Uncategorized

The Governor Wife Book 1 Page 4 Complete Novel

 

…… MATAR  GWAMNA….

 *©Azizat Hamza*

Lokacin da Ale Faruƙ ya auri Zainab Kurma matan sa uku ne, dan bai jima da sakin ta huɗun ba. Da ganinta da auren duka-duka sati huɗu ne.

Mama Asabe har ga Allah bata so aka yi auren ba, ba kuwa saboda halin Ale Faruƙ ɗin bane na auri saki sai dan saboda ayyukan da Kurma ke mata. Duk wani ƙarfin sana’arta to Kurma ce. 

Ita da Malam Sabo dai sun yi ƙarfa-ƙarfa sun mata gado da tabarma da buta daga nan kuma kowa ya tsuke Aljihun sa. Duk da kuwa irin kuɗin da Malam Sabon ya yaga a wajen Ale Faruƙ ɗin.

Inna Talatu wacce ta reneta lokacin tana yarinya da kuma wasu cikin ‘yan uwan mamanta su suka haɗu suka mata sauran kayan ɗakin.

Lokacin da aka kawo Kurma gidan ɗakin Iyani aka fara kaita wacce ta ke Uwargida sannan aka wuce da ita ɗakin Fulani wacce ta ke matarsa ta biyu a gidan, matar da ta zame masa ƙarfen ƙafa ita bata haihu ba amma ta ƙi tafiya duk da kuwa rashin mutuncin da take shukawa a gidan. Sai ɗakin Halime matarsa ta uku wacce shekaransu uku kenan da aure.

Lokacin da aka kaita ɗakin Tabawa ko kallon kirki bata yi musu ba, ta ɓantari goro tana taunawa tace “Faruƙu kenan. Abin nasa yanzu ya koma kan Miskinai. Allah rufa asiri”

 Inna Talatu ta harzuƙa zatayi masifa wata yayarta ta hanata. Kafin su fita kuwa Inna Talatun ta kirata da tsohuwar banza. Tabawa ta biyosu tana zagi tana tsinuwa amma babu wanda ya kulata.

Rayuwar Zainab a gidan Ale Faruƙ tamkar ‘yar aiki ce a gidan iyayen gidanta. Sati ɗaya da Ale Faruƙ yai yana kwasar amarci ya dinga tattalin Zainab, shi yake siyo mata abinci daga waje: nama, bredi, ƙwai da madara sune cimarta. Baiwar Allah har ta fara sake jiki tana godewa Allah tunda rayuwar da take ciki yanzu akwai daɗi ba kamar gidan Mama Asabe ba.

Lokacin da aka fara rabon girki nan ne ta ƙwammaci kiɗa da karatu. Gidan Ale Faruƙ babban gidane wadatacce dan kowacce mata ciki da falo gareta, shima sashensa ciki da falo ne, sai ɗakuna huɗu na yara sai ɗakin mahaifiyarsa Tabawa, sannan akwai ɗakuna uku a zaure na saukan baƙi. A lokacin daya auri Zainab ‘ya’yansa goma shabiyar ciki kuwa bakwai ne da iyayensu. ‘Ya’yan Iyani su guda shida, maza biyu,mata huɗu sai Halime dake da ‘ya ɗaya.

Da farko Fulani ce ta fara ɗaurawa Zainabu nauyin girkinta daga baya Iyani da Halime suka biyo baya. Kafin kace me gaba ɗaya ranakun girkinsu ita ke yi. Fulani kam hatta Sana’arta na shinkafa da wake da take da rana sai da ya zamo Zainabu ce ke yin komai , ita dai sai kawai idan ta gama ta zauna ta dinga siyarwa.

 A hankali Yaran gidan da suka ga iyayensu na saka Zainab aiki sai suka fara taɓawa suma. Lokaci lokaci sai su bar mata wanke-wanken gidan ko kuma  su jiƙa kayan wanki su ƙi wankewa saboda idan Kurma ta zo ta gani tana son amfani da baho ko bokiti dole sai dai ta wanke musu kayan tunda bata da mugun zuciyar da zata bar musu kayan a ƙasa. Ranan da ta fara zuwa ta ga sunyi haka, ɗakin yaran ta je tana musu bayani akan za tayi amfani da bahon wanki. Haka suka manna mata hauka akan basu san mi take faɗa ba, abin takaicin yawanci bahon nata ne dan Fulani da Halime basa taɓa barin nasu a waje. Ita kuwa Kurma ko bata fito da su ba yaran sukan shiga ɗakinta su ɗauka babu yadda ta iya.

Cikin zalunci da ake yiwa Zainabu ba abar Tabawa a baya ba. Itama ba ta taɓa ragawa Zainabun ba, dama duk cikin matan Ale Faruƙ babu wanda ta ɗauki mahaifiyarsa da daraja haka ma jikokinta. Kafin zuwan Zainabu gidan Tabawa ke wanki da kanta, haka ma abinci sai abinda aka zuba mata amma Zainabu Kurma bata taɓa mata rowan abinci ba haka nan wankinta da gyaran ɗaki duk ita ke yi.

Kafin shekara ɗaya  Zainab ta zabge ta koɗe. Aikin da take a gidan Ale ko rabinsa bata taɓa yi ba a gidan Mama Asabe.

Ale Faruƙ ya san mi yake faruwa a gidan tunda shi ba makaho bane amma halinsa dama shine idan mace ta shigo gidansa komai ta tarar ruwanta ne, sai dai ta ƙwaci kanta daga sharrin sauran matansa amma shi ba zai tanka ba.

Akwai lokacin da Zainab tayi ɓarin cikin sati uku bata sani ba bata ma san cikine ba dan jinin  al’ada ta ɗauka.

Tana zaune ne a gidan amma gaba ɗaya komai na gidan ya fita mata aka. Akwai lokutan da take tunanin gara kawai Ale Faruƙ ya saketa. Sai dai dokar sa ce baya sakin mace kafin ta cika shekara biyu. A cewarsa lokacin bai gama morar kuɗinsa ba. 

A cikin shekara na biyu da auren Zainabu da Ale Faruƙ ta sake samun ciki. Cikin yazo mata da laulayi mai tsanani amma babu wanda yake tausaya mata a gidan. Ba ta son warin abinci, bata cin abinci sai ƙanzo da kunun tsamiya. Idan za ta yi girki sai dai ta sa tsumma ta rufe hancinta saboda kar ta ji ƙanshin. Ranan da ta ƙi yiwa Fulani girki ta nuna cewa sai dai tayi tunda ranan girkinta ne haka ta mata chaa har da mata kashedin indai bata yi girkin ba za ta mata duka a gidan.

Ranan da Ale Faruƙ ya dawo ɗakinta, tace masa ya gayawa matansa cewa ba zata sake yiwa kowacce girki ba. Abin mamaki sai cewa yai tunda ta riga ta fara sai dai ta cigaba da hakan har zuwa lokacin da zasu ce ta dena. Abin ya ƙona mata rai. Bata taɓa tunanin kai ƙaran Ale ko matansa ba, koda wasu cikin ‘yan uwanta sun kawo mata ziyara nunawa take bata cikin matsala.

Washegari ta saka hijabi ta wuce gidan mahaifinsa.

Ɗan karatun allo da tayi kafin aurenta da shi ta  iya rubuta bayaninta da rubutun ajami a takarda ta miƙawa Mama Indo matar Gwani. Mama tana karantawa sai ga hawaye ya cika mata fiska. Tana tambaya ne akan ko addini ya bayarwa namiji daman ya yi rashin adalci tsakanin matansa. Sannan idan ta ƙi yiwa matan mijinta aiki akwai zunubi awajen Allah?

Mama bata bari Gwani ya gama karatu da almajiransa ba ta aika akan ya zo akwai matsala. Koda ta bayyanawa Gwani abinda Zainab ta faɗa ransa ya ɓaci sosai. A kullum tsakaninsa da Faruƙ shawara da addu’a domin muguwar tarbiyar da Tabawa ta bashi da kuma jahilci da ke damunsa shiyasa yake tafiyar da rayuwansa bisa ra’ayin kansa. Arziƙi dai Allah ya bashi amma ni’imar ilimi da kakansa Malam Falke keda shi, da Gwani keda shi da ƙannensa Malam da Zakari keda shi ya barranta masa. Bai nemi ilimi yana ƙuruciya ba kuma har yanzu da yake da damar neman ilimi kuɗi da mata sune a gabansa.

 Gwani ya fayyace mata hakkin mace akan mijinta da hakkin miji akan matarsa hakan yasa zuciyar Zainab ya ɗan yi sanyi.

Mama da kanta taje gidan ta tara matan Ale Faruƙ ta gaya musu saƙon Gwani akan duk wacce ta sake takurawa Zainab zai mugun saɓa mata. Yadda basa shakkan Tabawa haka suke tsananin shakkan Gwani.

Tabawa na zaune ƙofar ɗaki tana tauna goro ta fara faɗin “su matar Malam manya. Duk tsiyar ki dai Faruƙ ɗana ne. Idan Allah bai bashi ilimi ba ai ya bashi arziƙi” …

Daga ranan kowacce mata ta karɓi girkinta.

Cikin Zainabu na wata bakwai Gambo wata maƙociyarsu ta fita daga takaba hakan ya sa Ale Faruƙ ya fito nemanta. Kamar kowacce mace arziƙinsa, kyaun surarsa da kuma gulmar ƙarfinsa da matan daya saka suke, shi ya kwaɗaita wa Gambo shiga gidansa, sai dai ta san mata huɗu gareshi.

Halime, Ale Faruƙ yai niyyan saka saboda ta kwana biyu a gidansa amma tunda ta masa rantsuwar duk ranan da ya saketa sai ta yanke masa gaba sai ya chanja tunani. Ba zai saki Iyani ba saboda itace uwar manyan ‘ya’yansa sannan Fulani kuma ya rasa dalilin da yasa ya kasa sakinta. Kurma ce kawai zai iya saka a halin daya samu kansa sai dai kuma gaskiya bai shirya rabuwa da ita yanzu ba, har yanzu akwai ƙuruciya a tareda ita. Kuma ita kaɗaice macen da idan yace tayi abu za tayi idan yace ta bari ma zata bari.

Da dai yaga Alhaji Mato na ƙoƙarin kauda shi a wajen Gambo sai ya yanke ɗanyen shawaran sakin Zainabu.

Da sassafiya ya shiga ɗakinta ya miƙa mata takarda ya mata bayanin zata iya zama a ɗaya daga cikin ɗakunan gidan har ta haihu.  Ba tayi boko ba shiyasa ko karanta hausar daya rubuta bata iya yi ba. Zuwa tayi wajen Jamilah ɗaya daga cikin yaransa wacce take da ɗan hankali tace ta rubuta mata abinda Ale ya rubuta da ajami. Jamilah ta rubuta mata kamar yadda ya rubuta da Hausa *na saki Zainabu saki ɗaya* bayan ta karanta rubuntun da Jamilar tayi a ƙasan na Ale, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ɗauki takardar ta koma ɗakinta ta shiga haɗa kayanta. Zuwa ƙarfe sha biyu na rana ta gama tattara kayanta ta wuce gidan Inna Talatu. Ba zata iya komawa wajen Mama Asabe ba saboda a halin da take ciki wajen da zata samu kwanciyar hankali take nema.

A wajen Inna Talatu yar mahaifiyarta ce kaɗai zata iya samun wannan.

Haka kwanaki suka dinga tafiya har wata ranan Jumma’a ranan da cikin Zainabu ya shiga wata tara da kwana biyar ta haifi kyakykyawar ‘yarta.

Suna dawowa daga Asibiti da ɗanyan haihuwa haka ta ɗauki ‘yarta ta wuce gidan Gwani da ita haɗe da takardar da ta rubuta ranan da Ale Faruƙ ya saketa.

Gwani na alwalar sallar la’asar Zainab ta shigo ɗauke da jaririya a hannunta.

Tana zuwa gabansa ta ɗan rusuna sannan ta miƙa masa takardar hannunta.

Gwani da hankalinsa ya tashi da ganinta haka ya karɓi takardar yana ƙwalawa Mama kira.

Lokacin daya karanta takardar hawaye ya taru a idonsa. Tausayin ɗansa Faruƙ ya fi kamashi akan na Zainabu. Mama ta fito daga ɗakinta tana tambayar Zainabu yaushe ta sauka amma Zainabu bata kulata ba.

Gwani ya ajiye takardar ya ƙarisa alwalarsa sannan yai wa Zainabu alamar ta miƙo masa jaririyar. Zainabu ta miƙa masa ‘yar.

Gwani yai wa yarinyar kiran sallah a kunnenta na dama sannan yai mata iƙama a kunnenta na hagu kafin ya gama Mama ta shiga ɗakinta ta ɗauko masa dabino, dake cimar Gwani ne ba a rasawa a ɗakinta.

Huɗuba yaiwa ‘yar da suna Asiya Shahidah sannan ya shiga tofa mata duka addu’o’in da Zainabu ta rubuta a takardar data kawo.

Yai addu’ar kada Allah ya sa ta ɗauko ko ɗaya daga cikin halayen mahaifinta da ta kakarta Tabawa. Yai addu’ar ta zamo mai ilimi, mai tausayi, mai imani da riƙon amana. Yai addu’ar kada ta zamo azzaluma mai tauye hakkin mutane, yai addu’ar yadda mahaifiyarta bata ji bata magana Allah ya sa ta ji ta kuma yi magana. Yai addu’ar ta zama jaruma marar tsoro wacce akoda yaushe neman gaskiya da aiwatar da gaskiya shine halinta, yai addu’ar Allah ya kareta daga sharrin Mutane, Aljanu, Dabbobi da kuma Shaiɗan la’ananne. Yai addu’ar ta zamo abin alfahari ga iyayenta dama al’ummar musulmai gaba ɗaya. Ya ƙara da cewa  yana addu’ar ta samu tabarakkin mai sunanta wato Nana Asiyah.

Bayan ya gama addu’o’in sannan ya karɓi dabino a hannun matarsa ya gutsura ya tauna sannan ya sakawa Asiya a baki. Sai alokacin Zainabu ta fara murmushi.

Ita da Mama ne suka koma gidan Inna Talatu wacce ta birkice saboda rasa Zainabun da akayi a gidan…

A gidan Gwani aka yi suna dan kwana huɗu da haihuwan ya nemi Zainabun ta dawo gidansa. Kunyar Baban tsohon mijinta ya sa bata iya musawa ba. Ale Faruƙ ma dai nauyin Gwani daya ji ya sa shi kawo rago da kuɗi dan a yi suna da shi.

***

Tun kafin Asiya ta cika shekara biyu Inna Talatu ke yiwa babban ɗanta mai suna Nuhu kwaɗayin ya auri Zainabu. Matarsa ta farko ta rasu sannan Yahanasu da ya aura wacce ita ɗin ‘yar dangin mahaifinsa ce sai ta kasance fitinanniyar mace. 

Shekarar Asiya uku aka yi auren Malam Nuhu Principal da Zainabu Kurma. Lokacin da Ale Faruƙ ya ji labarin auren baƙinciki kamar ya kashe shi, duk cikin matan daya rabu da su babu wacce yake jin rabuwar da ciwo kamar rabuwarsa da Zainabu. Ya rabu da Halime ita kuma Gambo data shigo gidansa tama fi Fulani fitina.

Malam Nuhu Gidaɗo Malamin makaranta ne da ya kai matsayin Principal inda yanzu yake shugaban makarantar Special School Congo.

Matarsa ta farko Hassana sati biyar da haihuwa ta rasu hakan ya sa rainon ɗansa Ubaydullah ya koma wajen ‘ya uwarta Hussaina. Shekaru uku da rasuwan matarsa kafin Mahaifinsa ya haɗa shi aure da Yahanasu wacce take marainiya a lokacin.  

Lokacin daya auri Zainabu yaran Yaha uku ne duka mata. Aisha da suke kira da Ummi sai Fatima sai kuma Hindatu daga baya ne ta haifi Musa bayan ita Zainabun ta haifi ɗanta na fari wato Muhammad Habibu sai Lukman da suke kira da Gwani sai autanta Aliyu.

Sanda Zainabu ta tare ko wata huɗu batayi ba Malam Nuhu ya sata a makarantar kurame inda ake koya musu rubutu da karatu da kuma sana’o’i.  A nan ne ta koyi ɗinki da saƙa.

Asiya Shahidah ta taso ne tsakanin gidan Gwani da Inna Talatu bata zuwa gidan Mahaifinta sai dai idan shine yazo ya ɗauketa dan Allah ya saka masa ƙaunar Asiya. Saboda ita ne ma ya dage da zuwa gidan Gwani duk bayan kwana biyu maimakon da da sai yai sati biyu uku bai leƙa mahaifin nasa ba. A duk lokacin da ya zo idan yaji Gwani yana yabon kwanyar Asiya akan tana ɗaukan karatu sai ya dinga jin wani nishaɗi a tattare da shi. Duk yaransa a wajen Gwani suke zuwa ɗaukan karatu tun suna shekara biyu da rabi yake sawa a tisa ƙeyarsu wajen Mahaifinsa. Kuma duk cikinsu idan ka cire babban ɗansa Nafi’u daya rasu babu wanda ya taɓa ji Gwani ya yabi kaifin ƙwaƙwalwarsa kaman yadda yake yabon Asiya. Wani lokaci idan yazo sai ya ce Asiya ta ɗauko Allonta ta biya masa karatu ya ji. Duk da idan ka cire karatun sallah shi kam Jahilin Ƙur’ani ne hakan bai hana shi jin daɗin karatun Asiya ba.

 Allah ya buɗa masa arziƙi amma hakan bai hana wani lokacin ya ji kishin ƙannensa Malam da Zakari ba, wanda suma Malamai ne yanzu domin sunyi karatu mai zurfi.

Dake idan Asiya tazo gidan Ale Faruƙ damunsu take da rigima shiyasa basa ma son zuwanta gidan musamman Fulani da Tabawa. Bata taɓa yin shiru idan aka gaya mata magana.

Bayan Gambo tayi yayinta ta ƙare, lokacin maganinta ya dena ci, a lokacin ne kuma Ale Faruƙ ya lalubo musu wata mata mai suna Yawo. Daga chan wani ƙauye ta fito wanda ake yawan cewa ƙauyen akwai mayu a wajen.  Ba budurwa bace dan aurenta bakwai amma tacewa Ale Faruƙ aurenta biyu. A rumfarsa suka haɗu ta zo siyayya, farar fatarta ya ja hankalinsa.

Sati biyu da tarewarta Ale Faruƙ ya fara ciwo. Idan ya tashi da safe sai yaji duk jikinsa na masa ciwo musamman hannu da ƙafafuwansa. Tun yana iya fita kasuwa har ya koma zaman gida saboda ko bai fita ba haka kawai jikinsa sai ya dinga ciwo. Ya je Asibiti an bashi maganin ciwon jiki amma duk da haka abun ba sauƙi.

Ana hakane kuwa biyu daga cikin ‘ya’yansa suka rasu mace da namiji dukkansu ‘yan ƙasa da shekaru goma. Abin duniya yabi ya isheshi, rashin fita kasuwa kamar yadda ya saba duk ya saka shi damuwa dan gani yake baza a kula masa da dukiyarsa kamar yadda ya kamata ba…

A gindin wata bishiyar giginya wasu mata guda uku suka haɗu a talatainin dare. Cikon ta huɗunsu ta taho tana basu haƙuri akan dalilin rashin zuwanta taron nasu da wuri.

“Ni kam Yawo keda kike da nisa ya akayi kika rigani zuwa?” Wacce ta zo yanzu tayi tambayar tana kallon farar cikinsu wacce duk da kasancewar dare ne sosai farin fiskarta na haskawa.

Yawo tayi dariya tace “ai dokina shegen gudu gareshi.  Gashi chan na ɗaure shi a wancan bishiyar”

Matar ta juya ta kalli inda Yawo ta nuna mata sannan ta ƙyaƙyale da dariya tace “ashe zaki bani aronsa idan zan je taron mutanenmu da za ayi na ƙasa”

“A ina za ayi taron?”  Wata tsohuwa tukuf a cikinsu ta tambaya.

“Wancan shekaran anyi a Kaduna ne amma wannnan shekaran a Ogbomosho za ayi”

“Kai yayi nisa ba zan je ba” tsohuwar ta faɗa tana lashe baki ganin naman da aka kawo musu wacce jaririyar Gambo ce da ko wata bata cika ba.

“Kai! Yawo gaskiya aurenki da Ale Faruƙ akwai daɗi. Kullum cikin ƙoshi muke”

Yawo ta baza haƙora tana dariya tace ” nan gaba naman wancan ‘yarsa daya fi so zan kawo, nasan ba ƙaramin daɗi za ta yi ba”

Dukkansu huɗun suka bushe da dariya marar daɗin ji.

Washegari Asma’u ‘yar Gambo ta rasu. ‘Yarta ta biyu kenan a gidan Ale.

Da yamma Mama da Asiya da matar Baffa Malam suka zo ta’aziyya gidan.

Suna falon Gambo Yawo ta shigo gaishe da Mama. Suna haɗa ido da Asiya ta fara mata murmushi. Asiya ta ce ” Maman Rabi’u ga wadda ta cinye miki Asma’u” gaba ɗaya sai suka maida dubansu ga Yawo da Asiyar ke nunawa.

Yawo ta kama salati tana salallami harda fashewa da kuka.

Mama ta kwaɓi bakin Asiya tace “bana son shegen surutu Asiya. A ina kika ji wannan banzar maganar?”

Asiya ta tura baki tace “in ta cinye duka ‘ya’yan Baba ai shikenan, nikam bazata iya cinyeni ba”

Mama ta ranƙwasheta tace ta rufe musu baki. Sannan ta shiga bawa Yawo haƙuri.

Maganar ta tsaya a ran Mama shiyasa da suka koma gida tace zata  faɗawa Gwani idan ya dawo daga tafiya.

Ranan da dokin Yawo ya je Ogbomosho washegari Ale Faruƙ ya tashi ko yatsarsa baya iya ɗagawa. Yadda ka san wanda jikinsa ya shanye haka yake kwance a sanƙare ko’ina yana masa ciwo kamar anyita dukansa da taɓarya.

Bayan kwana huɗu da rasuwan Asma’u Gwani ya dawo. Da ya huta Mama ta gaya masa abinda Asiya ta faɗa, tareda faɗa masa cewa ranan da suka dawo, da dare Asiya ta dinga sunbatu cikin baccinta tana cewa babu wanda zai iya cin namanta.

Gwani ya ɗau Allo ya rubuta ayoyin shifa ya wanke da ruwan zamzam ya zuba a gora ya miƙe da kansa ya wuce gidan ɗansa.

Lokacin daya isa gidan kai tsaye sashin Ale ya shiga inda Ale Faruƙ ke shimfiɗe a kan tabarma a tsakiyar falonsa. Fulani da ɗansa Bello wanda shine babban ɗansa namiji ya gani a kusa dashi suna ƙoƙarin bashi kunu.

“Ya jikin nasa?” 

“Yau kam Malam ko hannunsa ya kasa ɗagawa” Fulani ta amsa cike da tausayawa mijinta wanda duk yadda yake tana sonsa a haka.

Bello ya taimakawa Gwani wajen bawa Ale ruwan rubutu. Bayan ya sha, Gwani ya karanto addu’o’i ya tofa a hannunsa  ya shafa masa a goshi, hannu da ƙafafuwansa. Da yamma ma yazo yai masa haka, washegari ma ya sake zuwa yai masa haka safe da yamma.

A rana ta uku kuwa da Yawo ta tashi hawa doki zata je majalisansu doki ya ƙi tashi, tayi tayi amma inaa ya ƙi ko matsawa gefe hakan ya sa ta haƙura da ɗaukansa. Da ta isa majalisa ta kai ƙorafin abinda ya faru wajen shugabarsu tsohuwa Ayya. Ayya tace ai mahaifin Ale Faruƙ ne ke shirin ɓata musu aiki kada ta bari ya sake zuwa wajensa. Naman Asiya ma da suke son ɗauka shima abin ya gagara shiyasa suka koma kan ƙanwarta Farida ‘yar Halime wacce nan da kwana uku zasuyi abincin dare da ita.

Washegari ya kama kwanan Yawo dan haka ita ce ta kasa ta tsare a gefen Ale Faruƙ. Ƙarfe tara na safe sai ga Gwani ya zo yiwa Ale addu’a. Yawo ta garƙame falon da kwaɗo ta zauna a dakalin ƙofar shiga falon, yana zuwa tace masa Ale na barci yace kar a tashe shi.

Gwani yace ta buɗe masa ƙofa ya shiga ya dubashi ba zai tashe shi ba. Yawo ta tura baki tace sai dai ya dawo wani lokacin. Yadda ta dage ba zai shiga ba ya sa ya juya ya tafi, cikin ransa yana tunanin tabbas maganar Asiya gaskiya ce. Da yamma tareda ɗansa Malam suka zo, nan ma a ƙofar falon suka tarar da Yawo tana zaune daram kamar da safe. Wannan karan sai da Iyani da Fulani suka leƙo suna cewa Yawo ta buɗewa Gwani ƙofa domin tunda ya fara yiwa Ale addu’a suka fara ganin sauƙi.

Tana cikin magana Malam ya fito da wata dorina ya tsura mata a jiki yana faɗin “ƙarya kike la’ananniya, ƙarya kike Mayya”

Yawo ta saka ihu tana kuka.

 “Kin cinye masa ‘ya’ya za ki cinyeshi ko? Asirinki ya tonu” ya cigaba da zaneta. Ƙoƙarin gudu take amma Gwani da sauran Matan da yaran Ale kusan biyar sun tare wajen sun hanata gudu. Bello ma daya shigo bada jimawa ba itace ya sunkuco ya shiga taya Baffan nasa dukan Yawo.

Sai da Gwani ya tsaida su kafin suka dena dukanta. Ya tambayeta ta faɗa musu gaskiya. Yawo baki da hanci duk jini ta fara cewa ta tuba a yafeta.

Baffa Malam ya daka mata tsawa hakan yasa ta fara faɗan abinda tayi tace da gaske ne ita ta cinye yara uku a gidan amma Ale Faruƙ doki take da shi bawai cinyeshi zata yi ba.

Tabawa da ke gefe tayo kan Yawo da gudu ta fara dukanta tana yaguni. “Shegiya ɗan nawa shine doki, ɗan nawa kika mayar doki”

Da ƙyar Baffa Malam da Bello suka janyeta akan Yawo.

Gwani yace su ɗaureta kar wanda ya sake taɓata amma ina, samarin anguwa sukace basu yarda ba aka fita da Yawo ana bugu. Lokacin data suma aka fara ƙoƙarin ƙonata saiga wata tsohuwa ta ratsa cikin mutane ta zo ta taɓa Yawo shikenan ita da Yawo suka ɓace. Mutane  kowa yai ta kansa sai ‘yan tsiraru da suke da ƙarfin zuciya suka tsaya suna ihu suna faɗin duk ranan da suka kama Yawo ko wani maye ko mayya a garin ƙonashi za suyi.

Kwana uku da aka cigaba da yiwa Ale Faruƙ addu’a ya warke sarai kamar ba shi ba. Lokacin da yaji labarin cewa Asiya ce ta fara gane cewa Yawo Mayya ce hakan ya sa shi dagewa Gwani akan sai dai Asiya ta dawo gidansa da zama. Gwani bai musa ba tunda dai ‘yarsa ce ya dai jaddada masa akan koyaushe Asiya ta dinga zuwa karatu.

Bayan Yawo sai da Ale Faruƙ yai shekaru huɗu kafin ya ƙara wani auren.

Dr Saifuddeen Sa’ad Kachallah saurayi ne mai kimanin shekaru ashirin da bakwai a duniya. A rana ta farko daya shigo jami’ar Congo a matsayin malami a ranan ƙaddararsa ta haɗu da ta Misturah Sulayman Adeyemi. 

Da ya gama duk abinda zaiyi a ranan sai ya tattara kayansa ya wuce wajen motarsa. Ishirwa yake ji hakan ya sa shi wucewa wani kiosk da ake saida kayan masarufi da ke kusa da shi.

Yace da yarinyar da ke tsaye a shagon ta bashi ruwa mai sanyi na gora, yarinyar tace babu sai dai na leda. Saifddeen ya ɗan gyatsine fiska sannan ya ce “ok kawo” 

Yarinyar ta miƙa masa ruwa guda biyu a leda, lokacin ne kuma wata budurwa baƙa ta iso kiosk ɗin ta ajiye litattafanta akan kantan wajen tana huci tace “Abeg Bisi give me cold water” 

Ya kalli budurwar da tayi maganar. Baƙa ce amma ba sosai ba tana da ɗan jiki amma ba zaka kirata ƙatuwa ba. Ɗan ƙaramin mayafin data yafa ta cire ta fara fiffita dashi saboda yadda take haɗa uban zufa, da gani ta sha tafiya cikin rana.

“Sista Mistura e take ye easy”

“Omo iya ko easy oo, Professor Badmus fe pawa, wahala re ti po”

Saifuddeen ya kauda kansa daga kallon budurwar ya miƙawa mai shagon naira ɗari biyu.

“Ha! Oga i no get change oo”

Ta kalli budurwar tace ” abi Sista Misturah e ni change ke bami se?”

“E lo?”

“200”

“Haa! Kilo ra?”

“Omi meji”

Saifuddeen ya katse hiransu da cewa ” i’ll come back for it tomorrow”

“Ok Sir”

Har ya juya ya fara tafiya sai ya dawo. Ba lallai ya tuna da chanjin ba gara kawai ya sayi wani abin ya bar mata sauran.

Bayan ta miƙa masa coke mai sanyi daya buƙata yace ya yafe mata sauran chanjin.

“Ode ni Bobo yi”

 Budurwar ta furta a fili. Suna haɗa ido da Saifuddeen tayi saurin kauda kai dan gani tayi kaman ya ji abinda tace.

Bayan tafiyar Saifuddeen ita da mai shagon suka yi gulmar shi inda Baƙar budurwar ke cewa Saifuddeen irin sabbin ɗaliban nan ne masu rawan kai da burga.

Kwanansa biyu da fara aiki inda ya ke ɗaukan ɗalibai ‘yan aji uku da ‘yan aji huɗu sai kuma masu yin masters.

Bai saba cin abinci a waje ba amma takanas Dr Hassan da office ɗinsu ke kusa yazo ya ja shi akan suje cin abinci.

Canteen ɗin da suka je na wasu yarabawa ne, daga bakin wajen an rubuta *Iya Bola’s Food*

Ba laifi wajen ya haɗu akwai tsafta amma duk da haka dan ta Saifuddeen ne ba zai ci abinci a wajen ba.

Bayan an serving ɗinsu abinci suna ci ya hango baƙar yarinyar ranan tana serving wasu abinci. Dr  Hassan ne ya fara cinyewa inda ya ce da Saifuddeen zai wuce aji yanada ajin ƙarfe biyu. A lokacin bai san halin Dr Hassan bane ya jawoka cin abinci yatashi ya bar ka ka biya masa. Saifuddeen ya cigaba da cin abinci ahankali, lokacin daya gama ya zauna saboda wajen da ake biyan kuɗin a cike yake da ɗalibai, gaskiya wajen ana ciniki.

Yana zaune baƙar yarinyar tazo kwashe masa kwanuka.

“How much?” Ya faɗa a hankali 

“400” 

Arhan abincin da ya ji ya sashi ce mata na duka biyu yake nufi. Ta kalli ƙwayar idonsa sannan ta kauda kai tace ” still 400″

Chanjin naira ɗari zata bashi amma yace ya yafe mata ya miƙe ya bar wajen ya bar Mistura da buɗe baki.

A ranan daya sake zuwa wajen shi ɗaya ya zo Mistura na ganinsa ta zo wajen da sauri 

“Mr keep the change what can i serve you?”

” jolof rice and fish”

“With Dodo abi with chips?”

“What’s Dodo?” Ya faɗa bil haƙƙi saboda bai sani ba.

Baƙar yarinyar ta ƙyalƙyale da dariya harda kama baki.

“Oga Ajebo, dodo is fried plaintain”

” Ok with Doodoo” ya ja sunan kamar dodon tatsuniya.

Lokacin da ta kawo abincin ta tambayeshi ko a aji ɗaya yake sannan a wani faculty.

Jin yace shi ba ɗan aji ɗaya bane ya sa ta tambayi ajinshi. Yai shiru yana kallonta saboda kamar kowa itama tunanin ɗalibi take masa. Ko ranan daya fara shiga aji ma ɗalibansa kallon raini suka masa sai da suka ji yace shi zai ɗaukesu darasi sannan jikinsu yai sanyi.

Lokacin da ta kawo masa abinci ta tambayeshi sunansa. Ya amsa da cewa

“Saifuddeen”

“Misturah, 400 lvl Economics. Tunda ka ƙi faɗamin wani aji kake, i can bet cewa ba zaka wuce 100lvl zuwa 200lvl ba”

“Miyasa kika ce haka?” 

“Kana yi kaman wani JJC”

Saifuddeen yai murmushi  ga mamakinsa sai ya ji tace ” kana da kyau and i love your smile”

“Misturah…Misturah…”

“Maaa” ta amsa tana barin wajensa da sauri.

Cikin sati biyu da yai yana zuwa wajen sai gashi ya san komai nata. Shi kansa ya rasa dalilin daya sa ya zama regular a wajen kuma in har bata wajen ba zai ci abinci ba sai ya tabbatar tana nan kuma ita tayi serving ɗinsa.

Iya Bola mai saida abincin Ƙanwar Mahaifin Misturah ce kuma a wajenta ta taso tun tana shekara takwas. Ita ce ta ɗauki ɗauyin karatunta har yanzu da take final year.

Bai sanar da ita ko shi waye ba saboda ya sani yadda ta sake jiki da shi idan har ta san lecturer ne ba zata kula shi ba. Da bakinta tace masa bata mu’amala da malamai.

A sati na biyar da fara koyarwarsa aka bashi ajinsu Misturah. Farfesan daya ke ɗaukansu ya tafi wani conference na sati uku a ƙasar America.

Dr Kachallah ɗalibai da Malamai ke kiransa kuma sunan ba baƙo bane a wajen Misturah dan taji labarin tsaurinsa a wajen ɗalibai ‘yan Pol science.

Lokacin da course rep ɗinsu ya gaya musu cewa Dr Kachallah ne zai ɗauki darasin Prof Badmus ta ji daɗi saboda ta tsani Prof Badmus, kowa ma a ajin ya tsaneshi domin yadda fiskarsa ke da muni haka zuciyarsa take. Yanada tsauri, baya sassautawa ɗalibai ko kaɗan gashi ba wai ya iya koyarwa bane dan ba a gane darasinsa.

Abinda Misturah ta sani gameda Dr Kachallah shine shi ɗin sabon Lecturer ne kuma yaro, dan sun ji ƙishin-ƙishin ɗin ko shekaru talatin bai kai ba sai dai akwai kwanya.

Lokacin daya shigo tana ƙoƙarin karanta wani journal ne da ya ke da nasaba da project topic ɗinta. Nitsuwar da ajin yai ya sa ta ɗago idonta car acikin na Saifuddeen da ke tsaye a wajen podium na ajin.

Da muryarsa mai sanyi yai bayani akan shi zai cigaba da ɗaukansu darasin Prof Badmus kafin ya dawo.

Sunan daya rubuta akan allo ta ƙurawa ido, da manyan baƙi ya rubuta *SAIFUDDEEN SA’AD KACHALLAH*

Sun gane darasin da yai musu sosai, sai dai matsalarsa ɗaya wato yawan jefo tambaya idan yana bayani. Haka kawai sai ya nunaka ya tambayeka wani abu sannan baka isa kace baka sani ba dan shi a ajinsa babu kalmar i don’t know. Ya fi so ko baka sani ba ka yi abinda bature ke cewa attempt, dole sai ka faɗi amsar a naka fahimtar.

Misturah kam kasa nitsuwa tayi dan gani take idonsa na kanta ko kuma idan yai tambaya ya nuna mutum yace YOU gaba ɗaya sai ta ji ƙirjinta ya buga dan gani take kamar ita zaice.

Basu taɓa fahimtar darasin Prof Badmus irin na yau ba. Daga su ‘yan Economics har ‘yan Political science da suke yin darasin tare kowa ya yarda akwai banbanci a koyarwar Dr Kachallah data Prof Badmus nesa ba kusa ba.

Daya gama darasi ya bada damar ayi tambaya yawanci matan ajin suka dinga ɗaga hannu suna masa tambayar shirme dan dai kawai ya kulasu.

Kamar kullum bayan yayi sallar Azahar  Iya Bola’s food ya wuce ya samu waje ya zauna yana jiran Misturah sai dai ko mai kama da ita bai gani ba. Kwana uku ya jera yana zuwa wajen baya ganinta. A rana ta huɗu sai ya zo da wuri ya kuwa ci sa’a tana nan.

“Sir mi za a kawo maka?” Tayi tambayar kamar a yau ɗin ne ta fara ganinsa.

“Misturah ya kamata muyi magana…”

“Munada Semo, sakwara, Amala, Eba, white rice, jollof rice…”

Miƙewa yai ya bar mata wajen, ta bi bayansa da kallo cike da mamaki.

Daga ranan bata sake ganinsa ba dama gudunsa ta fara yanzu kuma sai ta fara dakon zuwansa amma shiru. Idan yazo ajinsu kuwa ko gefen da take baya kallo hakan yai matuƙar damunta. Wasa wasa gaba ɗaya ta rasa nitsuwarta. 

Bayan sati ɗaya da yin hakan ta kasa ɗaukan shirunsa, ta kasa ɗaukan sharewar da ya ke mata.

Ta nemi inda office ɗinsa yake ta je ta sameshi dai dai zai fita ya tafi gida.

“Sir kayi haƙuri ranan…”

“No no no, ba laifin ki bane. I should have told you the truth tun ranan da kika tambayeni a wani aji nake”

“Kenan baka fushi dani?”

Sai da ya ɗau jakarsa sannan ya ce ” na baki space ne saboda kince bakya son kowacce mu’amala da malaminki. A da ni ba malaminki bane amma yanzu…”

Sai bayan sati huɗu daf za a fara exams da Prof Badmus ya dawo ya karɓi ajinsa tukunna Misturah ta sake jiki da Dr S S Kachallah. A lokacin da su kayi hutu lokaci zuwa lokaci ya kan je gidansu. Tun Iya Bola na mata faɗa akan mu’amalarta da Saifuddeen har tazo ta haƙura tunda ta nuna mata cewa ba soyayya suke ba sannan kamalar Saifuddeen ya sa Iya Bola ta fara yarda da shi. Gaba ɗaya kasancewarsa ɗan babban gida bai sa mishi girman kai ba.

A wajen Misturah ne Saifuddeen ke iya sakewa ya faɗi son ransa yai abinda ya ga dama. A wajenta ya koyi cin abincin da yake da nasaba da ƙabilun kudancin ƙasar. A wajenta yake iya sakewa ya fayyace mata damuwar ransa, a wajenta ya samu ƙwarin gwiwar fitar da rubutunsa na waƙoƙi wanda ada sai dai ya rubuta ya zuba su a wardrobe. Dalilinta ya wallafa littafin rubutattun waƙoƙi  da pen name Jabir Al Jabir yayi amfani da sunan na shekaru biyu kafin daga baya da suka rabu da Mistura ya koma amfani da suna KaSaSa.

Sai da Misturah ta gama aji huɗu tana jiran sakamako kafin Saifuddeen ya bayyana mata cewa yana sonta. Faɗuwa ne tazo dai dai da zama dan a wajen Misturah kam tun kafin ta san shi malami ne soyayyar Saifuddeen ya shiga zuciyarta.

Duk da ya san ba lallai bane a amince masa ya aureta kasancewa shi ba Bayarabe bane amma kuma ya ɗaura aniyar sai inda ƙarfinsa ya ƙare akan neman auren Misturah. Lokacin daya faɗawa Sikiru mijin Iya Bola cewa yana son ya turo magabatansa bai yi mamaki ba da yace masa sai ya nemi izinin ‘yanuwansa a chan gida.

Letter Sikiru ya fara turawa chan garinsu ya musu bayanin waye Saifuddeen amma da aka dawo da amsa sai ya ga cewa wai basu amince Misturah ta auri bahaushe ba.

Mamaki ya kamashi dan da alama basu fahimci wani Kachallan yake nufi ba. Haka ya shirya ya wuce garin Akure. Lokacin daya fayyace musu asalin wanene Saifuddeen Kachallah mantawa sukayi da batun kudu da arewa suka ringa kiran ai Nigeria ɗaya ce kuma ya kamata a daina nuna banbance-banbancen ƙabila ko yanki. Cikin kashi ɗari na danginsu kashi tamanin da biyar sun amince da auren bayan sun ji kuɗi da mulkin gidan da Saifuddeen Kachallah ya fito.

Bayan Saifuddeen ya samu amsar daya ke so daga wajen Sikiru sai ya gabatar da buƙatarsa na son auren Misturah wajen Alhaji Sani. Ga mamakinsa sai yace masa ko zai auri wata mace to bayan ya auri Bilkisu ne, dama jira yake ta ƙarisa jarrabawarta na ƙarshe ta dawo ya haɗasu aure.

Ba zai taɓa iya yiwa Baba musu ba shiyasa ya amince da hakan. Sun taso da Bilkisu kuma tsakaninsu akwai jituwa sai dai bai taɓa sawa ransa zai iya auren mai irin halayen Bilkisu ba. Girman kai, Shagwaɓa, kasala, zafin rai  da ma ra’ayin ƙin talaka sune halayenta da suka sha banban da tashi. A matsayin ‘yar uwa yana sonta amma a matsayin matar aure gaskiya…

Lokacin daya faɗawa Misturah hukuncin da aka  yanke masa ranta ya ɓaci sosai har take ce masa dama halinsu kenan ‘yan arewa, gashi tun bai aureta ba yana mata maganar kishiya. Sai dai soyayyar Saifuddeen ta rufe mata ido shiyasa ta amince zata zo gidansa a matarsa ta biyu.

Wata ɗaya da rabi Bilkisu ta shigo Nigeria, tazo ta tarar da tsarin da aka shirya mata. Za ayi bikinta da Saifuddeen nan da watanni biyu sannan za ayi na Misturah da Saifuddeen wata bakwai bayan aurensu lokacin Misturah ta gama bautan ƙasa.

Da soyayyar Saifuddeen ta taso kuma tun kafin ta tafi jami’a ta riga ta sanar da mahaifinta cewa idan ya haɗa aurenta da wani ba Saifuddeen ba bazata aure shi ba.

Lokacin data tsara rayuwar aurenta bata tsara cewa za tayi tareda wata bare ba. Ita da Saifuddeen za su gina rayuwarsu kuma babu wacce ta isa ta shiga tsakaninsu.

Sati biyu bayan ta iso Nigeria tasa aka fara yiwa Misturah transfer daga inda take bautar ƙasa kusa da Jahar Congo zuwa chan kudu. 

Bata taɓa ganin Misturah ba sai ranan data je gidansu ta kai mata letan relocation ɗinta tareda kashedin duk ranan data sake shigowa Congo saita sa an yankata sannan idan har bata sa an kashe maganar aurensu da Saifuddeen ba zata sa a kashe Iya Bola da iyalenta, ba nan ta tsaya ba har Akure tace za ta je tasa a ƙona family house ɗinsu da duk wanda ke ciki.

Dama anacewa Yarabawa da tsoro. Tuni Iya Bola da Sikiru suka shiga bata haƙuri yayinda Misturah ta riƙe takardan da aka miƙa mata tana furzar da numfashi mai zafi…

Ƙila Saifuddeen ba zai taɓa sanin dalilin tafiyar Misturah ba domin ranan daya je hira gidansu wasiƙarta Iya Bola ta bashi inda a wasiƙar Misturah ta bayyana masa cewa ba zata iya zuwa gidansa a ta biyu ba. Daren ranan duk yadda ya daure sai da yai hawaye saboda Misturah itace macen daya fara so a rayuwarsa. Bai nemeta ba kuma har bayan ya auri Bilkisu bai nemi inda Misturah take ba saboda shi mutum ne da baya son takurawa ɗanuwansa. Duk da yana sonta sosai amma hakan ba zai sa shi tursasa mata ba. Sai da shekaru suka ja kafin watarana daya haɗu da wata ƙawar Misturah ta gaya masa cewa Misturah tayi aure a Lagos. 

***

Tarihin gidan Kachallah ya samo asali daga ainihin wanɗanda suka kafa garin Congo. Lokacin yaƙe-yaƙe da Jihadi duka sunan gidan na nan. Sunada alaƙa mai ƙarfi da gidan Sarauta dan ko yau wani ya fito daga tsatson Kachallah yace zai zama Sarki babu wanda zai ja dashi dan kusan shekaru ɗari uku da suka wuce anyi Sarki Kachallah a garin wanda yai mulki na shekaru shabakwai.

Alhaji Habu Kachallah tareda matarsa Khadija wacce yanzu ‘ya’ya da jikoki ke kiranta da Hajiya Dadda sun haifi ‘ya’ya shida tare. Mariya Kachallah  itace ta farko wacce yanzu ita da mijinta da ‘ya’yanta suke zaune a Saudiyya, dan aƙalla yanzu zata kai shekaru arba’in a Saudiyya. Na biyun shine Sani Kachallah sannan Fatima Kachallah wacce ta jima da rasuwa amma ta bar ‘ya’ya uku a duniya. Aminatu Kachallah wacce kowa ke kira da Hajiya Umma ta shekara arba’in da biyu da mijinta kafin rasuwarsa kuma Allah bai bata haihuwa ba sai dai ita ta raini ‘ya’yan Yayarta Fatima wato Aisha, Abdullahi da Umar. Na biyar ɗinsu shine Sa’ad Kachallah sannan Hauwa Kachallah.

Alhaji Sani Kachallah ya auri mata biyu. Ta farkon Hajiya Maryam ta rasu ta barshi da ‘ya’ya biyu Fatima Batula da Aminatu. Yayinda matarsa ta yanzu Hajiya Aisha ta haifa masa Rufaidah, Bilkisu, Saudah, Khadija da kuma Halima.

 Sa’ad Kachallah a jami’ar Dares Salaam ta ƙasar Tanzania ya haɗu da Aysha Ali Jallow lokacin yaje wani conference ita kuma tana ajin ƙarshe a jami’ar.  A wajen conference ɗin sau uku tana ɗaga hannu tayi tambaya hakan ne ya saka ya shaida fiskarta har yaji ta burgeshi. Daga baya da aka gama taron ya nemi sanin ko ita wacece kuma bai sha wahala ba saboda ita ɗin ɗaliba ce mai ƙwazo da tayi suna a jami’ar.

Kaman wasa ya mata tayin soyayyarsa ranan farko daya je wajenta, amsar da zai fito daga bakinta shine ” I love Nigeria” daga haka bata ƙara da cewa komai ba hakan ya sashi tunanin ko bai mata bane. Wata ɗaya da komawarsa London ya samu wasiƙarta inda take cewa ‘yar fulanin Gambia zata je gida idan da gaske yake ya je ya samu mahaifinta amma ya shirya yaƙi da danginta duk da ma ta san ‘yan Nigeria jarumai ne.

Ousmana Jallow babban mutum ne a ƙasar Gambia, Shanu da Raƙuma da Allah ya azurta masa shi kansa ba zai iya lissafta adadinsu ba. Bafulatani ne mai riƙo da al’ada fiyema da addini wani lokaci. ‘Ya’yansa uku ne maza Aodullahe Jallow, muhammadou Jallow da kuma Ali Jallow. Gidansa ba a auren bare hakan ya sa yisu-yisu fulanin yankin kawai suke aure. Fulanin Senegal, Cameroon, Niger ko Nigeria duk bare ne a wajensa.

ya riga ya shirya haɗa auren jikarsa Aysha da kuma Boubacar ɗan Aodullahe Jallow, jira kawai yake ta ƙarisa bokon da ubanta ya sakata dole tayi sannan ayi biki. Fiqhu da psychology take karanta amma Fiqhun kawai aka gayawa Alhaji Ousmana shiyasa ya amince da karatun ba dan ya so ba sai dan yana son Ali  sosai.

 Yaƙi ne kawai bai tashi ba lokacin da magabatan Sa’ad Kachallah suka zo neman auren Aysha Jallow. Sannan ita Ayshar ta nuna Sa’ad take so Mahaifinta kuma ya goya mata baya tunda a cewarsa bai san da maganar za a haɗa ‘yarsa da Boubacar ba.

Cikin ‘ya’yan Ousmana Jallow Ali ne yai boko mai zurfi dan alokacin ma ya haɗa Phd ɗinsa a ɓangaren Economics.

Abu dai ta kai ta kawo saida Ousmana Jallow yace ya cire hannunsa a lamarin Ali da iyalinsa, yayi duk abinda ya so. 

Ali Jallow riƙaƙƙen ɗan boko ne da ko kaɗan baya so a tauye hakkin wani, shiyasa ma da ya nuna sai tilon ‘yarsa  tayi boko bai ji shayin ko mahaifinsa zai yarda ko ba zai yarda ba. ‘Ya’ya biyu ya haifa, namijin ƙanin Aysha ya rasu tun yana watanni kaɗan da haihuwa.

Ali bai damu ba da ‘yan uwansa suka ja baya da shi. Sanda magabatan Sa’ad suka dawo ya sa bikinsu nanda watanni huɗu lokacin Aysha ta gama karatunta.

Lokacin da akayi bikin abokanansa da ‘yanuwan matarsa ne kawai suka shaida amma nashi ‘yanuwan ba wanda yazo. Ousmana Jallow ya yi alƙawarin fishi da duk wanda yaje bikin. 

Haka akayi biki Amarya da angonta suka wuce Nigeria. Bikin nasu da watanni shida Ali Jallow da matarsa sukayi hatsarin jirgin sama lokacin zasu koma ƙasar America saboda aiki da aka bashi a United Nation (majalisar ɗinke duniya).

Labarin yazo wa Aysha daidai tana laulayi mai tsanani hakan yasa ta birkice sosai dan soyayyar uba da ‘ya dake tsakaninta da mahaifinta ba kaman na sauran ‘yanuwan mahaifinta Fulani bane. Mahaifinta zai zauna da ita suyi taɗi, ya saurari matsalarta ya bata shawara ba wai ya tursasa ta ba. Mahaifinta tamkar babban abokinta ne dan shaƙuwarsu da shi ta fi ta mahaifiyarta.

Kaman baki wata biyu bayan mutuwar Ali Jallow da matarsa Sa’ad Kachallah yai hatsari ya rasu yana hanyarsa ta zuwa airport zai je London. Wannan mutuwar ta girgiza Aysha matuƙa dan sai data koma tamkar wata zararriya. Cikinta na wata shida alokacin amma har ranan data haihu cikin ciwo take. Lokacin da ake nema mata magani ne wani malami yace ko kaɗan kar a bari ta bar gidan dan sammu ne a kanta,  idan suka bari ta fita ba zasu sake ganinta ba. Kullum cikin tsaronta ake kuma Alhamdulillahi maganin da ake bata ya sa bata samu ta gudun ba. 

 Ba ayi sunan Saifuddeen ba ta rasu hakan yasa Saifuddeen Kachallah bai san iyayensa ba sai a hoto da kuma bidiyon da akayi na biki dana wasu tarurruka da mahaifinsa ya halarta lokacin yana raye.

Sunyi mamaki matuƙa da babu ko ɗaya cikin ‘yanuwan Aysha da ya zo bayan an aika musu rasuwarta, infact sharesu suka yi kamar ba alaƙar dake tsakaninsu.

A ɓangaren Boubacar Jallow kuma ya kaɗu matuƙa da ya ji mutuwar Aysha. Shi ya saka a kashe Sa’ad sannan a hana Aysha zaman Nigeria, sannan shi ya sanar da Ousmana Jallow cewa Aysha da ɗan data haifa sun mutu dan shine ya karɓo wasiƙar da aka rubuto.

Kasancewar suna zargin sammun da aka yiwa Aysha daga ‘yanuwanta ne shiyasa tun Alhaji Habu Kachallah na da rai ya hana a kai Saifudden wajen ‘yanuwan mahaifiyarsa.

Rashin haihuwar ɗa namiji ya saka Alhaji Sani Kachallah ya ɗaura duk wata soyayyarsa akan Saifuddeen. Shi ya zaɓa mishi makarantar da zai je da abinda zai karanta wato political science inda bayan Saifuddeen yaje chan ne ya ɗauki major biyu wato Communication and Political Science a postgrad kuma yai History and International relation.

Saifuddeen ya fara koyarwa a jami’ar Congo har ya kai matsayin Professor yana shekaru talatin da biyar a duniya. Yayi Rector na Congo Polytechnic na shekara ɗaya da rabi har lokacin kuma yana koyarwa a Jami’a kafin Alhaji Sani yasa a bashi Kwamishinan ayyuka na jahar daga nan kuma ya jawo shi cikin siyasa tsundum inda rana tsaka yace masa “congratulations Saifu, kaine mataimakin Gwamna na jihar nan” ya yi maganar tun ma ba a fara maganar zaɓe ba sai gashi watanni kaɗan bayan haka Saifuddeen Kachallah ya tsinci kansa wajen yawon kamfen har kuma a kwana a tashi ya tsinci kansa a mataimakin Gwamna, sannan yanzu alƙalamin ƙaddararsa ta juya, ya wayi gari shine Gwamnan jihar Congo…

*GUZURIN TAFIYA*

“Asiya….Asiya”

Juyowa tayi ta kalli Mama ba tareda ta amsa mata ba.

“Ba za ki je ki gaida Baban naki ba. Sau biyu yana aikowa wai kije”

“Mama zan je gobe, na gaji”

“Ba abinda kika yi tunda kika zo gidan nan sai kuka. An gaya miki kuka na maganin matsala ne. Tashi maza ki shirya ki je ki gaishe shi kafin Magariba ta ƙariso”

“Mama ba zan iya fita yanzu ba. Dan Allah ki bari sai gobe”

“To ki kirashi ki gaya masa zaki je goben”

Hannu data ɗaga zata jawo jakarta sai data rintse ido saboda yadda zuciyarta ke sukan ƙirjinta. Missed calls ta gani dayawa a wayar wanda na Ubayd ne yafi yawa. Tun isowarta ta turawa Umma text ta sa wayar a silent ta jefata cikin jaka.

Numbar Ale ta kira taji shi a kashe, hakan ya mata daidai dan ba son magana da shi take ba.

“Numbarsa a kashe take” ta faɗa da muryar da yafi kama da raɗa.

“Ki tashi kiyi wanka kizo ki ci abinci. Haka kawai ki hana kanki sakewa saboda a kanki aka fara yaɗa jita-jita”

“Tashi maza kin ji. Barin cewa Ladi ta ɗeba miki ruwan zafi”

“Toh”

***

“Sumayye, Sumayye”

“Na’am Baba”

“Uban me kike a ɗakin ne. Ki fito mu tafi ko na barki a nan”

“Gani zuwa Baba”

Minti ɗaya sai ga Sumayya ta fito daga ɗaki sanye da hijabi ruwan toka wanda saboda akwai duhu zaka ɗauka baƙi ne. Babu wuta shiyasa gidan ya ɗau duhu, wata da taurari kuma  a daren kaman sunyi ƙaura.

Wayar latsawa ce a hannunsa amma yana dannata da ƙarfi kaman wanda idan bai yi hakan ba ba za tayi aiki ba.

“Baba gani”

Ya ɗan yi murmushi saboda bazawararsa da suke chatting tace tana jiransa ya zo ya ga kwalliya.

“Baba gani fa”

“To fasa mun kunne Sumayye.”

Sumayya ta fara tura baki wanda ba dan dare bane kuma hankalin Ale na kan bazawararsa  da ya gani.

“Kin ɗauko kazar?”

“Na ɗauka”

Ficewa sukayi daga gidan dan yana sauri daga wajen Asiya zai wuce wajen masoyiyarsa Lubabatu.

Cikin motarsa ƙirar peugeot 406  fara wacce aƙalla ta bawa shekaru shatakwas baya ya ɗau Sumayya suka wuce gidan Gwani wanda yanzu ƙannensa da iyalensu ke zaune a ciki.

Masallaci ya fara tsayawa ya gaisa da Baffa Malam wanda ke koyarda ɗalibai karatu sannan ya wuce cikin gida ɗakin Mama.

“Gashinan Anty Asiya Ale yace a kawo miki Kaza. Ni na soyata da kaina”

“Ki ajiyeta Summy ba zan iya ci ba”

“Dan Allah ki tashi ki ci”

“Salamu Alaikum”

“Amin Alaikas Salam. Bismillah”

“Ina wuninku dai” 

“Lafiya, Sannu da zuwa Ale Faruƙ” 

Mama ta miƙe daga kujera ta koma bakin gado gefen Sumayya.

Bayan sun gaisa da Mama sannan ya maida dubansa ga Asiya ya tambayeta ya hanya.

Daga inda Asiya ke kwance ta amsa masa da lafiya.

“Mama bata da lafiya ne? Ko za a kira Malam ya mata rubutu ko Asibiti zamu wuce?” yai maganar ba tareda ya tsaya ya ja numfashi ba.

“Taƙi cin abinci ne fa tunda ta iso”

“Wai haka Asiyata? Ke Sumayye baki bata kazarta bane?”

“Baba gashi nan ita tace ba zata ci yanzu ba”

“Ki daure dai ki ci kinji Asiya”

Kaman gaisuwar ce kawai ta kawoshi sai kuma bayan shirun minti biyu ya fitar da abinda ke ransa.

“Ke Sumayye ki bamu waje”

Bayan Sumayya ta fita daga ɗakin, Mama ta fara ƙoƙarin miƙewa Ale yace ta zauna.

“Asiyata ya jikin dai” bai jira amsarta ba ya cigaba.

“Wai asalin kuɗin da akace ‘yan adawan sun baki nawa ne? Tun da safe Malam Yusha’u da Alhaji Ɗansabo suke musu akan kuɗin nan, ni dai nace duk kuɗin Umaru Kwom ai ba zai baki ƙasa da Miliyan biyar ba ko?”

Kaman wanda aka tsikara haka Asiya ta miƙe zaune tana yiwa mahaifinta kallon  ƙurilla kamar yau ta fara ganinsa.

“Ba sai kowa ya san asalin kuɗin ba Asiya. Kinga bikin ki ya kusa idan kika bani miliyan biyu ko uku a ciki zan juya miki shi kafin lokacin biki”

Magana take son yi amma kukane ya ƙwace mata. Abin nata ya kai har mahaifinta ya tsaya musu da wasu akan kuɗin da ba ta san da su ba. Ba ma wannan ba, ashe har sunanta ya ɓaci a garin da take iƙirarin cewa nan ne asalinta.

“Lah! Daga tambaya sai kuka. To kiyi haƙuri”

“Ale Faruƙ inaga dai gara ka barta ta huta zuwa gobe sai kuyi maganar”

Bai musawa Mama ba ya miƙe ya musu sai da safe ya fice daga ɗakin. Sumayya dake zaune a balbalin Baaba Ladi matar Baffa Malam tana ganin Ale ya fito daga ɗakin Mama tayi saurin miƙewa ta wuce ɗakin da sauri.

Lokacin da ta shiga ɗakin kuka ta samu Asiya ke yi. Tayi saurin ƙarisawa wajenta ta shiga jijjigata tana bata haƙuri.

***

“Shi Malam Nuhu mijin uwarta ne, shi kuma Ale Faruƙ Uban daya haifeta kenan. Inaga dai chan garin nasu kawai zamu je saboda ayi komai daga tushe”

“Kana jina kuwa Saifu?”

“Baba, Bilkisu…” Gwamna ya faɗa cikeda damuwa 

“Idan ta dawo ka turo min ita, za muyi magana”

Daga haka bai sake cewa komai ba. Shima Gwamnan ajiyar zuciya ya sauke ya cigaba da taraddadin abinda zai faru idan Bilkisu ta dawo taji maganar auren daya ke shirin yi…

A daren ranan Gwamna ya wuce gidan Abba. Tunda ya fara yiwa Abba bayani Abban bai ce uffan ba, kansa na ƙasa ya kasa ɗaga ido ya kalli Gwamna. Magana ne yayi a taƙaice amma nauyinta zai iya kaiwa nauyin treloli goma.

Ba wai bai yarda da maganar Gwamna bane daya ce zai auri Asiya ne saboda ya kare rayuwarta. Girmansa ya wuce ya zo har gida ya masa ƙarya. Gaskiyarsa ya faɗa sai dai gaskiyar nauyi gareta. Idan har zai yi tunanin cewa auren Asiya shi zai sama mata lafiya to kuwa tabbas abinda ke bibiyan Asiya abune mai girma.

Asiya ‘yarsa ce kuma lafiyarta shine abu na farko da zai fara dubawa sama da komai. Ƙila ƙaddarar Asiya kenan, ƙila tsakaninta da Ubaydullahi sai dai alaƙar Ya da ƙanwa.

Ya kai minti biyu bai iya cewa komai ba. Ya sani, indai su Alhaji Sani Kachallah suka je gaban Ale Faruƙ gobe to an riga an gama dan maganar aurenta da Ubayd ta tashi kenan. Ya ji daɗi da Gwamna ya girmama shi bai manta cewa Ubaydullahi shine saurayin da zai auri Asiya ba.

“Ba a kai sadaki ba. Mun tambaya ne kuma an bamu kuma har an saka lokaci. Shi Ubayd akwai kuɗin sadakinta daya ajiye a wajena zuwa idan lokaci ya ƙarato sai na baiwa magabatanta, amma tunda Allah ya rubuta ba matarsa bace zan maida masa kuɗin gobe da safe idan Allah ya kaimu”

“Malam Nuhu…”

“Your Excellency nagode daka karramani, ka bani girma har kazo da kanka ka sanar dani komai. Ina addu’ar Allah yasa wannan haɗi ya zamo alkhairi a rayuwar Asiya”

Gwamna ya so yai wata maganar amma bashi da bakin yi. Duk abinda zai faɗa ba zai chanja abinda Abba zaiyi tunani akansa ba.

***

Kwanaki biyar kenan da zuwan Asiya gida. Kwana biyun farko zazzaɓi mai zafi ya sata a gaba. A kwana na uku ne ta samu ta fara warwarewa saboda ta rage tunani da kuka. Umma ta kan turo mata saƙo na ƙarfafa gwiwa kullum sannan Mama ma kullum tana cikin yi mata nasiha akan haƙuri da kuma yarda da ƙaddara.  A wannan lokaci ta so ace Gwani na da rai. Yadda duk lokacin data shiga damuwa yake karanto mata tarihin Nana Asiya dan ya nuna mata mai sunanta jaruma ce da bata taɓa karaya ba. 

*”Kina tunanin Allah ba zai jarrabce ki bane?”*

Kalamansa kenan ranan da tazo ta sameshi tana kuka saboda Ale Faruƙ ya gaya mata cewa ya karɓi kuɗin aurenta a hannun Alhaji Talba. Tana shekaru shabiyar alokacin, Alhaji Talba kuma zai iya kaiwa shekaru hamsin da biyu zuwa da biyar. Da kuka wiwi ta iso zauren Gwani inda yake koyarda wasu manyan Almajirai dama wasu ɗalibai magidanta dake ɗaukan karatu a wajensa.

Bayan sun keɓe ta fara bayani

“Shi Baba komai kuɗi komai kuɗi. Ni gaskiya ba zan yarda ya sayar dani ba, ai bance masa aure nake so ba. Ni gaskiya karatu zan yi” tayi maganar cikin kuka.

“Ishiru Uwata, faɗa mini mi aka miki?”

Asiya ta goge hawaye ta zayyane masa duk abinda ya faru kan cewa Ale ne da safe ya gayawa Iyani da Fulani cewa su shirya karɓan baƙi gobe za a kawo kayan gaisuwar Asiya.

Ta haɗa da cewa ” shi Baba rayuwarsa ta ƙare a kuɗi da mata. Abin kunya kwanakin baya daya saki Delu ina Bibalo ya auro. Bibalo fa, yarinyar da tun tana ƙarama take fama da  taɓin hankali. Tsofai tsofai da shi ya ɓata mata rayuwa gashi Aljanunta sun hanata zama a gidansa”

Jin irin maganganun nan na fitowa daga bakin jikarsa zuciyarsa ta shiga ƙunci. Yai saurin karanto Isti’aza a zuciyarsa sannan ya riƙo hannun Asiya yace 

*”Kina tunanin Allah ba zai jarrabce ki bane?”*

Tayi shiru tana kallonsa. Ya cigaba da yi mata nasiha tareda cewa ba abinda zata iya yiwa Ale sai dai ta rinƙa masa addu’ar Allah ya shirya shi, domin shi ɗin Uba ne gareta hakan kuma ba zai chanja ba har abada.

Bayan wannan abinda ya faru Gwani ya kira Ale Faruƙ ya masa faɗa yace bai hanashi aurar da ‘yarsa ba idan ya ga hakane mafi alkhairi amma matuƙar yana raye ba zai taɓa bari ya mata auren dole ba kuma ko yayi bai yafe masa ba.

Saboda fasa auren da akayi Alhaji Talba ba ƙaramin rigima sukayi da Ale ba dan sai da suka yi kaca-kaca da shi.

Wannan dalilin ne kuma yasa Asiya ta dawo gidan Gwani da zama permanently har lokacin data samu admission a Congo University ta koma gidan Ummanta da zama.

Ale Faruƙ na kasuwa aka zo aka sameshi da zancen daya saka shi shiga mota ba takalmi dan har sai daya fita daga motar ya tunkari motocin Alhaji Sani Kachallah daya taka wani ƙaramin kara mai tsini ya lura cewa ashe babu takalmi a ƙafarsa. Wannan bai karya masa gwiwa ba yai saurin cire karan a ƙafarsa sannan ya ƙarisa motar daya ke tsakiya wacce yake tunanin a nan babban baƙonsa yake.

Samun buɗi ya sa Ale Faruƙ ya gyara ƙofar gidansa dama sashensa, wanda yanzu falo biyu gareshi ta farko ta karɓan baƙi ta biyu kuma wanda yake kallo ya ci abinci sannan anan yake zama da ‘yan uwansa da abokansa na kusa lokaci zuwa lokaci.

Lokacin da Alhaji Sani ya fito daga mota har ƙasa Ale ya durƙusa yana kwasan gaisuwa fiskarsa washe kaman an masa albishir da Aljannah. Jiki na rawa ya masa jagora da tawagarsa ta mutum uku zuwa falonsa. Sai da suka zazzauna ya sake risinawa ya gaida su. Alhaji Sani da wani tsoho da yake tunanin zai kai shekaru casa’in sun girmeshi sosai amma sauran biyun ɗaga cikinsu zai kai sa’an Bellonsa sai ɗayan kuma dai zaiyi sa’an ƙaninsa Zakari.

Ƙokarin fita ya nemo musu ruwa yai amma Alhaji Sani ya dakatar da shi yace idan akwai wanda zai kira ya kira domin sun zo neman auren ‘yarsa ce.

Ale Faruƙ ya ɗau waya ya fara kiran Baffa Malam yace ya zo maza-maza akwai manyan baƙi na jiransa. Bai san wacce cikin ‘ya’yansa ake so ba amma cikin ‘ya’yan dake gabansa mata da suka kai aure ba suyi aure ba, su biyar ne. Asiya data haura ishirin, Nafisatu da Ɗayyiba da suke shatakwas sai Sumayya data ke shabakwai sannan Baraka dake shashida. Koma waccece a cikinsu Alhaji Sani na nunawa to ya bashi ita ne kawai, babu mahalukin daya isa ya hana. Gwani ne ya isa ya dakatar da shi akan lamurran ‘ya’yansa kuma Allah ya jiƙan rai ya jima acikin ƙasa.

Malam Audu maƙocin Ale ne ya fara isowa kafin Baffa Malam da Baffa Zakari wanda dama jiran baƙin suke dan tun jiya da dare Abba ya kira Baffa Malam ya sanar dashi abinda Gwamna yace da kuma matakin da shi ya ɗauka na janye neman da ɗansa ke yiwa Asiya. Baffa Malam da Baffa Zakari sun tattauna tsakaninsu kuma sun zuba ido ne tun jiyan suga yadda komai zai wakana tunda magana irin wannan Ale ne zai yanke hukunci ba su ba.

Minti bakwai da zuwan Malam Audu  suma suka iso, dake kujerun sunyi kaɗan A ƙasa suka zauna tunda uban gayyarma a ƙasa suka sameshi. Duk da Alhaji Mustafah Kachallah Baffa a wajen Alhaji Sani ya nemi su Baffa Malam su zauna a kujera, Baffa Malam da Malam Audu ne kawai suka zauna a kujera.

“Na bayar” Ale Faruƙ ya faɗa tun kan Alhaji Mustafah ya ƙarisa bayaninsa.

“Idan hakane zamu ajiye sadakin yarinyar da kuɗin mun gani muna so idan yaso a hankali sai a kawo sauran abubuwan. Sannan kuma idan babu matsala muna so nan da sati biyu ko uku a ɗaura auren”

“Wallahi ko yanzun nan kuka ce a ɗaura mun shirya”

Baffa Malam ya bi Ale da ido. Kuɗi ai ba hauka bane. Tunda ya shigo falon ya lura da yadda Yayan nasa ke yi kaman wani wawa a gaban waɗannan mutane. Ya yarda suna da kuɗi sunada matsayi, suna  da daraja a idon al’umma. Amma ba wannan bane zai sa kuma su basu wuƙa da nama a lamarin auren ‘yar su. Sunada ‘yanci ai. Ya dai yi shiru ne kawai saboda sanin halin Yayansa da yai, abune mai sauƙi a wajensa idan yai magana ya fara masa gori cewa ai shine Uban Asiya.

Miliyan ɗaya cash aka ajiye musu. Sadaki dubu ɗari biyar sauran dubu ɗari biyar kuma kuɗin na gani ina so kamar yadda suka faɗa. 

Su Baffa Malam ne suka raka baƙin waje  yayinda Ale ya shige ƙuryar ɗakinsa yana neman wajen yiwa kuɗin mafaka.

Sanda ya fito zai bisu ya ci karo da kayan da aka jibge a ƙofar falon, tarkacen kayan gaisuwane su buhun gishiri, buhun suga, kwalin sabulai, kwalin minti da cingam, damin goro kusan kashi goma da kuma ƙwaryan Zuma guda uku. 

Ya haɗiyi yawu ya yi waje da sauri lokacin har motocin baƙin sun riga sun juya…

***

“Ba zaku maidani mahaukaciya ba Baffa.  Ta ina za’a karɓi kuɗin aurena bayan akwai maganar aurena da Ya Ubayd. Baffa kaima ka koma son abin duniya ne kaman Baba?”

“Zauna Asiya”

“Noo Baffa. Ka gayamin gaskiya, kuɗi da mulki sun fara tsole muku ido kuma?”

“Ki zauna aka ce miki ko” Baffa Zakari ya daka mata tsawa.

“Wannan abin yafi ƙarfinmu.  Amma duk abinda kika gani ya faru da bawa to rubutacce ne daga Allah. Ki yi haƙuri ki rungumi ƙaddara. Insha Allah zamu cigaba da yi miki addu’a Allah ya tabbatar da alkhairi a rayuwarki”

“Shikenan dan kunga Gwani baya raye sai ku yanke hukunci bisa son zuciya. Baffa wannan son zuciya ne, da ku da Baba duk dukiya ce ta tsole muku ido. Ba zan auri kowa ba sai Ya Ubayd”

Daga haka ta bar musu ɗakin da gudu.

Ranan ƙarfe bakwai na yamma a gidan Abba ya mata. Tayi ta kiran nambobin Ubayd amma duka a kashe su ke. Hankalinta ba zai iya ɗaukan wannan abin ba. Ta yarda da ƙaddarar data faɗa mata na abubuwan da suka faru da ita cikin kwanakin nan. Yanzu ma maganarta ya ja baya a duniyar yanar gizo an koma gulmar wani ɗan film da aka ce yana luwaɗi.

Umma ma kamar kowacce Uwa ta damu da halin da ‘yarta ta shiga musamman data ganta a fige kamar kazar sadaka.

Ta yi iya baƙin ƙoƙarinta wajen nuna mata cewa hukuncin da aka yanke mata ana mata zaton alkhairi ne ba sharri ba.

” Addu’a shine abinda ya rage miki yanzu Asiya ba kuka ba”

Maganar Mama kenan lokacin da ta riƙe  mata ƙafa tana kuka akan ta tayata roƙon Baba da Baffaninta.

Itama Umman sunan addu’a take kira mata. Addu’a, Addu’a, Addu’a. Ta fa gaji da jin wannan suna.

Lokacin da tace zata fita, Umma cewa tayi sai dai dole su tafi da Gwani ko Aliyu. Dake Aliyun ne ke kusa shine ya rakata gidan su Umma Hussaina.

Rabonta da gidan ma zai iya kaiwa shekara.

Ta tsammanci samun Ubayd a gidan amma aka ce mata yayi tafiya.

Ta jima tana zaune a ɗakin Umma Hussainan kafin daga baya ta haƙura ta miƙe ta tafi ko sallama bata yiwa Umma Hussaina ba.

Damuwa kan chanja tunanin mutum matuƙa. Wasu lokutan Asiya sai ta shirya zata gudu sai ta fasa, wani lokaci kuma tayi tunanin ta kashe kanta ma kawai ta huta. A wasu lokutan kuma tayi tunanin samun bindiga ta je ofishin Gwamna ta bindige shege kowa ma ya huta. Wani lokacin kuma tayi tunanin ta haukace kawai saboda a dakatar da komai. Wasu lokutan ma zuciyarta na riya mata cewa ƙila ba Ale Faruƙ bane ubanta. Abin da ya fi riƙe mata rai ma bai fi yadda Ubayd ya ɓace mata ba, ga numbarsa da har yanzu bata shiga. 

Ta fara tunanin ƙila Gwamna ne ya sa aka ɗauke shi, an ƙi faɗa mata ne kawai.

Sati ɗaya tayi a gidan bata san inda kanta yake ba. Abba da Umma kullum suna nuna mata ta saki ranta komai zai zo ya wuce amma zuciyarta bai shirya ma yarda da zancensu ba balle har ya amince da shi. Ubaydullah shine masoyinta na farko kuma na ƙarshe, ita tunda ta taso ma bata taɓa son wani ba, ko crush na primary ko secondary school bata taɓa ba. Ubayd ta fara so tun lokacin da ya ɗauka mata tsumman abunta, tun lokacin bata san so ba.

Saboda Ubayd bata taɓa bawa wani damar shiga rayuwarta ba. Ko lokacin da take Jami’a da tayi tashe, samari ke mata chaa babu wanda ta taɓa buɗewa ƙofa. It has always being Ubayd and will always be.

Yayinda Asiya ke fama da damuwa, a chan gida kuwa Ale Faruƙ ya kasa ya tsare wajen ganin wannan biki ya tafi yadda ya kamata. Sati ukun nan gani yake kaman ba za su iso ba. Tun yanzu ya fara kiran kansa sirikin Gwamna har tambayar siriki yai da turanci aka ce masa Inlaw amma idan shi ya faɗa sai kaji kamar ‘yanlo yace.

Yi masa kirari da sirikin Gwamna kaga ya ɗau kyautan dubu ya baka mutumin da ɗarinsa idan ba a mace ba baya iya bayarwa. 

Tuni yasa aka yiwa gidansa sabon fenti. Matansa da sauran yaransa duk ya musu ɗinkin biki kala biyar biyar hatta yayyen Asiya da ke gidajen mazajensu ya aika musu da nasu kayan. Wannan kashe kuɗi ko a sallah albarka. Shi dai yanada abu ɗaya gidansa ana cima mai kyau amma wani siyan kayan sawa ko na ado to ko a sallah sai anyi da gaske, yawanci ma iyayen ‘ya’yan ke musu. Haka batun makarantar boko idan ka wuce sakandare sai fa ka tallafawa kanka. Mace ɗaya ce tayi karatu a ‘ya’yansa mata bayan Asiya, itama kuma a gidan mijinta tayi. Adda Hadiza kenan da ta karanci ɓangaren midwifery. 

***

“It was for political reasons Bilkisu” 

“Shine sai dai naji a bakin Babana”

“Sanda kika dawo bana gari  kuma wannan magana bata waya bace”

“Saifuddeen ka rasa wacce zaka aura sai ‘yar Kurma jikar maiƙusumbi” ta tintsire  da dariya.  “I’m sure ba wai zaka nemi haihuwa da ita bane ko? dan ba zan juri ganin ‘ya’yan guragu, kutare da makafi a gidan nan ba”

Gwamna yai seƙeƙe yana kallonta. Ita ce dai da take zuwa gidan marayu tana ɗaukan hotuna da naƙasassun yara.

“Na ɗauka baka ƙyamar nakasassu Bilkisu”

“Oh please Saifuddeen. Ka sani sarai campaign nake yi”

Ido ya zuba mata ya rasa ma mi zai ce. She never seizes to amaze him.

 

“And Darling, ka sani zan haƙura ne kawai saboda lokacin campaign ya kusa, bana son abinda zai ɓata maka ƙuri’u. Abu na ƙarshe kuma shine ka nema mata wani gidan dan a nan” ta juya yatsarta manuniya “ni kaɗaice Matar Gwamna”…

Back to top button