Uncategorized

Hukuncin Abincin Kirsimeti Ga Musulmi Fita Ta Farko

 HUKUNCIN ABINCIN KIRSIMETI

FITA TA 01

Muna farawa da miƙa cikakkiyar godiya ga Allah, muna neman taimakonshi da agajinshi, wanda Allah ya shiryar babu me ɓatar dashi, wanda yaɓata kuma babu wanda ze shiryar dashi.

Tsira da aminci su kara tabbata ga Annabinmu muhammad (s.a.w) da waɗanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka kamar yadda ‘yan uwa sukaga taken wannan lekca asama, to tabbas hakan shine takenta, wanda ita wannan lekca zamuɗanyi tsokacine gwargwadon abinda Allah Ya hore mana danganeda hukuncin halasci ko haramcin cin abincin kirsimeti dakuma abincin mauludi, zamuji hukuncin cinsu awajen musulmi

Aciki suratul Baqara Ayata 168, Allah ta’ala yace:

ﻳَﺎ ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟﻨَّﺎﺱُ ﻛُﻠُﻮﺍ ﻣِﻤَّﺎ ﻓِﻲ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ ﺣَﻠَﺎﻟًﺎ ﻃَﻴِّﺒًﺎ ﻭَﻟَﺎ ﺗَﺘَّﺒِﻌُﻮﺍ ﺧُﻄُﻮَﺍﺕِ ﺍﻟﺸَّﻴْﻄَﺎﻥِ ﺇِﻧَّﻪُ ﻟَﻜُﻢْ ﻋَﺪُﻭٌّ ﻣُﺒِﻴﻦٌ ‏( 168 )

Ma’ana YAKU MUTANE KUCI DUKKAN ABINCIN DA YAKE BAYAN QASA WANDA YAKE HALAS NE KUMA MAI DAƊI.

Malamai suna kafa hujja da wannan ayar wajen tabbatarda cewa asali gameda dukkan wani abinci shine halasci, kuma wannan ayar idan kaduba tafsiran malamai akanta zakuga sunfi rinjayar da magana akan dabbobi waɗanda ake yankawa, to asali gameda duk wani nama halasne walau an yankashi ko ba’a yankaba koda mushene duk asali gameda duk wani abinci shine halas, inkuma har wani yazo yace maka banda iri kaza toh katsareshi kace yabaka aya ko hadisinda Allah ko manzonshi suka haramta wannan abin, kubiyomu cikin lekcar zakuji ƙarin bayani

mma mukoma cikin suratul Aaraf ayata 30-31, Allah ta’ala ya ce:

ﻭَﻛُﻠُﻮﺍ ﻭَﺍﺷْﺮَﺑُﻮﺍ ﻭَﻟَﺎ ﺗُﺴْﺮِﻓُﻮﺍ ﺇِﻧَّﻪُ ﻟَﺎ ﻳُﺤِﺐُّ ﺍﻟْﻤُﺴْﺮِﻓِﻴﻦَ ‏( 31 ‏) ﻗُﻞْ ﻣَﻦْ ﺣَﺮَّﻡَ ﺯِﻳﻨَﺔَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟَّﺘِﻲ ﺃَﺧْﺮَﺝَ ﻟِﻌِﺒَﺎﺩِﻩِ ﻭَﺍﻟﻄَّﻴِّﺒَﺎﺕِ ﻣِﻦَ ﺍﻟﺮِّﺯْﻕِ

...KUCI KUMA KUSHA: KUMA KADA KUYI ƁARNA, LALLAINE SHI ALLAH BAYASON MASU ƁARNA (32) KACE, WANENE YA HARAMTA QAWAR ALLAH, WANDA YAFITAR SABODA BAYINSA, DA MASU DAƊI DAGA ABINCI…

Wannan ayoyin biyu su kansu dalilaine ƙarara akan cewa duk wani abinci aduniya asalinsa halasne matuƙar ba aya ko hadisine suka haramtashiba, wannan shine fassararda Ibn Abbas yaima wannan ayar, kuduba Tafsirin ƙurdubi.

Mukoma suratul Yunusa ayata 59 zuwa 60, inda Allah ta’ala yace:

ﻗُﻞْ ﺃَﺭَﺃَﻳْﺘُﻢْ ﻣَﺎ ﺃَﻧْﺰَﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻟَﻜُﻢْ ﻣِﻦْ ﺭِﺯْﻕٍ ﻓَﺠَﻌَﻠْﺘُﻢْ ﻣِﻨْﻪُ ﺣَﺮَﺍﻣًﺎ ﻭَﺣَﻠَﺎﻟًﺎ ﻗُﻞْ ﺁﻟﻠَّﻪُ ﺃَﺫِﻥَ ﻟَﻜُﻢْ ﺃَﻡْ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺗَﻔْﺘَﺮُﻭﻥَ ‏( 59 ‏) ﻭَﻣَﺎ ﻇَﻦُّ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻳَﻔْﺘَﺮُﻭﻥَ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟْﻜَﺬِﺏَ ﻳَﻮْﻡَ ﺍﻟْﻘِﻴَﺎﻣَﺔِ

Ma’ana KACE, SHIN KUNGA ABINDA ALLAH YA SAUKAR SABODAKU NA ARZIKI, SAI KUKA SANYA HUKUNCIN HARAMCI DA HALASCI A GARESHI? KACE; SHIN ALLAH NE YAYI MUKU IZINI, KO GA ALLAH KUKE ƘIRKIRAWAR KARYA? (60) KUMA MENENE ZATON WAƊANDA SUKE ƘIRKIRA ƘARYA GA ALLAH A RANAR ƘIYAMA??

Me karatu waɗannan ayoyin shimfiɗa muke maka saboda munaso kanka yazama awaye gameda dukkanin bayanan da za ka ji munyi acikin wannan lekca, bamaso muyi bayaninda zai zamanto shubiha kokuma ruɗi a gareku

Kuduba tafsirin ƙurdubi ƙarƙashin wannan ayar ta 59 suratul Yunusa, yace; Wannan ayar hujja ce musamman akan kore dukkan wani ƙiyasi matuƙar ya saɓama ƙur,ani ko sunnar Annabi (s.a.w).

Mu koma muduba Suratun Nahli ayata 116-117, Allah ta’ala yace:

ﻭَﻟَﺎ ﺗَﻘُﻮﻟُﻮﺍ ﻟِﻤَﺎ ﺗَﺼِﻒُ ﺃَﻟْﺴِﻨَﺘُﻜُﻢُ ﺍﻟْﻜَﺬِﺏَ ﻫَﺬَﺍ ﺣَﻠَﺎﻝٌ ﻭَﻫَﺬَﺍ ﺣَﺮَﺍﻡٌ ﻟِﺘَﻔْﺘَﺮُﻭﺍ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟْﻜَﺬِﺏَ ﺇِﻥَّ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻳَﻔْﺘَﺮُﻭﻥَ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟْﻜَﺬِﺏَ ﻟَﺎ ﻳُﻔْﻠِﺤُﻮﻥَ ‏( 116 ‏) ﻣَﺘَﺎﻉٌ ﻗَﻠِﻴﻞٌ ﻭَﻟَﻬُﻢْ ﻋَﺬَﺍﺏٌ ﺃَﻟِﻴﻢٌ ‏( 117 )

Ma’ana KUMA KADA KU CE, DOMIN ABINDA HARSUNANKU SUKE SIFFANTAWA DA ƘARYA, WANNAN HALAS NE, KUMA WANNAN HARAM NE, DOMIN KU ƘIRKIRA ƘARYA GA ALLAH, LALLAI NE, WAƊANDA SUKE KIRKIRAR ƘARYA GA ALLAH BAZASUCI NASARA BA, (117) JIN DAƊI NE KAƊAN, KUMA SUNADA WATA AZABA MAI RAƊAƊI.

Waɗannan jerangiyar ayoyinda muka kawo adunƙule sunayin bayanine gameda hatsarin cewa wani abu haramunne batareda ka rike hujja ahannunkaba.

Zan tsaya anan sai kuma darasi na gaba idan Allah Ya kaimu, za mu ji wadanne irin nau’ukan abubuwane Allah ya haramta ko kuma manzon Allah ya haramta, amma dai yanzu Inaso muriƙe wannan ƙa’idar cewa duk wani abinci da kagani a duniya to kaci abinka halasne ko menene walau anyanka ko ba’a yanka ba, kuma duk wanda ya ce maka karkaci abu kaza to kace ya baka aya ko hadisin da ya haramta.

Almajirinku ne kamar kullum

Jameel Alhasan Haruna kabo

(ABU ZULAIKHA)

ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ , ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ

Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illa h anta astagfiruka Wa,atubu ilaika

Back to top button