Uncategorized

Matar Makaho Part 1 Complete Hausa Novel

 MATAR MAKAHO

Chapter 1

By Rukayya Ibrahim.

Kuka nake baji ba gani bakin ciki ke dankare a cikin zuciya ta Wanda in har banyi kuka ba bazanji saukin suba Wai ni ce amarya amaryan ma na makaho mara ido na daga lulubena kasanciwar dakin akwai wutan nepa  glop ya haska Koh ido shiya bani Daman ganin daki dakin da Koh a mafarki van taba tunanin akwai ranan da Zan iyya rayuwa a irin Shiba Wai yau shi ake Kira da dakina na aure ni sumayya bansan lokacin da wani irin kuka ya sarkeni ba cikin takaici Mai tarin yawa ya Allah me naiwa Yan uwan mahaifina  da suka sakamin da wannan rayuwa Mai na tsare musu da suke mini irin wannan muguwar tsana da hassada ya Allah duk wannan magana cikin kuka nake yinsu  

Tsaye yake yafi minutes 30 Amma ya kasa karasawa cikin kofar wani irin fargaba ne dankare a cikin ransa Wai yau shine da mata sukutum Koh a mafarki Bai taba tunanin aure ba  kasan shiwarsa makaho maraya kuma Mara galihu sai abinda ya nemawa kansa Amma yau har Mata aka basa wance Bai taba tunanin samun taba amasayinsa na miskini  Anya zata karbesa a matsayin miji zata yarda ta rayu dashi cikin akwai Koh babu wannan sune abinda suka tsaya masa a Rai yayi ta maza ya daga kafarsa hade da Bismillah Yana tafiya da sandar sa Yana ma kansa jagora zuwa filin  kewayayeyyen kofar su Dan madaidaici ya juya ya tura kofar ya rufe harda lalubar sakata ya saka  a sannu a hankali yake takawa har yaji ya taba Dan tudu kadan  hakan ya nuna Masa ya iso dakalin kufar daki haurawa yayi sama Yana lalube tar yaji ya laluba ginin daki Yana bin ginin a hankali har yaji ya shafa window yanabi a hankali har yaji ya Kama labule mai masifan laushi da kamshi Wanda tunda yake a rayuwarsa Bai taba tunanin zai taba irinsaba kasan shewarsa  mutunne shi Dan babu ruwana ba ya maula Koh bara baya neman taimakon kowa in dai na abin duniya ne sai dai na lalurarsa Wanda ya zamto Masa dole 

Da sallama a bakinsa ya daga labulen tare da jingina sandar sa a kofar dakin ta waji ciki ciki na amsa sallamar itama Dan ta zama dole na daga kaina ina kallon wanda Koh ba’a fadaba nasan shi ake nufi da ango makaho cikin wani irin takaici nake kallonsa don matashine Wanda bazai Gaza shikara 28 zuwa 30  ba laifi makanta da wahalan rayuwa su kadai za’a kira cikas a tare dashi don kyekkyewa ne na karshe dogo fari tas wanda wahala ta kodar da fatarsa Amma duk da haka fatar daga Gani zatayi matsifar laushi   gemu mayalwaci sosai  ga idanu masu girma da haske amma mara amfani a ganina bakinsa madaidaici Mai shegen kyau ga hanci har baka Mai yalwan gera don daga gani yanada yalwan gashi sosai sai gashin kansa Mai yawa amma rashin samun wadasheshen gera sai ya Yi wani iri Amma daga Gani gashine na Fulani  asali duk da babu datti don fes Kan take  kiransa na zaratan mazane masu Kiran karfin sosai na kurawa kayan jikinsa ido wani kudadden yadine na shadda wando da riga Mai guntun hannu Wanda suka Sha ruwa sosai wai su ya saka kenan ranan aurensa daga Gani sune na gindin akwatin sa Koh Bai fada ba ni Kam na raya a Raina  kauda fuska nayi kamar bansan mutun ya shigo ba shi kuma cikin sanyin jiki da lalube yaji ya taka wani cafet Mai shigin laushi a cikin dakin duk da baya gani yasan tabbas Mai tsadane Koh me na dakin Nan don Bai mantaba dazun khadija take Masa gulma wai dakin Aunty’amarya Mai kyau da Kaya irin na gidan murtala Hon na unguwan su harma nata yafi nasu kyau tun daga lokacin jikinsa ya kara sanyi don ya tabbatar ba yar kananun mutane bane aka aura Masa a matsayinsa na makaho  da lalube ya iso tsakiyar dakin Wanda yaji abubuwa Kamar filo a xuzxube a kasar cafet in dakin  a hankali ya zauna tare da aje ledan dake hannun sa baka cikin zazzakar muryarsa Mai cike da Kamala ya gai Dani Koh juyuwa vanyiba don bana son ganin sama  bare  na sake Jin ya sake furta Ina wuni nayi wani dogon tsaki  Jin haka yasa shi Jin wani mummunan faduwar gaba Amma baice kome ba yayi shuru  munkai minti goma babu Mai shiwa kome sai Karan fanka Kiran OX babba wance Taki bawa dakin wani irin iska Mai sanyi  sosai  cikin rawar murya yace ga kaza nan kici sai muyi nafina mu gode wa Allah cikin zafin nama da takaici na hayyaya Koh Masa cikin fada Wanda duk Wanda ya sanni yasan ba halina bane Kuma Koh kyau Bata mini ba nace baza’a ci matseyacin kazar kaba kuma sallah kayi tayi har alfijir ya ketoh Bai shemin kome ba Amma kallo daya namar nasan maganar ta dake sa sosai  a hankali ya laluba yafita waji yayi iyya nemar buta Koh Randa baiji inda aka aje ba saboda duk kayan kofar an sauya Mata zama kasanciwar sabbi aka kakkawo hakan yasa ya koma dakin a hankali da sallama Ina dai zaune Ina  kalonsa yazo ya fara lalube a hankali ya daga labulen ya tura kofar ya rufe harda sakata cikin nutsuwa Naga ya fara lalube  ban ankaraba naji ya lalubu ni cikin wani irin shock daga ni harshi muka Masa baya shikam harda buge kafar sa da katakun gado cikin i’ina nace meye haka cikin Dan sanyi jiki yace kiye hakuri ina neman gadone Zan kwanta cikin gadara nace  wallahih bazan kwanta dakai gado daya ba gadai kujira a Chan jika kwanta a hankali ya fara lalube Ina dai zaune Ina kallonsa  haka ya ringa zagaya dakin daker ya gane kujiran a hankali ya zauna ya cire rigansa ya kwanta  a hankali cikin lumsheshen kujira na alfarma 3sita Nima kayan na cire tunda dai ba idone dashiba na ragi daga ni sai brz da siket nayi adu’a  na kwanta a hankali nake sauke ajiyar zuciya har bacci ya dauke ni  shikam ya kasa bacci sai tunane tunane yake yanason yin lafilfilu Amma ba Hali tunda baisa inda zai samu ruwa ba a kofar tasu Kuma baison zuwa rijiya a Darin nan gudun wani a cikin mutanen gidan su gansa su Masa abinda suka Saba rashin mutunci  a sannu a sannu wani bacci Mai Dadi ya daukesa don a tsawon rayuwarsa Bai taba bacci ana zafi da fanka ba sai yau lol asuba da gari amarya da ango.

Kiran farko akan kunnensa ya farka a hankali  tare da addu’an tashi daga bacci  kafarsa yazura ya sauke a kasan cafet da Bismillah ya mike saye ya fara laluben    rigarsa daya cire jiya da dare da zai kwanta cikin hukuncin Allah ya samu rigan ya saka a hankali ya nufi kofa cikin lalube ya gane kofar ya bude ya fita ya tuna baisan inda buta take ba don baiga tsohon tasaba sake dawowa yayi a  hankali yake lalube harya lalubo gado ba tare daya hauba yasa hannu yana laluben ta cikin sanyi Amma baijitaba a cikin ransa ya kitsima lallai wannan gadon babbane sosai  Hawa yayi a hankali Yana lalube har yaji hannunsa ya taba wani abu Mai masifan laushi sosai Kamar fatar jinjira  da sauri ya zari hannun cikin murya kasa kasa yake. Tattaba  filon da yaji kanta akai inda Allah ya Sosa ma Mai nauyin vaccine ita da Allah Bata San ya taba Mata jiki ba  cikin bacci take Jin ana bubuga Mata filo ido ta bude a hankali don baccin Bai ishitaba ta sauke idon ta a kansa Yana zaune kusa da ita cikin sauri ta Mike da masifa tace Kai lfy meya kahoka Kan gadona eye ,, cikin sanyi Wanda na Lura halittansane yace Daman buta nake so ki nuna mini na ibo Mana ruwa asuba tayi wani haushine ya kamani wannan miji ne Koh rainon sa zanyi Amma saboda albarkacin sallah yasa nace toh muje na dauki rigana nasa na fita a dakin nayi wajinda aka  kewayemin da fallange Dan madaidaici Wai kitchen na shiga kayan kitchen ne na alfarma kome yaji yar an rasa wajin sawa an koma da saura Kamar yanda aka maida kujiruna da wasu Abubuwan kayan dakina  masu yawan gaske na shiga na kunce butan a cikin kwalinsa na karfine cikin kayan da aka saimin da na roba na hada biyu na fitoh na samesa a saye yana jirana Mika Masa nayi cikin kaushin murya nace randuna na babu ruwa cikin lalube ya karbi butan hade da furta bara na ibo a rijiya kala bance Masa ba ya fita sai gasa ya dawo da ruwa a buta daya ya shigo ya ajimin ya koma ya dauko dayan ni kuma tuni na idar da alwala harna shiga daki na bude akwatina na dauki hijab da sallaya na shinfida na tada sallah 

Alwala yayi ya tafi masallaci  da sandar jagoransa  Ina idar da sallah nayi lazimi   har lokacin Bai dawo ba na daga idanu na na kalli agogon bango Wanda aka likawa bangon dakin karfi Shida saura  naja dogon tsaki Dan a lokacin aka dauke nepa ni kuma  bana iyya bacci ba AC Koh fanka Sam nasan Koh na kwanta bazan iyya bacci ba Ina zaune har karfi Shida lokacin gari ya waye dakin yayi haske  a hankali nake bin dakin da kallo dakine madaidaici sai gadona Wanda yaci Rabin dakin  da kujira dogo guda daya don sauran babu wajin zama Mai dasu akayi  plasma TV  ta gefin gadon aka makala don ba fili da waddrop ta daya gefen  sai kafet da su kushin da aka saka a tsakiyar dakin da karamin freezer ata bakin kofa  kayan sawana makil  a akwati set dake gefen Kan gado sai fankan kasa sune suka samu wajin zama a dakin  a hankali nakai hannu na dauki jakana na bude na dau waya ta Ina dannawa  tunda babu nepa bare na kunna TV an hadamin kayan kallo harda Star Time Ina  da sallama naji ya shigo dakin na amsa ya laluba kujira ya zauna cikin sanyi yace ina kwana kamar bazan amsa ba na amsa da lfy klau cikin sanyi yace me zakici na sai Miki  cikin mamaki da al’ajabi  Wai sayo abinci Ina amarya akawoni cikin gidansu Amma arasa Mai bani abinci sai ya siyo  duk da ban karewa gidan kallo ba nasan babbane tun jiya da dare  maganar sa ce ta dawo Tani daga duniyar tunani Dan wake Koh alele Koh kosai za’a karba miki cikin mamaki nake kallonsa sai Kuma naji ya bani tausayi tun jiya yake kokari yaga ya kyautata mini  yasa cikin sanyi nace Masa  

“Basai ka saya abinci ba, akwai kayan abinci, ruwa nake so, asaya da bread sai kayan meya” cike da kuzari ganin na masa magana, a taushashe sabanin jiya, ya Mike ya fita, Yana fita, ya laluba aljuhunsa Aiko Allah yasa,Yana da gudan dari biyu da dari, na cinikin mangoron sa na jiya, da safe da Yan change ya hada ya fita tsakar gidan, sai ji yayi an saka ihu da shewa, daga mata har matasan samarin, ana ga ango ga ango, wanda Koh tantama babu,duk wanda yaji yasan na raini wayo ne, da shikiyanci kasanciwar ya Saba da irin wannan tozarci na Yan gidansu, sai abin Bai  damunsa Sam, wuce warsa waji yayi, ya fita kofar gida, dayake bakin titi ne gidan nasu, yasa shi sayuwa a bakin kofar gidan, Bai jima ba dayake safiya ne, yaji Mai ruwa na bugawa kiransa yayi  duka ya saya,  ya hadasa da yaron makwantansu, ya nuna Masa kofar amarya, shi kuma ya shiga shagon haladu, sayan bread na dari Mai kyau ya hada da Lipton na goma, da sugan  hamsin, ya karasa table in gwanja yasai kayan meya ya hada ya kamo hanyan gida ,

Mai ruwa ya shigo da yaro “na tashi na fitar da randana, na roba Mai girma sosai irin Mai cin jarka Sha biyar innan, Mai ruwa na Gama juyewa, Yana shigowa ya biya kudin ruwan,  ya ajimin laidan cefenen “dauka nayi nawuce kitchen”, shi kuma ya fita, “kitchen na shiga kome an jiramin kuma ba laifi kitchen din ya dauki Rabin kayan da akai mini, gas na kunna na dauko dankalin turawa na fere na daura a tukunya, kwai na fasa na zuba kayan hadi na aji a gefe,  kettle na ruwan zafi, naso daurawa Amma ba nepa dole na daura bojuwa, ( tukunya) a dayan Kan gas in na zuba kayan kamshi da Lipton na rufe, naji” buruntun bude kofa lekawa nayi nagansa rike da Ghana must go na kaya madaidaici na kayansa ya shigo da lalube’ ya fada cikin dakin  yaje ya aje sai gasa ya fitoh yana lalube cikin Dan tausayin sa, wanda bansan Ina dashi ba, “nace maikake nema ne” ?   cikin sanyin halinsa yace bokati, “na mike na dauko masa” sabon boket, da kwandon soso, na kayana da soso sabo da sabulu, na wanka Mai sada  na akwatina,” hada a kwandon na Mika Masa” ya karba cikin lalube ya lalubi kwandon yace La!! ai Ina da soso  harda sabulu barshi kawai “cikin Jin haushi nace na sani ai na baka kayi dasu” Bai Musa ba ya karba yaje ya zuba ruwa a bokatin ya cika, da lalube ya shiga ban daki, ya ajiye ya dawo ya lalubi inda ya aji butar da yayi alwalan, asuba ya dauka ya cika ruwa ya wuce bayin, 

“Cikin kankanin lokaci na hada breakfast, Mai kyau na soyayyen dankali da kwai tie ga bread a gefe naji daki na dauko kazar dana Gama zagi jiya nazo na juye a kwando na makala gudun karya rube, da rana nayi meya dashi’ na fada dakin na kakkabe gado na jira filon Kan kujira, na share dakin na fesa turarukan daki, na fitoh na share baranda na hada da kasar kofar duk da ban taba share kasa ba,  sai dai tayis Koh seminti haka na lallaba na share,  Ina gamawa” Yana fituwa a wanka daure da zani, tsoho a kwankwaso hannunsa dauke da kayan sa daya cire, a boket Yana lalube ya dibe ruwa ya zuba a boket in, ya jika kayan ya mayar bayan gida ya aje, ya fito Ya shiga dakin, “na ibi ruwa Nima na shiga Wanka da soso da towel na  Ina fituwa na fada dakin, ban Damu ba, tunda ba kallo yakeye ba” “Ina shiga na gansa zaune a kasa ya chanja Kaya zuwa jallabiya fari duk da yasha ruwa jallabiyan, Amma a wanke tas, 

“na shiga na bude akwatina na dauki Kaya, rigane dogo na material Mai kyau  da tsantse, NASA na hada da hula fari na fita waji na shanya towel in a igiya da kayan da na cire samun kar suye tsami,  na shiga kitchen na dauko abincin na fada daki da  plet na zuzzuba karyawan na Mika Masa” “na ibi nawa nayi Bismillah Muka fara ci” babu Mai magana a tsakanin mu tunda yasa, abincin nan a bakinsa yake godiya wa Allah a zuciyan sa, daya mallaka Masa sumayya amasayin Mata, tunda zata iyya dafa Abu ta basa yaci Wanda rabon da adafa abasa tun kafun ummarsa tabar duniya shiyake sayawa kansa, abinci she yake nemawa kansa, 

 “muna tsaka dacin abinci naji an banko kofar shashin mu an shigo, ba sallama aka daga Mana labule dukkan mu dagowa mukayi don ganin wani ishanshen ne, haka sabanin shida Banga mamaki a fuskar Saba sai dai alamu sun nuna baiji Dadin hakan  ba, ya kurawa kofar ido Kamar Mai kallo yanda nayi sakake Ina kallon kofa cike da mamaki.

Budurwa ce  zata Kai kusan sa’ata cikin gadara da taunan cingum. tace amarsu ta ango karyawa ake ne? gashi nazo kallon dakin Amarya 

 ***kala bance Mata ba

 shema duk da baiji Dadin hakan ba Amma shuru yayi ba abinda yace ,haushi sosai naji Amma naja bakina nayi shuru don banda lokacin wannan Mai zubin karuwai,  abinci muka cigaba da ciii ba Wanda ya kulata cikin mu biyun,

cikin bacin Rai  tayi tsaki ta juya tafita.  Koh ido ba mudu bane yasan kema ni ba sa’ar yinta bane kallo daya tamin ta gane ni ba kallan raini wayo bane Kamar yanda suka Saba Raina Masa, 

**mamaki ne ya kamani, lallai sai nayi da gaske Zan iyya zama da Yan gidan nan. don dagani Basu da mutunci wallahi😒

Muna Gama karyawa ya mike  ya dauki kwanukan da mukaci abinci harda nawa ha Hada ya fita dasu a kitchen ya Ajjye,

Dawowa cikin dakin Yayi cikin sanyin halinsa ya bude baki a Hankali ya furta Zan fita wajin sana’a Koh akwai abinda Zaki bukata,?

 Kamar bazan tanka ba Amma na daure nace “babu”Koh zaka dawo kaci abincin  Rana”?  cikin natsuwa  yace min ah..ah  Zan saya naci sai yamma Zan dawo,

  “har Ina ne  wajen sana’ar taka” ? Cikin D’anjin Dadi jin Ina kulasa yace bakin titin kofar gida ta gefen shagonan,  su haladu 

** Ni Kuma Ina nasan wani Haladu bare shagonsa😏a Raina nake fada

Amma a zahiri cewa nayi “toh Inna Gama ka tura yaro yazo ya karba maka abincin”

 da zumudi yace toh ……toh Zan turo bayan azahar. Ya sa Kai ya fita

 ***Daki na koma na bubbude akwatunan Kayana na bubbude kayan  Ina jirawa a whtdp  wasu a dressed mirror kayane na alfarma   atamfufe  dinkaku  da Wanda ba dinkaku ba  takalma da jakunKuna gyeleluka abaya material duka na shirya Kayana a nitse make-up kit na aje sa a drowarn mirror    mayuka da turaruka na jirasu saman mirror. sauran kayan da suka rage na mai dasu cikin akwaiti ba wajen jirawa duk  ya cika ba fili na rufe na Mai dasu saman whdrp “,

 yarane  suka fara shigowa ba sallama ba gaisuwa suka shigo mini daki  harda Yan matan gidan suka cika dakin Wai sunzo kallon daki ga makwanta nata shigowa da sunan ganin daki Koh gulma ne oho,  ana haka aka kawo NEPA Daya Daga cikin Yan matan ta Mike ta kunna  TV 

haka aka  sake cika Wai ana kallo har baranda nidai abin daya isheni kawai na dauki wayata na fita waje,

 ” kitchen na wuce kazar jiya nake son hada miya dashi Amma kayan miyar jiya tayi kadan dole na shiga daki jakana na hannu mai kyau na dauka na fito waje budewa nayi na dau gudan dubu daya na aiki yaro a cikin Yan kallo kayan Miya Mai Dan yawa na Kara Masa da dubu biyu ya sayo harda kaza, don so nake na Kara na jiya bazai isaba ga yara a kofar.

Yaron na dawo mini da kayan Miya na fara aiki ba wance ta taimake ni Koh da jijjigen kayan Miya ne

 shinkafa da miya na dafa Ina Gamawa  na zuba a sabon kula Mai kyau na saka a basket da shukali da plt, na Koma dakin na bude freezer na dauki ruwan gora, na hada Masa a basket in na Ajiye, d’aid’ai yaron da Zai  aika ya shigo na basa.

 sauran abincin na zuba a babban faranti na hadawa yaran daban na sawa manyan daban daya ke nayi abincin da yawa sosai, Mika musu nayi ba kunya suka amsa  gabaki daya Koh kwanukan Basu daga ba suka barsa a Inda suka ci sun batamin daki  da datti sosai,

 na ibi nawa na zauna a baranda kan darduma  nayi Bismillah na fara ci ban tashi agunba saiga wani yaro ya shigo da sallama  amsa Masa nayi, “waalaikumu salam”ya gaidani,  “amsa wa nayi don naji dadin gaidani da yayi kaf yaran gidan da suka shigo ba Wanda ya gaidani Koh sallama babu,

Wai inji inji MAKAHO Mai mangoro aban abinci,

Wani Takaici ne ya kamani Wai sunan sama da MAKAHO ake kira “shap wallahih bazaiyu ba watoh nima haka za’a na kwatantani da MATAR MAKAHO Ina bazaiyu ba” duk Araina nake zancen nan. 

 Mikewa nayi na dauko masa basket in, basa nayi ya wuce 

azahar yayi Amma kaf yaran gidan ba Wanda yayi Haraman Sallah Nima bance musu kome ba, na mike na dauro Alwala na koma dakin Hijab na dauka na fitoh waje nayi sallah na kwanta a sallayan  Ina Danna waya,

  

Mutane Basu bar mini kofa ba har na Gama Tuwon dare na kwashe sukaci tukun suka fara watsewa daya bayan daya.  Har suka watse suna fita na share dakina na goge, dakin Yayi kaca kaca sosai chanja zanin gado nayi yara sun kakama mini na jikin gadon da hannu yayi daud’a na fesa Turarukan daki na wanke dakalin kafun  naji kofar yamin dama daman  shekan iska Mai Dadi, wanka na shiga a gurguje nayi alwala na fada dakin na shirya  nazo daukan turare Naga an min satan Mai Harda turare,

 Raina ya kara baci don na tsani mutun ya dauki abuna ban basa ba, na kudurta Araina bazan sake Basu wannan fuskan ba tunda basuda mutunci gobe ba shegen da zai shigarmin kofa😂( tab kofarki Koh na makaho) Kaya nasa na jona wayata a cherge da laptop  duka,

 **na koma gefen gado na zauna

tunani na shiga yi lallai rayuwa ba tabbas yau Koh mutun daya daga cikin dangina Koh kawaye, babu Wanda yazo.  watoh tunda talaka na aura kenan,? 

 alhalin duk wance tayi aure zuwa ake washe gari kallon gida da masu sallaman Amarya, a ranan. Amma ni ba Wanda yazo kallon daki ma bare sallama uhmm, 

Karfe biyar da rabi  MAKAHO ya dawo gida da kwandon abinci a hannu sai sandar jagoransa da lalube yakai kulan kitchen ya aje,  wanka yayi ya fada dakin Yana shiga na fita na basa waje ya shirya,

 Tana fita ya lalube Ghana must go insa ya dauki Kaya yasa ya fitoh waji lalube yayi ya dauki buta ya Kama alwala. ya  wuce masallaci,don har an Tada  sallah,

 **lokacin Nima sallah na Tayar ,Bai dawo ba sai da ya hada da isha’i Tukun ya dawo,

*** abinci na zuba Masa 

***na Koma Kan gado na zauna  TV na kunna na kamo Tashar Arewa 24  Ana cikin  Shirin kaddaran rayuwa.  bayan ya Gama cin abincin, kwanukan ya dauka yakai kitchen  hade da wanke hannu ya Sha ruwan Randa, ya shigo dakin, 

cikin lalube ya lalubo kujira ya zauna a hankali cikin magana Mai sanyi yace nagode da abinci yayi Dadi sosai Allah ya biya.” Amin” nace hankalina nakan TV,

 jawo laidar da ya shigo da ita baka yayi ya fitar da sabulu da omo.   sai wata laidar  mangoron yako, ya Miko mini ta inda yake tsammanin  saitin nake,

Cikin sanyin jiki da zullumin zata Amsa kuwa?

Yace ga mangoro ba yawa

***ban gwatselesa  ba na karba na mike naje na bude firij na aje.

 fita waje yayi, ya hada kayansa daya jika a ban daki da safe da Wanda ya cire dazun ya wanke ya shanya ya sake dawowa dakin yayi cikin magana d’ari..d’ari  yace Koh Zaki kawo kayanki Mai datti na wanke miki, 

***cikin mamaki nake kallonsa Wai ya wanke mini Kaya, lallai da wani idon Zan basa Kayana na fada a Raina, Amma a zahiri nace “ah ah na gode Zan bada wanki inya taru” baice kome ba ya lalube kujira ya zauna kawai yayi shuru ya kurawa TV da yake aiki ido kamar Mai kallo,

 ***abin har yaso bani dariya Amma na maze. muna zaune har goma, bacci na faraji,

mikewa nayi na chanja kaya  zuwa na bacci,  kashe TV da glop nayi na Kara gudun fanka zuwa 3 Addu’a bacci nayi na shafa na kwanta,

 a hankali  ya Tashi yaje ya  rufe kofar duk Ina jinsa dawowa  yayi  kwanta, kwanta a kujira  addu’an bacci yayi shima ya shafa. 

**Nima  gyara  kwanciya nayi,

Tun daga jiya zuwa yau, a Takure nake Sam ban Saba kwana da  namiji a daki ba, Amma ya zanye, dole na kwanta tunda daki D’aya ne bare na koresa falo.

Misalin karfe biyu na dare ya farka.

Dan a irin lokacin da yake tashi sallolin dare,

 mikewa yayi  ya riga ya gane ma’ajiyin Randa da buta fita yayi a dakin alwala ya daura ya dawo dakin,ya tada sallah sai uku ya koma ya kwanta, Kiran farko na asuba ya farkar dashi, Addu’a tashi daga bacci yaye.

A hankali ya sauka a kujira cikin sanyi ya lalube gadon ya tsaya a bakin  don bazai iyya Hawa ba kar a maimaita irin na jiya a hankali yake kiranta

 **sumayya!! sumayya!! *

**A hankali na bude idanuna cikin bacci nace “naji habba” baice mini kome ba ya daga  kafarsa a hankali da lalube ya bude dakin ya fita  **Niko waya na laluba a gefen filo don dakin ba haske na kunna hasken ya haska dakin sauka nayi Nima nayi waje don d’auro Alwala, **fitana yayi daidai da kammala tasa alwalan mikewa yayi Yana laluben sandanrsa,Harna kammala alwala Bai gane sandar ba. 

*Ina kammala alwala  na shiga daki daukar wayata nayi na fitoh na haska kofar  aiko Naga sandar Ashe faduwa yayi a kasa, dauka nayi na zungure sa da sandar a hannu *

 da sauri ya mika hannunsa ya amsa cikin sanyi sanyin sa yace nagode,

* batare da nayi magana ba don takaice waini sumy nice yau da miji MAKAHO shap wannan ai abin kunya ne ma Wanda ya sanni ya gansa a matsayin mijina, Tabbas nayi Wasa da Damata a rayuwa, shiyasa Allah ya jarabce ni a lokacin da ban taba tsammani Koh tunanin hakan ba,

 **Da sauri nayi istigifari na kauda tunanin a Raina 

* Koh amsa Masa banyi ba nayi shege daki na tada sallah, Ina idarwa Qur’an na dauka cikin jakansa Mai kyau na bude,

*nayi azkar in safiya, dana sabayi kullun na mike nabi lfyn gado bacci ya dauke ni,

 sai shidda da rabi ya shigo dakin da sallama hannunsa rike da bakar laida na kayan shaye da kayan miya Jin ba’a amsa ba  ya lalube kujira  ya zauna,  numfashi Daya ji kasa kasa hakan ya tabbatar Masa ta koma bacci a hankali ya mike,waje ya fita da lalube ya Isa kitchen aje laidan yayi ,

 shanyar kayansa ya dauko a igiya  ya nade ya shigo dakin ya lalube Ghana must go in sa  Daya aje a lungun kujira da firij yasaka kayan,ya dawo Kan kujiran ya kwanta a hankali wani irin bacci Mai Dadi ya sauke sa,

**Ban tashi ba, sai Takwas na safe shima ihu da ashariya na dandazon mutanen gidan Wanda Koh tantama banayi tambe ake, shiya farkar Dani,mikewa nayi sanye da kayan baccina Wanda na saka jiya da dare riga da wando Mai taushi sosai sai hulan bacci d’uka farare ne tas.

*  da sauri na dirko daga Kan  gado nafitoh dakin naje na rufe kofar shashen mu don nasha Alwashe yau bamai shigarmin kofa kallo Koh ganin daki bare naji yau da tambe aka tashi* 😂 (Anya ba tsoro ba kuwa?)

*Kitchen na wuce, ganin laidan kayan Miya a kasa,

* dauka nayi na bude    kayan miyane su tarugu albasa da tattasai sai dayan kayan shaye ne yau harda Madara, na laida da bouviter, bread, sugar, da Lipton,

 ruwa na zuba a kettle nasa Lipton, don yau muntashi da NEPA  na jona a socket  bude caton  indomie, na kayan garana laida biyu na dauka manya shap shap na daura na dau kwai na soya cikin 40 minutes na Gama hada breakfast na Kama shara,

✨ (tabbas aiki a wajen mace ribace babba duk kudin gidan ku duk mulki Koh gata ilimi da kyau in har mace Bata iyya girki ba gtoh Bata cika macen da za’a kira Tauraruwa ba Yan Mata a Kara bada himma karki xamantu baki da aiki sai adafa a baki kici ki kwanta kina Danna waya.koh makaranta kike zuwa at lest ki ware wasu lokutan  a Rana kina Taya ma’aifiyarki, 

aikin da kika tsana kina ga ana matsamiki ana bautar dake wallahih ribarta na zuwa don bakisan inda Allah zai kaiki ba)✨ *shawarace* 

**Tun sa’ilin da aka fara Yar Hali watoh dambe, a tsakar gidansu ya farka Amma Bai Mike ba har **fitanta da rufe kofar duk akan kunnensa duk yanaji Yana kwance ,

a hankali ya mike ya fitoh cikin sanyin halinsa da nutsuwa ya bude baki yake gai Dani,

**shuru na Masa naki amsawa * 

baiyi fushi ba ya kara tambaya ta, Koh Zan Kama Miki wani aiki ? Abin nasa harda rainin wayyo kenan, Wai ya kamamin aiki? da wani idon Amma saina maze nace “wanke-wanke nakeso kamin” ba musu ya lalube sandarsa da takalminsa shinyayye ya saka 

Da lalube harya lalube boket, ya dauka ruwa ya Iba a Randa ya aje a gefe da laluba har yakai cikin kitchen nidai Ina binsa da ido kawai, ganin garajen sa,

cikin tsawa nace “kaiiii aje kulanan abincine a ciki”

” tsaya na nuna maka kwanukan da  zaka wanke”

” Wai baka ganewa ne?

 Hala  banda rashin gani ma? harda rashin basira? zaka dauki kula kaje da nauye basiranka bazai baka abincine a ciki ba zaka zungumu??

Kala baice mini ba ya ajiye kawai ya jingina a gefen kitchen ya tsaya,

Zuwa nayi na dauki kwanukan nakai masa gefe na hada ruwan kunfa na aje kwando da kujira na tsaya agefe cikin masifa masifa nace gashinan Bismillah sai kazo ka wanke jiki a sanyaye yazo da lalube harya zauna Niko Ina saye a gefe ina ganin ikon Allah wanke kwanuka yake Kamar Mai ido tas suke fita Yana kifewa Kai Koh Mai ido albarka, mamakine y kamani Amma ban nuna Masa ba,

**Shara na kammala na gera daki na na jona kask’wan lantarki na zuba Turarukan wuta  a dakin fita nayi Naga har yanzun Yana Kan wanke wanke

Kwanukan akwai Dan yawa na abincin jiya da yara sukaci ban samu na wanke ba Harda na dare,

 *Wanka na shiga Ina fitowa na tarar ya kammala Yana zaune a kujiran tsugunne,

” Koh Mai ban shafa ba na zura kaya atamfa super Mai kyau siket da riga Mai k’wala da hannun roba* dinkin zamani

 *abinci na zuba ina ci  daidai lokacin shima wankan ya shiga  yana fitowa  wanka ya shigo dakin, Alhamdulillah Koh ba kome na Lura Yana da tsafta duk da bana rayawa a Raina Koh da Wasa zanyi rayuwar aure dashi Mai tsayi dole ya sake ni yaje ya nemi miskiniya irinsa Amma kafun lokacin bazan cutu da wari ba tunda Yana wanka ( lol😅uhmm muje zuwa zakiyi bayani )

*Fita nayi na basa waje*

Kaya ya saka wani jimemmen t-shirt da wando jeas duk da tsofene Amma sunyi Masa kyau sosai ya laluben kujira yayi ya zauna,

Ina waje ban kulasa ba naci gaba da cin abinci na kammala zamana nayi A wajen naki basa abinci shi kuma Bai tambaye ni ba   Danna waya nayitaye sai kusan goma na safe na iba Masa a plt da shaye a Kofi na shiga dakin na aje Masa na koma Kan gado na kwanta,

 ya jawo plt in yayi Bismillah ya fara ci

 

Yana tsaka dacin abinci  muka ji bugun  kofar shashen  mu mikewa yayi zaiji ya bude na dirko daka kan gado cikin fada fada nace “bazafa ka bude kofar nan ba don yau bamai shiga kofar nan ehen kaji na gaya maka don Naga alama Yan gidanku basuje islamiyya ba”

Baice mini kome ba ya koma ya zauna 

Jin Mai bugun yaki barin kunne na ya huta,

hijab na dauka na zura na fita ,don gani wani isheshshine,

Bude kofar naye idona y sauka akan wata yarinya kyakkyawa sosai  farace Mai Kama da MAKAHO sak banbancin ita mace Mai karancin shikaru 18 zuwa 19 she Kuma namiji ne sanye take cikin riga na kodadd’in shadda sai hijab wuyan duk ya sabule gashinta har ya leko ta gaban goshi,

*Tunda aka kawoni wanna kaddararerren gida ban ganta cikin yaran gidan da suka zo kofana ba,

Aunty Ina kwana tace 

hanya na Bata cikin dakewa nace “lafiya shigo”

Shigowa tayi daidai lokacin shi kuma ya fitoh cikin dakin murmushe dauke a fuskarsa itama murmushin take da sauri tazo ta amshi kwanukan hannunsa hade da gaishe sa ya amsa,Yana tambayar ta ya su Goggo Aminar,

Ta basa amsa 

Tace in nazo nace tana gaida Amarya,ta fada tana kallona 

Amsa Mata nayi ba yabo ba fallasa “Ina amsawa”

Fita zaiyi  hade da tambaya ta Koh akwai abinda za’a saya Kai tsaye nace “babu “sa Kai yaye ya fita hade da cewa Khadija in Zaki tafi ki biya ta guna, da toh ta amsa Masa

Nidai daki na wuce naje na kwanta  sai da Naji fitarsa tukum na kwala Mata Kira ” Khadija shigo daki Mana kina tsaye a waje” don haka kawai naji yarinyan ta kwantamin sosai a Rai duk da bansan Alakarsu ba amma nasan akwai alakar jini a tsakanin su,

Da sallama ta shigo dakin na amsa Mata tana kukarin zama a kasa nayi saurin cewa tahau kujira Amma Taki da kerta zauna, firij na bude na dauko mangoron jiya da yayanta ya kawo na hada Mata da drinks harda ruwa na aje mata hira take mini Kamar na saba da ganin akwai ta da surutu sosai tun Ina amsa Mata har bacci ya dauke ni,

Ban farka ba sai 1:30 na Rana shima kiraye kirayen sallane ya tashe ni sai a lokacin na tuna Ashe fa Ina da bakuwa,

A hankali na sauke idona akan kujiran da na barta akai da mamaki sai Naga wayam ba kome,

Sauka nayi a gadon na fita a dakin cike da mamaki nake bin kofar da kallo har idona ya sauka akanta cikin sabon mamaki ganin ta a cikin………………..

Back to top button