Uncategorized

Gwamnati Ta Fitar Da Sunaye Da Hotunan ‘Yan Boko Haram Da Suka Tsere Daga Gidan Kurkukun Kuje

 Gwamnatin Tarayya ta fitar da sunayen ‘yan Boko Haram din da suka tsere daga Gidan Kurkukun din Kuje, Abuja tare da ayyana su a matsayin wanda ake nema.

 A cikin wani bayani da Hukumar da ke kula da gidajen kurkuku ta fitar ranar Juma’a, ta roki duk jama’a su taya su neman ‘yan ta’addar da suka tsare daga kurkuku.

 Abin da ke tafe sunaye da hotunan fursunonin da’ yan Boko Haram 69 ne da suka tsere ne daga gidan kurkuku ranar 05/07/2022, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya fitar.

 “Duk wanda ya gan su, ko yake da wani bayani da zai taimaka ga kama su, ya taimaka ya kira wadannan lambobin: 07000099999, 09060004598 ko 08075050006, ko kuma duk wasu hukumomi mafi kusa. Za mu biye sunan duk wanda ya ba mu bayanin “, in ji sanarwar.

 Daga cikin sunayen akwai, Abdulkareem Musa, Abdusalami Adamu, Abubakar Abdulrahman Habibu, Abubakar Mohammed Sadiq, Abubakar Mohammed, Abubakar Yusuf, Adam Lawal Muhammad, Akibu Musa Danjuma,  Amodu Omale Salihu, Bello Haruna, Bilyaminu Usman, Bukar Ali, Ibrahim Mohammed, Ikya Abur, Ismail Idris Abdullahi, Modu Aji, Mohammed Sani, ds Musa Abubakar.

 Sauran sune, Mustapha Umar, Mustapha Umar, Shehu Abdullahi, Suleiman Idi, Suleiman Zacharia, Sunday Micheal, Yakubu Abdullahi, Yasir Ibrahim Salihu, Yunusa Mukaiya, Abdulmannan Obadiki, Abubakar Mohammed Musa, Abubakar Umar, Adamu Mohammed, Ahmadu Hagola, Asama Haruna Kanti , Baluye Modu, Bassey Victor Kingsley, Diko Iko, Fannami Alhaji Bukar, Faruku Waziri, Hassan Hassan, Ibrahim Musa, Idris Ojo, ds Ishaq Farouk.

 Sannan akwai Mohammed Goni Kyari, Mohammed Guja, Mohammed Saleh Buba, Mohammed Umar, Mukhtar Ussaini Khalidu, Musa Adamu, Musa Umar, Onyemire Asagba, Rabiu Shaibu, Sahabi Ismail, Sani Mohammed, Umar Ahmadu Ladan, Usman Balarebe, Yahaya Adamu Abubakar, Yusuf Yakubu, Abdulazeez Obadaki, Auwal Abubakar, Mansur Mohammed Usman, Mohammed Abubakar, Mohammed Jamiu Eneji Sani, Muazu Abubakar, Muhammed Sani Adamu, Muktar Umar, Nambil Zakari Gambo, Sadiq Garba Abubakar, Yazid Muhammed Usman, da Yusuf Ali Yusuf.

Back to top button