Uncategorized

Tubali Book 1 Chapter 4 complete Hausa novel

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

Ahmad na kashe wayartasa kuwa shima ya kashe data d’insa, saboda zuwa yanzu bacci sosai yakeji.

Duk da cewar yana iya kaiwa har 2:00 am a online, amma dai yau kam yayi tafiya ya gaji sosai, dole yana buk’atar bacci. 

Cikin abunda bai wuce 10mn ba kuwa bacci mai nauyi da gajiya ya d’aukesa. 

              Washegari.

Ajere suka dawo daga sallan asuba, Abba da Baba Mauɗo suna gaba kana su kuma suna biye dasu da Ari da Hadi.

Su a farfajiyar gidan suka tsaya wurin aiyu kansu.

Inda su kuma kaitsaye suka nufi babban falon gidan, koda suka k’arasa azaune suka samu Mamy hannunta rike da carbi tana ja, ganinsu da tayi dinne kuma yasa ta sakin murmushi, Yayinda Rayyern da kuma Ramadan suka gaisheta cikin girmamawa. 

Itakuwa Mamyn fuska asake ta amsa musu, tare da tashi ta had’a musu coffee mai zafi. 

Domin hakan  d’abiarsu ce dukansu, idan suka dawo daga masjid sai sunsha coffee. 

Bayan sun gama shan coffee dinne kuma kowannensu ya haura side d’insa.

Rayyern dai yana shiga bedroom d’insa, kwanciya yayi tare dajan blanket ya rufe jikinsa, bayan ya rufe idanunsa ne kuma, yasoma gabatar da azkhar d’insa na safiya, domin neman kariya daga wajen Allah Mahalicci mai kowa mai komai. 

Yana cikin yin azkhar dinnasa ne kuma bacci ya daukesa. 

7:00 am dai-dai kuma ya farka sakamakon alarm din gefen bed d’insa dake ta kara. 

Kaitsaye toilet ya wuce tare da Sakarwa kansa ruwa,  bayan ya kammala wankane kuma ya fito, inda ya kimtsa kansa cikin wasu had’add’u kuma tsadaddun riga da wando na leather suit navy blue colour, Yayinda long sleeve d’insa ta kasance sky blue, irin mai taushin nan. 

Tabbas bak’aramin kyau kayan yayi masa ba, Musamman da ya bayyana asalin kwarjini, haiba da kuma cikar zatinsa.

Uwa uba kuma ga wani daddad’an kamshin turaren dake tashi ajikinsa.

Wasu had’add’un navy blue toms kirar companyn Italy, daya saka ak’afafunsa ne kuma suka sake kawata kyawun Shigar tasa, Yayinda tsadadden agogon dake daure akan tsintsiyar hannunsa keta shining. 

Ahankali ya gama d’aura navy blue necktie awuyansa, tare da juyawa ya d’an kalli kansa amadubi, Tabbas shi kansa ya gamsu  sosai da sosai, da shigar,

Dan shigar tasa ta d’aukar hankali ne, musamman ma k’awataccen sajen dake kwance akan fuskarsa, wanda take bak’a sidik mai yawan sheki. 

Dan kawar da kansa daga Kallon madubi’n yayi, bayan yasa hannu ya d’auki briefcase d’insa, wanda ya saka duk wani abu mai mahimmanci nasa aciki. 

Kaitsaye cikin takunsa dake bayyana nitsuwarsa ya nufi hanyar fita daga cikin dakin, direct kuma falon k’asa ya nufo.

Koda ya fito falon acan kitchine ya hango Mamy tsaye tana aiki.

Yayinda Ramadan kuwa ke gefenta yana taya ta y’an wasu aikace aikace-aikacen masu sauk’i da maza zasu iya. 

Ido ya lumshe  tare da d’an takowa zai shiga kitchine din, saidai kuma maganan da yaji Ramadan na fad’a ne yasashi d’an daka tawa. 

Acikin kitchine din kuwa Ramadan ne tsaye yana ɓarewa Mamy Maggi yana mai cewa.

“Please Mamy tunda dai shi Hamma Rayyern yace muku, a fara yi min aure shi ko mgnar kansa ba yi yakeyi ba.

To nikam dan Allah da Manzonsa abani dama nayi dan Allah, Mamy kiyiwa Abba magana, nidai gaskiya aure nakeson yi.”

Ya kare maganar fuskarsa d’auke da zallar shagwab’a. 

Mamy dake tsaye kuwa murmushi tayi tare da d’an girgiza kanta, kana tace.

“Nidai ba ruwana kayiwa Hamman naka magana, ya gayawa Abbanku cewar ya barka kayi aure, domin Abbanku zaifi saurin aminta da maganarsa.”

Sake shagwab’e fuska Ramadan yayi, tare da karyar da wuyansa gefe, kamar zaice wani abu kuma sai yayi shiru.

Rayyern dake bayansu kuwa ɗan guntun murmushi yayi, tare da d’an d’aga sautin muryarshi, Cikin kulawa yace.

“Don’t worrie Ramadan, Isha Allah zan gayawa Abba cewar kanason aure ya barka kayi aurenka, ku haifa mana babies dozin-dozin ko zamu samu gidan nan zai daina zama shiru.” 

Juyowa dukansu sukayi suna kallonshi, Mamy kam mamakine ya isheta, sakamakon jin abunda Rayyern din ya fada, wato shi bazaiyi auren ba, saidai yasa ayiwa wani, har yau itakam tana mamakin hali irin na Rayyern, Sam kwata kwata mata basa gabansa, babu wata Mace daya tab’a gani arayuwarsa yace yana so, shidai hakanan yake tana fata Allah ya nuna mata sanjawarsa. 

Shikuwa Rayyern juyawa yayi kaitsaye ya nufi bedroom d’in Abba.

Koda ya isa kofar bedroom din yana knocking, Abba ya bashi daman shigowa, bayan kuma sun sake gaisawa ne, ya bud’e briefcase din dake rike ahannunsa, wasu files ya ciro daga cikin jakar, wanda yayi aiki a kansu tun jiya da yake cikin jirgi, mik’awa Abban files d’in yayi tare da cewa.

“Abba ga way’annan files d’in already nasaka hannu a kansu, sannan daga ciki akwai takardun engines din da muka saya a US.”

Kai Abba ya jinjina tare da karb’an takardun, cikin kulawa yace.

“Masha Allah, yaushe ne zakaje meeting d’in da zakuyi, naji ance harda govenor da ma wasu manya manyan Doctor’s, sannan tare da Ramadan zakaje ne?”

Sake gyara zamansa yayi kana aladabce yace.

“A’a Abba bada Ramadan zamu jeba, saboda yau suna da aikin da zasuyi anan cikin hospital shida Sulaiman, maganan shiga meeting din kuma 11:00 am daidai ne.”

Again kai Abba yasake jinjinawa cike da gamsuwa yace.

“Masha Allah To Allah Yabada sa’a.” 

Da Ameen ya amsa sannan ya mik’e tsaye, atare kuma suka fito  shida Abban nasa. 

Inda suka iske Mamy da Ramadan sun gama jere komai akan dining table.

Batare da wani b’ata lokaci ba kuma, suka zauna atare su duka suka soma cin abincin, kasancewar chips and sauce na egg da kuma fruit salad and ketchup Mamyn ta had’a musu, amma shidai yafi k’arfi wajen shan tea. 

Acan b’angaren Riyyam-Nsra kuwa yau tun tashinsa yakejin zuciyarsa wasai, ga kuma wani irin nishad’i da yakejin kansa aciki, sosai yakejin shaukin Nigeria na shiga jikinsa.  

Bayan yayi wanka ne kuma ya shirya kansa cikin, riga da wando masu kyau da tsada.

Waya da kuma earpiece d’insa ya dauka, kana anutse ya fice daga cikin dakin nasa, direct wajen hotel din ya fito, saboda hakanan yaji yanason zaga unguwar da yake, duk da kuma akwai restaurant acikin hotel din, amma yaji sha’awar zagawa ko zai samu wani difference restaurant dancin abinci. 

Haka dai yadinga dan tattaki acikin unguwar, har dai ya samu wani had’add’en restaurant ya tsaya anan yaci abinci, bayan ya gama ne kuma ya sake dawowa hotel d’in daya sauk’a, To anan nefa ya samu Nasir Ahmad yazo, cikin farinciki shida Nasir suka rungume juna, tare da zama suka fara hirarsu na yaushe gamo..

Gaba d’ayansu zaune suke akan dining table suna breakfast.

Yayinda kowannesu ke gudanar da harkar dake gabansa, amma Banda Junaid daya kafawa Jannart ido, wacce take zaune akan kujerar dake facing nasa.

Tayi kyau sosai cikin shigar maroon abayan dake jikinta, wanda ta sake bayyana haske da kyaun fatarta, kasancewar bata saka bra bane kuma, yasa ta jawo mayafin abayan nata ya sauk’a harkan kirjinta. 

Saidai kuma gaba daya kwata-kwata bata da wata nutsuwa awajen, saboda irin Kallon da taga Ya Junaid nayi mata, kwata-kwata ya hanata sakat, ta kasa koda cin abincin. 

Daddy ne ya kalleta kana cikin tsananin kulawa da so yace.

“Jannart kici abinci mana, kodai jikin naki ne?.”

Kanta ta d’an girgiza ahankali, cikin kuma muryarta da yayi sanyi sosai tace.

“A’a naji sauki Daddy.”

Kai Daddyn ya jinjina.

Shikuwa Junaid tsuka yayi azahiri tare da cewa.

“Bawani rashin lafiya dake damunta, iskanci ne da kuma zallan rashin gaskiya kawai, munafuka mai fuska da zuciya biyu” 

Ya k’are maganar yana mai saka k’afarsa ta k’asan dining table d’in ya take ta. 

Idanunta ta rumtse da k’arfi saboda zafin da taji na abunda ya mata.

Duk da cewar Daddyn nasu yaga hakan kuwa, amma baice kala ba saima ci gaba da cin abincinsa da yayi. 

Abdul ma da tausayin yar uwartasa ya cika masa zuciya kasa cewa komai yayi, domin yasani koda wasa yayi magana, yanzu sai Ya Junaid din yayi kasa-kasa dashi. 

Momy kuwa zuru tayi kawai tana kallonsu, domin har acikin zuciyarta ta kasa gane wani irin ahali ne take zaune acikinsu tsawon shekara da shekaru, har yau ta gaza gano manufar wasu daga cikin ahalin, abunda zata iya akullum kawai shine saka ido, da kuma jiran ranar da komai zai fito fili Jannart ta samu enci kamar ko wacce ɗiya a gidan ubanta, lokacin ɗaya taji idanunta na cicciko da hawaye sabida tausayin mairaini Jannart.

Asashin su Rayyern kuwa anutse duk suka kammala breakfast dinsu, bayan yayiwa su Abba da Mamy Sallama ne 

kuma, suka fito atare shida Ramadan zuwa compound din gidan, inda ya samu Hadi driver  d’insa na jiransa. 

Ganin ya shiga mota ne kuma yasa Ramadan shima shiga cikin tasa motar. 

Kaitsaye maigadi ya wangale musu Gatie suka fice daga cikin gidan. 

Suna hawa titi kuwa kowannensu ya kama hanyar inda zashi, Yayinda Ramadan ya wuce Mai-nasara hospital kaitsaye, shikuwa Rayyern government Hause ya nufa, domin acanne babban hall din da zasuyi taron yake.

Gaba d’aya compound d’in had’add’en wajen aciki yake da tarin manyan Mercedes benz, G waggon, da kuma range rover iri da kala, motoci ne duka da suka amsa sunansu ta manyan masu kud’i, Yayinda kuma kowa dake zuwa wajen ya kasance babban Doctor ne maiji da kansa, wanda kuma ya k’ware da sanin makamar aikinsa.

Gaba d’aya kowannensu sanye yake da suit ajikinsa, Yayinda kuma suke tafe cikin nutsuwa.

Sai-dai kuma ga mamakina duk inda Rayyern ya wuce sai naga wasu daga cikin doctors din na bashi girma, like suna respecting nasa, duk da kuwa cewar wasu da yawa sun fisa shekaru, amma sanin makamar aiki da k’warewarsa yasa suke jinjina masa. 

11:00 am dai-dai na cika kuma Gaba d’aya suka hallara acikin babban hall d’in, da tsaruwarsa ta zarce kwatantuwa, wanda cikin mutanen dake zaune awajen kuwa harda mai girma Govenor kano. 

Nanfa bayan kowa ya zauna suka shiga gabatar da taron nasu, inda d’aya bayan d’aya daga cikinsu ke tashi suyi bayani gamsasshiya, wanda kuma hakan tamkar k’arawa junansu sani ne sukeyi. 

Alhamdulillah dai sun gudanar da taron nasu yanda ya kamata, inda kowannensu ya fahimci d’an uwansa, bayan anci ansha ne kuma suka rufe taron da addu’a. 

Koda suka fito compound na hall d’in, kuwa tsayawa gaggaisawa da junansu sukayi.

Inda ananne kuma Dr. Lukman ya mikawa Rayyern d’in hannu sukayi musabaha.

Bayan sun gaisa d’inne kuma yakeyi masa murnar k’arin nasarar da yake ta samu, da kuma irin cigaban daya samu arayuwa. 

Dakai kawai Rayyern din ya iya amsa masa, domin magana bata wani fiye damunsa ba kuma ya gaji matuƙa da doguwar jawabin da yayi a likitance. 

Har ya juya zaitafi ne kuma maganar da Dr. Lukman din ke fada ya dakatar dashi.

Inda yaji yana cewa. 

“Please Dr.Rayyern Mai-nasara idan babu damuwa, muna gayyatanka wani zama da zamuyi yau a Dakata’s Company Nigeria Limited.”

D’an juyowa Rayyern yayi ya kalleshi, cikin rashin gamsuwa da kuma nuna shakka ako da yaushe yace.

“Ni kuma?”.

Da sauri Dr Lukman ya cire idonsa kan idon Rayyern ɗin tare da shakkarsa yace.

“Eh”.

 “Gaskiya bansan da zaman ba, impact ma banida wannan lokacin.” 

Ya k’are maganar agajarce yana mai duban agogon dake daure atsintsiyar hannunsa, hakanan yake Sam bayason wasa ko kuma raini.

Tabbas yana kiyaye kansa wanda kuma hakan d’abi’a ce dake cikin jininsa, awaje d’aya ne kawai zakaga murmushi da kuma fara’arsa, shine idan yana tare da Abbansa, Mamy da kuma Ramadan sai Baba Mauɗo, akasin haka kuwa Sam baya da sakewa da sauran wasu mutane, gentle mutum ne shi kuma straighforward, duk abunda ke bakinsa ya kuma san gsky ne shi yake fad’a, in ya ma daɗi ruwanka in kaji ba daɗi ma ruwanka.

 Sam arayuwarsa baya ta’ammali da  fad’an k’arya ko munafurci, hakan ba d’abi’arsa bace, then ba kuma ya shiga abunda bai shafe sa ba. 

Lips Dr.Lukman yad’an cije cikin kuma lallab’awa dayin k’asa da murya, yace.

“Please Dr. dan Allah karkayi rejecting gayyatarmu, domin kuwa zama ne da za’ayi da shuwagabannin companies masu ci ayanzu, ba kuma wani jimawa za’ayi ba only 1hour ma yayi, dan Allah da Manzonsa Dr. Rayyern Mai-sanara ka samu ka halarta, koda ace na tsawon 30mn ne!!!” 

Shiru yayi tare da d’an lumshe idanunsa, saboda gaba daya Dr. Lukman din ya kashe masa jiki daya ambaci sunan Allah. 

Tabbas akan komai idan ka ambata masa sunan Allah to yakanji zuciyarsa ta sake.

D’an numfasawa yayi tare da bud’e bakinsa ahankali yace.

“Is alright ba damuwa zanje, yaushe ne taron?”

Cikin hanzari da kuma Jin dad’i Dr. Lukman yace.

“Yau ne kuma yanzu nima can na nufa Insha Allah, ko zamu had’a hanya sainayi maka jagora.”

Kansa kawai ya jinjina, batare kuma daya sake cewa komai ba, direct ya nufi wajen motarsa, yana shiga kuwa Hadi driver yaja suka fice daga compound din wajen, ganin hakanne kuma yasa Dr.Lukman ma cikin sauri ya shiga motarsa ya rufa musu baya. 

Kusan atare kuwa suka iso babban company’n, Dakata wanda yakasance kayan masarufi ake sarrafawa aciki, Tabbas company’n yana da girma kuma yana da kyau ba laifi, saboda ank’awata cikinsa da abubuwa masu kyau.

Saidai kuma ga mamakin Rayyern kwata kwata babu wasu ma’aikatan kirki aciki. 

Haka dai Dr.Lukman yayi masa jagora harzuwa babban d’akin da sukeyin taro.

Koda ya shiga gaba d’aya mutanen dake wajen basu wuce su 18 ba, wanda kuma dukkaninsu suna zaune ne akan royal chairs.

Yayinda wani babban dogon table, wanda aka cika samansa da kayan drinks yayiwa gabansu k’awanya.

Akan daya daga cikin kujerun wajen Dr. Rayyern Mai-nasara ya zauna, wacce kuma ta kasance itace take facing na Barrister Kabir Saleh Dakata.

Agefensa kuwa Alhaji idi Sale Dakata ne zaune.

A hankali ya juyo ya kalli wani dattijon daya zauna ɗaya gefen nashi, Alhaji Abdu Tababa kenan.

 Numfashi ya ɗan fesar tare da ɗan kallon Barrister Kabir Sake Dakata.

Wanda tun shigowar Rayyern d’in ya kasa d’auke idanu daga kansa, domin hakanan yaji idanuwansa nayiwa Dr. Rayyern d’in Kallon sani, yanaji ajikinsa kamar a wasu shekarun baya masu tsayi ya tab’a sanin the same irin fuskar na, saidai kuma to Fuskar waye? Waya sani mai irin fuskar? 

Tambayar da bashi da amsarta, bashi kuma damai amsa masa haka yasa ya gaza janye idanunsa kan fuskar Rayyern yayinda yake motsa lips ɗinshi a hakali.

Shi kuwaRayyern ido ya ɗan zuba mishi a fakaice yana nazarto abinda ke zuciyarsa . 

Gaggaisawa sukayi amutumce kafun daga bisani Alhaji Idi Sale Dakata.

 Ya d’an muskuta ya gyara zamansa.  kana yace.

“Toh Alhamdulillah domin kusan gabaki d’ayanmu munsan abunda ya taramu da kuma musabbabin had’uwar mu anan wajen.

 Idan kuma akwai wanda zance baisani ba saidai wannan yaron wanda yazo yanzu.” 

Ya fad’i maganar yana nuna Rayyern da hannu,  cikin isa da gadarar dake bayyana cewar akwai wani abunda keyi masa suya a zuciya. 

Wanda hakanne kuma yasa Rayyern dago kai, ya soma bin kowannensu da idanu, yana mai karantar labarin dake zuciyoyinsu akan fuskokin su cikin hikima, da kuma haɗawa da ɗan lbransu da ya sani. 

Shikuwa Alhaji Idi Sale Dakata ci gaba yayi da cewa.

“kamar dai yanda kuka sani munzauna ananne saboda mu tattauna akan kasuwancin mu, sannan Rayyern kaida baka sani ba kasani, munyi wannan taronne nagamayyan manya-manyan company’s, saboda akwai buk’atar had’a kawunan mu, domin mu gudu tare mu kuma tsira tare bi ma’ana, mu had’e kasuwanci’n wuri guda mu haɗa hannu ta yadda zamu tsara farashin kayan abinci da sauransu a yadda mukeso..”

Ya dire ayar mgnar yana mai kallon.

Alhaji Abdu Tababa dake jinjina kai.

Kai Rayyern ya d’an girgiza tare da maida fuskarsa ya tsuketa waje d’aya,  domin lokaci guda ya dawo asalin Rayyern Mai-nasara dinshi, hazikin matashin da bayajin shakka ko tsoron duk wani magauci’nsa ya rigada ya gama saninsu in and  out yasan kowa yana da cikekken bayani kan kowansu. 

Gyara zamanshi yayi tare da maida bayanshi ya jingina da jikin kujera,

Kana ya ɗan juya kanshi hagu da damanshi.

Muskutawa yayi ya maida kujerar baya kaɗan kana ya ɗaura ƙafarsa ɗaya bisa ɗaya sabida zogin da yaji yatsarsa nayi mishi dan toms ɗin dake ƙafarsan ya takure yatsar da Jannart ta fasa mishi, cikin zuba musu ido ya sauƙe sassanyan numfashi, tare da cewa.

“Kuyi haƙuri”.

Yayi mgnar cikin mutuntaka da girmama su.

Cikin haɗe fuska Alhaji Yawale yace.

“A kan me? Me kake nufi da muyi haƙuri? Fito fili kayi mgn yadda zamu gane?”.

Numfashin mai nauyi ya fesar sabida, sarawar da kansa ya farayi sabida yadda suke mgn da ƙarfi.

Cikin nitsuwa yace.

“Bana buƙatar had’a hannu daku a cikin kasuwanci na!!!”.

Ya fad’i hakan in don’t care manner, domin iya gaskiyarsa ya fadi kamar yadda suka nemi ji. 

Idanu suka zazzaro gaba dayansu.

Yayinda Dr. Lukman dake gabansa ta  gefensa bisa hagu yace.

“Haba Dr.Rayyern ya zaka fad’i haka, agaban mutanen da yawancinsu sun haifeka, at least dai ai ya kamata ka daraja su ko dan sun fika gogewa a harkar tunda tun kan a haifeka suke juya kobo ta zama dubu…”

Wani irin kallo da Rayyern din ya watsawa Dr.Lukman d’inne yasashi saurin rufe bakinsa gum, saboda hatta hantar cikinsa saida yaji ta kad’a. 

“Bazan had’a hannu dasu ba, na fad’a na kuma sake maimaitawa Ni DR. RAYYERN BASHEER MUHAMMAD MAI-NASARA bazan had’a hannu dasu ba!!!”

Ya fad’i maganar da muryar dake bayyana iya gaskiya, da kuma zallan rashin tsoro ko shakkar kowa dake wajen.  

Gaba dayansu shiru sukayi sai Alhaji Ma’aji wanda yake da company’n Ma’aji and Sons ne ya d’an muskuta, tare da fad’in.

“Meyasa bazaka had’a hannu damu  ba?” 

Wayarshi ya ɗan zaro cikin aljihunsa kana ya ɗan danna kaɗan sannan ya medata cikin aljunsa tare da cewa.

“Awa ɗaya dana baku cikin ɗaƙiƙun rayuwata da Allah ya aramin, kunci 21mn saura muku 39mn, in kuma kun gamane zan tafi.”

Cikin hatsala Alhaji Yawale yace.

“Toh meyasa kace bazaka haɗa hannu da mutane ba”.

Juyowa yayi ya ɗan kalleshi kana yace.

“Sabida tafiyata da taku ba iri ɗaya bane.

Muddin muka ce zamu haɗa hannu, dole gefe ɗaya zai rinjayi ɗaya,

ta yiwu ku rinjayeni.

Ku ɓata min kekkyawan TUBALIn da aka ginamin.

Ko kuma Ni in rinjayeni in ruguza muku mummunan TUBALIn da kuka gina tun da daɗewa, in ɗauraku bisa tsarina wanda kuma nasan bazaku lamunci hakaba.

Dan haka muyi tafiyar a rabe shi yafi.

Domin ni dai a atafiyata talaka nake dubawa.

Ku kuma aljihunku kuke dubawa, ni kuma ba haka bace a tawa tafiyar, domin ahar kullum talaka nake dubawa, da rayuwarsu, manoman da suke noma abinci, su yake zuwa ya gagara yafi karfinsu, Yayinda ku kuma kunanan kuna juya abincin da suka noma da wahalarsu, yana zame muku manyan kud’ad’e,  Sam baku damu da talakan daya noma abincin ko yaci ya koshi ba, ko bai cika wannan duk ba damuwar ku bace, saboda haka.

 Bazan had’a hannu daku aci gaba da cutan talakawa ba, domin sudinma mutanene kamar kowa!!!”.

Wani  irin murmushi mai cike da tarin  ma’anoni Barrister Kabir Saleh Dakata yakeyi, yana mai kallon Rayyern ido cikin ido cike da alamun so, da kuma tsoro can ƙasan zuciyarsa.

Su kuwa sauran gaba ɗaya a hatsale suke 

Cikin yanayi  hasala Alhaji Idi Sale Dakata yace.

“Okay wannan dalilin shi yasa ka zagaya gaba d’aya, kan manyan  manoman da ƙanana da suke sayar mana da abinci ka hanasu sayar mana, har sai sun gama sun ware wanda zasu ci kafun su kawo mana mu mu saya?.” 

“K’warai kuwa hakane, saboda hakkinsu ne kuma guminsu ne, ya zama lallai tilas cutarwar da kukeyi musu ya isa haka, Manoma bawai bayinku bane, domin da ace babusu yau da dukkanku baku kai wannan matakin ba, har yaushe zaku daina ci gaba  da cutan mutanen da suke taimakon ku?.”

Ya kai k’arshen maganan nasa, cikin wata irin Muryar dake bayyana, cewa a shirye yake da yayi fito na fito da kowanne daga cikinsu, Sam babu alaman tsoron acikin zuciyarsa. 

Wani irin bak’inciki da kuma k’unci ne suka cika zuciyar Alhaji Idi Sale Dakata, wanda hakan yasa shi hasala, ak’ufule yace.

“Indai wannan k’udurin naka ne basai kana da rai da lafiya zaka cika saba, Lallai Tabbas ayi mugani idan zai yiwu!”

Cikin tsoro Barrister Kabir Saleh Dakata ya juyo ya kalli yayan nashi Alhaji Idi Sale Dakatan har ya buɗe baki zaiyi mgn kuma, sai yayi shiru ya juyo yana kallon Dr Rayyern Mai-nasara da yayi.

Murmushin dake bayyana izzarsa da fito da kwarjininsa, kana ya d’ago ya kalli Alhaji Idi Sale Dakata.

Cikin bayyana rashin tsoronsa yace.

“Kwarai saida rai da lafiya ake komai, amma kuma abun jin dadin shine babu wani mai rayawa ko kashewa sai Allah, babu kuma wani wanda ya isa yin abunda Allah bai nufa ba, koda wayeshi kuwa.” 

Sosai Alhaji Ahmed Tambari ya jinjina kanshi, hakama Barrister Kabir Saleh Dakata, fuskarshi suka zubawa idanu.

Suna tuno irin kamarsa da ya ƙalubalancu shekarun baya.

Dr Lukman kuwa rumtse idanunsa yayi sabida murya Rayyern na tuna mishi wata muryar data gabata.

Da ƙarfi ya kuma rumtse idanunshi sabida hatta ɗan maƙolloton wuyan RAYYERN irin na wancan mutumin ne.

Da sauri ya buɗe idanunsa jin Alhaji Abdu Tababa  na cewa.

“Tabbas babu mai rayawa ko kashewa sai Allah amma.

 Yaro ka san cewa komai akwai sanadi.

Toh Lallai watarana za’ayi sanadin da zuciyarka zata tsaya da bugawa ka kiyayi kanka.” 

Alhaji Abdu wanda yake aboki ga Alhaji Idi Sale Dakata ya fad’i hakan cikin hasala. 

Shikuwa Rayyern awannan karon dariya yayi harsaida fararen hakoransa suka bayyana, saboda shi gaba d’aya dattijawan ma gani yake kamar basu San mesukeyi ba, domin harya fara tunanin cewa girma ne kawai ya Kamasu. 

Mik’ewa tsaye yayi ahankali tare da daukar glasss dinsa dake aje bisa table d’in, taku daya  biyu yayi ya tsaya tare da juyowa ya kalli Alhaji Idi Sale Dakata.

Fuskarsa dauke da wani murmushi mai rugurguza zuciyar magauta yace.

“Idan akwai Allah to babu wani wanda ya isa da juyya RAYYERN Mai-nasara dole ya dakatar da Dakata in dai kan sayan k’udiri ne.” 

Cikin fushi Alhaji Idi Sale Dakata ya buga table din dake gabansa, tare da fadin.

“Karya kake yaro, wallahi kai karamin al’haƙine, domin kuwa mun munji da wayanda suka fika tauri da tsaurin ido ma, saboda haka kai ba komai bane.”

Still wani irin murmushi yayi Cikin kuma nuna halin ko inkula yace.

“Wai tsoro kuke bani ne?”.

A hatsale Abdu Tababa yace.

“Isa muke nuna maka”.

Ronƙofawa yayi kanshi kaɗan kana yace.

“Hmmmm nifa RAYYERN Ina da taurin kai, ni nan Rayyern babu wanda ya isa sakani abunda banyi niyya ba, haka kuma babu wanda ya isa sakani yin abunda zai sab’awa addinina, idan kuma kuna ganin wasa ne to Lallai magwaji ya gwada ya gani!!!.”  

Ya ƙarashe mgnar da ɗan sauti.

Kana ya D’an rank’wafo bisa kan Alhaji Idi Sale Dakata, cikin hade fuska da kuma zafin zuciya yace.

“Ina raga muku ne kawai saboda waɗannan fararen gemun dake kan fuskokinku, amma akasin haka hmmm nima zan iya take kowa kuma ya taku!!!”

Yana gama fad’in hakan ya juya afusace ya fice daga cikin dakin taron.

Dai-dai lokacin kuwa mota k’irar Black Benz ta faka a farfajiyar wajen,  ahankali Jannart ta zuro da kwawayan legs dinta waje, wanda suka sha dogon takalmi na al’farma, sannu ahankali kuma itama ta  fito daga cikin motar gaba daya.

Wata irin fitinanniyar gown ce mai masifar kyau ajikinta. Yayinda ta yane kanta da mayafin rigar, wanda hakan ya fallasa asirin kyawunta mai daukar hankali, daga gefen damanta kuwa Abdull ne ya fito, inda hannayensa ke dauke da wasu manyan basket guda biyu. 

Domin zuwa sukayi musamman dan kawowa su Daddyn nasu da kuma Barrister Kabir abinci, saboda sun shaida musu cewar suna da taron da zasuyi, shiasa Momy tayi girki na musamman aka kawo musu. 

Dai-dai isowar Jannart steps din da zata haura zuwa cikin hall din, shi kuma Dr. Rayyern ya fito daga cikin hall din ransa a matuk’ar b’ace ga wani irin masifeffen ciwon kai wanda ihun dattawan nan suka sakar mishi, ga yatsarsa dake zogi dan baima sha mgnin da safe ba.

Karab idanunsu suka sark’afe acikin na juna, saidai kuma ganinsa da Jannart d’in tayi ne yasa ta saurin janye jikinta baya.

A cikin hall ɗin kuwa gaba ɗaya sun hargitse kowa da abinda ke faɗi.

Haka yasa Barrister Kabir Saleh Dakata miƙewa da sauri ya nufo woje yana mai bin bayan Dr Rayyern Mai-nasara.

Shikuwa Rayyern kasancewar afusace yake shiyasa ko sake kallonta baiyi ba, direct ya nufi wajen motarsa wanda hakan yasa Jannart ta bisa da kallo. 

Har saida ya b’acewa ganinta.

Yayinda Barrister Kabir Saleh Dakata ma da yanzu ya fito sai binshi da idon yayi.

Abdull dake tsaye ne ya kalli Jannart tare da cewa.

“Ya dai kinsan sane?”

Dan kauda kanta gefe tayi, batare kuma da taja zancen ba tace.

“Eh muje kawai.”

Jin hakan ne kuma yasa Abdull Sakai.

Da sauri suka tsaya ganin ƙanin mahaifin nasu, sai dai hankalinsa baya kansu.

Motar Rayyern Mai-nasara ya zubawa ido.

Yana mai motsa lips ɗinshi a hakali.

Jin muryar Abdul ne ya sashi ɗan juyowa, ya amsa gaisuwar yayi tare da kayan kana yace.

Su tafi gida.

Daga nan suma suka juya gida.

Rayyern kuwa daga Cikin company din direct cewa yayi driver ya dawo dashi gida. 

Hakan kuwa akayi suka nufo gida kai tsaye. 

A nan Nassarawa G.R.A kusa. 

Riyyam-nsra ne ke tsaye ajikin wani tamfatsetsen gate na alfarma.

Wanda garin yawon zafaye anguwar da sukeyi ne da tattaki shida Nasir ɗin shi suka gilma ta gidan.

nan kuwa Nasir yace.

“Riyyam-nsra ya tsaya suyi video a gate ɗin gidan.

A hankali yake shafa tarin sumar dake kwance akansa.

Ahmad dake tsaye agabansa yana rike da, wayar Riyyam dinne yayi dariya tare da cewa.

“Nifa wallahi yanzu kam nagaji da rik’e wayannan, tun d’azun kake cewa zakayi video da waƙar hausa amma ka kasa, sai kace wani bak’o a harkar.”

Dariya shima Riyyam din yayi tare da cewa.

“Kafa san hausar tawa kar inje bin waƙar bai hauba.”

Murmushi Nasir yayi tare da cewa.

“No kada ka damu zaiyi.”

Murmushi Riyyam-nsra yayi tare da shafa sumar kanshi kana, ya ɗan ware sawunsa.

lokaci d’aya kuma ya nutsu, tare dasa Ahmad yayi start din videon,  cikin abubuwansa irin na tiktodians daya saba, ya soma rawa tare da bin wata waka dake tashi acikin wayar, inda yake cewa.

“Niba gida ba niba mota ba,”.

Yayi mgnar yana nuna gidan bayan nashi 

Kana yaci gaba da cewa.

“Bamai tarin dukiya masu yawa ba, Babana shiga gwamna ba, ba shugaban k’asa ba ba kuma member ba”.

Sosai Nasir yake murmushi yana jinjina mishi sabida yayi masifar kyau da bin waƙar hausa.

Cikin karsashin ganin Nasir na jinjina mishi yaci gaba da cewa.

“Banje makaranta maitsada ba, banje Dubai ba kuma banje London ba.

Gidanmu ba a G.R.A ne ba, ban d’auki selfie nasa Instagram ba.

 Ko zana zamma saniyar ware wallahi ni baza na zam makaryaci ba!!!” 

Sosai yake wani irin rawa mai ƙayatarwa yayi masifar kyau.

Dai dai lokacin kuwa Motar Dr  Rayyern Mai-nasara ta kunno kai dai dai wajen gate din, Yayinda motar Ramadan ma ta kunno kai ta b’angaren hagu, saboda shima yanzun nan shigowarsa cikin layin nasu. 

Atare suka ci wani irin birki  tare da zaro idanu saboda G…..

Ganin Riyyam Nsra da sukayi, domin daga Rayyern har Ramadan kusan atare idanunsu ya sauk’a akan matashin yaron dake tsaye ajikin gate din gidansu. 

Wanda shima kuma Rayyern din d’ago kansa kenan da zaiyi, ya sauk’e idanunsa akan na Rayyern dake zaune agaban  motarsa, inda yake zaune akan kujerar mai zaman banza, ya zauna agaba dinne kuma saboda lokacin daya fito daga hall din taro, na Dakatas company ransa a matuk’ar b’ace yake, wannan yasa bai tsaya wani tantance inda zai zauna dinba, kawai sai ya bud’e gaban motar ya shiga ya zauna. 

Sam kwata-kwata babu alaman murmushi akan fuskarsa, saima tsananin b’acin ran da yasa fatar fuskartasa tayi jajur, haka ma idanunsa, ga kuma wata yar jijiya da ta bayyana akan goshinsa,  sosai yakejin kansa na d’anyi masa ciwo, wanda kuma hakan ya faru ne saboda d’an yawaita magana da yayi yau din, da kuma ihun da way’ancan dattawan suka dingayi masa tsakar aka. 

“Laaah Hamma Rayyern!!” 

Riyyam-nsra dake tsaye fuskarsa d’auke da tsananin farinciki da kuma mamakin ganin Rayyern d’in ya fad’a, yana mai d’an matsawa daga jikin gate d’in, kaitsaye ya nufo wajen da motar Rayyer’n d’in ke tsaye.

Still fuskarsa dauke da murmushi yace.

“Thank God dama zan sake ganinka anan kusa, jiya kun b’acemin a airport nasha wahala sosai awajen neman ku.”

Idanu Dr Rayyern Mai-nasara ya lumshe duk da cewar, baya iya jiyo abunda Riyyam d’in ke fad’a, amma ya daiga bakin yaron na motsi kuma ya karanto abinda yake faɗin. 

Dai-dai lokacin kuwa daga cikin gidan, Baba Mauɗo ya wangale musu makeken gate d’in, wanda hakan yasa direct driver’n Rayyern din ya tura hancin motar ciki.

Wulgawan da motar tazo yine kuma yasa Naseer dake tsaye ya sauke idanunsa akan, wani handsome guy dake zaune acikin motar, wanda yake matuk’ar kama da abokinsa Riyyam-nsra.

Bakinsa ya wangale cike kuma da tarin mamaki yace.

“La Riyyam kalli wani maikama da kai.”

Murmushi Riyyam yayi tare da nade hannayensa akirjinsa, yana mai bin motar Rayyern da ta shige cikin gida da kallo.

Ramadan dake cikin motarsa kuwa, tun d’azu mutuwar zaune kawai yayi, tare da bud’e ido da baki yana kallon matashin saurayin, da yake ganinsa tamkar hoto copy din Yayansa Rayyern.

Lallai Tabbas wannan kamar da yake gani akan fuskar yaron, da kuma ta Hammansa Rayyern ta b’aci.

Cike da tu’ajjudi ya k’araso da motarsa zuwa bakin gate din gidan, tare dayin k’asa da glass din motar yana me sake Kallon yaron da har yanzu murmushi ke bayyane akan fuskarsa. 

Ganin kuma yaron ya dan juya masa baya, ya kuma tare masa hanya ne, yasashi danna horn.

K’aran horn dinne kuwa yasa Riyyam-nsra da kuma Naseer juyowa, suka sauk’e idanunsu akan Ramadan dake kokarin tura hancin motarsa cikin gidan. 

Idanunsu gaba d’aya suka zubawa fuskarsa, Yayinda lokaci daya Riyyam-nsra yaji wani irin abu ya daki kirjinsa, saboda Kallon fuskar Ramadan da yayi, ganin kuma kamar idanunsa na d’anyi masa gizo ne, yasashi sanya tafukan hannayensa yadan mutstsuke su.

Saidai kuma yin hakan da yayi ya sake tabbatar masa da cewar, bawai gizo idanunsa keyi masa ba, Lallai Tabbas fuskar wanda ke zaune acikin motar, tana shige da fuskar Mammy ce da kuma ta Zaytoon dinsa. 

Wani irin mamaki ne ya lullub’esa, Yayinda Naseer kansa shima daya ga kamannin fuskar Mammyn Riyyam dana Zaytoon, akan ta Ramadan dake zaune acikin motar yace.

“Allahu Akhbar Allah Mai girma Riyyam kalli wani maikama da Zayton da Mammy’n ka, gacan kuma wani mai kama da kai, kodai y’an uwanku ne sud’in?” 

Naseer ya kare maganar yana mai kallon, Riyyam wanda tuntuni ya nufi cikin gidan.

Ganin hakanne kuma yasa cikin sauri Naseer din rufa masa baya. 

Riyyam-nsra kuwa yana k’arasa shigowa cikin gidan, Dr.Rayyern Mai-Nasara na fitowa daga cikin motarsa, 

Haka ma Ramadan.

Cikin dan hanzari Riyyam din ya karasa, batare kuma da tunanin komai  ba, ya ware duka hannayensa tare da fad’awa jikin Rayyern d’in, ya d’an rungumesa da k’arfi.

“Naji dadin ganinka sosai Hamma Rayyern, nanne gidanku?, waye wannan Hamma Rayyern?” 

Riyyam-nsra yayiwa Dr. Rayyern duka tambayoyin, tare kuma da d’aga hannu ya nuna Ramadan dake tsaye, shima bakinsa d’auke da tarin tambayoyi. 

Tsumammun idanunsa ya lumshe ahankali, tare kuma da sauk’e wata irin ajiyar zuciya, Tabbas kafun iyanzu yanajin zuciyarsa na matuk’ar tafasa, saidai kuma gashi yanzu lokaci daya yaji zuciyar tasa nayin sanyi. 

Hannayensa yasanya ya d’an janye Riyyam daga jikinsa, kana ahankali yace.

“Eh. kanina ne, Ramadan.” 

Murmushin matuk’ar mamaki da kuma Jin dadi Riyyam yayi, cikin halinsa na faram-faram da sakewa, ya rungume Ramadan din, kana da d’abi’arsa ta wayewa yace. 

“Sunana Riyyam-nsra kuma naji dadin had’uwa dakai Hamma Ramadan.”

Murmushi mai dauke da wani irin Jin dadi, tare da zallan k’aunar yaron da yaji yana shigarsa alokaci guda Ramadan yayi, cikin kuma nuna zallan farincikinsa yace.

“Me too, amma wai a ina kasan Hamma Rayyern dina, da har kuke matuk’ar kama haka?”

Murmushi Riyyam-nsra yayi, kana cike da tsananin mamakin sautin muryar Ramadan irin tasa yace.

“Acikin jirgi muka hadu dashi jiya, nima nayi mamakin kamannin da mukeyi dashi sosai, amma kuma Allah babu yanda baya ikonsa, saboda haka ne ma ya zama Hamma na!!”. 

Riyyam ya kare maganar yana me bin Dr.Rayyern da kallo, wanda tuni ya soma tafiya harya kusa isa kofar da zata sada shi da babban falon gidan. 

Ramadan kuwa idanunsa yadan lumshe tare da sake rungume kyakkyawan matashin yaron ajikinsa, wanda ak’alla  shekarunsa baza su wuce 21 to 22 years ba, Lallai yaji matsanancin son yaron ajikinsa, har yakai ga yanajin inama da ace yaron zai zamanto k’ani agaresa, kamar yanda shiya kasance kani ga Hamma Rayyern, Tabbas yaji gamsuwa da yaron acikin zuciyarsa, Yayinda kuma kamannin Hamma Rayyern din dake kan fuskar yaron, yasanya shi jinsa awani waje na musamman a zuciyarsa. 

Hannun yaron ya kamo kana cikin kulawa yace.

“Masha Allah Riyyam-nsra mu shiga daga ciki, domin kuwa na kwad’aitu dason nunawa Abba da Mamy mu mai kama da Rayyern dinsu.” 

Murmushi sukayi su dukansu, kana Riyyam ya sake rik’e hannun Ramadan k’am acikin nasa, Yayinda acikin zuciyarsa yakejin wani irin nishad’i, ji yake tamkar ba yaune farkon fara haduwarsu ba, yanajin kamar tuntun tuntuni ya sansu, acikin wani bari na jikinsa. 

D’an juyowa Riyyam din yayi ya kalli

Naseer Ahmad dake tsaye, yana Kallon ikon Allah, tare da tu’ajjudin abunda ke faruwa. 

Alama yayi masa akan ya biyosu, hakan kuwa akayi cikin dan sassarfa Naseer ya rufa musu baya. 

Dr. Rayyern Mai-Nasara kuwa koda ya karasa cikin falon, direct part d’insa dake sama ya nufa, saboda ayanda yakejin kansa nadan sarawa, ba kuma yason wani abu da zaizo ya dameshi. 

“Abba! Mamy! Abbana!! ku fito kuga wani abun ban mamaki!!!”

Cewar Ramadan dake shigowa cikin falon, hannunsa rike dana Riyyam-nsra. 

Wanda kuma yanayin maganan nasa ne, cikin dan bayyana sautin muryarsa, ta yanda duk nisan dasu Abban suke zasu iya jiyosa, kasancewar kuma suna daya daga cikin bedroom din kasa, dake cikin falonne yasa, cikin sauri suka mik’e tsaye, tare da soma rige rigen fitowa asalin babban falon, saboda kiran da sukaji Ramadan d’in nayi musu,  yadan tsinkar musu da zuciya. 

Ai kuwa isowar su Ramadan din tsakiyar falon, yayi dai dai da fitowar su Abban. 

Fitowar daya haifar musu da wani irin bugun zuciya, tare da matsanancin firgici hadi da zallan mamaki.

A matuk’ar mamakance had’i da tu’ajjudi, Mamy ta dafe kirjinta tare da sake, ware Idanunta akan matashin yaron da hannunsa ke sark’afe dana Ramadan, wanda idan ba k’arya Idanun nata keyi mata ba, Lallai Tabbas kamannin d’anta Rayyern ne, kwance akan fuskar yaron. 

Cikin karfin halin daya kasa danne mamaki da tu’ajjudi’nta  tace.

“Ramadan waye wannan? A ina kasa moshi? Kamar fuskar Rayyern nake gani akan tashi fuskar, ko kuwa dai idanuna ne keyimin gizon hakan?” 

Murmushi Ramadan yayi, tare da sanya dayan hannunsa ya jawo Riyyam-nsra jikinsa, cikin kulawa kuma yace.

“Sam ko kad’an Mamy ba idanunki bane ke yi miki gizo, sunansa Riyyam-nsra, kuma tabbas yana matuk’ar kama da Hamma Rayyern dinmu, sannan Hamma Rayyern dinne ma ya samo shi, domin sun had’u ne a Ethiopia cikin jirgin da zai kawosu  Nigeria.” 

Shiru Mamy tayi tare da kafe yaron da ido.

Kamar dai yanda Abba ya kafesa da ido, baya ko k’yaftawa, domin tun Kallon farko da yayiwa yaron ya kasa dauke idanunsa daga kansa.

Wani irin bugawa yakejin zuciyarsa nayi, Yayinda wani abu ke tasowa tun daga cikin kasan kafarsa har zuwa tsakiyar kansa, Lallai Tabbas akwai kama aduniya, amma irin kaman Rayyern daya hango akan fuskar yaron tayi yawa. 

Ramadan dake tsaye kuwa ganin irin yanda fuskokin iyayen nasu, ke cike da zallan mamaki ne yasa shi, sakin murmushi tare da jawo hannun Riyyam-nsra suka k’araso kusa da iyayen nasu. 

Hannun Mamy Ramadan ya kamo, tare da d’an fad’ad’a murmushinsa, cikin kuma son basu cikakkiyar gamsuwa yace.

“Dan Allah Mamy ki kalli Riyyam da kyau, matuk’ar kama sukeyi da Hamma Rayyern dinki.”

Juyowa ya kumayi ahankali ya kalli Riyyam, wanda fuskarsa ke dauke da yalwatacciyar murmushi.

Shid’inma Murmushin yayi kana yace.

“Riyyam wannan itace Mamyn mu, Uwa d’aya tamkar da dubu, wannan kuma shine Abban mu, mahaifin daya kasance Garkuwa kuma jigo ga y’ayansa.” 

Yak’are maganar yana meyiwa Riyyam nuni, da iyayen nasu shida Dr. Rayyern. 

Yalwatacciyar fara’a ne ta bayyana akan fuskar Riyyam, Cikin matuk’ar ladabi da biyayya kuma yad’an durk’usa akan guiwowinsa, tare da bud’e bakinsa anutse yace.

“Abba da Mamy barkanku da gida, fatan zaku karb’eni kamar yanda su Hamma Rayyern da Ramadan suka amsheni, saboda daga yau Mamy kinzama mahaifiya agareni, haka ma Abba daga yau ka maye min gurbin Mahaifi.” 

Kusan daina bugawa zuciyar Abba tayi, alokacin da yaji saukar muryar yaron acikin kunnensa, saboda tsananin yanda yaji  muryar yaron tayi masa kama da ta Ramadan.

Yayinda daga gefe guda kuwa kwakwalwarsa ke neman juyewa,  saboda wani irin tsohon tunani mai karfi dake neman dawowa cikin lissafinsa, da sauri sauri zuciyar Abban ke bugawa, musamman ayanzu daya sauke idanunsa akan yatsun kafan yaron. 

Mamy kuwa da ayanzu taji zuciyarta nayin sanyi, hannayenta tasa ta d’an d’ago yaron, tare da sakar masa murmushi kana cikin tsananin kulawa tace.

“Insha Allah Riyyam mun karb’eka hannu bibbiyu kamar yanda su Hammanka suka karb’e ka.” 

Murmushin tsananin jin dadi Riyyam yayi, sai alokacin ne kuma ya dago kai ya sake Kallon Abban su Ramadan d’in, da har yanzu ya kasa dauke idanunsa akansa. 

Abban kuwa ganin Riyyam din na Kallon sa ne, yasashi dan sakin murmushi. 

Ramadan kuwa hannun Riyyam din ya kama suka dawo cikin falon suka zauna,  direct gaban fridgen dake cikin falon ya nufa, inda ya d’auko wa su Riyyam din bottle water da kuma fresh milk mai sanyi, ya basu suka sha shida Naseer da ya zama ɗan kallo.

Mamy kuwa da kanta ta k’arasa dining table, inda ta had’a musu lunch, saboda tuntuni rana tariga tayi.

Ramadan kuwa cike da soyayya yaja su Riyyam da kuma Naseer suka karasa kan dining table d’in. 

Bayan kuma sun zazzauna ne Mamy tayi serving dinsu, inda ta zuba musu lafiyayyar jalop rice din da tayi, wanda yasha kayan vegetables, da pepper chicken. 

Turawa kowannensu abincin tayi gabansa, tare dajan kujera itama ta zauna, anan kusa da Abba wanda shima yanzun ya karaso ya zauna.

“Rayyern fa ko bai dawo ba?”

Mamy ta tambayi Ramadan dake shirin kai loman abinci baki.

 

“Ya dawo amma ya haura sama, na daiga mood d’insa, kamar he’s tried, i think kuma stress din aiki ne.” 

Ramadan ya fad’a yana mai hadiye abincin dake bakinsa.

Kai Mamy ta jinjina cikin gamsuwa kana kuma ta d’ago kanta ahankali ta kalli Riyyam-nsra, fuskarta dauke da murmushi tace.

“Masha Allah Riyyam kaiko daga wacce k’asa kake?”

Riyyam dake cin abinci gyara zamansa yayi, tare da fuskantar Mamy’n, kana aladabce  cikin bagwariyar sausarsa yace.

“Ni d’an k’asar Ethiopia ne, acan mahaina da kuma y’ar uwata suke, acan aka haifeni kuma acan na taso nayi rayuwa, nazo nan Nigeria ne kuma saboda, abokina Naseer.”

Ya k’are maganar tasa yana me nuna Naseer dake shan Chapman din da Mamyn ta had’a. 

Mamy kuwa still murmushi tayi tare da soma cin abincinta. 

A Dai-dai lokacin ne kuwa Rayyern ya soma sauk’owa daga kan steps din falon, wanda ya sake shirya kansa cikin wasu had’add’un riga da wando, na normal jeans.

Sai-dai ganin da yayiwa su Abba da kuma Riyyam-nsra akan dining table ne, ya sashi tsayawa tare da zuba musu ido.

Abba kuwa da har yanzu baidainajin bugawar zuciya ba, d’ago kansa yayi ya kalli Naseer tare da cewa.

“Kai kuma a ina kake, su waye kuma iyayenka?” 

Jin tambayar da Abban yayi ne yasa Naseer gyara zama, cikin dan girmamawa yace.

“Sunan Babana Alhaji Ahmad Dasuki, mu asalin yan Nigeria ne, kuma muna zaune anan cikin garin kano unguwar Rijiyar zaki.” 

D’an Jim Abba yayi alamun dogon nazari, kana anutse yace.

“Sunan mahaifinka Alhaji Ahmad Dasuki, amma gaskiya bangane shiba.” 

Murmushi Naseer yayi, tare da cewa.

“Eh gaskiya bai shahara sosai ba, saboda ba a b’angaren kasuwanci yake ba, saidai Mamana yar gidan Malam MAI-NASARA ce, ni jikansa ne.” 

Lokaci guda walwalan dake kwance akan fuskar Abba ta kau, take duk wani annuri da murmushinsa suka gushe, badon komai ba kuwa saidan jin an ambata masa sunan Malam MAI-NASARA.

Ganin hakanne kuma yasa Ramadan, d’auke kansa daga Kallon Abban nasu da yake, inda ya sauk’e idanunsa akan Rayyern dake tsaye akan steps, wanda shi d’inma kuma Abban nasu yake kallo. 

Sam gaba d’ayansu basu San dalilin daya sa, Abban nasu baison gani ko jin wani abunda ya shafi Malam MAI-NASARA’n, basusan wannan sirrinba, haka kuma basusan dalilin ba. 

Kai Ramadan ya d’an sunkuyar ahankali cikin kuma rauni, dayin k’asa da murya yace.

“Abba yanzu ma abunda ya dawo dani gida kenan, dazu aka Kai mana Malam Mai-nasara hospital dinmu bashi da lafiya, hypertension and diabetes na damunsa, so akwai buk’atar Lallai lallai Hamma Rayyern ya duba sa, so Ya Sulaiman ya kikkira wayan Hamma Rayyern d’in amma kwata-kwata baya shiga, shiyasa na dawo gida saboda inasaka ran cewa zan iya samunshi, Dan gaskiya jikin Malam din ya tashi sosai!” 

Fuska Abba ya sake had’ewa tamau, cikin kuma nuna halin ko inkula yace.

“Babu inda Rayyern zaije, ai bashi kad’ai bane Babban Dr. acikin garin Kano, akwai Doctors da dama, akaishi wani asibitin mana.” 

Shiru gaba d’aya falon ya dauka, Yayinda Ramadan ya sunkuyar da kansa k’asa.

Shikuwa Rayyern dake tsaye idanunsa ya d’an rumtse, acikin zuciyarsa yana mai tambayar kansa, dalili da kuma hujjar da tasa Abban nasu bayason alak’arsu da Malam Mai-nasara, Tabbas da ace baisan waye mahaifin nashi ba, zuciyarsa zata iya sak’a masa abubuwa da yawa, saidai kuma amma yasan cewa mahaifinnasa mutumin kirki ne, babu yanda za’ayi wani mummunan tunani yayi tasiri acikin zuk’atansu sun san wayeshi mutun ne managarci daya ginasu kan kekkwan tubali nagarta.

Idanunsa da suke alumshe yadan bude, tare kuma da karasa saukowa akan steps din, kaitsaye ya nufo dining table din, duk da kuwa cewar har zuwa yanzu yanajin kansa nadanyi masa ciwo. 

Isowarsa dining table dinne kuma yasa duk suka dago kansu suka kalleshi, Yayinda Abban cikin matsanancin kulawa yace.

“Masha Allah Rayyern ka dawo, ya meeting din naku?”

Kujerar dake gefen ta Abban nasu yaja ya zauna, kana aladabce yace.

“Eh Abba na dawo, meeting kuma Alhamdulillah komai ya tafi yanda ya kamata.”

Kai Abban ya jinjina cike da gamsuwa tare da fadin.

“Alhamdulillah haka akeso ai akoda yaushe.”

Gyara zamansa yayi, kana ahankali cikin kuma yin kasa da murya, hadi da sigar roko yace.

“Abba dan Allah kayimini al’farmar samun daman duba Malam Mai-nasara, tunda Ramadan yace yana da buk’atar taimakona sosai, please Abba dan Allah me zai hana bazaka bari naje na dubashi ba!!” 

Ya k’are maganar tasa cikin k’ank’an da kai.

Yayinda Abba kuwa ya dauke nasa kan, tare da sake hade fuskarsa.

Ganin hakanne kuwa yasa Naseer zaro wayarsa, ya dannawa lamban Umminsa kira, cikin sa’a kuwa bugu biyu ta d’auki wayar.

Saidai kuma irin yanda Naseer din yaji sauti da Amon muryarta ne, yasa hankalinsa tashi.

Cikin fargaba yace.

“Ummi ya naji muryarki haka? meyake faruwa kodai jikin Malam ne ya tashi?”

Daga can b’angaren kuwa cikin sheshshek’an kuka Ummin tace.

“Eh Naseer jikin Malam ya tashi sosai, yanzu haka ankaishi Mai-nasara hospital, amma Dr da ya kamata ya dubashi bayanan, gashi kuma yanajin jiki sosai, domin sauran Doctors din da suka dubashi, sun tabbatar mana da cewar jininsa ne ya sauk’a, ga kuma diabetes.”

Idanun Naseer ne sukayi raurau lokaci daya kuma suka ciko da hawaye, ahankali yadan share k’wallan da suka zubo masa, kana yace.

“Kiyi hakuri Ummi Insha Allah Malam Mai-nasara zai samu lafiya, ki daina kuka muma zamu zo nan asibitin nida abokina Riyyam nsra.” 

Daga haka kuwa bai sake cewa komai ba ya kashe wayar tasa, ya maida ita cikin aljihu.

Sai kuma ya dago kansa ya kalli Abba wanda har yanzu kansa ke gefe.

Dan jan kujerar da yake kai baya yayi, tare da mikewa tsaye ya iso har gaban Abban ya durk’usa, cikin muryarsa irin ta masu neman al’farma yace.

“Dan Allah Abba kayi hakuri kabar Hamma Rayyern yaje ya duba Malam, yanzu haka Mamana kuka takeyi, kuma tace jikin Malam din ya tsananta sosai, dan Allah Abba kayi mana al’farma, Malam shine duk wani hasken cikin familyn mu, rasashi dai-dai yake da yankewar farincikin mu.”

Still Kai Abba ya sake kawarwa gefe batare daya ce komai ba.

Ganin hakannen kuma yasa gabaki d’ayansu sukaji zuciyoyinsu sun raunata, babu ma kaman Rayyern da hakanan yakejin duk wani al’amuran daya shafi tsohon acikin jinin jikinsa. 

Riyyam-nsra kuwa ganin yanda Abban ya kawar da kansa gefe ne, yasashi saukowa daga kan tasa kujerar shima ya durkusa agaban Abba’n.

Cikin sanyin da muryarsa tayi yace.

“Dan Allah Abba kayi hakuri, kabari Hamma Rayyern din yaje ya dubasa.”

Idanu Abba da ransa ke ab’ace ya rumtse, kamar kuma zaice wani abu saiya fasa hade da mikewa tsaye, kana yasa kai ya wuce bedroom d’insa kai tsaye…!

Back to top button