, in sha Allah zan koyi saka irinsu.”

Cikin jin daɗi Mom tace.

“Kai Alhamdulillah da naji daɗi haka kuwa Boɗɗo na”.

Sassanyan murmushi tayi tare da lumshe idonta kana tace.

“bari naje saina dawo.”

Kai Momyn ta jinjina tare da cewa tagaishe da Abba Kabir din da kuma matarsa, da yaransa. 

Da “to.” Jannart din ta amsa, kana tasa kai ta fice daga cikin falon.

Tana fitowa compound din gidan kuwa ta samu Baba Ado driver da guard dinta na jiran ta. 

Domin tuntuni Daddy da kansa ya Gaya musu cewa Jannart din zata fita.

Yayinda kuma ya jaddada musu kulawa da ita.

Kamar Koda yaushe kuma tana shiga cikin mota, guard din nata ma suka shishshiga cikin tasu motar, tare da rufawa motar da Jannart din ke ciki baya. 

Jin da tayi sunhau titi ne kuma yasa ta d’an jingina bayanta da jikin kujeran motar, tare da lumshe idanunta.

Ahankali take sauk’e ajiyar zuciya, Yayinda ayau din takejin kanta tamkar sakakkiyar tsuntsuwa. 

Lallai watarana tana fata da burin samun yancin kanta, watarana tana fatan yin yawonta ita kad’ai batare da wani ko wata sun bibiyeta ba, haka kuma watarana tana fatan sauyawar rayuwarta gaba d’aya. 

Yayinda kuma har acikin zuciyarta watarana take fata dason sanin kullin dake ƙule  Cikin  rayuwarta kamar yadda Barrister Kabir yasha faɗa mata. 

Shin Meyasa Daddy’nta ya sanya mata tsaro maitsanani har haka duk da kuwa tana gamsuwa da irin soyayyar da yake nuna mata, ɗari bisa ɗari.

Meyasa Yah Junaid ke bibiyanta da munanan halaye? Da mugun manufa. 

Yaushe ne canji zaizo cikin rayuwarta? Yaushe ne zatayi farinciki kamar kowa? Yaushe zataji kanta amatsayin Mace mai y’anci? 

Lallai watarana zuciyarta kan gaya mata cewa Sauyin rayuwa zaizo.

Sai-dai yaushe zaizo? Da wani dalili zai taho a wanne yanayin duk bata sani ba.

Wani irin numfashi mai dumi ta fesar, adai-dai lokacin kuwa suka iso kofar madaidacin gidan Barrister Kabeer dake nan Nassarawa G.R.A 

Wanda kuma isowarsu gidan yayi dai-dai da shigowar sak’o cikin wayarta. 

Jin alaman shigowan Sakon da tayi ne kuma yasa ta d’ago wayartata ta duba.

Ganin sakon da aka rubuta mata dinne kuma yasa ta. 

Jin wani irin bugun zuciya maitsanani.

Idanunta ta rumtse da k’arfi, cikin kuma muryarta da ke bayyana tsoro had’i da firgici Ta……

Ta buɗe idonta ganin sunan Yah Junaid na bisa screen ɗin wayarta ne yasa, ta fidda numfashin a hankali tare da cewa.

“Innalillahi wa’inna’ilaihi rajiun Yah Junaid Kuma?”.

Cikin tsoro  ta buɗe text ɗin dai-dai lokacin kuma mai gadin gidan Barrister Kabir ɗin ya buɗe musu gate.

Suka kutsa ciki.

“Dan ubanki ina kiranki bazaki amsa ba.

 Maza ki ɗaga ko in ɓaɓɓllaki in mun haɗu”.

 Cikin ƙarfin hali ta zuge zip ɗin Baby hand bang din ta cilla wayar kana ta zuge ta rufe.

Da sauri Aunty Dijat tace.

“Lah Hafiz ga Aunty Jannart tazo”.

Ta ƙare mgnar tana nufar inda motarsu Jannart tayi parking.

Hafiz kuwa da sauri ya juyo jin ance Jannart, cikin ware ido ya nufi motarsu a guje yana cewa.

“Oyoyo my Aunty, Hafiza ga Aunty Jannart tazo”.

Murmushi mai cike da jin daɗi Jannart tayi kana ta ƙarisa fitowa tare da ware musu hannayenta.

A guje suka abka jikinta su duka biyu.

Cikin jin daɗi da son yaran ta ɗaga Hafiza da bazata wuce 7 year’s ba.

Ruggume ta sukayi duka suna farin cikin ganinta.

Cikin kula, so, ƙauna, da tausayawa Aunty Dijat ta iso garesu fuska ɗauke da murmushi tace.

“Oyoyo Aunty Jannart, yau munji daɗin mu kin tunomo”.

Cike da happy tace.

“My Aunty kullum kuna raina”.

Hannu tasa ta amshi Hafiza tare da cewa.

“Zo nan kada ki karya min ƴata maza mu shiga daga ciki.”

Aifa tana faɗin haka Hafiz ya ɗiba a guje yayi cikin gida.

Ita kuwa Jannart juyowa tayi ta kalli Baba Ado dake gaisawa da Aunty Dijat.

Ita kuwa Aunty Dijat kamo hannun Jannart tayi suka juya suka nufi cikin gida.

Cikin murmushi ta juyo ta kalli Baba Ado dake cewa.

“Jannart muje ne ko mu jiraki”.

“A’a Baba Ado ku jirani Awa uku Daddy ya bani”.

Kai ya jinjina mata, kana ya koma wurin mai gadin gidan.

Su Sunday Kuma suka tsaya tamkar gumakan taɓo.

Daga bakin falon Hafiz keta rabkawa Barrister Kabir kira.

“Abba! Abba!! Kazo ga Aunty Jannart tazo”.

Da sauri Ya miƙe tsaye, tare da katse wayan da yakeyi wanda kuma dama akan wani case ne da zasu shiga gobe,

Cike da farin ciki ya fara tako steps ɗin sauƙowa men falon su.

Ita kuwa Jannart Murmushin jin daɗi takeyi wanda ke bayyana tsantsan jin daɗin da take ciki.

Ita kuwa Aunty Dijat kitchen ta nufa.

 fruits masu sanyi ta ciko mata plate dasu.

Kana da Bootle water.

Tana isowa Abba na ƙarasowa.

Kujerar dake gefenta ya zauna tare da sakin murmushi yace.

“Hafeeza zaki karya min cinyar ƴa ko”.

Murmushi tayi tare da ɗan zamowa kaɗan tace.

“Abba ina yini”.

“Lfy lau Alhamdulillah Jannart ya jikinki!?”.

Barrister Kabir ya faɗa cikin kulawa.

Yana mai kallon matarsa dake nuna tsantsan so ga Jannart murmushi yayi tare da cewa.

“A’a Khadijah kin mance Jannart ne da Asman kika kawo abu mai sanyi”.

Ita kuwa Jannart a hankali tace.

“Abba nayi sauƙifa zan iya cin komai”.

Kai ya jujjuya tare da cewa.

“A a ban yardaba”.

Da sauri Hafiz Wanda zai iya kai shekaru goma sha shida yace.

“Abba yau kawai a barta taci”.

Ina tuni Aunty Dijat ta juya kitchen.

Pepper chicken da yanzu ta gama aikinshi da zafinshi ta ɗebo, mata tare da haɗa mata tea mai zafi.

“Yauwa ci wannan bari su kuma na sa miki innabi da tufa ɗin a ruwa zasuyi ɗumi zuwa anjima sai kici”.

Murmushi tayi tare da cewa.

“Ngd matuƙa my Aunty”.

Haka nan sukayi ta nan-nan da ita tamkar suyi mata numfashi.

A can MAI-NASARA NIG LMT kuwa.

Dr Rayyern Mai-nasara ne zaune cikin nitsuwa yake duba bayananan da hukumar Road Safety, Suka turo mishi akan number motar daya tura musu.

Dan neman ƙarin bayanin.

Sanin waye shine yasa nan take suka turo mishi sunan mamalakin motar.

“Alhaji Idi Saleh Dakata.”

Shine abin daya mai-mai-ta kan lips ɗin shi.

Numfashin gajiya ya ɗan fesar kana a hankali ya kuma ci gaba da ganin jerin jadawalin numbers ɗin motocin da suke mallakinsa kab.

Ido ya lumshe tare da meda bayanshi ya jingina jikin kujerar a hankali.

Ya fara jujjuya kujerar, cikin sanyi ya fesar da numfashi mai sanyi tare da cewa.

“Uhummm!”.

Kana ya gyara zamanshi tare da ajiye wayar da tunanin waɗannan tsoffin gefe.

System ɗin shi ya jawo ya ci gaba da aikin daya shafi Campany’shi na neman ma’aikata…

Yah Junaid kuwa yau ji yake tamkar ya kashe Jannart in ya kamata sabida, video’nta da Ushe ya turo mishi lokacin da Rayyern ke samata al’kyabbar.

“Wato dai shegiyar nan tasan maza tasan garɗinsu, ni takeyiwa tereren bankaɗa in na taɓata.

Yau kuwa tabbas sai na caccakaki shegiya ƴar iska mai idon cin maza.

Yoh dama ya za’ayi wannan zuƙeƙeyiyar. Tarwadan kyau ta zauna babu masu lasarta”.

Kwafa yayi tare da ƙara yi mata text  cewa yana kiranta fa.

Dan shi masifar feelings yasa ya mance da cewa bata nan ma.

Gashi ya leƙa falo yafi sau uku Mom na zaune…

A gidan Barrister Kabir kuwa.

Hira sosai Aunty Dijat da Jannart Da Abba dasu Hafiz  sukeyi sunci sun Sha, sun kaiwa su Baba Ado ma, dan Aunty Dijat matar kwaraice.

Kiran sallan azahar da akayi ne, yasa Abba miƙewa shida Hafiz suka shiga sukayi al’wala bayan sun fito suka nufi masallaci.

Abba na cewa.

“Ku tashi kuyi salla, ko”.

To sukace.

Bayan sun fita Aunty Dijat ta miƙe tare da cewa.

“Muje muyi salla ko Jannart”.

Kanta a sunkuye tana yiwa  Hafiza kitson kalba ƴan ƙanana a tarin gashin ta tace.

“Nayi”.

Tayi mgnar a hankali kana a gajarce.

Murmushi Aunty Dijat tayi tare da cewa.

“Oho kinyi da mutanen Makka kenan”.

Cike da kunya tasa tafin hannunta ta rufe fuskarta cikin tsananin kunyar an gane tana fashin salla.

Ita kuwa Aunty Dijat murmushi tayi tare da wucewa Bedroom ɗin ta…

Bayan tayi sallan ne kuma ta fito ta sameta suna kitson.

Kitchin ta wuce Fruits ɗin ta kawo mata.

Kana ta zauna gefenta tare da miƙa mata fork.

Dai-dai lokacin Abba da Hafiz suka shigo.

Cikin kula Abba ya kalleta kana yace.

“Yauwa Jannart ku taso muje mall ku ɗan zazzaɓi abin da kukeso ko”.

Cikin jin daɗi tace.

“Abba muna kitso komai ma aka kawo mana muna so”.

Ya gane manufarta bazatace bazata jeba, amman ta bashi mgnar a dunƙule sanin tanada hujjar faɗin haka yasa yace.

“Daddy zaiyi faɗa ko?”.

Kai ta gyaɗa tare da gyara zaman kan Hafiza bisa cinyarta kana tace.

“Kuma nan ɗin ma awa uku fa ya bani. Gashi yanzu naci biyu saura ɗaya”.

Hannu ya miƙa wa Hafiz tare da cewa.

“Toh ba matsala kuyi kitsonku bari muje yanzu mu dawo, kada Daddy ya haɗa hardani ya tsire”.

Kai ta jinjina, har sunje bakin ƙofar fita kuma ya juyo cikin kulawa yace.

“Toh me da me kikeso in seyo miki?”.

Kai ta ɗan ɗago ta kalleshi tare da yin murmushi tace.

“Abba kayan hausawa”.

Cikin gamsuwa yace.

“Masha Allah Ina ga dai ɗiyata ta canza salon shiga ko”.

Cike da kunya tace.

“Eh Abba naga waɗanan can ɗin basu da rufin asiri kamar namu.

Yauwa Abba da hijabai”.

Ita dai Aunty Dijat murmushi kawai takeyi.

Shi kuwa toh yace kana ya fita.

Nan sukaci gaba da hira su kuma.

Da sauri Jannart ta ɗago kanta ta kalli Aunty Dijat jin abinda take cewa cikin hirar tasu.

“Uhm Jannart yanzu kam komai ya dai-dai-ta ai ko?”.

“Me ɗin fa My Aunty?”. Ta tambaya cikin rashin fahimta.

Gyara zama Dijat tayi ta fuskance ta da kyau kana a nitse tace.

“Kamar ci gaban rayuwarki mana, yanzu kin gama karatu, har kin fara aiki yanzu wata shida kenanfa da fara aikinki.

Toh yanzu kuma sauran miki me!?”.

Ido ta ɗan jujjuya kana a hankali tace.

“Ohon musu”.

Tayi mgnar a hankali.

Cike da mamaki Dijat tace.

“Su waye ɗin?”.

A hankali tace.

“Daddy da Yah Junaid mana”.

Ganin yadda Aunty Dijat ta zuba mata idone, yasa ta ɗan muskuta kana a hankali taci gaba da cewa.

 “Ban sani ba kam yanzu kam, sai kuma yadda Daddy yace ai!”.

Numfashin mai nauyi Dijat ta fesar kana a hankali tace.

“Uhmm Jannart kenan shin ke baki da tsarin kankine a kan komai na rayuwarki. Dole sai abinda Daddy ya faɗa?”.

Da sauri ta gyaɗa mata kai alamun Yesss haka ne.

Apple ɗin data ɗauka ta ɗan ɓantara kana a nitse tace.

“Har auren ma, in baice kiyiba bazakiyi ba”.

Tada Hafiza tayi ta zaunar da ita gefe dan ta ida Mata kitson.

Cikin sanyi tace.

“Eh mana”.

Ta bata amsa da ɗan guntun murmushi, kana ta ronƙofar da kanta tace.

“Toh My Aunty Aure kuma! Ni kuma zanyi aure ne?”.

Da sauri Dijat tace.

“Mun shiga uku bazakiyi aure ba?”.

Nannauyan numfashin ta sauƙe kana tace.

“Yoh Ni na sani ne ai sai yadda Daddy da Yah Junaid sukace, Kuma ma ni ban taɓa tuno aureba, tunda basuma taɓa yimin mgnar aureba toh ni wake sona ma”.

Cikin tsananin tausayawa yadda ake juya rayuwar ƴarinyar ya zama bata tsarawa kanta komai ma sai abinda su Junaidu suka tsara mata, a takaice ma suke juya motsin rayuwarta.

A hankali tace.

“Toh wai babu mai zuwa gunki ne? Wanda kuke soyayya ko mgnar aure”.

Ta kuma jefowa Jannart tambaya.

Inabi ta tsinka tasa a bakinta kana a hankali tace.

“Ni kuma wa zaizo wurina, wayema ya sanni.

Nifa da zan samu Yah Junaid yayi aure ya bar gidanmu da shike nan wlh bani da matsalar komai a rayuwata zanci gaba da zama a gidanmu a haka har gaban abadan.

Ko kuma ace na dawo nan da bani da sauran damuwa a duniya wlh Ni banma san menene soba bare kuma soyayya  bare batun aure.”

“Tirkashi”.

Shine abinda Dijat ta faɗa kana ta ture Hafiza daga jikin Jannart ɗin sannan a hankali tace.

“Uhmm koda yake ba mmki.

Toh dama ya za’ayi kiyi soyayyan waya isa ya isoki da kalmar so, yadda aka haɗaki da waɗannan bakaƙe kafuran ƙattin samudawan nan da ko yaushe suna biye dake tamkar inuwa.

Ina ai dama yana cikin manufar tosheki da akayi tako ina da gayya sabida kada wani ya kusanceki.”

Ta ƙare mgnar wasu siraran hawaye masu zafi na silalo mata.

Wanda haka yasa tuni itama Jannart idanunta suka cika da ƙwalla.

Cikin zubda hawaye Dijat taci gaba da cewa.

“A yadda Allah yayi miki cikekkiyar halitta mai nagarta wace ko mace ƴar uwarki bata gajiya da ganinki.

Ta yaya za’ace namiji kuma zai gaza sauƙe idanunshi a kanki da manufar so da ƙauna.

Toh ko nan wurin Abbankin adadin maza nawane suka zo da kansu dama waɗanda suka turo iyayensu kam sonki da neman aurenki wanda suke bada tabbacin tsoro ke hanasu fuskantar ki”.

Hannu tasa ta share hawayenta kana a hankali tace.

“My Aunty dole ne sai nayi aure? Ni kawai farin cikin rayuwa nake son samu”.

Cikin sanyi tace.

“Jannart duk wani farin cikin ƴa mace yana cikane in tana gidan mijinta kuma tayi dace da miji na gari.

Haka kuma duk farin cikin ƴa mace baya cika in batayi dace da miji na gari ba”.

A hankali tace.

“My Aunty Kenan dai dolen-dole  saida aure farin cikin ƴa mace yake cika!?”.

Cikin sauƙe numfashi Dijat ta riƙo hannunta kana ta fara zaiyyano mata ni’imomin dake cikin aure da matsayin zaman aure dama manufar aure a musulci…”

Ramadan ne zaune a ƙasa kusa da kujerar da Mamy ke zaune.

Wayarsa ce saƙale a kunne a karo na bakwai ya kira Riyyam-nsra sai ace mishi yana bisa waya.

“Yanzuma bata shiga bako?”.

Mamy ta tambaya cikin kula.

“Uhum inafa ina ga dai ko dasu Zayton yake waya da Mammynsu.

Tun ɗazu waya taƙi ƙare wa”.

Ramadan ya faɗa yana zura wayarsa a aljihu.

Gyara zama Mamy tayi tare da cewa.

“Toh Allah dai yasa lfy, kagafa yau ko breakfast baizo yaci ba, gashi yanzu har azahar ta gota bai kuma zoba”.

Kai ya ɗan jingina da kujera kana yace.

“Bari in nayi wonka, kafin in wuce asibiti sai in biya in kai mushi abinci.”

Da sauri Mamy tace.

“Yauwa yafi kam”.

Da sauri suka kalli Abba da shigowarsa kenan cikin haɗe fuska yace.

“Har ke ɗin ma, shisshigewa lamarin da bai shafeki ba kikeyi, to ya za’ayi in iya control ɗin yaranki da yimin yayuɓe-yayuɓe suna kawo min cikin gida. 

Toh me ruwanku dan bai zoba!?”.

Shiru sukayi baki ɗayansu

Saida ya tsagaita Ramadan ya ɗan longoɓar da kai tare da cewa.

“Afwan Yah Abba”.

Kai ya gyaɗa kana ya wuce falonshi na ciki.

A bakin gate kuwa Usman PA ne ya shigo da motarsa bayan Hadi ya buɗe masa.

Da sauri ya nufi wurin Baba Mauɗo bayan ya fito.

“Barka da yamma Baba Mauɗo”.

Cikin kulawa Baba Mauɗo yace.

“A’a Barka dai Usmanu! Kwana biyu shiru tunda kuka dawo bana ganinka ka bar Rayyanu shi ɗaya lfy dai ko?”.

Cikin son dottijon yace.

“Lafiya lau Alhamdulillah Baba Mauɗo, wlh da muka dawo ne Mama, ba lfy ashe ba ciwone matsalar ba, wai tayi kewan ƙannenta tofa dole ranarda muka dawo washe gari ta sani muka tafi Gombe bamu dawo ba sai jiya da dare da yake bamu taso da wuriba”.

Cike da kulawa yace.

“Masha Allah. Allah ya bada ladan ziyara, sai kuyi ta haƙuri damu, iyaye in an fara girma tamkar yara ake zama.

Allah yayi muku al’barka”.

Amin Amin yace.

Kana ya nufi cikin gida.

Da sallama a baki shi ya tura ƙofar falon.

Da sauri Ramadan yace.

“Wa alaikassalam, Yah Usman mutanen Gombe Kun dawo kenan”.

Murmushi yayi tare da cewa.

“Oyoyo Ramadan Alhamdulillah”.

Sai kuma ya juya.

Da sauri Usman ya nufi inda Abba ke tsaye rusunawa yayi tare da gaidashi.

Cikin kula Abba yace.

“Usman kwana biyu shiru”.

Cikin girmamawa yace.

“Wlh kuwa Abba sai jiya muka dawo”.

Ya faɗi haka tare da juyawa ya kalli Ramadan dake miƙo mishi hannu.

Musabiha sukayi kana ya kalli Mamy cikin mutuntaka yace.

“Barka da yamma Mamy”.

Barka dai tace tana mai nunawa Ramadan Fridge alamun ya kawo masa abin motsa baki.

Da sauri kuwa Ramadan ya nufi Dinning area juice and bootle water ya kawo mishi.

Kana yace.

“Yah Usman bari in haura sama in ɗan watsa ruwa”.

Toh yace.

Kana ya haura.

Shi kuwa Abba ne ya dawo tsakiyar falon.

Mamy kuwa abinci ta kawo mishi.

Kana ta nufi Bedroom ɗin ta.

Yanaci suna hira da Abba.

A can tahir hotel kuwa.

Riyyam-nsra ne zaune bisa kujerar dake gefe.

Video call yakeyi da Mammynsu cikin sauƙe numfashi yace.

“Alhamdulillah Mammy duk abinda muke zato hakane, wlh kuma duk abinda ya tsananta tsawon shekaru yana gab da sauƙaƙa. 

Sai dai ta ina? Ta yaya? Da yaushe? Zamu fito da manufarmu ta yaya za’a fahimcemu?”.

Ido Mammynsu ta limshe sai ga wasu irin zafafan hawaye kana a hankali tace.

“Riyyam-nsra nima kaina bani da sanin tudun dafawa

Kuma zuciyata ta ƙara kwaɗaituwa da tsatsonta.

Ta ina? Ta yaya? Yaushe? zamu samu nasara”.

Cikin ƙarfin hali yace.

“Mammy keda kike da Riyyam-nsra, kada ki damu ki bada yaƙinin ki a kaina in sha Allah zan kusanto miki da nesa kusa dake cikin aminci”.

Yadda yayi mgnar with full confidence ne yasata sakin sassayan murmushi.

Riyyam-nsra akwai ƙarfin hali da yarda da kai, idon ta ita nema da bazaima je Nigeria’n ba amman bisa ƙarfin halinshi yaje.

Kai ta jinjina mishi tare da yin murmushi, ganin ya sata farin cikine yasa shi cewa.

“Ina Deeda tsohuwa da Zayton?”.

Cikin sanyi tace.

“Sun tafi asibiti”.

Ya buɗe baki da nufin yin mgna kenan kuma wani kiran ya shigo ɗaya wayar tashi.

Da sauri yace.

“Yauwa Mammy sai anjima zamuyi mgn”.

Kan ta fargama ya katse kiran.

Kana ya amsa wannan kiran wanda shima video call ne.

Wata iriyar fitinenneyar miƙa yayi tare da zaro harshensa ya ɗan lashi lips ɗin shi.

Sabida gamo da katar da yayi da wata kekkyawar baby mai cikar haiba kalar Ethiopia’n Girl’s

Tana mishi Ethiopia’n dance.

Wanda take jujjuya mishi ƙirjinta da karkaɗa mishi su da karya kafaɗu irin dai rawar su nan ta sai kaci ka ƙoshi kan ka iya yinsa.

Ido ta jujjuya mishi tare da tsagaita wa da rawar kana cikin yin ƙasa da murya tace.

“I miss you  very very very so much sweetheart”.

A hankali ya miƙe ya koma bisa gado.

Idanunshi da suke juye sabida ganin ɗaya daga cikin abokan masha’arsa da suka haɗu sanadin TIKTOK cikin sanyi da kasalar wani irin masifeffen feelings da ya ziraro mishi kamar zai tsinke mishi jijiyoyin jiki yace.

“Nace muzo Nigeria kika ƙi, sannan kuma kina son tarwatsa min kwanya da begenki”.

Cikin iya shege ta zame wuyan rigar ta ta ɗanyi ƙasa dashi.

Kana tasa hannunta cikin rigar ta zaro mishi… Tare da cewa.

“Lollypop”….! Ɗaga nan sukaci gaba da lalatacciyar hirarsu, haka yasa Ramadan nata kira bai amsawa.

A can gidan Alhaji Idi Saleh Dakata kuwa.

Cikin hatsala Junaidu ya leƙo falon yana mai rabkawa Jannart kira kamar zai yage bakinsa.

“Jannart! Jannart!! Jannart!!!”.

Ya ida kiran da ƙarfi wanda yasa.

Mom dake Kitchen ta leƙo cikin taɓe fuska tace.

“Menene kake ta ihun kiran wacce bata gidan ma, sai ka tafi gidan Abbanku ai”.

Kwaffa yayi tare da watsawa Mom ɗin harara kana ya nufi Part ɗin Abbansu dan sai yanzuma ya tuno cewa bata gidanma.

Yana isa bakin ƙofar falon.

Dr Lukman da Alhaji Abdu Tababa suna isowa suma da alamun yanzu suka iso.

So kusan a tare suka shiga.

A falon suka samu Daddy wanda dawowarshi kenan shima nan suka zauna.

A gidansu Rayyern Mai-nasara kuwa, Ramadan ne ya fito riƙe da foodflakcs mai kyau. Usman na bayanshi.

“Eh ba asibiti ba yake Campany ya tafi tun safe bai dawo bama”.

Ramadan ya bawa Usman amsa wanda ya biyoshi da nufin zasu tafi asibiti.

Numfashi Usman ya sauƙe tare da cewa.

“Toh ni kam bari kawai in wuce can inda yake ɗin”.

Toh yace kana shi ya nufi hotel ɗin da Riyyam-nsra yake.

Shi kuma ya wuce campany.

Yana isa da mai a dai-dai-ta sahun ya tsaida shi bakin gate ya sallameshi.

Kana ya shiga cikin kamfanin. 

Mai napep ya juya.

Kasan cewar duk ma’aikatan wurin sun san PA duk wanda yasan Dr Rayyern Mai-nasara zai iya saninshi da PA hakan yasa kai tsaye ya wuce Office ɗin sa.

Cikin gajiya ya ɗago kansa ya kalli ƙofar Office ɗin da ake bugawa cikin sauƙe numfashi gajiya yace.

“Yesss coming”.

Cikin nitsuwa PA ya turo ƙofar.

Numfashi ya fesar tare da meda bayanshi ya jingina da kujera tare da kallon Usman murya can ƙasa yace.

“Sai yau?”.

Murmushi yayi tare da cewa.

“Wlh kuwa sai yau fa”.

Ya ƙare mgnar yana ƙoƙarin zama.

Sai kuma ya tsaya ganin uban gidan nasa ya miƙe tsaye.

Hannunshi yasa ya tattare system din ogan nashi da wayarshi kana yabi bayanshi dan tuni ya tafi.

Da sauri yabi bayanshi.

Bisa. libta ya hangoshi tanayin ƙasa dashi, da sassarfa ya mara mishi baya.

A haka har suka sauƙo hawa na biyu.

Suna sauƙa yayi maza yabi bayanshi ganin ya nufi hannun damanshi.

Tafiya mai ɗan tsawo sukayi kana suka isa wani wuri mai ɗauke da manya-manyan store’s masu masifar girma da faɗin gaske.

Wanda sun kai goma sha biyu.

Gaba ɗaya a rufe suke tsayawa ya ɗanyi kana ya juyo ya kalli PA tare da cewa.

“Muje ƙasa”.

To yace kana yabi bayanshi.

Suna sauƙa ƙasan kuma wasu stores ɗin suka samu kamar na sama.

Sai dai waɗannan su anata loda buhunan shinkafa shanshera ne buhu-buhu”.

Kai ya gyaɗa cikin gamsuwa kana suka sauƙo ƙasa gaba ɗaya.

Inda suka nufi can gefen baya wani ƙaton hall ɗin cike da enginer’s anata kafasu da haɗasu babu ƙaƙƙautawa.

Cikin nitsuwa yace.

“Lokacin salla yayi abar aiki aje ayi sallan la’asar”.

To sukace cike da jin daɗin kana suka bar aiyukansu.

Kana suka firfito.

Shi kuwa yayi gaba PA ya mara masa baya.

Suna isa parking lot Usman ya buɗe mishi mota gefen baya.

Kai ya jujjuya mishi kana ya shiga gaba mazaunin driver’n kana ya nunawa Usman gefenshi.

Yana son yayi tuk’i da kansa ne dan sanin akwai masu bibiyarsa.

Ana buɗe musu gate ya fita a nitse.

Karatun ƙurani ya saki sautin muryar Sheykh Jabeer Habibullah Nuruddeen Joɗa, (GARKUWA) Sassanyan sautinsa mai sauƙar da nitsuwa ya saki.

Kana ya saita hancin motar bisa titi ya fara takata a guje.

Dan so yake su samu jam’i sallan la’asar a Masallacin ƙofar gidansu.

Ana tada iƙama suna isowa.

Da sauri sukayi al’wala kana sukabi jam’i Allah yasa ba’a kere musuba.

Ana idar da sallan suka shiga cikin gida.

Tare da Abba da Baba Mauɗo, Hadi, Ari da Ramadan da Riyyam-nsra wanda suka juyo tare.

A bakin gate Usman ya zauna wurinsu  Baba Mauɗo.

Su Ramadan kuwa a babban falon suka zauna.

Shi kuwa Dr Rayyern Mai-nasara bayan Abbansu yabi har falonsu na ciki.

Gefenshi ya zauna tare da sauƙe numfashin gajiya kana ya kalli Abba dake cewa.

“Ya ka samu aiyu kan?”.

Cikin nitsuwa ya tonƙoshe sawunsa kana a hankali yace.

“Alhamdulillahi komai na tafiya dai-dai da izinin ubangiji. 

Shinkafar nan ma da muka saya ta manoman Adamawa can wajajen Gurin ta iso, kuma shinkaface mai kyau da in ganci dan Jamila ce sai kuma mahanga kaɗan ita tafi kyau a barta a ɗaya.”

Uhumm yanzufa wasan zai fara daga PAGE din gobe.

Back to top button