Uncategorized

Macijine Shi Page 31-32 Hausa Novel

Na mammy kabeer

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 31/32

_________________Saƙare,fattu tayi tana kallon macijin cike da tsantsar mamaki, kamar yadda macijin ke kallon fattu shima ido cikin ido.

Ahankali fattu ta lumshe idonta,tana mai ambaton sunan Allah,abin da ya bata mamaki shine,sam bataji tsoroba, saima bin jikin macijin da tayi da kallo,tabbas wannan macijin ta ne na yar ruga, kenan hakan na nufin Hammanta ne ya ƙara zama maciji? innalillahi ,yanzu yazatayi kenan?awane matsayin take idan bai dawo mutum ba?

Ahankali ta furta “Hammana” hawaye na zubowa daga cikin idanunta.

Shikuwa macijin yana ganin hawayen nan nata,ya  taho  zuwa gareta,yana zuwa ya hau kan cinyarta tare da nannaÉ—e jikinsa ya É—ora kansa akan kafaÉ—unta.

Lumshe ido fattu tayi cikin kuka tace ” dan Allah HAMMA  karka zauna cikin wannan yanayin,bazan iya rayuwa Ni kadai cikin wannan gidan mai aljanu ba, dazuma saida Hulwarka tazo ta  tsoratani, gaba daya ta sanja duniyar wannan dakin ,ya koma wata kala,kalli kagani yanzu yadda ya koma,Hamma inajin tsoro”fattu ta faÉ—a tare da É—ora hannunta akan macijin tana shafawa.

Dagowa macijin yayi tare da zuba mata idanu,itama kallonsa take hawaye na zubowa daga idanunta. Jikinta ya fara zagayewa yana yana nannaÉ—eta,kafin kuma yayi baya da ita akan gadon,kwanciya fattu tayi tare da runtse idanunta .

Ita kam tariga ta gama sallama wa rayuwa, tasan idan har macijinta bai  dawo mutum ba to mutuwa zatayi, ahalin da ake ciki yanzu tana jinsa ne har cikin ranta,kome takeyi shi take gani,ba abinda take bukata akullum kamar tajita kusa dashi,ta san duk ransa wani ya ganshi matsayin maciji ,to za’ayi Æ™oÆ™arin kashe mata shine,wanda tayi imanin duk randa aka  kashe Hamma, to tabbas da gawarsa za’a binnesu.

Shikuwa maciji bayan ya kwantar da fattu saiya zare jikinsa daga  nannaÉ—etan da yayi,sannan ya kamo bargon dake kan gadon ya lullaba ajikin fattu,duk abinda yake kallonsa fattu keyi cike da tausayawa,ace mutum yana komawa wata da bar daban?kuma mai haÉ—ari wacce kowa ke gudunta.saukowa yayi daga kan gadon tare da tsayawa daga can gefenta yana kallonta, itama kallonsa take ,kusan minti uku suna kallon juna,yayin da fattu ke zubda hawaye,juyawa yayi tare da nufar Æ™ofar dakin.

“Dan Allah Hamma ka dawo mutum,kada ka tafi ka barni,ina don kasancewa tare da kai,bani da kowa awannan sabuwar duniyar saikai”abinda fattu ta faÉ—a kenan lokacin da taga yana Æ™oÆ™arin ficewa daga É—akin.

Aikuwa tsayawa yayi kamar wanda yake sauraron me take faÉ—i .saida ta kai aya azancenta,kafin ya kalleta da idanunsa masu naunuka daban daban,sannan ya fice daga É—akin.

Kuka sosai fattu ta fashe dashi,tana daga kwancen nan,shikenan komai yazo mata Æ™arshe,idan  Hamma ya tafi ya barta,ita ahalin yanzu ma, ta fara tunanin kodai duniyar aljanu ya kawo ta?

Haka tayi ta kukanta tana daga kwance har barcine wahala yayi gaba da ita.

Karanta Littafin : Matar Hariji Complete Novel

Shikuwa Adeeb yana fita kai tsaye dakin daya baro ya nufa ,ahankali yake jan jikinsa , harya kai kan gadon ,hawa yayi tare da kwantawa lamo kamar baya nunfashi,rufe idanunsa yayi yana nishi da gyar, kafin kuma jikinsa ya kama girgiza sosai yana hayaÆ™i,  sosai dakin ya turnuÆ™e da hayaÆ™i kafin ya washe.

Ikon Allah Adeeb na hanga kwance akan gadon nan,ya duƙunƙune jikinsa,sai rawa yake kamar mai jin sanyi,ahankali ya ɗaya hannunsa dake ta faman rawa ya dage kansa,yana mai yamutse fuska ,da alama kan ke masa ciwo,kusan minti goma ya ɗauka cikin wanan halin kafin naga ya miƙe jiki ba kwari,ya nufi toilet ,wanka yayi tare da sake kaya,ya fito cikin fara tass ɗin jallabiyya.

Zama yayi akan wata kujera dake gaban gadon,kujerar tsabar kyanta ,kai kace da zallar kwal akayita.sai Æ™amshi  yake bugawa, kallon É—akin yake yana mai mamakin shidai yasan ya fita zuwa kitchen kuma har yayi girki,bayan nan kuma ya nufi dakin Hulwa, kuma…

Da sauri ya mike yana mai zafi ido,tabbas asume ya ganta aÉ—akin ,amma kuma me yasa shi yaganshi ana ?me ya dawo dashi É—akinsa.

Da sauri ya nufi ƙofa yana ficewa daga dakin,saidai yana fita kafin ya kai dakin nata,yaji sanarwar zuwan tareeƙ,kallon kofar Tata yayi sannan ya nufi bakin ƙofar shigowa falon, yana ɓudewa ya ga tareeƙ da kaya riƙi-riƙi ahannunsa.

Kallonsa tareeÆ™ yayi yace “yallaÉ“ai lafiya kuwa?

Ahankali Adeeb ya lumshe idanunsa kafin ya jinjinawa tareek din kai,alamu lafiya ba komai.

Shigowa tareeÆ™ yayi da kayan ya ajiye yana mai cewa”yallaÉ“ai idan an duba sai afadamin abinda babu aciki.” Nan ma dai kai kawai Adeeb ya daga sannan ya kalli kayan ,ledojine kusan guda goma manya-manya.

Kallon TareeÆ™ yayi na dan wani lokaci kafin yace “an shirya komai na zuwan gurin mai Abie”?

” Eh yallaÉ“ai komai ya kammala ,lokaci kawai muke jira” cewar tareeÆ™ kenan cikin girmamawa .

Jinjina kai Adeeb yayi kafin yace ” U can go” 

“Ok yallabai” 

TareeÆ™ ya faÉ—a yana mai barin falon .

Kayan da tareeÆ™ ya ajiye Adeeb yayi da kallo kafin ya É—auki leda É—aya yana É—an leÆ™awa, idanunsa ne suka sauka kan inner wear masu bala’in kyau da tsada,da sauri ya rufe ledar yana É—an kallon Æ™ofa, dan sosa kansa yayi kafin ya dauko bra guda É—aya da hannunsa yana mai kallonta,shiru yayi yana tunanin lallai zatayiwa fattu daidai,dan ahalin yanzu yana kallon abubuwan ta daya taÉ“a gani a toilet,murmushin yay tare da dan sosa kansa kafin ya É—auki ledojin duka ahannunsa yayi dakin fattun.

Yana tura ƙofar kuwa ya jiyo ƙinkishin kukanta,tana zaune a tsakiyar gadon ta haɗa kai da gwuiwa tana kuka.dan bata wani jima tana barcin ba ta farka kuma ita tsoro takeji taje ta taɓa kofar wannan hulwar ta kuma tsoratata.

Da sauri ya ƙarasa cikin dakin yana kallonta,tsayawa yayi akanta bayan ya ajiye ledojin dake hannunsa,sosai yake jin tausayin fattu cikin zuciyarsa,sam baya kyaunar ganinta cikin damuwa,yanzu zaiji zuciyarsa tayi masa zafi sosai.

“Hulwa ” Adeeb ya furta cikin muryarsa mai sanyi da nutsuwa.

Da sauri fattu ta É—ago kanta ,sakamakon jin Muryar Adeeb da tayi,

Ai bata san lokacin data diro daga kan gadon nan ba ta wani ƙanƙame Adeeb da iya ƙarfinta tana kuka,

“Hammana dama nasan bazaka gudu ka barni ba, Hamma na shiga damuwa sosai lokacin danaga ka koma macijin nan,nayi tunanin guduwa zakayi ka barni Hammana dan Allah karka rabu dani”fattu ta faÉ—a cikin matsanancin kuka,wanda zamu iya cewa na farin cikine.

Karanta Littafin : Yar Harka Complete Novel Document.

ahankali Adeeb ya lumshe idanunsa,tare da sakin ajiyar zuciya”har abada bazan taba rabuwa dake ba,ina tare dake komai rintsi komai wuya hulwatee” abinda Adeeb ya faÉ—a kenan , cikin zuciyarsa,amma azahiri kawai rungume fattu yayi shima ,yana mai shafa bayanta ahankali.

Kuka sosai fattu keyi tana kara rungume Adeeb,bazata iya faÉ—in irin farin cikin da take cikiba, 

” Ya isa haka kukan ” Adeeb ya faÉ—a yana mai É—ago kanta.komar da kan nata tayi tare da kara kwanciya akan faffaÉ—an Æ™irjinsa.

Murmushi kawai Adeeb ya tsinci kansa dayi,yana mai shafa bayan fattu,sosai yake jin wani nishadi idan fattu ta ruƙunkume shi nan ,ji yake kamar su tabbata ahaka.

Bangaren Fattuna dai hakan ne ,ji tayi bata don rabuwa da jikin Adeeb ɗin,dan ba ƙaramin nutsuwa take samu akan wannan ƙirjin nashiba.

Kusan minti goma suna rungume da juna ,kafin Adeeb yayi karfin halin cire ta daga jikinsa yana mai cewa” waike bazai sakeni ba saikin karyani?kin fiye son jiki fa” ya faÉ—a  yana É—an harararta .

Kai ta duniyar Æ™asa kafin tace “Hamma yunwa nakeji” kallon inda ya ajiye abincin dazu yayi kafin ya janyo table É—in zuwa gaban gadon,

”  Zauna “yace mata.

Zama tayi abakin gadon tana kallonsa,farin ciki fal cikin ranta.

Tea ya haÉ—a mata sannan ya mika mata flate É—in kwan da bread zuwa gabanta.wani bowl ya mika mata ta wanke hannunta,kafin ta fara cin abincin,lallai fattu na jin yunwa ,dan kuwa tass ta kawar da abincin nan,shidai kallonta kawai yake,azuciyarsa yace “wannan badai ciba” tana gamawa tayi hamdala tana mai lashe lips É—inta,É—ago kai tayi suka haÉ—a ido da Adeeb ,saikuma kunya ta kamata,ganin yadda ta kawar da uban abincin nan.

Shikuwa Adeeb cewa yayi ” kin koshi ko zaki Æ™ara dan naga kedin akwai ci kamar Gara”

Dan shagwabe fuska tayi kafin tace “Allah Hamma abincinne ke wuce silik -silik,ba dan ma na cinyeba.ta faÉ—a tana kallon farantin.

Ƙureta kawai yayi da ido yana kallonta baice komaiba,dagowa tayi suka haÉ—a ido ,harararta yayi yace “zaki fara kallonsa ko” girgiza kai tayi tare da maida kanta Æ™asa.”zanyi sallah Hamma”ta faÉ—a kanta a Æ™asa.

Nuna mata toilet yayi da hannunsa ,ba tare da yace komai ba.

Mikewa tayi yake bakin ƙofar ta tsaya tare da juyowa.

Yana kallonta baice komai ba,dan yasan me take nufi,ita komai bata iyaba

Saida yayi jimmm!kafin ya mike ya Æ™arasa jinkin Æ™ofar, ya murda handle É—in yace “kin gani haka ake yi”jinjina kai tayi tare da mamakin wai Æ™ifama sai anwani murÉ—ata kamar kan fanfo”

Maida Æ™urar yayi ya kulle sanan yace “buÉ—e”kallonsa tayi kafin ta kalli Æ™ofar, hannunta ta sanya tayi kamar yadda yayi aikuwa saiga Æ™ofa ta bude.wata dariya ce ta kwacewa fattu ganin tayi nasarar buÉ—e kofar tace ” hahhahhh laaaah Hamma dan Allah kaga abin sauÆ™i wllh kuma budewa daÉ—i”ta faÉ—a tana kara sanya dariya cikin farin ciki.

Shikansa Adeeb dariyar tayi har saida fararen haÆ™oransa suka bayyana.jijjiga kai yayi kafin ya wuce ciki yana faÉ—in”Allah ya shiryeki”

Komai saida ya nuna mata ,sanan yasa ta kunna da kanta,aikuwa fattu gaba É—aya yau ta zama kamar wata shasha ,data kunna abu yayi zata kama dariya,wataran harda É—an tsallenta takeyi.

Shidai fitowa yayi ya barta dan tayi wanka da alwala.

Bude kayan da tareeÆ™ ya kawo yayi ,wata doguwar pink É—in riga ya dauko da mahaifinta ya ajiye mata,sannan ya dauko wani fant da bra ya ajiye akan gadon,sannan fice.

Karanta Littafin : Abban Sojoji Hausa Novel


Bayan fattu tayi sallah ne taga kaya akan gado,É—auka tayi tana kallon kayan,sunyi mata kyau a ido sosai ,amma saita ajiye da sauri tace “Æ™ilama na hulwar tasane ,Ni wllh na tsani wannan hulwar” ta faÉ—a tana hararar kayan.

Adeeb me ya shigo cikin dakin da sallama can ƙasan maƙoshinsa.

Tsayawa yayi yana kallon fattu ganin bata sake kayan daya ajiye mata ba.

” Baki Ga kaya bane kika maida wannan. Dan Æ™azanta” Adeeb ya faÉ—a tana hararar fattu.

“Kayi hakuri Hamma nayi tunanin  a hulwar taka ne ai” fattu ta faÉ—a tana daga kayan,

“Hamma wannan fa ” ta faÉ—a tana daga bra É—in nan.

” Baki san me ake yi da itaba  maza ki shirya ina jiranki” ya faÉ—a harararta tare da ficewa daga É—akin.

Fattu kuwa data rasa ya zatayi da bra É—in na sai kawai ta sanya kayanta haka tayi waje .

Tana fitowa Adeeb ya biya da kallo ganin bata sanya bra dinba ,yace ……..

Mu hade next page banda cajine.

Mrs babi ce💘💘💘

Back to top button