Uncategorized

Macijine Shi Page 15-16 Hausa Novel

Na mammy kabeer

(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 15/16

Kuyi join grp É—in da zaku samu more update na MACIJI NE

NIMCY LUV HAUSA NOVELS 

Albishirinku masoya,ga dama ta samu ga mai buƙatar a tallata mata hajarta,to ashirye nake dan tallata mata cikin farashi mai sauƙi,dan haka idan kin shirya sai kiyimin magana .

________________Wata irin Æ™ara da guguwa ne masu  matuÆ™ar Æ™arfi da firgitarwa , suka cika dakin.ta yadda koda tafin hannunka baka iya gani tsabar duhun da É—akin yayi,ga guguwa sai juyawa take aÉ—akin.

Ko kaÉ—an hakan bai tsorata baffa ba ,saima cigaba da yayi da karanto ayoyin shifa daga cikin alÆ™ur’ani mai girma yana tofawa asaitin dayasan macijin nan yana gurin ,duk da duhun daya mamaye É—akin.

Fattu kuwa wani irin tsorone da fargabar suka baibayeta , jin yadda macijin nan yake wata irin murɗewa da sakin wani sautin ƙara mai ban tsoro ,sannna kuma sai takejin yana ƙara mata nauyi sosai akan cinyarta.

Cikin tsoro da ruÉ—ewa ta lalubo hannun baffa tace ” wayyo baffa tsoro nakeji,wllh kamar yana rikiÉ—ewa ne zuwa wata halittar ,yayimin nauyi akan cinyata baffa, baffa ina tsoron kar wani abu ya faru”Fattu ta faÉ—a cikin rawar murya mai cike da tsoro.

Hannunta baffa ya riÆ™e shima cikin yanayi na son kwantar mata da hankali yace”karki damu Fattu ba abinda zai faru sai alkairi,kici gaba da karanto addu’oi kina tofa masa  in Sha Allah komai yazo Æ™arshe “baffa ya faÉ—i hakan tare da ci gaba da karanto zafafan addu’oi yana tofawa macijin.

Fattu ma É—aurewa tayi taci gaba da karanto addu’ar tana tofamasa, jikinta sai rawa yake,yadda takejin alamun sauyin halittar da macijin nan keyi.idanunta arufe gam-gam.

Kusan shuÉ—ewar mintina biyar zuwa bakwai, duhun nan ya fara yayewa ,ahankali hasken tocilolin su baffa  ya fara gauraye dakin.

Salati baffa ya farayi da Æ™arfi da kiran sunayen Allah yana mai kabbara. “La’ilaha illallah muhammadur rasulullahi sallallahu alaihi wasallam,ya Allahu Ya rahmanu ,ya hayyu ,ya Æ™ayyum,Allahu akbar, Allahu akbar “abinda baffa keta faman faÉ—i kenan cike da ta’ajibi da jinjina wa Æ™udurar Ubangiji,cikin hanzari ya janyo zanin rufuwarsa ya lulluÉ“awa maciji ,daga cikinsa zuwa Æ™asansa dan ba kaya ajikinsa.

Jin yadda baffa ke tafaman kabbara da salati ne ,yasa Fattu buÉ—e idanunta cikin nutsuwa da kuma jarumta ,har zuwa lokacin bata fasa karanto addu’oi ba.akan fuskar baffa ta sauÆ™e idanunta ,gaba É—aya baffa ya shiga al’ajabi da mamakin abinda idanunsa suka gane masa.dan har lokacin yana kallon macijin ne Æ™uri kamar ya sami talabijin.

Ahankali Fattu take sauÆ™e idanunta zuwa kan cinyarta,wata irin bugawa zuciyarta tayi ,lokaci É—aya komai nata ya tsaya cak. Sai wata irin rawa da jikinta ya kama kamar zata karkarye,ta É—auki kusan minti biyu cikin wannan halin kafin taja wani dogon numfashi tana mai buÉ—e baki tace”ba…..f..ff..fa …mumm…….tttuummm….nnnee…..a..Mamman.cc…..iiii…..sai kawai ta sulale ta faÉ—i Æ™asa daga zaunen da take.

Ba komai bane ya sanya Fattu shiga cikin wannan halin ba , face ganin wani zankaɗeɗen haɗaɗden saurayi ,fari ƙal-ƙal da tayi kwance ya kifa cikinsa akan cinyarta,maimakon macijin dake kwance akan cinyar ta ta.

Kuma wannan shine dalilin salati da baffa keta rafkawa cikin kushu’i da tsarkake baiwa da buwayar mahalicci.lallai duniya ta zama abinda tazama ,yanzu mutum ne aka mayar dashi dabba?maciji?kuma ga dukkan alamu wannan ba É—an yankin nan bane ,dan ko kaÉ—an baiyi kama da mutanen mu ba.

Ahankali baffa yayi kokarin janye shi daga kan cinyar fattu ya kwantar dashi rigingine akan tabarmar.

Hannu baffa ya sanya ya gyara masa zanin daya lulluÉ“a masa dan rufe masa al’aurarsa.sannan ya ture gashin daya lulluÉ“e fuskar mutumin.

“Masha Allah ,watabarakallahu fi ahsanil kaliÆ™in”baffa ya faÉ—a adaidai lokacin da yayi arba da fuskar kyakyakywan matashin mai cike da haiba da kwarjini,ga kyan zati.

Kallonsa baffa yake ƙuri yana jinjina kai cike da mamaki da alhini,lallai duniya abin tsoroce, rayuwa bata da tabbas,Allah ka karemu,ka rabamu da sharrin maƙiya da mahassada. Baffa ya faɗa acikin zuciyarsa yana kallon bawan Allahn.

Ruwa baffa ya ɗebo ya yayyafawa fattu ,ahankali ta fara motsi tana buɗe idanunta ,tar ta buɗe idanun ta sauƙesu akan baffa, kusan minti biyu tana kallon baffa.

“Sannu Fattu kinji?tashi ki zauna kiga ikon Allah ,tashi kiga taimakon da kikayiwa rayuwar wannan bawan Allahn.

 Baffa ya faÉ—a yana nuna mata inda macijinta yake kwance.

Zabura tayi ta tashi zaune  cikin tsoro tana kallon inda baffa ya nuna mata,da sauri ta matso kusa da baffa ta riÆ™e shi gamm! Jikinta sai rawa yake tace “na shiga uku baffa wllh aljani ne wannan ba mutum bane, daga maciji ya koma siffar mutum ,baffa wllh bamu san me zai koma ba nan gaba ,baffa atsorace nake”ta faÉ—a idanunta yana zubar da hawaye.

Ahankali baffa ya kamo hannunta yace “habaFattun baffa ,kin manta ne?macijin nan ne fa ,wanda yake taimakonki cikin hukuncin ubangiji, shine kuma kikejin tsoro yanzu?kin manta da halaccin sa gareki?meyasa bazaki tsaya tare dashiba?alokacin da yake buÆ™atar taimakonki kema?ki kwantar da hankalinki Fattu ina ji ajikina wannan bawan Allah shine zai zame miki bango kuma tsanin da zai haÉ—aki da innarki”baffa ya faÉ—a cikin yanayi na son kwantar mata da hankali.

Murmushi Fattu tayi cikin kwarin guiwa tace “hakane baffa ,kuma zan kula da bawan Allahn nan  in Sha Allahu ,harya sami lafiya”ta faÉ—a cikin kwarin guiwa,saidai har zuwa lokacin tsorone fal cikin ranta.ahankali ta matsa kusa da macijin saidai can nesa kaÉ—an dashi ta zauna .

Kallonsa take cike da mamakin tsantsar kyan da Allah yayiwa wannan bawan nashi, ita kam tunda take arayuwarta, bata taɓa ganin wani mutum mai kyan wannan bawan Allah ba.

Dan duk kyanta da ake faɗa ,tayi imani bata kama koda ƙafar wannan bawan Allahn ba.

Ahankali ya fara motsi yana ɗan juya kansa hagu da dama.sai kuma ya fara ɗan fizge fizge kamar yana ƙoƙarin tuna wani abunne ko kuma yana son farkawa daga wani mummunan mafarkin .

“Baffa kaga abinda yake “Fattu ta faÉ—a cikin zabura tana kallon baffan.

Wata yar jarka baffa ya É—auko ya buÉ—e ,ahankali yafara shafa masa ruwan dake cikin jarkar. ahankali  maciji ya sauÆ™e wata ajiyar zuciya mai Æ™arfi yana sauÆ™e numfashi ahankali ahankali.

Addu’oi baffa yake tayi cikin wasu magunguna kala-kala yana shafawa bawan Allah nan da yake kwance ,wanda zuwa yanzu jikinsa yayi sanyi,ba kamar dazu da yayi zafi Æ™au-Æ™au ba.

Tun daga ƙafafuwansa Fattu ke kallonsa har zuwa fuskarsa,masha Allah.

Wannan mutumin ya haÉ—u ta ko ina ,anya ma wannan ba haushene?ko bafulatanine irin mu?kai gaskiya wannan bayajin Hausa ko fulatanci,ohhh Ni Fattu yanzu wanann macijina  ne haka ?dama da mutum nake ma’amula  ashe?waye wannan bawan Allahn?su waye sukayi  masa wannan shirin haka?me yayi musu ?inane garinsu?meye sunansa?waÉ—an nan  sune tambayoyin da Fattu ke buÆ™atar amsarsu ,saidai ba mai bata amsar sai wannan bawan Allah.

Baffa ma tunani yake wannan bawan Allah daga ina yake? ,waye yayi masa wannan sihiri?koma dai menene yayi masa maganin da duk sihirin mutum bazai yi tasiri akanshi ba da yardar Allah.

Suna nan zaune jigum jigum, cike da fatan Allah yasa ya farka ba tare da wata matsalar ba,kawai suka ga ya fara motsi karo na biyu,saidai wannan karon ba fizge -fizgen yake ba ,kawai dai ya ɗan riƙe kansa yana kuma yatsina fuska.

Ido suka ƙura masa ba wanda yayi magana ,daga Fattu har baffa,kowa yayi shiru yana kallon ikon Allah.

Ahankali bawan Allahn nan ya fara bude idanunsa yana ɗan lumshesu ,kafin ya buɗe su tar kamar lantarki dan tsananin haske da sheƙin da suke yi.

Ƙur ya ƙure rufi bukkar dakin baffa da idanu,baya ko ƙiftasu,tunani yake ina ne nan?waye ya kawo shi nan?kuma yaushema suka zo nan ɗin?

Yunƙurawa yayi ya tashi zaune ahankali yana cije light pink lips ɗinsa .kallon ɗakin yake cike da mamaki ,har ya juyo zuwa inda su baffa ke zaune shida Fattu sunyi masa ƙuri suna kallonsa,baffa ya fara kalla cike da rashin sani.

“Sannu bawan Allah ka tashi ?meke maka ciwo yanzu ?me kake ji ajikinka” baffa ya faÉ—a lokacin da suka haÉ—a ido da bawan Allahn .

Ahankali bawan Allahn ya lumshe idanunsa tare da jingina da jikin bangon É—akin.yana mai dafe kansa ,dan ciwo yake masa sosai.

“Ayya Fattu inaga fa wannan bayajin  hausa ,kuma bayajin filatanci  miÆ™amin wannan kwaryar In bashi magani ,da alama kanshi ke ciwo.

Cewar baffa kenan, dayaji yayi magana amma bawan Allahn bai bashi amsaba.

Ahankali Fattu ta miÆ™e ta É—auki kwaryar ta miÆ™awa baffa ita ,tana mai cewa “baffa gashi,kuma kamar ma yana jin yunwa ko ?kaga yana shafa cikinsa”ta faÉ—a tana kallon yadda bawan Allah ke shafa cikinsa zuwa Æ™irjinsa wanda gashi yayi kwance luf-luf akai.

Ahankali bawan Allah ya É—ago kansa yana kallon saitin dayaji sassanyar muryar Fattu na tashi. 

Aikuwa karaf idanunsa suka gauraye cikin na juna ,wata irin faÉ—uwar gabace ta ziyarcesu alokaci guda, da sauri bawan Allahn ya kawar da kansa  yana mai dafe Æ™irjinsa,dan sosai Æ™irjinsa ya buga.

Bangaren Fattu ma kuwa,wata irin bugawa Æ™irjinta yayi, wacce har saida taji numfashinta ya É—auke ,wani jiri ne ya É—ebeta ,tayi baya luuuuuuu zata faÉ—i,Æ™ara ta kwalla cike da jin tsoro tana mai runtse idanunta, saidai kuma kafin ta kai Æ™asan taji ta faÉ—a kan wani lallausan  abu mai kama da katifa tsabar laushi.

Ahankali ta buÉ—e idonta ta sauÆ™esu akan………

Muje zuwa masu karatu yanzu muka fara.

Taku ce dai anty mammy

Mrs babi💘💘

Share and comment fisabilillah

More comment 

More typing.

Back to top button