Uncategorized

Maciji Ne Page 67-68 Hausa Novel

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 67/68

_______________Da sauri ammi ta taso cikin tashin hankali da fargaba,dan kuwa tabbas tasan wani yaji me take cewa. 

Fattu kuwa tsabar ruɗewa da shiga tashin hankali tama rasa ina zata dosa,tsoro ya cika mata zuciya ganin ammi ta nufo inda take ,saidai cikin wannan yanayin ne taji an fizgeta da mugun ƙarfi anyi waje da ita.nan take tsoronta ya kara rubanya.buda baki tayi da nufin kurma ihu ,dan atunaninta masu kashe tan ne suka kamata.saidai gam!aka rufe mata baki,bata yadda zatayi ihu.kuma cikin wani irin sauri mai kama da gudu akayi waje da ita,ta wata hanya da bata nan ta shigo ba.

Ammi kuwa tayi iyakar dubanta ,amma bata ga kowa ba,kuma tabbas tasan anshigo cikin dakin nan,to waye?dan duk ta kora yan aiki can farfajiyar gidan dan tasami damar yin wayarta.

Ko dai Adeeb ne?kai bashi bane ,dan kuwa Adeeb baya zuwa gareta ba tare da yayi sallama ba.toko nanny ce ?kai idan nanny ce zan iya cimma ta kafin ta gudu,wai waye wannan yake son shiga rayuwata ne?waye yake son bakuntar lahira kwana kusa?na rantse da Allah idan na gano ko waye saina hukuntashi, hukunci mai tsanani.yanzu dole mu sake sabon tsari dan wannan kam ya rika ya lalace”ammi ta fada cikin zafin zuciya da kunar rai.

Download>>> The Governor Wife Book 3 Complete Document

Tana nan tsaye Zulaihat ta shigo dakin ba ko sallama,kawai ammi sai ganin mutum tayi bukut ya shigo cikin falon.guri ta nema ta zauna tare da ƙurawa ammi ido.

Harara ammi ta Banka mata tana tunanin koma dai Zulaihat É—in ce ta shigo dazu da tasan Zulaihat ba hankali gareta ba?

“Ke Zulaihat kece kika shigomin daki dazu kina Min labe?”ammi ta fada cikin haÉ—e fuska.

Wani shegen kallon Zulaihat ke jifan ammi dashi,kafin ta fara magana “lallai ma ammi har kina tunanin akwai wanda zan zauna inayiwa labe?to me zan labe naji,bayan duk wani tuggun da ake Æ™ullawa ina sane dashi,me kuma za’a boyemin ?kinsan Ni bana munafurci kai tsaye nake Abunda naga dama “Zulaihat ta faÉ—a cikin rashin kunya tana wani juya ido.

Kallonta ammi tayi cikin tsantsar É“acin rai da tsanar halayen ta na rashin kunya kafin tace ” yanzu kina Min wannan gatsalin kike son na aura miki Dana?to wllh gara ki nutsu Dan bazan yarda ki auri Adeeb da wannan shegen halin naki ba,domin shirme zakiyi tayi mana,idan mun saki aiki”ammi ta fada cikin faÉ—a -fada.

Wata irin dariya Zulaihat tayi tana kallon ammi kafin tace “Kinga ammi ki daina min tsawa keba uwata bace,ko iyayena lallaÉ“ani suke ,kuma da kike cewa zan bata muku aiki,ku atunaninku idan anyi auren biye muku zanyi in cutar da abin sona,?wllh garama ku nutsu daga ke har daddy na Dan kuwa rungumar mijina zanyi musha soyayya ,kuma duk wanda yayi yunkurin cutar da shi ,wllh saina kashe mutum,kinsan nima na iya dabancin”Zulaihat ta faÉ—a cikin gadara tana kallon ammi ido cikin ido.

Baki buÉ—e ammi ke kallon Zulaihat,lallai yarinyar nan ta wuce yadda suke tunani,Gara ta lallabata,karta jika mata aiki,dan haka cikin dan murmushin yake ammi tace “kai Æ´ata dadina dake baki san wasa ba,yanzu saiki maida abu gaske,ki kwantar da hankalinki,kinsan nima bazan taÉ“a bari a cutar min da Adeeb ba, dama nayi tunanin bakinsu É—aya da mahaifi ki,shiyasa na fadi hakan”ammi ta fada cikin murmushin yaÆ™e tana hararar Zulaihat Æ™asa Æ™asa.

Download>>> Muhibbah Complete Document

“Ato Gara dai mutum ya kula wllh ,dan zan iya komai akan abinda nake so”Zulaihat ta faÉ—a tana mai gyara zamanta zuwa kwanciya,tare da lumshe idonta kamar zatayi barci.

“Zanyi makaganinki daga ke har uban Maki shegiya”ammi ta fada cikin zuciyarta,tana shigewa daki,cike da tunanin mafita.

Ba’a dire fattu  a ko ina ba, sai cikin wani daki mai dan duhu, wanda kana iya ganin mutum ,amma bazakaga fuskarsa kai tsaye ba.

Koda aka direta sam ba’asakar mata baki ba.

Fattu kuwa banda rawa ba abinda jikinta keyi,sai ƙoƙarin cire hannun mutumin take daga bakinta, ammata kasa .

Cikin nutsuwa da kwantar da hankali ya fara magana “ki nutsu ,niba cutar dake zanyi ba,koda na bude miki baki to karkayi ihu “

Cikin hanzari fattu ke jinjina kanta idonta yayi zuru zuru ,burinta kawai tajita free.

Ahankali ya dannan makunnar dake gefensa,nan take dakin yayi haske ta yadda kana iya ganin komai.

Da sauri fattu ta daga idanunta tana kallon mutumin,

“Hamma tareeÆ™”ta fada cikin rawar murya,”ka bani tsoro Hamma tareeÆ™,meke faruwa cikin gidan nan,wacece ammi ?meye alaÆ™arta da hammana?fattu ta faÉ—a cikin muryar kuka tana kallon tareeÆ™.

Shima kallonta yake zuciyarsa na masa zafi ,yayi fatan ace Adeeb da kansa yaji wannan maganar ba wani ne yaji ba.

“Ki kwantar da hankali ki fateema,da sannu zaki fahimci komai “

Ya fada tare da É—auko wayarsa yayi kira.

“Ummee kuzo ina nan cikin dakin baya”haka kawai ya faÉ—a ya kashe wayar.

Kallonsa fattu keyi jikinta har lokacin rawa yake ,tana cikin shock da zallar mamaki,kujera tareeÆ™ ya nuna mata tare da cewa”ki zauna anan fateema ” jiki ba kwari fattu tabi bango ta zauna aÆ™asa ba tare da ta hau kan kujerar da tareeÆ™ ke nuna mata ba.zallar mamakin ammi da al’ajabi ta ke É—awainiya da fattu,yanzu duk zaman da sukayi dama  ammi tasan asalin iyayenta?kuma ita ta sace sarÆ™arta wacce take matsayin shaidar da zata sadata da iyayenta na asali?amma menene ribar ammi nayin hakan?wane amfani zata samu?lallai dole ta sanar da Hamma wannan maganar .

Bude kofar da akayi ke ya katsar mata da tunaninta ,da sauri cikin tsoro ta kalli bakin ƙofar,nanny ce ta shigo ita da amma.

Da sauri fattu ta mike cikin rawar jiki ta Æ™anÆ™ame nanny tare da sakin kuka mai ciwo da radadi,” nanny wai zasu kashe min hammana ,kuma nima zata kasheni ,sannan tace tasan asalin iyayena ,amma bazata bari muhadu dasuba.nanny wacece ammi ?meye alaÆ™arta da hammana,anya kuwa itace ta haifeshi ?fattu ta faÉ—a tana mai dago kanta tare da kallon nanny.

Download>>> Kishin Balbali By JUT Complete Document

Cike da tausayin fattu nanny ta riketa ajikinta Tana mai shafa bayanta ,alamun rarrashi,kafin tace “ki kwantar da hankalinki É—iyata,ba abinda zai sameku da yardar Allah,kuma yau zan sanar dake alakar dake tsakanin Adeeb da amminsa” cewar nanny Tana me zaunar da fattu akan kujera.

Amma kuwa tana tsaye ta kafe fattu da idanu,tabbas hasashenta ya tabbata ,dan kuwa ba tun yau take zargin cewa  fattu yar sarauniya suhaimat bace,dan kuwa tasha ganin irin sarÆ™ar wuyan Fattu atare da iyalin suhaimat,bayan nan sai kayi duba na tsanake zaka gano tsantsar kamar dake tsakanin fattu da suhaimat É—in.aikuwa insha Allahu yau ba sai gobe ba zata sanar da fattu wacece ammi.

Cikin kuka fattu ke kallon nanny kafin tace “Dan Allah nanny ki sanar dani ala’akar dake tsakanin hammana da kuma ammi,ko zuciyarta zata sami salama,ji nake kamar zan mutu,banson wani abu ya sami hammana nanny Ina kaunar hammana fiye da yadda nake son kaina idan wani abu ya sameshi wllh mutuwa zanyi”fattu ta faÉ—a cikin kuka mai ban tausayi.

Hawaye nanny ta goge tana mai kallon fattu kafin tace “In Sha Allahu ba abinda zai sami magajin fada ki kwantar da hankalinki É—iyata.

Hannun fattu amma ta kamo cikin sanyin murya tace “kiyi shiru ,ki kuma kwantar da hankalinki,dan yau zaki san abubuwan da  baki sani ba abaya,dan haka ki adana hawaye ki zai miki amfani nan gaba “cewar amma tana kallon fattu cikin tausayawa.

Share hawayen kuwa fattu tayi tare da kafe nanny da ido,zuciyarta na bugawa kamar ana. Kada ganga.

Ahankali nanny ta fara magana”ammi ba itace asalin wacce ta haifi Adeeb ba,amma itace wacce ta rike shi bayan ta kashe mahaifiyarsa.”

Dararararmmmm gaban fattu ya bada sautin karar da saida ta kusan faduwa tana daga zaune.

Ai Ni kaina saida na tsorata na jefar da wayar nan dan tsoron jin abinda nanny zata faÉ—a .

Muje zuwa masoyan fattu da Adeeb .

Download>>> Tsintacciya Complete Document

Sai mun haÉ—e anjima in Sha Allahu.

Anty mammy ce 

Mrs babi 💘💘

Share and comment fisabilillah.

More comment 

More typing.

Back to top button