Uncategorized

Kara Girman Kugu (Hips)

Bari mu fara da masu neman karin ‘Hips. ’ Ina son a fahimci cewa girman kugu halitta ce, wasu matan har kauce hanya suke yi, su je a saka musu kugun roba.

 Kun ga akwai alamar kauce hanya a nan ke nan.

 Akwai nau’in ababen da mace za ta rika ci, sannu a hankali, kyan diri da halittarta za su kara fitowa, ita ma za ta rika ji ta kara cika, ta yi kyau.

Karanta>>> Hanyoyin Da Zaku Bi Domin Karin Kiba Ba Tare Da Kunsha Maganin ba

Masana a wannan fannin, sun bayar da shawarwarin amfani da

☜ Abarba, 

☜ Ayaba, 

☜ Gwanda,

☜ Kankana

☜ Zuma, 

☜ Madarar ruwa. 

Karanta>>> Amfanin  Zobo Ga Lafiyar Jikinmu 

Karanta>>> Tsumin Matan Aure  Don Inganta Auratayya

Karanta>>> Tasirin Da Tazargade Ke Yi Ga Lafiyar Mata

A kan hada su waje guda, a markada su, har sai sun zama ruwa, sai a dan kara zuma da madara. Bayan wannan, mace za ta rika sha a koda yaushe. Haka kuma kina iya samun Zogale dafaffe, ki hada da ganyen Alayahu, ki zuba Tumatiri da Albasa, ki yi kwadonsu, ki rika ci.

 Haka nan za ki rika yin wadannan kayan lambun da ki ka markada, sai ki rika sha misali da asuba ko da sassafe kafin ki fara cin komai.

Karanta>>> Sirrin Gyaran Nono Kashi Na Daya

 Insha Allah za a dace.

Back to top button