Uncategorized

Ka San Lambobin Da Za Ka Danna Ka Duba Jarabawarka Ta JAMB Da Aka Saki Yanzu?

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’in Najeriya (JAMB) ta sanar da sakin sakamakon jarabawar bana 2022 da dalibai suka zana a fadin Tarayyar kasar nan.

Sokoto: Zanga-zanga ta ɓarke kan kamen da ‘yan sanda suka yi bayan kashe Deborah Samuel

 

Shugaban sashen hulda da jama’a na Hukumar JAMB, Fabian Benjamin, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar, kamar yadda TheNation ta ruwaito.

 Ya bayyana wa dalibai da suka zana jarabawar cewa za su iya duba sakamakonsu a wayoyinsu na tarho.

[Sautin Murya] Innalillahi wa’innah alaihi Raju’un kalaman da ta fadi akan fiyayyen hallita

 

A cewarsa, su tura sakon akwatin SMS ‘UTMERESULT zuwa 55019 a wayar da aka musu amfani wajen don duba sakamakon UTME, abin da kowane dalibi ke bukatan yi shi ne tura UTMERESULT zuwa 55019 da lambar wayar da aka yi amfani wajen rijista, za a turo musu sakamakon.

 Wannan ita ce hanya daya tilo da aka samar don duba sakamakon a yanzu don wasu dalilai.

Back to top button