Uncategorized

Asirin wasu daga cikin daractotin kannywood ya tonu.

Batun yadda ake biyan Yan Film Kudin aikinsu da alama ya raba kan masana’antar shirya finafinai ta Kannywood gida biyu. 

Tun bayan da BBC ta yi fira da Ladin Cima wacce aka fi kira da Mama Tambaya ko kuma Tambaya ta Mallam Mamman a shirinsu na DAGA BAKIN MAI ITA sai ka-ce-na-ce ya barke a tsakanin masu bada umarni da kuma furodusoshi.

 An yi wannan hirar ne da Ladin Cima tun 14 ga watan Nuwamba shekarar 2021 a lokacin ne BBC suka tura mutun biyu daga cikin ma’aikatanta domin yin hira da dattijiwar Kannywood mutun goma 11. Ana saka bidiyon shirin ne daya bayan daya a kowacce ranar Alhamis . Wannan ne yasa ba a saka hirar da aka yi da Ladin Cima tun wancan lokacin ba.

 Hajiya Ladin Cima ko kuma Tambaya ta Mallam Mamman kamar yadda ma’aikatan Kannywood ke kiranta ta shaidawa BBC Hausa cewa kudin da ake biyan ta basu haura dubu biyar ba. Wannan magana ce ta ja hankalin mutane da yawa, inda suke bibiyan daraktoci da furodusoshi da bakaken maganganunu. Wannan ne yasa sauran Daraktoci da Furodusoshi, irin su Ali Nuhu da kuma Falalu A Dorayi suka fito suka bayyanawa duniya cewa suna biyan Ladin Cima kudin aiki ne fıye da Dubu Arba’in. Inda kuma ta bayyana cewa an yi haka bayan sake hira da BBC ta yi da ita. Duk da Ali Nuhu da aka fi kira da Sarkin Kannywood ya ce ba za a rasa masu biyan ta 2,000 ko 5,000 ba, amma bai kamata Ladin Cima ta yi musu kudin goro ba.

ƘARIN LABARAI

Ana ci gaba da tona wa yan kannywood asiri akan fitar da BBC Hausa suka yi da Ladi Cima

Cikin ƙunar rai Jaruma Nafisat Abdullahi ta mayar wa da Naziru Sarkin waƙa raddi.

 

Wannan hira dai ta zama silar budewar wani babban al’amari da ya dade yana ciwa sauran ma’aikata tuwo a kwarya. Domin tun ranar Alhamis batun da ake ta tattaunawa kenan a shafuka daban-daban. Su ma sauran al’umma ba a bar su a baya ba, domin sun shiga zancen dumu-dumu tare da bijiro da tambayoyi daban daban da suka shafi Kannywood.

 Girma da matsayin da masana’antar Kannywood ta kai wurin kyautata wa, da fadakarwa da kuma samar da aikin yi ba abin mamaki ba ne don wannan ya ja hankalin mutane. Manyan jarumai irin su Nafisat Abdullahi, Nuhu Abdullahi, Hadiza Gabon, Rukayya Dawayya da Tijjani Asase duk sun yi gugar zana a shafukansu. Wasu kuma daga cikin su irin su Adam A Zango da Rahama Sadau su ka nuna alamar bakinsu da Goro, wato sun dinke shi duk da akwai abin fada. 

Wasu na ganin abin da Hajiya Mama tambaya ta yi ba ta yi daidai ba wasu kuma na ganin hakan shi ne daidai a yayin da wasu su ka yi halin ko ina kula da lamarin. 

Yan Ba Ruwana. 

A ranar juma’a. Rahama Sadau ta a shafinta na Instagram ta wallafa, hmmmmmm da wata alamar rufe baki. Adam A Zango kuwa a ranar Asabar sai ya wallafa wani bidiyon wata waka mai taken shiru da yan amshi a bayansa. Nafisat Abdullahi, kuma kira tayi ga jarumai da su daina karɓar aiki idan har farashin da Furodusa ya ba su bai musu ba. Duk da kuwa ta nuna Shakku, amma ta ce ba mamaki hakan na iya faruwa. 

Magana Zarar Bunu.  

Naziru sarkin waka ya saki wani bidiyo a shafinsa na Instagram inda yake kara jadadda maganar Mama gaskiya ne, har ma ya kara da cewa wasu yan matan Film din ma, sai sun bada kansu kafin a yarda a saka su a film. Wannan maganar tashi zamu iya cewa ita ce ta kara hura wutar rigimar. 

Nuhu Abdullahi ya ce da zamu fito muyi magana da mutuncinku ya zube. Shi ma wannan maganar tasa ta jawo ka-ce-na-ce. 

Wasu kuma irinsu Ali Artwork sun goyi bayan maganar Sarkin Waka duk da kuwa ya soki wasu daga cikin.

 Kira Ga Sulhu.

 Sauran jarumai da dama sun yi magana cikin ruwan sanyi domin kwantar da hankali abokan aikinsu, sun yi matukar kokari wurin ganin sun kashe wutar da ke cigaba da huruwa. Kamar irin su Tijjani Asase da kuma Sabir Abdul. Musbahu M Ahmed wanda yaya ne ga Sarkin waka, jan kunnen Yan Film yayi kan su guji furta maganganun da zasu jawo rigima.

Back to top button