Uncategorized

Macijine Shi Page 13-14 Hausa Novel

Na mammy kabeer

(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚

Free book

Page 13/14

____________________”Wayyo Allah na Mai taimako kana ina?kazo gareni,ina buÆ™atar tallafinka,ahhhhhhhhh !!!fattu ta kwalla Æ™ara mai tsananin Æ™arfi lokacin da taji hannun maigari na Æ™oÆ™arin taÉ“a mata dukiyar fulani tana mai buge hannunsa daga kan Æ™irjinta.

Ɗaga hannu maigari yayi cikin fushi ya sake ɗauke fattu da wani gigitaccen mari,dan ya fuskanci tana ƙoƙarin kawo masa cikas akan ƙudurinsa,shikuwa ya rantse yau bazai bar wannan damar ta wuce shi ba.

“Dan ubanki ki tsaya nayi- nayi abinda ke gabana,wllh yau ko ubankine bukar zai zo gurin nan bai isa ya hanani aiwatar da Æ™udirina akanki ba”mai gari ya faÉ—a yana Æ™ara Æ™oÆ™arin maida hannunsa gurin dake tsole masa idanu,wato  breast É—in fattu.

Saidai kafin hannunsa ya sauÆ™a ga inda yayi nufin ,yaji  wata irin shaÆ™a da tunda yake arayuwarsa bai taÉ“a tsintar kansa cikin irin makamancin wannan shaÆ™ar a aduniya ba.

Ta ko ina yaji shi aɗaure dam-dam kamar ƙullin buhun goro.

Cikin azaba da fizgar magana mai gari yace “wayyo Allah hannuna,na shiga uku wayyo zan mutu”  ya faÉ—a idanunsa azazzare kamar zasu fito tsabar azaba.

Cikin hanzari fattu wacce idanunta ke rufe, ta riga ta gama fitar da rai ta sadaÆ™ar cewa yau shikenan ta rasa budurcinta ,dan ta san ba mai zuwa ya ceceta ,koda tayi ihu ba mai jin sautin ihunta,sakamakon ruwan saman da ake tsugawa.ba zato ba tsammani tajiyo ihun maigari lokacin da maciji yayi sama dashi  ya cilla shi can gefe guda ,bayan tabbatar da cewa mai gari ya suma.ji kake Æ™asss-Æ™asss,hannu da Æ™afar mai gari na bangaren dama sun karye.

Da sauri fattu ta kalli inda akayo jifa da mai gari dan tabbatar da cewar shiɗin ne kokuma yaya.aikuwa cikin wani irin farin ciki da murna ta yunƙura da ƙyar ta zauna tana kuka da dariya,sai kuma ta tafi gareshi cikin rarrafe tana zuwa inda macijin ke tsaye yana huci ya ƙure mai gari da ido,da alama yana son ganin maigari ko zaiyi wani motsin ne yaje ya ƙarasashi,duba da yadda yake ta uban huci ya kafe mai garin da ido.

Fattu na zuwa ta wani kwaÆ™ume  macijin zuwa jikinta ,ta Æ™anÆ™ameshi tana kuka kamar ran ta zai fita,kukanta na dalilai biyu ne,dalili na farko shine ganin macijinta na nan araye ba mutuwa yayi ba,kuma masu neman shi basu ganshi ba.na biyu kuma yadda yazo ya kawo mata É—auki adaidai lokacin da ta fidda rai da  cewar zata rasa abu mafi muhimmanci arayuwarta.

“Ina ka shiga mai taimakona?na shiga damuwa na rashin ganinka, naji tsoron ko sun kamaka sun kashe ,dan Allah karka Æ™ara yin nesa dani na tsawon lokaci irin haka,kalli yadda suke son kawar min da budurcina, bansan me na tsare musu ba ,kowa nufinsa ya cutar dani,kai kadai ke sona,sai baffana ,bana son na rasa É—aya daga cikinku ,kune rayuwata,farin cikina da jin daÉ—ina,mai taimakona ina sonka har cikin zuciyata, ba ruwana da kasancewarka wata halitta ta daban,Dan kafiyemin halitta irin tawa sau dubu”duk cikin kuka fattu ke faÉ—in WaÉ—an nan maganganu,yayi da take Æ™anÆ™ame da macijinta kamar zata maida shi cikinta.yadda ta Æ™anÆ™ameshi, kai kace uwace ake Æ™oÆ™arin rabata da É—anta.

Ahankali macijin nan ke sauƙe wani irin numfashi kamar yana hurawa fattu iska mai sanyi ,da alama dai rarrashinta yakeyi,dan yadda yake huro iskar yana wani rufe ido da buɗewa shine zai fahimtar da kai cewar rarrashinta yake .

Zare jikinsa yayi daga ƙwaƙwumar da fattu tayi masa ya zagaye west ɗinta ,Amma Sam bai matseta ba ,sannan ya shigo da kanshi ta ƙirjinta yana kallon fuskarta yadda hawaye yayi faca -faca kan kyakkyawar fuskar tata.kallon -kallo ake tsakanin fattu da macijinta ,kallo yake mata irin na tausayawa dan abin mamaki ne sosai idan kaga yadda ya wani marairaice fuska yana ƙifta idanunsa tare da ɗan matso da kansa saitin fuskarta,sai kuma ya kwantar da kan nashi saitin da hawayenta ke tsiyaya, ta ɓangaren dama, sannan yayiwa ɓangaren hagun ma haka.

“Dariya mai haÉ—e da kuka fattu take yi cike da tsantsar Æ™aunar wannan halitta ,hannu ta sanya ta share hawayen daya Æ™ara zubowa tace “na daina kukan mai taimako tunda baka so ,bazan Æ™ara ba ka gani ma ko “ta faÉ—a tana mai Æ™ara shafe idanunta ,saidai wasu hawayen na Æ™ara zubowa.

Zare jikinsa yayi yana mai hawa kan wuyanta zuwa kanta saiya leƙo da kansa ta saman kanta ,idan ta ɗago da nufin kallonsa saiya silale ya koma wuyanta ya ɓoye kansa abayanta.

Dariya fattu take cikin farin ciki da ganin cewar wai wasa yake mata dan ta sami nutsuwa ta daina kukan ,dan haka lokacin daya É“oye abayanta sai tace “wayyo ni fattu mai taimakona ya É“ata, ya zanyi da rayuwata ,ina kake abinsona shikenan masu son cutar dani zasu sami dama akaina wayyo ga mai gari nan ya taso”ta faÉ—a cikin yanayi kamar tana son yin kuka .aikuwa cikin sauri macijin nan ya haye kan cinyarta yana mai fasa kai da wani kalle -kalle ya miÆ™a kansa can ya dawo dashi can yana huci.

Dariya fattu tayi tace “nima ramawa nayi tunda ka boyemin ” ta faÉ—a cikin shagwaÉ“a kamar wacce ke gaban baffanta ko innarta.

Juyowa macijin yayi yana kallonta sai kuma ya É—ora kansa daidai saitin zuciyarta yayi lamo ,tare da rufe idanunsa.ahankali ta sanya hannu tana shafa kyakyakywan jikinsa mai matuÆ™ar santsi da laushi.kusan minti biyar suna haka,yayinda ake tafaman zuga ruwan sama ,can gefe kuma mai garine shame shame akwance baya motsi.kallon mai gari fattu tayi ,sai taji tsoro ya cika zuciyarta,kodai shima mutuwa yayi, dan ita tama manta da batunsa aÉ—akin sam,idan kuma ya farka ya Æ™ara dawo mata fa ,gara fa su gudu daga É—akin nan tun kafin jama’a su ankare dasu.

Cikin muryar tsoro tace “mai taimako ya kamata mu gudu gida karya farka ko wani yazo ya gammu dashi ahaka”ta faÉ—a tana kallon macijin dake kwance akan Æ™irjinta,da alama kuma yana jin daÉ—in kasancewarsa ahakan.

Ahankali ya ɗago kansa tare da silalewa ƙasa yayi hanyar ƙofar fita daga bukkar,wacce mai gari ya barta abuɗe tsabar jaraba na cinsa.

Binsa fattu tayi da sauri ,harta fita saikuma ta dawo ta ɗauke tocilan nan ta mai gari ,dan taga garin yayi baƙi ƙirin kuma har lokacin ruwa ake.

Suna fita fattu ta kama sauri -sauri gudu-gudu ,tana tafe tana haska tocilan É—in nan ,yayinda mai taimako ke biye da ita cikin salon nashi gudun ,saidai suna tafe yana zagayeta ,dan bata kariya ta kowacce kusurwa.

Suna zuwa gida kai tsaye fattu É—akin baffa ta nufa,tana zuwa ta shiga É—akin ahankali tana haska tocilan É—in hannunta.Allah sarki baffa yana kan sallaya ya É—aya hannunsa sama yana ta addu’a,juyowa yayi dan ganin hasken da ake haskowa.

“Waye anan”ya faÉ—a yana kunna tashi tocilan É—in.

Ai da sauri ya miÆ™e tsaye yayi kan fattu,yana mai cewa”fattu kece alhmdllh fattu na ba abinda ya sameki,?ina mai garin?waye ya fito dake?baffa ya jero mata waÉ—annan tambayoyin alokaci guda yana mai shafa kanta cikin farin ciki .

Ahankali fattu ta kalli gefenta ta Æ™asa inda macijin nan ke nannaÉ—e ya fasa kansa yana kallon baffa.tace “baffa wannan ne ya taimakeni, kuma shine macijin daya hukunta su jauro “ta faÉ—a tana haska macijin da tocilan.

Da sauri baffa yaja baya yana faÉ—in”subhanalla fattu wannan ai MACIJINE ,meye haÉ—inki dashi,matsa daga gareshi maza karya cutar dake” baffa ya faÉ—a cikin tsoro yana mai kamo hannun Fattu.

“Baffa ka kwantar da hankalinka ,ba abinda zai min ,domin mun jima tare dashi,zauna baffa in baka labarin haÉ—uwata dashi ,sannan baffa macijin nan yana cikin matsala ,dan da alama anyi amfani dashi wajen yiwa wani asiri.

Zama baffa yayi ahankali kan sallarsa ,idonsa akan macijin nan ,daya matso kusa da fattu wacce ke zaune kusa da baffanta,kallon ikon Allah baffa keyi, yadda macijin nan yayi kane-kane akan cinyar  fattunsa ya waniyi lub kamar jariri akan cinyar mahaifiyarsa.

Kallon fattu baffa yayi ,yaga ko ajikinta saima hannu data É—ora akan bayan macijin tana shafawa.

“Ina jinki fattu faÉ—a min komai dan hankalinta ya kwanta”

Nan fattu ta fara bashi labari tun daga farko har kawo yanzu.

Sannan ta É—ora da cewa “baffa dan Allah mu taimaki wannan macijin dan wllh yana cikin matsala ,bakaga yadda ya koma ba lokacin dana ke masa karatu,mu cire masa wannan masifar dake jikinsa”ta faÉ—a tana nunawa baffa waÉ—annan layun dake wuyan macijin.

Cike da mamaki da al’ajabi baffa ke kallon macijin ,wanda ya Æ™ara kafewa jikin fattu yana kallon baffa da kuma fattu.baffa yace “haÆ™ika akwai wani É“oyayyen al’amari dangane da wannan macijin ,kuma in sha Allah zamu taimaka masa iyakar Æ™arfin mu,tun kafin mai gari ya farfaÉ—o ya É—auki matakin kashe macijin nan ,yanzu kije kiyi alwala ki dawo,dan  mu fara aiki akansa.

Cike da É—oki fattu ta amsa da” to baffa na ina godiya agareta sosai”sannan ta ajiye macijin gefen baffa tace “mai taimako ai kasan baffana ko?to katsaya agurinsa yan zu zan dawo kaji”ta faÉ—a cikin murmushi tana shafa bayansa.

Kallo ta kawai yayi kafin ya kwantar da kansa ajikin gangar jikinsa dake nannaÉ—e.

Bayan fattu tayi alwala ta dawo dakin ne ta gabatar da sallolin dake kanta ,sannan tayi addu’ar samun nasara akan ceton macijin nan ta shafa.sanna ta juyo gurin baffa wanda ke ta tofa addu’a cikin wata Æ™warya ,zama ta gyara tana mai kallon baffa da jiran ya kammala addu’ar sa.

Shikuwa macijin nan yana ganin fattu ta zauna ya silalo ya dawo kan cinyarta ya kwanta,gaba É—aya jikinsa asanyaye yake,kamar wanda yake tsoron faruwar wani abu.kallonsa fattu tayi tace “mai taimako ba abinda zai sameka ka kwantar da hankalinka ,in Sha Allahu zamu cire maka duk wani sihiri da akayi amfani dakai wajen yinsa”ta faÉ—a tana mai shafa lallausan san jikinsa mai santsi.

MiÆ™a mata kwaryar nan baffa yayi yace karÉ“i wannan fattu ki yayyafar masa ajikinsa ,kinayi kina karanta ayatul kursiyyu da falaÆ™i da nasi, duk abinda zaki gani karki tsorata kinji ?”baffa ya faÉ—a yana mika mata kwaryar,dan shikam ya gama fahimtar abubuwa da dama aka. Macijin nan.

Karɓa fattu tayi cikin nutsuwa ta fara karatun tana kuma shafa masa ruwan rubutun nan ajikinsa.

Ikon Allah,ai da fara shafa masa ruwan nan ajikinsa ya fara wani irin motsi da jijjiga ,yana murÉ—ewa ,baffa kuma saiya ci gaba da addu’a yana tofa masa.

Ahankali hannun Fattu ya kai kan waɗaɗan na layin dake wuyan macijin nan,aikuwa damƙarsu tayi da Bismillah ta fizge da ƙarfin gaske.

Wata irin Æ™ara da guguwa ne suka turnike dakin gaba É—aya baka iya ganin komai sai duhu…..

Masu karatu mutara gaba dan jin ya zata kaya.

Takuce dai Mrs babi💘💘

Back to top button