Uncategorized

IDON NAIRA Chapter 1 Hausa Novel Document – Aihausanovels

IDON NAIRA Hausa Novel Written By MAMUHGEE

Posted by AiHausa Novel
Price 400
Category Hausa Ebooks
Uploaded On 26 Jan, 2023
Upload Time 8:29 pm
Hits 218 Views
Author

Mamuhgee

Writer Group

Nil

Novel Genre

Comment No Comments

IDON NAIRA Hausa Novel Written By Mamuhgee

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_

*_A RUBUCE TAKE !!!_*
        (K’addarata)

      *Huguma*
Arewabooks: huguma

Free page 01

     Babban falo ne,wanda yake malale da marron din carfet mai taushi da kuma saitin kujeru kalar labulen wadanda suka yiwa falon qawanya,a tsare falon yake,ta yadda duban farko kuma kai tsaye ba zaka dauka falon tsohuwa bane,saboda ya wadata da kayan alatu na rayuwa bakin gwargwado.

         Daga tsakiyar falon,mamallakiyar falon ce zaune saman carfet din,babbar macace wadda gashinta mai tsaho da kuma santsi ya fara bayyanar da furfura saman sumarta,kana iya hangen hakan sakamakon gocewar daurin dankwalin dake kanta,fara ce sol har yellow takeyi,tsufanta bai boye kyan siffa da take dashi ba,wanda da alamu ta sameshi ne tun daga zamanin quruciya kawo yau,kana kallonta kasan ba cikakkiyar bahaushiya bace,hakanan kammanninta bana fulani bane.

       Daga gabanta kuma wata matar ce da suke diban kamanni da ita,saidai nata shekarun gaba daya ba zasu rufa talatin ba,ita dinma fara ce sol kamar matar dake zaune kusa da ita,wanda kana dubansu zakasan cewa ‘ya da uwa ne,yaro ne saman cinyarta tana shayar dashi,dattijuwar mahaifiyar tata kuma tana daga kayan dake gaban nasu

“Duk da kayan sunyi kyau humaira,amma gaskiya nafison wadanda sukafi wadan nan tsada,Banason siyawa widad kaya masu sauqin kudi,gwara masu dan tsada da inganci” mai da dubanta halimatu tayi ga kayan tana sake qare musu kallo duk kuwa da cewa itace ta siyosu da hannunta,kayan irinsu ta siyawa yaranta,ta siyama widad din irinsu ne a nata zaton shine qarshen abinda zatayi ta burge ummu,saita maida dubanta ga dattijuwar

“Ummu,yanzu duk kyan wadan nan kayan basuyi miki ba?” Kai ta girgiza

“Basuyimin ba,kuma tunda nace basuyimin ba ai sai a canzo ko?,tunda dai kudina na saka zan siya,ba kudin wani bane” baki halima ta tabe tana sanya hannunta guda daya tana tattara kayan gefe,zuciyarta cike fal da bacin rai,akwai maganganu da yawa a ranta,amma tasan bata isa ta fadesu ba,yanzu yanzu rai zai iya baci indai akan widad ne

“Kin karba min kudin a wajen yaayan?”

“Yace sai ya dawo zai bayar na ajiye miki” sake baci ranta yayi,wannan karon ta gaza boyewa

“Uhmmm,Allah sarki,to Allah yasa suna da rabon saka ankon” kallonta ummu tayi ba tare da tace mata komai ba,idan da sabo ta saba da irin wadan nan dabi’un,ta rasa me yasa suka gaza fahimtarta,tana ganin son rai ne kawai da son kai irin na dan adam.

          “Latifa!” Ummu ta waiwaya bayanta inda qofar kitchen dinta yake ta qwala kira,daga ciki aka amsa sannan mamallakiyar sunan ta fito,wankan tarwada ce,mai matsakaicin jiki,a nutse ta qaraso

“Gani ummu”

“Shiga dakina saman pillow akwai purse dita ki daukomin” amsawa tayi da to sannan ta juya.

           Saidai bata ko kai ga isa dakin ba,ihu ya karade gidan cikin wata siririyar murya,ihu ne sosai hade da kuka.

          Da sauri Latifa ta dakata da tafiyar,sannan ta waiwayo tana duban ummu,itama ummun ita take kallo,fuskarta cike da tsoro

“Ummu kamar muryar widad fa” kai ta jinjina da sauri

“Haka nake shirin fada nima”

“Yo wace idan ba ita ba?,kaf gidan nan waye yake wannan tabarar idan ba ita ba?” Dauke dubanta ummu tayi daga kan.haliman zuwa ga ladifa,wadda tuni ta fara nufar qofa

“Yawwa,dubamin ita don Allah latifa”

“Yanzu kuwa” ta amsata tana ficewa daga falon.

          Yaronta halima ta kwantar a gefe sannan ta miqe itama tabi bayan latifan tana qunquni cikin ranta.

          Babbar harabar gida ne wadda ke dauke da interlock shimfide a ko ina,duk da irin girman harabar gidan,jikin kowacce katanga data zagaye gidan dake dauke da sassa sassa guda biyar shukoki ne da.flowers da sukabi bangon gidan suka zame masa ado.

          Daga bakin daya daga cikin sassan gidan wasu daga cikin ma’aikatan gidan ke tsaye,daga inda kake kana iya hangota,yarinya ce da duka duka ba zata wuce shekara goma zuwa sha daya a duniya ba,farace sol,irin farin nan me cakude da surkin jaa,ma’abociyar yalwatacciyar suma me santsi data sauko har zuwa bayanta ta kuma bazu har saman kafadunta saboda tsallen da take faman yi tana kuma dage maroon din doguwar rigar dake jikinta,manyan idanunta cike da hawaye da suke saukowa saman kumatunta wasu na zirara har gefan dogon hancinta da ya gauraye da majina da hawayen

“Babu komai fa widad,na gaya miki na cire shi tun dazu” wata mace dake tsaye a gafe sanye da riga da zani na atamfa ta fada tana qoqarin riqe yarinyar.

         Dai dai lokacin latifa ta qaraso halima na biye da ita

“Meye haka?,me ya faru?” Yayi tambayar tana nufar widad da keta zabga tsalle da kururuwar kuka

“Tana tsaka da barci a falona bayan sun gama guje gujensu,kawai ina kitchen ni da marka na jiyo ihunta,da nazo sai tace wai kyankyaso ne ya shige mata riga,dana duba sai naga ashe qwaro ne dan qarami,na daukeshi aka fitar dashi,amma tace kyankyaso ne,nayi duban duniya ban ganshi ba” tsaki halima taja

“Iskancin banza da wofi ne da zallar tabara data yi mata yawa,wuce mu tafi kafin na tsitstsinka miki mari” ta fada cikin tsawa

“A’ah dakata a duba matan halima” latifa ta fada tana tsugunna wa gaban widad din,ta dage rigar tata da kyau sannan tace

“Kalli ki gani,babu komai a jikinki” cikin tsoro dubi fararen qafafuwanta,ganin ba komai din kamar yadda latifa ta fada,saita gyada kanta,saidai kuma har yanzu batabar kukan da take ba.

          A gaba halima ta sanyata tana ta faman sababi m,wannan ya sake tunzura kukan widad din,har suka isa qofar falon ummu.

         “lafiya ko?,me akayi mata?” Ummu ta fada idanuwanta da hankalinta gaba daya yana kan widad,tambayar data yi mata sai ya zamana kamar an tunzura ta,cikin sassarfa ta shige falon,tana kuma isa ta fada jikin ummun tana sake sakin kukan.

“Me kuwa akayi mata banda tsoron banza da wofi da take dashi,wallahi ummu sakalcin yarinyar nan ya fara yawa,haba” halimatu ta fada cikin huci tana neman saman kujera ta zauna kamar zata fashe

“Kin taba gani haka kawai mutum yana kuka ne?,ke me yasa kike haka?”ummu ta fada tana jifanta da harara

“Kyankyaso ne ummu yabi ta jikinta,an cireshi amma ta dauka bai fita ba” latifa data shigo ta sake yima ummu bayani tana dosar kitchen.

          Waiwayawa ummun tayi tana jifar halimatu da harara

“To kinji,amma shine zakice kukan banza takeyi?,bayan kinsan widad da tsoro,kinsan kuma halittarta ce a haka?”

“Da sakalci wallahi ummu,haba don Allah,ko nabiha da take qanwarta bata wannan abun sai ita shafaffa da mai”

“To anji,saiki rufawa mutane baki hakanan” ummun ta fada tana maida hankalinta ga widad dake kwance saman cinyarta tana share hawaye

“Sannu kinci abinci?” Kai ta girgiza alamun a’ah

“Anty madina ta zuba mana,sai nayi bacci”

“Shikenan,tashi maza kije latifa ta zuba miki,idan miyar tayi miki yaji ta zuba miki wadda takeyi yanzu tunda naji kamar ta soyu,ki biya bandaki ki wanke fuskarki,bazan sake bari kije ko ina cikin gidan nan ki kwanta bama bare irin haka ta sake faruwa” miqewa widad tayi a hankali ta soma barin wajen,sai data shiga dakin ummun ta wanke fuskarta kamar yadda tace matan,ta cire rigar jikinta saboda jiqewa da tayi ta saka wata,riga da zani ne,da qyar ta iya daura zanin saboda rashin iyawa da rashin sabo sannan ta wuce kitchen wajen latifa.

         “Halimatu,banason irin wannan dabi’ar nasha gaya miki,idan baku tausayawa widad ba bai kamata ku sata a gaba ba”

“Nifa ba a gaba na sakata ba ummu,sakalcinta yayi yawa ne,fisabilillahi duk cikin gidan nan wace ake nunawa gatan da kike nuna mata?,ai ba ita kadai bace jika a gidan,sannan ma girma takeyi fa,nan da shekara uku tsaf xa’a iya tayar da batun aurenta,niba tsangwamarta nake ba,so nake naga ta gyara” ido ummu tadan zuba mata na wani lokaci kafin ta janye dubanta daga gareta,ta fuskanci ba zata gane ba

“Allah ya kyauta” kawai ta sake cewa,tasa hannu ta janyo purse din da latifa ta ajjiye mata,ta bude ta fidda ‘yan dubu dubu ta lissafa ta miqa mata

“Gashi,ki lissafa ki cire kudin da zaa qara na kayan da zaki canzo din,ragowar ki siya ma yaran sauran abinda ya rage” hannu biyu tasa ta karba tayi mata godiya,duk daba haka taso ba,ta rasa me yasa ummun take kasa dai daita widad da sauran jikokinta.

        Sanda ta shiga kitchen zamanta tayi wajen latifa bayan ta zuba mata abinci,tana ci suna hira,sai ka rantse da Allah ba ita ta gama sambada ihun ganin kyankyaso ba,tana ta zubawa latifa surutu ita kuma tana biye da ita,wannan yasa akwai shaquwa sosai tsakaninsu,kusan tana daya daga cikin wadanda basuson kukanta cikin gidan.

         Sai data cinye tas sannan ta ajema latifa kwanon ta sauka daga kujerar data hau kai ta zauna

“Kizo ki wanke hannunki mana kafin ki fita” latifa ta waiwaya tana ma widad magana,wadda tuni ta kusa qofa tana sude hannu

“Ina zuwa,zan wanke a wajen anty madina,na manta na baro alawar madarata dazu a can,Allah yasa su faruqu basu shanyemin ba” bata ko sake tsaiwa sauraron latifa ba tayi qofa abunta.

         Su uku ne yanzun zaune a falon sabanin dazu,anty halimatu,ummu da kuma wani baqon daban.

KARANTA ZAFAFA 2023

*IDON NERA By Mamuh ghee*

          Matashin saurayine fari ne shima kamar yadda na lura da kusan mafi yawa na launin fatar jama’ar gidan farare ne,yana da sassalkan gashi mai santsi gami da duhu,kamar yadda sumar  qabilar larabawa ko buzaye suke da ita,sanye yake da shadda dinkin zamani da ya zauna masa sosai a jikinsa,kanshi babu hula,hannunsa riqe da wayarsa yana dannawa,gefe daya kuma suna hira da ummu da anty halimatu.

         Turus widad tayi tana kallonsa,ta tsareshi da idanu duk da babu wanda ya ankara da fitowarta a cikinsu,dubansa take tana jin wani haushi yana cikata,tsaki taja a hankali don kada su jiyota,sai kuma ta tura baki gaba kamar zata saki kuka.

         ,juyawa tayi kamar zata koma cikin kitchen din,amma kuma saita sauya shawara,saboda tasan indai ta koma din ummu tasan tana can kuma zata kirata ta fito,abinda bata so din kenan,sai ta dawo tana duban bayan kujerar falon,akwai hanya da zata sadata har qofar falon,don haka ta duqa ta fara tafiya a durqushe ta bayan kujerun,gabanta yanata faduwa,fatanta Allah yasa kada ummu ta ganta.

         A hankali ummu ta waiwaya zuwa sashen kujerun,motsi take jiyowa,saita sauke idanunta zuwa qasan kujerun,fararen qafafuwan widad ta hanga,dariya taso subuce mata amma saita danne,ba tare da kowa dake wajen ya ankara da abinda ke faruwa ba tace

“Widad!” Idanunta na kan qofar falon,ba zaka zaci ta ganta ba,cak widad ta tsaya tana zare manyan idanuwanta waje,gabanta yana faduwa,tana jin kamar ta juya ta koma,amma kuma idan tace zata koma din asirinta zai tonu

“Widad,ko bakya jina ne?” Ummu ta sake kiranta tana kallon sashen da alamu suka nuna a nan take a tsaye,saddaqarwa tayi,ta tabbatar ummu ta ganta,don haka sai kawai ta miqe tsaye,fuskarta a daure,ta tattare dan qaramin bakinta ta turoshi gaba,sannan ta fara takowa zuwa inda suke.

        Dukkansu suka bita da kallo,halimatu ta tabe baki tana dauke kanta,haushin widad din yana sake kamata,ummu kuwa girgiza kai kawai tayi,cikun zuciyarta tana cewa

“Allah ya kyauta aikin quruciya”.

          Ta bangarenshi kuwa da kallo ya bita,ya kafeta sosai da idanuwansa,irin kallon da sautari abokansa kan masa dariya,su kuma ce sukam basuga abun kallo ga qwaila kamar widad ba,tun tana tsumman goyonta Allah ya jarabceshi da soyayyarta,har yau kwanan gobe kuma babu abinda ya canza a zuciyarsa game da ita,saidai ita din da baiga alamun koda sakewa dashi tattare da ita ba bare akai ga zancan soyayya,soyayyar da yake da yaqinin bata santa bama,batasan kuma mece ce ita ba,shi yake saka ran ta koya daga gareshi,saidai bata sakewa dashi bare ta bashi wannan damar,tako ina bashi da matsala,yasan zaya sameta za’a bashi ita kamar yadda yake muradi,amma kuma babbar matsalar daga gareta ne.

          “Bakiga mutane ba ba zaki gaishesu ba?” Ummu ya fada tana hade fuskarta tsam waje daya,duk yadda takai ga gantanta widad da nuna soyayyarta a gareta,amma bata da sassauci wajen tarbiyya.

          Kamar wadda aka sheqawa mari haka ta waiwaya gareshi

“Yaya mahfood ina yini?” Tattausan murmushi ya saki yana kallonta,kanta babu dankwali kamar yadda ya santa,bata qaunar daura dankwali sam

“Lafiya lau widadun ummu,ya makaranta?” Bata amsa masa ba,saita juya ga ummu tana bata rai

“Gani ummu” ummun na shirin miqewa tsaye tace

“Bani nake nemanki ba” saita miqe a abunta tana riqe da hijabinta a hannu

“Muje ki gyaramin wardrobe dita kafin ki wuce gida” ummu ta fada tana yin gaba.

         Miqewa halimatu tayi ta saba yaronta a kafada tabi bayan ummun tana cewa

“Har yau ita widad din dana koyawa yadda akeyi bata koya din ba kenan?”

“Nidai ba wannan na tambayeki ba,in zakimin kimin,idan kuma fashin baqin naki zakiyi ki barmin kayana,ko intisar tazo sai tayimin” jin ummun ta fara mita saita tsuke bakinta,tabi bayanta kawai din kawai,sai falon ya rage saura su biyu.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!


*_DOGUWAR TAFIYA CE,WADDA KE QUNSHE DA TARIN DARUSSA,TAFIYA CE MAI DAUKE DA WANI IRIN SALON KISHI,GOGAYYA CE DA FAFATAWA TSAKANIN MABANBANTAN MATSAYI BIGIRE GAMI DA MATAKI NA RAYUWA_*

*_Ta fita zurfin karatu_*

*_Ta fita yawan shekaru_*

*_Ta fita wayo dabara da siyasa_*

*_GOYON KAKA CE_*
*_SAKALTACCIYA_*
*_ME QANANUN SHEKARU K’WARAI_*

*AKWAI TAZARA MAI TARIN YAWA A TSAKANINSU,KWATANKWACIN SAMA DA QASA*

*AMMA DUK DA HAKA TA CITA DA YAQI*

*GARIN YAYA?*

*_Kin karanta HANGEN DALA?,to ba shakka wannan tafiyar ta fishi zafi darussa da kuma ilimi a cikinta(in sha Allah)_*

*_ku taho kawai muje,kuyi jumurin bibiyata,kamar yadda aka saba har kullum,babu gaggawa cikin tafiyata_*😄✋🏽

*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*

*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*

Littafi daya—400
Biyu—600
Uku—-800
Hudu—–1k
Biyar din duka—-1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa ‘yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+227 90 16 59 91

Littafi daya—450CFA
biyu—650CFA
uku—-850CFA
hudu—-1050 CFA
Biyar—-1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥

Download

Click the below button to download, pls in case you get trouble trying to download kindly drop a comment.


Download any type of hausa novel which include Hausa Love, Adventure, fiction, Fantasy and other genre Hausa Novel paid and free and read them in confort of your zone at ArewaBooks.Com

Author’s Contact

  • Name : Bilkisu Abdullahi
  • Wattpad Handle : @ Bilyn Abdul
  • Nick Name : Bilyn Abdul
  • Whatsapp Number : 08119237616
  • Nationality : Nigeria
  • Email :
  • Group : Haske Writers Association

The Book is not free

Back to top button