Uncategorized

Anga watarn Ramadan A Nigeriya Na 2023

π—”π—‘π—šπ—” π—ͺ𝗔𝗧𝗔𝗑 π—₯𝗔𝗠𝗔𝗗𝗔𝗑 𝗔 π—‘π—œπ—π—˜π—₯π—œπ—¬π—”


Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Sultan Sa’ad Abubakar III ya sanar da ganin jinjirin Watan Ramadan a Najeriya.

A wani jawabi da ya gabatar, Sarkin Musulmin ya ce an ga jinjirin watan na Ramadana a daren Laraba, inda ya ce Laraba din 22 ga watan Maris 2023 ce ranar karshe ta watan Sha’aban na Shekarar Hijira ta 1443.

Sannan ya ce Alhamis 23 ga watan Maris 2023 ce ranar farko ta watan Ramadana na Shekarar Hijira ta 1443.

“Ζ³an uwa al’ummar Musulmi, bisa ga sharuddan Musulunci, muna sanar da ku cewa yau Laraba 29 ga watan Sha’aban shekara ta 1443 bayan Hijira, wanda ya yi daidai da 22 ga watan Maris shekarar 2023, an kawo karshen watan Sha’aban na shekara ta 1443,” in ji Sarkin Musulmi.

“Mun samu tabbacin ganin Watan Ramadan daga kungiyoyi da shugabannin Musulmi daga koina a cikin kasar nan, kwamitocin tantance ganin wata na kasa da na jihohi sun tantance kuma mun tabbatar.”

Karanta>>> Fassarar Mafarkin Ruwan Sama

Allah Yasa mu fara a Sa’a

Back to top button