Uncategorized

Hotunan jerin motocin alfarma 10 masu matukar tsada a duniya

– Bugatti La Volture Noire itace motar da tafi kowacce mota tsada a duniya, inda ta wuce sauran motoci kamar Royce Rolls da Mercedes Benz

– Duk yadda Rolls Royce Sweptail take da aji da tsada, sai dai ta biyo bayan La Volture Noire wadda kudinta ya kai kimanin dala miliyan $13 (N4,953,000,000)

– Daga Leykan Hypersport tazama ta 9 yayin da Bugatti Veyron ta zama da 10, kuma duk ana sayar da su dala miliyan 3.4 (N1,295,400,000)

A yayin da ake ganin motoci a matsayin babbar bukata ta rayuwa domin kaiwa da kawowa, a wani bangare kuwa ana kallonsu a kayayyakin alfarma da kasaita masu bayyana yawan dukiya.

Kamar yadda Digital Trends ta bayyana, a 2022 an samu wasu kasaitattun motoci masu matukar tsada. A wannan jerin mota kirar Bugatti La Volture Noire ce ta fi kasaita inda ake siyar da ita a N7,239,000,000.

Duk da ficen da Rolls Royce ta yi, za ka iya tunanin za ta wuce Bugatti. Amma sai ta zo a ta biyu inda mota kirar Sweptail take biye da farashi N4,953,000,000.

Akwai kala-kalar kirar Bugatti wadanda suka bayyana a mataki na farko, uku, biyar da kuma goma.

Mafi arhar Bugatti sune Bugatti Veyron da Leykan masu farashi N1,295,400,000. Ga jern motocin alfarma 10 da suka fi tsada a duniya.

1. Bugatti La Volture Noire – $19 million (N7,239,000,000)

2. Rolls Royce Sweptail – $13 million (N4,953,000,000)

Masallacin Ka’aba da kuma wasu Gine-gine 10 mafiya darajar kudi a duniya 

3. Bugatti Centodieci – $8.9 million (N3,390,900,000)

4. Mercedes Benz Maybach Exelero – $8 million(N3,048,000,000)

5. Bugatti Divo – $5.9million (N2,247,900,000)

6. Koenigsegg CCXR Trevita $4.8 million (N1,828,800,000)

7. Lamborghini Veneno – $4.5 million (N1,714,500,000)

8. Lamborghini Sian – $3.6 million (N1,371,600,000)

9. Leykan Hypersport – $3.4 million (N1,295,400,000)

10. Bugatti Veyron $3.4 million (N1,295,400,000)

Back to top button