Uncategorized

Daudar Gora Page 1 Hausa Novel By Bilyn Abdull

     ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

      (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

 𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم*

_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_Ɗan ɗano daga Zafafa biyar😋😋_*

………Kwanakin mako uku kenan da shuɗewar komai amma komai ya kasa mantuwa a zukatansu. Kuzari ya samu rauni kamar yanda dukkan karsashi ya gujema gangar jiki. Duniya ta masu ƙunci, ƙunci irin wanda har ƙarshen numfashi da wahala su manta. Farin cikinsu ya zama fansar damuwar wasu, wasun da kansu kawai suka sani basa kallon na ƙasa da su. Da ace ƙarfin iko a hanun kowanne ruhi yake a zahirin rayuwa, da ita ce zata zama mace ta farko a duniya mai ƙarfin ikon da zai girgiza zukatan kowaɗanne irin azzalumai. Kafin shuɗewar makwanni uku masu ɗauke da kundun baƙin ciki rayuwar ahalin Mal. Zayyan tamkar dutsen lu’u-lu’u suke a cikin tsakkiyar zinare. Ba magana ake akan dukiya ba, dan tana a cikin jerin abu mafi rauni da suke ɗauka ko amsa sunan ko kallo farin ciki. ana magana ne akan kammaluwar ahali masu matuƙar ƙaunar juna zunzurutu mara gauraye. Masu kuka a yayin zubar hawayen ɗayansu, masu dariya a yayin farin cikin ɗayansu, masu jiyya a yayin ciwon ɗayansu, masu zama komai a lokacin da komai yake abu ɗaya a hanunsu.

       𝕽𝖚𝖒𝖆𝖓 babbar ƙasace a tsakkiyar wani babban tsibiri a wani ƙarni daya shuɗe kafin yau, ƙasace mai yawan arziƙin zinare yankin nahiyar Africa. Ƙasar Ruman nada babbar Daular mulki data ƙunshi manyan sarakuna masu ɗunbin tarihi kala-kala da labaransu bazai taɓa kasancewa shuɗaɗɗe ba a duniya. Ba arziƙin zinare ne kawai suke da shi ba, sunada nau’i-nau’in kayan itatuwa da wajajen noma harma da kiwon dabbobi da akan fita da su ƙasashe daban-daban ko’a shigo cikin ƙasar a saya. Al’ummar wannan ƙasa sun kasance wasu irin ƙyawawan mutane masu kwarjini da cikar haiba, sai dai duk da ƙyawun da mafi rinjayensu ke da shi hakan bazai hana a samu masu ƙarancin ƙyawun ba. Sunada yawan addinai da ƙabilu tamkar kowacce ƙasa, sai dai mafi rinjayen ƙabila sune masu yara yaren rumanci, sannan addinin musulinci yafi kowanne addini ƙarfi da rinjaye. Abu mafi mamaki a ƙasar ta Ruman shine, duk da ƙarfi da rinjayen da addinin musulinci ya samu suna girmama al’adunsu na kaka da kakani musamman ƙarfin iko. Ƙarfin iko nada matuƙar tasiri a ƙasar Ruman ainun, hakama al’adu da girman masautunsu na taka rawar ganin hana dukkan abinda turawa suka zo musu da shi taka rawar gaban hantsi a garesu bayan ilimin boko, duk da suma sun shiga cikin ƙangi na mulkin mallakar turawan a ƙarnin daya shuɗe. Babu wani mulki dake da tasiri sama dana sarautunsu tun a farkon ƙarnikan baya har zuwa yau ɗin nan da suke rayuwa bisa mulkin mallakar sarakunan dake mulkin mallakar su. 

         𝕯𝖆𝖚𝖑𝖆𝖗 𝕽𝖚𝖒𝖆𝖓 itace babbar masarauta da dukkan masarautu ke ƙarƙashin ikonta bama su talakawa kaɗai ba. Itace tamkar fadar shugaban ƙasa a wasu ƙasashe. A maimakon mulkin siyasa, su 𝐃𝐀𝐔𝐋𝐀𝐑 𝐑𝐔𝐌𝐀𝐍 itace babbar masarauta mai faɗa aji akan komai da kowa na ƙasar Ruman, komai yana tabbatuwa ko akasinsa da ƙarfin ikon sarki mai mulki a kujerar wannan daula. Bama gasu talakawa ba, babu wata masarauta a cikin kasar Ruman data isa koda ɗaga murya a bayan idon Daular Ruman saboda karfin ikon mulkin 𝐒𝐡𝐚𝐡𝐚𝐧-𝐬𝐡𝐚𝐧 (King of kings). Ƙarfin mulkin wannan Daula yakai a duk faɗi da ƙasar Ruman ke dashi babu wani mahaluki da zai iya faɗar siffa kai tsaye ko kamanni na sarkin da duk zai mulki daular ruman tun zamanin ƙarnikan baya, saboda tsantsar girmamawa da akema sarakunan wannan Daula ko iya ɗaga kai a musu kallon ƙurulla na kusa babu maiyi, daga nesa kuwa fuskokinsu ababen kwarjinine irin na masu mulki da a ranar wasan al’ada na kowanne shekara ake iya ganinsu a zahiri daga nesa bisa keken doki. A tsari da ƙa’idar daular ruman dukan yarima mai jiran gado daya shiga shekaru bakwai na girma za’a ɗaukesa kowa ya daina ganinsa, a sirrance zaiyi ilimin zamani dana addini dama duk wata rayuwarsa irin ta kowa. Bayan cikar shekarun girma a garesa za’a fara bayyanasa ga sarakunan sauran masarautu cikin shigar da ƙwayar idonsa kawai zasu iya gani. Nuna yarima mai jiran gado ga sauran masarautu na nufin alamar mahaifinsa zaiyi murabus kenan ya ɗaurasa a karagar mulki basai bayan ransa ba. Sarkin kuma da baya buƙatar hakan bazai taɓa bayyana yarima ba ga kowa har sai bayan mutuwarsa. 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐇𝐚𝐲𝐬𝐚𝐦 𝐢𝐛𝐧 𝐀𝐛𝐝𝐮𝐥𝐥-𝐌𝐚𝐣𝐞𝐞𝐝 shine sarkin daular ruman daya shuɗe aka ɗora ɗansa ɗaya tilo bisa karaga. Shi kaɗai ya haifa a duniya, shine kawai magajinsa sai mata huɗu da saɗaka daya bari. A yanda tarihi yazo ba’a taɓa 𝐒𝐡𝐚𝐡𝐚𝐧-𝐬𝐡𝐚𝐧 mai ƙarfin iko da daularsa ta gagari duk wani jar fata nunawa yatsa ba kamarsa, ya shimfiɗa mulki a Ruman dama yankin Africa gaba ɗaya, izzarsa da ƙarfin mulkinsa yasa ba masarautun Ruman kawai ba, dukkan masarautun Africa na biye da shi da girmamawa da tsoro mai ƙarfi. Ya tara arziƙi mai ban tsoro da ban mamaki, ya kuma shimfiɗa ayyuka da ba Ruman kawai ba, Africa gaba ɗaya bazasu iya mantawa ba. Kaf ƙasashen jajayen fata masu faɗa aji na tsoro da shakkar 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐇𝐚𝐲𝐬𝐚𝐦 𝐢𝐛𝐧 𝐀𝐛𝐝𝐮𝐥𝐥-𝐌𝐚𝐣𝐞𝐞𝐝.   Sarki Haysam ya raini ɗansa ɗaya tilo tamkar sauran shuɗaɗɗun sarakuna koma fiye da su, dan saɓanin sauran yarima da tarihinsu ya shuɗe shi wannan yariman tun a shekara uku na haihuwarsa babu wanda ya sake ganinsa kojin labarin inda yake rayuwa. Sai dai a kullum akanji sunansa a bakin Tajwar Haysam fiye da sau goma, ambaton sunansa shine mafi yawan magana dake fita a bakin Tajwar. Hakan kan saka razani da tabbatuwar shi wannan yarima zai kasance na daban a dukkan sarakunan da suka shuɗe kenan. Tabbas hasashen mutanen ƙasar ruman ya rabbata, dan kuwa dai kam da gaske 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐄𝐬𝐡𝐚𝐚𝐧 𝐢𝐛𝐧 𝐇𝐚𝐲𝐬𝐚𝐦 𝐀𝐛𝐝𝐮𝐥𝐥-𝐦𝐚𝐣𝐞𝐞𝐝 ya zama sarki na daban a cikin dubban sarakuna, tare da labari mai ban tsoro da razani fiye dana mahaifinsa. Kamar yanda ƙa’idar daular ruman take bayan cikar shekara talatin da biyar yarima Eshaan ya bayyana a ƙasar haihuwarsa ta Ruman, sai dai kamar kowane yarima na baya babu mai iya ganin fuska ko suffarsa ta ainahi, hatta da idanunsa ma shi babu wanda zai iya ganin koda ƙwayar cikinsu sakamakon glass dake sakaye da su. Bayan gama bayyanashi ga masarautu da wata ɗaya kacal Tajwar Haysam  bin Abdul-Majeed yay murabus aka ɗaura yarima mai jiran gado bisa kujerar mulkin daular ruman tare da auren mata huɗu galla-galla daga mabanbanta masarautu masu ƙarfin faɗa aji a kasar ruman. Kwanan 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐄𝐬𝐡𝐚𝐚𝐧 bakwai akan karagar mulki Tajwar mai murabus Haysam bin Abdul-Majeed ya kwanta jiyya, jiyya ce data girgiza kowa ta kuma bada mamaki, dan kuwa kwanansa ɗaya tak yace ga garinku nan. Kwatanta tashin hankalin da ƙasar Ruman ta shigama a lokacin bazai lissafu ba. Ƙura bata lafa ba mutuwar ɗaya daga matan 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐄𝐬𝐡𝐚𝐚𝐧 ta sake bayyana, kwana ɗaya da mutuwarta watama ta sake mutuwa a washe gari amare suka rage saura biyu. Al’amari ya fara saka zukatan jama’a hasashen da babu damar cewa komai. Wata biyu tsakani ɗayar matar ta uku ta sake mutuwa saura ɗaya. Tofa babbar magana. Abu mafi girgiza zukata shine mutuwar ɗayar data rage a shigar sabon wata. Kenan matan Tajwar 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐄𝐬𝐡𝐚𝐚𝐧 da mahaifinsa sun gama mutuwa kaf a cikar wataninsa uku da hawa karagar mulkinsa da kuma aurensa. Abun ya taɓa zukata aynun, sai dai babu wanda ya iya ko tari saboda tsoro. Sai dai abu mafi tsayawa arai a cikar wata na shidda aka sake ɗaura auren 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐄𝐬𝐡𝐚𝐚𝐧 𝐢𝐛𝐧 𝐇𝐚𝐲𝐬𝐚𝐦 𝐀𝐛𝐝𝐮𝐥𝐥-𝐦𝐚𝐣𝐞𝐞𝐝 da wasu matan biyu daga gidajen masarautun kasar ruman. Labarin bai canja ba, dan kuwa suma sun mutu ɗaya bayan ɗaya kafin cikar shekararsa guda da hawa mulkin. Abin al’ajabi aka kuma sake aura masa wasu biyun daga wasu masarautun, suma ɗin dai kamar ƙiftawar ido nasu labarin ya shuɗe a cikin shekara ɗaya. Haka aka sake ɗaurama Tajwar Eshan aure da wasu mata daga mabanbanta masarautu da tsoro bazai barsu hana auran ƴaƴansu ba, haka kuma suka mutu suma ya kasance duk ya auri yarinyar kowace masarauta goma da suke da su. 

         Zuwa yanzu ba shakka da tsoron ɗaga murya bane kawai a zukatan mutanen ƙasar Ruman, hatta numfashi suna yinsane tamkar ɓerayen dake a ƙarƙashin tsaron maguna. A tunaninku yaya sautin fitar numfashin zai kasance?😭.

★★_________★★

     

      Sunanta shine 𝕱𝖆𝖗𝖊𝖊𝖉𝖆𝖍 na yanka, sai dai iyayeta da dukan jama’a na mata alkunya da 𝑰𝒇𝒇𝒂𝒉. Su huɗu iyayensu suka haifa, itace auta a cikinsu. Hanash! Shine namiji babba. Arfa! ita ke bi masa, Fariha! Itace ta uku, sai ita auta 𝑰𝒇𝒇𝒂𝒉. Sunan mahaifinsu Zayyan!, amma suna kiransa Babiy, mahaifiyarsu Jamaima! Suna kiranta Ummu. Ƙasar Ruman ƙasarsu ce ta gado tun iyaye da kakanni, nan kaɗai suka sani, anan kuma kaɗai suke rayuwa. Kamar yanda na faɗa muku a tun farko ƙasar Ruman ƙasace mai tarin arziƙi nau-i daban-daban da ake kaikawo da su a cikin ƙasa da wajenta, tun daga kan zinare, noma, kiwo, ƴaƴan itatuwa dama wasu daban lissafo ba. Sai dai duk da wannan tarin arziƙi da ALLAH ya basu hakan bai hana kasancewar wasu a cikin matsayin talakawa ba. Kamar dai su 𝑰𝒇𝒇𝒂𝒉, mahaifinsu talaka ne mai rufin asirin ALLAH. Manomi kuma makiyayi, a nomansa harda noman zuma yakeyi. Dukkan wani nau’in zuma zaka samesa a hannunsa, wannan yasa yake mu’amula da daular ƙasar Ruman. Duk da ba masu arziƙi bane su mahaifinsu mutumne mai tsantseni da taka tsantsan, sannan ya tsaya tsayin daka wajen ganin sun samu ilimin addini dana zamani irin na yara ƴan gata. Gidansu gidane mai ban sha’awa da birgewa a ɓangaren mu’amulantar juna mai cike da soyayya da ƙauna. Basu da wani buri sai na faranta ran juna, a koda yaushe zaka samesu cikin nishaɗi dan talaucinsu bai taɓa kasancewa damuwa ga rayuwarsu ba ko nakasu ga farin cikinsu. Idan ɗaya na ciwo sukan kasance tamkar su duka suke ciwon, idan ɗaya na farin ciki sukan kasance su duka cikin farin ciki. Sune abokai kuma kawayen junansu harda iyayensu. Sunada tarin burika na rayuwa dana kai da kai, wasu a rubuce, wasu a ƙayyade a cikin zuciya, wasu a bayyane, wasu a adane a ƙasan zukata. wasu sun cika, wasu ƙaddarorinsu masu ɗaci da saka zubar hawaye dake gudana a halin yanzun sun yanke igiyar kaiwa ga samun cikarsu. Labarin sauyawar tasu, da yankewar tasu ya farane daga wata rana dake dai-dai da cikar sauran kwanaki huɗu na zagayowar bikin al’ada da ƙasar Ruman ke gudanarwa. Ranar da tarihinsu bazai iya gogewa ba, zukata bazasu iya mantawa ba, lissafin faruwarsu da shuɗewarsu bazai taɓa daina maimaita kansa ba koda a bayan rai ne.😭

         A kowane karshen wata Babiy ke kai zuma tulu uku daular ruman, amma a duk bikin shekara na al’ada tulu goma yake kaiwa dan shi kaɗai ne yardajje a manoman zuma da sarki ke iya amfani da zumar dake zuwa daga hanunsa tun zamannin Tajwar Haysam. Koda ya mutu kuma 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐄𝐬𝐡𝐚𝐚𝐧 bai daina amsa ba. Sai dai kuma duk da wannan yarda a kullum zagaye suke da tsaro ta fannoni daban-daban duk a dalilin zumar da Babiy kan samarwa Tajwar. A ranar data rage sauran cika kwanaki huɗu na bikin al’ada rashin jin daɗin jiki ya saka Babiy bama Hanash damar tafiya dasu duka cikin ƙaton gidan gonat da yake noman zuma domin ɗurasu a sabbin tulunan da za’akai daular ruman. Da’ace yasan anjimarsa ko ƙaddararsa data ahalinsa da bazai taɓa barin wannan lokaci zuwa ba koda a mafarki. Sai dai kash, ƙaddara ta riga fata inji masu iya magana. Cike da farin ciki suka fita, dan kuwa a shekara sau uku kacal Babiy ke barinsu shiga cikin lambunsa. Ba lambun kawai ba, hatta fita koda ta zuwa makarantace suna yintane cikin shiga mai lulluɓe dukkan kamanni, domin kuwa ƴaƴan nasa na ɗauke da wani irin sirrin ƙyawu mai ɗaukar hankalin duk wanda zaiyi tozali da su, dan haka kullum cikin shigar larabawa suke harda niƙabi, idanunsu kawai ake iya gani da tafukan hanunsu, a yau kam sai suka fita a asalinsu batare da sanin iyayensu ba duk da kuwa suna dai sanye da abayoyin, sai dai babu niƙabin. Su kansu da’ace sun san abinda ke biye da rayuwarsu da zasu ninka niƙabi kan niƙabi ne har sama da sau sittin idan zai nisanta zuwan almakashin daya datse walwalin zinaren farin cikin zukatansu.

     Sun isa lambu sun gudanar da ayyukan da Babiy ya umarcesu cike da farin ciki da nishaɗi, suka tsinko tarin ƴaƴan itatuwa kowa da nasa da burin abinda zaiyi dashi a ranar bikin al’ada dake tunkarosu. shigarsu gida dai-dai da isowar tambura da bushe-bushen algaitu masu ban mamaki da al’ajab a cikin kunnuwansu dama dukkan sauran talakawan gari, dan abune da ba’a sabaji ba sai a wasu lokuta na gittawar Tajwar daga can kan hanya bawai a cikin anguwa kamar hakan ba………..✍

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+22799643131

Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

Back to top button