Uncategorized

Illolin Da Yawan Shan Ruwa Mai Sanyi Yake Yi Ga Lafiyar Jikin Dan Adam.

1. TSAIDA BUGUN ZUCIYA:- Bugun zuciya shike gyara dumin jiki da daidaita numfashi, to ruwan sanyi yana sa bugun zuciya ya rika raguwa har takai ga tsayawa.

2. LALATA TSARIN KAYAN CIKI:- Shan ruwa mai sanyi yana tattare hanji guri daya, sai ya sanya abinci yaki narkewa da wuri, hakan kan jawo matsalar hanji (ulcer kenan), ko kuma tashin zuciya.

3. Masu shan ruwan sanyi:- Za su rika  yawan zubda miyau/yawu da kaki, ko tashin zuciya, ko saurin kullewar ciki.

Karanta>>> Yadda Zaku Kula Da Fatar Jikinku A Lokacin Sanyin Nan

Karanta>>> Hanyoyin Da Zaku Bi Domin Karin Kiba Ba Tare Da Kunsha Maganin ba

4. DAUKE KARFIN JIKI:- Duk da cewa shan ruwan sanyi kan sa mutum yaji dadi, amma a hankali yana dauke masa karfin jiki, saboda yayin da ruwan mai sanyi ya shiga jikinsa, dole sai na’urorin jikin sunyi kokarinsu na ganin sun maida wannan ruwan ya daidaita da dumin jikin, hakan yanasa suyi rauni sakamakon kokarin da suke yana wuce haddi. 

Ko kun lura duk sanda kuka sha ruwan sanyi sai kunji duk jikinku sanyin ya ratsa kaman farkon zazzabi, a hankali kuma sai kuji ya daina.?

5. CIWON MAKOGWARO DA DAKUSHEWAR MURYA:- Yawan amfani da ruwan sanyi yana lalata jijiyoyin makogwaro, har sukai ga basa amfaninsu.

 Idan ya kai shekaru arba’in sai ya fara fama da ciwon makogwaro da dakushewar murya, ko muryar ta fashe.

6. CIWON HANTA DA KODA:- Dukansu suna bukatar wadataccen ruwa a jikinsu, don haka yayin da mutum ya zama yana amfani da ruwa mai sanyi, zai zamo su kuma suna cutuwa ta yanda aikinsu zai fara kasa, in haka ta samu mutum ya shiga matsala.

Danna Rubutun Domin Karanta Abubuwan Dake Haifar Da Tusar Gaba

7. BUSAR DA RUWAN JIKI:- Akwai na’urori a jikin dan Adam da aikinsu shine sadar da ruwa ko ina a jikin mutum, ta yanda ko ina na jikinsa zai samu damar motsawa cikin nishadi.

To wadannan naurorin sukan yi sanyi sakamakon ruwan sanyi, sai su zama so weak.

8.. MATSALAR MA’AURATA:- Wannan abune tabbatacce harga likitocin zamani cewa: shan ruwan sanyi yana raunata mazantakar namiji, yana kuma busar da mace.

9. Shan ruwan sanyi:- In  mahaifar mace  nada rauni yana iya hana ta haihuwa. 

10. Shan ruwan sanyi:- Yana tsinka maniyyin namiji ya zama yana saurin inzali, ko kuma ya rage masa kuzari. 

Karanta>>> Hanyoyin Da Zaku Bi Domin Karin Kiba Ba Tare Da Kunsha Maganin ba

11. Shan ruwan sanyi:- Yana dauke ni’imar jiki mata da miji  su zamo basa gamsuwa da junansu.

12. BASIR:- Shan ruwan sanyi tattare hanji yake, hakan yana kawo mutum ya kasa bayan gida, sai basir/ zafi (dankanoma) ya kama shi.

13. Ciwon 6arin kai:- Wanda ke shan ruwan sanyi, gefen kansa zai rika ciwo, hakan  yana kashe jijiyoyin ido a daina gani sosai.

Jama’a Ayi Hattara Jama’a Sannan A Tura Wa ‘Yan Uwa Su Amfana.

Back to top button