Uncategorized

Daudar Gora Page 3 Hausa Novel By Bilyn Abdull

    ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

      (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

 𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

*_3_*

_____________

_*MAAB LUXURY HOME!!* Sabuwar duniyar hamshakan mata da ƴaƴan gata.💞_

_*GIDAN* ƙawa da ƙawata gidajen da suka cika gida._

_*SABUWAR DUNIYAR* Amare da uwargidan data amsa sunanta ƴar gaban goshi._

_*MAAB LUXURY HOME* wata duniya ce ta ƙawa da ƙawata gidajenmu da kayan ƙyale-kyale na burgewa da ɗaukar hankalin duk wani mai kallo_.

_*SUNYI FICE* Fice irin na ɗaya a cikin tsara, sune na farkon fari, a farin da za’a kira fari a kowace irin duniya._

_*A GAREMU* ba sitturu na alfarma da kawa ne kawai ke tabbatar da mu hamshakai ba. Sai mun haɗa da ƙawata gidajenmu da kayan MAAB LUXURY HOME zamu kasance cikakkun ƴan gata ababen kallo da nunawa sa’a koda a cikin dubun da sukafi dubu._

_*MAAB LUXURY HOME* sun takaita mana dukkan wahalar nema ko order a kasashen ketare ta hanyar wadatamu da galla-gallan kayayyakin adon gidajenmu_

_*MAAB LUXURY HOME.* Duniyar kayan Kitchen da decoration din gida na keta raini._

_*INA UWARGIDA INA AMARYA!!?* Ku ziyarci shagon mu dake No 22 Ahmadu Bello Way, Kano state. Ko kuyi order daga shafin mu na Instagram @maabluxuryhome. Ko Facebook @maabluxuryhome. Ko Ku nememu a lambar waya *08034631010*._

*_Mai azama shi za’a kira dana farkon fari😉. Bara nai sauri nawa suzo hannuna kafin a kwashe😁⛹🏼‍♀️⛹🏼‍♀️⛹🏼‍♀️._*

______________

………A wannan gaɓar haukane kawai ya rage wannan ahali suyi, dan duk dauriyar Babiy ya kasa danne raɗaɗi da zafin da yakeji. Itako Iffah kalaman dake fita a bakinta kausasa sun saka kowa ke ɗaukar tama zare kawai. Daga ƙarshe maganin barci aka ɗura mata. Bata tashi farkawa ba sai a ƙauyen da kakanninsu ke rayuwa. Wato iyayen Ummu. Rayuwa a ƙauyen Jumna a gareta tamkar mai gushewar hankali ya zame mata. Domin bata gane komai sai sambatu da kalamun ɗaura ɗammarar ɗaukar fansa ga duk ahalin Daular Ruman. Ba ƙaramin dagewa da jajircewa kakannisu da su Babiy sukai ba a kanta wajen ganin ta samu lafiya ta dawo hayyacinta. A cikin watanni takwas ta rasa yayunta guda biyu, wannan babban tarihine da bazai gogu a zuciya da ruhinta ba har karshen rayuwarta. Bayan jiyyar watanni kusan uku ta dawo hayyacinta. Sai dai ta daina fira’a da kowa, an daina ganin dariyarta ko farin cikinta. Babu abinda ke’a ranta sai buri da ƙudirin ɗaukar fansa. Tama kanta alƙawarin ita da hannunta zata kashe *_Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-majeed_*. Bayan nan idan itama an kasheta burinta ya cika na kawar da azzalumin sarki mai mulki irin na fir’auna a ƙasarta a cikin al’ummarta….

  *_(Babbar magana. Tayaya wannan buri naki zai cika Iffah😱? Sarki mai cikakken iko irin Tajwar Eshaan, mai amsa sunan Shahan-shan da ko fuskarsa babu wanda ya iya sani a cikin kasar Ruman har yanzun. Anya kuwa….? To mudaije zuwa wai mahaukaci ya sai kura😬🤧🚴🏼)_*

       

      ★★★

       “Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un” bakinta ke ambata cikin firgici da rawar jiki sakamakon farkawar da tayi daga mummunan mafarkin daya risketa a cikin barcinta. Ta dafe kanta dake wata irin sarawa na ciwo tamkar ana mata luguden taɓaren daka a tsakkiyarsa, gaba ɗaya jikinta ya jiƙe da zufa tamkar tayi wanka. Kusan watanni biyar kafin mutuwar ƴan uwanta da fara canjawar salon mafarkainta saɓanin na baya, abu mafi tsoratarwa kuma kusan mafarki ɗaya ne ke maimaita kansa a kowane barcinta idan ta kwanta. Sai dai mafi tashin hankalin a yau yayi kamanceceniya da na wasu dare da tarihi bazai taɓa mantawa da shi ba a cikin rayuwarsu ita da ahalinta.

     “Nina Arfa! Nina Fariha!”.

Ta ambata a zahiri zuciyata na ƙara ƙarfin gudu, yayinda hawaye suka shiga rige-rigen sauka a kumatunta. Tabbas irin wannan mafarkin tayi a daren da suka rasa Arfa, hakama daren mutuwar fariha. Yau kuma gashi ta maimaitashi akan kanta. Itama kenan zasu rasata?. Kai ta shiga girgizawa wani kuka masu ƙarfi na sake tahomata, hannu tasa ta toshe bakinta gudun kar sautinsa ya kai ga kunnen kakanninta. Sai dai aikin gama ya gama. Dan kuwa muryar kakanta takeji jikin ƙofar ɗakin nata a hankali yana ambatar sunanta. Da sauri ta shiga goge hawayen, kafin ta tashi daga shimfiɗar barcin nata wadda karan gado ne da katifar rimi. Mayafi ta ɗauka ta yanama jikinta, ta ƙarasa ga ƙofar ta buɗe…

      “Kina lafiya kuwa ɗiyar nan?”.

Ya faɗa cikin kafeta da idanu. Kanta dake rissine ta jinjina masa, cikin son danne kukan dake yunƙuromata ta bashi amsa.

    “Ina lafiya Kaka”.

  Jin shiru bai sake cewa komai ba ta ɗago ta dubesa a karon farko. Shima dai kallon nata yakeyi tamkar mai nazari. Sake maida idonta tai ƙasa, hawayen da take faman riƙewa suka ɓalle mata da gudu. Bata san ta ambaci “Kaka nima zasu kashe muku ni ko?. Inaji a jikina nima zaku iya rasani nan kusa tamkar yanda muka rasa su Nina Arfa”. Rawar da jikinta ta fara ta sata zubewa a gabansa kuka na ƙwace mata. Kusan minti biyu baice da ita komai ba, ita kuma ta kasa tsaida kukan.. Jin saukar hanunsa saman kafaɗarta ya sata haɗiye kukan, ya ɗagota tsaye yana ɗan murmushi dake sake bayyana tsufansa. Gefen mayafin jikinta ya kama ya shiga goge mata hawayen. “Fareedatu! Ki kwantar da hankalinki, insha ALLAHU babu abinda zai faru da ke, mafarki ai ba gaskiya bane ba. Suma su Arfa kwanansu ne ya ƙare, koba komai kuma sun rasu a gidan aurensu. Wannan kawai ya ishemu farin ciki”.

    Kanta ta jinjina masa tana sauke ajiyar zuciya a jajjere. Ya cigaba da shafa kanta a hankali har zuwa wani ɗan lokaci. “Kije kiyi addu’a ki kwanta abinki da safe zamuyi magana”.

     A hankali tace, “Kaka ina son zuwa naga su Ummu gobe to dan ALLAH”.

        Da sauri ya girgizamata kansa. “A’a bazai yuwu ba Iffah, iyayenki sun kawoki nan ne domin kuɓutar dake, taya kike tunanin zan barki komawa cikin daular Ruman?. Tun ina ƙanƙanin yaro nake bauta wa masarautar Ruman, bayan mutuwar mahaifina na cigaba da bautar saƙa kayan doki a garesu kamar yanda mahaifina ya barmin gado, a haka na haifi ƙanin mahaifiyarku shima ya mayeni, gashi har girma ya riskesa shima yana bauta musu. Mun rasa ɗan uwan mahaifiyarku a yaƙin kare daular Ruman, mun rasa Arfa, da Fariha. Ke ɗaya da kika rage mana da yayanki wajen mahaifiyarku kuma sai muyi wasa da rayuwarki? Bazai yuwuba jeki kwanta…”

     Batare daya sake bata damar yin magana ba ya juya ya koma bayan ya jamata murfin kofar. Da kallo kawai ta bisa hawaye na silalo mata. Duk yanda taso komawa barcin bayan tafiyarsa hakan ya gagara, zuciyarta ta kasa fita da ga ƙangin fargaba, da gaske tanajin matuƙar tsoro bayan rasa Fariha da Arfa da sukai watanni ƙalilan da suka shuɗe itama su rasata, tanaji zuciyar ahalinta bazata iya ɗauka ba idan itama suka rasatan. Wasu zafafan hawaye suka sake silalo mata masu raɗaɗi da saka ƙuna a ƙirji……

          ★★★

   “Iffah! Iffah!!…..”

Sautin ƙwala kiran sunanta daga muryar kakarsu da suke kira Iyyani ya sakata fitowa daga banɗaki data zagaya domin yin fitsari. Turus ta tsaya tare da haɗiye maganar da zatayi tana mai kallon ɗan-uwanta Hanash dake zaune gefen kakar tasu a ƙarƙashin bishiyar ɗoruwa da take a tsakar gidan. Murmushin da yakemata ta maida masa, kafin ta ajiye butar hannunta ta ƙarasa garesa. Dab da shi ta zauna tana mai ɗan rungumesa ta gefe da faɗin, “Ina kewarku Akhi”.

        Murmushinsa ya sake faɗaɗa yana mai kallon fuskarta. Ya kai hannu ya shafi yalwataccen gashin kanta da mayafin ya zame mai tsaho da santsi. “Muma muna kewarki Little angel. Gidan duk ya sake zama mana babu daɗi”.

   Yanda maganar tasa ta ƙare cikin rauni itama sai idonta ya cika da ƙwalla. Amma sai ta dannesu da murmushin mai ɗaci tana kaɗa kanta kawai.

         “Tashi ki bashi ruwa mana, k haka ake tarbar baƙo a garinku”.

  Baki ta ɗan tura gaba da kallon Iyyani mai maganar, tayi hakane danta katse raunin data hanga a fuskokinsu. Ta miƙe tana bata amsa cike da shagwaɓa. “Iyyani laifinkine fa, ban taɓa ganin matar da bata tattalin mai gida ba irinki, dole Yayana ya miki kishiya”.

     Daƙuwa tamata cikin gatsina fuska. “Ungo naki nan Fareedah, yo bandama lalacewa mizanyi da wannan faratun mai kama da jar tsada tuzurin banza”.

KARANTA ZAFAFA 2023

*IDON NERA By Mamuh ghee*

         Hanash ya tsuke fuska yana kallon Iyyani. Murmushi Iffah tayi tun kafin ya faɗi abinda ke bakinsa. Dan dama inhar suka haɗu da Iyyani sai ta hasalashi take jin daɗi shi da Arfa akan ƙinyin aure, duk da bawani shekarune da shi ba, dan ashirin da shida ne kawai, Arfa nada ashirin da uku, Fariha nada ashirin da ɗaya. Iffah nada goma sha takwas….

        Iffah ta dire masa abinci da ruwa ta sake kaiwa zaune kusa da shi sannan ta dubesa. “Akhi yasu Babiy suke?”.

    Ya nisa a hankali bayan ya dire moɗar ruwan daya sha. “Duka lafiya suke. Suna gaisheki ke da su kaka. Duk da suma dai nan da kwana kusa zamu ma dawo nan ɗin muma. Yanzu haka nazo duba can tsohon gidanmu ne dan asan gyaran da za’ai masa”.

    Sosai ta kafesa da ido ita da Iyyani. Kafin cikin ƙarfin hali Iffah tai magana. “Amma Yaya su Babiy basa ganin rayuwa zata mana wahala anan sakamakon bamu sababa sam. Sannan ayyukansu dake acan miye makomarsu? Da karatunmu muma?. Abinda ya faru ya riga ya faru, tunda hannayenmu bazasu iya maidosu ba, mi zaisa zukatanmu bazasu cigaba da haƙuri ba. Barowarmu cikin Daular ruman tamkar munji tsorone, ko sake sakin rayuwarmu a hanun waɗanda kansu kawai suka sani…….”

      “Tsoro halak ne Iffah. Bama muba mafi yawan masu yara mata sunata barin daular ruman a yanzu domin tseratar da ƴaƴansu daga auren jeka nayika. Karatun ƴammata yana neman tsayawa cak, kowace na tsoron fitowa ta zama nama a hanun hadiman daular ruman. a yanda lissafin yake a yanzu an rasa mata goma sha huɗu fa, a tunaninki kafin ƙarewar wannan shekarar ba’a rasa fin hakaba duk da bawai ya cigaba da auren bane.”

         Wasu hawayene masu ɗaci da ƙuna suka silalo ma Iffah, tai saurin saka gefen mayafinta ta share tana murmushin takaici. “Niko a ganina gudu bashine mafita ba, muryoyinmu ya kama mu ɗaga wa duniya kowa yasan halin da muke ciki, idan har a ƙasar Ruman babu wani sama da nasa mulkin ai a sauran ƙasashen duniya akwai wanda suka fisa…”

    “Humm Iffah ke yarinya ce har yanzu.”

  “Sosai kuwa Hanash. Shiyyasa bata gane komai sai abinda yanzu take zuwa da shi”.

          “Humm Iyyani kenan”.

Iffah ta faɗa a yanayin jin raɗaɗi a maƙoshinta. Su duka kallonta sukai, sai dai ta ɗauke kanta gefe tamkar bata gansu ba. Daga haka babu wanda ya sake cewa komai har tsahon wani lokaci. Iyyani ce ta canja hirar da wani abu daban har Hanash ya kammala. Tare da shi suka fita wajen duba tsohon gidan da kakaninsu da suka haifi Babiy ne suka rayu a ciki, dan sudai tunda suka taso a cikin birinin daular ruman suka san kansu duk da a ɗan gefen gari suke acan ɗin ma. Sai dai su shigo cikin ƙauyen Jumna a matsayin duba kakannin nasu. zuwa yanzu su duk sun rasu, shiyyasa gidan ya kasance babu kowa. Duk ma ya rusa ya fita hayyacinsa dan ginine na jar laka tamkar yanda duka gidajen ƙauyen suke. Sun ɗan jima acan suka dawo, sun iske kaka ya dawo shima daga fitar da yay tun ta safe gona ɗebo sassaƙe-sassaƙen magunguna. Ƙara zaman tattaunawa sukayi iya su uku, ita dai Iffah bata cewa komai. Daga ƙarshe ma tashi tai ta shige ɗakin kwananta. Bata sake fitowa ba sai da kaka ya neme ta. Sassaƙe-Sassaƙen magungunan daya ɗibo ɗazun ne a gabansa, kowanne ya ɗauresa daban-daban. Ya turamata babban robar da suke ciki… “Zaki fara amfani da su Iffah, bana son kiyi wasa dan ALLAH. Waɗannan kuma hayaƙine, a kowacce duhun magriba ki tabbatar kinyi turarensu, wannan kuma a ruwan wanka ne, da kin idar da sallar asuba ki zubasu cikin ruwa kaɗan ki cire kayanki ki tabbatar duk jikinki ya samu”.

        “Tofa kaka wannan ɗin kuma duk na miye?”. Iffah ta tambaya cikin nuna mamaki.

   Idanu ya tsiramata na kusan mintuna uku tamkar mai nazari, sai kuma ya ɗauke kansa da wani yanayi mai wahalar fassara. “Faruwar ƙaddararmu bashi ke nuna baza’a sake jarabtarmu ba. Idan jiya ta shuɗe da ɗaci zata iya yuwuwa yau ɗinmu da dariya zata kasance, sai dai sanin mike a gobenmu al’amarine mai girman gaske, damin gaibunmu ce ita ALLAH ne kaɗai masanin mi zaizo.”

        Kallon juna sukai ita da Hanash, Iffah ta ɗan ɗage kafaɗa cikin yanayin ban fahinta ba, shima sai ya kaɗamata idanu alamar shima hakan take. Atare suka maida dubansu ga kaka. Amma sai ya kauda kansa alamar baya buƙatar kowacce irin tambaya daga garesu. Iffah ta jinjina kai kawai alamar ko’oho. Sai kuma ta miƙe tana mai faɗin, “Ni dama fa na yanke shawarar zanbi Akhi mu koma. Tunda dai naji sauƙi gara naje na koma makaranta anata wuceni a darasi”.

       Ba karamin waro idanu Hanash yay ba, zaiyi magana kaka ya dakatar da shi ta hanyar yin murmushi da kaɗa kansa. “Ita rayuwa rubutacciya ce tunkan halitta, an rubutatane da alƙalamin da ba’a goge rubutunsa, babu wani hannu daya isa gogeta koda da ƙarfin iko. Dole ne sai anyi hakan, ko muna so ko bama so mashin nan sai ya isa inda aka aikashi. Domin ita *KIBIYAR AJALI! SULKE BAYA TARETA SAI TA GITTA*”.

        A rikice Hanash ya tari numfashinsa. “Kaka bana gane dunƙulallun zantukan nan naka, ka fito fili dan ALLAH ka sanar mana mi kake son faɗa…”

      “Hanash! Lokacin faɗar baiyiba ai, nima kurman baƙin kawai na gani, fassarar sai UBANGIJI”.

     Sosai Hanash ya sake tsare fuskar kaka da idanu, kamar yanda itama Iffah tai tsai tana kallon nasa. Su dukansu sun jima da sanin kaka mutum ne hatsabibi, dan kuwa mahaifinsa gawurtaccen masanine da azamaninsa akan kallesa tamkar matsafi ko wani mai gani har hanji, sai dai kasancewar bai ajiye buzu ya zauna akan iya wannan al’amarin ba yasa ake shakkar faɗa, yana bada taimako na magani akan abubuwa daban-daban musamman harkar aljanu komai ƙarfinsu da shaiɗancinsu. Sannan yana sana’arsa ta saƙa kayan kwalliyar doki. Kaka ya gaji abubuwa da dama a garesa, sai dai shi ya watsar da harkar bada maganin dan shima dai a karan kansa yana ta’allaƙa sanin mahaifin nasa da bokancin, duk da dai bai fito fili ya bayyana hakan ba kuwa, amma rashin maida hankali akan abinda ya shafi hakan zaisa ka zargi ko haka ɗinne. Akwai kayan aiki na mahaifinsa da yawa a killace a wani waje da shi kaɗai ya sani, kuma tun bayan mutuwarsa shi ya tattare su ya killace su…………✍

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+22799643131

Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Back to top button