Uncategorized

Tsatsuba Book 5 Littafin Yaki Na Abdulaziz Sani M/Gini

 

Ku Taba Nan Domin Karanta Littafin Tsatsuba Na Ɗaya Wannan Abdulaziz Sani M/Gini Ya Rubuta.

TSATSUBA

Littafi Na Biyar (5)

Part A.

Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

08138873799 For More Littattafan Yaƙi 

.

Lokacin da jaruma siyama da sadauki darkus suka bingire kasa suna fitar da numfarfashi kamar ransu zai fita a dai dai wannan lokaci ne aka buga gangar tsayar da yaki sannan alkalin gasa ya rugo izuwa cikin tsakiyar fili ya fuskanci jama a yace yaku jama a kuyi sani cewa wannan gumurzu tsakanin sadauki darkus da jaruma siyama babu zakara a tsakaninsu wato sunyi MUTUWAR KASKO don haka zasu sake haduwa a zagayen karshe na wannan wasa wanda za ayi rana i ta yau don haka yanzu zamu kirawo jarumai na gaba domin aci gaba da wannan gasa, gama fadin hakan keda wuya sai aka dauke sadauki Darkus da jaruma siyama daga cikin filin aka kaisu can gefe daya maimakon a shigar dasu cikin wannan asibiti wanda aka tanada domin yiwa jaruman gasar magani, dalilin da yasa kuwa ba a shigar da su cikin wannan asibiti ba shine babu mai wani babban rauni a cikinsu akan hancinsu da bakunansu ne kadai jini ke diga lokacin da jaruma siyama ta dawo cikin haiyacinta sai ta dubi inda su sarki hulbasu ke zaune tana mai mamakin dalilin da ya hana mahaifinta zuwa inda take a lokacin da hankalinta ya gushe bayan an tsayar da wasansu, bisa mamaki sai siyama taga babu mahaifinta a inda yake zaune amma kuma sai taga shardila ta kura mata idanu ko kiftawa batayi duk da cewa kuwa ta rufe fuskarta da bakin kyalle idanunta kadai ake gani nan fa hankalin siyama ya dugunzuma ainun in ba don ma ta hango mahaifiyarta ba ta taso daga inda take zaune ta taho wajenta ba da mikewa zata yi ta bazama mahaifin nata Hailur, da isowar zalima wato mahaifiyar siyama sai ta rungumete cikin murna tana mai yi mata jinjina bisa bajintar da ta nuna a wannan wasa da tayi.

.

A dai dai wannan lokaci ne wani likita yazo garesu da nufin zai duba tafiyar siyama amma sai zalina ta tsaidashi tace babu wani likita da zai duba lafiyar yata face ni don haka mun gode bama bukatar taimakonka, koda gama fadin hakan sai zalina ta bude wani kullin tsumma dake hannunta ta dauko wani ruwan magani a cikin wata yar doguwar kwalba ta mikawa siyama siyama ta karba ta bude murfin kwalbar ta sa abakinta tasha mukurwa biyu kacal sannan ta rufe kwalbar ta mai dawa zalina.

.

Faruwar hakan keda wuya sai jinin dake yoyo a hannun siyama da bakinta ya tsaya cak kamar bai taba diga ba kuma nan take taji duk gajiyar dake jikinta ta dauke fuskarta ce kawai da idanunta a dan kumbure sakamakon naushin da darkus ya yi mata a can gefe daya kuma likita ne ke duba sadauki darkus ana sa masa magani a kan hancinsa don tsaida jinin dake yoyo koda darkus ya dawo cikin hayyacinsa ya waiga bayansa yayi arba da jaruma siyama sai ya daka mata harara yaji ya tsaneta fiye da komai a rayuwarsa, nan take zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone bisa ganin cewa yarinya karama ta gagareshi a filin gasa, nan fa ya fara tunanin cewa ta kowanne hali sai ya kaita kas a zagaye na biyu da zasu hadu wato a wasan karshe da za ayi na gasar idan rana ta zagayo kuma babu abinda zai yi ya dawo da kimarsa da mutuncinsa a birnin face ya kashe wannan karamar yarinya siyama ya zamana cewa ta mutu murus har lahira a cikin filin gasa.

.

Koda mai gabatarwa yazo tsakiyar fili yaci gaba da jawabi sannan ya kirawo sunayan jarumai na gaba wadanda zasuyi fafata a wannan gasa.

.

A dai dai wannan lokaci ne sarki hulbasu ya dubi Hailur yace yakai abokina hakika ka baiwa yar ka horon yaki na ban al ajabi domin ta bani mamaki matuka kuma akwai alamun cewa zata iya lashe wannan gasa amma ka sani cewa lashe wannan gasa ba abune mai sauki ba saboda babu irin abinda jaruman gasar nan basayi don ganin sukai gaci, suna yin tsafi tuggu da makirci iri iri don ganin sun sami nasara ta kowacce hanya don haka dole ne kasa ido akan yarka domin daga yanzu rayuwarta na cikin hadari kada ka tafi izuwa gida kai tsaye daganan ina son ku biyoni izuwa cikin gidan sarautata domin ku dauke hankalin makiya dolene ku sauya gidan zama kuma nima zan baku shawarwari da taimako.

.

Wai shin ma kasan kuwa irin ladan da yarka zata samu idan ta lashe wannan gasa ta jarumtaka ? Koda jin wannan tambaya sai hailur ya sunkui da kansa kas saboda yaga shardila ta kalleshi don kada taga kwayar idanunsa ta shaidashi sai yaki yarda ya dago kansa sa ar ma da yayi ko kadan bata jin abin da suke tattaunawa shi da sarki kasancewar suna magana ne cikin kus kus yadda babu mai iya jin abinda suke tattaunawa

.

Hailur ya risina cikin girmamawa yace yakai abokina wane irin lada za a baiwa yata idan ta lashe wannan gasa sarki hulbasu yayi murmushi sannan yace da farko dai za a bata babbar gona guda daya daga cikin manyan gonakan garin nan gami da dinare dubu dari bakwai sannan kuma zan bata mukamin shugabar dakarun dake tsaron lafiyata muddin zata iya rantsuwa bisa rike amanata da kuma siyar da rayuwarta don kare tawa idan har ta sami wannan mukami zata rinka samun albashi mafi tsoka a kan duk albashin da ake biyan dakaruna daga wannan matsayi kuma zata iya zama sarkin yakin birnin nan gaba daya bayan ta fuskanci wadansu jarrabobi da matakai.

.

Duk mutumin da ya sami wannan dama wacce yarka ta samu dole ne ya fuskanci makiya da yawa daga cikin manyan fadawana domin sun san cewa zai zone yafi su matsayi da arziki, lokacin da sarki hulbasu yazo nan a zancensa sai hankalin hailur ya dugunzuma ainun take yaji yayi nadamar sanya siyama a cikin wannan gasa saboda dalilai guda biyu dalili na farko shine yanzu ya sanya rayuwar siyama a cikin hadari domin zata tara abokan gaba wadanda za su rinka farautar rayuwarta kamar yadda mai jin kishirwa ke neman ruwan sha, abu na biyu kuma idan ta tsallake kowanne hadari da dukkan matakai da zata nisanta dashi inma bai yi sa a ba ya rasata gaba daya kamar yadda ya rasa matarsa shardila wacce ya tabbatar da cewar tana dauke da juna biyu a lokacin da suka rabu.

.

A yanzu da hailur yaga yarima hulkas sai ya fara tunanin ko dansa ne wannan yaro ko kuma dan sarki shardas ne

tabbas babu mai bashi amsar wannan tambaya face shardila da kanta kuma yana shakkar ya sadu da ita domin idan wani daga cikin dakarunta ya gansu komai ya dagule kenan domin sai sarki shardas ya samu labarin cewa yana raye to ba mashi ba matarsa zalima da yarsa siyama ma rayuwarsu ta shiga hadarin da shiba zai iya kare suba hailur ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa yace ta yaya zan iya saduwa da shardila a sirrance ba tare da kowa ya ganni ba ko yaji babu wanda zai iya taimaka mini na iya ganawa da shadila asirrance face sarki hulbasu, hailur baya son sarki hulbasu ya san cewa shine ainihin abokin gabar sarki shardas wanda tuni aka dauka cewa ya mutu tun shekaru bakwai baya, hailu na cikin wannan tunani ne yaji an ruguntsume da wani masifaffen azababben yaki a tsakiyar filin gasa koda ya daga kansa yayi arba da jaruman biyu dake fafatawa a filin gasar sai ya cika da mamaki, ba komai ne ya sashi wannan mamaki ba face ganin cewar dayansu amintaccen yaronsa ne sadauki Ruhaisu jarumin da ya aminta dashi dari bisa dari a cikin dukkanin yaransa lokacin a yake kan matsayin shugaban kabilarsu.

.

Koda hailur yayi arba da ruhaisu sai farin ciki ya lullubeshi domin indai ruhaisu na tare dashi zai iya nemo masa ire iren sauran jama arsu da sukayi saura a raye domin su sake tayar da kabilarsu kuma su taimaka

masa wajan bashi kariya dashi da iyalansa jarumin da yake karawa da ruhaisu kuwa wani narkeken katone wanda ya ninkashi girma da tsayi sau uku kuma a zahiri ma yafi shi surar sdaukantakada jarumtaka ana kiransa da suna Jamar, amma suna fara artabu sai jamar ya raina kansa domin ruhaisu yafishi zafin nama da iya yaki nan da nan ya rikitashi kuma ya kuntatashi sai gashi Jamar yana ta ja da baya kuma yana ta kokarin kare kansa baya ma iya kai hari koda ruhaisu ya tabbatar da cewar yafi jamar iya yaki da fadan hannu sai kafa sai ya shammaceshi ya daka tsalle sama ya doki habarsa da guiwarsa ta dama saboda karfin dukan sai da jamar yayi sama a lokacin da jini yai tsartuwa daga cikin bakinsa yana saman kafin ya fado kasa sai ruhaisu ya kara dukan kirjinsa da karfin gaske kawai saiji akayi jamar ya fado kasa tim kamar giwa ta fadi kuma ya baje kas a sume ko kyakkyawan motsi ba yayi.

.

Koda ganin haka sai filin gasar ya rude da shewa aka kama yiwa ruhaisu tafi da jinjina ba don komai ba sai don saboda shine jarumi na farko da ya fara lashe wasansa na farko a cikin kankanin lokaci da fara gasa tunda ko rabin sa a ba ayi ana gumurzun ba ya sami wannan nasara ana cikin wannan yanayi ne hailur ya dubi sarki hulbasu yace hakika wannan jarumi ya burgeni matuka zan so na gana dashi, koda jin haka sai

sarki hulbasu ya yi murmushi yace ai wannan mai saukine zan shirya duk yadda zaka gana dashi nan ba da dadewa ba yanzu ina so kaje ka ruko yarka da matarka ka shigo cikin tawagata domin mu shiga cikin gidan sarautata tare

.

Koda jin haka sai hailur ya dubi sarki hulbasu cikin alamun damuwa yace bana son na shiga cikin filin nan ranka ya dade ka taimaka min ka aika wani daga cikin hadimanka ya taho da siyama da zalina koda jin wannan batu sai sarki hulbasu yayi murmushi yace shikenan an gama, nan take sarki ya kira wani hadiminsa ya turashi yaje ya taho da jaruma siyama da mahaifiyarta suka shigo cikin tawagar sarki hulbasu.

.

Koda hailu ya yunkura zai mike tsaye daga kan kujerar da yake zaune sai santsi ya kwashe shi ya zame zai fadi kasa a lokacinne rawanin da hailur ya rufe fuskarsa dashi ya zame kafin ya mayar da rawanin kan fuskarsa shadila ta yi arba dashi domin ya hada idanu da ita cikin kaduwa yai sauri ya mayar da rawanin ita kuwa shadila sai ta kame a inda take tsaye saboda tsananin mamaki da kaduwa da murna bata san sa adda hawaye ya fara zubo mata ba…

.

Duk da cewa itama ta rufe idanunta da bakin kyalle sai da sarki hulbasu ya lura da halin da take ciki amma sai ya basar yayi kamar bai fahimci komai ba ita kuwa luzuraina sam bata lura da duk abinda ke faruwa ba yarima hulkas ne ya lura da irin satar kallon da mahaifiyarsa ke yiwa abul siyama kuma yaga sa adda hawaye ya zubo mata, nan take hankalinsa ya dugunzuma ainun ya rasa dalilin faruwar wannan lamari don haka sai zuciyarsa ta kama zargi da wasu wasi amma ya kasa gane abin ma da yake zargi da wasi wasin a kansa haka dai sarki da mukarrabansa suka mimmike tsaye a cikin filin gasar aka kawo musu dawakansu suka hau sannan suka fice daga cikin filin gasar dakaru na zagaye dasu gaba da baya da kuma tsakiyarsu.

.

Ashe tun sa adda aka gama fafatawa tsakanin sadauki darkus da jaruma siyama tuni sadauki darkus ya kebe da wadansu zakwakuran yaransa ya basu umarni akan cewa da zarar sun ga jaruma siyama da iyayanta sun fito daga cikin filin gasar a kashe su a sirrance ba tare da kowa ya gane abinda ya kashe sun ba baya ga wannan mugun abu da sadauki darkus ya shirya ashe shima sarkin yakin sarki hulbasu ma ya tura wadansu yaran nasa ma a sirrance sun je can hanyar bayan gari sun labe rike da da kwari da baka sun dana kawai jira suke suga giftawar jaruma siyama da iyayenta akan hanyarsu ta komawa gida su sakar musu harbi su kashesu lokacin da shi sarkin yaki wanda ake kira suna RINZALU da kuma sadauki darkus suka ga cewa siyama tare da iyayanta sun shiga cika da mamaki kuma hankalinsu ya tashi saboda sun san cewa lallai dukkan shirinsu ya watse, nan take sarkin yaki rinzalu ya nufi tawagar ta sarki da nufin ya shiga cikinsu amma sai yaga dakarun sarki na musamman masu tsaron lafiyarsa sun shiga gabansa sun hanashi shiga cikin tawagar. Al amarin da yai matukai baiwa sarkin yaki rinzalu mamaki kenan kuma ransa ya baci saboda ba a taba hanashi shiga cikin tawagar sarki ba sai yau nan take ya fara tunani a cikin zuciyarsa yace wai shin wane irin matsayi ne da jaruma siyama da iyayanta a wajan sarki hulbasu haka har da yake kare rayuwarsu wai shin ma yaushe ya san su har da suka sami matsayi a wajansa kamar haka amsoshin da rinzalu ya kasa baiwa

kansa kenan haka dai ya hakura yana ji yana gani ya juya da baya yaje ya shiga cikin sauran yan uwansa.

.

Ayi hakuri mu kwana anan sai kuma Allah Ya kaimu gobe da yardar Allah, kafin nan dai ni ɗin ne Abubakar Saleh AlQuyraemey.

TSATSUBA

Littafi Na Biyar (5)

Part C.

Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

08138873799 For More Littattafan Yaƙi 

.

.

Lokacin da aka iso cikin gidan sarautar sarki Hulbasu sai ya kama hannun hailur ya jashi har izuwa cikin kuryar turakarsa suka zauna aka kawo musu abinci da abinsha shi kansa hailur yayi mamakin yadda sarki hulbasu ya aminta dashi haka cikin kankanin lokaci alhalin sau daya rak suka taba ganin junansu

ma wannan haduwar ta yau itace ta biyu amma ya aminta dashi kamar haka Hailur yace a cikin ransa wata kila saboda abin karamcin da nayi masa ne a daji shi yasa ya saka mini da irin wannan tarba, bayan an kawo musu wannan abinci da abin sha na alfarma sai sarki yayiwa hailur tayi amma sai hailr ya kasa cin abincin ya kura masa idanu kawai a lokacin da tuni Sarki ya gabatar da wajan loma biyu yana shirin kai ta uku kenan sai ya lura da cewa hailur baya cin abincin kuma yayi shiru fuskarsa na nuna alamun tunani.

.

Koda ganin haka sai sarki Hulbasu yai murmushi a gareshi yace kwantar da hankalinka ya kai abokina kayi sani cewa a halin yanzu matarka da yarka jaruma siyama suna can tare da matata da kuma gimbiya shadila matar sarki shardas cikin aminci suna cin irin wannan abinci dake gabanmu koda jin haka sai hailur ya saki ajiyar zuciya tare da jinjina kai alamar gamsuwa da furucin da sarki Hulbasu yayi masa nan ya saki jikinsa ya fara cin abincin, har suka ci suka koshi dayansu bai kara cewa uffan ba sai bayan sun nutsu sannan sarki ya dubi hailur yace yakai abokina kayi sani cewa hankali shine yake gani amma ba idanu ba tabbas akwai boyayyen al amari a tare dakai wanda kake boye mini amma ina so ka sani cewa ba a boyewa abokin kuka mutuwa yakamata ka gane cewa shi masoyi na kwarai har abada masoyi ne shi kuwa masoyi zaka sameshi mai rike amana da kare masoyinsa da sallama rayuwarsa a gareshi a koda yaushe komai RINTSI DA TSANANI, na rantse maka da girman iyayena da kakannina ba zan taba cin amanarka bakona juya maka baya musamman idan kayi la akari da irin taimakon da kayi mini a cikin daji wanda har na mutu ba zan manta dashiba, ina son ka saki jikinka da zuciyarka ka sanar dani duk abin dake faruwa shin menene tsakaninka da shadila matar sarki shardas?

.

Na lura da duk abin da ya faru dazu a tsakanin kai da ita a filin GASAR JARUMTAKA, naga hawaye na zuba a cikin idanunta sa adda rawanin fuskarka ya kwaye tayi arba dakai, shin kun san juna ne dama ?

.

Ka sani cewa ko ka sanar dani wannan sirri ko ka ki tuni yanzu rayuwarka da ta iyalanka tana hannuna domin inda ban shigo daku nan ba cikin gidan sarautata tuni kun dade da zama gawa, lokacin da sarki yazo nan a jawabinsa sai hailur yaja dogon numfashi ya ajiye sannan ya dubeshi a lokacin da idanunsa suka ciko da kwallah yace yakai wannan sarki mai Adalci kayi sani cewa gimbiya shadila matatace a baya kafin sarki shardas ya mallaketa, koda jin wannan batu sai idanun sarki hulbasu suka zazzaro tsoro ya kamashi kuma jikinsa ya kama kyarma shi hailur sai yaci gaba da bayani yana mai cewa a ranar angwancina da ita ne sarki shardas da dakarunsa.suka kawo ma kabilarmu harin Mamayar bazato sukayi ta ragargazar dakarunmu kuma suka kame matayanmu da yawa a matsayin bayi ni ne kadai jarumin da na gagaresu har ma nayi gumurzu da sarki shardas amma a karshe ya jefani kasa daga saman wani tsauni mai tsananin tsawon tsiya sanadiyar da na rasa hannuna guda daya na hagu kenan kuma kafata guda daya itama ta sami wannan nakasa ta shagidewa, nidai kawai farkawa nayi na tsinci kaina a cikin wata bukka a tsakiyar daji koda na yunkura domin na mike zaune sai naji na kasa domin gaba daya jikina babu kuzari, yayin da na sake yunkurawa domin na yaye mayafin da aka lullube ni dashi akan shimfidar da nake kwance sai naji babu hannuna guda daya na dama, nan take na kwarara wani uban firgitaccen ihu cikin tsananin bakin ciki da razana.

.

Faruwar hakan keda wuya sai ga wani dattijo tare da wata kyakkyawar budurwa sun shigo izuwa cikin bukkar da shigowarsu sai suka durkusa a gabana dattijon ya dubeni a dimauce yace yaro me ya faru gareka ka tsandara wannan uban ihu haka shin wani mugun mafarki kayi ko kuwa wani mugun abune ka gani.

.

Sa adda naji wannan tambaya sai hawaye ya zube mini na dubi dattijon cikin nutsuwa nace me yasa kuka ceci rayuwata baku barni na mutu ba yanzu menene amfanin rayuwata a doron kasa tunda na rasa komai da kowa nawa kuma na rasa lafiyata ina mai rokonku daku gaggauta kasheni yanzu domin na huta da bakin cikin dake nukurkusar zuciyata yayin da na zo nana zancena sai dattijon da wannan kyakkyawar budurwa suka kamu da tsananin tausayina.

.

Dattijon ya kalleni yace samari hakika kana da nisan kwana a duniya domin a tarihin wannan tsauni wanda ka fado daga kansa fiye da shekaru dari bakwai baya ba a taba samun mahalukin daya fado daga kansa ba ya rayu sai kai muma nan da ka ganmu muna zaune a cikin wannan daji mun fitone daga cikin wata babbar kabila da ake kira BANU IKHLAS. kamar yadda sarki shardas ya karar da kabilarka haka muma ya karar da tamu kabilar ni da wannan ya tawa ce zalina kadai muka tsira da rayuwarmu alokacin.

.

Sa adda ya kawo farmaki zuwa kauyanmu nida ita

bama nan muna cikin daji muna yin farauta bayan mun dawo mun iske iyayanmu da yan uwanmu da duk danginmu sun zama gawa sai muka kama kuka mutum daya kacal muka samu da sauran numfashi a jikinsa shine ya gaya mana cewa sarki shardas ne da kansa shida dakarunsa suka zo sukayi mana wannan mummunar barna da dai muka ga cewa ba zamu iya daukar fansa a kan sarki shardas ba sai muka hada kayanmu muka sake komawa cikin daji muka ci gaba da farauta, amma bamu zauna a waje daya ba sai muka ci gaba da tafiya muna ketawa ta gefen garuruwa da kauyuka amma bama zama a inda babu cibiyar ruwa. Tabbas ruwan dake kasan wannan tsauni da ka fado ne ya kawoka nan domin daga can zuwa nan tafiya ce ta kwana saba in da hudu, sa dda mahaifin zalina yazo nan a zancensa sai na cika da tsananin mamaki kuma na sake kamuwa da bakin ciki mara misaltuwa don haka ban san sa adda na fashe da kuka ba ina mai cewa ina ma na mutu ban rayu ba sakamakon fadowa daga kan wannan tsauni tun da yanzu bani da kowa kuma bani da komai a wannan daji, koda jin wannan batu sai tausayina ya kama zalina da mahaifinta zalina ta dubeni tace yakai wannan jarumi ma aboci kwarjini da jarumtaka ka yi sani cewa yadda baka da komai da kowa a wannan duniya haka muma muka kasance ni da mahaifina amma tunda yanzu kaddara ta hadamu mun sameka ka samemu, zaifi kyau mu rungumi kaddara bisa yadda ta samemu mu ci gaba da rayuwa ko don nan gaba mu ga yadda karshen mulkin sarki shardas zai kasance koda kuwa mu bazamu iya ganin karshen nasa ba, ka sani cewa babu wani abu madawwami kuma komai nisan jifa kasa za fado, don haka duk abinda sarki shardas ke takama dashi watarana sai ya fado kasa tunda idan ba mutuwa akwai tsufa akwai lokacin da yanaji yana gani ba zai iya yin zaluncin da yake yi ba yanzu koda mu bamu ga wannan lokaci ba ina son ire irenmu sugani.

.

Lokacin da zalina tazo nan a zancenta sai jikina dana mahaifinta yayi sanyi saboda mun san cewa duk abinda ta fada gaskiya ne, tun daga wannan rana zalina da mahaifinta sukaci gaba da jinyata har na sami lafiya ya zamana cewa ina iya mikewa tsaye na dogara sanda na bisu izuwa daji don yin farauta amma fa duk sa adda na dubi hannuna na hagu naga babu shi kuma naga kafata ta dama ta shagude sai na fashe da matsanancin kuka na bakinciki domin gani nake kamar rayuwata bata da wani sauran amfani duk sa adda na fara wannan kuka sai zalina da mahaifinta sunyi da gaske sannan suke rarrashina na dawo cikin hayyacina….

TSATSUBA

Littafi Na Uku (5)

Part C.

Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

08138873799 For More Littattafan Yaƙi 

.

Duk sa adda na fara wannan kuka sai zalina da mahaifinta sunyi da gaske sannan suke rarrashina na dawo cikin hayyacina wani abin mamaki wanda ya daure min kai shine duk da cewar na rasa hannu daya da kafa daya ko kadan ban rasa karfin damtse na ba da kuma iya yakina don haka duk sa adda muka shiga daji farauta duk muguwar dabbar da ta zo gabanmu take nake gamawa da ita, komai yawan gungun yan fashi kuwa idan mukayi gamo dasu ni kadai nake tarwatsa su, amma zalina da mahaifinta suna taimaka mini saboda sun kware ainun a iya harba kibiya. A lokaci guda kowannansu na iya harba kibiyoyi bakwai sai dai kaga maza na zubewa kasa yayinda tsinin kibiyoyinsu suke ratsa kirazansu, A kwana a tashi sai na sami wata bakwai tare da su zalina ya zamana cewa na shaku dasu ainun musamman zalina wacce komai tare muke yi shimfidar barci kawai muke rabawa.  A hakane na fuskanci cewa soyayya ta shiga tsakaninmu amma dana tuna cewa ni fa yanzu masaki ne bani da hannu daya da kafa daya sai na ga cewa idan na nemi soyayyar zalina na cutar da ita.  kuma idan na tuna cewa na rasa masoyiyata shadila sai naga cewa ai na gama soyayya a duniya don ba zan taba samun wacce zan sota ta soni ba

kamarta bisa wannan daliline na rinka danne soyayyar zalina a cikin zuciyata kuma duk sa adda naga zata nuna mini soyayyar tata saina bagarar.

.

Ni abinda yake bani mamaki ma shine me zata yi da masaki muna cikin wannan hali ne mahaifin zalina ya kamu da cuta mai tsanani wacce takai shi ga kwanciya, abu dai kamar wasa kullum sai ciwo ya rinka gaba ya zamana cewa ba a samun sauki. Al amarin da ya dugunzuma hankalinmu kenan muka rasa sukuni da kwanciyar hankali ita kuwa zalina kullum bata da aikinyi sai kuka da bakin ciki da kyar nake iya rarrashinta, ba komai ne yake sata

wannan yawan kuka ba sai ganin cewa babu alamar samun lafiya ga mahaifinta kuma ga dukkan alamu ciwon nasa bana tashi bane, wata rana na tashi da sassafe ina shirin tafiya daji domin naje nayi farauta naman da zamu ci da rana a lokacin zalina na can wajan kogon da muke kwana ta dora tukunya akan wuta tana dafa mana abincin kalaci sai mahaifin zalina ya kira sunana a lokacin da nake daf da fita daga cikin kogon. Cikin tsananin mamaki na juyo na dubeshi saboda rabonsa da ya budi baki yayi magana tun daga ranar da ya kwanta wannan cuta, cikin matukar sanyin jiki na karasa daf dashi na tsugunna a gabansa inamai kura mas aidanuna ya shi kuma sai ya kamo hannuna ya dora akan kirjinsa ya dafe hannun nawa da dukkan hannayansa biyu sannan ya budi baki da kyar yace yakai hailur kayi sani cewa wannan ciwo nawa bana

tashi bane mutuwa zanyi kuma a koyaushe wa adina zai iya cika ina neman Alfarma guda daya jal a wajanka alfarmar kuwa itace ina son ka auri zalina, koda jin wannan batu sai zuciyata ta buga da karfi na dubeshi cikin mamaki nace yakai abul zalina ai idan kace na auri zalina bakayi mata adalci ba domin kana sone ta auri nakasashshe koda jin haka sai tsohon yayi murmushin karfin hali ya dubeni cikin nutsuwa yace yakai hailur kayi sani cewa a zahiri kake nakasashshe amma a zuciyarka kafi ta lafiya sannan kuma har yanzu sadaukantakarka da jarumtakarka suna nan basu ragu ba dai dai da matsayin kwayar zarra ina son ka sani cewa yata ta kamu da tsananin sanka a cikin wannan hali da kake ciki na nakasa kaga kenan ashe soyayyarta itace soyayyar gaskiya ka auri yata zalina ko don saboda ka samu zuri ar da zasu ga bayan babban makiyinmu sarki shardas ka sani cewa kowacce mace tana son ta auri namijin da zai iya kare mutuncin ta da rayuwarta koda kuwa shine yafi kowa nakasa a doron kasa lallai ku cika mini burina na ganin bayan sarki shardas wannan itace kadai wasiyyata a gareku, ashe duk wannan bayani da mahaifinta yake yimini zalina dake can kofar kogo tana sauraro don haka sai ta kasa cigaba da aikin da takeyi ta koma gefe daya ta zauna tana ta faman kuka, koda na fito daga cikin kogon dutsen rataye da takobina da nufin na shiga daji don gabatar da farautar sai naga zalina tana ta kukanta..

.

Al amarin da yasa na gane cewa lallai duk taji abinda muka tattauna kenan dani da mahaifinta cikin sanyin jiki na karasa gareta na zauna daf da ita kanta na sunkuye sai na tallabo habarta da lafiyayyen hannun nawa kuma na share mata hawaye muka kurawa junanmu idanu sannan na dubeta nace shin kin amince na zama abokin rayuwarki.

.

Koda jin wannan tambaya sai zalina ta murtuke fuska daga can kuma sai ta rungumeni ta kama kyalkyala dariyar farinciki muna rungume da juna mukaji motsi a bayanmu a firgice muka juya da sauri sai mukaga she mahaifin zalina ne ya fito daga cikin kogon dutsen yana dogara sanda da kyar yana numfashi sama sama.

.

A guje na janye jikina daga cikin na zalina na karasa gareshi na rukoshi na zo dashi wajan zalina itama ta kamashi muka zauna gaba daya sannan ta dubeshi cikin alamun tsananin damuwa tace haba ya kai Abbana yaya kai da kake cikin wannan hali zaka taso kayi tafiya sa adda abul zalina yaji wannan tambaya daga bakin yarsa zalina sai ya dubeta yayi murmushin karfin hali yace yake yata ai dole ne na taso ko don naga abin farinciki na karshe wanda idanuna zasu gani wanda shine amincewar junanku akan aure lallai ina so naga wannan aure naku da idanuna kafin rai yayi halinsa, nan take tsohon ya yiwa hailur bayanin yadda zasu daura auren bisa al adar su kabilar wato kowannansu ya yanki dan yatsansa ya diga jininsa

a cikin ruwa bayan jinin biyu ya gauraye sai kowannan su ya sha ruwan nan take kuwa muka aiwatar da hakan, muka rinka shan ruwan muna kallon juna cikin murmushi har sai da ruwan ya kare kaf.

.

A dai dai wannan lokacine farinciki ya lullube abul zalina ya dubi hailur yace yakai babban gwaro kayi sani cewa yanzu ka zama na zalina kuma zalina itama ta zama taka babu abinda zai rabaka face kaddara ko mutuwa, wannan dama shine manufar shan jinin juna da kukayi, bisa al adar kabilarmu a ranar da miji ya mallaki matarsa babu abinda zasu fara face zuwa daji farauta tare, don haka yanzu saiku tafi sannan da ku ka samo shi zaku kawo a gasa muci muyi walima da farin cikin aurenku, koda

jin wannan batu sai na dubi abul zalina cikin alamun damuwa nace haba yakai abul zalina yaya za ayi mu tafi daji mu barka kai kadai a nan alhalin kana cikin wannan halina rashin lafiya, 

.

Koda jin haka sai abul zalina ya dubeni cikin murmushi yace kada ka damu dani lallai zakuje ku dawo kuma ku sameni cikin koshin lafiya da sauki fiye da ko yaushe wannan shine abinda na gani a mafarkina na daren jiya bisa wannan dalili ne ma a yau din nan na sami saukin da har na iya mikewa tsaye na taka kafafuna na fito daga cikin wannan kogo haka dai abul zalina yaci gaba da rarrashinmu har ya samu ya shawo kanmu muka amince da barinsa a wajen amma kafin mu tafi sai da ya rungumemu yana ta dariyar farinciki bayan ya janye jikinsa daga cikin namune mun juya zamu tafi izuwa cikin daji sai zalina ta waigo ta dubeshi take ta hango kwalla a cikin idanunsa.

.

Al amarin da ya dugunzuma hankalinta kenan ta dubeni tace yakai mijina nifa zuciyata bugawa take da karfi ji nake kamar idan muka dawo ba zamu riskeshi a raye ba ni kaina naga alamun hakan a tare da mahaifin nata kuma duk kalaman da yake yi na bankwana ne amma don kada hankalin zalina ya tashi sai naki sanar da ita haka dai muka nausa cikin daji muna waigen Abul siyama shi kuma ya bimu da kallo yana yi mana murmushi har muka kule muka daina hangoshi.

.

A sannan ne kuma muka falfala da azababbn gudu izuwa cikin daji mukayi ta tsala gudu ba sassauci muna neman dabbar dajin da zamu samu babu abinda zai baka mamaki face yadda nake iya gudu ina dogara sanda alhalin kafata guda daya bata da kyau kuma har tserewa zalina nake yi a gudun ni ina rike da takobi ne kuma karshen sandar da nake

dogarawa mashi neita kuwa zalina a hannunta kwari ne kuma ta rataya kwanson kibiyoyin kwarin a bayanta don haka ita bata rike wani makami sai kwari da baka.koda muka nausa cikin daji sai muka rabu ni kuma nayi gaba ita kuma tayi yamma sannan kuma muka baiwa junanmu tsawon rabin sa a akan mu hadu a bakin wani dutse dake can tsakiyar dajin kowannanmu na rataye da kaho a bayansa wanda duk sa adda ya shiga wani hadari wanda ba zai iya kubutar da kansa ba sai ya busashi komai nisan inda yake dan uwansa zai iya jiyowa har yakai mas dauki shidai wannan kaho na sihirine kuma gado ne a kabilar tasu zalina kuma mutum ba zai iya mallakarshi ba face ya kasance dan kabilarsu ko kuma ya auri jinin Kabilar.

.

Bayan mun rabu a cikin daji nida matata zalina sai muka wanzu muna masu neman abin farauta baji ba gani, lokacin da naga na shafe dan dogon lokaci ina neman abin farautar ban samu ba sai hankalina ya dugunzuma ainun saboda ina ganin cewa ai abin kunyane ace a ranar daurin aurena na kasa farauto abincin da zamu ci nida amaryata…

.

Zan dakata nan sai kuma Allah Ya kainu gobe insha Allahu afin nan daga mai ɗebe maku kewa AlQuyraemey nake cewa ku huta lafiya.

Ehm Al amin Ahmed Misau, Guyson ko A square

Ina cikin wannan haline naga wata barewa ta

nufo inda nake cikin azababben gudu gashi dai

barewar ta hangoni a gabanta rike da makami

amma ko shakkar tunkaro ni batayi ba

dada durfafo ni takeyi al amarin da yasa na fahimci

cewar lallai masifar da ta korota ta nufoni don tsira

da rayuwarta ta wuce tawa hadari, ai kuwa ban ankara ba

sai naga ashe wani murjejen zaki ne ya tasota a gaba

tun daga nesa dana hango zakin ya falfalo da azababben gudu

har tashi sama yake saboda karfin gudun nasa

kuma harshensa na zazzagowa waje daga cikin bakins ana gane

cewa lallai

wannan zaki a cikin muguwar yunwa yake

koda naga cewa barewar nan so take ta wuce ta gabana

domin ta tsira da rayuwarta sai na yunkura cikin zafin nama na

daka tsalle sama a lokacin da itama barewar ta daka tsalle da nufin ta shallakeni

muna haduwa a saman na soketa da mashina ta

zama gawa na duro kasa bisa kafafuna barewar

na sakale a jikin mashin nawa, ai kuwa sai wannan zaki

yayi tirjiya a lokacin da tazarar dake tsakaninmu

bata wuce taku goma ba

nan fa muka fara kallon kallo tsakaninmu da murjejen zakin

nazarin da zakin yake yi shine ni zai farwa sannan

ya dauke barewar ko kuwa barewar zai karba

ni kuwa nazarin da nakeyi shine ta yaya zan iya

.Ya kasance shi ba karamin tashin hankali bane

duk da na san cewa na sha yin gumurzu da manyan

dabbobin daji ina samun nasara a kansu sai da

zuciyata ta karaya akan wannan zaki domin ban

taba yin gamo da tsohon zakimai girma da kwarjinin wannan ba

nikam tuni na gama aiyanawa a raina cewa

duk rintsi ba zan iya sallama barewar ba ga wannan

zaki koda hakan na nufin zan rasa rayuwata

kawai sai na cake mashin nawa a cikin kasa

wanda ke dauke da barewar sannan na buda hannuna

mai rike da takobi ina mai

gyara tsayuwata kuma na koma gefe daya na tsaya ina

mai baw azakin zabi tsakanin barewar da ni kaina

ya zabi wanda zai fara afkawa

take zakin yayi wani irin

gurnani mai ban tsoro wanda yasa hantar cikinsa ta kada amma da na tuna cewa

amaryata

zalina na can fa tana farauta a cikin wannan daji

wata kilama yanzu ita ta dade da samo nata abin

farautar taje inda mukayi zamu hadu ta zauna

tana jirana sai naji zuciyata ta kekeashe ga barin dukkan tsoro…..

Kamar hadin baki sai nida zakin muka falfalo

da gudun tsiya izuwa kan juna muka dako tsalle

sama a tare kafin nayi wani yunkuri na saran zakin

ko sukarsa da takobina tuni shi ya sa kirjinsa ya

bangajeni

ai kuwa sainaji kamar aksusuwan kirjina sun

kakkarye nayi can baya da karfi bayana ya gwaru

da jikin wata bishiya na fado kasa a matukar galabaice

ina aman jini ta hanci da baki, koda zakin yaga

halin da na shiga sa adda shima ya duro kasa sai

ya wangame baki ya kwalla wani uban ruri anda

ya fi wanda yayi a baya mai nuna kuranta kansa

da dai yaga na kasa tashi ina ta numfashi sai

ya wuce ta gabana ya daka tsalle da nufin ya suro

wannan barewa dake sakale a jikin mashina

ni kaina ban san yadda akayi ba na sami gagarumin

karfi da kuzari kawai gani nayi na mike tsaye zumbur

na daka tsalle daga inda nake na rungumo zakin

kafin bakinsa ya cafi barewar mun fado kasa tim !

Nan fa muka kama kokawa a kasa muna ta birgima

idan zakin ya danneni yana kokarin kafa min

hakoransa sai na juye dashi nima ina kokarin

turmushe shi da karfin tsiya domin na hallakashi

sai da muka shafe kusan sa a daya muna ta bakin

artabu ya zamana cewa zakin ya karkarce jikina

da kaifin faratan hannayansa yai mini raunika

masu yawa jini na zuba a jikina amma kuma ya kasa

kafa min hakoransa a jikina

lokacin da jiri ya fara dibana na tabbatar da cewar ina daf

da halaka sai zuciyata ta kufulo cikin tsananin

zafin nama na suri zakin na dokashi akan wani

katon dutse nan take kan zakin ya dagwargwaje ya

zama gawa

A sannan ne na yanke jiki na fadi kasa cikin mugun yanayi

da kyar na iya bude jakar guzurina na fiddo magani

na shafa akan raunikan jikin nawa da hannu daya

wadansu raunikan ma dake gadon baya na in da

hannuna ba zai kai ba ban sami damar sa musu

maganin ba

a sannan ne na dauko battar ruwana na bude nash

Sai da na dan huta naji karfin jikina sannan na mike

tsaye na dauki gawar zakin na saba a kafadata

amatsayin abincinmu na rana itama barewara

sai na barta a jikin mashin nawa naci gaba da tafiya

na nufi inda zamu hadu da matata zalina

hakika SADAUKANTAKA tana da rana tabbas in ba don

na kasance sadauki ba da babu yadda za ayi na iya daukar

wannan katon zaki har na sabashi a kafadata da

hannu daya kuma naci gaba da tafiya alhalin ina

rike da barewa bisa mashina, haka dai naci gaba da

tafiya har na iso inda zan hadu da zalina matata

tun daga nesa kuwa na hango zalina zaune akan

wannan dutse tana hange hange da waige waige

ko zata gano ni, har ma ta zaku tana mikewa tsaye

akan dutsen

ai kuwa tana hangoni dauke da zakin da kuma barewa

sai ta cika da tsananin mamaki, cikin tsananin

murna ta duro kasa daga kan wannan dutse ta farfalo

da gudu izuwa gareni ta rungumeni koda taji

raunika a jikina sai ta janye jikinta daga cikin nawa

da sauri ta dubi sauran raunikan na jikina, take

hawaye ya kwararo daga cikin idanuwanta ta

dubeni cikin alamun tausayi tace yakai mijina me yasa

ka sai da rayuwarka don kawai ka cika wannan ka ida

ta al adarmu

Sa adda naji wannan tambaya sai na bushe da dariya

nace

yake matata kiyi sani cewa ko a tamu al adar namiji

baya samun matar aure a cikin sauki har sai ya

sha bakar gwagwarmaya ta hanyar gasa a neman

auren,

kuma gasa ce mai hadarin gaske wacce mutum ma

zai iya rasa rayuwarsa gaba daya, nan dai muka juya

da baya muka nufi hanyar gida, muna cikin

tafiya ne na dubi zalina na bushe da dariya, Al amarin

da yai matukar bata mamakikenan

ta dubeni tace yakai mijina kai kuwa menene dalilin

yin wannan dariya taka, kawai sai nayi ajiyar numfashi

nace gani nayi nidake mun shafe sama da sa a biyu

a cikin nan muna farauta amma ke ko fiffiken dan

tsako baki samo ba, dajin wannan batu sai itama ta

kyalkyale da dariya tace ni kaina na yi matukar mamakin

yadda ko tsuntsu guda ban iya harbowa ba daga sama

alhalin ga su nan birjik suna ta kaiwa da komowa

a sararin samaniya sai dana yi asarar kibiyoyina

sama da guda talatin, kai bama tsuntsaye ba hatta

kananan dabbobin daji sai dana kasa tsere da wajan

guda bakwai amma da zarar sun shiga cikin duhuwa

saina nemesu sama ko kasa na rasa su

koda jin haka sai nayi dariya nace ai kin san cewa komai

sa a ne da rabo

haka dai muka ci gaba da hira har ya rage saura tafiya

kadan mu iso gida

kwatsam muna cikin tafiya sai zalina tayi tuntube ta fadi a lokacin da zuciyarta

ta fara bugawa da karfi, cikin sauri na ajiye mashina

mai cake da barewa na tasheta zaune na dubeta

cikin kaduwa ina mai dudduba jikinta nace lafiya

kuwa menene ya sameki, zalina tayi ajiyar zuciya

ta dubeni cikin alanun firgici kawai sai naga hawaye

ya zubo mata take ta fashe da kuka tana mai cewa

naji a jikina cewa mahaifina yayi kaura, koda jin haka sai

nima hankalina ya tashi na dubeta cikin kwarin guiwa

nace ke haba ! Tashi mu karasa gida mahaifinki na

nan raye

kawai dai zuciyarki ce take raya miki hakan

nan dai na tasheta muka mike tsaye har zuwa wannan

lokacin ina dauke da wannan katon zakin a kafadata

ga kuma barewa a jikin mashina

haka dai muka

cigaba da tafiya harmuka

Iso gida

tun daga nisa muka hango Abul zalina kishingide

a jikin dutsen kogon da muke kwana ya dora

kafarsa daya akan daya yana barci, kuma ga sanda

a hannunsa in ba don dora kafarsa da yayi ba daya bisa

daya da kuma sandar da ya rike a hannunsa da dole ne

ace ya mutu

Al amarin zalina kuwa lokacin da ta hango mahaifinta

a cikin wannan hali tun daga nesa sai jikinta yayi sanyi

Al amin Ahmed Misau Nake Guyson Ko A square

zuciyarta ta karaya kawai sai ta yarda bakan dake

hannunta ta falfala da gudu izuwa gareshi tana

isa gabansa sai ta kura masa idanu koda taga

idanunsa a kafe suke ko kiftawa basa yi kuma babu

inda yake motsi daga cikin gabobin jikinsa sai ta

fada kansa ta rungumeshi tana mai tsandara uban

ihu sannan kuma ta fashe da kuka

koda ganin abin da

ya faru sai nima na rugo da gudu ina dogara sandata

ina isowa na warbar da wannan zaki na kafadata

kuma nayi jifa da sandata da mashin da barewar

ke tsire akai

kawai sai na tsugunna kasa bisa guiwoyina na fara

kuka aka rasa

wanda zai rarrashi wani tsakanina da zalin

nikaina Al amin Na tausaya musu gaskiya

da wannan gagarumin rashin mahaifin ta da sukayi

sai da muka shafe kusan sa a guda muna kuka sannan na

mike tsaye naje na kama kafadar zalina na

tasheta tsaye na shiga rarrashinat, sai da ta dawo cikin

hayyacinta sannan muka fara shirye shiryen

binne gawar mahaifin nata, tun daga wannan rana

muka bar wannan daji ba tare da fatan komawa cikinsa

ba

ko don ziyara ga kabarin mahaifin nata wanda ke cikin

wannan kogon dutse

haka dai mukaci gaba da tafiya a cikin daji mu

kwana nan mu tashi can ba tare da sanin inda muka

dosa ba muna neman inda yake da ni ima mu zauna

muci gaba da rayuwarmu, sai da muka shafe watanni

shida cur muna tafiya sannan muka iso wani daji dake

cikin nan kasarka ta Askandariyya, A nan ne muka zauna

muka ci gaba da rayuwa nida matata zalina inda

muka gina wata yar bukka a gefen wani tsauni

inda muke kwana har ma muka kafa wani garken dabbobin

gida muna kiwo bamu da wata sana a face farauta

kuma mu kan kai fatun dabbobi cikin birnika mu siyar

mu siyo abin da muke bukata da silallan da muka

sayar da fatan dabbobin dajin sannan mu dawo

dajin da muke da zama ba tare da mun taba sha awar

yin rayuwa ba a cikin gari har muka samu rabon

haihuwar Yata SIYAMA

tun siyama tana da shekara biyar a duniya na fara bata

horon yaki har ta cika shekara tara kuma duk irin horon da za a baiwa

babban mutum shi nake bata

hakika siyama tasha bakar wahala sosai a wajen

horon yaki kamar zata rasa ranta kuma sau tari sai

uwarta tayi ta

kuka idan taga tana shan wahalar taji kamar ta

hanani bata horon amma idan ta tuno da irin

kisan gillar da sarki shardas yayiwa kabilarsu da

zuri arsu da tawa sai ta hakura, haka dai siyama taci

gaba da koyon yaki har ya zamana cewa nima

ta fini jarumtaka juriya da naci, a bangaren iya farauta kuwa

ni kaina sai da na cika da mamaki bisa ganin irin

abubuwan al ajabin da take yi a daji da kuma irin

kwarewar da ta samu ta iya harbin kibiya fiye

da mahaifiyarta

bamuyi shawarar sanya siyama a cikin gasar jarumtaka

ba don komai sai saboda mu jarraba karfin

damtsenta da kuma iyakar jarumtakarta kuma

burinmu shine taci gaba da baiwa kanta horo gami da

tanadin daukar fansa akan sarki shardas, ina mai tabbatar

maka da cewa

yanzu haka ko sunan sarki shardas siyama taji

an ambata sai zuciyarta ta kama tafarfasa kamar zata

kone saboda irin kiyayyar da muka cusa mata

kuma a kullum bata da burin da yafi na mu kyaleta

ta tafi zuwa birnin shardas ita kadai ta shiga har

cikin fadarsa ta kashe shi amma na gaya mata cewa

ba zata taba samun nasara ba a kansa a yanzu face

idan ta mallaki wata Hula da ake kira HULAR LAMSARA

koda Hailur yazo nan a labarinsa sai idanun sarki

hulbasu

suka zazzari ya kamu da tsananin tsoro gami da

mamaki saboda rabonsa da yaji an ambashi sunan

wannan hula ta LAMSARA tun yana yaro karami sai kuma

yanzu da yaji a bakin hailur, tabbas ya sami labarin

hular lamsara a wajan kakansa wato wanda ya haifi ubansa amma bai kara jin

labarinta ba kawo i yanzu

sai da sarki Hulbasu ya baza fatake jarumai da

mayaka izuwa sassan duniya domin su nemo

masa wannan hula ta lamsara amma ba a samu wanda ya jiyo labarin inda

hular take bama

sarki hulbasu yayi gyaran murya sannan ya dubi

hailur a natse yace hakika jikina ya bani cewa lallai

akwai wani babban sirri a tsakanin shardila matar sarki shardas

kuma ina mai tabbatar maka da cewa idan sarki shardas ya gano cewa kana nan

a raye kuma anan cikin yankin kasata tobama kai ba

ko iyalinka hatta nida kaina bz an zauna lafiya ba

don zai iya zuwa ya yakeni ya kawai da mulkina

koda jin haka sai hailur ya dubi sarki Hulbasu yace

yakai wannan sarki mai Karamci me yasa ka taimakeni

Alhalin ka san cewa yin hakan hadarine ga rayuwarka

da mulkinka

koda jin haka sai sarki hulbasu yayi gyaran murya

gami da ajiyar zuciya sannan yace A rayuwata

babu abinda na tsana sama da zalunci kuma mahaifina

kafin ya gushe ya bar mini wasiyya akan cewa

idan har ina son nayi nisan kwana akan karagar mulina to

dole ne

Na guji aikata zalunci ga talakawa na dama duk

wadanda suke karkashina ko kasa dani kuma na

kwatanta adalci a tsakaninsu gwargwadon iyawata

ina so ka sani cewa har yanzu sarki shardas bai san

komai ba dangane da wanzuwarka ko baiyanarka a cikin aksata kuma

dolene kaci gaba da boye kanka har izuwa lokacin da

zaka iya fuskantarsa, duk da cewa yanzu kaga matarka

shadila da kuma danka yarima Hulkasa

amma dole ne ka hakura da mallakarsu har sai nan

da zuwa lokacin da ya dace, idan ba haka ba kuwa zaka

rasa su ne gaba daya kuma kai kanka ma zaka rasa kanka

ba zan hanaka ka gana da shadila ba amma kada ku

kuskura ku bari wannan yaro hulkas ya san cewa

kaine mahaifinsa kuma kada ku bari ya san duk abinda

ya faru a baya

hakan ba zai haifar muku da komai ba face rugujewar dukkanin burikanmu

gaba daya da kuma salwantar rayukanmu

yayinda sarki Hulbasu yazo nan a zancensa sai hankalin

hailur ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe har hawaye ya zubo masa kuma

zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda

fishi

ya dubi sarki hulbasu yace yanzu kana nufin kace dani

inaji ina gani zan hakura da matata wadda aka

rabani da ita a daren angwancinmu da ita na farko kuma na hakura da

dana wanda tun yana ciki bai san cewa nine ubansa ba

gashi har ya cika shekara bakwai a duniya, ka sani cewa har kwnaan gobe zuciyata bata

bayar da soyayyarta ta gaskiya ba ga kowa face shadila

ina son shadila fiye da yadda nake son kaina

Al amin ahmed Misau Nake Shin tayaya kake tunanin

zan

yarda ta sake kubuce min a karo na biyu al halin ban taba

zaton cewa zamu sake hadu wa ba a cikin wannan

duniya

koda hailur ya zo nana a zancensa sai hawaye ya zubowa

sarki Hulbasu al amarin da yai matukar girgiza

hailur kenan kuma yai matukar bashi mamaki

ya dubeshi yace yakai abokina inda dalikin zubar

wannan hawaye naka mai tsada koda jin wannan

tambaya sai sarki hulbasu yaja dogon numfashi

sannan ya sa hannu ya goge hawayansa ya dubi

hailur cikin alamun karayar zuciya yace yakai abokina

kayi mini tambayar da ta fama min tsohon ciwon dake cikin

zuciyata ne kuma shine asalinsanadin da yaja

mummunar kiyayya tsakanina da sarki shardas inaso

ka sani cewa duk irin kiyayyar dakake yiwa sarki

shardas bata kai koda rabin wacce nake yi masa ba

domin duk ladabin da nake yi masa a yanzu na

dole ne saboda yafi karfina kuma bana son abinda zai

taba kasata da jama’ata, ka sani cewa bakincikin

sarki shardas ne ya kashe mahaifina kuma sarki

shardas ne sanadin dana rasa dana na fari YARIMA

HUZEIN

Cikin alamun tsananin mamaki da kaduwa hailur ya

dubi sarki hulbasu yace tayaya mahaifinka da danka

huzein suka gushe

koda jin wannan tambaya sai hawaye ya sake zubowa

sarki hulbasu ya dubi hailur cikin nutsuwa yace

yakai abokina ka saurari labarin da zan baka yanzu

dukkanin amsar tambayar da kayi min yanzu tana

cikinsa……

.

JARUMA SIYAMA DA MAHAIFINTA HAILUR SUNA CIKA

BURINSU NA DAUKAR FANSA AKAN SARKI SHARDAS ?.

.

MAI ZAI FARU IDAN SARKI HULBASU YA GAMA BAIWA HAILUR

LABARIN MUTUWAR DANSA DA MAHAIFINSA ?

.

A WANNE HALI SHADILA TAKE CIKI BAYAN TAYI ARBA DA TSOHON MIJINTA HAILUR ?

.

YAUSHE YARIMA HULKAS ZAI SAN CEWA HAILUR SHINE

MAHAIFINSA NA GASKIYA

.

Marubucin littafin Wato Abdul aziz sani M/ Gini yace

mu hadu a Littafin Tsatsuba na (6) Don jin

cigaban wannan kayataccen kasaitaccen labari

mai dumbin darasi fadakarwa da nishadantarwa

Mai debe muku kewa a kullum da ko yaushe.

Suleiman Zidane Kd 09064179602:

Back to top button