Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 7 Complete Hausa Novel

 

“Meyasa kikace kar ya sha”

“Nidai kawai kahana shi sha kar ya sha tea din nan”

Jawwad ji yayi gaba daya ta firgice masa

“Amma meyasa kikace kar ya sha?”

Sekuma tarasa mezata ce masa

“Am…emm.. Idan ya sha ze iya yin amai gara kaimasa tofi na ayoyin Qurani ya sha kafin kabashi abinci in Bahaka ba, ze iya bashi matsala eh..m.. In…nima malaminmu ne yafada mana a Islamiyya”

  Da Jawwad yaji haka da sauri yasa hannu ya karbi cup din tea 

Daga hannun Jalal

Jalal ne ya kalleshi

“Meye haka kuma?”

“Kanwarka tace karka sha tukuna, Dan huta ina zuwa”

“Kaga ni bani yunwa fa nakeji yaushe zan tsaya biye maka yarinya Karama tana juya ka”

ya yunkura ze karbi cup din tea daga hannun Jawwad yaji kansa ya kara nauyi dan haka ya koma ya zauna yana jujjuya kan

“Sannu bros”

Jinjina kai kawai Jalal yayi

Kamar yadda Jalila ta gayawa Jawwad yaje fridge ya dakko ruwa ya karanta ayoyin Qurani ya busa masa a ruwan yazo ya tsiyayo a cup ya bashi 

Hannu yasa ya karba ya shanye ya ajiye kofin, ko minti biyar beyi da shan ruwan ba ya mike ya tafi bandaki ya dinga wani irin bakin amai

Jawwad ne ya bishi yana masa sannu ya kwashi mintuna yana amayar da wani bakin abu

Seda Jawwad ya Dan tsorata 

Karanta Littafin>>> Yar Harka Page 1-10 Hot Romantic Hausa Novel

“Jalal mutafi Asibiti your condition is getting worst jin ciwon nan nake kaman a jikina”

Ture Jawwad yayi ya tafi ya kwanta gaba daya jikinsa ya mutu ga wani mugun Jiri dayakeyi

Jawwad ya biyo bayansa, Dan kura masa ido yayi yaga jijiyoyin kan Jalal duk sun mike fuskarsa tayi Ja

Gefen gadon ya zo ya zauna yasa hannunsa akan Jalal yana masa karatun Qurani a hankali 

Wani baccin wahala ne ya kuma awon gaba da Jalal abun mamaki a cikin baccinsa ya dinga Jin sautin karatun Jalila Wanda ya dinga jin nutsuwa tana saukar masa

Jawwad ne ya mike ya nufi gida don tafiya masallaci lokacin salla la’asar yafara gabatowa

Cikin Gida ya shiga ya tarar da Nana tana video game maama kuma ta Dan kwanta a akan kujera tana kallon Nana

Sallama yayi suka amsa gaba daya

“Maama sannu da Gida”

“Yawwa ya jikin Jalal din”?

“Da sauki maama”

“Allah ya sawwake”

“Ameen”

Ya amsa

“Nana babu abunda kika iya se shirme,

Jalila tana can tayi abun arziki ke kam shirirtarki ta fiye miki”

Attention dinta gaba daya Nana ta bashi

“Allah Yaya me Jalilan tayi”

“Gasar karatun Qurani sukaje abuja jiya, tazo na biyu, amma se rikici takewa Ummi wai ita na daya take so”

“Dan Allah Yaya dagaske amma naji dadi, ga fitina ga kwanya Allah sarki Jalila Allah yakara hasken makaranta”

“Ameen kema se ki dage kidena wannan shirmen”

Duk abun nan maama bata ce uffan ba

  “Amma shine ko ta gayamin amma kai ta gaya maka dani take zancen”

Nana tafada tana Dan bata rai

“Aini kullum se munyi waya da ita”

“Ai Yaya dole muje Kaduna we have to celebrate the victory of my great sister bari Abba ya dawo”

Download>>> Ingarman Namiji Complete Document

Nana tai maganar tana murmushi

   “Karki fara, kwata² yaushe ta bar gidan nan kike zancen, wani zakuje to babu inda zaku, nasake naji kin tambayi abbanku zakije sena bata miki rai sha³ kawai,

Kaikuma naga zakewarka akan yarinyar nan yafara yawa ka kiyayeni  Jawwad in bahakaba daga kai har ita senaci mutuncinku,”

Maama ce tayi wannan maganar cikin fada da fushi gaba daya suka bita da kallo

Ajiyar zuciya Jawwad yayi ya dan girgiza kai

“Allah yabaki hakuri ya huci zuciyarki za a kiyaye insha Allah”

Ya Fita yabar parlour itakuwa Nana zunbura baki tayi itama ta barwa maama parlour

“Lallai in ban dageba maganar Yaya mairo na shirin zama gaskiya zakuci kaniyarku sena raba Ku da yarinyar nan”

Se bayan magariba Jalal ya kuma ta shi wannan karon seya jishi sakayau babu ciwon kan se rashin kwarin jiki

Wanka yaje yayi ya rama wasu daga cikin sallolin dabe ba ya bar wasu Jeje ya kira a waya yaji yana ina yagaya masa

Kaya ya canza ya dauki motarsa ya bar gidan kai tsaye club din da yake haduwa da Jeje ya tafi kamar kullum yauma club din cike yake da “ya’yan da suka rasa mafadi maza da mata kowa na sharholiyarsa matan nan wasu sunyi shiga half nicked wasu na rawa yayinda wasu suka kama daki suna shagalinsu 

Jeje naganinsa ya washe baki yana masa sannu da zuwa gaisawa sukayi Jalal yasamu guri ya zauna Jeje ya tafi kawo masa mutuniyar tasa wato giya

Duk gigin matan gurin nan basa zuwa inda Jalal yake saboda sun San halinsa basa gabansa shidai ze sha giya yayi mankas amma be yadda yayi zina ba

Jeje ne yasamu guri ya kira Hanna

” kina ina ne?”

“Ina Gida mana”

Hanna taba shi amsa

“Muna tare da mutuminki fa yanzu haka”

“Dan Allah dagaske dazu Dana kirashi abokinsa yace min bashi da lafiya”

“Ke dalla rabu da wannan sakaran kilma karya yakeyi”

“I wish in samu dama in fito yanzu inzo in ganshi”

“Ke rufamin asiri yanzu ma abu zan karbo masa ke dai kicigaba da kokari”

“Karka damu kaman yazo hannuna ya gama ne”

“That’s good seda safe”

Sukayi sallama da jeje ya tafi bar domin karbo giya 

Bayan ya karbo ne yazo ya nemi guri ya zauna ya Tarar da Jalal yanata salansa yana bawa sama hayaki tabarsa kawai yake sha

Jeje ne ya tsiyayawa Jalal giya a cup ya tura masa gabansa 

Wayar Jalal ce ta fara ringing ya Dakota seyaga unknown number seyaki dagawa ya cigaba da abunda yake haka wayar taita ringing

“Maza wayarka fa ake kira”

Sedayaja wasu seconds sannan yabawa Jeje amsa

“Nagani”

Dan tabe baki Jeje yayi yacigaba da shan giyarsa 

Messages ne suka dinga shigowa wayarsa

Tsaki yayi ya dau wayar yafara duba messages din

       “Haba fitilar rayuwata         meyasa zakamin rowa, just want hear your sweet voice

I really care for u, bazan iya bacci ba in banji muryarka ba love u baby

         From your lovely bae”

Ire² wannan messages dinne ake ta turomasa tsaki yayi sannan ya danyi shiru yana zancen zuci anya kuwa Ilham ce take turo masa wannan messages din, wacece ta kira dazu sukayi waya da Jawwad?

Ya tambayi kansa still wayar ce tafara ringing da Sauri Jalal ya yinkurin dagawa domin yiwa ko wacece rashin mutunci seyaga Jawwad ne yake kiransa dan zaro ido yayi sannan ya daga wayar

“Jalal kana ina?”

Jawwad ya tambayeshi

“Na dan fitane”

“Hmmm daga samun saukinka harka fita ko ka tafi gurin Wanda sukafi kowa mutumci a idonka shikenan seda safe”

Jawwad ya katse kiran mikewa Jalal yayi yadauki mukullan motarsa ze fice

Jeje ya kalleshi

Download>>> Matar Hariji Complete Document

“Ya dai ba dai tafiya zakayi ba?”

“Tafiya zanyi mana dama bana jin dadi Jawwad yaje bana nan naji ransa a bace dole in tafi inje ba shi hakuri”

Wani bakin cikine ya tokarewa jeje ji yayi kamar ya rufe Jalal da duka,

Yadda Jalal baya son bacin ran Jawwad da iyayensa yakewa haka da ya dace 

Anya ba asiri Jawwad yayiwa Jalal ba jeje yayi maganar a zuciyarsa

Shikam Jalal besan yanayi ba dan tuni ya bar gurin

Ilham ce ke ta safa da marwa a dakinta tare da fatan Jalal ya sha tea din nan da se tafi kowa farin ciki gajiya tayi da tunane² dan haka ta yanke shawarar ta dan fita taje gurin Nana 

A daki ta tarar da Nana suna waya da Jalila dan haka ta nemi guri ta zauna daga baya data fuskanci Nana da Jalila take waya seta wani hade rai

“Naji kaman kinyi bakuwa se anjima”

Jalila tayi maganar

“Ba wata bakuwa ceba Ilham ce fa”

“Hh kice Juliet ce, to kice mata a dai dinga sassauta masa adena wahalar dashi”

Dariya Nana tayi tare da fadin

“To Ilham kinji dai sakon Jalila”

Tsaki Ilham tayi dan yanzu ta kara tsanar Jalila mussaman akan abunda yafaru shekaran jiya Jalal ya dinga zaginta 

“Kinga ni na tafi nazo gurinki kina rainamin hankali”

Ilham tai maganar tana mikewa 

Nana tayi saurin rikota tare da kashe wayar 

“Ke bakisan wasa ba indai Jalila ce wataran se ta saki kuka”

Da Sauri Ilham ta kalleta “kamar ya?”

“Eh mana ai ita yayinda taga ba kyason abu to lokacin zata dinga yimiki dan tabaki haushi”

“Wallahi nafi karfin kamata wata Jalila ta Sani kuka”

“A’a dai yadda kike da saurin fushin nan Lokacin daza tasaki kukan ma baki Sani ba

Amma abunda yake burgeni da ita shine akwai kwanya musabaka sukaje Abuja fa tazo ta biyu”

“Ai nasani”

Ilham tabata amsa

“Ya akayi kika Sani?”

“Ke ni mu bar wannan zancen Nana damuwata kullum karuwa take akan Yaya Jalal amma gani nake ba wadda tsana kamar ni”

Ta karasa maganar cike da damuwa 

Nana ta dafa ta

“Ilham ba tsanarki yai ba kinsan shi kawai miskiline baya son shiga sabgar mata mazan ma kinga ba kowa yake kulawa ba Sam baya son mutane watakila fa a ransa yana sonki, inaga Ku da haka naku labarin soyayyar ze fara”

Nana tai maganar cike da kwarin gwiwa

“Dagaske Nana kumafa se hakan yakasance ko?”

“Sosai makuwa wannan ai ba abun mamaki bane”

“Shiyasa kike burgeni Nana bakiji yadda hankalina ya dan kwanta da maganganun nan nakiba”

“Ai irin miskilan mutanen nan abune mawuyaci kagane inda sukasa gaba da wuri karkiyi mamaki sonki yana nan fal a zuciyarsa”

“Allah yasa haka Nana”

“Ai hakanne ma insha Allah Mrs. Jalal to be”

Haka Nana ta dinga ziga Ilham tana kwantar mata da hankali Akan abunda bata da tabbas akai

Jalila tana daki tana gugar uniform zasu koma makarantar boko Ummi kuma tayi bakuwa 

Jalila taji kaman ana harbe² a waje da sauri ta fito tsakar Gida 

“Ummi bakiji karan bindiga ba”

Bakuwar Ummi tace

“Wani captain ne na sojoji yake tarewa a anguwar nan bakiga wani kerarren Gida ba da aka gama kwanan nan ai nasane wallahi gidan ya keru kaman a kasar waje “

“To shine kuma za a zo a cikamana kunne da karar bindiga saboda shirme, ni gidan ma nakeso in gani inga iya keruwarsa”

“Allah yabaki sa’a kije Neman magana duk yadda zasuyi dake se dai suyi dan ba abunda zan iya indai sojojine zaki yabawa aya zakinta”

Ummi tai maganar cikin bacin rai shiru Jalila tayi ta koma daki

Download>>> Ana Dara Ga… Complete Document

Jawwad ne yakema Jalal fada akan fitar da yayi daga samun saukinsa 

Yayinda Jalal ke bashi hakuri

“Ai gani dai na dawo ban zauna a can ba hankalinka ya kwanta”

“Bawani hankalina ya kwanta kabata min raine ka dinga sassautawa kanka wannan abubuwan dakake durawa cikinka”

Hade rai Jalal yayi “naji kuma ina nace kayi hakuri “

“Haka ka iya ai saura ka kara fita”

Jawwad yayi maganar da alamun gargadi

Dariya Jalal yayi 

“Sorry yayana bazan kuma fitaba a yau insha Allah”

Murmushi Jawwad yayi sannan ya fita

Bayan fitar Jawwad 

Jalal ya saka wayarsa a caji ya mike yatafi cikin Gida part din daddy yaje suka sha hira 

Cikin hikima daddyn yake masa nasiha 

“Daddy nima bana jin dadin abunda nake amma kacigaba dayimin addu’a wataran zakaga kaman banyiba”

“Nima ina fatan hakan yaron kirki”

Se kusan shabiyundare Jalal ya fito daga part din daddy shima mummy ce taje part din daddy shiyasa ya fito

Ilham tana kwance akan kijerun parlour tana kallon Bollywood

Waiwayawa tayi taga Jalal

“Sannu Yaya ya jiki?”

“Da sauki”

Rannan a hade Yabata amsa ya fice

Yana zuwa dakinsa ya tarar missed calls kusan takwas

Da wannan unknown number din

Tsaki yayi yaje yayi wanka yazo ya nemi gurin kwanciya ya dakko wayarsa hotonsa ne da Jawwad akan wallpaper dinsa kallon hoton yayi sunyi kyau a hoton matuka murmushi yayi ze bude what’s app dinsa message ya shigo wayarsa budewa yayi

    “Haba baby at least ko sau daya yakamata ka dau wayata kasan kuwa yadda zuciya ta takeyi I feel u in my every heart beat, nayi missing innocent face dinka gashi kaki yadda ko muryarka inji help me baeb na damu da kai

           From ur lovely Bae”

“Wai wannan wace irin Jaraba ce haka, wace ce wannan take Neman yimasa kutse haka a cikin rayuwarsa shi baze iya wannan shirmen ba wannan soyayyar duk haukane da bata lokaci”

Yana cikin wannan mitar ne wayarsa kuma takama ringing unknown number din ce dai

Dagawa yayi a fusace

“Waike wace irin mahaukaciyace karfe nawa yanzu nibana wannan haukan ki kyaleni tun kafin ta kaimu ga bata miki rai”

           “Wow komai naka birgeni     yake baby jin muryan nan taka kawai ta isheni bacci me dadi,

Mark you ba abunda zakamin Wanda ze batamin rai 

Love u…….

Katse wayar yayi ya kasheta gaba daya ya jefa wayar kasa nonsense yafada a hankali

Washe gari bayan sallar asuba Ummi taga Jalila ta koma bacci

” ke baby ba ankoma school ba kwana biyu da komawa amma kina nade a Gida tashi ki shirya yau makaranra zaki tafi”

“Ummi bangama shiryawa ba in nagama zan koma”

“Aikuwa sekin koma yau din nan”

“Ummi bani da socks fa, kuma ni sekin canzamin school bag zan koma”

“Kibari inzo gurin nan baki tashi kinyi shirin makaranta ba ni da kene”

Ummi ta fita daga dakin Ummi na fita Jalila tacigaba da baccinta har kusan karfe bakawai Ummi tazaci Jalila ta tashi amma tana zuwa ta tarar da ita a cikin bargo

Ran ummjne ya baci ta yaye bargon ta Dala mata duka tashi dan kaniyarki dama baki tashi ba tashi kisa uniform kitafi

“Ummi dan Allah kiyi hakuri,  banga socks dina bane”

Girgiza kai Ummi tayi

Download>>> Kwarata Complete Document

“Allah ka shiryamin yarinyar nan, ai tunda baki gadama ba nasan bazakiba zakiga tsiya”

Wunin ranar Sam Ummi taki kula Jalila

Ta dinga binta tana bata hakuri tana mata magiyar ta saimata wata jakar daga karshe seda Ummi ta bata kudin Jaka da socks din hankalinta ya kwanta 

Amma Ummi tace bazata fita ba seda yamma

Washe gari se bayan sallar la’asar sannan Jalal ya kunna wayarsa amma yana kunnawa sakonine sukacika masa waya wasu na bin wasu

“Wannan wane irin Jaraba ce haka”

Sakonta na karshe ya duba  “Baby in baka bude wayarka    ba zanzo har inda kake, tun safe nakasa nutsuwa ko har yanzu baka da lafiya ne?

Na damu da kai baby

         From your lovely Bae”

“Wannan wace irin Jarababbiya ce da take uzzurawa rayuwata ne”

Yana cikin wannan tunanin Sega Ilham ta shigo da kayan abinci ta samu guri ta ajiye

“Yaya ga abinci inji mummy

Harta mike zata fita ya kira sunanta 

“Ilham”

“Na’am”

“Zo nan” seda cikinta yayi kara gabanta ya fadi Allah yasa ba wani abun nayi masa ba jiki a sanyaye ta nufi inda yake guri ya nuna mata kusa dashi ta zauna wayarsa ya dakko ya shiga messages din nan ya nunamata

“Ke kike turomin wannan shirmen ko?”

Gabanta ne yafadi ita ba tuhumar dayake matane ta sata faduwar gaba ba se fargabar wace wannan take shirin yi mata kutse

“Tambayarki fa nake”

Jiki a sanyaye ta daga kai ta kalleshi 

“Bani bace ba”

Jawwad ne ya shigo

“Inyee yau zumunci ake jine Yaya da kanwa”

Basu kulashiba ya karasa ciki ya zauna yaga ran Jalal a bace Yana ma Ilham magana

“To waye?”

Jalal Ya tambayeta 

“Ya za ayi in sani yaya, nidai nasan bani bace”

Tabashi amsa hawaye na gangarowa daga idonta

“Uban me na miki zakimin kuka”

Wani irin kallo tayi masa

“Yaya Jalal tambayata kake meyasa nake maka kuka ko?

Ina nuna kulawata akanka, baka damu dani ba bakajin me nake ji a raina hasali ma ka tsaneni, amma wata a waje tana shirin rusani ga sakonin da take turomaka, kuma kake tuhumata ni ina naga fuskar da zan turo maka wannan sakonnin “

Cikin hargowa ya mike ze zazzaga mata bala’i 

Jawwad ya ga tsananin kishi kwance a idon Ilham, tausayinta ne Yakama Jawwad dan haka  ya dakatar dashi 

“Ilham gaskiya ta fada Jalal”

Jawwad Ya kalli Ilham yace

“Tashi kikoma ciki”

Sannan ya kalli Jalal

Yamma nayi  Jalila ta shirya ta dau kudin safa da Jakarta tayi waje 

Kai tsaye inda ake fadan gidan sojan nan ta nufa daga waje ta karewa gidan kallo 

Aranta take fadin gaskiya gidan nan ya hadu saura kuma inshiga inga meye a ciki yadda ya hadu daga wajen nan cikin kuma ai nasan yafi haduwa.

Download>>> Yaro Ne Complete Document

Daga nan ta mika ta nufi inda zata sayi jaka amma seta hango wani kanti da sojoji a bakin gurin dan haka ta yanke shawarar zuwa taga meye akeyi a gurin 

Kai tsaye ta kutsa cikin kantin wani soja ne ya daka mata tsawa yace ta tsaya a waje se sungama sun tafi tukuna 

“Dan Allah kabari abu zan siya kawai in tafi ni ba gurinka nazo ba “

Zekuma magana wani sojan yace ya batta ta shiga

Tana shiga taga wani babban mutum a zaune akan kujera fuskar nan tashi murtuk babu annuri 

“Ina wuni”

Jalila ta gaisheshi be amsa ba

“Baba gaisheka fa nake nace ina wuni”

Dan juyowa yayi ya kalleta ya danyi murmushi jin takirashi da baba 

“Lafiya kalau sannu yan mata”

“Yawwa”

Ta sai chocolate dinta ta mutumin nan yace abawa Jalila shize biya

Seda ta risina sannan tace

“Baba nagode sosai”

“Bakomai adinga shan chocolate din a hankali yana kashe hakori”

Murmushi Jalila tayi ta  fito “aikin banza na daukama wani abun ake a gurin to me sojoji suke anan ko gadinwa suke oho”

Ta siyo Jakarta ta fito dayake kusa da kantin ake saida jakunkuna 

ta hangi mutumin dazu ya fito daga kantin nan ze shiga mota se ya yadda wallet dinsa da sauri ta je ta dauka, amma tuni sunyi nisa sun bar gurin sun nufi layin gidan wannan sojan

Ta dinga jujjuya wallet din nan kawai ta tafi Gida da wallet din

Bata nunawa Ummi ba ta boye wallet din

Ta faki idon Ummi taje ta dau wallet din ta bude kudin kasar wajene a ciki da ID card bata tsaya bin ta ID card dinba ta aje wallet din cikin sabuwar jakar makarantar ta cikin litattafanta

Washe gari Ummi ta tursasata ta shirya ta tafi makaranta, ta wannan layindai na gidan nan Jalila tabi dan takuma ganin gidan nan kuma ko Allah zesa taga mutumin nan

Tanata kallon gidan wani soja ya kalleta 

“Ke me kike kallo wuce ki tafi makarantar ki”

Ya mutsa fuska Jalila tayi

“Ina ruwanka da makaranta ta?kallo kawai zanyi in tafi”

“Ba a son yawan ganin mutane a arear gurin nan saboda tsaro dan haka wuce ki tafi”

“Did I look like criminal, da uniform dina na makaranta balle kace wani abun zanyi, sekace gidan shugaban kasa naga dai gidan mutum ne ba aljan ba in me gidan yasan bayaso a dinga wucewa ta hanyar gidan ai da seyaje duniyar wata ya Gina gidan ba duniyar mutane ba”

“Kut wace irin yarinya ce wannan?”

Aikuwa sojan nan beyi wata² ba ya zare beilt da nufin ya koya mata hankali se su kaga wasu motoci suna shigowa Latin manyan motoci ne glasses din duk tint ne mutumin jiya da ya sai mata chocolate ne ya fito daga daya daga cikin motocin

Wannan sojan da ya zare belt ne ya kame yana saramasa da ido yai masa magana sojan ya tsaya

“Laa baba ina kwana”

Jalila ta tsuguna tana gaisheshi “lafiya kalau Yar baba, meyahada ki da wannan”

Ya nuna mata sojan nan da ya biyota 

Bata boye masa komaiba ta gayamasa murmushi yayi a ransa yace lallai wannan yarinyar Yar rigima ce amma a fili yace

“Yar baba yanzu kin makara ki tafi makarantarki rabu da shi 

Kai baka ganin Yar makaranta ce kawai daga kallon Gida se a ce za a bigeta ina nema mata afuwa”

Jalila tasaka hannun a Jakarta ta dakko wallet din nan ta mika masa 

Karanta Littafin >>> Macizai ne Page 1-10 Hausa Novel 

“Jiya ka yaddashi bayan kafito daga kantin nan”

Hannu yasa ya karba tasan ce kuwa yana ta dubawa tun jiya be ganta ba yayi zaton yayi miss placing dinta ne

Murmushi yayi “nagode sosai Yar baba Allah ya albarkaci rayuwarki “

“Ameen nagode”

Ta juya ta tafi hanyar makarantar su ta makara sosai amma taci sa’a ba malami a ajinsu dan haka ta shige tanufi ajinsu

Class dinsu ne ya kaure da hayaniya ga Queen ta dawo nickname dinta kenan a makarantar boko Queen J 

Kai tsaye bayan sungama murnar ganin juna da yan ajinsu gurin zamanta ta nufa amma me setaga wata hakima ta hakimce mata a seat Jalila dai bata Santa a ajinsu ba maybe newcomer ce dan haka Jalila tace

“Sannu dai excuse me gurin zama nane ina bukatar zan zauna”

Banza yarinyar tayiwa Jalila 

“Ko kurma ce ne? Nace kifito nan gurin Jalila ne fada tace”

“Wallahi mun gaya mata har malamai sun San nan gurinkine amma tace ita kuma dole anan zata zauna”

Cewar wata daliba

Ita kuwa sabuwar zuwan nan bata da niyyar magana balle Jalila tasa ran zata tashi sema wani kashingida tayi ta kurawa Jalila ido tana hura hanci tana kallon Jalila up and down

“Ke yau kome kikeji zan sauke miki shi yau koda uban me kike yawo wallahi sekin bar seat din nan uwarkice ni a rashin mutunci”

Dariya yarinyar tayi “ok yi abinda zaki iya nikuma na miki alkawarin kawo karshen rashin kunyarki a yau base gobe ba”

“Queen J dan Allah kiyi hakuri ki kyaleta babanta fa babban sojane ranar Monday aka kawota”

Wata dalibar tai maganar tana kokarin Jan hannun Jalila

dukan benci Jalila tayi 

“Wallahi ko Yar gidan bullet ce, ke Allah yasa baban tane AK47 wallahi seta tashi this is my kingdom, in ubanta ya tsaya mata ni Allah ya tsayamin, Kafin kiyi maganina ni zan fara maganin wannan izzar taki, ko kina wa kowa hauka ba ayiwa Jalila”

Hannu biyu Jalila tasaka ta fizgo yarinyar nan daga cikin benci aikuwa yarinyar nan ta wankawa Jalila mari,

Wasu daga cikin dalibai suka tafi kirawo malamai domin raba fadan nan

Amma tuni Jalila ta rama marin nan ta kara mata wani, Jalila ta dage ta hankada yarinyar nan kan bencina nan take goshinta ya fashe jini yashiga fita.

Jinine ya wanke mata fuska ta fasa kara yarinyar tayi, itako Jalila ko ajikinta, hakan yayi dadi² da isowar class mastern su Jalila hankalinsa ne ya tashi ganin duk saurin da yayi Jalila ta riga tayi aika² be kara tsurewa ba seda ya tabbatar da wadda aka fasawa goshi salati yayi, Hanan Abdurrasheed Yar gidan babban captain din sojan ruwa da aka kawo ranar litinin ita Jalila ta fasawa kai shi kansa ba yadda beyiba ya canzawa Hanan gurin zama saboda yasan me gurin tafi kashi doyi wato queen J,  amma hanan yarinyar akwai izza da jin kai, tace ita dole nan gurin takeson zama,

yanzu yasan ba Jalila ba su Kansu makaranta Ta janyo  musu

“Jalila mene haka kika aikata, wannan wane irin shirme ne, yaushe ma kika dawo ne bansaniba memakon kizo kigayamin seki dauki doka a hannu kalli haukan da kikayi”

“Niba hauka nayiba daba ta mareni ba inaga da hakan bata faruba”

“Shut up zaki gane kuranki ubanta sojane insuka casaki inaga daga yau kindena Neman magana”

“Wai da anyi magana se afara maganar babanta sojane, 

Allah sarki mukuma ‘ya’yan Allah bani marasa gata, wallahi ko Yar gidan rocket ce bata isa ta mareni in kyaleta ba”

Ya fuskanci babu alamar nadama tareda Jalila Dan ko kadan bata tsorata da abinda tayi ba itakuwa Hanan tuni aka tafi da ita school clinic akaimata dressing daga nan Hanan bata saurari kowa ba ta fice daga makarantar duk yadda akayi a dakatar da Hanan amma tayi waje ta tafi gida

Jalila aka kira office din director

Aka dinga mata fada kowa da abunda yake fada a cikin malamai wasu abun kirkinta wasu akasin haka ciki hadda wata malama ta zage ta dinga zagin Jalila matar a bayan layinsu Jalila take, Jalila ta taba fada da Yar malamar, Dan haka dama tanajin haushin Jalila.

Karanta Littafin>>> YEL Hausa Novel Document

“Dama wannan yarinyar ba tarbiyyace da ita ba, bata da mutunci Sam dama ina za a samu wata tarbiyya a gurin Yar mace”

Jalila ce ta daga kai da sauri ta kalleta

“A’a madam adinga hakuri Jalila yarinyar kirkice, tana da tarbiyya ita dai matsalarta da students ne ga tarin alkhairanta ga makarantar mu dabazamu manta ba”

Cewar director

“Hmm yallabai baka San yarinyar nan bane uwatta Sam bata son laifinta ita ta sangarta ta lalace, amma yarinya sekace Yar daba, takama Yar mutane ta fitar mata da jini, dama charity begins at home duk abunda yarinya takeyi to haka taga uwatta tanayi”

“Sir kaimata magana kartakuma zaganmin uwa duk zaginta ta tsaya kaina takuma zagina sena rama, uwa ba tafi uwa ba”

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun Jalila ta daban ce 

Jalila koma class dinku yanzu”

Cewar director ita kuwa Jalila ta mike ta koma ajinsu

“Dan Allah kalli yadda take ikrarin zata zageni yarinyar nan kawai a koreta shine mafita”

Inji malamar dazu

“Korarta ba shine mafita ba yarinya ce me matukar kwazo in muka koreta munyi asara babba”

Cewar wani malami

“Hakane kam wan mahaifinta abokina ne bazan taba korar masa ya ba, kuma duk fitinarta bantaba ganin tayiba se yau yanzu dai mahifiyarta zamu  gayyota tazo mu zauna da ita dakuma wakilinta Dan na tabbatar, Yar gidan sojan nan se sunzo makarantar nan”

“Allah yasa suci kaniyarta sumata dukan tsiya”

“Haba madam in “yarkice fa baza kice haka ba ai shi da na kowa ne addu’a yakamata ayi mata Allah ya shirya Allah kalli dai yasan abunda zata zama nan gaba”

Inji director

Hanan ce ta shiga tangamemen palour tana kuka wata babbar mace ce zata yi shekaru arba’in da takwas amma Hutu yasa in ka ganta seka zata batafi shekaru talatin da biyu ba, gefenta kuma ga wani babban mutum shima yana shan tea

“Ke Hanan meke faruwane ne yasameki haka a fuska” 

Matar Tai maganar cikin iyayi da isa

Mutuminne ya kalli hanan shima 

“Auta meyasami goshinki haka meyafaru?”

Hanan kuma fashewa da kuka tayi ta kwashe abinda yafaru da karya ta fada tace Jalila tamata duka ta dinga gwarata da bango tana zaginta

“Amma auta kin bani kunya kamar ba Yar Dana Haifa a cikina ba ki tsaya wata yarinya tamiki duka hada fasa miki goshi kamata yayi insa bulala in zaneki ai”

  “Wannan wace irin magana ce kakeyi haka a dakar min yarinya haka daga shigarta makarantar, wace Yar marasa galihun ce ta isa tayiwa y”ata haka in kyaleta wallahi senaga gatanta a gurin nan senaga uban da ya tsaya mata, se nasa an kulleta daga ita har ubanta”

“No ban yadda ba kinsan ita Hanan din metayi yarinyar tayi mata haka mubi komai a hankali ki bari gobe in Allah ya kaimu da kaina zanje makarantar indai yarinyar ce bata da gaskiya semusan abinda yakamata muyi’

” daddy ance mata baba na soja ne fa amma secewa tayi wai ko Yar gidan bullet ce, Allah yasa Kaine AK47″

Abun ma dariya yabawa baban Hanan

“Lallai yarinyar nan tana da karfin hali”

Itakam Maman Hanan iya wuya ta kulu taso ace baban Hanan ya kyaleta data nunawa yarinyar banbancin civilian da kuma kaki, zata so taga uban daya tsayawa yarinyar nan ko baban Hanan be saniba seta koyawa yarinyar nan darasi seta nuna mata banbancin dake tsakanin yayan farar hula dakuma “ya’yan rainon bullet. 

    Tun kafin a tashi daga school wannan malar taje gidansu Jalila tagayawa Ummi abunda Jalila tayi bayan haka hadda cewa itama Jalila ta zageta tsaf 

Hankalin Ummi yayi matukar tashi da jin abunda Jalila tayi taita bawa malamar hakuri

Ilham ta dawo daga makaranta amma har taje ta dawo bata fuskanci komai ba, kamar yadda Daren jiya batayi bacci ba tunda Jalal ya nuna mata messages din wayarsa da yake tuhumarta akai, hankalinta yaki kwanciya tun jiya take takura kwakwalwarta domin kokarin gano wadda ke turowa Jalal wannan sakon amma takasa tuna komai, a iya saninta ba ya muamala da mata, to ta Yaya? wacece wannan take kokarin rusa nawa shirin ita ta kafa kanta,

Jikinta a sanyaye taje tayi wanka amma takasa cin abinci “ko gurin Nana zanjene ko zata tayani gano wacece ta, tambayi kanta

Kodayake yanzu ta dawo daga makaranta kar in takuramata koma inje tana wayar da wannan sha³ Yar uwatta ta

Da sauri Ilham ta mike JALILA tafada a fili, tabbas JALILA ce itake turomasa wannan sakonin dan babu Wanda yakewa Jalal shishshigi in ba itaba iya sanina Jalal baya kula mata ko a family 

  Amma indai na kara bincike na tabbatar Jalila ce sena yi maganinta babu wata “ya mace data isa tayi takara dani a soyayyar Jalal, wallahi JALAL nawane ni kadai, duk macen datayi yinkurin yin takara dani senaga bayanta

se yanzu nagane wato duk wannan shishshigin da take masa Ashe sonsa take 

To ba ta isaba wallahi

Download>>> Cousin Ne Complete Romantic Novel Document

Koda aka tashi daga makaranta Jalila hankalinta kwance ta taho gida tare da kudurcewa a zuciyarta setaje gidan malaman nan data ce mata ‘Yar mace ta mata warning dan bata hakura ba, 

Gida ta tafi ta shiga da sallama amma Ummi bata amsa mata ba dan haka kai tsaye dakin Ummi ta nufa 

Ummi nakan sallaya ta idar da salla tana lazimi Jalila ta wuceta ta canza kaya zuwa towel taje tai wanka tai salla tasaka uniform din islamiyya amma still Ummi bata kulata ba

“Ummi wai baki ganni bane, yau ko sannu dazuwa bakice minba se fushi kike wai mena mikine?”

Still Ummi batace mata komai ba gaban Ummi taje ta zauna

“Ummi wai meyene”?

Janyota Ummi tayi gabanta ta zuba mata kyawawan maruka guda biyu

” wato Jalila duk kokarin danake akanki inkika fita abinda zuciyarki tagaya miki shi kikeyi,

Kin fasawa Yar mutane goshi, kinzagi malamanki wannan itace tarbiyyar danayi miki ko?

To yanzu zankira Abban Jawwad in aka kashe case din nan gobe in Allah ya kaimu,

Koshi ko Jawwad wani yazo ya daukeki sukoma can kanon dake,

Lokaci yayi dazan koma dangina kema kikoma hannun wan ubanki tunda ba kya tausayina,

“Yar gidan babban captain fa na sojoji Jalila me nake dashi da Zan iya wannan rigimar dakika dakko, kano zaki koma nagaji, gaskiyar mahaifinki kafin yarasu da yace tarbiyyar mace seda tsayayyen namiji bazan iyaba Jalila nagaji”

“Har anzo angaya miki karya da gaskiya kekuma kin yadda ko Ummi to walla…..

” rufemin baki Dan ubanki”

Da sauri Jalila ta kalli Ummi bata taba jin Ummi tayi zagiba

“Akan kujerar zama ko? kikayi wannan aikin ko ubankine ya sassaka kujerar kokuma akai na  haifeki dazaki daki Yar mutane akai kujerar banza,

Kuma saboda baki da kirki ki dubi malama ramatu Dan an miki magana ki zageta ko Jalila”

Se yanzu Jalila ta gane malama ramatu CE tazo tagayawa Ummi

“Wallahi Ummi malama ramatu munafuka ce bafa haka..

” Ai bazaki canza ba, hali indai nakine bazaki canza ba agaban nawa ma kuma zagin malamar ki kike ko?

“Wallahi niba malama ta bace yan primary take koyarwa bata taba koyamin uwar komai ba”

“Yayi miki kyau ina fada kina fada”

“A’a Ummi Dan Allah kiyi hakuri karkiyi fushi bazan karaba”

“Aini nagama yanke hukunci Abbanku zan kirawo azo a maidake kano, nima gurin nawa dangin zan koma”

“Ummi wai dagaske kike, dan girman Allah kiyi hakuri nace mikifa bazan karaba ni wallahi bazan koma kano ba”

“Sekuma kiyi ai tunda ni kin rainani gara kikoma gaban Zainab itace daidanki”

“Na shiga uku wallahi Ummi kafata kafarki ko bangon duniya zaki tafi ko a kafa sena biyoki, wallahi bazan kuma ba dan Allah Ummi, wallahi banason zuwa kano”

Banza ummi tayi mata ta dakko wayarta tana kiran Abba yayinda Jalila ke gabanta tanata faman kuka

Jawwad ne ya dawo daga makaranta ya gaji matuka kaya wanka yayi yai salla ya tafi gurin Rabin ran nasa wato Jalal

“Dan uwa ka dawo daga makarantar kenan sannu da zuwa”

“Yawwa bros Sannu da hutawa”

Jawwad yafada yana Neman gurin zama 

“Nagaji sosai Jalal,”

“Nagani a idonka ai yau kukayi tests din ko?”

” eh yaune Alhamdilillah test din duk se godiyar Allah sunyi sauki sosai kuma hada jajircewar ka da addu’arka proud of you dan uwana rabin jiki”

“Kajika kaifa kake karatunka bani nake maka ba wannan kan naka akwai ja mutumina i wish nike da kwanyarka”

“Amma fa ka zageni Jalal, kasan ban isa inyi karatun dakayi a bayaba in kana waje wayake Neman irinmu, Jalal wai yaushe zaka koma makaranta ne kai?”

“Zan koma amma ba yanzuba, bana son wannan zancen zomuje muci abinci”

“A ina kuma ga abinci can a Gida zuwa nayi muje mu ci”

“koma inane muje daganan kasha ice cream ka dan huta, ka huce wannan gajiyar “

“Kaikake koyamin kwadayi fa”

Dariya sukayi gaba daya

“Kasan wani abu Jawwad?”

“A’a seka fada?

Download>>> Kadangaruwa Complete Document

” wallahi wata mayyace take uzzurawa rayuwata gashi tayi hiding number balle insata a black list, kullum seta kirani kota turomin messages ni na rasa yadda zanyi, wallahi na gane wacece setayi Dana sanin wannan gangancin da take min”

Dariya sosai Jawwad yayi 

“To kai meye abun damuwa aciki, dan ance ana sonka”?

“Mtseww kai kafiya shirme Jawwad ni bani da lokacin wannan shirmen, inyi rayuwata ni kadai ya fiyemin, duk yayinda ka gayyoto mata cikin rayuwarka kamar ka gayyatowa kanka matsalane”

Dariya  Jawwad ya dingayiwa JALAL seda Jalal yafara jin haushi sannan ya dena

“Jalal wayagaya maka mata matsalane, mata ni’ima ne, tabbas akwai daga cikinsu masu matsala, amma akwai na kirki sosai, soyayya akwai dadi mussaman in kayi dace da mosoyi na kwarai, bazaka gane hakan ba seka fada tarkon soyayya”

“Hmm mata duk matsalane indai irinsu Ilham ne duk matsalane”

“Hmm bazaka gane ba Jalal”

“Eh naji bazan ganeba”

“Lokaci ze ganar da kai ai”

“Eh naji mutafi”

Jeje ne yakira Jalal yana son su hadu Jalal 

Shikuma yace masa ya fita shida Jawwad bazeyiwu su hadu yanzu ba

Gurin cin abinci suka tafi shida Jawwad

Bayan sungama cin abinci ne suna hira aka kira Jawwad lambar Ummi yagani ya kara nutsuwa ya dau wayar 

“Salamau alaikum Ummi barka da rana”

“Yawwa barka Jawwad ya kake ya mutan gidan”

“Kowa lafiya Ummi ya Jalila”

“To lafiya kalau za a ce meyasamu lambar abbanku nakira bata shiga”

“Inaga inda yake ne ba network, amma lafiya Ummi”

Ajiyar zuciya Ummi tayi ta kwashe kaf abunda yafaru tagayawa Jawwad

“Yasalam Ummi kiyi hakuri insha Allah komai zezo da sauki, yanzu bana Gida idan na koma zanwa Abban bayani insha Allah, kiyi hakuri Ummi dan Allah kinsan har yanzu yarinya ce”

“Ba batun yarinta  Jawwad tsabar rashin hankaline kawai

” adai yi hakuri Ummi “

Haka dai sukayi sallama Jawwad ya dafe kai 

“Ohhh my God sisy ba dai rigima ba”

“Ya dai meyafarune?”

Jalal ya tambayeshi, Jawwad ya kwashe komai ya gayawa Jalal,

Dariya Jalal ya dinga yi kaman wani tababbe

“Kan bala’i wannan yarinyar Yar bala’ice wallahi, kaga zancena ko Jawwad, nagaya maka mata matsalane, mussaman irin wannan kanwar taka zama da ita seda panadol”

“Hmm haba Jalal kaima kanwarka ce, Jalila bata son raini bata yadda da wulakanci ba nidai fatana Allah yasa kar baban yarinyar yayi mata wani abu”

Wata dariyar Jalal yakumayi

“Kamar ya kar yayi mata wani abu “yarsa fa ta Daka, aigara suko yamata hankali yadda gobe bazata kuma ba,”

Yayi maganar yana dariya 

“Haba Jalal Yar gidan Abee ce fa, in duniya da gaskiya bekamata kace haka ba”

“Hakane Jawwad kaima kace wani abu amma kasani bataji, in mutum yana rashin kunya in besamu dai² da shiba baze dena ba

  “Wow tauraro a cikin taurari kaina mussaman ne ban taba tunanin kana dariya haka ba, bakaga yadda dariya kemaka kyauba”

Gaba daya suka waiga domin ganin me maganar Hannah ce budurwar dasuka hadu da ita wancan karon, tayi maganar tana karasowa inda suke guri tanema ta zauna

“Jarumin maza meyabaka nishadi kake wannan dariyar haka ka fi ko yaushe kyau ko dan uwan ne yake baka nishadi”

Ta karasa maganar tana kallon Jawwad

“Uban wa yace kizo inda nake, me kike Nema a gurina ne kin uzzuramin kindami rayuwata meye hakane, waima wayagaya miki ina nan da kike bina”?

  Wani kasaitaccen murmushi Hannah tayi

“Call me by my name Hannah, or any special name u choose,

Kasan ita zuciyoyin masoya kaman wireless ne, our hearts and souls are always connected, dan hakazuciyarkace tagayawa tawa zuciyar kana nan shiyasa nazo kuma nayi sa’a nasameka zuciyarka kawai nake bukata Jalal, in har kabani zaka huta da nacina, akasin haka kuwa zan cigaba da hanaka sukuni cikin dare ko rana har sekabani abunda nakeso”

Wani wulakan taccen kallo Jalal yai mata ya watsar da ita bece mata komai ba

Jawwad ne ya danyi gyaran murya 

“Kinaji Hannah already Jalal akwai wadda takeson Sa kanwarsa ce kuma kinga…..

Dagawa Jawwad hannu Hannah tayi

” haba dan uwan masoyina meye laifina anan dan ina kokarin cikawa zuciyata burinta, kowa iya allonsa ya wanke, tayi nata kokarin nima inyi nawa wadda tai galaba ta kafa soyayyarta a zuciyarasa shikenan, ni Hanna babu macen data isa tayi takara dani akan soyayya,

Jawwad son danakewa dan uwanka ko matansa hudu sena kori biyu ya aureni saboda space din daya yamin kadan,

Kar ace rashin adalcin nawa yayi yawane da se ince seya kori kowa ya aureni saboda shidin nawane ni kadai”

Saroro Jawwad yayi yana kallonta

“In kagama jin tatsuniyar kazo mutafi inada abunyi” Jalal yafada yana mikewa

Hanna ma mikewa tayi tazo gabansa kaman zata shige jikinsa se wani irin fitinannen kamshi take 

“Babyna kabani dama ko sau dayane in gwada maka yadda nake sonka mana, kuskurewa bukatata shizesa incigaba da uzzura maka har gidanku nasani zaka iya ganina a kowani lokaci, karkayi mamaki nasanka farin Sani a yadda kake a haka nake sonka, zan iya komai akanka, kagayawa kanwarka ta janye kudirinta na sonka ta barmin kai in bahakaba”

Ta kashe masa ido daya daga nan tai tafiyarta,p babban abunda yabawa Jalal mamaki dayakasa yimata komai

Jawwad ne ya janyo hannunsa suka hau motarsu suka nufi Gida

“Jawwad ka yadda mata matsalane, abunda zuciyarsu ta raya musu kawai shi sukeyi, yanzu ga haukan da wannan tayi min, amma zan dau mataki akai”

“Kabi komai a hankali Jalal, kasan in mutum yana kan ganiyar so makancewa yake so ba karyane ba, ka dena wulakanta Wanda yace yana sonka kai baka san a ya zaka fara taka soyayya ba,

Amma wannan Hannah ka nemi tsari da sharrinta because Dana kalli cikin idonta ya tabbatar da she mean what she said”

Haka suka cigaba tattaunawa har suka iso gida

Bayan sallar isha’i Jawwad yaje part din Abba ya tarar dashi shi ka dai, yagaya masa abunda ya faru jinjina kai Abba yayi 

“Hmm Jalila iya rigima, halin mahaifinta ta dakko bata son raini Allah ya kaimu goben, zan San yadda za ayi”

Da asuba Abba ya taho kano be gayawa maama abunda ya faruba ya dai cemata zeyi fitar asuba zashi wani guri

  Still wannan Daren ma messages din Hannah suka dinga shigowa wayarsa seda yagaji ya kashe wayar 

Washe gari da safe Jalila ta shirya ta tafi makaranta, Daren ranar addu a ta kwana  tanayi 

Ba wai Allah ya sassauta fitinar da ta dakko ba, se dai Allah yasa kar Ummi ta korata kano

  A hanyar makaranta ta hadu da yayan lubabatu data tsokana ranar akayi Sa a ya ganeta, ta Ganshi sarai amma taki guduwa tacigaba da tafiya a hankali,

Zuwa yayi ya sha gabanta 

“Ke karamar Mara mutunci ni kika zaga ranan ko waike Yar iska”

“Wallahi kasake ka tabani sena tara maka jama’a nace zaka lalata ni shekara goma sha hudu ce zakayi a gidan yari bayawa”

“Au tunaninki barazanar ki zata hanani in casaki senaga uban da ya tsaya miki”

“Bari kaji in gaya maka idan kana shan kwayarka tagaya maka karya kayiwa mutane hauka, to karkayi gangancin gwada kwayarka akaina,

Dan wallahi sena kulla maka sharrin dazaka kare rayuwarka a prison”

Kafin kace meye wannan Jalila ta ware murya ta fara ihu iya karfinta hankalin jama’a ne yafara dawowa Kansu ana fara taruwa ta silale ta gudu ta nufi makaranta

Abunda yasa ta guduma gudun kar takuma shiga wata cakwakiyar bata fita daga wadda take ciki ba ga Ummi tace zata maida ita gidan su Jawwad da setasaka anmasa duka

  Tana zuwa ajinsu ta tafi taje gurin zamanta ta hakimce ba tareda ta kula kowaba, “Allah ya biya Queen J Dama tunda yarinyar nan tazo kanta yake hayaki, se wani takama take, malamai ma kaman wani tsoronta sukeji segashi kinyi maganinta”

Haka dai seatmates dinta suka dinga zigata ita dai Jalila hankalinta yana kan batun Ummi

Bayan anfita break an dawo ba dadewa Hanan ta shigo ajin tana kallon kowa a wulakance ga malami a ajin amma Hanan batabi takan malamin ba ta tako

Tazo gaban Jalila

“Sannu uwar rashin kunya, dama na miki alkawarin kawo karshen rashin kunyarki,

Yau zakigane kin taba Yar gidan bullet kizo office bullet yazo da kansa”

“Amma kin bani kunya da kikazo da bullet kawai, ai na dauka barikin zaki dakko gaba daya su taho da egwa yadda in sun markadeni baza ageneniba dan dai bullet, ai bullet yayi kadan aga bayana dashi”

Jalila takarasa maganar hade da tsaki”nonsense “

Mikewa Jalila tayi tai gaba ta wuce hanan

Wato Jalila Yar bala’ice babu alamar risina a tare da ita tun tasowar Hanan take taka Wanda taga dama take jefa tsoro a zukatan duk Wanda yai kuskuren shiga hanyarta saboda takamar ubanta wani ne amma yau ta hadu da wadda tafita rashin mutunci

Haka ta bi bayan Jalila suna zuwa harabar ofishin director Jalila sukayi clashing da malama ramatu aikuwa Jalila ta tsaya

“Ita wutar munafiki ko tana karkashin jahannama ne, 

Kekam baki dace da malamar makaranta me bada tarbiyya ba kema kina bukatar me baki”

Jalila ta gayawa malama ramatu sannan tai gaba abinta

Tana shiga office din director ta tarar da mutane ba Wanda ta kula kuma bata kalli suwaye a ciki ba ta shige.

Yayan Hanan se kallon Abba yake kaman yasan shi.

Tunda Jalila ta shiga office din taje tasamu guri ta durkusa kanta a sunkuye kai kace wata mutumiyar kwarai ce

Ga director na makarantar, ga Ummi, da Abban su Jawwad, sekuma baban Hanan da yayanta, se mukarabbansa da suke waje bakin office din sekuma Jalila da hanan dasuka shigo yanzu

Baban Hanan Bin Jalila yayi da kallo sannan yayi Murmushi a zuciyarsa indai wannan ce zata aikata don bata da tsoro

Kanta a sunkuye tace “Abba ina kwana”

“Lafiya kalau Jalila ya rashin ji”?

Shiru tayi ba tace komaiba

“Abbanki kawai kikasani ko Jalila,?”

Director ya tambayeta batace komai ba still shiru tayi

“Was nake gani haka kadai ace Yar baba ce wannan?”

Da sauri ta dago ta kalleshi dan murmushi tayi se yanzu ta ganeshi mutumin nan ne daya hana wannan sojan zaneta, Wanda ta tsinci wallet dinsa

“Sannu baba ina kwana”

“Lafiya kalau Yar baba”

“Dake akayi fadan kenan, dama haka kike da fada, ai wannan sister dinki ce” ya nuna hanan

“Ni ba sister na bace nikadai Ummi ta Haifa, se kanwata daya Nana” Jalila tai maganar ba tare data dago ba

Dariya tabasu gami da mamaki babu nadama a tare da Jalila ita haryanzu a ganinta ba laifi tayiba tunda ita aka takala da fada

“Daddy wai kasantane”?

Yayan Hanan yai tambayar yana kallon mahaifinsu

“Eh nasanta ‘yata ce shekaranjiya Allah yabani ita”

Baban Hanan yabada amsa

Ya kalli Abba da Ummi 

“Ai Dana San itace ma bazanzo ba yarinyarku mutuniyar kirkice, fitina CE kawai ta yara kuma ga dukkan alamu bata son wargine ko Yar baba?”

Ya tambayeta yana murmushi 

“Komai ya wuce amma Yar baba kidena Neman magana kinji yarinyar kirki kin dagawa mamanki hankali da babanki, gaskiya suna sonki dayawa”

Gyada masa kai Jalila tayi

“To baba na dena insha Allah”

A ranta kuwa tace dama wai wannan shine captain din da ake ta fada wani salihi dashi haduwar mu biyu be tabamin rashin mutunci irin na sojoji ba

Ni na daukama zanga tunda ga bakin office anfara kwallo dani

“Daddy wai yanaga ka maida abun jokes jini fa ta fitar min kuma ta zageka”

Hanan tai maganar cikin shagwaba da hawaye a idonta

“Ohh sorry dear itama yata ce daga yau na hadaku kawance”

“What ba dai dani ba wallahi, Allah ya kiyaye”

Hanan tai maganar cikin tsiwa

“Baba nikuma na karbi kawancen nagode sosai daga yau tazama kawata”

Jalila tai maganar tana murmushi tare da kallon hanan

“Allah yayi miki Albarka Yar baba”

Abun ya daure musu kai yaushe mutumin nan yazo anguwar amma har yasan Jalila gaskiya a sojojin ma yana da matukar kirki, gaba daya kasa cewa komai sukayi

“Daddy ni gani nayima tana kama da Hanan wallahi”

Yayan Hanan ya fada yana kuma kallon Jalila 

“Nima nagani Abdallah”

“Kinsan Aliyu Usman Imam”

Yayan Hanan ya tambayi Jalila 

Dagowa Jalila tayi ta kalleshi

“Kai Yaya Jawwad kake nufi ga Abbanmu nan” ta nuna masa Abba “no wonder naga suna kama kuma ance  shine abbanki shine class ref dinmu a BuK yana da kirki ga kokari amma gaskiya shi ba fitinanne bane kamarki”

“Waze hada ma shi Jawwad yaron kirkine kaman ma ba  sunansa Aliyu ba amma wannan sekace kura saboda fada”

Ummi tayi maganar tana nuna Jalila

“Dan Allah kuyi hakuri bazan karaba Insha Allah”

Takoma gaban Abba shima ta tsuguna

” Abbana Dan Allah kaima kayi hakuri nadena insha Allah, Dan Allah kuyi hakuri”

Kara birge baban Hanan tayi tasan tayi laifi kuma ta bada hakuri, ita damuwar iyayenta ce bata so yaji inama Hanan ce keda wannan tarbiyyar tayi laifi tabada hakuri ai sedai in kaga dama ka kasheta ko ka barta da rai amma bata laifi ta bada hakuri indai Hanan CE

Director ko a ransa yace lallai wannan yarinyar ita fushin iyayenta ne a gabanta bata damu data bawa su Hanan hakuri ba suda akayiwa laifi a fili kuwa yace

“To Alhamdilillah tunda itama ‘yarka ce mungode da wannan karamci naka yallabai,

Kamar yadda ka fada Jalila yarinyar kirkice saboda a dalilinta makarantarmu tasamu awards, tana da kokari ga hazaka, muna alfahari da ita a cikin dalibai, ita babba damuwarta ita da dalibaine, shima kuma insha Allah daga wannan shikenan tace bazata karaba”

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Director yayi maganar yana kallon Captain Abdurrasheed 

“Hakane dama dan Adam Tara yake be cika goma ba, muna kara bada hakuri dai ayi hakuri”

Abban Jawwad ne yai maganar yana kuma kallon baban Hanan

Itakam Jalila bataga dalilin bada hakurin dasu Abba suke tayi ba

“Karku damu ba komai yariga ya wuce ai, Allah ya shiryamana yara gaba daya, yayi musu albarka”

Suka amsa da Ameen gaba daya

Haduwar da akayi domin hukunta Jalila da yin sasanci se yakoma haduwar hada zumunci inda hira ta barke a office din director

Malaman da suke ta jira suga an fara casa Jalila se sukaga akasin haka

Daddyn Hanan ne yagaya musu yadda yasan Jalila daga ranar da ya saimata chocolate zuwa tsintar wallet dinsa, har exchanging lambar waya captain yayi da Abba, sukayi sallama kowa ya watse 

Ummi ta saka Jalila a gaba Abba ya dauke su zuwa Gida

“Impossible wallahi a fitarwa da yata Jini sannan kace wai ba komai ka kyale yarinyar ta daki banza akan me?

” look safiyya shi da na kowane, kinsan halin Hanan sarai itama wani lokacin ta fiye fitina, da wulakanta mutane, for now ayi hakuri na rufe wannan case din”

“Aikuwa be rufu ba ni a gurina, dan mene Za a daukarmin yarinya sannan kace ka rufe case, waye uban yarinyar da yatsaya mata ta dokarmin yarinya”

“Ohhh my God mum Abdallah kinfiye rikici fa, wallahi ba Yar wani bace ba kawai dai she’s so kind, yarinyar and she regrets what she did, ni yarinyar ma tausayi tabani wallahi mamanta duk ta damu, gashi kuma kanwar abokin Abdallah ce”

“Kaga ya isa haka bana bukatar jin wani abu ya isheni haka, ko uwar abokin Abdallah ce senasa an koyamata hankali balle wata kanwar aboki, in kai ka hakura ni ban hakuraba wallahi… 

” Enough “

Ya daka mata tsawa nan take ya juye ya koma sojansa fuskar nan kaman be taba dariya ba

“Idan kika kuskura kikayi wani abu akan yarinyar nan kinsan meze biyo baya kinsanni sarai”

Yayi maganar cikin tsawa sannan ya fice ya bar mata dakin

“Wai Jawwad meyake damunka ne tun dazu ka kasa zama, ka kasa tsaye se zagaye kakeyi”

Jalal ne dake kwance akan gadon Jawwad yai maganar yana kallon Jawwad

“Ta yaya zan iya zama bansan wani hali akeciki ba ko sojan da Jalila ta dakarwa yarinya ya hakura, bansan me ake cikiba nakira wayoyinsu gaba daya basu daga ba Allah yasa dai lafiya, Allah yasa basuyi mata wani abun ba”

Jawwad yai maganar cikin damuwa

Dariya Jalal yayi “to meye abun tada hankali in suka karairayota se ka tafi Kaduna jiyya”

Jalal ya karashe maganar yana dariya

Tsaki Jawwad yayi Wanda yayi dai² da ringing din wayar Jawwad

Da sauri ya dakko wayar yadaga a zatonsa Abbana

“Hello hey Aliyu yakake”

“Ina lafiya Alhamdilillah , amma ban gane me magana ba”

“A Rasheed ne”

Aka bashi amsa

“Ohhh Abdallah ban dauki muryarka bane, kuma bani da wannan lambar taka”

“Wallahi kuwa na canza layine”

“Allah sarki ya kake ya mutan gidan”

“Kowa lafiya Alhamdilillah, yau naga kanwarka”

“Kanwata wacce kenan ai Nana tana kano”

“Ba itaba wata Jalila”

Gaban Jawwad ne yafadi

“A ina kaganata ya akayi kasan kanwata CE?”

Download>>> Silar Fyaɗe Complete Novel Document

“Sabani suka samu da Hanan mummy ta daga hankalinta mukaje nida daddy, har muka hadu da abbanku”

Ajiyar zuciya Jawwad yayi sanan yace

“Alhamdilillah Abdallah ya ake ciki Dan Allah kuyi hakuri kabawa daddy hakuri,”

“Karka damu, ai ba abunda yafaru daddy yace “yarsace itama, kanwartaka ce Yar daruce Aliyu bata da tsoro”

“Nagode sosai Abdallah,”

“Ba komai Aliyu, nima kanwata CE, kuma wani abun mamaki suna matukar kama da Hanan din”

“Allah sarki Dan Allah kayimin godiya agurin daddy”

“Ba komai Aliyu girmankane “

Sukayi sallama, nannauyar ajiyar zuciya Jawwad yayi tare da fadin

“Allah gatan bawansa, kaga abun mamaki Jalal, Allah ya tsallakar min da baby, basuyi mata komai ba, Ashe kanwar abokina CE sukayi rigimar da ita, kanwar A rasheed CE yarinyar”

Dariya Jalal yayi

“U escape this time around, se Ku kiyayi gaba, Dan ba kullum ake kwana a gadoba”

“Eh munji, for now we are safe, se dariyarka ta koma ciki”

Jawwad yayi maganar yana kallon JALAL yai murmushi tareda shafa sumarsa

Jalila CE da umminta se Abban Jawwad a parlour

“Inaga lokaci yayi dazaka cika wasiyyar mahaifin JALILA, ka dauketa ta koma gabanka, nima in koma Gida, JALILA ba ta jin magana, kullum cikin Neman magana take, bataji Sam abunda zuciyarta ta raya mata shi takeyi, ayi mutum ba hakuri kullum cikin Neman magana”

“Haba ummina tun jiyafa nake baki hakuri ashe baki hakura ba

Nace fa bazan kara ba”

Jalila tayi maganar idonta taf hawaye

“Yi min shiru bazan hakuranba, ke banda Allah yasa mutumin kirki ne baban yarinyar nan da yanzu wani zancen ake ba wannan ba,

Ke ba Yar uban kowa ba, amma har kina ikrarin ko Yar gidan bullet ce ko, 

Kanaji har wallet ya Yar ta dauka, da sunyi bincike suka ganota a gurinki sunanki barauniya, wannan halin naki in kika cigaba a haka to wahala zaki sha, ayi mutum fada kaman kura”

Abba ne ya nisa ya danyi murmushi sannan yace

“Haba ummu Jalila, babynki fa ba haka kwai takeyiba,

Kin manta marigayi shima haka yake baya daukar raini, gashi na jama’a kinfi kowa sanin halinsa ba wasa”

“Amma be kai wannan yarinyar ba, JALILA fa da kudinta seta saka ta sai rigima koda uban waye,

Duk rigimar Abu Jalila mutumne simple kuma yana da kawaici, amma ita sun raba hanya da hakuri”

“Ummu Jalila kenan kin manta biyuce ta hadarwa Jalila, kefa jinin sarauta ce akwai wannan izzar ta sarauta a jikin Jalila, haka zalika mahaifinmu, babansa shine sarkin Fulani a rigarsu, kinga ba yadda za’ayi Jalila ta yadda, da raini Jinin sarauta na zagayawa a jikinta

Mikewa Jalila tayi ta bar dakin ta koma dakinta ta kifa akan katifa tana kuka, bataji sallamar Siyama ba saboda kukan da takeyi se kawai ganinta tayi a gabanta, dafa Jalila Siyama tayi

“Aminiya meya faru? Garinya haka ta faru a school? Jiya da yau banjeba bana jin dadi dazu ake gayamin abunda yafaru tsakaninki da hanan nasanta babanta abokin Abba ne Sam bata da kirki Yar gadarace”

Siyama tayi maganar cikin damuwa

“Kinga ni ba itace agabana ba

Aminiya kinji wai Ummi sena koma kano gidansu Yaya Jawwad nikuma wallahi bazan komaba bana son zaman garin nan”

“To aminiya saboda me? Meye a ciki Dan kin koma?”

“Au haka zakice ko? Dama ba kya sona, hmm Dan bakisan abunda dangin Maman su Nana din nan sukemin ba, ga wannan mugun abokin Yaya Jawwad din, Siyama bana son rabuwa da Ummi wallahi tun jiyafa nake bata hakuri amma taki hakura yanzuma zancen takeyiwa Abba fa”

“Ki kwantar da hankalinki aminiya, nasan kawai dan kin bata mata Raine amma bazata bari kikoma yanzu ba”

Mikewa Jalila tayi ta dakko wayarta ta fara kiran wayar Jawwad

Lokacin Jawwad ya tafi masallaci yabar wayar a dakin

Dan haka Jalal ya duba wayar cwt sisy ya gani akan screen din wayar

Tsaki Jalal yayi, ya daga wayar amma yayi shiru bece komai ba

“Yayana dan Allah ka kira Ummi kabata hakuri, tun jiya nake bata hakuri amma taki hakura, tace sena dawo kano, dan Allah yayana, ka tayani bata hakuri maybe kai inka bata hakuri ta hakura wallahi nadena sata magana, bazan iya rayuwa babu ita ba “

Tai maganar cikin sheshshekar kuka

Bece komai ba ya kashe wayar

“Fitinanniya kawai yanzu ma kin kira danki kuma daga masa hankali, shikuma duk yabi ya wani rude ya biyemiki, kina son ummin kike daga mata hankali “

Yai maganar cikin mita bayan h ya katse wayar, kuma kira Jalila tayi amma yayi rejecting kiran ya kashe wayar gaba daya,

Jalila ta dubi Nana

“Nana Yaya Jawwad yayi fushi dani, yaki cewa komai, kuma ya kashe wayar Sa”

Share mata hawaye Siyama tayi

“Calm down Aminiya, seta yiwu beji dadin abunda kikayi bane, amma shima ze huce”

Download>>> Kadangaruwa Complete Document

Abun duniya duk ya ishi Ilham tarasa abunda yake mata dadi gaba daya wani mugun kishine yake damunta akan Jalal, se yanzu take tabbatarwa kanta tafada soyayyar Jalal fiye da yadda take tunani,

Dan haka bayan an tashi daga makaranta gidansu ta wuce taje tasakawa maminta kuka ta gaya mata abunda ke faruwa

“To kekam meye na damuwa duk kin daga hankalinki kalli yadda kika rame fa, naga dai Soyayyar ta wucin gadi ce burinmu na cika shikenan”

Mami a gurinki ce soyayyar dan lokaci ce se yanzu nagane dagaske soyayyar Jalal ta Huda zuciyata bana tunanin zan iya rabuwa da shi ILHAM tai maganar a zuciyarta 

A fili kuma tace

“Mami duk da soyayyar wucin gadi ce amma kuma in shirinmu ya rushe fa?”

“Inkinga shirinmu ya rushe to sakacinkine, indai kika dage komai zezo dai² da yadda muka tsara, kedai kicigaba da amfani da magungunan danake karbo miki, sannan duk abunda zemiki na wulakanci kidena fushi kici gaba da binsa,

Randa ya shigo hannunmu kuma”

Bata karasaba se wani Murmushi da mamin tayi 

“Kiyi kokari ki gane wadda take turamasa sakonnin, itama zamuyi maganinta”

gyada kai Ilham tayi cike da kwarin gwiwa, Aranta tace “da kaina zanyi maganin ko wace, Jalila kinyi gangancin fara soyayya da abunda nakeso zakiga tsiya”(nikam nace Allah sarki Jalila bata San anayi ba)

Haka Ilham ta shirya ta nufo hanyar gida, harta wuce part din Jalal kawai ta dawo ta nufi hanyar part dinsa tana zuwa kofar bedroom dinsa ta tsaya tana tunanin me yakamata tayi

Shikam Jalal Yana kashe wayar Jawwad shikuma tasa wayar tafara ringing lamba ce amma ba suna dan haka beyi tunanin komai ba ya dauka

“Oughhh baby tun safe banji muryarka ba ina kewarka sosai

A ina zamu hadu ne please, am missing you so badly, said something please, ko muryarka inji mana”

“Waike wace irin mace ce Mara kamun Kaine? Ki rabu dani nagaya miki meyasa kike min shishshigi ne bana son yi miki rashin mutunci fa”

  Wani murmushi Hannah tayi cike da kissa ta kara kashe murya cikin shagwaba tace

  “Babyna komai zaka kirani dashi fa bazanji haushi ba, ni komai naka burgeni yake, ko da zakamin duka ne a gaban jama’a, I wish halinku daya Da Jawwad da komai yazomin da sauki, nasan da shine ze tausayamin halin danake cikin amma a yanzu ma karkayi tunanin zan karaya, yanzu ko ka fadamin inda kake ko inkira Jawwad in tambayeshi, kuma ko inane biyoka zanyi”

“Karki fara Jawwad daban ni daban, Jawwad ne yake lallabaki, kuma shi yahana tun farko in nuna miki waye Jalal, kishiga hankalinki, wannan shine gargadina dake na karshe

Ilham dake bakin kofa kuwa daskarewa tayi

Ya tabbata Jalila ce Wato dama Jalila ce kenan, itace take son Jalal take turo masa messages haka, gashi yana cewa yana kyaleta saboda Jawwad, lallai Jawwad ma munafiki ne 

Wani baking kishine ya ciwota Bata San lokacin data karasa dakin ba tasa hannu ta fizge wayar daga hannun Jalal tayi jifa da ita tana wani irin huci wayar ta tarwatse a gurin.

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button