Uncategorized

Tsatsuba Book 7 Littafin Yaki Na Abdulaziz Sani M/Gini

Ku Taba Nan Domin Karanta Littafin Tsatsuba Na Ɗaya Wanda Abdulaziz Sani M/Gini Ya Rubuta.

TSATSUBA

Littafi Na Bakwai (7)

Part A

Marubucin Littafin

Abdul azis Sani M/Gini

Posting by..

Abubakar Saleh AlQuyraemey

 

Lokacin da Sarki Hulbasu ya gama fadawa dansa yarima Huzein wannan bayani sai ya rufe idanunsa a lokacin da hawaye ya zubo masa cikin tsananin bakin ciki mara misaltuwa ya yanga Yarima Huzein tare jini yai tsartuwa daga cikin wuyan huzein a lokacin da Hulbasu ya kurma uban ihu na takaici da bakin cikin ganin cewa ya yanka dansa da hannunsa shi kuwa mahaifin Sarki hulbasu wato Sarki yana

ganin sa adda Hulbasu ya yanka yarima huzein da hannunsa sai nan take ya hadiyi zuciya ya sulale ya baje a kasa matacce.

.

Koda sarki hulbasu yaga mahaifinsa ma ya mutu kuma ga gawar dansa yarima huzein a gabansa sai ya kama sambatu yana kai kawo a tsakanin gawarwakin biyu tamkar mahaukaci sabon shiga shi kuwa sarki Shardas sai ya bude da dariyar farin ciki yayi ta kyalkyala dariyar tamkar ba zai taba dainawa ba da sarki hulbasu yazo dai dai nan a labarin da yake baiwa hailur sai yayi shiru sa adda hawaye ya zubo masa yana hada idanu da hailur sai yaga shima hawaye ke sartu akan kumatunsa yana mai kurawa hulbasu idanu cikin tsananin tausayawa.

Hailur yaja dogon numfashi yace tabbas cin zarafin da sarki shardas yayi maka ya ninka nawa saboda kai ya tilastaka ka yanka danka da hannunka kuma ya zamo sanadin mutuwar mahaifinka kuma yanzu gashi ya mai daku bayinsa tunda duk arzikin kasarku wajansa yake komawa, hakika damu daku yanzu bamu da wani makiyi a doron kasa wanda yafi sarki shardas, kuma a halin yanzu yafi karfinmu babu abinda zamu iya yi masa kuma muna cikin mugun hadari na masifarsa domin da zarar ya fahimci cewa ina raye kuma ina tare dakai mu duka har iyalanmu tamu ta kare, koda hulbasu yaji wannan batu sai yai ajiyar zuciya cikin alamun tsananin fargaba da takaici sannan sai jikinsa ya kama tsuma zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone, yace to yanzu shike nan haka zamu cigaba da zaman jiran ranar da sarki shardas zai gano sirrinmu sannan yazo ya gama damu hailur ya girgiza kai yace babu wani abu wanda ba zai yiyu ba a cikin wannan duniya face ba a jarraba shiba komai nisan jifa kasa zai fado kuma komai karfin mutun da isar mulkinsa akwai ranar da zai fadi babu wata cuta wacce bata da magani kamar yadda boka zamaranu ya shaida maka cewa zaka iya hallaka sarki shardas amma sai an mallaki hular lamsara to me zai hana mu tafi neman wannan hula tunda ance mai nema yana tare da samu gwara mu rasa rayukanmu a kokarin neman wannan hula da dai mu zauna har makiyinmu yazo ya samu nasarar hallaka mu muna ji muna gani ka sani cewa ba karamin aiki bane a gabanmu idan har muna son mu ga bayan wannan babban makiyi namu dolene sai mutum ya sadaukar da wani abu idan yana son ya sami wani da farko dai dolene ka ajiye sarautarka kuma ka cire dukkan tsoro daga cikin zuciyarka dolene mu kawai da gaba dayan dakarun sarki shardas da hadiman da suka rako matata domin mu aiwatar da abinda ke gabanmu ka ayyana a ranka cewa zamu fita neman hular lamsara ne ba don komai ba sai domin mu dauki fansa akan sarki shardas shin yanzu zaka iya hakura da karagarka ta mulki da kuma kasarka da jama arka domin cika wannan buri naka?

.

Koda jin wannan batu sai hawayan takaici ya zubowa sarki hulbasu yace ai bani da wani zabi wanda yafi na hakura da komai din nayi wannan gagarumar tafiya in ba haka ba kuwa zan rasa komai da kowa nawa yanzu akwai abu daya nake tunanin yadda zamu sami nasarar yinsa a cikin nasara wato yadda zamu iya kawai da dakarun da suka rako shadila, 

.

Koda jin wannan batu sai hailur yayi murmushin yake yace haba ya shugabana a cikin kasarka fa suke wadannan dakaru ai kowa a gida sarkine, ni ina da shawara bisa yadda zamu kawai da su cikin kankanin lokaci a saukake ba tare da mun fuskanci wata matsala ba shawarar kuwa guda biyu ce da farko zamu iya amfani da sanya musu guba a cikin abincinsu duk suci su mutu idan kuma wannan hikima bata yi aiki ba sai mu ritsasu a cikin masaukinsu mu da dakarun masu yawan da ya ninka nasu sau uku mu yakesu, ni ka bar mini jagorancin dakarun da za suyi wannan aiki iana mai tabbatar maka da cewa zan yi iya kokarina na tabbatar da cewar dayansu bai tsira da rayuwarsa ba don kada yaje ya kai wa sarki shardas labarin abinda muka aikata, lokacin da sarki hulbasu yaji wannan shawara guda biyu na hailur sai yaja dogon numfashi gami da ajiyar zuciya kuma ya dubeshi cikin

alamun damuwa da fargaba sannan yace da farko dai idan muka yi yunkurin kashesu da guba ba lallai bane ya kasance cewa dukkaninsu zasu ci abincin kaga kenan akwai yiyuwar wani daga cikinsu ya tsira da rayuwarsa kuma ya sulale daga cikin birnin ya gudu bamu sani ba idan kuwa hakan ta faru asirinmu ya gama tonuwa haka kuma muka ce zamu yakesu anan cikin birnina a masaukinsu jama a zasu jiyo kururuwar yakin koda kuwa cikin dare ne sannan kuma ka san cewa suma fa zakwakuran mayaka ne wadanda suka san TUGGUN YAKI za a iya samun wani daga cikinsu ya sami damar sulalewa ya gudu idan ma hakan bata faru ba babu mamaki a cikin jama ar gari akwai dan leken asirin sarki shardas mai sa ido akan wadannan dakaru Nasa da suka rako gimbiya shadila izuwa kasata don haka ko wani dan motsi ya gani wanda bai yarda dashi ba yana iya garzayawa yakai labari, lallai akwai mummunan hadari a cikin duk wadannan batu sai ya numfasa yace ya kai abokina yakamata ka sani cewa matsoraci bashi zama gwani ko waye don haka dolene mutum ya siyar da ransa wajan neman sa a bisa bukatar dake gabansa ko ka so ko kaki ko ka gudu ko ka tsaya watarana sai sarki shardas yazo ya cika da yaki har gida tinda shi makiyi har abada a cikin kokarin ganin bayan makiyinsa yake.

.

Lokacin da hailur yazo nan a zancensa sai jikin sarki hulbasu yayi sanyi ya gamsu a ransa cewar bashi da wani zabi wanda yafi ya yi amfani da wannan shawara ta hailur don haka sai yayi shiru yana tunani har izuwa tsawon yan dakiku daga can kuma sai ya dago kai ya dubeshi yace na amince da duk shawarar da ka bani a daren yau zan hadaka da amintaccen sarkin yakina domin ku shirya duk abinda kuke ganin ya dace akan wannan makiyi namu nidai kawai na baku wuka da nama amma ina son ku gaggauta shirya yin wannan gagarumar tafiya tamu ta neman hular lamsara.

.

Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube hailur yayi godiya sannan ya mike tsaye da nufin ya fice daga cikin dakin sai sarki hulbasu ya ruko hannunsa yace ya zaka tafi baka tsaya kagana da tsohuwar matarka ba babu wanda ya isa ya raba Hanta da jini soyayyarka da matarka shadila tafi gaban wani dan adam ya rubuta saboda tsoron sarki shardas ba zan hanaka ka gana da ita ba tuni na shirya wannan ganawa naku.

.

Koda gama fadin hakan sai sarki hulbasu ya tafi zuwa bakin

kofar wannan daki da suke zaune ya kira sunan wani hadimi

nasa yace dashi ya ruga izuwa can cikin gidan sarautar bangaren matarsa ya taho da shadila cikin hanzari hadimin yace an gama ya shugabana nan take ya ruga da gudu izuwa cikin gidan sarautar shi kuwa sarki hulbasu sai ya yiwa Hailur sallama ya tafi tafiyarsa keda wuya sai farin ciki mai dumbin yawa ya turnuke hailur yaji kamar duniyar nan gaba daya aka bashi don haka sai ya mike tsaye ya kama kai kawo fuskarsa cike da annuri gami da farin ciki wanda ba zai misaltu ba yana cikin wannan haline yaji an turo kofar dakin an shigo cikin sauri ya waigo kawai sai yayi arba da shadila a tsaye ta kura masa idanu tana zubar da hawaye daki daki nan take shima idanunsa suka ciko da kwallar ya fara zubar da hawaye tsawon yan dakiku sun kurawa junansu idanu suna ta zubar da hawaye kamar ba zasu daina ba daga can kuma sai suka yi murmushi a tare suka ruga suka rungume junansu kuma suka fashe da kukan farin ciki na sake saduwa suna masu kankame juna sosai ba tare da son saki juna ba sai shadila ta ce yakai mijina yanzu ashe kana nan raye a cikin wannan duniya amma ban sani ba?

.

Koda jin wannan tambaya sai hilairu ya janye jikinsa daga cikin nata suka fuskanci juna yace yake abar begena dare da rana kiyi sani cewa ban taba mancewa dake ba tsawon dakika daya daga sa adda muka rabu kawo i yanzu ban taba zaton cewa zamu sake saduwa ba a cikin wannan duniya tunda ke kanki kin sa a ranki cewa na mutu na sani cewa sarki shardas ya aureki bisa dole to amma abu daya nake so na gani shin kin haife cikin dana dana barshi a tare dake ko kuwa sarki shardas ya kasheshi.

.

Koda jin wannan tambaya sai shadila tayi shiru ta kasa bashi amsa cikin hanzari hailur ya janye jikinsa daga cikin na shadila ya girgiza kafadunta ya ce cikin daga murya ki gaya mini gaskiyar ala amari kada ki boye mini komai shin dana yana raye ko ya mutu koda jin haka sai shadila ta fashe da kuka ta kasa bayani saboda tsoron abinda zai biyo baya kwatsam sai sukaji an turo kofar dakin an shigo duk su biyun

suka waiga bayansu a firgice da sauri don ganin ko wane ne ya shigo ba wani bane face yarima Hulkas tsaye idanunsa suna zubar da hawaye kuma ya kurawa hailur idanu koda shadila taga hulkas tsaye a gaban hailur kuma taga irin kallon da yake yi masa har yana zubar da hawaye sai ta kamu da tsananin tsoro jikinta ya kama tsuma saboda ta fahimci cewar abinda take tsoron kada ya faru ya gama faruwa.

.

Cikin sanyin jiki da alamun tsananin takaici hulkas ya nufi inda shadila ke tsaye a lokacin da hailur yabi hulkas da kallo ko kiftawa baya yi domin ya gane cewa lallai wannan yaro hulkas dansa ne domin hatta irin gabobin jikinsa iri daye ne nan take shima hailur yaji idanunsa sun ciko da kwallah lokacin da hulkas ya iso daf da shadila sai ya kama hannayanta ya ruke yace yake ummina menene dalilin da yasa tuntuni baki shaida mini cewa sarki shardas ba shine mahaifina ba, kinsan irin tsananin son da nake yiwa sarki shardas, kuma kinsan yadda na shaku da shi ainun tun ina kankani kawo i yanzu, yanzu da wanne ido zan fuskanceshi A matsayin babban makiyina Alhalin shine ya rene ni ya inganta rayuwata ki sani cewa sarki hulbasu ya bani labarinki kaf da asalinki da yadda sarki shardas ya murkushe jama arku kuma ya jefe mahaifina karkashin wannan tsauni mai mugun zurfi sannan ya kamaki da karfin tsiya ya Maisheki matarsa har da dub irin barazanar da yake yi miki akan kada ki sanar dani komai sannan ya sanar dani yadda sarki shardas ya tilastashi ya yanka dansa na cikinsa sanadin da ya zamo mutuwar mahaifinsa ya kunsa masa bakin cikin da har abada ba zai gushe ba a doron kasa tabbar sarki shardas ya cika babban azzalumi da babu kamarsa a doron kasa kuma dolene na kasheshi da hannuna, koda yarima Hulkas yazo nan a zancensa sai ya kurma uban ihu kuma ya durkushe kasa bisa guiwoyinsa biyu ya fashe dda matsanancin kuka koda ganin haka sai itama shadila ta fashe da kuka ta kasa rarrashinsa cikin sanyin jiki hailur ya dingisa ya isa gaban hulkas ya sunkuya ya dafa kafadar hulkas, koda hulkas yaji hannun hailur ya tabashi sai yai shiru tamkar daukewar ruwan sama sannan ya dago kai suka kurawa junansu idanu a lokacin da kowannansu ke zubar da hawaye har izuwa tsawon yan dakiku daga can kuma sai hulkas ya mike tsaye zumbur ya rungume hailur suka fashe da kuka a tare komai rashin tausayin mutum idan yaga lokacin da wannan da da mahaifinsa suka rungume junansu alhalin basu taba ganin juna ba basu san juna ba sai yau dolene zuciyarsa ta karaya ya tausaya musu.

.

Koda ganin abinda ya faru sai farin ciki ya lullube shadila sai da hailur da hulkas suka dan jima a kankame da juna sannan hailur ya janye jikinsa daga cikin na hulkas ya dubeshi a cikin

nutsuwa yace yakai dana ina son ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi ka sani cewa komai yana da lokacinsa ina mai tabbatar maka da cewa a halin yanzu in da duniyar nan gaba daya zata taru kaf ba zata iya kawar da sarki shardas ba saboda yana kan sharafinsa babu mai iya ganin bayansa a yanzu face jarumin da ya mallaki HULAR LAMSARA; 

.

Bisa wannan dalili ne ni da sarki Hulbasu muka yanke shawarar mu rokeku kuma mu kawar da dukkanin dakarun da suka rakoku sannan mu bazama duniya neman Hular lamsara saboda kai kanka yanzu rayuwarka na cikin mugun hadari idan har shardas ya gano ka san cewa shine ya tarwatsa rayuwar mahaifinka na asali ba zai barka da raiba to amma akwai wata matsala guda daya, koda jin wannan batu sai hulkas ya dubi hailur cikin alamun matukar mamaki yace yakai abbana me cece matsara kuma Hailur yace sarki shardas ma ba zai iya hallaka ka ba face ya samo wannan hula ta Lamsara kuma a halin yanzu tuni shida bokansa sun fita farautar wannan hula sun bar garinku a cikin mugun hali domin yanzu haka ana fama da fatara yunwa da fari a kasar tun daga ranar da kuka baro birnin kai da mahaifiyarka ya zamana wajibi mu gaggauta tafiya neman hular lamsara tun

gabanin makiyinmu sarki shardas ya rigamu samu.

.

Koda jin wannan batu sai hankalin yarima Hulkas ya dugunzuma ainun ya rasa abinda ke masa dadi a duniya musamman da yaji cewar mutanan kasarsu na can cikin mugun hali na fatara da yunwa kuma ga batun gagarumar tafiyar dake gabansa ta neman hular lamsara hular da babu wanda ya san inda take….

.

Kai bari dai na dakata A nan domin nima naje nayi shirin tafiya neman wannan hula saboda naga Alamar sun tsorata suna tsoron fita nemanta amma akwai wanda zai iya rakani kuwa hahahaha

Kafin nan Nine

Abubakar Saleh AlQuyraemey

Samanja 

Karanta Littafi>>> Tsatsuba Littafi Na Uku (3)

TSATSUBA

Littafi Na Bakwai (7)

Part B.

Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

08138873799 For More Littattafan Yaƙi 

.

Hular da babu wanda ya san ina take…Shikuwa yarima barmas tunda suka shigo cikin wannan daki tare da yarima hulkas ya zauna a gefe daya yana ta sauraran bayanin da Hailur ke yiwa hulkas sai takaici da tausayi suka sashi ya kama zubar da hawaye dama da dadewa mahaifin sarki hulbas ya bashi tarihin yadda sarki shardas ya tilastashi ya yanka dan uwansa yarima Huzein wato yaya ga yarima barmas sanadin da ya zamo na mutuwar kakansa kenan nan take zuciyar yarima barmas ta kama tafarfasa kamar zata kone babu abinda ya tsana a duniya sama da sarki shardas A cikin wannan haline aka ga kofar dakin ta sake budewa saiga Hulbasu tare da matarsa Luzuraina da kuma jaruma siyama

tare da mahaifiyarta zalina har da sadauki ruhaisu tsohon yaron hailur.

.

Koda ruhaisu yayi arba da hailur sai ya kamu da tsananin mamaki kawai sai ya ruga gareshi suka rungume juna cikin farin ciki mara misaltuwa suka kama kyalkyala dariyar murna sannan ruhaisu ya janye jikinsa daga cikin na hailur ya risina a gareshi cikin girmamawa yace ya shugabana ko a mafarki ban taba zaton zan sake ganin wannan fuska taka ba bare har na rungumi jikinka mai daraja ka sani cewa har yanzu akwai sauran jama armu da yawa suna rayuwa a boye cikin dazuzzukan wannan birni da muke ciki.

.

Koda jin wannan batu sai farin ciki ya sake lullube hulkas yace nayi matkar farin ciki da jin wannan albishir naka kuma lallai ina bukatarka tare da sauran wadannan jama a tamu, ka sani cewa ga shadila Allah ya dawo mun da ita don haka akwai gagarumin aiki dake gabanmu wannan yaro da kake gani wato yarima hulkas shine dan da  nabar shadila tana dauke da cikinsa.

.

Koda jin wannan batu sai hawayan farin ciki ya zubowa  ruhaisu ya ruga wajan hulkas ya rungumeshi a dai dai wannan lokaci ne yarima hulkas ya dubi siyama sa adda hawaye ya zubo masa sannan ya bude hannayansa yace da ita ‘ ashe ke yar uwata ce ban saniba?

.

Taho gareni yake yar uwata rabin jiki cikin matukar murna siyama ta ruga izuwa ga hulkas suka rungume junaa. A sannan ne zalina da shadila ma suka durfafi junansu suna murmushin saduwa suna haduwa sai suma suka rungume junansu zalina na kuka tace yake gimbiya hakika kaddara ce ta rabaki da mijin kwarai wanda babu kamarsa a wajena a cikin dukkan mazajen duniya amma tunda gashi yanzu ubangijinmu ya dawo miki dashi inaso mu hadu mu biyu nida ke mu bashi farinciki irin wanda bamu taba bashi ba a rayuwa ki dauka cewa yaune wannan dare na farko na amarcinku ehm keda shi don haka na baki kwanaki goma domin jiya ta dawo yau.

.

Koda jin wannan batu sai shadila ta sake kankame zalina a kirjinta da kyau cikin matukar farin ciki tana mai yi mata godiya, nan take sarki hulbasu ya dubi matarsa luzuraina yace dake da shadila da zalina ku tafi ku bamu wuri zamu yi ganawa ta musamman mu shida dinn nan ba tare da wata gardama ba kuwa sai matan uku suka fice daga cikin dakin suka bar sarki hulbasu, hailur da sadauki ruhaisu, siyama da hulkas da kuma barmas sannan kuma sai nan take dukkaninsu suka zauna tsawon yan dakiku dayansu bai ce uffan ba can sai sarki hulbasu yayi gyaran murya yace abinda yasa na taraku a nan shine kowannanku ya san cewa gimbiya shadila tazo nan birnina tare da tsaro na dakarun sarki shardas su dubu bisa jagorancin SADAUKI MARZANU, yanzu ina son na ajiye mulkina na tafi neman HULAR LAMSARA domin mu kare kanmu gaba daya daga sharrin sarki shardas don haka ina neman shawararku bisa yadda zamu yi dasu sadauki marzanu a mataki na farko da kuma yadda zamu kai ga cimma burinmu lallai ina son kowannanku ya bude kwakwalwarsa yayi tunani mai kyau.

.

Koda sarki hulbasu yazo nan a zancensa sai kowa yayi shiru aka rasa wanda zai fara yin magana koda ganin haka sai Hulkas yayi gyaran murya ya dubi sarki hulbasu cikin natsuwa yace ya shugabana ni shawarar da zan bayar itace kada muce zamu kawar da su sadauki murzamu a nan cikin birninka kawai a bari a gama kammala wannan gasa ta jarumtaka sai muyi shiri gaba dayanmu a matsayin zamuyi musu rakiya izuwa can karshen gari muna isa can saimu shammacesu mu afka musu mu kawar dasu gaba dayansu, mu tabbatar da cewar dayansu bai tsira da rayuwarsa ba amma idan mukace anan cikin wannan gidan sarauta zamu yakesu babu mamaki akwai yan leken asirin sarki shardas anan cikin garin wadanda suka sa ido akan su murzanu wanda da zarar abu ya samesu zasu iya gaggauta sanar da sarki shardas, koda hulkas yazo nan a zancensa sai ruhaisu ya dubi hailur da sarki hulbasu yace a matsayina na wanda ya dade yana jagorantar mayakan hari na sumame na yarda da shawarar yarima hulkas dajin haka sai hulbasu da hailur suka yi murmushi sannan sarki hulbasu ya dubi hailur yace yau nima zan fara shirye shiryen wannan tafiya a sirrance ba

tare da kowa ya sani ba sai a ranar da zamu tafi ne zan tara yan majalisata na sanar dasu cewar zan raka gimbiya shadila izuwa ga kasarta don tsoron kada a sami wata matsala.

.  

Akan hanya na fuskanci fishin mijinta kuma nan take zan bar galadima jiran karagata saboda shine kadai mutumin dana tabbatar da cewar zai iya rike amanata idan kuma akwai wani mai wata shawarar ne a cikinku ya fada.

.

Koda sarki hulbasu yazo nan a zancensa sai jaruma siyama tayi murmushi tace ina so ku sani cewa sai munyi taka tsantsan sosai akan dukkan shirinmu saboda maso abinka yafika dabara, kuma ma su iya magana sunce kifi na ganinka mai jar koma, ina mai tabbatar muku da cewa sadauki marzanu da sauran dakarunsa mutum dubu biyu ba kanwar lasa bane domin sun zuba ido sosai akanmu ko yaya suka ga wani mosti wanda basu yarda dashi ba sai sun dauki mataki, abu na biyu kuma shine sarkin yaki sadauki darkus ma yanzu dolene su sa ido akanmu gaba daya musamman bisa ganin cewa sarki ya bani kariya nida iyayena shin bakwa tunanin cewa zasu iya hada kai dasu sadauki murzanu domin gano sirrinmu. 

.

Koda jin haka sai sarki hulbasu ya girgiza kai yace tabbas hakan zata iya faruwa amma zanyi amfani da damata ta sarki nima nasa amintattuna su zuba ido akansu suyi nazarin dukkan motsinsu da shirye shiryensu abinda nake so daku shine mu dukkannan jarumaine don haka ina son kowa ya jajirce iya yinsa a ranar da zamu gama dasu sadauki marzanu domin mu tabbatar da cewar gaba dayansu ba wanda ya tsira mu bar ganin cewa zan tanaji amintattun dakaruna masu yawa a ranar da zamu fita wannan yaki wadannan mutane suna da matukar hadari da wannan furuci nake sallamarku amma banda abokina hailur.

.

Koda jin haka sai kowa ya mike tsaye ya nufi kofar fita daga cikin dakin amma banda yarima hulkas domin tsayawa yayi yana ta kallon hailur har saida sarki hulbasu ya dubeshi yace kada ka damu yakai yarima yau tare da mahaifin naka zaka kwana don haka kabi abokinka barmas nan da wani lokaci ma a cikin daren yau zamu sake haduwa gaba dayanmu.

.

Koda jin wannan jawabi sai yarima hulkas yayi murmushi sannan ya juya da sauri ya fice daga cikin dakin fitarsa keda wuya sai sarki hulbasu da hailur suka mike tsaye Hulbasu ya kama hannun hailur lafiyayyen ya jashi yana dingisa daya kafar suka fice daga cikin dakin suka durfafi wani bangare daban a cikin gidan sarautar yar gajeriyar tafiya suka yi suka iso wani babban falo wanda aka kawatashi ainun da shimfidu na koren kilishi da kuma korayen kujeru manya na alfarma kai ! Hatta labulayen dakin koraye ne komai a wajen kore abin gwanin ban sha awa babu mutum ko daya a cikin wannan katon falo kuma ga shi tsaf tsaf sannan an zuba kayan Alatu iri iri a cikinsa masu tsananin ban sha awa akwai dakuna guda bakwai a cikin wannan falo gami da kewaye guda biyar kowanne daki an sanya luntsumemen gado a cikinsa mai dauke da shimfidu masu taushin gaske, su kansu kewayen sama da kasansu da jikin bangwayensu dutsen lu’u lu’u ne kuma bahon wankan a cikinsu na zinare ne cike da ruwa mai kamshin turaren miski ga furanni kala a cikinsa sai da sarki Hulbasu ya zagaya da hailur cikin gaba dayan wadannan dakuna da kuma makewayin duka sannan ya dubeshi yace yakai abokina anan nake son kaci amarcinka da matarka ta farko shadila.

.

Koda jin wannan batu sai mamaki turnuke hailur yace haba ya shugabana ya nida nake talaka ba dan kowa ba zakace na zauna a cikin irin wannan kasaitaccen daki alhalin ni gaba dayan rayuwata ma a daji nayi ta lokacin da sarki hulbasu yaji wannan batu sai nan take yaji ya kamu da tsananin tausayin hailur har lwallah ta cika masa ido amma sai ya dubeshi cikin

murmushi yana mai dafa kansa yace yakai abokina shin ka manta ne cewa kai shugaba ne guda na kabila babba kaima sarkine kuma bana fidda ran cewa nan gaba zaka zama sarki don haka komai kyan daki da cikar kawarsa dai dai ne dakai, ni yanzu zan tafi izuwa ga iyalina ka zauna a nan ka jira Uwargidanka shadila zata zo ta riskeka nan ba da dadewa ba amma ka sani akwai walima ta musamman wadda na shirya a tsakanin iyalina da naka iyalin kadai domin tayaka murnar sake saduwa da danka da matarka a cikin daren yau don haka kayi zaton amsa gayyata koyaushe, koda gama fadin hakan sai sarki hulbasu ya juyaya fife daga cikin kasaitaccen falon ya bar hailur a tsaye yanata kalle kalle cikin tsananin farin ciki domin ji yake kamar a yau an mallaka masa komai

dake cikin wannan duniya.

”      ”      ”

A can turakar gimbiya luzuraina kuwa wato matar sarki hulbasu tuni ta zauna tare da gimbiya shadila zalina da siyama an kawo musu gasashshen naman kaji da yayan itatuwa suna ci suna hira cikin nishadi amma kuma hankalin shadila a tashe yake domin ta kasa cin komai ta sunkui da kanta kas tana tunani a lokacinda zuciyarta ke ta bugawa da karfi cikin alamun tsananin tsoro da fargaba.

.

Koda luzuraina ta lura da halin da shadila ke ciki sai ta kama

hannayanta ta rike ta dubeta cikin alamun nutsuwa tace yake kawata wai shin wane irin tunani mai zurfi kike yi ne haka wanda har ya hanaki sukuni ?

.

Koda jin wannan tambaya sai shadila tayi doguwar ajiyar zuciya. Sannan ta dubi luzuraina dasu siyama tace a cikinku

kaf babu wanda yasan sharrin sarki shardas sama dani yaki dashi dai dai yake da mutum daya jal yace zai tari gaba dayan halittun duniya saboda karfinsa da sharrinsa ya wuce tunanin mai tunani, ta yaya kuke zaton cewa gaba dayanmu nan zamu iya tsira daga sharrinsa alhalin ya fimu duk wani abu da muke takama dashi.

.

Koda jin wannan batu sai luzuraina ta numfasa tana mai dafa kafadar shadila tace yake kawata kiyi sani cewa masu iya magana sunce mai laya ya kiyayi mai zamani !

.

Ko shkka bana yi cewar komai nisan jifa kasa zai fado a saboda haka dole ne karen bana yayi maganin zomon bana

ki sa a ranki cewa wannan yaki ne tsakanin Gaskiya Da Karya da karfin gaskiyar mu ne zamu sami nasara akan wannan babban azzalumi wanda ya dade tsawon shekaru yana cutar da al umma haka dai luzuraina tayi ta kwantar da hankalin shadila tana lallabata har ta shawo kanta taci abinci ta koshi

suna kammala wannan cin abincine sarki hulbasu da hailur suka shigo cikin turakar.

.

Koda ganinsu sai kunya ta kama shadila ta sunkui da kanta kas ta kama murmushi na murna da farinciki ita kuwa zalina sai ta mike da sauri ta tarbi su sarki hulbasu tana mai yi musu barka da zuwa sannan ta dubi hailur cikin raha da zolaya ta ce to ango saboda doki ma ba zaka bari nakai maka amaryar taka ba shine ka biyota ?

.

Caraf sai sarki hulbasu ya tari numfashin hailur ya dubi zalina yace ke kuwa waya gaya miki cewa ta zama amaryar tasa ai dole ne da farko mu warware auren dake tsakaninta da sarki shardas sannan a daura mata sabo da hailur a sannan ne ta cika amaryarsa, tuni na gama shirya yadda za a tafiyar da bikin wannan aure a yau din nan cikin dare za a kara gabatar da gagarumar walima.

.

Koda jin wannan batu sai mamaki da farin ciki ya kama hailur da shadila har dama yarima dasu siyama sarki hulbasu ya dubi luzuraina yace dama wannan sakon muka zo mu sanar da ku kawai don haka idan lokacin walimar yayi zamu turo manzo ya tafi daku izuwa can inda za a gabatar da ita, AlQuyramey nake cewa haka kuma idan lokacin cigaba da wannan littafi yayi zakujini wato dai Gobe kenan.

Karanta Littafin>>> Tsatsuba Littafi Na Huɗu (4) 

.

TSATSUBA

Littafi Na Bakwai (7)

Part C.

Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

08138873799 For More Littattafan Yaƙi 

.

Idan lokacin walimar yayi zamu turo manzo ya tafi daku izuwa inda za a gabatar da ita, koda gama fadin hakan sai sarki hulbasu ya kama hannun hailur suka juya suka fice daga cikin turakar, fitarsu keda wuya sai shadila ta rungume zalina tana mai cewa godiya a gareki mara adadi yake abokiyar zamana domin na san cewa duk wannan shiri naki ne tabbas kin dawo mini da farin cikin rayuwata  wanda ya fiye mini komai a cikin wannan duniya kiyi sani cewa koda zan sami dare daya ne jal na wannan farin ciki na mutu ya fiye mini shekaru dubu da zanyi nan gaba na zauna tare da babban makiyi shardas.

.

Koda zalina taji wannan batu sai tausayin shadila ya turnuketa har hawaye ya zubo mata ta sake kankameta a jikinta tace yake abokiyar zamana kiyi sani cewa dole ne nasoki kuma na kaunaceki dari bisa dari kuma na san martabarki a cikin zuciyarsa kece masoyiyarsa ta farko a rayuwa kece kika sha wahalarsa duk da cewa nima nayi wahala dashi amma ai kin kunshi bakincikin dako rabinsa ni ban kunsa ba sa adda shadila taji wannan batu na zalina sai taji itama ta kamu da sonta fiye da ko yaushe don haka sai ta kara kankameta a jikinta suka kama kukan murna yayinda yarima hulkas da jaruma siyama suka ga haka si suma suka kamu da tsananin tausayin iyayen nasu har hawaye ya zubo musu a tare, kawai sai siyama ta kama hannun hulkas ta ja shi suka fice daga cikin dakin suka nufi wani bangare daban a cikin harabar gidan sarautar sai da suka iso wani fili mai fadi inda babu jama a wanda ya kasance mai shirun gaske sannan suka zauna tsawon yan dakiku dayansu baice uffan ba sannan siyama tayi gyarar murya tace yakai dan uwana kayi sani cewa nayi matukar farinciki dana san cewa ashe ina da dan uwa a cikin wannan duniya wanda muke uba daya. A farkon haduwata dakai naji ina sonka So irin wanda mace ke yiwa namijin da take fatan zama abokin rayuwarta amma yanzu da na gane cewa kai muharramina ne sai naji nafi kaunarka fiye da ko yaushe a matsayinka na jinina don haka

kukanka kukana ne kuma farincikinka nawa ne mahaifin nan namu ya dade yana bani horon yaki saboda kawai na dauki fansa akan ubanka na karya wato sarki shardas ko a bayan ransa, shin yanzu zaka bani hadin kai mu hada karfi da karfe domin cika wannan bavvan buri na mahaifin mu?

.

Ka sani cewa raina ba a bakin komai yake ba akan wannan al amari shin zaka iya cire soyayyar sarki shardas dake cikin ranka ka kasheshi da hannunka.

.

Koda siyama tazo nan a zancenta sai idanun yarima hulkas suka ciko da kwallah nan da nan hawaye ya kama sartu akan kumatunsa, Al amarin da ya karya zuciyar siyama ke nan ta rungumeshi kuma itama ta fara kukan cikin sanyin jiki hulkas ya janye jikinsa daga cikin nata suka fuskanci juna a lokacin da kowannansu ke zubar da hawaye hulkas yace yake yar uwata kiyi sani cewa bazan iya cire son sarki shardas daga cikin zuciyata ba amma zan iya kasheshi da hannuna ba don komai ba sai domin a halin yanzu babu mutumin da na tsana sama dashi a doron kasa na tsaneshi ne saboda zaluncin da yayiwa iyayena da kuma munafurtata da yayi ya rinka wahalar da mahaifiyata tsawon shekaru da shekaru amma yana nuna mini cewa shi masoyinta ne na kwarai, ban taba sanin cewa har dukanta yake yi ba a boye a bayan idanuna, shin yanzu ke a cikin zuciyarki kina da yakinin cewa zamu iya gano inda Hular Lamsara take har mu mallaketa mu sami damar da zamu dauki fansa akan sarki shardas alhalin bamu san a inda take ba kuma bamu san wanda ya san inda take ba.

.

Koda yarima hulkas yazo nan a zancensa sai jaruma siyama taja dogon numfashi sannan ta kama hannayansa biyu ta rike suka kurawa juna ido sannan tace yakai dan uwana kayi sani cewa a cikin wannan duniya babu abinda ba zai yiyu ba face wanda ba a jarraba yinsa ba shin baka da labarin  yadda akayi JARUMI HANTARU ya sami nasarar dauko Takobin SAIFUL LUJARA ? yasha bakar wahala kuma yasha

gwagwarmaya da manyan sadaukai irinsu RABBASU wadanda suka fishi karfi amma saboda sa a da naci gami da rabo sai da yakai ga gaci.

.

Shin baka da labarin jarumin nan mai mashin GALILUL HARAS ? wato SADAUKI SHADDADU shima yasha bakar wuya gami da gwagwarmaya kafin ya mallaki wannan mashi to a yanzu ma ina ji a jikina cewa kaine jarumin da zai mallaki HULAR LAMSARA sai dai kuma ……

.

Koda siyama tazo nana a bayaninta sai muryarta ta shake da kakarin kuka ta kasa karasa abinda take son fada ta fashe da kuka sosai al amarin da yai matukar dugunzuma hankalin yarima hulkas kenan ya sake rungumeta a kirjinsa yana mai cewa haba yake yar uwata menene na kuka me zaki boye mini alhalin ni dan uwanki ne na jini to ki sani cewa na san abinda kike boye mini wannan abu ba komai bane face duk wanda ya mallaki wannan hula ta lamsara sai ya rasa rayuwarsa kuma a tafarkin SOYAYYA zai hallaka kamar yadda ragowar JARUMAN DUNIYA biyu suka hallaka. Tuni na dade da jin tarihin wannan manyan makaman yaki guda uku kuma na sani cewa nine na ukun nasu nasan cewa mutuwa zanyi to amma ki sani cewa ni yanzu nayi matukar farin ciki da ya kasance bake bace masoyiyar da zan mutu a tafarkin soyayyarta ba ke yanzu yar uwata ce ta jini wadda na tabbata da cewar ko bayan raina zata iya kula da mahaifiyata lokacin da yarima hulkas yazo nan a jawabinsa sai jaruma siyama taji kaunasa ta kara linkuwa a cikin ranta don haka sai ta sake rungumeshi suka fashe da kuka gaba dayansu sai da suka dan jima kankame da junansu sannan jaruma siyama ta janye jikinta daga cikin na yarima hulkas ta mike tsaye kawai sai ta juya masa baya tace wane shiri ka fara yi domin ka kai ga wannan matsayi na zama JARUMIN DUNIYA na uku mai

hular lamsara?

.

Yakai dan uwana kayi sani cewa ba a zama wane a banza dole sai an sha bakar wuya da tarin gwagwarmaya, koda jin haka sai yarima hulkas ya mike tsaye yasha gaban siyama yace yanzu wane irin shiri kike nufi zanyi ?

.

Jaruma siyama tayi murmushi tace dole ne ka cigaba da baiwa kanka HORON YAKI har ka sami wanda zaka iya zuwa inda hular lamsara take ka daukota a halin yanzu bincike ya nuna cewa kai da sarki shardas kuna bukatar wannan hula ta lamsara kafin dayanku ya sami nasarar hallaka daya shi dai sarki shardas a halin yanzu yana da karfin da zai iya zuwa wannan wuri da hular lamsara take bisa taimakon bokansa to amma inda matsalar take shine dashi da bokan nasa basu san a inda hular lamsara take ba sai dai kuma akwai wanda suka nema wanda shine kadai zai iya yi musu jagora izuwa wajen ba wani bane ba wannan jagora nasu face wani hatsabibin Tsohon Aljani wanda a halin yanzu duk fadin duniya babu Aljanin da yafishi yawan shekaru babbar magana yafi kowa sanin sirrin wadannan manyan makaman yaki guda uku wato takobin saiful lujara, mashin galilul haras

da kuma hular lamsara shidai wannan tsohon aljani ana kiransa da suna ARWASUL MASADUL.

.

Aljani Arwasul masadul yana da tsananin karfin gudu a cikin sararin samaniya domin daga birnin hindu yana iya zuwa birnin sin a cikin abin da bai wuce sa a biyu da rabi ba don tafiyar da bata wuce ta kwana talatin ba kuwa a cikin abinda

bai wuce wasu yan dakiku ba yake kammalata ya kasance bashi da takamaiman wajan zama kuma yana iya zagaye duniya kaf a cikin yini daya kuma kullum sai ya zagayetan ma ana dai  baya zama waje daya tamkar shanshani komai karfin sihirin tsafin boka bai isa ya iya ganin a inda aljani arwasul masadul yake ba kuma bai isa ya kirashi ya amsa kiransa ba haduwa da aljani arwasul masadul sai babban rabo da sa a kawai neman Aljani arwasul masadul dai dai yake da neman jaki mai kaho idan kuma har mutum yayi dace haduwa dashi tofa duk abinda ya bukata daga gareshi indai akwai shi a cikin wannan duniya to zai kaishi inda abin yake a cikin kankanin lokaci Inda matsalar take shine aljani Arwasul masadul baya yawo a cikin siffarsa gaskiya Littafin nan nikaina da nake typing dinshi duk da na jima da karantashi yana sake kayatar dani uhm kufa ? Yakan rikida ne izuwa siffar bil adama sau tari ko ta dabba ko ta kwaro don haka sai mutum yaci jarrabawarsa sannan yake taimakonsa babbar illar aljani arwasul masadul itace ba a rudarsa da dukiya ko mace ko mulki, kuma bashi da tausayi ko jin kai shi kawai yana da wadansu ka’idoji ne wadanda  sai ka cikasu sannan zai taimakeka kuma dole sai ya zauna tare dakai tsawon kwana uku yaga ka cika ka’idojin babu wanda yasan wadannan ka’idoji na aljani arwasul masadul, baya ga haka aljani arwasul masadul yana da karfin damtse na rikakkun zakuna guda dubu dari da tamanin kuma duk duniya babu mai karfin sihirinsa na tsafi amma wani abin al ajabi a tare dashi shine babu abinda ya tsana sama da kudi ko mulki kuma babu abinda yake so sama da jarumi mara tsoro kuma mai sa a ya kai dan uwana kai mutum ne mai tsananin sa a bisa duk abinda kasa a gabanka sannan kuma na fuskanci cewa ko kadan baka da tsoro bisa wannan dalili ne nake da yakinin cewa zaka mallaki hular lamsara kafin sarki shardas ya fita nemanta, ka sani cewa sammako anema ba shine samu ba kai dai kawai ka nemi sa a da dace, lokacin da jaruma siyama tazo nan a jawabinta sai yarima hulkas ya kamu da tsananin mamaki ya dubeta yace yaya akayi kika san duk wadannan al amura koda jin wannan tambaya sai siyama tayi murmushi tace na taba haduwa da Aljani Arwasul masadul kuma na cinye jarrabawarsa a lokacinda nake yawon farauta a cikin daji kuma nayi mu amala da shi ta tsawon kwana uku ba tare da na san ko shi waye ba lokacin da yagabatar da kansa a gareni kuma ya fito mini a siffarsa ta ainihi sai ya tambayeni abinda nake bukata a cikin wannan duniya ya kaini inda abin yake domin na mallakeshi.

.

Koda naji wannan tambaya daga gareshi sai nayi murmushi nace abinda nake bukata ba zaka iya bani shi ba cikin mamaki aljani arwasul masadul ya dubeni yace ke yarinya kin yi babban kuskure da kika fadi haka ki sani cewa komai yawan dukiyar da kike bukata zan kaiki inda take kuma na kwasheta nakai ta inda Kikeso a cikin dakiku kadan idan mulki kike so na kowacce kasa a cikin wannan duniya zan iya baki shi koda karfin tsiya a cikin dakiku kadan ke idan ma duniyar gaba daya kike sonki mulka zan iya yi miki sanadin hakan to menene kuma abinda kike ganin cewa zai iya gagarata sa adda naji wannan batu na aljani arwasul masadul sai nayi murmushi a karo na biyu nace yakai wannan aljani ka sani cewa duk abinda ka ambata bana bukata ko daya daga cikinsu face ina son ka hana aikata zalunci a doron kasa a tsakanin al ummar mutane da aljanu da kuma tsakanin dabbobi da kwari sannan ka hana zubar da jini a ko ina na duniya ya kasance duk duniya kowa na son kowa ana zaman lafiya babu batun sata ko kwace babu fyade kuma babu bambanci tsakanin attajiri da talaka da kuma tsakananin bawa da sarki wadannan abubuwa sune kadai cikar burina na duniya idan har ka har ba zan gansu da idanuna ba bana fatar nayi doguwar rayuwa a cikin wannan duniya domin takaicin rashinsu ne zai zama babban bakin cikina.

.

Koda nazo nan a zancena sai naga hawaye ya zubowa Aljani Arwasul masadul yasa hannayansa biyu ya dafa kafaduna ya ce kece bil adama ta farko a duniya data taba burgeni a cikin jinsin mata kuma ban taba haduwa da mai irin wannan ra ayi naki ba ba wani abu bane yasa kika ga na zubar da wannan hawaye baface takaicin kin tambayeni abinda har na mutu ba zan iya samarwa da wani shi ba ina mai tabbatar miki da cewa aduniya ba za a taba zama lafiya ba domin a hakan ta fara kuma a hakan zata kare wannan shine tarihin da na riska a wajan kakana na dari da ashirin kuma nayi imani da wannan tarihi, yake wannan jarumar mata hakika ba zan taba mancewa dake ba a rayuwata domin ni a wajena kece jarumar jarumai wadda bata damu da komai na duniya ba yaune ranar karshe ta saduwata dake kuma ba zaki sake ganina ba har izuwa ranar da zan mutu ko ke ki mutu amma ina fatan nayi miki taimako a sirrance ba tare da kin sani ba kafin karshen rayuwata ina mai yi miki fatan nasara da sa a a rayuwarki bisa wannan buri naki da naji kin ambata daga yau nayi alkawarin cewar ba zan sake zaluntar wani bil adama ba a doron kasa kuma ba zan taba taimakon wani azzalumi ba amma lallai ki bar wannan al amari sirri karki gayawa kowa face jarumin da kika tabbatar da cewa shine zai kawo karshen zalunci, shugaban azzalumai na wannan zami a cikin jinsinku na bil adama da wannan furuci nake yi miki bankwana na karshe.

.

Koda aljani Arwasul masadul yazo nan a jawabinsa sai hawaye ya zubo mini na rungumeshi ai kuwa sai naji shima ya fashe da kuka daga can kuma sai haji babu shi a jikina ina bude idanuna na nemeshi sama da kasa na rasa yau shekara uku kenan da faruwar wannan al amari kuma ban taba baiwa kowa labarin abinda ya faru ba sai yanzu da nake sanar dakai saboda zuciyata ta yarda kuma ta aminta cewa kaine jarumin da zai kawo karshen zaluncin shugaban azzalumai na bil adama wato sarki shardas.

.

Koda siyama tazo nan a zancenta sai yarima hulkas yaji gaba daya tsigar jikinsa ta tashi kuma yaji cewa a zuciyarsa ta aminta da duk abinda siyama ta fada dari bisa dari saboda haka sai ya sake kamo hannayanta ya rike yace yake yar uwata kiyi mini Alkawarin cewar zaki kasance a tare dani a cikin wannan doguwar tafiya da zamuyi ta neman hular lamsara kuma zaki taimakeni da ranki da dukkan karfinki kuma babu abinda zai rabamu face mutuwa domin a yanzu ne na tabbatar da cewa kece rabin jikina idan babuke babu abinda zan iya aiwatarwa na dangane da babban burin dake gabana saboda ra ayina ya kasance iri daya da naki kinga kenan burinmu duk iri daya ne ni dake.

.

Koda jin wannan batu sai siyama ta rungume yarima hulkas ta fashe da matsanancin kuka. Al amarin daya karya zuciyar sa ke nan  shima ya fashe da kukan aka rasa wanda zai rarrashi wani a cikinsu.

.

Lokacin da dare ya soma yi ne wata kuyanga ta taho turakar gimbiya luzuraina ta risina ta  kwashi gaisuwa gareta sannan tace ya shugabata sarkine ya aikoni nayi muku jagora zuwa dakin walima ke da amarya shadila koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube luzuraina da shadila dama tunda aka watse aka barsu su biyu suna ta hira ko gyangyadi basuyi ba tuntuni duk su biyun sun caba ado don haka sai suka mike tsaye zumbur da nufin su fita amma sai shadila ta rike hannun luzuraina suka tsaya ta dubeta tace ba zan iya zuwa wannan dakin walima ba face bisa jagorancin abokiyar zamana zalina don haka sai dai mu biya ta dakinta mu tafi tare, koda jin wannan batu sai luzuraina tayi murmushi tace ai rashin hakuri kikayi ai dole ne mu nemi sa hannun uwar gida a cikin wannan al amari don haka muje gareta yanzu Nima kuma bari naje ga neman kudina yanzu.

.

Kafinnan Nidinne dai

AlQuyramey

Karanta Littafin>>> Tsatsuba Littafi Na Shida (6)

Littafi Na Bakwai (7)

Part D.

Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

08138873799 For More Littattafan Yaƙi 

.

Ba tare da wani bata lokaci ba kuwa sai luzuraina ta kama hannun shadila tajata suka fice daga cikin dakin itama wannan kuyanga da tazo domin tayi musu jagora izuwa dakin walimar sai ta koma bayansu sukayi ta ratsawa ta gaban dakarun dake tsaron gidan sarautar suna wucewa ta cikin kofofi.

.

Abinda ya daure musu kai shine a wannan dare gaba daya hadiman gidan sarautar babu su  wadanda komai dare a cikin kai kawo suke suna gabatar da ayyukansu su kansu dakarun tsaron a yau sun kasance kalilan basu da yawa kuma sune amintattu wadanda koyaushe suna tare da sarki basa rabewa.

.

Koda ganin wannan sauyin yanayi sai mamaki ya turnuke shadila ta dubi luzuraina a cikin dan alamun tsoro tace yake kawata menene dalilin daya sa naga komai na gidan nan ya sauya a wannan dare ba haka na saba ganin abubuwa suna gudana ba, koda jin wannan batu sai luzuraina tayi murmushi tace ba komai ne ya kawo haka ba face tabbatar da sirrin daurin wannan aure da zai gudana  daga sanin makiyanmu.

.Tsatsuba Na 1 Complete Littattafin Yaki By Abdulaziz Sani M/Gini | https://www.aihausanovels.com.ng/2022/07/tsatsuba-na-1-littattafin-yaki.html

Koda jin haka sai farinciki ya lullube shadila ta kama murmushi  tayi shiru bata ce komai ba, haka dai suka cigaba da tafiya suka iso kofar dakin da zalina take, da isowarsu sai luzuraina ta kwankwasa mata kofar tace yake uwargidan hailur ki fito ki raka amaryarki izuwa ga angonta kafin luzuraina ta gama rufe bakinta tuni an bude kofar dakin kawai sai suka ga zalina tsaye a gabansu ta caba ado na gaban kwatance tamkar itace amaryar kuma fuskarta cike da annuri gami da murmushi kana kallonta ka san cewa

tana cikin matukar farin ciki tana ganin shadila sai ta rungumeta tamkar wacce taga yar uwarta ta jini sannan ta kama hannunta tajata suka yi gaba tana mai cewa muje na damkaki a hannun masoyinki na kwarai koda jin wannan batu sai shadila da luzuraina suka cika da mura nan take wannan kuyanga ta shige gaba tayi musu jagora izuwa dakin walimar, falo ne babba mai matukar tsawo da fadi wanda sarki hulbasu ke yin babban taro a cikinsa musamman a lokacin da ya gaiyato manyan baki daga kasashen duniya babu kowa a cikin wannan babban falo face sarki hulbasu hailur da yarima hulkas dakuma jaruma barmas sai kuma amintattun hadiman sarki hulbasu

da amintattun kuyanginsa gaba daya teburan dake cikin wannan falo an cika samansu da kayan alatu na abinci dana shaye shaye kala kala na alfarma babu irin kalar da babu, a gefe daya kuma wadansu makadane da mawaka na sarki suma amintattunsa ne wadanda babu yadda za ayi su bayyana sirrinsa domin tun zamanin kakansa suke yin wannan aiki.

.

A can wani bangare na daban kuma wadansu kyawawan yan mata ne su  takwas sanye cikin fafaren tufafi wadanda suka kasance yan rawa sun kama tamkar gumaka da babu ruhi a jikinsu koda shigowar amarya shadila da su zalina cikin wannan babban falo sai makada suka fara wani irin kida mai taushi da dadin gaske su kuma wadannan yan mata yan rawar dake kame suka fara yin rawar Mawakan kuwa sai suka kama rera wata irin waka mai dadi suna ambaton sunan shadila suna kodata gami dayi mata kirari nan take wannan al amari yayi matukar burge kowa a wajan Abdul Aziz sani Madakin gini yace’ Hatta ni da nake baku wannan labari ban san sa adda na kama yin rangaji ba ina jin waninirin nishadi da farinciki a zuciyata’ 

.

Bayan mawakan sun gama koda amarya shadila saikuma suka kama wasa ango hailur shima suna yi masa kirari bisa irin gwagwarmayar da yasha a rayuwarsa tamkar a gabansu komai ya wanzu dolene abin ya burge mutum saboda irin hikimar da aka yi amfani da ita kuma dole ne mutum yaji ya kamu da tsananin tausayin wannan ango da amarya domin kuwa a takaice aka bayar da tarihin soyayyarsu da yadda aka rabasu da karfin tsiya hatta sarki hulbasu dasu yarima hulkas basu san sa adda suka kama zubar da hawaye ba marubucin littafin ma yace Nikaina a yanzu naji idanu na sun ciko da kwallah ana cikin yin wannan waka ne falon yayi tsit tamkar babu wani mahaluki daya mai numfashi a cikinsa sakamakon tsayuwar masu kida da wakar suma yan matan nan yan rawa suka kame kam.

.

A dai dai wannan lokaci ne kofar falon ta bude sai ga sadauki Ruhaisu ya shigo tare da wani dattijo wanda shima asalinsa dan kabilar su hailur ne

kai tsaye suka nufi inda hailur da shadila suke suka kamo hannayansu suka taho dasu izuwa tsakiyar falon suka daura musu sabon aure bisa al ada irin tasu faruwar hakan keda wuya sai yanayin sararin samaniya ya sauya nan take ya zama tamkar na damina hadari ya gangamo aka fara wata irin TSAWA DA WALKIYA mai tsananin ban tsoro. A dai dai lokacinne da wannan abu ya faru sarki shardas na cikin wani kurgurmin daji tare da bokansa abin dogaronsa sun yada zango a cikin wani kogon dutse suna barci amma ana tafka wannan tsawa sai sarki shardas ya farka firgigit A firgice zuciyarsa na daka da karfi, babu abinda ya fado masa a Rai face matarsa shadila, take yaji a jikinsa cewa lallai wani abune ya faru ga shadila domin wannan tsawa da walkiya da aka tafka ba na zahiri bane ishara ce, Aljanunsu na tsafi suka yi masa bisa abinda ya faru cikin gigita sarki shardas ya tashi bokansa daga barci ya dubeshi yace yakai abin dogarona kayi sani cewa lallai akwai wani abu ya sami matata shadila maza ka duba mini abinda ke faruwa.

.Tsatsuba Na 1 Complete Littattafin Yaki By Abdulaziz Sani M/Gini | https://www.aihausanovels.com.ng/2022/07/tsatsuba-na-1-littattafin-yaki.html

Koda jin wannan batu sai bokan ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya dubi sarki shardas cikin nutsuwa yace ya shugabana ai dama tun kafin mu baro gida idan baka manta ba na gaya maka cewa a cikin wannan tafiya da yarima hulkas zaiyi ne zai sami damar da zai iya cutar da kai to ka sani cewa duba maka wannan al amari ba zai haifar da komai ba face dakushe maka zuciya gami da karyar da ita akan babban aikin dake gabamu na nemo inda hular lamsara take ka sani cewa baka da wata mafita wacce tafi ka hanzarta mallakar wannan hula ta lamsara kafin makiyanka su rigaka lallai kana da babbar dama ta samun haka tunda ka rigasu fitowa neman nata amma ko yaya ka darsa batun soyayyarka akan shadila a cikin ranka to lallai zaka rasa nasara.

.

Koda bokan yazo nan a zancensa sai hankalin sarki shardas ya dugunzum ainun fiye da ko yaushe ya dubeshi a fusace sa adda zuciyarsa ke tafarfasa yace ka gaya mini cewa mun fito ne neman wani Aljani wai shi arwasul masadul kuma tunda muka baro gida muke ta keta dazuzzuka birane da kauyuka barkatai amma ko alamun wannan aljani bamu gani ba bamu san yaushe zamu hadu da shi ba, kuma bamu san a inda zamu  ganshi ba anya kuwa baka ganin cewa wahalar banza muke yi ? 

.

Koda sarki shardas yazo nana a zancensa sai bokan ransa ya baci yace ashe akwai ranar da zaka yi kokwanto akan abinda zan gaya maka shin ka manta ne cewa nine na tsareka na baka dukkan kariya daga sharrin dukkan makiyanka tun kafin ka hau karagar mulki shin ka manta cewa zuri ar gidanmu sun shafe sama da shekaru dari suna bauta a gidanku cikin amince da kauna ??

.

Babu yadda za ayi na bata yaudararka ko na gaya maka karya dolene ka kasance mai hakuri gami da juriya komai dadewar shekarun da zamu yi muna yin wannan tafiya kafin mu hadu da aljanu Arwasul masadul koda kuwa sai mun tsofe tukuf fatanmu dai shine nasara da sa’a.

.

Koda gama fadin hakan sai bokan ya koma ya kwanta yaja bargonsa ya lullube jikinsa gaba daya saboda hunturun sanyin dake kadawa a cikin dajin

yaci gaba da barci abinsa tamkar a cikin dakin matarsa yake a lokacinn da kuune baya jin sautin komai face na manyan dabbobin daji ababan tsoro shi kuwa sarki shardas saboda zuciyarsa na suya don tsananin fushi idanunsa sun bushe babu alamar jin barci kuma ko kadan baya jin uban sanyin da ke kadawa haka dai ya zauna yana ta tunanin zuci gami da wasu wasi a ransa bisa yin abinda yake ganin cewa shine zai fishsheshi wata zuciyar tace dashi : wai shin yama za ayi ace duk irin wannan masifaffen karfin damtsen nawa da kuma karfin sihirin tsafi ace ba zan iya kashe wannan yaro hulkas ba ?

.Tsatsuba Na 2 Littattafin Yaki Na Abdulaziz Sani M/gini | https://www.aihausanovels.com.ng/2022/07/tsatsuba-na-2-littattafin-yaki-na.html

Wai shin ma menene dalilin da yasa duk abin da wannan bokan yazo mini

dashi sai na amince shin bokaye basa yin karya ko kuskure ne a bincikensu da furucinsu,?

.

Aljanu ne fa suke sanar dasu komai kuma su kansu aljanun suna shirya karya kuma suna yin son zuciyarsu kamata yayi na yi watsi da shawarar wannan boka akan batun neman wannan hula ta lamsara kawai na juya da baya na tafi izuwa birnin hulbasu naje na kama yarima hulkas a gaban mahaifiyar tasa shadila nayi masa yankan rago duk da cewa ina kaunarsa !!

.

Koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubo masa kuma wata zuciyar tasa ta daka masa tsawa tace shin baka da hankali ne yanzu kana nufin kace zaka yanka yaron da ka raina da hannunka wanda ka kaunaceshi tamkar dan cikinka, idan har zaka iya aikata hakan to tabbas dan da ka haifa da kanka ma zaka iya kasheshi !!

.

Koda gama aiyana hakan sai hawaye ya zubo wa sarki shardas a karo na biyu ya kishingida akan shimfidarsa ya lumshe idanunsa domin yayi barci amma sai barcin ya gagara.

.

A takaice dai yadda yaga rana haka yaga dare da asubar fari boka nata faman shara barci abinsa sai sarki shardas yaji yana sha awar ya shiga daji yayi farauta ko ya harbo wani tsuntsu ko kuma ya samo musu dabbar da zasu yi kalaci da ita saboda ya gaji da cin irin abincinsu na guzuri wanda suka tanada, ba tare dasarki shardas ya tashi bokansa daga barcinsa ba sai ya mike tsaye ya dauki damararsa ya daura ya gyara zaman takobinsa a cikin kufenta sannan ya dauko kuttun kibiyoyinsa ya sakashi a kafadarsa ya rike sandar bakan a hannunsa yana gama wannan shiri sai ya fice daga cikin wannan kogon dutse da suka kwana yana sanda don kada ma boka labarusa ya farka daga barcin ya hanashi fita wannan farauta, nan da nan sarki shardas ya kutsa cikin dajin yayi nisa cikinsa yana ta dube dube leke leke da neme neme sama da kasa gabas da yamma kudu da arewa a cikin kowanne sako kwari da tudu har  cikin ramuka sarkakiya da duhuwoyi amma ko gafiya bai gani ba bare ya sami abin farauta har tsawon sa’a guda

Al amarin da yayi matukar bashi mamaki kenan nan har tsoro ya dan darsu a cikin zuciyarsa yace ya za ayi ace duk girman wannan daji da kuma tarin ni’imar dake cikinsa amma ace babu dabbobi dake rayuwa a cikinsa?

.Tsatsuba Na 2 Littattafin Yaki Na Abdulaziz Sani M/gini | https://www.aihausanovels.com.ng/2022/07/tsatsuba-na-2-littattafin-yaki-na.html

Ko dai wata annoba ce ta kashesu gaba dayansu a lokaci guda ? Idan hakane kuwa ai yakamata ace annobar ta bar gawar koda daya ne daga cikinsu, koda sarki shardas ya gama aiyana hakan a cikin zuciyarsa sai yaji wata irin iska mai karfin gaske ta giftashi ta samansa, cikin hanzari ya daga kansa sama domin yaga ko menene ya gifta din kawai sai yaga ashe wata jibgegiyar halitta ce mai manyan fuka fuki amma saboda tsananin karfin gudunta ya kasa gane ko dabba ce ko aljan ko kuma tsuntsu domin kafin giftawar ido halittar ta bace a cikin sararin samaniya cikin matukar karfin hali sarki shardas ya yunkura da nufin ya tashi sama da karfin sihirinsa na tsafi amma sai yaji ya kasa tashi saman al amarin da yai matukar razanashi kenan kuma yai matukar bashi mamaki saboda wannan shine karo na farko a rayuwarsa da ya taba jarraba amfani da karfin sihirinsa na tsafi yaki yayi tasiri amma da yake shi sarki shardas mutun ne wanda bai san tsoro ba kuma yana da dakakkiyar zuciya sai kawai ya falfala da masifaffen gudu yabi bangaren da wannan jibgegiyar halitta tabi, sai da ya shafe sa a guda yana gudu yana daga kansa sama ko zai hango halittar kuma yana duba kasa ko zai ga alamun sawunta idan ta sauko kasan amma bai gani ba, kwatsam yana cikin falfala wannan azababben gudu da dube duben halittar nan ko sawunta kawai sai ganin wani katon kogi yayi a gabansa saura kiris ma ya fada cikinsa yayi turjiyar bazata ba a bakin gabarsa cikin tsananin sauri da zafin nama, tsayuwarsa a gaban kogin keda wuya sai yaga tsakiyar kogin ya kumburo sama wani abu mai girman gaske na shirin fitowa daga karkashinsa aikuwa kafin yayi wani yunkuri sai ga wannan jibgegiyar halittar ta taso izuwa saman kogin ta dora kafafunta guda hudu a samansa tamkar kasa ta taka ita dai wannan halitta mutum bai isa yace ga abin da take kama dashi ba ita ba tsuntsuwa ba, ita ba dabba ba, kuma ba aljana ba tana da tsananin muni gami da matukar kwarjini da ban tsoro kawai sai halittar ta juyo da kanta ta kurawa sarki shardas idanu ba tare da tayi wani yunkuri ba

koda ganin hakan sai sarki shardas ya durfafi halittar  har sai da yaje dab

da ita sannan ya dubeta ba tare da nuna alamun wani tsoro ba yace yake wannan halitta waye kai kuma menene dalilin da yasa kaine kadai halittar dake rayuwa a cikin wannan daji mai tarin ni’imomi haka ? 

.

Koda jin wannan tambaya sai halittar ta bushe da mahaukaciyar dariya mai kama da saukar kwarankwatsa tayi ta dariyar kamar ba zata daina ba lokaci guda kuma sai ta turbune fuskarta ta dubi sarki shardas cikin nutsuwa tace

yakai wannan hatsabibin bil adama kayi sani cewa babu wata dabba ko wani kwaro ko mutum ko aljan da ya isa ya shigo cikin wannan daji har ya rayu na tsawon dakiku dari face ya kasance mashahurin matsafi abin kwatance don haka nayi maka jinjina kai da bokanka labarusa kafin halittar ya gama rufe bakinsa tuni sarki shardas ya tari numfashinsa yana mai cewa wane ne kai

kuma menene dalilin da yasa wannan daji ya zama daban da kowanne daji dake nahiyar nan.

.

Koda jin wannan tambayoyi sai halittar ta sake bushewa da dariya akaro na biyu sannan tace ni kaina bansan kaina ba tunda ban san asalina ba amma dai na san na kawo i yanzu babu uwa babu uba don haka ko suna bani dashi, koda jin wannan batu sai sarki shardas ya fusata, sannan na fusata ya dubi halittar cikin fishi tare da daka mata tsawa yace kada ka raina mini hankali mana ai ko a ina ka rayu zaka iya sakawa kanka suna ko kuma a saka maka

tunda ba zai taba yiwuwa ba ace ka ray a inda babu aljan ko mutum.

.

Koda jin haka sai halittar tayi murmushi tace yakai wannan sarki kayi sani cewa hakuri na daya daga cikin tafarkin dake kai mutum izuwa ga nasara bisa abinda yasa a gabansa kai kuwa baka da hakurin sarki shardas najin haka sai ya kara fusata da fishi mai tsanani ya zare takobinsa ya dubi halittar cikin fushi yace  tabbas bani da hakuri kuma babu wani mahaluki wanda ya taba gaya mini magana haka cikin gadara kamarka haka kuma babu wani abu da na taba sashi a gabana ba tare da nayi nasara ba saboda haka kaima sai na jarraba sa a ta akanka domin na san ko kai waye ne.

.Tsatsuba Na 2 Littattafin Yaki Na Abdulaziz Sani M/gini | https://www.aihausanovels.com.ng/2022/07/tsatsuba-na-2-littattafin-yaki-na.html

Koda gama fadin hakan sai sarki shardas ya daka tsalle sama tamkar an harboshi daga cikin baka yayi sama izuwa kan halittar yakai mata wawan sara a wuya cikin bakin zafin nama halittar ta sunkuya takobin sarki shardas ta sari iska kafin sarki shardas yayi wani yunkuri tuni halittar ta maka masa jelarta akan kirjinsa saboda karfin dukan sai da sarki shardas yayi baya a sama tamkar an janyeshi da majajjawa yaje ya gwara bayansa a jikin wata katuwar bishiya sannan ya fado kasa tim a cikin matukar galabaice yana kumallon jini ta baki da Hanci kuma ya kasa mikewa tsaye koda halittar taga

ta sami wannan nasara sai ta bushe da dariya tare da bude fuka fukanta tayi sama tana mai cewa ya kai wannan sarki hakika ka cika wahalalle kuma asararre domin girman kanka da rashin kunyar ba zasu taba kaika ga samun nasara akan abinda ka sa a gabanka ba ina yi maka bushara da cewa kayi babbar asarar damar da ba zaka kara samun kamarta ba kafin sarki shardas ya daga kansa sama domin yaga bangaren da halittar tayi  a sama tuni halittar ta bace bat a cikin gajimare tamkar bata taba wanzuwa ba…….

.

SHIN WANNAN WACCE IRIN HALITTA CE

.

SHIN WACCE IRIN DAMA SARKI SHARDAS YAYI ASARA WADDA BA ZAI SAKE SAMUN KAMARTABA?

.

YAUSHE YARIMA HULKAS ZAI SAMI NASARAR MALLAKAR HULAR LAMSARA HAR YA GA BAYAN MAKIYINSA DA YA DAUKA A MATSAYIN MASOYINSA WATO SARKI SHARDAS ?

.

INA LABARIN SU SARKI HULBASU DA HAILUR DA SABUWAR AMARYARSA SHADILA DA AKA SAKE DAURA MUSU AURE A BIRNIN SARKI HULBASU ?

.

SHIN SU SARKI HULBASU SUNA SAMUN NASARAR HALLAKAR DA DAKARUN DA SUKA YOWA SHADILA RAKIYA BA TARE DA SUN BAR KODA DAYANSU YA TSIRA BA BALLE YAJE YA SANAR DA SARKI SHARDAS ?

.

WANNE IRIN AZABABBEN YAKI ZA AYI A GABA ?

.

SHIN YARIMA HULKAS YANA FADAWA TARKON SOYAYYA WADDA HAR ZATA ZAMO SANADIN RASA RAYUWARSA ?

.

TSAKANIN SARKI SHARDAS DA YARIMA HULKAS WAYE ZAI SAMI NASARAR MALLAKAR HULAR LAMSARA ?

.

SHIN ABUBAKAR SALEH ALQUYRAEMEY ZAI SAMU DAMAR KAMMALA MUKU POSTING DIN WANNAN LITTATTAFIN KUWA ?

.

Marubucin Yace Mu Hadu A Littafi Na Gaba Wato Littafi Na 8 Don Jin Cigaban Wannan Kayataccen Kasaitaccen Labari sai ku dannan bulun rubutun nan.

  

Back to top button