Uncategorized

Sanadin Labarinah Chapter 2 By Hafsat Rano Zafafa2022

SANADIN LABARINAH

HAFSAT RANO


              Free Page (2)


©®Hafsat Rano 

***Rayuwar ta tun bayan da ta bude ido ta ganta a gaban baffan ta, bata san wani abu daya danganci mahaifiyarta ba, bata san wacce irin rayuwa mahaifiyar ta tayi ba har zuwa ranar da ta koma ga mahaliccin ta, ranar da ta zama silar zuwan ta duniya itace ranar da tayi silar mutuwar ta. 

   A duk lokacin da ta bukaci sanin wani abu na daga sashe na rayuwar ta sai Baffa yace mata ba yanzu ba, sai ta girma ta mallaki hankalin kanta. Ta kan yawan tuna mahaifiyar ta duk da iyakar sanin hoto kawai tayi mata,amma ta gaza manta zanen fuskarta a cikin zuciya da kwakwalwarta. A yau da ta samu wani abu da ya danganci mahaifiyarta sai taji tamkar ta san wani sashe na labarin ta, wani sashe me matukar muhimmanci a kundin rayuwar ta. Sake damke su tayi da kyau, ta samu kasan kayan ta, tayi musu boyo me kyau, irin boyon da zaka yiwa duk wani abu me matukar muhimmanci a gareka.

    Gidan su ta shiga kanta tsaye cike da karsashin ganin ta, tayi saurin fadawa kanta cike da murna da dokin ganin ta, rungumeta tayi a jikin ta tsam zuwa wani lokaci kafin ta saketa tana dariya.

Karanta>>>> Babu So Chapter 2 By Billyn Abdull

“Jidda.”

“Na’am…” Ta amsa cike da zumudi sannan ta zauna a gefen ta, 

“Ya jikin naki?”

“Da sauki.” 

“Sannu. Allah ya kara sauki.”

“Amin.” Ta amsa sai ta mike, taje ta kawo mata ruwa sannan ta fita zuwa dakin ta, ta tura kofar ta shiga ta soma harhada kayanta waje daya, zuciyar ta cika fal da farin ciki. Kasancewar kayan ba masu yawa bane yasa ta gama hade su kaf, ta fito zata koma taji suna magana da Baffa sai ta fasa ta samu waje ta zauna har sai chan da aka kwala mata Kira, ta tashi da sauri taje, Baffa yace ta dauko kayanta tazo.

      Zama tayi a gaban baffan ta tankwashe yar kafarta, kayan ta dake cikin yar karamar ghana most go ta sake rik’ewa gam tana sauraron maganganun dake gudanuwa tsakanin Baffan da Innajo.

“Jidda amana ce a wajenki Innajo babu yadda zan yi ne amma da babu yadda za’a yi na rabu da ita, sai dai tana bukatar kulawar uwa a halin yanzu, dan haka na baki amanarta, idan kika ci amanarta ba zan yafe miki ba, ita din marainiya ce, bata san mahaifiyar ta ballantana wani dangi na kusa, ni kadai ne gatanta, sai ke yanzu da na damka miki amanarta a hannunki.”

“In sha Allahu zan rike amana, nagode nagode da karamcin ka gareni, in sha Allah Jiddah ba zatayi kuka ba, kuma nayi alkawari duk sanda akayi hutu zan kawo maka ita nan, nayi wannan alkawarin.”

“Shikenan,ubangiji Allah ya baki ikon rike amanar da kika dauka.”

“Ayi dai mu gani idan iska zata hura wuta.” 

Lami tace tana daga kan kofar dakin ta, kallon ta Baffa yayi ya girgiza kai kawai, itace ummul’aba isin da yasa zai bawa kanwar tasa Jidda, ba dan haka ba babu yadda zai ya rabu da ita dan ganin ta kadai yake rage masa kewar marigayiya, amma babu yadda ya iya, hakan shine maslaha akan irin kuntacacciyar rayuwar da Jiddan take fuskanta a cikin gidan mahaifin nata a gaban idon sa bashi da ikon hanawa ko tsawatarwa saboda lalurar da ta sameshi ta ciwon kafa. 

“Ku tashi ku tafi kar kuyi dare a hanya, Allah ubangiji ya kaiku lafiya.”

“Amin Baffa.” Tace cikin yar siririyar muryarta da take nuna tsantsar yarintar ta

“Allah ya kiyaye kinji? Ki rike abinda na fada miki kar kiyi wasa dashi, in sha Allah ba zaki yi kuka ba.”

Da kai ta amsa masa, ta mike Innajon ta mika mata hannu ta karbi kayan, sannan tace

“Zamu tafi Lami, sai ki zuba ruwa a kasa kisha, kuma in sha Allah sai mugun nufin ki ya koma kanki.”

Karanta>>>> Inayah Chapter 2 By Mamuhgee

Abun ka da me jiran kiris sai gata a tsakiyar tsakar gidan tana huci tayi kan ta

“Ke har kin isa ki fadan magana? Waye be san rayuwar wahalar da kike a gidan miji ba, bora wadda bata da maraba da yar aikin gidan.”

Wani kallo Innajo tayi mata, maganar tayi mata mugun ciwo amma sam sai taki nunawa, ta rike hannun Jiddah ta soma tafiya

“Yaya mun tafi, Allah ya kara lafiya.”

“Amin, Allah ya tsare, ki kirani da zarar kun sauka dan Allah.”

“In sha Allah.”

Cikin daga kafa suke fice daga gidan, ya saka hannu ya share guntun hawayen da suka zubo masa, kansa a kasa yana sauraren maganganun da Lamin take ta farfad’a cikin daga murya dan Innajon ta jiyo ta. Sai da taji tashin motar su sannan ta shiga daki tana cigaba da sababi.

***Mota ce irin golf din nan Alhaji yayi mata shatar ta, su biyu ne a bayan motar lokaci zuwa lokaci sai ta kalli fuskar Jiddah tayi mata murmushi, maganganun Lami sun yi matukar tasiri a zuciyar ta, bata da maraba da bora kamar yadda ta fada amma ya zatayi? Ta ta kaddarar kenan, zata jira zuwa lokacin da Allah zai kawo mata dauki ko ta samu sauki a zuciyar ta. Tafiya ce ta kimanin awa daya da rabi sannan suka iso, daf da magriba me motar ya sauke su a kofar gidan, idanun Jidda suka fito waje tana kallon in da suka zo din, gida ne matsakaici me bakin gate, tura yar karamar kofar dake jikin gate din tayi hannun ta daya na rike da kayan Jiddan daya kuma hannun Jidda ne. Abu ce ta fara ganin su, ta taho da sauri ta karbi kayan hannun ta sannan tace

“Sannu da hanya Anty ” 

“Yawwa sannu Abu.”

Ta amsa sannan ta cigaba da tafiya zuwa wata kofa dake kallon gabas, irin kofar nan me hannu biyu,da glass me kauri a tsakankanin kowanne waje, duhun magriba ya mamaye babban falon nasu Amma duk da haka kana iya ganin mutane a zazzaune, sallama tayi yaran suka amsa, dama kuma su din ne zasu amsa uwar gayyaar ko kallo bata ishe ta ba, tana hakimce a saman kujera cikin yanayin rashin jin dadin ganin su.

“Anty sannu da zuwa.”

Yaran suka shiga jera mata sannu, Usman da Muhammad suka taso da gudun su, suka rungume ta, ta daga su sama daya bayan daya tana dariya.

“Anty wace wannan?”

Amira ta tambaya tana leken fuskar Jidda da ta rakube a bayan Antyn.

“Ina ruwan ki Amira? Bana son shishigi fa.”

Hajjajun dake hakimce ta tsawatar mata tana jan tsaki, murmushi Antyn tayi kawai ta girgiza kai sannan tace

“Yar uwa kuma kawa na kawo muku Amira, gata nan sunan ta Jidda.”

Shiru Amiran bata ce komai ba tana tsoron sake magana tasan halin Mama sarai zata iya bugunta akn haka.

“Muje Jidda, naji ma an soma kiran magriba.” .

Suka wuce su zuwa wani dogon corridor da zai sada su da bangaren Antyn, daidai lokacin aka kawo wuta, Abu ta ajiye kayan Saudan sannan tace

“An gama tuwon Anty, na fadawa Mama dai a zato na ko har na tafi baki dawo ba.”

Karanta>>>> Farhatal Qalb Chapter 2 By Nana Hafsat

“Sannu da aiki, kin yi saurin gamawa ma.”

“Wallahi, gani nayi garin damina, gwara kayi da wuri kafin ruwa ya sakko.”

“Gaskia kam.”

“Akwai abinda zaa yi ne kuma?”

“Umm, babu gaskia,zaki tafi ko?”

“Eh idan ba abinda za’a yi ba.”

“Babu, bari na diba miki yar tsarabar kauye ba dai yawa.”

“Aikuwa nagode Anty.”

“Zo Jiddah.” ..

Ta yafito ta da hannu, suka shiga daya daga cikin dakuna ukun dake dan madaidacin falon Antyn.

“Ga dakinki kinji, zauna bari na sallami Abu nazo sai na nuna miki yadda komai yake, ki saki jikinki kinji?”

Da kai ta amsa tana kallon dakin, fita tayi taje ta sallami Abun sannan ta dawo tace tayi alwala, itama taje dakin ta, tayi alwala sukayi sallar a tare, sannan ta kunna mata kallo tace tana zuwa. 

Part din Maigidan ta nufa bayan ta dora ruwa a saman gas din dake kitchen din bangaren nata, ta gyara masa dakin duk da kafin ta tafi ma sai da ta gyara amma tasan da gayya Maman zata bata musamman toilet, haka ko yaushe take sake gyarawa idan zata shiga ta bata sau dubu bata kuma taba tanka mata ba, yau din ma sai da ta sake gyarawa ta kunna turare sannan ta fito, ta dawo ta samu ruwan ya tafasa ta cika flask sannan tayi masa tuwon alkama wanda zai ci yanzu da kuma safe, ta zubawa Saudah a ciki ta kirawo ta kitchen din duk dan ta sake da ita, ta karba ta fita, Usman da ya gama zaman falon ya shigo ya haye kafar Jidda yana mata magana

Karanta>>>> Gurbin Ido Chapter 2 By Safiyya Huguma

“Kece Yayarmu da Anty tace zata kawo mana ke?”

Gid’a masa kai Jidda tayi, sannan tayi masa murmushi

“Zaka ci tuwo?” Tace masa tana kallon plate din dake gabanta.

“Naci tare da Muhammad, amma zan kara naki.”

“Toh muci.” 

Ta tankwashe kafarta shima sai yayi yadda tayi, suka shiga cin tuwon a tare, har suka gama Anty na ta kaiwa da komowa a tsakankanin bangaren Maigidan da nata, sai da ta gama hada masa komai sannan ta nutsu ta zauna taci abincin ta watsa ruwa dan a gajiye take jin ta sosai dan ba wani zama tayi ba tunda suka shigo. Wajen takwas da arba’in Baban ya dawo, sun idar da Isha Usman yayi bacci, Antyn tace itama Jiddan taje ta kwanta, ta rakata har daki ta nuna mata duk abinda zata bukata ta kawo mata ruwa saboda dare sannan ta dauko Usman ta dawo dashi dakin tayi musu addua sannan ta kashe musu wutar dakin ta nufi bangaren Baba.

***A zaune ta samesu da Mama, ta bararraje tamkar kwananta ne ranar, ta bude masa abincin har ya soma ci yana bata labarin kasuwa, wani banzan kallo maman ta watsa mata, tayi tsaye ranta na sosuwa da abinda ake mata, dagowa yayi ya kalle ta, 

“Halima, karaso mana kika ja tunga anan, kinga yayarki ko? Wai kin sha wahalar hanya shine take taimaka miki da wannan babban aikin.”

Yake tayi ta karaso ta zauna daga kubin damar sa, ta gaishe shi a ladafce ya amsa mata yana tambayar yadda ta baro su

“Ina fatan dai kafar Yaya da sauki.”

“Alhamdulillah dai toh.

“Allah ya bashi lafiya, zan yi kokari a weekend din nan naje na sake dubo sa, ina yar taki? Kin taho da ita ice ko?”

“Eh tayi bacci.”

“Ok madallah, na ganta gobe idan Allah ya kaimu.”

“Amin.” Tace sai ta mike ta shige bedroom din ta zauna a sanyaye, sama-sama take jiyo hirar su har wajejen goma na dare sannan taji tafiyar Maman. Kwanciya kawai tayi dan babu kuma bukatar ta sake komawa falon.

Karanta>>>> Babu So Chapter 2 By Billyn Abdull

GA TSARIN YADDA FARASHIN SU SUKE;

ZAFAFA GUDA BIYAR 1  PAGE 1 NA KOWANNE BOOK A KODA YAUSHE INSHA ALLAH . KAMAR KO WANI YI. FARASHIN NA NAN AKAN NERA DUBU DAYA

ZAFAFA BIYAR

Littafi daya 300

Littafi biyu 400

Littafi uku 500

Littafi hudu 700

Littafi biyar 1k

GURBIN IDO

SAFIYA HUGUMA

SANADIN LABARINA

HAFSAT RANO

INAYAH

MAMUHGEE

FARHATAL QALB

NANA HAFSAT

(Miss Xoxo)

BABU SO

BILLYN ABDUL

ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES!! WANNAN SASHI NE NA BANGAREN YAN ZAFAFA NA MUSANMAN DA KE SON KARANTA SHAFUKAN LITTAFAN ZAFAFAN SAMA DA DAYA. TO KU SHA KURUMIN KU. KUDIN VVIIP NA ZAFAFA NERA DUBU BIYAR NE KACAL NA DUKKANIN BOOKS DIN BIYAR. A KALLA A RANA ZAKU DINGA SAMUN SHAFUKA 10 KOWANNE BOOK SHAFUKA 2 KENAN.

PAY 5K FOR ZAFAFA BIYAR VVIP SUITE SECTION. MAXIMUM OF 10 PAGES DAILY, 2-2 PAGES OF EACH BOOK. MAKING 10 PAGES IN WHOLE. LITERALLY

SANNAN AKWAI TSARIN VVIP NA BOOK DAYA GA MASU RAAYIN VVIP NA BOOK DAYA KO BIYU KO UKU KO HUDU GA KUDIN SU KAMAR HAKA;

BOOKS HUDU 4500

BOOKS UKU: 3500

BOOKS BIYU: 2500

BOOK DAYA: 1500

BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK

4 BOOKS  4500

3 BOOKS : 3500

2 BOOKS : 2500

1 BOOK: 1500

MUNA TALLATA HAJOJIN KU CIKIN FARASHI MAI RAHUSA

TALLA SAMAN SHAFI

DAYA NA BOOK DAYA :1000

TSAKIYA 800

KARSHEN SHAFI 500

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

BANK NAME: ZENITH BANK

ACCOUNT NAME: HAFSAT UMAR KABIR

ACCOUNT NUMBER: 2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA DA SHEDAR A TARE:

09134848107

 BIYAR_

*_INAYAH_*

_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*

_BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK_

_4 BOOKS  4500_

_3 BOOKS : 3500_

_2 BOOKS : 2500_

_1 BOOK: 1500_

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107

Back to top button