Uncategorized

Allahu Akbar: Shekaru 7 kenan da rasuwar Marigayi Rabilu Musa Ibro

 

A irin wannan rana ta 9 ga watan Disamba 2014 Allah Ya yiwa Rabilu Musa wanda aka fi sani da Dan Ibro rasuwa kafin rasuwarsa kwararren dan wasan barkwanci ne na Hausa a Najeriya mai shiryawa jarumi kuma mai bayar da umarni na fina finan Hausa. Ana kallonsa a matsayin jagoran cigaban masana’antar fina finan Hausa na Kannywood, ya ciyar da masana’antar gaba sosai har zuwa lokacin da Allah ya yi masa rasuwar sa a shekarar 2014.

An haifi marigayi Rabilu Musa Ibro a shekarar 1971. Ya yi karatun Firamare dinsa a Danlasan da ke cikin karamar hukumar Warawa.

Sannan kuma ya yi Sakandare a Kwalejin horon malamai ta Wudil (Teachers College). Daga nan ne ya shiga aikin gidan Yari (Prison Service) a shekarar 1991. Ya yi shekara takwas Ya na aikin Gandiroba inda ya kai matakin insfekto, daga nan ne ya bari ya cigaba da sana’ar wasan kwaikwayo.

Rabilu Musa Ibro ya fara sana’ar Fim a tun ya na aji uku na makarantar sakandare. Ya na da Mata  uku da Yara takwas akwai : Jamila, Kubra, da Auta.

Daga cikin yaransa akwai: Faisal, Jawahid, Lawiza, Abdul-Mummuni, Sannan akwai Asma’u, Annabe, Sa’adiyya, Akwai wani yaro kuma da ya Haifa ya sa sunan mai gidansa wato Baba Yaro.

Kafin Rasuwarsa Ya bayyana Ciroki a matsayin dan wasan hausa abokin sana’ar sa da ya fi burgeshi.

Da aka tambayi Rabilu Musa ibro dan wasan santimental da ya fi burgeshi sai yace “Adamu Usher, ka ga wannan, yana bani sha’awa. Saboda ba shi da girman kai, ba zan manta ba lokacin rasuwar kulu da Yautai, tun daga farkon rayuwa mu na tare da su.” In ji Ibro.

Rabilu Musa ya shahara sosai a harkar fina finan hausa kadan daga fina finan sa sun hada da Andamali, Bita Zai Zai, Ibro Aloko, Ibro Angon Hajiya, Ibro Dan Fulani, wasu wakoki daya shahara dasu sune Bayanin Naira, Idi Wanzami, Direba Makaho.

Kalli cikakken bidiyo


Daga cikin dubunnan fina finansa ibro ya bayyana cewa ya fi son wadannan fina finai “Akwai Kauran Mata, Kowa Ya Debo Da Zafi, da kuma Mai Dawa.

Ibro ya bayyana ya fi son tuwon dawa a bangaren abincinsa, fannin sutura kuma sai yace “Na fi son yadi wanda zan shekara da shi ina gurzawa, ba in sa Shadda ba kwana biyu in ga tana kodewa.

Da aka tambayi Marigayi Ibro a lokacin ya na raye me ya fi bakanta masa rai a kan harkar sana’arsa sai yace“ Ni abinda yake bata mani rai kawai a wannan sana’a bai wuce rashin hadin kan ‘yan wasa ba. 

Rabilu Musa Ibro Ya amsa kiran mahallicinsa ya na da shekaru 43, a duniya. Daga ƙarshe muna rokon Allah ya kyautata makwancinsa In tamu ta zo Allah Ya sa mu cika da imani.

Ameeeeeeeeeeen

Back to top button