Uncategorized

Macijine Shi Page 33-34 Hausa Novel

Na mammy kabeer

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 33/34

________________Fattu kuwa data rasa inda zata maƙala wannan abun ,sai kawai ta sanya kayanta haka ta yi waje gurin Adeeb, kafin ta fita daga ƙofar saida ta buɗe ta rufe kusan sau biyar,idan buɗe saitayi dariya ta ƙara rifewa, sannan ta buɗe,murna take sosai itama yanzu ta iya buɗe kofar yan wata duniyat.

Tana fitowa kuwa Adeeb ya bita da kallo, so yake yaga ko tasaka wannan abun,saidai kamar yadda ya tsammata ,bata saka É—in ba kuwa,dan haka  kallonta yayi tare da dalla mata harara yace ” kingama shiryawa kenan?” Kai fattu ta daga masa tana gyara lullubin da tayiwa matakin kamar wata amarya,ta rufe kusan rabin fuskarta ,sannan ta kama wuyan ta rike Æ™am da hannunta.

Shiru yayi yana É—an wani tunani,shi baisan ta yaya zai faÉ—a mata cewar tasaka bra É—in ba,dan haka sai yace” ina wannan abun da kika tambayeni na menene?”ya faÉ—a yana kallonta.

Itama kallonsa tayi kafin tace ” na barshi agurin ne ,dan bansan a ina ake sakawa ba” ta faÉ—a tana Æ™ara riÆ™e wuyanta, dan kar mayafin ya faÉ—i.

Kallonta yayi  har  zaiyo magana sai kuma ya fasa ,wayoyin  da tareeÆ™ ya taho masa da su ya É—auki daya daga ciki , ya daga tare da kiran tareeÆ™ .

Yana dagawa yace “ka tahomin da make up artist yanzu ta shirya yarinyar nan” 

“Ok sir ” tareeÆ™ ya faÉ—a yana mai kiran wata number.

“Koma daki” Adeeb ya faÉ—a yana mai mikewa shima ya bar gurin.juyawa tayi ta koma tana mai tunanin kodai tayi masa wani abunne ? Taji yace ta koma É—auki?zama tayi bakin gado tana mai cire mayafin nan ,dama duk ya isheta.gashin kanta ta shafa,tun wannan daurin dake kanta ,shine har yanzu,kuma kan nata Æ™aiÆ™ayi  yake mata amma Indai ta  zata Æ™aramin wanka saita nemi omo ta wanke kan dashi .

Karanta Littafin : Macijine Shi Complete Novel

Ba komawa saiga tarin ya shigo gidan,waya ya kira Adeeb yake sanar dashi sun karaso.

Cewa Adeeb yayi ya nuna mata É—akin farko  shikuma yashigo É—akin hutu.

Kasancewar ba inda tareeÆ™ bai sani ba acikin gidan,dan haka ya nunawa matar wacce take balarabiya ce dakin yace tayiwa yarinyar ciki duk abinda ya dace .

Shikuma ya shiga dakin da Adeeb ke ciki.

Da sallama ya shiga dakin,Adeeb na kwance akan gado, ba barci yake ba ,amma idanunsa alumshe suke .zama tareeÆ™ yayi yana mai cewa” yallaÉ“ai fatan dai kana cikin Æ™oshin lafiya” 

Ahankali Adeeb ya yunÆ™ura ya tashi zaune,kallon tareeÆ™ yayi kafin ya sauke ajiyar zuciya yace ” tareeÆ™ ina tunanin  abinda nayi ne ,kada yarinyar nan taga kamar na cutar da itane”Adeeb ya faÉ—a yana kallon tareeÆ™ da yanayin damuwa akan fuskarsa.

“Ko kaÉ—an yallaÉ“ai,idan har tayi tunani zata gane baka cutar da itaba, kuma Allah yaga niyyarka, kayi hakan ne dan kare martabarta da kiyaye hakkin Allah, amma yallaÉ“ai mai zai hana kasanar da ita abinda ke faruwa ,dan gudun samun matsala nan gaba”tareeÆ™ ya faÉ—a yana mai kallon ogan nashi .

Shiru Adeeb yayi na kusan minti biyu kafin yace” no tareeÆ™ ,she’s too young ace munyi wannan maganar da ita,is better mubar maganar atsaninmu har zuwa lokacin da Allah zai bayyana iyayenta,inyaso saina basu ita ahannunsa,sannan kaga tayi free .

“Shikenan yallaÉ“ai amma yanzu kana ganin ,zaka kaita can gidane,ko kuma zata zauna anan?”tareeÆ™ ya faÉ—a yana kallon Adeeb da jiran jin me zaice.

Kusan minti biyu Adeeb ya É—auka kafin yace” ko zamanta anan tare dani akwai matsala tareeÆ™ bana so wataran zuciya ta Kani ga aikata wani abun da zai zamo na cutar da ita,zan kaita can gida gurin ammi  ne tunda nima mafi zama can din” ya faÉ—a yana mai lumshe idanunsa.

” Hakan yayi yallaÉ“ai, Allah ya baka nasara akan kudirinka na alkairi” tareeÆ™ ya faÉ—a cike da Æ™aunar ogannasa.

“Ameen “Adeeb ya amsa ahankali tare da kwanciya.

Ita kuwa wannan matar mai make up,kasancewar tareeÆ™ yayi mata bayanin komai tun kafin su zo gidan,dan haka da sallama tashi ga cikin dakin,juyowa fattu tayi da sauri tana kallon matar.

Murmushi matar tayi tare da kama hannun fattu ta miƙar da ita tsaye tana murmushi,

Kallonta kawai fattu keyi cikin tsoro da rashin sanin ko itaÉ—in wacece?

Cikin harshen larabci matar ke cewa” kai masha Allah yarinya mai kyau da daukar hankali,gaskiya kina da sihirtaccen kyau,Æ´ata, zanyi Mali kwalliya mai kyau kamar ke” ta kai karshen magannarta tana murmushi. ita dai fattu kallon matar take tana tunanin wannan É—in kuma daga ina ?wacece?kodai itace hulwar?

Ahankali matar ta kama fattu ta zaunar da ita bakin gadon,gashin fattu ta fara warwarewa, ” kai masha Allah,kina da gashi mai tsananin kyau,samun irin gashinki ba kowacce mace ba,larabawan ma” matar ta faÉ—a cikin harshen labarci,

Ita dai fattu tayi gurum cike da tsoron matar,gashi kuma ta kasa koda yunÆ™urin gudawa ne bare ta tsere.haka matar ta kama fattu sukaje toilet ta wanke mata kanta tass,sanann suka fito. 

Gaban madubi ta kai fattu tare da ɗauki handryer ta busar da kan na fattu,mayuka kala-kala ta shafawa fattu akanta,kan kame tuni kan fattu ya ɗauki wani sheki da ƙamshi, ita kanta fattu wani sawai takejin kan nata.

Gyara mata kan tayi sosai sannan ta ɗaure mata shi da wani ƙaton ribom mai kyau.

Kwalliya tayiwa fattu cikin nutsuwa ba mai yawa ba,daga powder sai lips da kwalli ta sawa fattu a idonta,irin sakun nan da larabawa keyi,kusan rabin ido.

Kai fattu fa tayi mugun kyau fuskar nan Tata kamar farin wata dan haske,kwalliyar ta karbi fuskarta sosai,kodan ba tabayin kwalliyar tayi ba oho?

Ledojin nan mata ta buÉ—e tare da É—auko wata bakar doguwar riga,dama kuma kayan duk dogayen riguna ne masu kyau da sutura jiki.

Har zata dauko su bra,sai taga wata akan gadon ,dan haka sai bata daukoba.

Karanta Littafin : Matar Hariji Complete Novel

Wani Æ™aton towel ta É—auko ,dake gefen kofar bandakin asaÆ™ale ,mikawa fattu tayi tare da cewa ta cire kayan jikinta ,saita sanya bra É—in sannan tasa kayan nan.cikin harshen larabci matar ke magana.dan bata san cewa fattu bata jin larabci ba,dan kuwa ita tayi tunanin fattun Æ´ar Misran  ce itama.

Kallon fattu tayi gurum! Kamar kurma,dan bata san me matar ke faɗi ba.ganin fattu bata karɓi towel ɗin ba tana zaune kawai yasa matar tunanin kodai kurmace?

Kwatance ta farayiwa fattu da hannu,cikin ikon Allah kuwa fattu ta gane wai rigar zata cire ta É—aura towel din .karÉ“a fattu tayi tare da daura towel din asaman Æ™irjinta.murmushi matar tayi tare da É—aukar bra É—in ta mikawa fattu.kallon brar fattu tayi tare da kallon matar” tab Ni nasan me zanyi da wannan abun da kina wani mikomin” fattu ta faÉ—a cikin ranta tana mai turo baki tare da kauda kanta.

Murmushin matar tayi tana mai rayawa aranta  ,kodai fattun kunyar saka bra É—in take?dan ga dukkan alamu wannan ne karonta na farko asaka bra É—in.

Cikin hikima da dabara matar ta sakawa fattu bra bayan sun sha artabu,dan fattu sam ƙin yarda tayi da farko, aganinta wannan hulwar so take ta gane mata abubuwa,amma cikin hikima matar tayiwa fattu munin ba ganin jikinta zatayi ba tana son rufe mata jikinta ne,sannan ta dagawa fattu rigar jikinta tare da nuna mata itama ta saka irinta.sai lokacin fattu ta fahimci inda ake saka bra ɗin.ikon Allah wato suma waɗannan abubuwan harda jakar da ake boyewa?lallai zakaga abu da yawa idan baka mutuba.

Aikuwa tsif bra din tayiwa fattu ajikinta,Dan dama koda tareeÆ™ yaje karbowa cewa yayi budurwa yar kimanin 16 za’a haÉ—awa kayan,

Saidai fanties É—in duk sun mata kaÉ—an sosai,da gyar matar ta samo mata wani mai kama da gajeren wando sannan  tasaka.

Da kanta ta sanya rigar ajikinta,masha Allah masu karatu duk wanda yaga fattu awannan lokacin zaiyi tunani wata fattun aka sake,dan tayi kyau har ta gaji da yin kyan.

Tauraruwa matar ta fadawa fattu ajikinta masu daɗin ƙamshi,sannan tayi mata rolling ta ɓame da wani kyakykyawan abinda ake riƙe mayafi dashi dan gudun zamewa.

Sosai matar ke yaba kyan da Fattun tayi , ga sarƙarta sai walwala take,matar sai kallon sakar take cike da jinjina irin kuɗin da aka batar wajen siyanta,kafin ta kama hannun fattun ta juya da ita gaban madubi.saida gaban fattu ya faɗilokacin datayi arba da kyakyakywar fuskarta jikin madubi,hannu tasa tare da shafa fuskartata,dan tabbatarwa itaɗince kuwa.

Ƙuri!! Fattu ta kure kanta da kallo ta jikin madubi,wai dama haka take  ko kuma dai ba ita bace wannan É—in?anya matar nan ba sake mata fuska tayi ba ?dan dan ita bataga tsohuwar fuskarta ta da ajikin madubin ba.

Murmushin tayi lokacin data É—an mintsini hannunta kadan,kuma  taji zafi.

Wllh nice ,nice fattun baffa, gaba daya na zama Æ´ar gayu aradu zan tsula tsiya, wayyo Allah na ,ina Hamma yazo ya ganni ,yaga yadda na koma fattu Æ´ar gayu.

Juyowa fattu tayi tana kallon matar nan, fuskarta dauke da murmushi, itama matar murmushin tayi tana yaba kyau da Allah ya ba faytu.

Wayar matar ce tayi ƙara hakan yasa ta dauka ba tare da tace komai ba ta kara akunnenta,

“To yallaÉ“ai ganin nan”

Shine abinda matar ta faÉ—a tana mai haÉ—a jakarta ,sallama tayi fattu bayan ta rungume fattun.

Koda matar ta fita tsayawa fattu tayi jikin madubin nan tana ƙara kallon kanta,tajita nan ta juya can tana dariya ƙasa -ƙasa.

Adeeb ne ya shigo ɗakin sanye da farar jallabiya mai tsananin kyau da ɗaukar ido,kansa kuma hiramine sai wannan baƙin abun da suke ɗorawa asaman hiramin, ba ƙaramin kyau yayi ba sai sheƙi fuskarsa keyi.

Tsak !ya tsaya abakin Æ™ofar yana mai faÉ—in “masha Allah,watabarakallahu fi ahsanil kaliÆ™in” lokacin da yayi arba da Æ´ar gayu fattu,wacce Bama tasan yana gurin ba,kallon kanta kawai take ,ta taÉ“a nan ta taÉ“a can.

Saida yayi gama Æ™ureta da kallo,yaga dai idan ya biye ta kallonta to zasu kwana anan ba tare da ya gaji da kallon nata ba,dan haka sai yayi É—an gyaran murya  kafin yace ” idan kin gama kalle madubin zo mutafi.

Karanta Littafin : Walijam Complete Novel

Sai lokacin fattu ta an kare da Hammana nata na gurin” cikin jin daÉ—i ta nufeshi tana murmushi,” Hamma kalli yadda matar nan ta sauya min fuska? Wllh gani nake kamar bani ba “fattu ta faÉ—a tana dariyarta mai burge wa da ban sha’awa.

Kallonta kawai Adeeb yake ,dan shikam ya rasa bakin magana ma,gaba É—aya fattu ta sanya shi cikin wani yanayi na ruÉ—ewa da zallar kyanta.

Ita kuwa tana tsaye gabansa sai rangaji take ,jinta take kamar sarauniya yau É—in nan.

Ahankali Adeeb ya kai kallonsa kan waÉ—an nan abubuwan na fattu, ajiyar zuciya ya sauke ganin yanzu kam ta saka wannan abar.dan haka hannunta kawai ya kamo sukayi waje.

Sai lokacin fattu ta sami damar kallon tsarin falon,sama gidan baki É—aya .

Suna tafe amma fattu na waige waige,ikon Allah Allah garin daÉ—i na nesa,ashe su amaÆ™abarta suke,anya kuwa wannan gidan ba aljannar duniya bane.ahankali tace ” kaikuwa Hamma dan Allah wannan gidan na waye?”ta faÉ—a tana kallon yadda yake danna nonbibin bude Æ™ofar.

Kallonta yayi bayan sun fito farfajiyar gidan,kafin ahankali yace “nawa ne”

Baki fattu ta buÉ—e cike da mamaki kafin tace ” ikon Allah, to Hamma a ina ka sami kudin gina wannan gidan, dan nasan aradu zai kai kusan dubu saba’in ko tamanin ” ta faÉ—a tana irin jinjina kan nan  na ta kwaso kudi da yawa.

Dariya ce ma ta kama Adeeb ,saidai kasancewarsa ba mai yawan dariya ba yasa yayi murmushi kawai ,kafin yace ” ki tara kuÉ—in da kika faÉ—a kibani na baki gidan” ya faÉ—a cikin nishadi,haka kawai yake jinsa cikin wani irin nishaÉ—i dajin daÉ—i 

Kama baki fattu tayi cikin zato ido tace”woooooh Ni É—iyar baffa,ina zanga wannan uban kuÉ—aÉ—en? saidai idan  kaina san siyar insamu, Ni wllh bazan gina gida irin wannan ba ma,haba saikace wanda zan zauna da aljanun duniya acikin” ta faÉ—a tana wani dan taÉ“e baki irinna rufamin ashirin nan.

Kallonta Adeeb ya É—anyi, yadda take ta zuba masa surutu,ashe dama tana da surutu haka?yanzu ta sake dashi sosai,kuma ya fuskanci idan suna tare sam bata fiye lura da wasu abubuwan da zata gani taji tsoroba.

Dai dai nan suka kawo wajen ajiye motoci,kafin su karasa saiga tareeƙ ya fito daga cikin wata rantsatstsiyar mota Black,mai baƙin gilasai,motace yar ubansu wacce kana gani kasan anyi barin kuɗin agurinta.

Bude musu motar yayi yana ɗan satar kallon fattu,wai zuƙi haka yarinyar take dama,gaskiya yana fatan Allah yasa wanan alherin da suka ƙalla karya kunce .

Harararta Adeeb yayi cikin jin haushi yadda ya kafawa fattu idanu yace ” to yi da gaske ka cinyeta” ya faÉ—a cikin harshen larabci yana hararar tareeÆ™ .

Dan sosa kai tareeƙ yayi yana murmushi,azuciyarsa yana faɗin lallai yallaɓai irin wannan kishi haka kiri-ƙiri?hmmmmm .

Shiga motar sukayi fattu na ta kallon yadda motar take wani sukuf da ita ,kamar siffar wani kwaron, 

Kallon Adeeb tayi wanda ya jingina kansa da jikin kujera as usual idanunsa alumshe.

“Hamma  wai a wannan duniyar da mukazo, acikin kwarya ake yawo ne?”ta faÉ—a tana mai riÆ™e haÉ“a.

Idonsa daya ya buɗe tare da kallon ta ,yana rasa mai zai ce mata dan takaice wai motace ƙwaro,kai fattu sai gyaran Allah.

Ganin yayi shiru ta kuma cewa “Hamma yanzu kuma wace duniyar zamu?”

Kai Adeeb ya dafe cike da gajiya surutu yace ” duniyar cinye mutane masu surutu” ya faÉ—a yana harararta.

Allah Sarki fattu dagalo!!tayi tana kallonsa cikin mutuwar jiki ,kafin ahankali ta ɗan matsa kusa dashi tare da kamo hannun rigarsa ta rike tayi kalar tausayi sosai ,ashe duk murnar da take dama duniyar cinye mutane zasu koma,?shikenan bazata ƙara ganin baffanta ba?

Ahankali tace “Hamma baffa….

“Hihhhhhhhh” Adeeb ya fada yana mai É—ora danyatsarsa  akan  bakin fattu,sannan ya kwanto da kanta zuwa kafaÉ—arsa.

Kwanciya tayi lamo cike da tunani kala kala aranta .

Tafiya sukayi mai É—an nisa kafin naga sunzo gaban wani irin makeken  gida mai matukar girma da Æ™asa,girman gidan yayi haÉ—a anguwanni manya guda uku,get suka nufa ,suna idan akaga tareeÆ™ sai abude masa cikin girmamawa,ba wanda ya kula da Adeeb dake bayan motar,dan glass É—in bakinsa sosai.

Saida suka wuce manyan get bakwai ,kafin suka nufi wani get mai matukar kyau da girma,wani irin walwali get É—in keyi kai kace da zallar kwal akayishi.

Daga samansa kuma wasu danjojine masu ruwan kwal ke rubuta,

 Well come to the King palace cikin manyan baki.

Ahankali get din ya buÉ—e bayan wata doguwar na’ura ta danno kai ta haske ko ina cikin motar .

“YallaÉ“ai mun karaso” tareeÆ™ ya faÉ—a yana É—an juyowa kadan.

Shiru Adeeb yayi yana mai jin wani irin kewa da damuwa azuciyarsa.” TareeÆ™ how long na dauka ba’asan inda nake ba?Adeeb ya tambaya cikin sanyin murya.

“YallaÉ“ai  5 months 3days” tareeÆ™ ya faÉ—a cikin jimami.

Runtse idanu Adeeb yayi tare da budewa ,da sauri kuma ya yunÆ™ura  tare da dauke kan fattu daga kafaÉ—unsa,wacce tayi lamo kamar mai barci tsoro duk ya gama cika mata ciki.

Fitowa yayi daga motar kafin ya fara takawa cikin nutsuwa da jin  kewar iyayensa.

Da sauri fattu ta fito daga mota ita ta riga da gudu tabi bayan Adeeb,Allah yasa flat shoe ne akafarta.saurin kamo gefen hiraminsa tayi ta riƙe gan cikin hannunta.yana jinta baice mata komai ba ,har suka kai bakin ƙofar.

Ahankali ya nuna fuskarsa jikin wani dan madubi,wani dogon layine naga yana zagaye fuskar tashi,kafin kofar ta buÉ—e da kanta,yana sanya kafa  cikin wani tafkeken falo ,naji wata murya ta dauki 

Magana,” Well come home prince Adeeb Muhammad Ashraf ,your hinest you have a big surprise to see ” 

Karanta Littafin : Tsintsacciya Complete Novel

Masu karatu fattu fa gaba É—aya ta tsure da  ganin irin duniyar da suka shigo,wani irin mahaukacin falone ,wanda ta ko ina matsalar benece acikinsa, ga wani dan banzan sanyi da Æ™amshi dake dukan hancin ta.nan da nan jikinta ya kama rawa.

Ta rike hannun Adeeb gam-gam cikin nata.

Kamo hannun nata yayi tare da kanta zuwa cikin tsakiyar falon,wanda da gyar fattu ke taka ƙafarta dan wani irin kaishi da taji a ƙasa dakin.

Zaunar da ita yayi yana mai kallonta,

“Ki zauna anan, za’a shigo dake yanzu.” 

Adeeb ya faÉ—a yana mai kallon yadda jikinta ke tsuma.

Hannunsa ta kara damkewa kafin tace “Hamma tsoro nakeji sosai” ta faÉ—a cikin rawar murya.

Hannun nata ya kama ahankali ya kai bakinsa ya sunbata, kafin ya shafa gefen fuskarta ,yace kijirani kinji ” yana faÉ—in haka yabi matakalar dake  tsakiyar falon yayi sama.

Kallo fattu tabishi dashi cike da tsantsar tsoron wannan guri.hawayene ya zubo mata sharrrrr!! Daga idanunta,ahankali ta sanya hannu ta share wahayen .

Shikuwa Adeeb wani haÉ—aÉ—den part É—in naga ya nufa asaman,hadimaine birjik farfajiyar gurin kowa da abinda yake ,tafiya yake cikin sauri da sassafar,ba abinda yake so da buri illa yayi ido hudu da abinsa.wata baiwa ce ta ankare da Adeeb,cikin hanzari ta zube Æ™asa tana faÉ—in 

Takawarka lafiya ,dan sarki jikan sarki,yarima mai jiran gado,alherin Allah ya kai maka.

Da sauri duka suka ankare da abinda baiwar nanke fadi,cikin azama da tsantsar farin ciki sauran ma suka zube ƙasa suna kwasar gaisu da murnar ganin Adeeb,ba wanda Adeeb ya kula kai tsaye dakin mahaifinsa ya nufa.

Ahankali ya buÉ—e kofar  cikin sanyin murya yayi sallama.

Wani farin Balarabe dattijone kwance akan wani lafiyayyen gado irin na sarakuna masu ji da kansu,gefensa kuma wani likita ne ke ƙoƙarin daura masa ruwa ahannunsa,

Sai wani mata guda biyu dattijai, sunsha ado da gwala-gwalai na alfarma ,ko wacce tana inbakiyi bani guri,

Sai wani farin matashi zaune kusa da dattijon nan,ya riƙe hannunsa.

Cikin azama dattijon ya wani zabura tare da sauÆ™owa daga kan gadon yana mai goge idanunsa,kafin cikin rawar murya yace ” habeebee Adeeb ” 

Ya faÉ—a tana nuna gofar dakin ,inda Adeeb ke tsaye ,cikin shaukin ganin mahaifin nashi.

Gaba dayan yan dakin ne suka biyo suna kallon ƙofar dakin,aikuwa Adeeb ne ya dawo,prince Adeeb ya dawo gida.

Da gudu Adeeb ya karaso cikin dakin tare da rungume dattijon nan ajikinsa tsantsan yana mai faÉ—in,” habeebe rurh cikin kuka”

Shima kuka kawai dattijon nan yasa tare da ƙanƙame Adeeb ajikinsa.

Matan nan kuwa kallon kallo naga sun fara cikin rudewa da shiga kokwanto.

Masu karatu  muje zuwa yau dai ga fattu cikin gidan sarautar Masar,koya zata kasance?

Ga kuma Adeeb jikin mahaifinsa .

Sai mun hade next page.

Anty mammynku ce 

Mrs babi💘💘💘

Share and comment fisabilillah

More comment 

More typing.

Back to top button