Uncategorized

Matar makaho Part 18 complete hausa novel

 MATAR MAKAHO

Chapter 18

Babane tsaye akan kafarsa yana gyara yayin dake kan bukkar sa, da mamaki Al’ameen yace ikon Allah baba menake ganin nan?

Da sauri baba ya juya da mamakin ganin Muhammad ya dawo daidai lokacin nan, Alhalin ba lokacin ake tashi aiki ba, lafiya ka dawo yanzun?

Kai zan tambaya dai baba, na ganka tsaye akan kafafunka, kaida ka karye?

Zoka zauna muhammad muyi magana?yace yana zama akan taburma.

Ba musu Al’ameen ya zauna a kusa da baban.

Muhammad ina fatan kaga abinda nake so ka gani koh?

Da sauri Al’ameen ya warware rawanin sa, kamar ya baba kuma me kakeso na gani?

Muhammad Abinda yasani yin haka badon kome bane, illah don naga kaje da kanka gidan sarkin nan, tunda na ganka jikina ya bani wani abu, kamar dake tsakanin ka da muhibbat da muwaddat ya baci sosai, haka sarki ma duk da rabona dana ga fuskar sa, bazan iyya tuna ranan ba Saboda dadewar da nayi bana gani, Amma fa ka sani nasan sarki tunkan yahau mulki,  yanda kaga fuskar ka, haka fuskar sa yake sai dai ka nuna masa yaranta?

Me kake nufi baba bangane ba, wai sarkin da naga fuskar sa a rufe kana nufin yana kama da yara biyu dana gani innan?

Kwarai muhammad duk da dai akan samu mutum, ya samu mai kamar sa a duniya Amma kaman ku dasu Akwai alamun jini.

Baba ni bani da kowa a nijar fa bansan kowa a nan ba.

Toh Amma kaman nin ku, ku hudun nan yayi yawa muhammad?

Bamu hudu bane mu biyar ne, da kanwa ta.

Muhammad niba yaro bane, Amma tunda kace haka shikenan, amma dai zaka cigaba da zuwa aiki har lokacin da na yanke akan zancen kafata, tunda ba kariyar gaske nayi ba baikamata na koma ba yanzun?

Shikenan baba zan cigaba da zuwan,har randa zaka koma aikin, ina su gidado ne tunda na shigo ban gansu ba?

Sunje kasuwa yi mana sayayyan kayan abinci.

Tashi muhammad yayi ya ibi ruwa ya shiga band’aki wanka yayi ya shige d’aki ya kwanta, tunanin duniya ya dame sa, duk sanda ya lumshe idanunsa yaran nan yake gani wanda baba yace masa muwaddat da muhibbat wai suna kama da sarki, kenan suna kama dashi, kai shikam bai gane kan Al’amarin nan ba, wani zuciyar na kawo masa wani tunani,  amma kokarin tunkude sa yake don yasan abune da kamar wuya.

Yana kwance har gidado da badaru suka dawo kasuwa, yana jinsu suna ta girki da jido ruwa Amma bai koh fita ba.

Har suka kammala aikin dare abinka da gidan gauraye, bayan sunci abinci suka wuce masallaci.

Daren nan sukutum muhammad baiyi bacci ba, sai kusan asuba bacci ya d’auke sa.

Washe gari muhammad yaje aiki kamar jiya bayan sun gama shayin safe,  yaukam had’a masa akayi da yawa a tire, ya wuce dashi falon , da sallama ya tura kofar falon ba kowa a falon sai kamshin turare dake tashi aka tsakar falon, wucewa falon maimartaba yayi a hankali ya tura kofar da sallama.

Sarauniya ce cikin Alkimba a zaune akan kujera hannunta dauke da kumshen lalle ja abinka da farar fata sosai yayi kyau, sai sarki dake kujeran sa na special kamar kullum fuskar sa a rufe, sai muwaddat da muhibbat dake zaune akasan kushin sai tsohowar nan dake zaune a kujera tana magana da nabila, ke nabila nafa fahimci babu wanda ya bata ku sai lawiza(sarauniya) ace mutum ya dage sai yayi turanci abinda bama amfani muke dashi anan ba?

Kai mahmah karfa ki manta a abroad nake karatu kuma ashan basu san wani abu wai French koh buzanci ba,  da turanci kawai ake Amfani kinga kuma nan gaba muwaddat da muhibbat suna gama secondary suma chan zasu, shiyasa nake saba musu tun a gida mahmah, nabila tace.

Murmushi sarauniya lawiza tayi tana kallon mijinta da kwata kwata hankalinsa baya wajen su, hankinsa bama a wajen su yake ba, hawaye ne ya cika mata ido, ta rasa yaushe ne ita da yaranta zasu samu lokacin sa? abu tsawon shekaru abu d’aya, tun yaransa na kanana suke korafi har yanzun sun girma har yabi jikinsu, Abban muwaddat……bata karasa ba sukaji sallamar muhammad.

Amsa masa mahmah tayi, ya karaso cikin falon yana gaidasu da turanci lawiza da su muwaddat ne suka amsa sarki kam koh d’ago kansa baiyi ba bare Amsa gaisuwa, mahmah kam baki ta kama sai kuma tayi shuru batace kome ba.

 a kan table ya aje shayin ya siyaye a kofuna yazo ya aje musu, yana kokarin tashi saiga wasu zaratan maza sun shigo falon cikin sallama, maza ne guda biyu d’ayan zaikai shekara 40 d’ayan kuma zaikai 33 zama sukayi akan kujerun falon suna gaida mah mah da buzanci bayan ta amsa suka juya wajen sarki sauka gaidashi hannu kawai ya d’aga musu.

uncle Ango, nabila tace tana dariya

Hararan ta mai shekara 33 yayi ke wallahi bana wasa dake? zan saba miki fa.

Dariya muwaddat ta sake kai uncle jiya mafa aunty Amarya tazo  school namu, ta kawo mana special Anko in mu na yaran Ango.

Ganin bakin yasa muhammad siyaye musu shayi suma, don shidai duk hiran da suke baji yake ba, kasancewar da yare suke magana, yazo ya jera musu a gaba, har zai mike kawai kafarsa ya taka na nabila, 

 ai da sauri ta mike cikin masifa, kai wallahi kaji na rantse maka ka fita idanuna, kai wani irin masifa ne,haka kawai kabi ka sani a gaba da fitina tunda ka fara aiki a gidan na kake takalata tun jiya?

Kiyi hakuri don Allah bada sanina bane, muhammad yace da sauri yana matsawa gefe duk da sumayya ta masa rashin mutunci a farkon zamansu, Amma bata taba masa a cikin mutane ba, koh zata masa masifa sai insun kasance su biyu, amma wannan a gaban sarki take masa zagi haka bataji kunyar mulki ba? a take yaji wani irin tsanar yarinyar.

Ke nabila matsalata dake kenan rashin hakuri da rashin kunya, d’aya daga cikin mazan ya fad’a yana mamakin rashin kunyar nabila

Gaskiya nabila halinki sai Allah ace ke a rayuwar ki rashin kunya ne baya baki kunya a gaban Abba kike irin wannan tsewar kamar ba sarki bane a gaban ki?

Kunya ne ya kamata da sauri ta sunkuyar da kanta kasa, cikin sanyin jiki ta fita a falon, muhammad ma hakuri ya kara basu ya fita, yana fita yaga nabila tsaye alamu dai shi take jira.

Wallahi wallahi in baka fita idanuna ba zan maka rashin mutuncin da ba’a taba maka ba, matsiyaci kawai shashasha duk cikin turanci take maganar.

Kala muhammad baice mata ba ya nufi kofa, sai masifa take Amma shi koh juyowa baiyi ya kara ganinta ba, yana gaba tana baya har suka fitoh a flat in sarki ta shiga nasu, muhammad kuma ya wuce sashen shayi.

*****************

Sumayya na bude kofar falon khadija ta gani tsaye da kaya a hannu, da mamaki tace”tsayuwar me kikayi a nan kuma,  kika kasa shigowa koh rashin gaskiya ne”?

Ah ah aunty yanzun nake kokarin shigowa.

“Aiko kwara ki shigo inkam” tace tana koma ta zauna a kan katifa.

A hankali khadija ta karaso falon kayan dake hannunta ta kai d’aki, sai kuma ta makale taki fitowa gabaki d’aya fargaba ne a Ranta, ganin fuskar sumayya a hade.

“Khadija wai tsayuwar me kike a bakin kofar nan ne da bazaki shigo falon ba”?

A hankali ta shigo falon tana rabe-rabe a jikin falo a nesa da sumayya ta tsaya.

“Waike khadija meye haka? zama zakizo kiyi muyi magana”

Kiyi hakuri Aunty wallahi ni bansan da maganar wayar nan ba, kawai sai naga ya bani shine fa danaki karba ya shigo falo.

“Nidai bance kome ba nace kizo ki zauna muyi magana”

A hankali ta matso ta zauna a bakin katifar.

Kallonta sumayya tayi “menene tsakanin ki da kalamu-wahid”?

Wallahi Aunty babu kome a tsakanin mu dashi kawai fa mutunci muke,  kuma aunty koh soyayya zanyi sai nayi da d’an yaron nan?

“Oh yaro koh lalle kam waya gaya miki ba’a auren yaro ai da ba’ayi da bazan aure yayanki ba”

Kai Aunty yayana fa ya baki shekaru 4 rus fa, Amma kalamu bazai girmeni da 2 years bama.

“Kwadaiji dashi wallahi ina nan ina zuba ido, kuma ga wayar taki saiki rike, tace tana mika mata kwalin wayar”

Amsa khadija tayi da sauri ta ruga d’aki da gudu tana murmushi don wallahi ba karamin son waya take ba.

“Khadija dawo nan”

Jin abinda sumayya tace yasa khadija dawowa ta zauna.

Kinga khadija waya a zamanin nan cikin kaso goma ya kwashe kaso 7 na hanyar lalacewar yara, sauran 3 nan sune ake amfanuwa, ki kula da wayar nan ban baki ita don kiyi abinda ranki yake so ba, kinga waya sirrin mutum ne wani bazaka taba tunanin koh yatsa aka saka masa a baki zai tauna ba,  Amma in aka amshe wayarsa abinda za’a gani bamai kyau bane?na barki ki rike wayar nan ne saboda kalamu Amma ki rufamin asiri ki ji tsoron Allah ki kiyaye shiga inda bai dace ba”

Insha Allah aunty zan kiyaye.

“Yauwa sannan zaki iyya hawa online Amma ban yarda ki d’aura hoton ki ba sam banaso” 

in Allah ya yarda Aunty

“Toh tashi ki tafi d’akin”

D’akin khadija ta shiga ta had’a wayarta daman oready ya saka mata wayar a cherge, ya saka mata sim suka, tana kunna wayar aiko ta shiga latsawa, ya sauke mata facebook whatsApp da instagram harda telegram duk ya bubbude mata account, call ne ya shigo wayar da sauri tayi picking ganin  rubuta daya bayyana Nurul-Qalbi a screen in, tana d’agawa taji yayi sallama hade da kiranta da kanwar sa.

da masifa ta fara magana, Allah ya sauwaka ka zamo yayana wallahi wane kai kaji na fad’a maka.

Shuru yayi bai mata magana ba, jin baiyi magana ba yasa ta dawowa hayyacinta cikin kunya ta Amsa sallamar, tana masa godiyan waya daya bata.

 baiyi magana ba har lokacin, ita ma shuru tayi kamar yanda yayi,sai da yayi minti biyu yace mata ta hau whatsApp ya mata messenge.

Kashe call in tayi ta hau whatsApp ganin akwai enough card a wayar.

Khadija kamfa gabaki d’aya yau waya ya d’auke mata hankali sosai, tana gama girkin ta, ta nuke a d’aki sai hira suke da kalamu,  Abin har yaso bawa sumayya dariya daga zaran khadija taji motsen zata shigo d’akin saita kifa wayar ta kama baccin karya, Amma batace mata kome ba tunda yanzun hutun makaranta suke, sai kalamun yazo zata masa fad’a maganar karatunsa karya biye shashanci.

Ranan fa khadija a d’aki tayi shimfida a kasan tiles ta kwanta da waya a hannu, sumayya ita kad’ai ta kwana a falo.

***************

Yau kwanar muhammad 25 yana zuwa aiki gidan sarauta, zuwa yanzun ya fara fahimtar Halin mutanen gidan sosai,  especially nabila ba karamin haushin yarinyar yake jib, bad’an kad’an ba, yau tun Asuba yayi wanka yabar gidansu,  kasancewar yaune za’a fara bikin kanin sarki(Ramadan) kamar yanda yaji ana fad’a, shiyasa tun asuba zasu tafi aiki,  don shirya shayi mai yawa da zai d’auke mutanen biki zasu wuni sha,  duk lokacin da aka nemi shayi a samu kar ya kasance babu, aiko hakance tun safe da sukaje basu zauna ba daman har yanzun ba’a sakar ma muhammad hannu ya girka shayi shi kad’ai ba,  anfi sashi ya rarrabawa mutane.

 yau haka ya wuni aiki saiya kaiwa flat innan yana dawowa a bugo telephone in kitchen ace yakai shayi, gabaki d’aya yayi mugun gajiya.

Haka muhammad sukayi ta fama da aiki har na tsawon kwana 4,  sai yau aka d’aura aure, da misalin karfe 4 na yamma liyafa aka had’a a tsakar farfajiyar gidan, manyan sarakuna da manyan kasa ne makil a ciki, masu kudi da shuni, tunda aka fara bikin sarki bai hallaci koh wani liyafa ba sai d’aurin aure da wanda yanzun ake, muhammad ne ya karaso filin yana raba shayi koh wani table yana aje musu nasu dayake taron na mazane da mata, kuma tarone na manya yasa Al’ameen yake bin kome sannu sannu karyayi kuskure koh laifi, kwala masa kira nabila tayi ganin ya wuce table nata da suke xaune da kawayen ta,  bai aje musu shayi ba zai tafi next table, kai malam bazaka kawo mana namu shayin ba!!

Cikin haushi yazo zai dongora mata shayin a gaban table inda suke, by mistake kafarsa ta harde da cafet inda aka shimfid’a a kasa, kawai shayin ya watsale sai jikin kawar nabila, ihu kawar ta saka wanda yaja hankalin jama’a, ai nabila na ganin haka batayi wata-wata ba ta tsinke muhammad da mari.

Kafun ta sauke hannunta muhammad ya bata wasu tagwayen mari hagu da dama, masu masifar zafi ihu da sake cikin azaba don a tsawon rayuwar ta bazata iyya tuna lokacin da aka bugeta da wayon taba.

Yayan nabila dake gefen su ne ya mike cikin zafin nama ya d’aga hannu zai wanke Al’ameen da mari, da sauri Al’ameen ya cafke hannunsa cikin matsanannin cin bacin rai ya nuna mustapha da yatsa, jikinsa har rawa yake cikin kakkauran murya yace karka kuskura ka tabani..

Ai bai karasa maganar ba Ramadan(Ango)daya karaso wajen don abin sosai yajawo hankalin jama’a ganin mai aikin gidan sarauta ya mare yar gidan, cakumo kwalar muhammad yayi cikin zafin nama hade da kai masa naushe a fuska, da sauri Muhammad ya kauce a zafafe wanda yayi sanadin yagewar kwalar rigansa da ramadan yake rike dashi.

A take Ramadan ya ja da bawa tare da kwalo ido waje, jikinsa har rawa yake yana nuna wuyan Al’ameen, sai kuma cikin sauri yasa hannu akan rawanin fuskar sa zai…

Da sauri muhammad ya damke rawanin sa, ya hana Ramadan bude masa fuska, menene haka? banaso karka kuskura ka bude mini fuska.

Har lokacin jikin Ango rawa yake cikin mamaki yace a ina ka samu sarkan nan,  waya baka wanene kai?da karfi yace security.

Jama’an gurin duk sun mike banda sarki dake zaune akan kujera duk rikicin da ake baiko d’ago kansa ba bare yasan abinda ke faruwa.

Mustapha ne yayi magana a rude wallahi sarkan ne, sarkan magadan masarauta ne, a ina ka samo sarkan nan?yana maganar yana kai hannunsa wuyan Al’ameen zai duba sarkan.

Da sauri Al’ameen ya buge hannunsa, Shuru yayi yana kokarin barin filin, da sauri Ramadan ya jawo sa baya yana kwalawa Yayansa kira, da sauri sarki ya juyo yana kallon Ramadan da mamakin kiran gona da yake masa?

Yaya sarkan magada ne a wuyan wannan me kawo shayin, kuma yaki bari aga fuskar sa, bamu yarda dashiba suspect ne?

Ai kafun ma ya gama magana saiga sarki ya sauko a kujera da hanzari ya nufi inda suke tsaye, daga isarsa hannu yasa a kamo sarkan yana kallo sai kuma jikinsa ya fara rawa ya kamo rawanin fuskar muhammad.

Da sauri muhammad ya dafe Hannun sarki dake kan fuskar sa yana girgiza masa kai, alamun rashin son hakan.

Shima sarkin girgiza kai yayi, hakan yasa muhammad sauke Hannunsa akan na sarki.

A Hankali yake warware Rawanin kansa, tsaf gashinsa ya bayyana mai masifar tsawo da sheki, a hankali ya warware na fuskar sa, da sauri ya dafe kirjinsa cikin tsananin mamaki da sauri yace muhammad!!!!!bai karasa ba kawai hancin sa ya fara tsiyayo da jini a hankali ya fara lumshe ido sai kuma ya yanke jiki zai fadi, da azama muhammad ya taro mahaifinsa da sauri ya rungumi abinsa cikin matsanan ciyar mamaki jin sarkin ya Ambace sunan sa.

Zuwa fadawa sukayi aka kewaye sarki muhammad ne ya ciccibi sarki har cikin flat nasa, atake gida ya rude da koke koke, ga masu tsananin mamakin muhammad da abinda ya had’asu da sarki harya Ambace sunan sa?

Bayan Ankai sarki d’aki likita da abokan aikinsa suka rufu a kansa, yayinda Ahlin gidan ke make a babban falon fada, daga maza har mata harda wa’inda muhammad bai taba ganinsu ba, mikewa yayi zai fita a falon da sauri Mahmah ta riko hannunsa, ina zaka yaron nan?

Gidan mu mana ba aiki bane ya kawoni mama?yace yana kallon nabila dake rakube a jikin kujera fuska jajjawur ga jini ya taru a idanunta da gani dai ta maru.

Wani irin ka tafi kuma kaje ina baka ga Halinda d’ana yake ciki ba? kuma na tabbata yana farfadowa kai zai nemi gani.da gorancen hausar ta take magana.

Toh ni kuma so nake na tafi gida ranki ya dade, in Allah ya kaimu gobe ai zanzo aiki duk maganar da zamuyi sai muyishi?

Ramadan ne ya mike,Hala nan dajine da bazaka iyya kwana a cikiba?

Ban saba kwana  gida irin wannan ba,  kasa bacci zanyi, yace yana fita a falon babu wanda yayi yunkurin hanasa, sai rakasa da ido sukayi.

Muhammad na zuwa gida gabaki d’aya abin duniya ya damesa, amma baicewa baba kome ba, shima baiyi magana ba duk da yaga sarkan wuyan Al’ameen Amma baice kala ba.

Yau koh abincin dare kasa ci yayi,  badaru da gidado ne sukaci gabaki d’aya jikinsa yau A sanyaye yaki kome yanayi a sake kamar mai ciwon fata.

Har dare bai rumtsa ba, tunani kawai yake a ransa, donshi dai bai gane inda abinnan ya dosa ba, menene Alakansa da mutanen nan shi zaman kasar ma ya isheshi kuma ya rasa hanyar da zaibi yabar kasar gabaki d’aya, yau wani irin kewar iyalinsa yame dason jin duminta, ba irin tambayar duniya dasu gidado basu masa ba Amma bakome yake ce musu.

Da misalin karfe 2:30 sukaji ana bugun kofar gidan, babane ya fita zai duba koh lafiya yayinda muhammad ke kwance duk da idanunsa biyu Amma bai mike ba.

Baba bai jima da fita ba sai gasa ya shigo d’akin su muhammad, mikewa yayi yana kallon baba.

Muhammad ka fitoh ana sallama dakai?

Da mamaki yace dani kuma baba, sallamar ma tsakar dare?

Ka tashi daga gidan sarautane.

Gaskiya baba kace musu su bari sai gobe, koma menene in gari ya waye sai ayi bawai a tadani tsakar dare ba kamar tashin duniya.

Muhammad yaushe ka koma mara kunya ban sani ba?

Kayi hakuri baba

Tashi kawai kaje kaji da wani sako aka turosa?

Mikewa yayi kawai ya sanya kayansa ya fitoh a d’akin, kallon mutumin da aka aiko wajen sa yayi, lafiya malam?

Lafiya muhammad ana neman ka a fada.

Tsakani da Allah in Ana son ganin mutum sai azo tsakar dare ya kirasa ai naga gari zai waye?

Babane ya kallesa, muhammad ka iyye bakinka banason irin wa’innan kalami,  bai dace da kai ba, don haka ka bisa kuje bakasan menene dalilin kiranka ba,  ya kamata kaje kaji.

Baiyi magana ba kawai ya nufi hanyar kofar gidan, binsa a baya mutumin yayi daman da mota yazo ba musu muhammad ya shiga suka wuce.

Daga isarsu masarauta gidan kaman rana koh ta ina fitilune haske kaman farin wata, ga mutane a tsatsaye kamar rana bakin dake gidan duk basu tafi ba, Al’ameen na fita a motar gabaki d’aya aka ringa binsa da ido har suka ratsa babban falon sarki, suna shiga mahmah da lawixa harda su ramadan muwaddat nabila duk suna cike a falon wasu kamma kuka suke fuskar lawiza da mahmah jazir alamu kuka sukasha, da sallama ya shigo falon amsa masa sukayi suna mikewa tsaye gabaki d’ayansu, binsu yayi da ido sai kuma ya nufi kofar d’aya falon, ya shiga yana shiga duka suka rufa masa baya zuwa ciki, tunda ya tinkare kofar bedroom yake jin salati ga sunan sa da ake kira da sauri ya cusa kansa adakin.

Sarkine kwance akan gado yana tari jini na biyo bakinsa yana Ambatun sunan muhammad, ai Al’ameen baisan lokacin da yayi super ba ya isa garesa koh tsawon shekaru nawane bazai taba manta wannan fuska ba bare shekarun da baiwuce a kirgasu ba,  hawaye ne ya cika masa ido ganin halinda mahaifinsa abin sonsa ke ciki, duk da ya rayu da takaicin gudunsu dayayi Ya kuma sha Alwashin duk randa ya gansa zai basa mamaki shima, amma bai d’auka zai gansa a irin wannan halin ba, karasawa yayi garesa a hankali ya kamo hannayensa dake dafe a kirjinsa cikin kuka yace Abbajoooo!!!me nake gani haka ka rufa mana asiri kar maraicin ya mana yawa?

Ai jin muryar sa da sauri yusuf ya mike ya rungume d’ansa a zaune, tunda ya hau karagan mulki ba’a kara ganin hawayen saba sai yau, hawaye ne yake siyaya a idanunsa, ganin haka yasa muhammad fashewa da kuka mai matukar karfi yana banbare Abbajon sa a jikinsa, tare da kallon doctor dake gefe, habba bawan Allah jini nefa kebin bakinsa kun barsa haka?

Kayi hakuri yallaboi wallahi tun da ya farfado anyi anyi ya tsaya a basa taimako yaki gashi ciwonsa baison damuwa Amma yaki ya saida hankalinsa.

Jin haka yasa muhammad kokarin mikewa tsaye,Ai da sauri yusuf ya rikosa da karfi tamkar uwar da za’a rabata da jaririnta, fuskar muhammad ya rike sai kuma ya soma magana a hankali, tabbas jini yafi ruwa kauri, babu tantama wannan jini nane muhammad nane koh babu sarka a wuyanka akwai alamun jini muhammad ku yafe mini.

Ah ah Abbajo ka rufa mini asiri karkace haka kayi hakuri ka rayu damu yana magana yana kuka.

A hankali sarki yace muhammad dukkan mai Rai mamaci ne in lokaci yayi dole mu amsa kiran mahalincin mu.

Don Allah Abbajo kabar irin wa’inan magana, likita kazo ka taimaka masa, da sauri likitan ya maso da taimakon muhammad suka gogi masa jinin dake bakinsa ya taimaka masa ya shiga toilet ya shanja kayan daya baci, daidai ya fitoh har muhammad ya sauya zanin gado.

Yana fitowa ya kwanta likitan ya d’aura masa ruwa da Allurai ya fita, a hankali yusuf ya kama hannun d’ansa sosai ya zurawa muhammad ido yana kara tasbihi a zuciyar sa yaushe yabar muhammad yaro karami d’an shekara 13 Yau shine ya zama cikeken mutun tamkar shi a lokacin da ya barsu muhammad?badon shekaru ba koh yau duk wanda yaga muhammad zaice shine.

Na’am Abbajo.

Ya Aishan Adara?

Jin tambayar da ya masa sai da gaban sa ya fadi, a halinda mahaifin sa yake cikin nan bai kamata ya kara d’aga masa hankali ba, cikin sanyin jiki yace, Tana Lafiya Abbajo.

Murmushi yusuf yayi cikin karfin hali, nasan xuwa yanzun ta rage masifa koh? nama san itama ta tsufa kamar ni?

Hhh bata tsufaba tana nan da kyawun ta daka sani, kuma yanzun sam bata fad’a da kowa.

Ah ah muhammad fadi gaskiya dai nasan maman ku, saidai in ba’a bata mata rai ba?

Dafa gaske nake.

Ta yafe mini?

Babu abinda ka mata abbajo asalima ita ke neman yafiyar ka, don gaskiya yayi halinsa bayan bakai, meyasa Abbajo kayi fushi ka tafi ka barmu, kana rayuwan ka cikin mulki da kudi mukuma baka damu da kalar rayuwar da muke ba?

Girgiza kai kawai yusuf yayi baibawa muhammad Amsa ba, ya sake jefo masa wani tambayar, ya jikin salim nasan zuwa yanzun kam yagirma don zai fika jiki kasan jikin mamanku garesa?

Kwarai ma kuwa abbajo salim ya warke sosai sai godiyan Allah.

Su lawiza da suka jima a bakin kofa suna kallon ikon Allah wai me yusuf yake nufi da yaron nan ne basu gane ba, kasa magana sukayi ganin kamar ma basu san da zaman suba sai hira suke, hakan yasasu juyawa suka fita a d’akin ganin lokaci d’aya jikin yusuf yayi sauki gashi sam ba hausa suke ji sosai ba, duk da su mazan suna hausa tsabanin mata da kwata kwata bayi suke sosai ba sai jifa jifa,

Haka yusuf da muhammad suka ringa hira na yaushe gamo, Amma sam muhammad bai fad’awa yusuf mutuwar Aisha ba koh salim, sai asuba da sukayi sallah doctor yazo ya cirewa yusuf laidan ruwan, suka kwanta tare a Royel bed na sarki bacci ya d’auke su.

**************

Sumayya ciki ya shiga wata bakwai yanzun sosai tayi wani irin kumbura, har yakai yanzun bata iyya tashi da kanta sai khadija ta kama hannunta ta jata da karfi saboda nauyin cikin,  abincin ma yanzun bataci daga ruwan zafi sai tie koh nama.

Kalamu-wahid da khadija yanzun kam an dinke sosai suka shaku kalamu na zuwa gidan sumayya akai-akai gashi yanzun har kwaryan tuwo yake dashi akofar sumayya na rana,kamar yau sumayya ta gaji da kwanciyar da khafija keyi a kasan tiles hakan yasa ta kiran ta hade da mika mata kudi taje ta sai karamin katifa, Amsan kudin tayi tace bari tayi wanka.

Tana shiga d’aki messenge ta turawa kalamu akan zata fita, kafun ta shiga wanka.

Tana fitowa shiryawa tayi ta fita da niyar tafiya kasuwa, tana nufar get ta bude da murmushi a fuskar ta ganin kalamu tsaye sanye da  jamfa wando da riga yayi matukar masa kyau abinka da bakin mutun sanye da farin kaya, mota ya bude mata ta shiga shima ya zagaya ya shiga yaza suka cillah kasuwa.

Duk yanda yaso ya saya mata katifa da kudinsa taki yarda, yace zai cikimata ta d’auki babba, amma taki tace aunty zatayi hulo itakam babu ruwan ta.

Tare suka dawo kasuwa ya sauketa a get nasu, ta shiga da katifar ta da kanta don tace karya shigo kar aunty ta mata fad’a, sunje kasuwa dashi bada izininta ba, ba musu shima ya shige gidansu bai matsa mata ba.

Bayan isha’i sumayya ne  kwance a falo, yayinda khadija na cikin daki suna hira da kalamu a waya, kamar a mafarki taji sallamar sa a bakin kofar falon su, da sauri ta mike zaune tana mamakin sa na rashin fad’a mata yana zuwa Alhalin kuma waya suke da juna yanzun, kalamu!!!!

Ta cikin wayar taji yace ke don Allah fitoh ki bude mini kofa.

Ba musu ta fitoh a d’akin kallon sumayya dake falo a kwance, tana bude kofar ya shigo gaida sumayya yayi ta Amsa masa sama-sama don yanzun koh yawan magana bata so.

Aunty daman wajen ki nazo?

“Khadija basa wajen zama”

Zama yayi akan kushin da khadija ta aje masa, itama ta koma gefe ta zauna.

Aunty daman nace mezai hana khadija ta shiga islamiyyar mu ?nayi magana da ita tace nini tun saukar ta na farko bata kara komawa tushi ba.

“Gaskiya ne kalamu koni ina son khadija ta koma islamiyya, nama laila magana akan koh akwai islamiyya a kusa, shine tacemin yaranta babansu ke koyar dasu, ni kuma bana son khadija taje wajen sa d’aukar karatu”

Gaskiya ne Aunty kinga kuma zuwan weekend ne aje 3 adawo 5 ?

“Shikenan kalamu sai Allah ya kaimu next week sai na had’aku ka kaita don ni ba iyya taka kafar nake sosai ba”

Eh aunty daman na kammala mata kome yanzun ma uniform na kawo mata da form sai a cika mata sati mai zuwa ta fara zuwa.

“Lallai ma kalamu toh Allah dai biya ka”

Ameen ya Amsa yana kallon khadija dake murmushi a boye.

“Yauwa kalamu daman akwai abinda nake son na fad’a muku kaida khadija”?

Zuciyar suce a tare ya buga da sauri suka kalli juna sai kuma suka juya suka kalli sumayya har suna had’a baki, Aunty Allah dai yasa lafiya??

“eh daman akan kune, ba kome bane  illah abu d’aya zuwa biyu, ina so daga yau…………..

✨Ruqeenjalal✨

Back to top button