Uncategorized

Matar Makaho Part 14 Hausa Novel

 MATAR MAKAHO

Chapter 14

Bayan Auren abie da safina, a lokacin safina tafito da duk wani mugun halinta a gidan, ta buwayi kowa, har dada bata ragarwa ba, shikuma abie daman ba sonta yake ba,  shiyasa sam koh ana meeting, safina naci musu mutunci baya saka bakinsa a maganar, tunda su suka kakkaba masa ita, badason rasa ba.

A lokacin safina tasaka sumayya a gaba da duka zagi, sai da dada ta sanar da abie, ranan da yasan abinda safina ke aikata wa yarinyar sa in baya nan, baraxanan  sakin ta yayi ya zazzage ta, kai ranan anyi kwanan bacin rai a gidan.

safina ganin auren ta zai iyya mutuwa yasa ta shafawa kanta lafiya, bata koh ga maciji da sumayya, daman ba’a hannunta take ba, a hannun Dada ne.

Lokacin da sumayya takai shekara 12, har lokacin safina(momy)bata haihuba, kuma abie bai wani damuba, tunda yana da sumayya, duk wani soyayya da kulawa sumayya na samu a gidan, baga bappanayen taba, ba dada ba ga abien ta, momy ce kawai bata kaunar ta, har lokacin safina na tare da nafisa, duk da nafisar ta koma gidan tsohon mijinta, lokacin.

Haka kawai sumayya ta waye gari duk yan gidansu basa kaunar ta, daga su babuji har matan su, dada karan kanta bata shiga tsabgarta sai in babu mutane a wajen, ga tsoron momy da suke, da bin umurnin ta kome tace jiki na bari zasuyi inka cire abie,  sosai sumayya ta shiga wani irin mawuyacin hali, abie inta ne kawai ke tsaya mata akan kome, baya taba yarda a cutar da ita, kuma duk wanda yama yarsa abu a ranan zaiga bacin ransa, ana hakan ne fa momy rana tsaka ta dake sumayya, wai ta b’ata mata labulen d’aki da lalle, a ranan abie saki d’aya ya mata ya korata.

Amma safina taki tafiya, dada tace sayya maidata d’akin ta, ganin matsaloli da sumayya keta fuskarta a lokacin, ga kananun shekaru, abin harya fara tayar mata da kewar mahaifiyarta, yasa abie saka a FGGC boarding school, ta cigaba da rayuwan ta a hostel, shikad’ai ne gatan ta, sai wata rana Dada tana zuwa mata visiting a boye, kuma tace mata karta fad’awa kowa tazo wajen ta, sumayya koh marmarin komawa gidansu hutu batayi, amma hakan take komawa in anyi hutu tana Allah Allah a dawo hutu.

Sumayya lokacin da ta cika budurwa, ta tashi da wani irin hali, akwai jijida kai da ganin tafi kowa, kasancewar ta mai kyau, ga Arzikin gidan su, ga rashin sabo da mutanen gidan,  ga rashin mafadi don har lokacin xaman hostel take.

Sumayya inta dawo hutu duk yanda saurayi zai biyota, saita raina masa arziki gani take kamar tafi karfin sa, in kuma yakasan ce mai kudi sosai, sai taga kamar zata samu wanda ya fisa, in mai kyaune sai taga kamar nan gaba zata samu wanda ya fisa kyau, sumayya nada kawaye, koh saurayin kawarta ta gani ta ringa dariya kenan, tana kushe sa mummuna talaka kaza kazan, wasu Friends inta da dama in auren su ya tashi basa gayyatanta, saboda rainin wayo da take zuwa ta musu a wajen biki.

Lokacin da sumayya tayi candy, taci jamb A lokacin tana da shekara 18, aka shiga university sai abin ya d’ara na da, ganin yanda ake tururin sonta, babu ranan da zata fita ba’a biyo taba, hatta cikin gidan su Abdul(wanda lokacin da sukaje gida, bayan aure aka mata wulakanci, yace zai rage musu hanya ita da khadija)da kaninsa sunsha dambe akanta, Amma haka ta murza ido tace basu mata ba, karshe dai Abdul aure yayi,  harda yaransa biyu ya fita harkar sumayya.

Sumayya bata gane kuranta ba, sai lokacin da takai shekara 23 lokacin ta kammala digree inta har tayi service, zuwa lokacin duk samarin ta sunja jiki da ita, kowa yana baya baya koh hira suke ta sako musu zancen aure, sai su kama kaucewa wasu kamma gudu suke, rabin kawayen ta duk sunyi aure, sai d’aid’aikune suka rage.

Bayan dawowar ta gida lokacin yaran gidansu sun d’ara nada, a yawa wasu sunyi aure wasu na aiki, itama rashin miji yasa abie nema mata aiki a bank nasu dayake aiki , dayake statistic ta karanta, tana aikinta tana samun Albashin ta, Amma maganar samari fa babu yanzun, ita karan kanta aure take so Amma babu mazan, ga kyau ga aiki ga kudi, mijine kawai matsalar ta.

Shekara 2 sumayya tana aiki a bank lokacin tana da shekara 25 a duniya, ganin haka yasa dada nema mata maganin farin jini, amma ina tayi tayi abin shuru, karshe dai dada ta nemi kanin abdul ya dawo su daidaita da sumayya, amma ba kunya a idon abie yace shi bazai aure sumayya ba, yarinya yar 15 xai nema ya aura ba rikekkeyaba abinnan yama abie zafi matuka, hakan yasa sa zagin kanin Abdul sosai abin ya zama babban magana.

Wannan dalili yasa babuji rantsuwa sai sumayya ta fitoh da mijin aure nan da wata uku, tunda dai zaman ta a gida fad’a zata had’a  a tsakanin su, kamar yanda momy ta kitsa musu, don Abie indai akan sumayya ne baya ganin kowa da gashi, jin abinda akace ma sumayya yace sam bai yarda ba, ga yaransu su kubra da miemie sun girmi sumayya ba’a saka musu ka’ida ba sai yarsa.

Kuka dada tasa akan abie zai nuna musu iko da sumayya, abinda ya sa abie yarda kenan, sumayya har wata uku ya shige bata samu miji ba, su babuji sukace aikin da take shiya hanata aure, hakan yasa sukasa abie dakatar da aikinta.

Sumayya kam ganin an rabata da aikin ta da tafi so, don lagon sumayya kenan, kace zaka kaita garin su mamanta, koh kace makaranta, hakan yasata d’aukar takardun ta, ta tafi asibiti neman aiki babu wanda ya sani.

Dayake result nata nada kyau, yasata samun aiki a pharmacy tana musu lissafin kudin magani.

Kullum take fita aiki, ba tare da aisan ina take zuwa ba, abie bincike yayi ya gano aiki take zuwa, wannan ne  dalilin kwace mata ducument da yan uwan mahaifinta sukayi, sannan suka rabata da aikin ta.

Ta dawo zaman gida, daga baya taga bazata iyya ba, tanemi shagon make-up tana zuwa training,  daman ta iyya lalle, da sukaga ba sarki sai Allah, yasasu barinta tana zuwa koyon make-up in, basu hanata ba.

Sumayya ta cigaba da koyon make-up, har ta iyya aka sallame ta, taso abie ya bude mata nata shagon, Amma yaki karshe dai kawaye da yan gidansu, in sun tashi aure koh yan unguwansu take ma, ana hakan ne lokacin Aikin hajji yayi, kamar koda yaushe daman duka gidan ake tafiya hajji koh wani shekara, amma bana sunce baxasu ba, sumayya da abie suje.

Ba musu sumayya suka tafi aikin hajji, wanda zuwa lokacin bazata iyya kirga sau nawa taje ziyaran d’akin kaba ba, bayan sallah abie ya dawo, sumayyya kam daman akwai yar babuji dake aure a saudi, kin dawowa tayi ta zauna agunta har sai da tayi wata 7,lokacin ta cika shekara 26 ta dawo,  kamar wasa tana  dawowa yan gidan sukace sun mata miji, akwai wanda ya ganta yana so, hankalin sumayya ya tashi a lokacin, amma abie ya kwantar mata da hankali, akan zaiyi bincike akan mijin.

Duk yanda abie yaso yan uwansa su sanar dashi waye ne mijin, sunki Amsa d’aya suke basa, shine sun isa da yarsa, haka ba yanda ya iyya dagashi har sumayya suka zubawa sarautan Allah ido, sumayya duk azanta wani shararen mai kudi za’a aura mata, koh d’aya daga cikin samarin gidan.

Abu kamar da wasa, ya zama gaske don maganar auren sumayya babu inda baije ba,  sai shirye shirye ake duk da ba auren soyayya bane, sumayya ta kwantar da hankalin ta koh banza tasan mijin classic za’a bata koh ajeboter.

RANAR D’AURIN AURE

Sai da sumayya ta tuno da mahaifiyar ta, haka kawai ranan tunda ta tashi sai kuka take,  shi karan kansa abie a zullumin rabuwa da yarsa yake, yasan ba’a kyauta mata ba sam.

A waje kofar gidan shugaba, ake shirye shiryen d’aurin aure, sumayya dake d’aki da kawayen ta Ansha kwalliya kamar me, za’a aure classic kanta sai wani kara fashewa yake yanzun kam koh kukan ta daina,  ji kawai sukayi Ana Alhamdulilahi An d’aura auren sumayya Abdulsalam shugaba, tare da Angon ta Muhammad Al’ameen yusuf, akan sadaki naira dubu 20, da mamaki sumayya tace “dubu ishirin kuma?wani irin mijine haka dubu ishiri ai mu tunda muke aure a gidan nan ba’a taba biyan sadaki haka ba”

Kawarta ce ta kalleta, kai sumayya sadaki fa Albarkansa ake nema, ba yawa ba kika sani koh mijin Alu-sunnah ne, irin samarin nan ne ustaxai, ga gemu ga d’angalalen wando kinsan fa irin su sunfi dadi love.

Gabaki d’aya kawayen dake d’akin dariya suka saka da shewa, don harga Allah sun d’auka mai zafi sumayya zata aura, sanin da suka ma halinta na rainako, ke ina ga fa irin samarin nan ne yan  20 something zuwa 30.

“Allah ya sauka bakin ki ya sare guntun kashi, habba 30 ai nima na fara jin kamshin, 30 ina laifin 35 irin ya bani shekara 9 nan” sumayya ta bata amsa 

Duka suka kwashe da dariya, ana ta nishadi, kamar daga sama suka fara jin hayani yana tashi a babban falon gidan, muryar abie ne yake cewa bai yarda da auren nan ba, bazai yafe ba arasa wa za’a aurawa yarsa sai miskini, saboda babuji yaga ba yar gaddafi bane koh Abubakar shiyasa har ya iyya had’ata da yaron nan, yau sai an raba auren bai yarda ba, jin haka yasa sumayya da kawayen ta rugawa da gudu suka shigo falon don jin ba’asi.

MAKAHO ne ya ganta yana so, ba sai a basa ba tunda ba manemi bane da ita, babuji yace.

Kafun abie yayi magana sukaji timmmm sumayya ta yanke jiki ta fad’i jin wai MAKAHO aka aura mata ita sumayya.

***********

Bayan sumayya ta farfado duk borinta da masifar abie, dada tace a yau innan sai ankai sumayya gidan mijin ta, koh ta d’aga masa nono, ba yanda abie ya iyya yana ji yana gani aka sabi yarsa a mota, tare da babban mota na kayan d’akin ta, dana gara wanda kome set uku aka mata gado uku kujeru uku firij uku kome uku uku aka mata hada kayan kitchen, kawayen ta fa sun samu abin yi, sai dariya suke suna yad’a mata bakar magana,  especially wa’inda sukayi aure, sumayya a ranan tayi kuka har saida tayi Addu’a Allah ya d’auki ranta,saida wata yar uwar su na gembu ta mata wa’azi kar bacin rai yasa tayi sabo.

Ai bata tashi ganin bacin rai ba, saida motar su tayi fakin a kofar gidan Adara, wani gidane irin na talakawa mai jan kasa sai kofar gidan da babu kofa, lulubi aka mata suka shiga gidan, amma kamar ba gidan da za’a kawowa amarya ba, babu wanda ya tarbesu asalima kowa harkar gabansa yake kamar ba’aga zuwansu ba, tambayar kofar amarya sukayi aka nuna musu, wani samurmurin d’aki koh kewaye sa ba’ayi ba, d’akine d’aya kankani wani rubebe dashi, ihu sumayya tasa ta tsunguna agun tana sakin kuka itakam tata ta sameta.

Ga auren MAKAHO ga talauci dame zataji,  Allah ya isa ta farama su babuji, tana sun cuceta, a hakan dai aka wuce d’akin, yar uwar dada ce ta tura rubebben kofar da koh sakata bazai zauna ba tsaban rubewarsa, suna bude dakin ba laifi a wanke yake sai dai babu kome sai cinyayen taburma da ghana must go na kaya kad’ai a d’akin, su karan kansu masu jeren ma sun rasa ta ina zasu fara, wanda aka kawowa set uku shine aka samu d’aki d’aya karami.

Da gudu sumayya ta b’anbara ta bar gidan, kawai su dada na zaune sukaga amarya ta faso da gudu ta dawo gida”wallahi bazan xauna agidan shan ba”wannan shine abinda sumayya tace, kuma ba wanda yayi maagana.

Wannan hajiya yar uwar dada ita tayi waya aka kira mata kafinta, a take yaxo shida abokan aikinsa uku,suka buga musu kofar daki, a ka cire tsohon dayake yammane, wasu daga cikin yan uwan,  kwana sukayi washe gari kafintoti suka gama aikinsu, sun kewaye kofar da falange an mata band”aki a kofarta, an saka silif da kitchen da baranda, Amma fa kaya bai d’auka ba koh set d’aya basu samu shigaba,  haka aka juya da sauran kayan.

Abie da kansa a ranan da , dadare ya dawo da sumayya bisa umurnin dada,haka aka watse aka bar sumayya da halinta,  wasu sun mata wa’azi wasu kam magana suka gaggaya mata.

Sumayya tunda suka watse aka barta kuka take,  gashi dare ne tana zaune akan gadon tana kuka cikin bakin cikin wannan al’amari,  sai a ranan wani irin kewar mahaifiyarta ya kamata da ace mamarta na tare da ita da abubuwa zasu mata sauki.

Duke take tana kuka baji ba gani wai itace da aure a irin wannan gida……………..

Tas sumayya ta sanar da Ammar duk irin wahalar da tasha, da burinda taci na ganin tayi wa muhammad wulakanci, harsai yaji a jikinsa kafun tanemi sakin ta, amma saboda kyawawan halinsa da hakurinsa don babu abinda sumayya bata masa ba, amma bai taba nunawa koh a fuska ba, bai taba riketa , da wani manufa a ransa ba, kullum kokarin faranta mata yake, wannan sune makamin da yayi tasiri wajen mallakar zuciyar sumayya,  taji zata rayu dashi a haka, sannan ta d’auki auren su da Al’ameeen isharane Allah ya nuna mata, akan halinta, kuma ta karbe kaddarar ta, tazauna da mijinta….

cigaban labari………

“Sannan yau suce wai na rabu dashi akan me”?

D’aga ido Ammar yayi ya kalli sumayya da khadija dake kuka, lokaci guda, sumayya!!ya kira sunan ta.

“Na’am”

Kukan ya isa haka abinda nakeso dake shine ki d’auki duk abinda ya faru a matsayin jarabawa, kamar yanda kikace, naji duk abinda iyayen ki suka miki, Amma ke me kika fahimta akan auren ku da muhammad, da gaske bashi yace yana sonki ba?

Gyara xama sumayya tayi ta zayyana masa labarin muhammad, da irin wahalhalun da yasha.

Tabbas Ammar ya tausayawa rayuwar su muhammad, kuma a cikin labarin sa da sumayya ya auna wasu abubuwa da dama akai, sai kuma abu na biyu, sumayya kina nufin mamar ki sunan ta hafsa sannan yar maiduguri ce?

“Eh Amma bansan  a ina take a maidugurin ba”

Amma naji mahaifin ki yace zai kaiki wannan karon.

“Ni yanzun bata maiduguri nake ba, ta mijina nake”

Sumayya kiyi hakuri ki koma gidan naku,  tunda naga iyayenki zama a gidan Adara ne basaso kiyi, in Allah yasa Al’ameen ya dawo,  kinga shikenan sai ki dawo d’akinki, in ma basason zaman gidan ne, nizan nema muku wani gidan saiku koma, amma a halinda kike cikin nan ya kamata ki kula da kanki, juna biyu ne dake ga dp ki na hawa, koh kinaso ki rasa babyn nakune?

“Ah ah yaya Ammar”sumayya ta amsa masa.

Yauwa koh kefa kiyi hakuri ki koma gidan kinji?insha Allah auren ki da muhammad bazai mutu ba.

Kuka sukaji da karfi a gefen su, khadija ce ke kuka.

Kee lafiya menene haka?

Kallonsa khadija tayi da haushi jin tambayar da ya mata, toh ba kai bane kake cewa Aunty ta tafi, toh ni kuma in zauna dawa?

Da goggo mana zaki zauna, ba za’a bude makaranta gobe monday ba?saiki cigaba da zuwa kafun yayan ki ya dawo.

Kuka khadija ta sake, shikenan aunty yanzun tafiya zakiyi ki barni.

Toh koh zaki bita ne gidan nasu?koh taki bin umurnin iyayen ta akanki?khadija iyaye fa ba wasa bane?ammar yace cikin haushi

Shuru ta masa, sai ga likita yazo ya basu sallama, don sumayyar ba wani jin jiki tayi ba,   ruwan da aka saka mata ya kare.

Suna Fitowa taga Ahlin gidansu tim a cike a haraban  asibitin, kala batace musu ba Tana bin Ammar a baya,  ga khadija a gefe.

Tashi sukayi suka bisu a baya har packing space, sumayya motar Ammar tayi niyar shiga Amma dada tayi tsalle ta dire akan ba inda sumayya zata shiga, sai motar gidansu.

“Kinsan Allah dada in kika matsamin saina fasa bin naku naga ta tsiya” sumayya tace.

Yi hakuri kawalli jeki shiga na Abokin mijin naki.

Shiga motar sumayya tayi ta kalli khadija dake tafiya a hankali kamar kwai ya fashe mata a ciki, daga ka ganta kasan tana cikin matsanan cin damuwa, “ya Ammar ka fad’a musu bazan koma yau ba sai gobe, sutura driver yazo ya d’auke ni inna shirya kayana”

ba musu  Ammar ya fita a motar daidai lokacin khadija ke kokarin shiga, yaje ya sanar dasu basu wani d’aga hankalisu ba sukace goben insha Allah abie da kansa zaizo d’aukar ta, in kayan sawane ma?ta bari kawai za’a saya mata sabbi.

Amma sumayya tace ita sai ta kwana washe gari zata koma gidan su.

Bayan isar su sumayya gida, Ammar tafiya yayi, khadija ta kalli Auntin ta, yanzun Aunty da gaske zaki tafi ki barni?shikenan ni babu yaya babu ke banida kowa yanzun sai goggo?

“Khadija baxan barki ba koh babu yayan ki Zan kula dake, guduwa zamuyi daga jalingo, gobe goben nan da asuba zamu bar gari

“Zamu bar garin”

A matukar Mamaki khadija tace, barin gari kuma Aunty?

“Eh khadija barin garin zamuyi don wallahi baxan iyya xama a gidan muba, yanzun kwata-kwata naji bana kaunar gidan, da zama a cikinsa, kinga yanzun ma tashi ki tafi wajen shagari kice masa karya rufe shago, bayan isha’i muna zuwa akwai maganar da zanyi dashi, kibi gidan goggo ki d’auko abubuwan ki masu Amfani harda takardun ki, kiyi sauri kizo mu shirga kaya”

Aunty ban gane ba?wani irin abune haka ni gaskiya nama hakuri, ki koma gidan naku Allah ya dawo da yaya lafiya, yanzun in muka tafi yaya ya dawo bamu nan ba?

Cikin jin haushi sumayya tace”sai dai ke ki zauna, koh zaki bini koh bazaki bini ba zaman garin nan bazan yisa ba kinji na fad’a miki”

Shuru khadija tayi tana nazarin sumayya koh dai bata da lafiya ne? ace mutum lokaci d’aya ya birkice haka, Amma dai batayi magana ba tasa hijab nata zata fita.

“Khadija”

Na’am aunty.

 “Ban saki ki sanar da kowa maganar nan ba,  koh goggo ban yarda ta sani ba, inta tambaye ki me zakiyi da abinda kika d’auko kice mata nina ce ki d’auko kayayakin ki, na nan yayi datti”

Toh aunty kawai khadija tace ta fita.

Bayan fitar khadija, akwatuna sumayya ta saukar, tana shirga kayan ta kama daga na sawa harna amfani, daman har yanzun akwai wa’inda bata dinka ba, hotonan su data lika a bango duk ta cire ta saka a akwati,da system inta, sauran kaya daya rage ta barsu a wardrop, kayan muhammad ne kawai bata taba ba, kome nata ta d’an tattara harda make-up ket nata, saida ta cika akwatuna hudu da kit da kaya, ta barwa khadija akwati d’aya tasa kayanta a ciki.

Khadija na dawowa ta sata had’a kayanta a akwati d’aya, da dare ita da khadija suka shiga keke-napep da akwatunan kaya, ba tare da y’an unguwan su luraba shagon shagari ta kai ta ajeye, shikaran kansa yayi mamakin kuma ya tambaye ba’asi, amma sumayya tace ya bari gobe zata masa bayani yanzun dai karya sanar da kowa, gobe da asuba ya bude shago tana zuwa.

Ba musu ya aje mata kayan, bayan sun koma gida waya sumayya ta d’auka ta kira principal nasu khadija, ta masa bayanin tafiyan gaggawa ya same su, suna bukatan transfer letter na khadija, ba musu yace gobe da safe tazo school ta karba.

Karfe uku na asuba sumayya ta tashi,  tafasa ruwan zafi tayi, tayi wanka tasa khadija wankan asuba suka shirya cikin hijabai manya da socks, saboda yanayin garin, zanin gadonta guda uku dake d’akin ta dauko ta lulube gado ta da d’aya, d’ayan kuma kujera ta lulubawa, d’ayan kuma wardrop, zaninta babba ta lulube TV dashi.

Dayake sunyi Alwala sallah kawai sukayi taja kofar d’akin ta rufe da kwado, key ta aje a inda Al’ameen yake ajewa in basanan, fita sukayi ita da khadija kam sai binta take, ba halin magana babu kome a hannun sumayya sai purse nata, wanda waya da ATM ke ciki sai y’an changen da baza’a rasa ba, shagon shagari suka wuce kamar yanda sukayi Alkawari, haka take don shagari ya bude musu shagon, tattara akwatunan sumayya take don burinta kar gari ya waye tana sintali bata fita ba.

Aunty sumayya wai don Allah meke faruwa ne?

“Shagari zamu bar gari ne da khadija”

Barin gari kuma Aunty, wani abin aka miki?

“Ba kome shagari gida akeson na koma ni kuma yanzun bana kaunar komawa gida”

Toh yanzun wani gari zaku tafi, gashi jiya na saro kaya, kwata-kwata dubu 100k ne a hannu na bara na d’auko muku?

“Tsaya shagari daman Wannan kudi bana muhammad bane na Ammar ne, don haka kaci gaba da kasuwancin ka kamar da, duk ranan da Ammar ya nemi kudinsa saika basa,  uwar kudin kuma saika kama kasuwa dashi nasan zuwa yanzun ka kusa ninka kudin biyu, abinda nake so dakai shine in muka tafi kayi Register n jamb in lokaci yayi, ka koma makaranta, har ka kammala da kudin da kake nema, tunda mai shagon baya nan babu Amfanin kana ta tara Arziki bakaci,kayi Amfani dashi Allah yasama kasuwar Albarka.

Ameen Aunty nagode Allah ya bayyana oga, amma don Allah ki karbi kudin aunty sumayya karki ce ah ah.

Ganin ya nace yasa sumayya karban 50k tabar masa sauran don yaro tausayi yake bata.

 in babu damuwa ki bani number ki duk lokacin da akaji labarin oga saina kiraki, yace yana kallon khadija dake rabe a gefe tana hawaye haka kawai yau take jin wani irin kewar sintali, yanzun tafiya zatayi tabar sintali harda garin gabaki d’aya.

“Gashi ” sumayya ta mika masa wayar sa daya bata tasa masa layin ta,shiya tare musu keke-napep da asuban nan ya loda musu kayansu, akwati shida rus a ciki mai keke yaja machine insa, a hankali khadija ta leko kanta tana d’agawa shagari hannu wanda hawaye ya cika masa ido, don shi harga Allah son khadija yake kawai kunyar fad’a mata yakeji ganin kankantar shekarun sa, dayasan irin wannan rana zaizo dako ba kome tasan da sonta a ransa, koh ina taje tasan tana ransa.

Bayan su sumayya sun tafi road block da asuban nan, tama rasa wani gari zatace zata kuma gashi tana son barin khadija taje ta karbo mata transfer letter nata, na makaranta maganar karatunta karya koma baya, aje khadija tayi a gefen tashar ta kama hanyar science, ba ita ta samu ganin principal ba sai kusan 7:30, ya kaita wajen exam officer daker dai ta samu transfer letter in, tasha ta koma amma zuwa lokacin duk mototi sun tashi sai kalilan suka rage, wajen da khadija take ta nufa, har lokacin tana zaune da tulin akwatunan su a gaba, abin duniya ya dame ta.

“Kee khadija tashi ga mota shan naga ya kusa cika muje muji na wani garine”

Mikewa khadija tayi, aunty kin samu lettern ne?

“Eh na samu khadija daker baki ga har gari ya waye mini ba”?

Gaskiya ne  muje toh aunty .

Wajen motar suka nufa suka tambaye ta wace gari ne, akace musu motar Abuja ne saura mutum uku, babu wani shamaki sumayya suka shiga, dayake motar babban mota ne ba karami ba, akwai space, Alelen akwa sumayya ta sai musu na 200, da gyada na 100,  ta had’a musu da goran faro biyu,  sai masa na 150, suka shiga dashi motar, suna shiga koh, aka samu mutum d’aya ya shigo aka tada mota, lumshe ido khadija tayi hankalin ta a tashe yau za’a bar gari.

Sumayya kam koh a jikinta, sai cin Alelen ta take tana had’awa da ruwa, koh a jikinta bata san inda zasu ba, bata da wanda ta sani a Abuja Amma koh a kwalar riganta.

Haka khadija da sumayya suka wuni a mota, don an sauke su sun sake shiga wani,  khadija ta kasa cin kome, amma banda sumayya kome ta gani in an saya a hanya, saya take taci abinta, har mangari ba suka isa Abuja aka sauke su a tasha saboda yanayin tafiyar su .

Sumayya gabaki d’aya tayi laushi likis don ita ma ba wani tafiye tafiye take a mota ba, sai yanzun takejin gajiya ga karamin ciki, tama rasa ina zasu nufa gabaki d’aya gashi mangariba yayi, a gefen tasha ta samu suka zauna ga kayansu a gabansu tirim, gabaki d’aya ta galabaita a zaune suke har isha’i suna tasha, a zaune tama rasa wazata tambaya inda zasu samu wajen kwana, banda hotel.

Kamar daga sama taga wata ta dafa mata kafad’a da sauri da d’ago”laaa laila kece”?sumayya tace cikin mamaki.

Oh duniya nifa tun mangari ba danazo tashan nan, nake ta kallon kamar kece kamar bake ba, sumayya naga kinyi jiki gaki a tasha nasan kuma kinfi karfin tasha, wallahi har zan tafi daga baya kawai na fasa nace bara dai na sake tabbatar wa bake bace.

“Wallahi nice laila”

Amma sumayya meya ajeki har war haka a tashan nan, gaku mata kuma ba sana’a ne ya kawo kuba?

“Wallahi laila bana da inda zan sauka zaman da nayi nan, ina tunanin ina zani kowa na tambaya sai yace wai sai dai hotel”

Toh yanzun dai dare ne ki tashi muje mijina baya gari saiku kwana washe gari zamu tattauna ki dubi gabaki d’aya kin jirkita.

Mikewa sumayya tayi a hankali laila da khadija ne suka tattara kayan zuwa cikin mota.

Suna isa wani gidane d’an madaidaici mai kyau sosai irin gidajen hayan nanne na zamani, ba ruwan wani da wani, kowa sa sassan sa amma dai  gidan ya had’u, sashen laila suka shiga, yana d’auke da two bedroom da falo da toilet a ciki sai daining Area, ga tiles kota ina,  irin dai gidajen hayan Abuja nan, gashi a unguwa mai kyaune akwai gidajen manya a unguwan sosai.

Bayan sun shiga kofar laila d’aya d’akin laila ta sauke sumayya, wanka sumayya tayi da khadija, laila ta kawo musu abinci sukaci, kwanciya sumayya da khadija sukayi a kan katifar dake cikin dakin, kayayyakin su a gefe, a haka bacci ya d’auke su tsabar gajiya.

************

Ta bangaren mutanen jalingo…

Tun da safe Ammar ya shirya yazo gidan su sumayya, lokacin karfe 9 na safe, yana isa kofar Adara ya tura yaro ya kira masa sumayya, amma yaro ya dawo yace masa sumayya bata nan kofarta a rufe.

A zaton Ammar koh su abie da sassafe suka zo suka tafi da sumayya, hakan yasa-sa wucewa gidan goggo ya aika yaro ya kira masa khadija, ba’a jima ba saiga goggo da yaron sunfitoh tare.

Bayan sun gaisa goggo ke sanar dashi ai khadija na gidan sumayya agun ta koma da zama, da mamaki ammar yace ai gidan yaje ya tura yaro,  yaro yace basanan.

Da mamaki goggo ke kara maimaita basanan kuma?kamar ya don ita dai batasan wainar da aka toya ba jiya.

Kadai san halin yara wani sa’in suna da iyya shege taima ma basu je kofar sumayyar ba suka dawo sukace maka bata nan, inba haka ba ina sumayya zata da safen nan?

Ammar baiyi magana ba ya juya ya koma kofar gidan Adara, wannan karo da kansa ya shiga har kofar sumayya, turus yayi ganin kwado a makale a kofar abin Al’ajabi toh koh yan gidan nasu sun d’auke tane? gashi yan gidan Adara ba mutunci bane dasu bare ya Tambaye su.

Fita yayi  kofar gidan ya tsaya yama rasa me zaiyi don shi gabaki d’aya tunanin sa ya basa khadija tabi sumayya gidansu kenan, kuma me yasa basu ma goggo sallama ba,motar sa yake kokarin shiga saiga mototin su abie, dakata wa yayi yajira sukayi packing yana mamakin ganinsu.

Matsawa yayi garesu suka gaisa, Anan nefa yakejin wai sunzo d’aukar sumayya, da mamaki yake sanar dasu ai sumayya bata nan kofar ta a rufe tun 9 yazo mata sallama amma bai ganta ba.

Ai abie baisan lokacin da ya zauna a dakalin kofar gidan adara ba, ya dafe kansa shikam ya shiga uku, Anya sumayyar sa daya sani ne mai tsananin sonsa da masa biyayya Amma yau ya zana mata layi ta ketare, sai yanzun yake nadamar auren ta a gidan Adara,  don shi duk ya ta’alaka rashin jin sumayya, da auren tan nan da suka mata, tunda har tasan tasa kafa ta gudu, don dada da kanta taje kofar sumayya ta sake lekawa taga a rufe, ga shagari dayazo wucewa ma ya musu bayanin tun asuba sumayya suka bar gari, waya Ammar ya fitar yayi ta kiran sumayya amma bata d’agawa,  Abie ma yayita kira Amma ba’a picking karshe dai dukansu suka d’unguma har tasha, Amma koh maikama da su basu gani ba,  kowa suka ma kwatance sai yace bai gansu ba.

Haka abie suka dawo da sanyi jiki gabaki d’aya hankalin sa a tashe,  yar yarinyar sa guda d’aya dayake da ita, tasa kafa ta shiga duniya ita da ba sanin kowa tayi ba ina ta shiga, Ammar karan kansa tafiyar sumayya ya d’aga masa hankali, wani irin abune haka sumayya ta aikata yanzun barin gari da tayi menene Amfanin sa,  yau in muhammad ya dawo fa, me zaifad’a masa don Allah, gashi wani Al’amari mai girma dake zuciyar sa yana shirin fiddawa sumayya tasa kafa suka gudu da khadija shidai ya bonu.

***********

Washe gari bayan sumayya sun tashi da asuba sunyi sallah wayar ta ta d’auko wanda tasa a silent ta bude ganin miss call na yan gidan su, da sabon number har da messenge yasa ta bude wayar ta zaro sim in dake ciki ta bude Aljuhun akwatinta ta saka sim in a ciki, sannan tama khadija gargadin karta fad’awa kowa gaskiyar abinda ya kawo su Abuja,  koda kuwa laila ce ta bari da kanta zata mata bayani.

Khadija ce tama laila shara da moping in tiles, sumayya kam bacci ta koma don har yanzun akwai gajiya a jikinta, sai kusan 10:00 suka karya su uku saboda yaran laila biyu ne kuma duk sun tafi makaranta abinsu.

Laila ce ta kalli sumayya,sumayya gaskiya nayi mamakin ganin ki a tasha jiya, garin yaya zakizo gari bakisan kowa ba?gari ma irin Abuja sumayya wallahi jiya ban d’auka ke bace don rabon mu dake tunda muka gama school, ban sake saki a ido ba,dayake a lokacin bata mu ake ba manyan yara.

Dariya kawai sumayya tayi tana kallon laila, Allah sarki rayuwa da laila ba karamin sonta take da kawance ba, amma  kullun sai tayita wulakanta ta , gashi yau itace ta mata rana gaskiya ne da akace A rayuwa koh wani mutum yana da ranan sa”wallahi laila  tafiyar gaggawa ce,  bamma sa tsamanin Abuja zanyi ba”

Bangane ba sumayya?gaki na ganki da ciki don nasan wannan jikin naki da biyu ne.

“Hhhh kai laila ba halin nayi jiki kenan”?tayi maganar tana kallon khadija data mike ta koma d’akin da suka sauka, jin hiran nasu na manya ne.

Ah ah sumayya wannan jikin yafi karfin jikin jin dadi, kinga yanda kirjinki ya ciko ga hips yafi kome cika kamar me, ga jikin ki ma yayi d’anye.

“Ke abar zancen nan ni duk ba wannan ba, a ina xan samu gidan haya kamar nakun nan, na kama”?

Ah ah sumayya baki bani Amsa ta ba tukunna?cikine dake koh ba ciki ba?

” cikine laila”

Ok Aure kikayi ne, kuma meya kawoki Abuja da yarinyar shan?

“Aure nayi laila, dalilin zuwa na kuma mijina akayi kidnap insa shiyasa nima na gudo daga Taraba na dawo nan” 

Baki da gidan iyaye ne? naga dai ke yar masu haline baza’a rasa tsaro a gidan kuba ai?

“Kinga laila rabu dani bana sha’awar komawa gidan mu kwata kwata wallahi, kawai in zaki nema mini mafita ki nema min tunda kikace mijinki yau zai dawo kinga bai dace mu zauna miki a gida ba”

Kwantar da hankalin ki sumayya, in gidane zaki samu don wannan gidan ma za’a samu waje, Amma sumayya kinsan rayuwar Abuja ba d’aya bane da Taraba koh? gidan nan da nake ciki dubu dari biyar ne a shekara , haka mijina ke biya.

“Karki damu indai kudin hayan ne zan biya laila ba damuwa, har school nake son ki taimaka naje na saka khadija”

Sumayya kamar nawa kika shigo dashi abuja ne wai?

“Million d’aya da dubu d’ari hudu”

Hhh lallai sumayya don kunzo da wa’innan kudi kike tunanin zama a Abuja, nifa bawai na yarda dake da abinda kikace bane, na sanki sarai da zurfin ciki, Amma fa ki sani wallahi wa’innan kud’aden da kikazo dasu wallahi bazasu miki kome ba, saidai in kin shigo da result naki nasa mijina ya nema miki aiki koda a office insu ne?

“Laila banzo da kome daya shafe karatuna ba, sannan ni ina da sana’a wanda nake saka tsammanin zan iyya neman na kaina da shi, kuma yarinyar nan kanwar mijina ce, marayu ne su biyu Iyayen su suka haifa,mijina bayanan shiyasa narike ta a hannu na,  kuma karatun ta nada muhimmanci aguna”

Toh wani sana’a kenan kike bayan Lalle sumayya? Ita khadijar bata da dangi ne?

“Harda make-up kuma khadija ta iyya kitso inso samune shago nake so na kama sai mu fara muga yanda Allah zaiyi damu”

Anya kuwa sumayya gaki da ciki in kika haihu d’awainiyar abinda kika haifa zai dawo kanki,  ga khadija ga kudin haya ga kayan da zaki sawa d’akin da zaku kama,  ga kudin makarantar ta anya abinnan zai hadu kuwa?

“Insha Allah laila Allah zai dafa mana, yanzun dai so nake kimin hanyar da zansamu dakin gidan nan da kikace ya saura, don so nake kafun mijin naki ya dawo mun bar muku kofa,  tunda kikace jiya ma kinje d’aukosa a tasha kika samu bai iso ba,  motar  su ta samu matsala” 

Ba kome tashi toh muje gidan, mai gidan yana tsallaken titi bara na kira mijina na fad’a masa.

Ok sumayya tace suka wuce gidan mai gidan hayan, bayan laila ta nemi izinin mijinta a waya.

Bayan sunje a take sumayya ta wuce bank dayake babu halin transfer, tunda ba sim a wayar ta, kudin hayan suka kawo wa mai gidan,bayan sun dawo kudi sumayya ta baiwa khadija da laila suka tafi kasuwa, ita kuma bude d’akin da suka kama tayi, sashen mai kyau two bedroom da falo ga daining area ga toilet a cikin koh wani daki, ga kitchen a ciki daki dai mai kyau dashi yasha tiles kamar d’akin laila, kome a ciki.

Bayan su khadija sun dawo katifa suka sayo babba, da zanin gado sai hot plate mai kai biyu, da sandan moping sai bokati biyu,  soson wanka dadai d’an abubuwan Amfani daidai talaka, bujuwan su biyu, khadijar ce ta ibi ruwa a panpon gidan ta wanke musu d’akunan tayi moping, yana bushewa suka shimfid’a katifar a falon, suka kai sauran kayan da suka saya  kitchen, suka shigar da akwatuna su cikin d’ayan d’akin, suka kwanta a katifar su ita da khadija a falo sosai gidan ya musu d’adi ganin kowa na d’akinsa babu tsegumi kamar gidajen hayan da suka sani.

***********

Ta bangaren Al’ameeen, suna zaune a gindin bishiyar ga gajiya ga yunwa, Gidado dake gefene ya fashe da kukan bakin ciki, Al’ameen da yaron fulanin nan sukayi wajen sa da sauri, duk da raunukar dake jikinsu, don gabaki d’aya kafafunsu kayoyi sun bula gashi hannun muhammad sai yanzu yake jin tsamin sa ga giransa dake ciwo, Gidado lafiya kuwa ?sukace har suna had’a baki.

Kuka gidado ya sake da karfi, sai kuma ya bude baki Amma ya kasa magana, da hannu kawai ya nuna musu gefen jikin bishiyar da yake.

A matukar kidime muhammad yace, innalilahi wa’inna’ilahi raji’un sarin ka yayine gid’ado………… 🍀

✨Ruqeenjalal✨

Back to top button