Uncategorized

Macijine Shi Page 9-10 Hausa Novel

Na mammy kabeer

(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚

Page 9/10

__________________Nan da nan fusatattun rugar suka nufi gidan malam bukar ,dan aiwatar da ƙudirin lamiɗo.

Allah Sarki fattu kuwa a wanann lokacin tana É—akinta cikin jimami da tunanin abinda ta  gani yau É—in nan,haka nan ta tsinci kanta da son sanin menene wannan abubuwan dake motsi aÆ™asan wuyan maciji? wanda tun daÉ—ewa bata taÉ“a ganinsu ba sai yau,waya sani ma ko wani akayiwa asiri ajikin macijin ?tabbas zatayi iya Æ™oÆ™arin ta dan ganin ta raba macijin nan da wannan abubuwan ,ta yadda koda wani aka yiwa asiri  ta hanyar macijin, to asirin zai karye .sannan tana fargabar gwogwgo ta gano cewar tana gidan kuma bata É—ebo ruwan ba.kuma ahalin da ake ciki yanzu bazata iya komawa rafin nan ba ,.dan ta tsorata dasu jauro .

Hayaniyar mutane ce ta cika gidan  nasu fattu ,wanda haka yasa gwogwgo hansai fitowa dole badan ta soba, Dan har lokacin nan ita da yaranta ba wanda yayi sallar asuba.

“Kai su waye haka suka zo suka cika mana gida da  ihu kamar ana yaÆ™i?”cewar gwogwgo hansai tana gyara daurin Æ™irjinta dake Æ™oÆ™arin kuncewa bayan ta fito daga É—akin.

“Aa meye hakan arÉ—o ?lafiya na Ganku da yawanku kun shigo?ta tambaya lokacin da idanunta ya sauka akan mutanen da suka cika gidan,kusan duk mazan garin ne.

Cikin masifa wanda aka kira da arÉ—o yace “wllh yau saimun É—auki mataki akan bukar da fattu ,haka kawai yarinya ta fara kashe mutane ,kuma ta rasa ta kan wa zata fara sai É—an gidan lamiÉ—o ?wllh yau sai mun kashe Shegiyar yarinyar nan”ya faÉ—a yana wani zazzaro idanu kamar zararre.

Eh wllh afito mana da ita kawai mukaita gurin lamiɗo ya bamu izini mu kashe mayya.gaba ɗayan mutanen gurin suka faɗi haka cikin nuna fusata da ƙosawa abasu fattun .

Wani irin farin ciki da jin daÉ—ine ya kama gwogwgo hansai ,shikenan zata rabu da alaÆ™aÆ™ai cikin sauÆ™i Allah yasa akasheta kowa ya huta ,dama su haÉ—a da bukar É—in da yake É—aurewa fattu gindi ,koba komai shanunsa sun zama nata.gwogwgo hansai ta faÉ—a cikin ranta.kafin ta kalli arÉ—o da sauran mutanen tace “aikuwa idan aka kasheta an kyauta ,dan nima nan wllh so take ta cinyeni nida yarana, jiya da kyar mukasha data maÆ™uremin wuya wai saita cinyeni, ku É—an jira kaÉ—an yanzu zaku ganta shegiya gantalalliya,banma san inda ta tafiba, dama haka takeyi kullum inta fice yawon iskanci bata dawowa da wuri,tana can gurin maza”gwogwgo hansai ta Æ™arasa maganarta tana mai buga hannu acinya.

“Aikuwa yanzu zamuje mu nemota ko ina ta shiga,wasu sutafi bakin rafin wasu sushiga jeji, mukuma zamu jira ana “cewar arÉ—o kenan yana kafe sandarsa akasa,sannan ya gyara tsayuwarsa.

Duk wannan abunda ke faruwa akan kunnen fattu, tana jin komai ,saidai tashin hankali,firgici tsoro da kuma ruÉ—ewa sun hanata koda yin kwakwkwaran motsine .

Numfashinta ma da ƙyar yake fita tsabar ruɗewa.

Ta shiga uku !shikenan yanzu kasheta za’ayi?laifin me tayi da za’a kasheta?me baffanta yayi ake nemansa shima? Dama jauron mutuwa yayi ? innalillahi !!!yanzu ya zatayi.

Wani kukane ya kubce mata cikin sauri ta toshe bakinta tana kuka sosai kamar ranta zai fita,ji take dama tana da ikon É“acewa, tabbas da ba abinda zai hanata É“acewa ta bar duniyar ma gaba É—aya.

Ahankali ta miÆ™e cikin sanÉ—a ta leÆ™o da kanta ,ba Æ™aramin tsoro tajiba lokacin da taga mutanen da suka zo tafiya da ita.shikena kawai ta mutu,yanzu shikenan bazata cika burinta na ganin innarta ba?wayyo “Allah ka kawomin É—auki “ta faÉ—a cikin raunananiyar  muryarta mai cike da tsantsar  tsoro.

Ahankali ta Æ™ara leÆ™o da kanta waje ,cikin rashin Sa’a kuwa sukayi ido huÉ—u da dan gidan gwogwgo hansai umaru.wanda hayaniyar mutane tasa suma suka farka.

“Laaaah aradu gwogwgo ga fattun can cikin É—akinta tana leÆ™owa”ya faÉ—a yana nuna É—akin da Fattu ke ciki

.cikin hanzari fattu ta koma cikin É—akin tana mai runtse idonta ,tare da dafe Æ™irjinta.”shikenan sun ganni wayyo Allah na baffa,wayyo MACIJINA kana ina  kazo ka taimakeni zasu kasheni wayyo ni fattu”fattu ta faÉ—a tana mai leÆ™a hanyar nan da macijin Kebi idan zai bar É—akin nata inya zo kamar Zariya  haka take bankada hanyar macijin da hannunta.

“Munafuka ,mayya dama kina ji ana neman ki shine kika É“uya nan?to fito yau dubunki ta cika ,mutuwa zakiyi wllh saikin bar duniyar nan yau nima na huta da ganinki ,maza arÉ—o zoka tafi ta ita gata nan”gwogwgo hansai ke faÉ—in wannan maganar tana daga bakin Æ™ofar dakin Fattu,dan tun lokacin nan da tasha matsa agurin  maciji bata Æ™ara shiga É—akin Fattun ba.

Aikuwa kafin ta rufe baki su arÉ—o sukayo kan Fattu suna janta.

“Wayyo Allah gwogwgo karki bari su tafi dani zasu kasheni ,wllh ban aikata komai ba wayyo Allah na gwogwgo ki taimaka min”abinda Fattu ke faÉ—i kenan tana miÆ™awa gwogwgo hannu cikin kuka mai tsanani.

“Ai wllh dana taimakeki gara hannuna ya karye Shegiyar yarinya ,kutafi da ita  can ku kashe banza” gwogwgo ta faÉ—a tana  kaÉ—a hannu irin yadda ake korar kaji ,cikin farin ciki take maganar.

Ihu Fattu keyi tana kuka,amma haka suke janta  kamar akuya aÆ™asa, suna cikin tafiya ne ,saiga baffa aguje yazo gabansuu ya tsaya riÆ™e da sanda yana ta haki,dan yana can bayan gari ya sami labarin abinda ke faruwa acikin garin da gidansa,shine ya rugo yazo .

Aikuwa Fattu na ganin baffa ta Æ™ara fasa ihu tana cewa” wayyo baffana ka taimakeni zasu kasheni” ta faÉ—a tana miÆ™a masa hannu,abin tausayi dukta susuce tayi buju buju da jiÆ™aÆ™kiyar Æ™asa.kallonta baffa yayi 

Cikin bacin rai mai tsanani ya ce.

“Sakarmin yarinya arÉ—o,  kona rotsa maka sandar nan akanka” baffa ya faÉ—a cikin hargowa da Æ™araji,

Kasancewar baffa kowa  ya sanshi arugar mutumin kirki ne ,sam ba ruwansa da shiga harkar wani,sanan kuma shine ke ja musu jam’i ,hakan yasa suke É—an ganin girma da mutuncinsa, dan haka cikin Turo baki da hura hanci  arÉ—o yasaki hannun Fattu wanda ke mata azabar ciwo da raÉ—aÉ—i,yana mai cewa”ato lamiÉ—o ne dai yace mu taho daku,dan haka ya zama dole ayiwa lamiÉ—o biyayya”ya faÉ—a yana hararar gefensa, dan yaji haushin sakin wannan hannun na Fattu mai shegen laushi da daÉ—in taÉ“awa da baffa yasa yayi.lol

Fattu kuwa yana sakar mata hannu ,da rarrafe ta Æ™ara so gurin baffa ta rirriÆ™e shi tana kuka da faÉ—in”wllh baffa ba abinda na aikata,ban kashe jauro ba ” ta faÉ—a cikin matsanancin kuka da tsoro, jikin ta sai rawa yake.

RiÆ™ota baffa yayi cikin tausayawa yace “na sani Fattuna,baki kashe jauro ba ,kuma ba wanda zai kasheki, Allah na tare dake kinji”?ya faÉ—a cikin sigar rarashi,sannan ya kalli arÉ—o yace”kai arÉ—o ka kiyayeni ,karka Æ™ara Æ™oÆ™arin  sake aikata irin wannan dabbacin akan Æ´ata, saboda baka da hankali shine zaka rinÆ™a janta aÆ™asa. Kamar wata dabba ?jahilan banza jahilin hofi,muje gurin mai garin zanji idan shiyasaka wannan É—anyen aikin”baffa ya faÉ—a cikin mugun bacin rai yana mai riÆ™e Fattu suka nufi faÉ—a.

LamiÉ—o na hangosu ya fara lasar baki ya kure fattu da idanu kamar maye , yana kissima abubuwa da dama cikin ransa….

Manage please yau ina busy,Dan banyi niyar typing bama yau wllh.

Masu karatu me lamiÉ—o ke nufine shima?

Hmmmmmm kubiyoni mu hade bayan sallah     danjin yadda zata kaya.

Kafin nan ina mana fatan yin salla lafiya,sannan aci Nama ahankali kar azo ana …….

Taku anty mammy 

Mrs babi,💘💘💘

Back to top button