Uncategorized

Inayah By Mamuhgee Complete Novel

INAYAH

        (Riba Biyu)

Mamuhgee

1

Please masu daukamun Sunayen books da Labarai suna sauyawa suyi nasu lamarin ina ganinku dan Allah ku daina ba kyau, kuma masu copying nagani allah ya kyauta ngd duk cikin Qaunace allah yaqaro kauna🥰

BismillahirRahmanirRaheem

Tasowa tayi ahankali tana takowa zuwa tsakar gidansu datake jiyo maganar mahaifiyarta da yayyunta maza tareda kishiyar mahaifiyartata suna magana duk a jujjuye sbd hankalinsa daya tashi lokaci daya cikin mummanan yanayi da tashin hankalin mugun labarin dayazo musu yanzu yanzun.

Karanta>>> Gurbin Ido… Na Huguma (Zafafa2022)

Ita kanta hankalinta baa kwance yakeba dama can sbd halinda take ciki na jinyar mijinta dake kwance asibiti Yana jinyar accident dasukai kwana biyu dasuka wuce a hanyarsa ta dawowa daga gurin daurin auren qaninsa dasuke uwa daya uba daya,

Kaman a fizge kunnuwanta suka jiyo mata abinda babban yayanta Umar ke fada saidai Sam takasa fahimtar abinda yafada din zahirance Dan haka tana buqatan jinsa da kyau,

Ta qaraso jikin kofar ta yaye labule ta fito tana kallonsu daya bayan daya fararen idanuwanta dasuka jima da shigewa ciki ciki sbd damuwar datake ciki kwanakin,

Suma ita suke kallo Kaman yanda take binsu da kallo kowannensu fuskarsa cike dauke da alhini dakuma tausayinta Dan kuwa Rashin miji a irin shekarunta abin tausayi 

Ga Kuma ‘da da ciki dake jikinta.

Kallon mahaifiyarta tayi taga yanda tayi qasa da Kai cikin yanayi na hawayen dasuke Neman saukar mata takasa kallon Yar Tata 

Dan haka ta kalli kishiyar mahaifiyarta kai tsaye tace”

Inna Menene duk kukai wani iri haka?

Lafiya kuwa?

Wani abin yakuma faruwa ne?

Maida kallonta tayi kan yayyunta dake tsaye suna kallonta tace”

Yaya Umar,Yaya kabiru?

Lafiya duk kukai shiru haka?

Jikin Abban Abdul ya tashi ne?

Ajiyar zuciya Yaya kabirun ya sauke tareda gyara tsayuwarsa ya kalleta da Dan alhininsa irin na maza masu taurin zuciya Kai tsaye yace”

Khadija bayan barowarki asibiti yanzu Allah yayiwa Salisu cikawa……..

Bai qarasa ba ta waiwayo gefensa tana kallonsa cikeda zallan mamaki da faduwar gaba muryarta na gwamutsuwa tace”

Yanzu fa na Barosa Yana barci,

Wanka fa kawai zanyi nakoma asibitin shine zaace ya rasu????

Yanzu yanzu fa?

Da sauri innar ta riqota cikin tausayawa tace”

Hadiza karkiyiwa ubangijin haka,

Tawakkali zakiyi tunda kinsan dai baa wasan mutuwa…

Idonta na sauya zuwa ja da hawayen dake kokarin cikowa saidai taurin zuciyarta ya hanasu fitowa 

ta katse innar da cewa”

Inna bacci nabarosa yanayi fa,

Yaji sauki sosai yau,

Rasuwa fa akace,

Mutuwa fa kenan, ya tafi ba dawowa har abada,

Ta Yaya zanyi…….

Cikin Dan daga murya Yaya kabirun yace”

Ke Khadija Menene hakan?

Rasuwa fa akace Miki salisun yayi,

Ki nutsu ki fahimci ita rasuwa babu ruwanta da yanzu yanzun dakike fada,

Kiyi gaggawar bude hankalinki ki fahimci abinda yafaru dake,

Salisu ya rasu bazai taba tashiba……

Bakinsa take kalla kanta na juyawa 

Zuciyarta na harbawa da mugun qarfi Kaman zata faso kirjinta,

Mamarta ta kalla idanuwanta na qafewa taga alamar gskiyar zancensa akan fuskan mamar,

Ta waiwaya ta kalli Yaya kabiru Shima hakan tagani.

Wani busasshen yawu ta hadiye wanda har yankan maqoshinta yake

Ta juya kai tsaye Takoma dakin mama ta dauki doguwar hijabinta data cire bayan shigowarta gidan ta zira ko waya da kudin adaidaita Bata daukaba ta fito ta zira slippers din mamarta daya Da nata takalmun daya batareda ta luraba ta nufi kofa tana jefa ka kawai dan bata cikin hayyacin kallon gaban nata

asibitin take buqatan isa kawai.

Inna ce tayi saurin janyo nata hijabin tabi bayanta tana Kiran sunanta,

Mamarta kuwa kallon Yaya Umar tayi tana cewa”

Bisu kabasu kudin adaidata ban Saka ran kowannensu ya daukaba.

Juyawa yayi ya bisu

A titi yayi saurin taddasu ya ciro 1000 ya miqawa Inna Yana cewa”

Ga kudin adaidata Inna

Ki lura da ita Inna kartaje asibiti tayita wainnan maganganun 

Tawakkali akeyi kifada mata Inna.

Da sauri innar ta qarasa gurin hadizar daketa zuba sauri tana tafiya ta riqota ta riqe hannunta gam tana kokarin Kiran sunanta saiga adaidata gabansu ba Bata lokaci suka fada ciki 

innarce tafada masa asibitin da zasu

Khadijan kuwa Banda rawa babu abinda qafafunta da hannuwanta keyi.

Isarsu asibitin ko Gama tsayuwa baiyiba Khadija ta sauka tareda wucewa da sauri ta nufi hanyar Emergency ward da har lokacin Salisu anan yake.,

Tun daga nesa Yan uwan Salisu din maza da mata suka hangota tana tahowa a gigice ko ganin gabanta batayi 

Hankalinsu yakuma tashi da tsananin tausayinta dan haka da yawansu suka qara fashewa da sabon kukan Rashin Dan uwansu.

Tana qarasowa da kallo tabisu daya baya daya taga yanda mahaifiyar salisun ke rusa kuka take taji Rabin jikinta na neman mutuwa ta qarasa dakin tashige da gudu ta nufi gadonsa da gawarsa kawai ta tadda a rufe da zanin gadon data zo masa dashi yau da safen.

Tsawonsa ta kalla tareda hannuwansa da aka miqar,

Kasa gasgatawa tayi Saida takai hannu ta yaye zanin tayi arba da kyakkawar fuskarsa ta asalin fulanin Yola….

Mummanan bugawa zuciyarta tayi ba tsammani idonta yarufe tana kokarin zubewa Inna tayi saurin tarota tana Kiran sunanta Amma Sam batajinta sai neman somewa takeyi.

Da sauri hajiyarsu salisun ta qaraso tana cewa”

Ku koma gida da ita karta shiga wani Mummanan halin ga juna biyu a jikinta.

Qwacewa takeson yi Dan Bata tunanin zata bar gawar salisun ta tafi koina Amma batada qarfin motsawa bare magana Dan bakinta take ya manne Kaman an Saka mata glue.

Karanta>>> Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)

Tana kallon gawar mijinta Salisu aka jata aka fice da ita har waje aka kuma sakata napep tareda Inna da qanwar salisun suka nufi can gidan iyayen salisun.

Suna isa ko tsakar gidan Bata qarasa shigaba ta yanke jiki ta fadi jini nabin qafafunta.

Hankali tashe sukai kanta tareda ciccibarta zuwa dakin hajiyarsu salisun Inna na Kiran sunanta hankali tashe.

Jini sosai take zubarwa Wanda ya tabbar musu da cikin zubewa ne yayi babu tantama Dan haka basuyi wani yunqurin maidata asibiti ba haka Inna da dattijuwar gidan qanwar mahaifinsu suka taimaka mata gurin ganin jinin yagama zuba ta Dan gyara.

Kururuwar koke koken da gidan ya dauka ne ya tabbatar musu da isowar gawar Salisu gida

Tana jin hakan ta rintse idonta cikin tsananin azaba sauran abin dake cikin nata ya qarasa zubowa sai alokacin wani irin gunjin kuka Mai tafe da radadin zuciya ya kufce mata.

Inna dake kanta ta qara matsowa tana dafata cikin tausayawa jin irin girman kukan datake,

Kuka takeyi sosai zuciyarta na radadin Rashin mijinta uban ‘danta dakuma wannan cikin daya qwallafa ransa akansa,

Ashe tareda cikin zasu bar duniya Rana daya shiyasa Allah ya saka masa tsananin kaunar cikin abokin tafiyarsa ne kenan.

Bata damu da yanayin datake ciki ba 

Haka ta dafa ta miqe tsaye tareda qarasawa tsakiyar bayin dakin hajiyar ta wanke jikinta daqyar sbd tsananin rawar da hannuwanta da qafafunta keyi.

Fitowa tayi Kai tsaye ta karba zanin da inna ke miqo mata ta daura wani irin tsananin jiri da ciwon mara Mai tsananin gaske Yana nukurkusarta Amma taqi yarda tazauna Kai tsaye ta fito tsakar gidan sanyeda hijabinta tanajin yanda tako ina gidan ke amsa amon kukan Yan uwan Salisu.

Gawarsa dake shimfide a dakin da zaai masa wanka ta nufa ta zube gabansa tafara rero wani irin gunjin kuka tana Kiran sunansa.

Duk yanda akaso janyeta kasawa akai sbd kuka takeyi sosai zuciyarta na tsananin qunar Rashin mijinta datake tsananin so da kauna yau gashi ya tafi yabarta cikin duniyar da kowa babu abinda yasani sai kansa,

Ina zata da ‘danta Abdul Wanda tasan babu Wanda zai daki kirji a cikin danginta Kona salisun ya tallafi rayuwarsu.

Lokacinda za ai masa wanka da sirita aka samu aka janyeta daga dakin musamman da itama wani irin gagarumin zazzabi ya rufeta lokaci daya dakuma sabon jinin daya Kuma balle mata sai alokacinma kowa ya San da Bari tayi.

Baa kaita asibiti ba a dakinta dake gidan aka kwantar da ita kasancewar a gidan suke zaune tareda iyayen salisun tunda dagasu har iyayen ba masu hali ban Dan hakan nema sukeda daki daya tal da Dan qaramin palo da bandaki acikin palon,

Tana daki ana fama da ita har aka tafi da gawar makwancinsa,

Iya fatu aka kirawo makociyarsu Mai karban haihuwa ita tazo ta duba hadizan ta tabbar musu da cikin yagama zubewa 

Nan aka shiga wani jimamin aka fara kulawa da hadizan.

Sbd yanayin jikinta dakuma zaman gaisuwar da ake gidan yasa dole Inna ta zauna tareda ita tadawo da kwana gidan tunda maman hadizan bazatazo ta zauna ba.

Sosai take fama da jinyar kanta bayan kwana biyu da rasuwar sbd takasa daina kukan mutuwar Salisu,

Salisu mijine ma gari Kuma uba nagari hakama ‘da na gari gun iyayensa.

Cikin kwana biyu duk tabi ta yamutse da tsananin damuwa dakuma ciwo dake damunta na tsananin ciwon mara na barin datai.

Karanta>>> Babu So… By Billyn Abdul (Zafafa2022)

Angama zaman gaisuwar har anyi sati biyu babu wani Abu daya sauya daga gareta saima sabon ciwon damuwa daya kamata Sam takasa fita daga halin damuwar Rashin mijinta,

Inna na tareda ita har lokacin Kuma dai ita zata zauna da itan har tsawon watannin dazata Gama takabarta kafin sukoma gida tare.

Abdul Yana gurin mama dama tun tana zaman jinyar abbansa asibitin kafin rasuwar tasa Dan haka kullum a daki suke wuni daga ita sai Inna,

Abincinta Wanda yake kicin dinsu tun Wanda salisun ya siya shi Inna ke dafa musu yana qarewa babu Wanda yakawo musu wani saidai aka ringa Basu daga cikin gidan Idan an dafa,

Wanda ake basun baya wani isarsu itada innar dan haka so da yawa innar Idan taci na safe yafe mata na ranar take ita taci,

Itakuma Idan anbasu na daren saitace ta koshi saita barwa innar taci.

Tun daga Nan yanayin yafara kulle musu 

Da innar dai taga daga ita har hadizan sunfara dogayen wuyan yunwa Kamar Yan gudun hijira dole taje gida ta sanarwa mamar hadizan sukai shawara akaiwa Umar da kabiru magana akan su taimakawa hadizan da abinci

shine suka Dan fara taimakawar duk bayan kwana biyu suna Bata dubu daddaya ko dari Biyar Biyar.

Tun suna Bata tana samun na siyan abinci da Kamar su sabulun wanki hardai Suma ana Jan lokaci suka daina sbd Suma da nauyin nasu iyalan akansu dan haka suka koma Yar gidan jiya.

Watan salisun uku da satittika da rasuwa gabaki daya rayuwarta ta juya mata upside down sbd hajiyarsa itama ta kanta takeyi Dan dama shine kawai Mai tausayi da tallafa mata acikin yayanta shiyasa itama bazata iya daukan nauyin hadizarba Dan haka kowa tasa ta fisshesa akeyi a gidan.

Hadizar ta rame ta hargitse ta sauya kamanni sosai bayan dogon wuya da dogon hanci sai ido dasuka fito kaman me Neman allura a duhu haka Takoma dama ita Inna sun saba da talaucinsu Dan haka masifar quncin Rashin ba wani damunta tayiba Kaman dai yanda tausayin rayuwar hadizan tafi damunta sbd tasan wani sabon gararin ne zata tadda gida koda tagama zaman takabar sunkoma.

Ta bangare daya tunda tayi barin cikinta lokacin rasuwar Salisu har yanzu takasa ganewa lafiyaarta sbd ciwon mararta yi yakeyi Yana tasan mata,

Wani lokacin idan yatasar mata Kaman zata rasa ranta haka take fama dashi Amma Bata taba zuwa asibiti ba Dan babu hali,

Ko innar dasuke tare Bata sanarwaba Dan karta daga mata hankali bayan daga ita har mamarta tada hankali kawai zasuyi basuda wata mafitar.

Cikin wani irin tsanani da matsuwar Rashi da tarin damuwa tagama zaman takabarta suka fara Shirin tattarawarta komawarta gidansu.

Hajiyar Salisu tayi sabon kukan mutuwarsa lokacinda hadizan zata tafi,

Tanajin inama tanada halin cigaba da kulawa da matar salisunta da ‘dansa data riqesu

Amma batada Wannan halin,

Ko Abdul dinma tana tsananin kaunarsa saidai bazata iya riqonsaba shiyasa batamayi maganar karbarsaba,

Da mahaifinsu salisun Shima Yana raye tasan bazai taba barin hadiza da Abdul din su tafi ba.

Ita kanta hadizan ta San cewa Rashin halin ne yasa hajiyar batai yunkurin cewa a bar mata abdul ba Dan tunda salisun ya rasu itama yanzu abincinta neman gagarta yake

Gwara tabarwa hadizar ‘danta tasan duk tsanani zata nema ta kula dashi.

MAMUH

Karanta >>> Sanadin Labarina By Hafsat Rano (Zafafa2022)

GA TSARIN YADDA FARASHIN SU SUKE;

ZAFAFA GUDA BIYAR 1  PAGE 1 NA KOWANNE BOOK A KODA YAUSHE INSHA ALLAH . KAMAR KO WANI YI. FARASHIN NA NAN AKAN NERA DUBU DAYA

ZAFAFA BIYAR

Littafi daya 300

Littafi biyu 400

Littafi uku 500

Littafi hudu 700

Littafi biyar 1k

GURBIN IDO

SAFIYA HUGUMA

SANADIN LABARINA

HAFSAT RANO

INAYAH

MAMUHGEE

FARHATAL QALB

NANA HAFSAT

(Miss Xoxo)

BABU SO

BILLYN ABDUL

ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES!! WANNAN SASHI NE NA BANGAREN YAN ZAFAFA NA MUSANMAN DA KE SON KARANTA SHAFUKAN LITTAFAN ZAFAFAN SAMA DA DAYA. TO KU SHA KURUMIN KU. KUDIN VVIIP NA ZAFAFA NERA DUBU BIYAR NE KACAL NA DUKKANIN BOOKS DIN BIYAR. A KALLA A RANA ZAKU DINGA SAMUN SHAFUKA 10 KOWANNE BOOK SHAFUKA 2 KENAN.

PAY 5K FOR ZAFAFA BIYAR VVIP SUITE SECTION. MAXIMUM OF 10 PAGES DAILY, 2-2 PAGES OF EACH BOOK. MAKING 10 PAGES IN WHOLE. LITERALLY

SANNAN AKWAI TSARIN VVIP NA BOOK DAYA GA MASU RAAYIN VVIP NA BOOK DAYA KO BIYU KO UKU KO HUDU GA KUDIN SU KAMAR HAKA;

BOOKS HUDU 4500

BOOKS UKU: 3500

BOOKS BIYU: 2500

BOOK DAYA: 1500

BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK

4 BOOKS  4500

3 BOOKS : 3500

2 BOOKS : 2500

1 BOOK: 1500

MUNA TALLATA HAJOJIN KU CIKIN FARASHI MAI RAHUSA

TALLA SAMAN SHAFI

DAYA NA BOOK DAYA :1000

TSAKIYA 800

KARSHEN SHAFI 500

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

BANK NAME: ZENITH BANK

ACCOUNT NAME: HAFSAT UMAR KABIR

ACCOUNT NUMBER: 2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA DA SHEDAR A TARE:

09134848107

Back to top button