Uncategorized

Fitacciyar Jarumar Kannywood, Aisha Najamu Tayi Bikin Cikarta Shekaru 28 A Duniya (HOTO)

 Jarumar Kannywood, Aisha Najamu wacce aka fi sani da suna (Aisha Izzar so) ta saka wasu kayatattun hotuna a shafinta na instagram yayin da take murnar cika shekaru 28 da haihuwa.  Jarumar Kannywood, Aisha Najamu na daya daga cikin hazikan jarumar Kannywood a cikin shirin da yafi kowanne shiri farin jini mai suna Izzar so.

 Aisha Najamu kuma da wasu Furodusoshi ke nema a halin yanzu, tauraruwarta tana kan ganiyar haskawa a masana’antar fina-finan ta kannywood.

 Kalli Wasu Hotunan Jarumar a kasa.

 

 

An haifi Aisha Najamu a ranar 7 ga Maris, 1995, iyayenta ne suka haife ta kuma suka rene ta a jihar Jigawa.  Aisha Najamu ta kammala makarantar firamare da sakandare a mahaifarta jihar Jigawa.  Bayan kammala karatunta na Sakandare aka daura auren Aisha Najamu, Inda Allah Ya yi wa auren albarka ta haifi ‘ya’ya maza biyu kyawawa.

 Hotunan bikin ƙarin shekara na Aisha Najamu sun dauki hankulan mutane a shafukan sada zumunta musamman masoyanta na instagram.

Back to top button