Uncategorized

Matar Makaho Part 17 Hausa Novels

 MATAR MAKAHO

Chapter 17

A ranan da aka nad’a yusuf a ranan mahaifinsa yake sanar dani, akan na fad’awa yusuf ya d’auko iyalansa, ya masa hakan ne don yaga zai masa biyayya koh zai bijire masa, Amma tunda ya yarda da auren lawiza kuma ya hau karagan mulki ya yafe masa duniya da lahira.

A hankali yusuf ya kalli mahaifiyarsa, mahmah meyasa kika hanani?

Kayi hakuri yusuf nayi hakan ne don banason kayi nisa dani, nayi tunanin koh inna sanar dakai hakan zaka iyya bijire wa mulki.

Ramadan ne ya kalleta Amma wallahi mama baki kyauta ba, duk irin ciwon da yaya yake Amma mahmah baki tausaya ma d’anki ba?kowa yasan dalilin ciwon yaya yusuf Amma ga magani a hannunki mahmah kika kasa basa habba mama mulki yafi lafiya ne?

Kuka mahmah ta sake tana nuna Alhininta.

Kaga ramadan ya isa haka mahmah uwatace har abada babu wanda yakai uwa son d’anta don haka ni mama bata mini kome ba.

Jin abinda yusuf yace sosai jikin wasu yayi sanyi, Al’ameen hannu yasa a wuyansa ya zaro sarkan tare da mikawa mahaifinsa, Abbajo ga sarkanku a sawa wanda ya dace?

Kallonsa zulkiflu yayi, akan me zaka cire,  wayace maka baka dace da magaji ba?

Ah ah uncle kai ya dace kasa koh uncle Ramadan nikam banida sha’awar sarauta so nake nayi karatu mai zurfi na zama soja mai mukami.

Kowa dake wajen da kallo yabi muhammad jin abinda ya fad’a, murmushi sarki yayi hade da cewa yan uwansa, bazan tilasta muhammad ba daman na basa sarkane badon na shaida shine magaji ba, na basane don na gane sa aduk shekaru da zai gabato duk da Akwai kamar jini, Amma zan aje shaida don haka Za’a d’aurawa zulkiflu.

Da sauri zulkiflu yace Ah ah wallahi yaya nikam banaso gaskiya, amini afuwa adai bawa Ramadan.

Ba musu aka d’aura wa Ramadan sarkan magajin masarauta, sannan a mana booking in fly next week zamu shige nageria.

Jin Abinda sarki yace yasa zuciyar muhamamd rawa, ganin wani rawan jiki da mahaifinsa keyi zashi nageria duk zatonsa matarsa na raye, Abbajo nace dukan mu zamu wuce ne?

Ah ah muhamamd bazamu wuce mu biyar ba,  tunda in muka d’auko su dawowa zamuyi nan?

Shuru muhammad yayi yana kallon Mahaifinsa, ya sake juyawa ya kalli mama kamar hadin baki suka had’a ido da nabila kauda fuskar sa yayi.

Waini muhammad baka bamu labarin abubuwan da suka shafeka ba, da Alakar ka da sarkin shayi da yaran nan?, zulkiflu yace yana nuna su gidado.

Da sauri muwaddat tace eh hakane Akki.

Kasa magana yayi yana kallon yusuf, gyad’a masa kai yusuf yayi Alamun yayi maganar sa,  A hankali ya fara basu labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyar yusuf da wahalar da suka sha da abubuwan da suka faru da ubangari da zainab, da mutuwar Maminsa da kaninsa harda Aurensa da sumayya, sai dai bai fad’a musu dalilin da yasa aka aura masa ita ba, don baidace yace dangin ta sunyi mata kazafi ba, har kawo zuwansa cameroon.

Muhammad na bayani mutane wasu na kuka wasu na salati wasu najin haushin zainab da mahmah data hana a d’auko yaran yusuf, kuka itama mahmah ta sake tana cewa su muhammad su yafeta ta cutar dasu.

Yusuf kam zaune yake akan karagan mulkinsa sosai fuska tayi zahur, jijiyoyin fuskarsa ya mike alamu dai ran maza ya baci, gashi a fada yake dole ya matse irin na sarakun, abin tsoro koh bacin rai da tausayi baya bayyana a fuskarsu mundin suma gaban jama’arsu.

A take aka matso da tafiya zuwa jibi in Allah ya kaimu da rai da lafiya sai NIGERIA!!!!!!

Mikewa yusuf yayi ya koma falonsa kafun kowa ya mike ya fita, nabila kam jiki yayi sanyi saibin mahmah take a baya, yayinda muwaddat da muhibbat suka likewa d’an uwansu sai hira suke masa da tambayarsa labarin khadija, sosai yaji wani irin farin ciki ganin yan kannensa, lawiza ma tashi tayi batama kowa magana ba tayi flat nata, da fari tad’au abin da zafi Amma jin irin wahalar da su muhamamd sukasha da mutuwar Aisha sai taji jikinta yayi sanyi.

***************

Sumayya ce zaune a kitchen tana girka pepper chicken zallah, don ita yanzun nama kawai takeci sai shayi, yanzun ma khdija taje islamiyya ne shiyasa ta shiga kitchen da rarrafe zata girka abinci.

Sai karfe 5:21 khadija ta shigo falon da sallama, sanye take da riga da wando sai hijab babba na islamiyya, hannunta d’auke da jaka.

Amsa mata sumayya tayi tana binta da kallo ta rasa meke damun khadija a kwana biyun nan, gabaki d’aya ta shanja bata da nutsuwa sam, kullum ta zauna shuru koh aiki ta sata bata gamawa akan lokaci, shiyasa wasu aikin take lallabawa tayi duk da nauyin cikinta, don yanzun saidai ta ja ta shiga d’aki indai khadija bata nan”khadija zonan”?

Ba musu ta kwabe hijab nata tazo ta zauna kusa da sumayya, Aunty gani.

“Khadija meke damunki”?

Babu Aunty

“Wani irin babu kome, ki dubi halinda kike ciki duk kinsa rayuwar ki a garari, sai kinzo kin samu ciwone a koma ana sayan magani koh yaya”?

Babu kome fa Aunty

“Bankai ki fad’amin damuwarki ba koh”?

Sunkuyar da kai khadina tayi bata iyya cewa sumayya kome ba, tana wasa da yatsarta.

“kunyi fad’a da kalamu ne kwana uku yau baizo ba”

Wallahi Aunty bansan meke faruwa ba yau kwana uku bai kirani ba, inna kirasa wayar sa a kashe.

“Ok abinda ke damunki kenan?amma meyasa baki tambaye kannensa ba tunda islamiyyar ku d’aya kuma boko ma d’aya”

Wallahi Aunty kunya nake ji, karsuce da wani abu.

“Kunya?lallai khadija bakisan inda ke miki ciwo ba, yaro kullum sai yazo wajen ki kwana uku bakisa sa a idanunki ba, bazaki iyya shigiyarsa  ba?

Sai gobe innaje school saina tambaye falmata(kanwarsa)

” ohon miki”

Tashi khadija tayi jin amsar da Auntin ta ta bata.

Washe gari bayan khadija ta dawo gida take sanar da sumayya ai kalamu ba lafiya yana hospital, kasancewar sumayya tayi nauyi, khadija ce tayi girki mai rai da lafiya, kawarta ta rakata suka je asibiti wajen kalamu, sosai suka samu jikin nasa yad’anyi sauki, kuma taji dadin tarbar da aka mata maman sa nada kirki sosai, haka ma babansa, wanda ke d’auke da zanen kanuri a fuska, amma mamansa bata dashi, haka kannensa sukayita tsokanarta wai budurwan kalamu ne,  sosai tayita jin kunya.

************

Kwana biyu da muhammad yayi a gidan sarauta, da ace zasu hadu da wanda yasansa a baya indai ba farin sani ba,  bazai ganesa ba, ya samu gata kota ina bana wasa ba yayi kyau ya kara fresh yana cin mai kyau yana shan mai kyau, ya kwanta a maikyau baida buri daya wuce yadawo yaga matarsa abar sonsa, sannan yana iyya bakin kokarinsa wajen ganin mahaifinsa bai saka damuwar rashin Aisha da salim ba, sosai yake kula dashi baya barinsa shi kad’ai mundin yabar fada, toh zasu kasance tare haka yan uwan babansa na sonsa, kannensa ma duk ya shaku dasu, nabila ce kawai bata samu fuska a wajen saba duk da mahmah tasata ta basa hakuri kome ya wuce, kuma ya nuna ya hakura Amma bata ganin fuska koh hira yake tazo wajen sai yayi shuru abinsa koh ya tashi.

Su gidado da sarkin shayi duk sun dawo gidan da zama.

Waya mai tsada zulkiflu ya saya masa da kayayyakin sawa masu yawa, wanda zaina sawa.

Kamar yanda Aka saka rana yaune za’a diro nigeria, maimartaba ne da mahmah sai muhamamd da zulkiflu Adda maisara, dayake su muwaddat na jarabawa an barsu da lawiza a gida, karfe 2 na rana jirginsu ya d’aga zuwa Kasarmu ta gado!!!!!

Sun sauka lafiya, suna fita a jirgi dayake sarki  yasan da zuwansu yasa suka samu tarba na musamman direct gidan sarki suka nufa, duk da muhammad yaso ya fara zarcewa sintali sai dai ba dama.

Bayan sunyi wanka sunci abinci,kasa hakuri yayi ya ce zaije sintali ramadan ya rakasa a mota tare da driver.

Tunda suka shigo sintali yake bin koh ina da kallo  yana tuna abubuwan da suka shude watan nin baya, har kofar gidan Adara akayi packing in motar,jikinsa har rawa yake  yana Allah Allah ya fitoh, saura kad’an ya buge kafarsa saban sauri ya bude motar ya fita,  gashi daman yammane ana shirye shiryen kiran mangariba, abin mamaki yana fita babu wanda ma ya zaci shine, harya ratsa mutane sai binsa ake da kallo ganin babbar motar da ya sauka a ciki.

Shiga gidan adara yayi kamar yanda ya tsammani hakan ce ta faru, wato jama’ar gidan na tsakar gida, duk juyawa sukayi suna kallonsa harya karaso tsakar gidan, gaidasu yayi da sauri gabaki d’ayansu suka Amsa hade da shiga shock, indai ba gizau ba Al’ameen ne, duk gatan da ya samu bazai hana su kasa gane saba.

Da sauri iro ya mike bura uba wanake ganin nan kamar muhammad ina ka shiga?

Bai samu daman basu amsa ba, kofar su kawai ya nufa cikin sauri ya bude kofar shashen, da mamaki yakebin kofar ganin duk datti, Alamu dai an dade ba’a share ba da sauri ya karaso kofar, yana bin koh ina da kallo,da sauri ya shiga kitchen insu ga mamakinsa kome a zaune yayi kura, da sauri ya fitoh a kofar, daidai lokacin Ramadan ya shigo gidan, da sauri muhammad ke tambayar yan gidan da har yanzun suke a tsaye sun maidashi madubi,tambayar su yayi ya yaga kofar sumayya a kulle?

Inna asabe ce take sanar dashi ai ba’aga sumayya ba, kama kai kawai yayi yana salati, da sauri ya fita a gidan da kafa ya taka har gidan goggo, yayinda su iro ke mara masa baya, duk inda suka wuce saisu cewa mutane ga MAKAHO ya dawo ga makaho, har gidan goggo va tare da wani neman izini ba ya shiga gidan.

Goggo dake zaune a gindin bishiya, gabaki d’aya ta rame ta zama abin tausayi zaune take tayi tagumi, jin sallamar muhammad yasa ta mike da sauri, wanake ganin nan kaman muhamamd?Allahu Akbar Allah mungode maka sai kuma ta fashe da kuka tana rungumar Al’ameen.

Saida tayi kukanta mai isarta kafun Suka gaisa na yaushe rabo, hade da karama mujammad karin bayani akan batan su sumayya, wanda shagari ya sanar dasu guduwa sukayi bawai sacesu akayi ba, sosai muhammad yaji wani irin ciwo na abinda dangin sumayya sukayi bayan rabuwar su,  taya zasuce ya rabu da matarsa akan wani dalili, anan yake sanar da goggo abubuwan da suka faru sannan yace mata yana son zuwa gidan su sumayya don ganawa da iyayenta, koh Allah yasa sunsan inda sumayya zata iyya zuwa.

Ba karamin mamaki Goggo tasha ba jin wai yusuf sarkine yanzun, Allah sarki duniya, mikewa gogho tayi tad’au hijabinta suka fita gidan da Al’ameen, ai suna fita kofar gida, me zasu gani mutane ne makil a kofar gidan, sunzo kallon Al’ameen don lokaci d’aya labari ya samesu makaho ya dawo yayi kudi, goggo ma a take ta kara musu da wani ai yanzun d’an sarki ne babansa yana mulkin wani gari, a nijar, muhamamd in ma kudi ya ciro a Aljuhunsa ya rarraba musu dubu bibbiyu.

Yana gama raba musu kowa ya watse yana saka masa Albarka, harya juya zasu shiga mota,don driver yajawo ramadan dake ciki har kofar gidan goggo, yana shiga tun daga nesa ya fara jin ana kwala masa kira oga oga oga!!!!

Shagari ne ya iso wajen da gudu, da ido muhammad ke binsa koh ba’a fad’a ba yasan shagari ne daga muryarsa ya gane sa.

Oga sannu da dawowa ka dawo lafiya, yanzun Abdu ra’uf kece mini wai ka dawo.

Murmushi muhammad yayi, lafiya Alhamdulilah shagari.

Da sauri shagari yace munyi kewarka oga shagon mu ya bunkasa nima, yanzun ina makaranta bara na kira Ammar na sanar dashi daman ina da number sa?

Ah ah basai ka kiraba ka bani number sa zan kirasa.

Kallon ramadan da goggo dake mota shagari yayi sai kuma ahankali yace oga tafiya zakayi ne?

Ah ah shagari ina Taraba har sai anga sumayya.

Number Ammar ya basa sukayi sallama suka tafi, dayake shugaba family house sanannen gidane kuma driven dan garine, yasa da kwatance suka gane gidan, goggo ramadan da muhamamd suka shiga gidan,ganin zubinsu yasa mai gadin basu hanya suka wuce cikin compound, ya shiga gidan don musu sallama da mai gidan, ba’a jima ba saiga Uncle Abubakar ya fitoh suka gaisawa, sannan suka gabatar masa da kansu, kuma suna son magana da mahaifin sumayya, da rawan jiki Abubakar ya musu iso zuwa cikin gidan, da gaggawa ya hado kan mutanen gidan a falo, kowa na zazzaune don su daman ba farin sani sukayiwa muhammad sosai ba, a d’auren aure suka fara ganinsa hakan yasa basu wani ganesa ba, gashi ba’a makaho yake ba yau.

Bayan sun zazzauna wannan zaman ma ba momy a ciki, a nitse goggo ta musu bayanin ga mijin sumayya ga kuma bappansa ta nuna Ramadan, da mamaki suke tambayarta ba’ance mijin sumayya makaho bane kuma ya bata.

Ramadan ne ya musu bayanin kome a take jikinsu yayi mugun sanyi, sannan suke sanar dashi rashin ganin sumayya anyi iyya bincike Amma shuru, duk inda ake tsammanin zataje ba’a ganta ba, abie har wani ya samu ya tura unguwan su Hafsa a maiduguri a dubo masa koh sumayya ta gane gidan kakan ninta shan taje, amma an samu tabbacin banan sumayya taje ba, Asali ma hafsa tayi aure bata maiduguri yanzun.  

Hankalin muhammad ba karamin tashi yayi ba, fiye da hankalin yan gidan duk da abie ya shiga damuwa don har rama yayi mai tsanani, suna tsaka da maida zancen sukaji an turo kofar falon koh sallama babu.

Gabaki d’aya suka juyo suna duban falon,  safina ce ta shigo Alamu dai daga unguwa take, duk suka bita da kallo itama, d’aga ido tayi ta kalli jama’an falon da karfi ta kwala kara ta zube a kasa sumammeya..

Da sauri dada tayi kanta, sabanin Abie da sauran yan gidan dako a jikinsu alamu dai ba karamin tsanarta sukayi ba, muhammad ma mikewa yayi shida ramadan suka nufi kan momy, da taimakon su aka kaita asibiti don anyita watsa ruwa bata farfado ba, gashi yan gidan koh a jikinsu, sune suka d’auketa har asibiti suka biya kudin kome suka tafi suka barta da dada, gida suka koma bayan isha’i suke sanar dasu yusuf abubuwan da ya faru da batar da sumayya tayi,sosai suka nuna Alhininsu  da damuwa sosai muhamamd ya basu tausayi yaro tun yana karami yasan wahalan duniya, har tashinsa ma yayi gwagwarmaya.

Washe gari da sassafe saiga Ammar a gidan sarauta, daya samu aka barsa ya shiga ya tura wani dogari yace ana sallama da muhamamd bakin Niger, ba’a jima ba sai ga muhammad ya fitoh, tun daga nesa yake kallon muhamamd kamar bashi ba gabaki d’aya rayuwa ta sauya, sanye yake da jallabiya yar saudi sai hula taba kaji hadisi,  sosai yayi kyau saidai fuskar sa a tamke take alamu baya cikin walwalarsa, yana karasowa da sallama a bakinsa, amsa masa Ammar yayi ai yana jim muryar Ammar da sauri ya rungume sa, cikin farin ciki suka hau hira har cikin gida muhammad ya shigar da Ammar suka gaisa da yan uwansa da mahaifinsa,  sai a lokacin yake sanar dashi ai shagarine ya kirasa yake sanar sashi muhamamd ya dawo, yana gidan sarki kuma ya basa number Amma shuru Al’ameen bai kirasa ba shiyasa yabuga sammako yazo ya gansa.

Abinci aka kawowa Ammar, suna zaune a d’akin da aka sauke muhammad ana hira da labarun abubuwan da suka faru a baya harda Ramadan, kawai saijin muryar jama’a sukayi a sashen sarki, dayake window d’akin da aka sauke muhammad yana saitin sashen.

Mikewa sukayi gabaki d’ayansu suka zagaya zuwa falon sarki,family shugaba ne, suka gaishe dasu abie, aka daura zancen batan sumayya kowa na kawo shawaran sa, karshe dai akace za’a dage da rokon Allah da sadaka sannan za’a zuba jami’an tsaro a bincike su, kafun kowa ya watse, daman yan gidan su sumayya gaida yusuf sukazo da mahaifiyar sa tare da bada hakuri akan abinda ya faru kuma ba laifi sun nuna musu bakome, kome ya wuce Allah ya kiyaye na gaba.

Satin yan nijar biyu a taraba ba’aga sumayya ba, gashi kaf gidan su an duba hotonan ta duka ba’a gani ba, hatta dakin su muhammad ya koma yayi bincike sap baiga wani hoto ba, don sumayya ta tafi da hotunan su, gashi na wayar maimuna kanwar Ammar ma, wayar ta lalace harma ta saida ta, bare su samu hotunan su, da yake yanzun zamani ya sauya ba kamar daba, mutun ya bata a gari ma  ba’a ganesa sai da rabo bare a kasa sukutum, dole tasa Yusuf komawa dasu ramadan aka bar mahmah da muhammad, kafun su tafi saida aka sai musu gida mai shegen kyau a Amazon suka koma ciki su uku harda goggo,  kasancewar mijinta ya rasu bayan tafiyar sumayya hakan yasa muhammad d’aukar ta suka koma gidan su  suna zaune tare da mahmah.

Wasa wasa saida muhamamd suka share wata biyu a jalingo Ana kan bincike har yanzun shuru ba’aji duriyar sumayya ba, koh khadija sosai abin ya dame muhammad koh abinci baya iyyaci sosai, ba irin tunanin da baiyi ba don shi gani yake saceta akayi tunda makiyansa suka iyya saka a kashesa, Amma ammar na yawan kwantar masa da hankali ba kad’an ba.

Ta bangaren safina dai tunda ta farfado a gadon asibiti ta makance bata gani kwata kwata haka magana ma bata iyyawa saboda bakinta daya koma gefe, fuska ya karkace  ya murd’u ya wainu wanda likitoti sun tabbatar hawan jinine daya hau lokaci d’aya, daya bugar da ita ta fadin nan, shine ya kaushar mata da fuska, sai dai makantar ne basu gano sila ba, kuma kaf gidan babu wanda ya damu da lamuranta sai dada ita ke jinya amma hatta abie yaji ya tsaneta hakama y’an gidan wanda basu san dalili ba,  dada ma daurewa take Amma ba kaunar safinan take ba yanzun.

Ammar  ne zaune a falon gidan su shida kannen sa, abinci yake ci gabaki d’aya hankalin sa nakan TV, yayinda iyayen sa ke hiran batar sumayya da dawowar Al’ameen wanda Ammar ke kawo musu zancen, don iyayen sama sunje har gidan muhammad, suka masa jaje, kaninsa ne kawai baya falon.

Kwala masa kira yaji kaninsa yayi daga d’aki sai gasa ya fitoh da gudu hannunsa d’auke da waya yana zuwa baiyi magana ba, kawai ya mikawa Ammar wayan.

Kallon wayan yayi hotunane akayi posted nasu a instagram guda uku, Khadija ce sanye da uniform ita da wani bakin yaro wanda zaiyi sa’ar ta koh ya fita da kad’an shima da uniform in nurse suka d’auki hoto a unguwa mai kyau, sai na biyun tana sanye da uniform in islamilayya nan ma su biyu sai na ukun ita da yaron suna sanye da kayan hausa atamfa da shadda.

Jikin Ammar na rawa yake tambayar Abdul wanene yaron nan?

Aboki nane kalamu-wahid, school namu d’aya  dashi a abuja naga yayi post kuma naga kamar khadija?

Ba kama bane Abdul itace, yanzun kasan inda yaron yake takamamme a Abuja?

Eh na sani yaya don inban manta ba kafun mu dawo hutu yayi ciwo danaje asibiti dubasa na samu an sallamo sa, so yamin kwatancen gidan su naje.

Waya kawai Ammar ya fitar a Aljuhunsa yana lalubar numban muhammad gabaki d’aya yabi ya gigice. 

*******************

Kalamu yaji sauki har ya dawo da normal life nasa, a haka sukaci gaba da rayuwa abinsu cikin farin ciki duk da basa rasa kalubalen rayuwa.

Sumayya ciki ya shiga wata tara duk rashin tausayin mutun inya ganta sayya tausaya mata, cikine yayi kato matuka yayi tsayi ga nauyi don yanzun koh tafiya bata iyyawa sai dai rarrafe abin tausayi bata fita koh ina daga falo sai toilet khadija ke kome wani sa’in kalamu zaizo ya tattara wankin ta ya kai mata dana khadija, wani sa’in har girki yake zuwa ya taya khadija in ayyuka sun mata yawa, sumayya kam yanzun sai a hankali, koh riga bata iyya sawa sai wasu manya manyan vest na gwanjo da zani shine kayanta, sosai laila ke tausaya mata.

Yau laila da mijinta harda yaranta sunyi tafiya zuwa Adamawa wajen dangin mijinta, bayan isha’i kalamu yazo ya kawowa sumayya balankun nama, amma ta kasa ci saboda ciwon kanda ke damunta, suka sha hira da khadija suna cin nama, bai koma gida ba sai kusan 9 ya ma khadija sallama ya wuce, don zuwa lokacin sumayya ta dade da kwanciya.

Da misalin karfe 1 na dare sumayya ta farka jin wani irin matsetsen fitsari  daya kamata, mikewa tayi zaune a hankali jin fitsari ya cika mata mara, gashi dare ne batason shiga hakkin khadija, yasa ta rarrafawa ta shiga bedroom da rarrafe har cikin bandaki, tsungunawa tayi, tayi fitsari ai tana gamawa taji bayan ta ya kama ga wani irin c..

Bayan ta ya rike sosai ga wani irin ciwo da taji a maranta lokaci d’aya ta gigice tana salata tunda take bata taba jin ciwo irin na yau ba, Ambaton Allah kawai take a ranta gabaki d’aya ta had’a gumi, jin wani abu na zuba babu control ya sata tsorata ruwa ne yake dundula, salati ta sake hade da kwalawa khadija kira.

Khadija dake bacci kamar a mafarki taji muryar sumayya mikewa tayi ta nufi ban d’akin da sauri ta bude wazata gani? sumayya ce duke jikinta sai rawa yake gabaki d’aya ta had’a gumi a tsorace take tambayar ta haihuwa ne? sumayya bata samu Amsan bata ba, nuni kawai ta mata ta kira mata mota su tafi asibiti, ba musu khadija tad’au hijab tasa akan kayan baccin jikinta, ta ruga da gudu ta fita a falon, sakatan get in ta zare ta fita bakin kwalta, abinka da dare koh tsuntsu bata samu ba koh ina shuru, kuka ta sa da gudu ta dawo cikin gidan, kofar d’aya makwanciyar su ta wuce tana buga wa,  amma basu bude ba gashi kaf gidan babu mai mota koh mijin laila ma ba motar bane dashi.

Haka da dawo sashen su, tana shiga zuwa lokacin jikin sumayya ya kara tsanani sosai koh zama ta kasa har lokacin tana tsungune.

Da sauri ta d’auki wayar ta layin kalamu ta kira, sai da ta masa kusan 4 miss call kafun ya d’aga cikin muryar bacci yake tambayar ta lafiya?

Ai tana sanar dashi da sauri ya mike ya zura jallabiyar sa ya fitoh a d’akin sa, harya tura kofar falon su zai fita saiga nannen sa ta fitoh daga dakin  ta, tambayar sa tayi ina zaije a daren nan?

Sanar da ita yayi Auntin khadija ba lafiya tana labour, tambayar sa tayi mijin tafa,Amsa ya bata shidai bai taba ganin mijinta ba, yama ga alamu bata da miji, jin haka yasa nanne d’aukar hijab nata ta sanar da mijinta zasukai sumayya asibiti, suka fitoh tare dashi  mota kalamu ya fitar suka shiga sai get insu sumayya, fita nanne dashi sukayi zuwa ciki.

Zuwa lokacin sumayya tayi laushi sosai koh gane wake kanta bazata iyya ba, dayake dare ne nanne da khadija ne suka ririketa yayinda kalamu ya diauki akwatin ta, data jima da shiryashi a zaune, rufe musu kofar yayi suka tafi asibitin da sumayya ke awo.

Suna zuwa aka karbesu nanne na zaune a waje ita da khadija, kalamu keta hidima na sayyan abubuwan da aka bukata koh zama bai samu, har 4 na asuba sumayya haihuwa ya gagara, gabaki d’aya karfin ta ya gama karewa sai da aka kira Assalatu kafun haihuwa yazo gadan gadan, cikin hukunci Allah sumayya ta haifi yaran ta guda biyu wanda koh sanin wani iri ta haifa bata sani ba, tsabar wahalar da tasha, tadai san ta haihu sau biyu, Alluran hutu aka mata bayan an kimtsata a take bacci ya d’auke ta.

******************

Bugu d’aya Al’ameen ya d’auka a take Ammar ke sanar dashi anga wajen da khadija take,  suna Abuja.

Ai muhammad baisan lokacin da ya wantsalo daga kan kujeran falo, a take yayi sujjada akan tiles yana wa Allah kirari, goggo da mahmah dake zaune a kasan falo suna cin abinci da sauri suka mike suna tambayar sa lafiya?ai da sauri ya mike ya rungumi mahmah cikin farin ciki yake sanar da ita anga sumayya anga sumayya tana Abuja.

Ai sosai suka nuna farin cikin su goggo harda kuka, a take Muhammad ya fitar da waya ya kira abie ya sanar dashi akan yanzun nan zai tafi gidan su Ammar zasu wuce abuja.

Hanasa Abie yayi yace ya bari sai da safe sai subi fly zai sa a nema musu ticket sai su tafi tare da abie, ai a take goggo ma tace zata mahmah ma tace ita ma, dada dake kusa da abie tace itama baza’ayi ba ita ba, duk yanda abie da muhammad sukayi da tsofinnan su zauna a Taraba, su zasuje su dawo da sumayya amma kememen sukace kafar su kafar su abie, haka ba yanda abie ya iyya duka aka musu booking in fly tare da kiraye kirayen waya har nijar aka sanar dasu an samu wajen da suke, suma sun sanar dasu a cikin satin nan suna zuwa gabaki d’ayan su.

Washe gari tun sassafe suka bar Taraba muhammad koh bacci jiya kasawa yayi,   dada ma haka ta watsar da safina tace sai taje taga jikallen ta, Ammar ma tasa Abdul yayi a gaba tare zasu ya nuna musu gidan su kalamu.

Karfe 9 su muhammad suka dira a Abuja, dayake yana da aboki, tun a taraba ya kirasa akan suna zuwa, tarba suka samu daga wajen abokin abie shiyazo ya d’aukesu a Airport, direct gidan su kalamu suka wuce, Amma abin haushi basu sami kowa ba wai Suna asibiti, haka mai ganin ya sanar dasu Alfarman ganin baban kalamu abie ya nema ba musu, mai gadi ya shiga ga sanar dashi,  aiko sai gasa bayan sun gaisa ne sukace masa suna son sanin asibitin da kalamu sukaje in ba damuwa.

Ganin girman su da kudin su, gashi kamar ba lafiya ba, hakan yasa baban kalamu yace musu bara ya bisu asibitin, shiga mototi sukayi ya kira nanne ya tambaye ta asibitin da number room nasu, da mamaki yake tambayar ta koh lafiya jin muryar ta ya dishe-dishe alamu dai ba lafiya ba, koh tayi kuka, ya tambaye ta lafiya tace masa ba kome, kashe wayar yayi ya sanar dasu abie ga asibitin da suke.

Suna isa asibitin muhammad da gudu ya ruga bayan sanar dashi block inda suke koh kunyan su abie baiji ba da gudu yayi block in mutane sai kallonsa suke, da sauri sauri ya shiga d’akunan one by one yana dubasu, ana ukun ne ya shiga koh sallama babu ganin mace kwance akan gado ga yara sa’o’in juna zaune rike da jinjiraye a hannayen su, da sauri suma suka juyo jin mutun a d’akin babu sallama.

Ai da sauri khadija ta mike ta kwala ihu yaya!!!!!!!! Da sauri kalamu dake kusa da ita rike da d’ayar babyn da sauri ya cafke wance ke hannun khadija, don saura kad’an ta buga jinjira, da gudu khadija tayi wajen muhammad batayi wata wata ba ta rungumi d’an uwanta tana fashewa da kuka yaya, kaine koh mafarki nake?

Khadija nine nine khadija ina Aunty ki?

Allahu akbar yaya kalli nan tace tana nuna masa kan gadon da sumayya ke kwance har yanzun tana bacci.

Da sauri ya ware idanun sa yana kallon sumayya sai kuma ya juya ya kalli kalamu, ya sake kallon khadija?

Gyada masa kai tayi tana murmushi, shima murmushin yayi sai kuma ga hawaye, tare da matsawa kusa da gadon da sumayya take kwance, dukawa yayi akan gwuwar sa hannu yasa a hankali yana shafa fuskar sumayya,  dake kwance sanye da kayan asibiti, tayi kyau tayi fresh irin na masujego, wannan ce sumayyar tawa ashe haka take da kyau masha Allah?

Itace yaya kaga wa’innan jarirai nakane.

Da sauri ya juya yana kallon kalamu da sauri ya mike tsaye hannu yasa ya Amshi babies in yana kallon su, yarane mata masu tsananin kama da junan su tamkar An raba kunu a kofi, gasu masu tsananin kama dashi kome nashine a fuskar yaran, gasu farare tass, rungumarsu yayi ya fashe da kuka.

Toh ragon maza baka da aiki sai kuka, mahmah da suka shigo cikin d’akin tun d’azun, amma basu ma san da su ba.

Da sauri ya nufi mahmah yana ce mata, mahmah kalli yaran nan, wai yarana ne kallesu fa ga sumayya mahmah kyakkyawa fa sosai?

.

Sunkuyar da kai abie yayi yana mamakin surkin nan nasa yau koh dai ya mantasa a wajen ne, shima da sauri ya nufi wajen da yarsa ke kwance, zama yayi a bakin gadon yana shafa gashin kanta daya hargitse koh ribon babu.

Mahmah ce ta karbi baby d’aya dada ma ta karbi d’aya goggo kam baki kawai ta sake tana bin kowa da ido, kalamu kallon babansa yayi dake gefe, ya gaidashi, amsawa yayi yana tambayar sa mai jiki.

Matsawa kusa da abie muhammad yayi ganin sumayya ta fara motse, a hankali ta bude idanunta dalilin kukan da yaranta suka sake dukan su biyu.

Tana bude idanunta bata sauke sa akan kowa ba sai muhamamd dake kanta a tsaye, kamar a mafarki haka ta kalli abin da sauri ta mike zaune har tana kokarin zamowa kasa, da sauri ya tarota, bi a hankali sumayya jikin ki ba kirfi.

Ai jin abinda yace da sauri ta riko hannunsa gam tana kwalama khadija kira, Amsawa khadija tayi da sauri ta karaso wajen”khadija yayanki ke mini gizau na kamasa “

Aunty ba gizau bane yayane

“Yaya kuma khadija mijina fa baya gani yau kuma naga wannan na gani”?

Aunty ya warke ne.

Ai sumayya najin haka ta sake dariya cikin farin ciki koh damuwa da jikinta batayi ba ta rungume mijinta, don ita sam hankalin ta vaikai wajen mutanen d’akin ba.

Mikewa abie yayi dasu mahmah zasu fita a dakin su basu waje don sukam kunya ne zai kashe su.

Nanne dake toilet tana wanke kayayyakin sumayya daya baci, tun d’azun take jin surutai a d’akin mikewa tayi tsaye da boket na kaya a hannunta ta bude kofar toilet ta fitoh, Wai khadija da kalamu anya kuna da hankali kuwa mara lafiya na bacci kuke surutai da wa……bata karasa ba tayi turus ganin jama’ar dake shirin fita a d’akin dasuka juyo suna kallonta.

Dada ce ta kama salati tana tafa hanneye, wanake ganin nan?

Abie ma da sauri yace Hafsa??

Nanne kam bata wani nuna reaction ba,  dayake tun daren jiya data gane sumayya tasan tabbas zata ga su abie, duk da saurin da take tabar asibitin kafun suzo don ita batasan sumayya gudu tayi ba, haka ma batasan itace Aunty khadija ba sai daren jiya.

Nanne bata wani Amsa ba bare ma ta nuna tasan abie, sai tsayuwar da tayi tana kallon sumayya data sake muhamamd tana kallonta sosai irin kallon nan na kewa da soyayya, cikin kuka tace” ummi”?

Sai a wannan karo nanne tayi magana, Na’am momcy?

Da sauri sumayya ta sauka akan gadon tana takawa a hankali cikin dauriya tayi wajen mahaifiyarta fad’awa tayi jikinta tana kuka yau kam ta rasa ina zata sa kanta, murnan samun babies koh murnan ganin mahaifiyarta koh mijinta dole tayi kuka, ummi karan kanta hawaye ne ya cika a idanunta tana shafa kan sumayya ya isa haka momcy yi shuru kinga ba lafiya bane dake koma ki kwanta, tana maganar tana rike da hannun sumayya har ta kaita bakin gadon ta aje ta.

Waini yau hafsa nake gani ne koh gizau idanuna kemin koh mafarki nake ne?

Itace dada Abie yace yana dafe kansa cikin takaici da bakin cikin abubuwan da suka faru a baya.

Mijin hafsa ne yace, Hafsa kin sansu ne daman nina d’auka koh iyayen yarinyar nan ce? 

Baban kalamu ne da kakarsa wannan kuma Addansa ce ta nuna sumayya.

Daga sumayya har kalamu da Abie a tare suka jefowa Hafsa tambaya lokaci guda, baban kalamu wani kalamun?

Da sauri abie yace hafsa ban gane ba wanene kalamu.

Nuna masa kalamu tayi dake tsaye cikin shock na abinda nanne tace, yanzun wai sumayya Addansa, ta yaya kamar ya?baigane ba?

“Ummi kina nufin kalamu d’an uwa nane”?

Hafsa kina nufin wannan yaro, yaro nane?

Kallon sumayya da abie hafsa tayi jin tambayar da suka jefo mata, eh kawai tace tana kama hanyar kofa zata fita tare da kallon mijin ta, yauwa Alan guburo mutafi naga dangin ta sunzo zasu zauna a gunta.

Ah ah hafsa zuwan mu bazaisa ki daina hidima da yarki ba.

Ah ah dada zan tafi , Allah ya sauwaka momcy. 

“Ameeen ummi in zaki dawo a kawo mini sabulun wanka”

Toh momcy muje kalamu koh zaka zauna ne?

Ah ah nanne muje yace yana kallon abie da mamaki wai wannan ne babansa, shi abin ma yajisa wani banbara kwai.

Kokarin fita a dakin suke a hankali abie ya kama hannun kalamu daya wucesa zai fita a d’akin, kalamu bazaka ma abie magana bane?

Murmushi kalamu yayi sai kuma yaji hawaye ya taro masa, abie ashe kanason na maka magana, shine zaka kyamace ni ka kyautata rayuwar yar uwata, amma ka wofantar da nawa rayuwar ka barwa uwata ni, na zauna a matsayin agola a gidan da, bana ubana ba ya maye gurbinka ina Amfani da sunan sa koh a makaranta, bai taba nunawa duniya bashi ya haifeni ba koni bansan bashine mahaifina ba, sai yau akan me zan maka magana ni bansan wani uba ba sai ……..

“bai karasa ba sumayya ta mike ta wanke sa da mari cikin bacin rai ta soma magana, karka kuskura ka fara abinda zai dame ka wallahi kayi kad’an ka zagar min uba na barka,ni a haka nake son abina koma me zaimin bazan taba kinsa ba” sai kuma ta kama kuka.

Da sauri nurses dake falo suka shigo d’akin, akan surutun dake tashi, hakuri aka basu akan za’a kiyaye magana ne mai muhimmanci ake, ganin kalarsu yasa su barinsu a dakin.

Daker aka samu suka sassanta nanne ta koma gida dasu goggo yayinda mazan kuma suka koma hotel sumayya ma ita da dada kadai aka bari a hospital.

Washe gari aka sallame ta saboda kyaun da jikinta yayi, don haihuwar duk da yazo da gardama amma tana haihuwa shikenan.

Gidan nanne aka maidata bata koma gidan hayansu ba,sosai ake kula da ita muhamamd a rana sai yazo sama da sau hudu, sai da sumayya ta kwana hudu da haihuwa kafun suka koma shirye shiryen dawowa jalingo don anan ake son yin taron suna gashi yan nijar ma sunce suna shirin zuwa, duk yanda sukayi ta rokon nanne ta biyosu taki tace bazataki bin umurnin mahaifinta ba na raba kanta da zuriyar shugaba, saida mijinta ya nuna bacin ransa da nuna mata yaranta nada hakki akan ta, sannan kalamu bazaiji dadin hakan ba tunda shima so yake yaje yaga dangin babansa, daker dai ta Amince washe gari da sumayya ta cika kwanan biyar sukabi jirgi saijalingo.

Muhammad murza idanunsa yayi yace a gidan sa da babansa ya sai masa a Amazon sumayya zata sauka, ba musu duk da abie yaso ta koma gida Amma ganin hafsa da Al’ameen basason hakan.

Gidan sumayya ta sauka dayake babban gidane ga d’akuna shiyasa gidan ya d’auke su,  duka harda su hafsa falmata su babayo muhamamd goggo dasu mahmah, kalamu kam shugaba family house ya sauka kuma ba karamin farin cikin ganinsa sukayi ba.

Babu inda haihuwar sumayya bai bazu ba jama’a sai tururuwan zuwa dubata suke harda yan Abuja laila ma daga adamawa ta gangaro, a ranan yan nijar suka diro nageria gabaki d’aya yan uwan yusuf ne harda shi karan kansa ma, wannan zuwa harda lawiza da nabila, sosai gidan ya dad’a cika da yan uwa kota ina yan gidan shugaba ma tun a washe gari suna matan suka diro, yusuf a gidan sarki ya sauka dayake suma ana gobe suna suka zo, kai sumayya taga jama’a iyya jama’a ga wani irin lalle da aka watsa mata mai masifar kyau da ketson suna duka.

Yau take suna yara sunci suna NA’IMA da NA’IFA , tun Asuba yan gidan Adara suka diro su inna asabe inna lami Ana gindin murhu a sauke wanshan a d’aura wanshan, shanu uku aka yanka da rago biyu,  duk suna ta kan gyaran nama, ga abinci kala kala, gashi koh ina ka leka zakaga group group na mata kowa da angon su mai zafi,  wanda abie ya d’auki nauyi duka, yan nijar nasu da ban haka dangin adara, yan shugaba family house ga yan gembu, ashan gefe naga MATAR MAKAHO FAN’S  ansha anko na Atamfa mai ratsen flower green ana zazzaune ana dirkan shinkafa a manyan tireruka hhhhh.

Sumayya dake sanye da wani hadedden material gown wanda yasha dinki ga sarka na d’anyen gwal da sarki ya bada aka kawo mata, sarkane da dankunne sai warwaro ga agogo mai zafi na mata duka, tasha heavy make-up sai d’aukan hotuna suke da kannen Ammar dake sanye da Ankon su, khadija da kalamu dake zaune a gefe suna cin shinkafa.

Muhammad da Ammar harda su ramadan zulkiflu gidado badaru duk yanzun sun chanja kamar basu ba, suna zazzaune a kofar gida a rumfar da aka kakkafa abinci suke ci mairai da lafiya.

Tun daga nesa suke jin ihun yara da mutane suna rugawa a guje, da sauri suka mike gabaki d’ayansu suna kallon abinda ke faruwa.

Mutum suka gani kamar mace ne koh na miji bazasu gane ba, kadangaru manne a jikin sa tana gudu suna binsa wasu na jikin ginin unguwan suna rugowa suna binta sosai kota ina kadangaru ga wasu runduna na binta a baya, sai wata mata dake gefenta rike da sharbebeyar bulala tana kad’a mai kadangarun suna tafiya a haka.

Da sauri su muhammad suka ruga cikin gida da gudu har ana rige rige, ganin wajen da suke suka nufo.

Suna shiga suka rufe kofar gidan da karfi suna ji sai bugawa matar take akan don Allah abude mata, kiri kiri su muhammad sukaki budewa har abin yaja hankalin matan dake compound sosai, dada dake rike da jinjira zata kaiwa kawayen ta dake falo a zaune ssga dayar, itace taji hayaniya aje jinjiran tayi ta fitoh compound, ganin su muahmamd da jama’ar tsakar gidan a tsaye yasata karasawa bakin get in tana tambayar dalili, kafun ma su muhammad suyi mata bayani tuni tasa hannu ta zare sakatar get in, ihu Ramadan ya sake tsabar rikita yare ma ya fara.

Dada na budewa idanunta ya sauka akan matar dake rike da bulala kwalalo ido tayi cikin mamaki tace  wanake gani anan kamar Nafi………….

kafun ma ta karasa maganar ta idanunta ya sauka akan wance ke tsaye mammanne da kadangaru ga bataliya a kasa, ai ihu dada tasa ta ruga ciki da gudu, da sauri inna lami tazo  zata rufe get aida sauri wannan matar ta banke kofar ta kora mai kadangaru ta shigo, itama  shigowa tayi, ai ana ganinta, ihu ne yake tashi abinka da mata atake masu Aljanu Aljanunsu ya soma tashi, gidan suna gabaki d’aya ya rikice ya zama gidan tsere kowa gudu yake yana burmuwa falo wasu kitchen masu Aljanu kam sun zuzzube…………..

✨Ruqeenjalal✨

Back to top button