Uncategorized

Rundunar Sojin Najeriya ta zata hukunta wata Soja saboda yin soyayya da dan bautar kasa

 Rundunar Sojojin Najeriya ta ce tana ladabtar da wata Soja da ta tsunduma cikin shaukin soyayya da wani dan bautar ƙasa a wajen horar da masu yi wa kasa hidima (NYSC).

 Kakakin rundunar, Onyema Nwachukwu, ne ya bayyana hakan a wani martani ga wani bincike da PREMIUM TIMES ta yi a ranar Lahadi.

KARANTA: “SHIN KO UWARGIDAN SHUGABAN KASA BUHARI TANA DA CIKI KUWA?”

 Wani faifan bidiyo na wani dan yiwa ƙasa hidima da wata soja mace a sansanin horas da masu yi wa ƙasa hidima NYSC a jihar Kwara a kwanan baya ya bazu ta yanar gizo.

 A daya daga cikin faifan bidiyon, an ga dan bautar ƙasar da sojar suna tattaunawa a wani wurin da ake kyautata zaton filin faretin ne na sansanin Yan bautar ƙasar.

Daga nan ne kuma suka ci gaba da tattaunawa a tsakanin su har aka ga ya dauko zobe ya durkusa a gwiwa daya ya yi wa sojan tambayar shin ko zata amince da kudirin sa.

Daga nan ya ci gaba da sanya mata zoben a ɗan yatsanta, dukkanin su cike da farin ciki gami da murna.

 A wani bangaren na bidiyon kuma an nuna yadda masoyan suka ci gaba da musayar kalaman soyayya, har dan bautar ƙasar ya cire wa sojan hula ya saka a kansa.

 Daga nan sai suka fara sumbatar juna  cikin jin daɗin ba tare da sanin cewa  sauran membobin ƙungiyar suna ɗaukar su ba. 

 Bayan faruwar lamarin dai an samu labarin cewa Sojoji sun tsare sojan, lamarin da ya sha suka sosai a shafukan sada zumunta.

KARANTA: “SHATU GARBA YAR KANO TA LASHE GASAR SARAUNIYAR KYAU TA NAJERIYA 2021”

 A martanin da ya mayar, Mista Nwachukwu ya ce rashin da’a ne ga mai horawa ya yi hulda da wadanda ya ke horar da su.

 Ya bayyana lamarin a matsayin ‘yan uwantaka ta fuskar soja.

 Ya ci gaba da cewa babban rashin da’a ne ga ma’aikatan soja su rika yin soyayya yayin da suke sanye da kaki.

 “Rundunar Sojin Najeriya tana da  dokoki da ka’idoji da ke jagorantar jami’an mu a duk lokacin da aka tura su bakin aiki.

 “Sojan macen da ake magana a kai ta keta dokokin aikin soja.  Na farko, ’yan uwantaka a lokacin da suke aikin hidima a sansanin NYSC.  Wato shagaltuwa da sha’awar dangantaka da wanda ake horaswa.

 “Na biyu, dole ne ma’aikaci ya yi aiki na tsawon shekaru uku, kafin ya cancanci yin aure.

 “Na uku, ta bijire wa ka’idoji da umarni na amfani da kafafen sadarwar zamani na Sojojin Najeriya.

 “Na hudu, yin soyayya a lokacin da take sanye da kayan aiki”

KARANTA: “GWAMNA AMINU TAMBUWAL YA BADA UMARNIN A KAMO MAWAƘIN DA YA WAƘE BELLO TURJI”

“Na biyar kuma, halinta bai dace ba ga kyakkyawan tsari da kuma horon soja.  Duk abubuwan da ke sama, idan sun tabbata sun saba wa dokokin da ba su da kyau tare da ladabtarwa.

 “A matsayinta na ma’aikaciya, aikinta shi ne horar da ‘yan bautar ƙasa kuma kada ta kulla wata alaka da kowannensu,” in ji shi.

 Mista Nwachukwu ya ce, da tunanin jama’a zai bambanta da a ce soja namiji ya nemi wata mace da ta yi horo, ya kara da cewa (jama’a) za su ga ana cin moriyar hakan.

 “An samar da wadannan ka’idoji ne da nufin samar da ingantaccen shugabanci da kuma da’a a cikin Sojoji.  Idan zan iya tambaya, idan sojan namiji ne fa?  Ta yaya jama’a za su fahimci matakin nasa?  Tabbas, da an yi la’akari da cewa yana yin lalata ne da ita wadda yake horaswa. 

 “Haka kuma a nan.  Sojojin Najeriya kamar sauran su, muna da ka’idojin ladabtar da su, sabanin na sauran al’umma.  Kowane ma’aikaci da kansa ya dauki nauyin aiwatar da wannan doka,” in ji shi.

Back to top button