Uncategorized

Addu’ar kariya daga sharrin Sihiri, Mayu da Kambun Baka.

Idan kana tunanin anyi maka sihiri ko anyi ma wani ɗan uwanka, ko kuma matsalar Maita (Kambun baka) to ga hanya mai sauki kuma halastacciya.


Da farko dai dole ka sanya hakuri da Tawakkali gami da tsoron Allah acikin zuciyarka. Ka fidda ƙiyayya ko zargi atsakaninka da duk wani Musulmi. Sannan ka aikata wannan fa’idar:

1. Asamu ruwa cikin Bokiti, ka samo ganyen Magarya guda 7 ka dandaƙasu akan dutse da dutse sannan ka zuba acikin ruwan.
Ka tsoma babban yatsan hannunka na dama acikin ruwan. Ka kusanto da bakinka daf da ruwan. Sannan ka karanta wadannan ayoyi da surorin:

1. Fatiha.

2. Suratul Baqarah ayah ta 1-5. da kuma ayah ta 102-103. da kuma ayah ta 163-164. Da kuma ayah ta 255 – 257. Da kuma 285-286.

3. Suratul Aali ‘Imran: Ayah ta 18-19.

4. Suratul A’araf: 54-56. da kuma 117-122.

5. Suratul Yunus (AS): Ayah ta 81-82.

6. Suratul Taaha (AS): Ayah ta 69.

7. Suratul Mu’umineen: Ayah ta 115-118.

8. Suratul Namli: Ayah ta 50-53.

9. Suratul Furqaa: Ayah ta 23.

10. Suratul Saaffat: Ayah ta 1-10.

11. Suratul Ahqaaf: Ayah ta 29-32.

12. Suratul Rahman: Ayah ta 33-36.

13. Suratul Hashri: Ayah ta 21-24.

14. Suratul Jinn: Ayah ta 1-9.

15. Suratul Fili.

16. Suratul Ikhlaas.

17. Falaqi da Naas.

18. Suratul Yaseen.

Kana karantawa, Numfashin karatun yana sauka akan ruwan. Ba zaka cire hannunka ba, sai ka gama. Idan ka gama kayi salati ga Manzon Rahama (S.A.W.) kayi addu’a.

Za a riƙa sha kullum, kuma ana wanka dashi (wato shafawa ajiki baki daya). Har tsawon sati biyu. In sha Allahu kowanne irin sihiri ne, to Allah zai karyashi.

Hakanan za’a iya rubuta wadannan ayoyin da tawada mai tsarki sannan awanke da ruwan Zam zam ko ruwan sama, ariƙa sha har ya ƙare.
Sannan za’a iya karantawa acikin Man Zaitun ko Man Habbatus Sauda sannan arika shansa, ko kuma cinsa acikin abinci. Kuma ana shafawa.
Ana so Marar lafiyan ya yawaita Sadaqah da Istighfari da Salati ga Manzon Tsira (S.A.W).

Daure ku tura zuwa ga yan uwa da abokan arziki.

Back to top button