Uncategorized

Da mutane ke bada makullin Aljanna da ba za su ba ‘yan fim ba, Hauwa Waraka

 

A wata irin da BBC Hausa a shirin Daga Bakin Mai Ita da suka yi a ranar Alhamis, 21 ga watan Yulin 2022, Jaruma Hauwa Waraka ta bayar da tarihin tarihinta.

 Da farko ta fara da bayyana cewa sunanta Hauwa Abubakar amma an fi saninta da Hauwa Waraka, an haifeta a garin Jos amma a garin Kano ta girma.

Da aka tambayeta yadda aka yi ta shiga fim, ta ce da farko bata san menene fim ba ma.  Akwai wasu ‘yan uwanta ne da suka kai ta Sabon Titi da ke Kano inda asalin ‘yan fim suke, daga nan ta dan fara shiga harkar jefi-jefi.

 An tambayeta da fim din da ta fara, inda tace ta fara da kananu ne wadanda ba ita bace jarumar da ta haska fim din, don ko shirin Waraka wanda tayi fice dashi ba ita babbar jaruma a fim din.

 Ta ce bayan ta dan yi fina-finai ta bar industiri na kusan shekaru 5 zuwa 7 wanda daga bisa ta dawo.  Dama kuma asali bata san menene fim ba dama kawai tana yi ne sama-sama.

 Da aka tambayeta dalilin da yasa take fitowa a mutimiyar banza, sai tace ta san babu kyau a musulunce ayi shaye-shaye, da sauransu, amma kawai suna yi ne don fadakarwa kuma ita har yau bata shaye-shaye.

 Tace bata jin dadin kallon da mutane suke yi mata, amma kuma tunda babu mai wuta ko Aljanna, ko kadan bata damuwa.

 Ta ci gaba da cewa:

“Na yarda da Allah, na yarda da mazonnin Allah, na yarda da sunnoninsa, na yarda da mala’ikunsa, na yarda da littafansa, kuma na yarda da ranar kiyama, kuma na yarda da kalmar La’ilaha illallahu Muhammadar rasulullahi sallallahu alaihi wa sallam.

“Kuma ni abinda nake gaya wa al’umma na san mutum dai bai da makullin wuta bai da makullin Aljanna. Balle yace ai nine mai makkulin wuta, wuta zan kai ka ko kuma nine mai makullin Aljanna, Aljanna zan kai ka.

“Don majority mutane kallon da su ke mana, inda su suke bada Aljanna, majority mutane ba za su ba dan fim ba. Magana ta gaskiya, saboda akwai mutanen da ko sunana aka kira, sai kaji sun ce wannan makamashin wutar? Ni kuma naga baka da wuta baka da Aljanna. Allah shi ke bada ita ba mutum ba.”

Back to top button