Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 33 Book 2 End

  

Tunda aka gama biki Maama bata dawo ba, seda takuma kwana goma a Bauchi, taji dadin zaman garin sosai, gashi mutane ne masu karamci da son ‘yan uwa, Abba ne yazo ya dauketa suka koma gida kanon dabo. 

Bangaren Angwaye da Amare da sukayi Auren soyayya Se shan soyayya da kauna suke, tsakanin su banda Jalila da Jalal da babu wanda yake neman wani  a tsakanin su,

Jalila ita wannan zaman hutun ya isheta, ita dama kano suka batta tayi zamanta a gurin Maama ya fiye mata wanna zaman.

Tana ta zancen zuci ne Husna ‘yar gidan Anty ta shigo da waya ta mikowa Jalila, Jalila tasa hannu ta karba, video Call ne ta ďaga wayar tana ďagawa taga fuskar Jawwad cikin sauri ta mike zaune 

“Yaya Jawwad kaine?”

“Nine Baby, yaya borno yasu Anty?”

“lafiya kalau Yaya Jawwad, kayi kiba sosai kaman ba kaiba, ina Hanan?”

“tana kitchen tana girki, kema gaki nan kinyi kibar ai, ya mijin naki?”

Tabe baki Jalila tayi tace “yana can lagos” Hanan ce ta taho da gudu ta haye kan cinyar Jawwad tace 

“Hi queen, ya kike?”

“Wow Hanan, wannan kwalliya haka, masha Allah, naji dadin ganinku wallahi nayi farinciki, Allah ya albarkaci rayuwar aurenku, yara muku kaunar juna”

Tausayinta yakama su Jawwad, Hanan tace “Jalila kunyi waya da Nana kuwa?”

“Eh munyi waya da su, ya Abuja ya zaman kadaici?”

Jawwad yace 

“muba ma zaman kadaici ko My sugar, masu zaman kadaici suna Azabtar da zukatansu sun san kansu” yai maganar yana kallon Hanan, Hanan tace “Sosai makuwa, ba wani kadaici, kullum muna tare, kema kice akaiki gidan mijinki kigani in zakiji wani kadaici”

“Allah ya kiyaye” Jalila ta fada tana harar Hanan. Wayar Jawwad ta fara ringing, Jalal ne yake kiransa, Jawwad yace 

“Baby mijinki ke kirana, bari inje in amsa” Hanan ta zauna akan kujera tace “Jalila wai yaushe zaku sauke wannan taurin kan ke dashi ku fuskanci juna?”

“Hanan ya kikeso inyi ne? Nagaya muku Jalal ba sona yake ba, kawai an lika masa ni ne, tun lokacin biki nake rashin lafiya be nemeni ba, ko ta kaina bayabi, se ranar da ze tafiya ya ajiyemin takadda, sam be damu dani ba, Hanan ku kukayi dacen Auren soyayya amma bani ba, nasan da Ahmad na Aura baze watsi da lamarina ba” kan Jalila ta gama maganar har hawaye ya wanke mata fuska. Cikin taushin murya Hanan tace

“Jalila, kina da Aure yanzu be kamata kidinga ambaton wani namijin ba, Sannan Jalila kinsan halin mijinki tun kafin kuyi Aure, bashida shiga sabagar mutane, dukda ke matarsa ce yanzu, Amma kiyi hakuri, komai ze wuce Jalila, kalli yadda kikayi kyau kamar a saceki a gudu, i wish yana nan yaga wannan kwalliyar taki se ya rude, waima me suke bakine kikayi wannan kyan”

Murmushin takaici Jalila tayi tace

“Hanan kenan, kina tunanin zanyi wani abu daze gani ya yabane? Ko ya burgeshi, shi ba sona yake ba kawai an aura masa ni, be damu da yasan a halin da nake ba balle ya yaba kwalliya ta, se an jima ki gaida Yaya Jawwad. 

Jalila ta ajiye wayar ta dora sabon kuka me sauti. 

ji tayi an dafata, ta dago ta kalli wanda ya dafata Husna ce fuskarta dauke da damuwa tace 

“Sorry dear, please stop crying, kidena kuka ko tunanin broz Jalal baya sonki, is not like that, ina kula da yadda kuke share juna kedashi, which is total bad, an riga an daura Aurenku, kamata yayi ku manta da abunda ya wuce, Jalal has a social disabilities at times, tun lokacin da yakoma drunker, mutane suke kyamarsa he decided to isolate himself from the people, he dint interact with people as before, believe me he loves you bazaki gane hakan ba sekin zauna da shi, yanada kirki sosai, ki dena yawan kukan nan please “

Jinjina mata kai Jalila tayi Husna tace

” Yawwa mrs Jalal, Jalal bashi da matsala bayan ta shaye2, zaki maida shi yadda kikeso, yana sonki ne shiyasa yakeyin abunda kike so, ba dan haka ba a duniya akwai abunda ba wanda ya isa Jalal yayi wani abun yayi. Husnah ta cigaba da rarrashin Jalila, a lokacin take gayawa Jalila Tanada Aure, mijinta baya gari ne, shiyasa itama tazo tayi zamanta a gida. 

Ilham takasa zaune takasa tsaye, kwanata kusan shida a gidansu suna sakawa da warwara akan yadda zasu bullowa lamarin ita da umanta, yanzunma zancen da suke kenan 

“Umma kin san kashinmu ya bushe idan yarinyar nan ta tare da Jalal, aikin ze lalace ne fa, zamu rasa komai, jiran da mukayi tsawon shekaru mu dauki fansa ze tashi a banza ne, indai yana tareda yarinyar nanmun rasa komai, daular da muke hange bazamu sameta ba” 

Umman Ilham taja numfashi ta hura hanci tace

“Bazan taba yadda tsawon wannan lokacin daukar fansa ta ya tsaya akan lalacewar Jalal ba, dole in wulakanta khadija in mallake dukiyar da take takama da ita, sena ga ta wulakanta daga ita har Habib din” 

Ilham tace “Umma to tayaya?” 

“ki kylaeni kawai, nasan abunda zanyi, tunda ke kinkasa abunda ya kaiki gidan tsawon lokaci” 

“Umma kenan, ba kasawa nayi ba, nayi iya yina, ba daban wannan Jalilan ba da tuni an wuce gurin, Amma ni hankalina a tashe yake umma, kin san abunda Aure ga Jalal yake nufi fa a shirin mu, so soyayya da wata mace bayanni ga Jalal kim san barazana ce a garemu, wallahi ko bacci bana iyayi” 

“ni nace ki bar komai a hannuna, nasan me zanyi” 

“Shikenan Umma” 

Mummy har gidansu Jawwad taje da kanta, ta tarar da Maama tana ta fama da aikin gida. Cikin fara’a Maama ta tareta tana mata sannu da zuwa 

Aikuwa a fusace mummy tace

“kinga niba yashe bakinki nazo gani ba, ba hakoranki nazo ki nunamin ba, baban su Jawwad na nan ne? 

” A’a baya nan lafiya kuwa? “

” ina fa lafiya, saboda tsabar munafunci a haďa kai da ke a cuceni, a Aurawa Jalal wannan yarinyar dake kanki kinsam bata da cikakken Asali, meyasa baki yadda an

An aurawa ďanki ba se nawa ďan, wannan yarinyar mara mutunci akan me?  Sumi2 da ita kamar ta Allah amma tana bin ďana”

Maama tace

“Subhanallah  ni kaina ban san da batun ďaurin aurensu ba se ana i gobe ďaurin Aure, kuma iyayensu mazane suka yanke wannan hukuncin baniba, da amincewar mahaifinsa aka aura masa ita” 

“ke kikasani koma suwaye suka amince, saboda tayi kwantai tarasa miji se abawa ďana, Allah kadai yasan abunda aka dukunkune aka bashi” 

“Mummy Jalila ba kwantai tayi ba, tanada masoya, Allah ne yayi matarsa, Sannan be kamata kidinga wannan maganganun ba karkizo kiji kunya wataran kamar yadda naji kunya nima, Ni data zauna taredani tayi zaman hakuri dani na tabattar Alkhairi ce ga rayuwar Jalal, a irin zamanbda tayi a hannuna nasan halinta”

“kinga dan Allah ki sauraramin bana bukatar jin wa’azinki, tunda baya nan, ki gaya masa ya shirya karbar karamar bazawara, dan sena kashe Auren nan, ban ga dacewar Jalal da wannan yarinyar ba” 

Maama tace “Shikenan duk yadda kika gani, komai ya samu bawa mukaddarine, dadinta ma ďan naki ba wani kintsatse bane balle aji haushi dan an rabu da shi, naga ke kanki baki isa da shi ba, temaka masa akayi aka bashi yarinyar nan, kuma duniya da gaskiya baki isa ki biya Jalila da mahifiyarta abunda tayiwa ďanki ba”

Maama takarasa maganar tareda shigewa ta bar Mummy a gurin. 

Mummy ta dawo gida tana cizon ya tsa, tana tunani iri2 a ranta. 

Jalila hankalin ta ya ďan kwanta, Husna na debe mata kewa suna hira lokaci zuwa lokaci, sannan duk lokacin da ta keso zata ari waya takira wanda takeso, Mijin Antyn Jalal professor Aliyu Ishaq  yana koyar da darasin turanci a saudiyya, be fiye zama ba, yana da tarin Ilimi, gashi mutumin kirki ne, yana da barkwanci da raha, Girmama shin da Jalila da take da yadda yaga tana gudanar da Al’amuranta yasa take burgeshi, yayiwa Jalal murnanr samun yarinya me kwazo da tarbiyya kamar Jalila. Be kara sarewa da lamarin Jalila ba seda Antyn ta bashi labarin irin Abubuwan da Jalila ta dingayi da kokarinta akan rayuwar Jalal, ya zamana Jalila tana sakewa da shi fiye da kowa a gidan, kamar yadda Ake kiransa Abee haka take kiransa, Jalila tana son mu’amala da mutane masu ilimi dazata Amfana dasu, indai Abee ze fito parlour Jalila zata zauna Suyita hira tana masa tambayoyi akan abubuwa da dama, shikansa duk lokacin da be ganta ba ya dinga tambaya tana ina kenan, yana mamakin kaifin hankalin ta da basirarta, gata da ilimin Addini “

Yauma na gama dinner, Amma Jalila tanata hira da Abee tana bashi labarin irin fituntunun data dingayi lokacin kuruciya suna ta mata dariya, Hajiya Salma tace

“Nikam Alhaji Aliyu me kayiwa Jalila haka take sakewa da kai hada hira, mu kaman tsoronmu ma takeji” 

Jalila tayi murmushi tace “Bahaka bane ba, Jalila Aliyu Imam, shine cikakken sunana, kuma Kafin Babana ya rasu Abee nake ce masa” 

Anty tace “Haba shiyasa wannan shakuwa haka, Ashe ya da uba ne” 

Abee yace “Eh ya ranku, yata kuma sirikata kuma malamata” 

Zare ido Jalila tayi tace “Wace ni, se dai in durkusa a koyamin, Seda safenku” Jalila ta fada tana mikewa tsaye, sukayi Sallama ta tafi dakinta. 

Bayan tafiyarta Abee yace “Kuna ganin raba yaran nan yanada wata fa’ida ne? Yana can matar tana nan” 

Anty tace “Eh mana, muna so mugane dagaske yana sonta ne kokuwa?” 

Abee yayi murmushi yace “Lallai kun manta waye ďan naku ne, shikenan Allah ya tabattar da alkhairi, Amma nayiwa Jalal murna samun yarinyar kirki kamar ta, tanada hankali sosai” 

Haka dai suka cigaba da tattaunawa. 

Jalalila kamar kullum ta gama wannan wankan turaren, ta shirya a cikin wata doguwar riga, dayake Anty sunyiwa Jalila sayayyar kayan sawa dana kwalliya tana kan wani karamin kujera tana gyara gashin ta. 

Husnah ce ta shigo dakin tana murmushi tace 

“Maigidanki yana hanya, broz Jalal zezo ba sanarwa ba komai, kuma nasan badan ke ba bazamu ganshi ba, tashi muje ayi masa girki, Anyiwa me kitso waya tana hanya, ki taso muje” 

Hade rai Jalila tayi tace “ba wani girki da zanyi, kuma ni ku kyalemin kaina a haka” 

Husnah tace 

“Haba Sister meyasa haka ne?” (nikam nace baki san halin Jalila da taurin kai ba) 

Jalila tace “wai meye Amfanin inta bawa kaina wahala akan wanda be damu dani ba? Watana daya da kwana Goma a gidan nan ko ta waya baya kira balle yaji ya nake, seni zan ta faman wahala akansa” 

Ajiyar Zuciya Husnah tayi tace 

“Kina da gaskiya Jalila Amma hakurin dazakiyi yanzu baze kai na baya ba, ki bari ki kama shi a hannu, daga nan seki rama, taso muje su Mummy suna parlour” 

Jalila bata da zabi sena ta mike tabi bayan Husnah, suna zuwa parlour Hajiya Salma tace 

“Yawwa Jalila, Jalal yayi waya yakusa isowa maiduguri, me kitso tana hanya, dama lallanki jiya akayi shi, in an gama kitson kafin ya karaso ayi masa girkin. 

Jalila ta samu guri ta zauna ba tareda tace komai ba, Husnah ta zauna a kusa da ita tana mata magana kasa2

“please sister idan yazo karki hade masa rai haka, karki biye masa dan Allah, ki bawa mara ďa kunya” 

Ita dai Jalila jinsu kawai take. 

Tunda Daddy ya tafi be kara dawowa Nigeria ba, Mummy tarasa me yake mata daďi, in dai Jalal ya zauna da yarinyar nan to zata kwace mata shine gaba daya, dan tun kafin ya aureta ma yana sonta tunda yanajin maganar ta, tarasa ta inda zata bullowa lamarin, gashi a yanzu tasan bata isa taje maiduguri tayi musu tijara ba. 

Kafin Jalal ya karaso har angama yiwa Jalila kitso, kitso akayi mata kanana sosai, gashi hannunta ya sha lalle, duk inda ta gifta kamshi take, ga fatarta ta kara kyau se sheki take. 

Anty tace ” Jalila me yakamata ki girkawa Jalal ne? Mara nauyi sosai tunda naga alamar shigowar dare zeyi” 

Dan zumbura baki Jalila tayi tace “befiye cin Abinci da daddare ba yafi shan tea ko fruit, wani lokacin koya ci Abinci seya sha tea da daddare” ta fada tana dan tura baki cikin ko in kula

Boye dairiyar su sukayi, banda Husna da seda ta dara, tace “Ya akayi kika san haka?” 

“Nike musu girki shida Yaya Jawwad a gida” tabata amsa

Anty tace “Ke Husnah ina ruwanki ne? Jalila ki dafa masa abunda kika ga ya dace kawai” 

Jinjina kai tayi ta tafi ďakinta. 

.

Seda ta tafi sukayi dariya, Hajiya Salma tace “Kai lamarin yaran nan sesu, ni ban san wanda yafi wani taurin kai a cikin su ba, ana so ana kaiwa kasuwa” 

Anty tace “Jalal yafita taurin kai, bafa yanzu yafara sonta ba shi, Jalal ya dade yana sonta, nasan komai, Dan yaga ya samu yanzu shine yake basarwa kaman be damu da ita ba” 

Hajiya Salma tace

“Aike ta hannun damansa ce kinsan komai akansa, Allah ya daidaita tsakani” 

Suka Amsa da Ameen 

Lokacin sallar magariba Jalal ya iso gidan, ya sha tafiya dan a mota yazo ya gaji sosai, Jalila bata san ya karaso ba, har bayan sallar isha’i tana palourn Abee yana mata bayani akan wani littafi da yake son wallafawa, Husnah tana gefe tana dan tsoma musu baki lokaci zuwa lokaci, zaman da Jalila  tayi da su tafara gane yarensu kadan2, kaman gaisuwa da yaren. 

Suna hira kai kace ‘ya da ubane, Anty ta shigo palourn tace

“Jalila kina nan, tun dazu Jalal ya iso fa, nazata kina can kina shiryawa ne, kije ki shirya ki kaimasa Abincin” 

Jalila ta dan langabe kai tana kallon Anty. A ranta tace “Sekace wani mijin kirki ko wadda zata biki anata in shirya, bayan nasan ko kallo ban isheshi ba” 

Abee ya kalli Anty yace “Madam jeki zamuyi magana da’ yar auta ta” 

“to shikenan nidai ayi Sauri, in ba sokuke yayi zuciya ba ya tafi” ta fada tana shirin barin palourn tareda yin murmushi, Ameera tana zaune bata fita ba. 

Abee yace

“Jalila tambayar ki zanyi, ki gayamin tsakani da Allah, in dai kin baban dani ki gayamin kina kuwa son Jalal?” 

Taji ya mata tambayar ba tareda ta shirya jin hakan ba. 

Hade fuska ta danyi tace “Ni dai ban sani ba ko ina sonshi, shima fa baya sona” ta karasa maganar kaman tana shagwaba

Fuskarta ya kalla, Akwai alamar kuruciya sosai a tareda ita, yarinya ce me tunani irin na manya, Amm lokuta da dama kuruciya tana dawainiya da ita. 

Yace “Shikenan daughter Allah ya daidaita ku, ki cigaba da hakuri zaki fara sonsa, Mijin kine yanzu, ki manta da halinsa kinemi Aljannar ki, kuma insha Allah komai ze wuce” 

Jalila tace “to Abee nagode” harzata fita Husnah tace “Jirani muje in miki kwalliya, nasan idan na kyaleki ba zakiyi ba” 

Ta tasa Jalila a gaba zuwa ďaki, ta ďakko mata wani material baki da adon jan flowers, riga da skirt ta mikawa Jalila ta karba tana zumbura baki ta saka, tayi kyau sosai, Husnah ta bata turaruka ta shafa, kamshi dai kam ya riga yagama kama jikin Jalila a gidan nan, Husnah tace

“bari in miki kwalliya” 

“ni ba wata kwalliya daza’a yimin” 

“Jalila ya hakane? To sa kwalli da jan baki mana” 

Jalila ta saka kwalli se jan baki Ja, tasaka kwalli, tayi kyau sosai, Husnah ta bata karamin gyale Ja akanta, Jalila ta kalli kanta a mudubi, kayan nan sun kamata sosai ta kalli Husnah tace “Nikam gyalen nan yayi min karami gaskiya, ki bari in saka babba” 

“Haba Jalila, gurin mijinki zaki fa, Mijinki ne ba wani ba, in kuma kinki in barki da su Mummy” 

Husnah tasata gaba zuwa Kitchen ta shirya mata kayan Abincin a tray ta rakata har kofar palourn da Jalal yake tace

“please Jalila don’t mess up, karki bani kunya dan Allah” 

Jalila ba tace komai ba ta shiga gabanta se faduwa yake yi, Sallama tayi sannan ta shiga, bata tabaccin ya amsa sallamar nan tata. da farko dakin kamshin turarensa yakeyi, Jalila na shigowa kuwa temperature dakin ta canza zuwa kamshin turaren jikinta, kallo daya tayi masa ta dauke kanta, kanan kayane a jikinsa amma yayi kyau sosai sumarsa se kyalli take, duk ya dena saka wannan kalar dayake wa gashinsa, ya dora kafarsa akan center table, ko a ina zata ajiye tray din oho, ta gefen ido ya dan saci kallonta, tana zuwa bata kula shi ba ta ajiye tray din a kasa, ta juya zataje ta zauna hakan ya bashi damar kare mata kallo, tubarkallah she has a very beautiful heart and body structure, Jalila tana da kyau ga kyakywan surar jiki, ga zuciyarta me matukar tausayi, matsalarta taurin kai da Izza wani lokacin. 

Taje ta nemi guri ta zauna a kujerar da take kallonsa ta dora kafa daya kan daya tana kada kafa tareda dauke kanta gefe tana wasa da yatsun hannunta. 

Jalal a ransa yace ‘Tsabar wulakanci ko ta gaisheni kota ce min ya hanya ba ruwan ta dani, hakan na nufin dagaske bata sona ne? Ko kuma tsabar rigima da taurin kaine? ” Jalal ya gaza gano amsoshin tambayoyin sa, to bata kulashi da sannu da zuwa ba ma balle yasa ran zata zuba masa Abincin. 

Kallon ta ya kumayi, kayanta cif jikinta ga mayafin iyakarsa wuyanta, hanun nan yayi kyau da lalle, kanta ba dan kwali dan haka yana iya ganin tsagar kanan kitso dake kanta. 

Itama Jalila a ranta mita take “tsabar wulakanci koma ya tambayeni ya nake, bayan tafiyar sa ya na karke, ya tafi ya barni ba lafiya koya bugo waya yaji ya jikina, ya sani a gaba da kallo yaki cin Abincin in baze ci ba ni in tafi, mtseww ta danyi tsaki, tsakin ya fito fili ba tareda sanin ta ba. 

Saurin dagowa yayi suka haďa ido ta basar. 

Mikewa yayi ba tareda ya kalli inda Abincin yake ba ya mike ze fice, itama ta mike da sauri tasha gabansa suka tsaya suna kallon Juna, lokaci na farko da suka kasance tare tun bayan daura Auren su

“lafiya meye haka?” ya tambayeta

“ya zan kawo Abinci ka tashi baka ciba? Salon in koma ayita tuhuma ta” 

“in sun tuhumeki kice su koya miki yadda ake kula da miji, dan baki iya ba” Ta dan yatsina fuska ta kalleshi 

“Waye mijin? Aini banga miji anan ba, kaima yakamata a koya maka yadda ake kula da mace dan….. Se kuma tayi shiru ganin yadda ya kura mata ido, Ashe fa yanzu mijinta ne, ba kowace magana yakamata ta gaya masa ba

“Ni kike cewa bakiga Miji anan ba ko?, Nagode sosai, matsa kibani guri in wuce” 

Hanya ta bashi ya fice daga dakin, bata bi ta kan kayan ba itama tayi waje abunta. 

Washegari ma da Safe Aka sa Jalila ta kai masa Abinci, haushin taki kulashi jiya yasa beci Abincin ba yakuma barinsa. 

Yana fita ya tafi gurin Abee, bayan sun gaisa Abee yanata tsokanarsa, Jalal yace

“Abee so nake kasa baki su kaimin matata, ko in dauketa mu tafi basu sani ba” 

Abee yace “A’a baza’ayi haka ba ai, kwantar da hankalinka, ko gobe kake so za’a kaimaka ita zan saka baki suba ka ita, na goyi bayanka tunda Daddynka yana jin nauyinsu, ina dalili kanada Aure amma sun barka kana ta fama sun rike maka mata” haka Abee ya lallaba Jalal ya tafi. 

Yaje yasamu Anty yace mata “kinga tun wuri kubawa yaron nan matarsa yana son abarsa, yamuku kawaici amma kunki ganewa” 

Anty tace “Abee Akwai dalilin da yasa muka riketa anan ne” 

“A’a Ku bashi matarsa kawai, in baso kike kiga tafara miki laulayi a gidan nan ba, sannan ku kwasheta ku kaita” 

Zare ido Anty tayi “Haba dai” 

“Eh mana, yanzu da muka rabu da shi yake gayamin insa baki ku bashi matarsa” 

Aimin hakuri fa rashin posting akan lokaci, abubuwa sunyimin yawa, adinga min uzuri nagode da kulawarku

Vote and

Share please 

I want comments not stickers or just thanks 

Daga alkalamin Aysher cool 

🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️

What’s app only 07063065680. 

Follow me onWatpad @Ayshercool7724 

                        

    🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 

                  *ABDUL JALAL*

             _Story, writing and edited _

                             

                            By

                  AISHA HUMAIRA

                  ( _Daddy’s girl_) 

*PERFECT WRITER’S* 

*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ’𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼’ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

            PART 2         

                          _PAGE 5️⃣2️⃣ 105

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam. 

Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka

Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba. 

Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina

07063065680 

Or email address @ www.humaira17@gmail.com

Watpad @Ayshercool7724 

      

             _MY FIRST NOVEL _

Zare ido Anty tayi tace “gaskiyane Abee, tunda ya iya budar baki yace a bashi matarsa he mean it, zanyiwa Anty Salma magana gaskiya, a bashi iga suje can su karata, tunda be san abun Arziki ba” 

Abee yace “gara dai kuyi tunani, wannan ba mafita bace ku bashi matarsa kawai” 

Tunda Abee ya bashi goyon baya A ranar Jalal ya shirya ya tafi kano ko sallama basuyi da Jalila ba, dan in dai suka hadu fada zasuyi. 

Yayi waya da Daddy ya gaya masa yana son zeyi magana dashi, Daddy yayi masa Alkawarin zezo Nigeria su hadu a kano. 

Ba zato ba tsammani Ilham ta dawo taga motar Jalal a harabar gidan, ai a guje takarasa cikin gidan ta nufi dakin  Mummy tana kwala mata kira, 

“Mummy Kinsan Jalal ya dawo kuwa?” 

Mikewa Mummy tayi “dagaske ko wasa”? 

“Wallahi dagaske nake, ga motarsa can” 

Jinjina kai Mummy tayi tace “Shikenan rabu dashi, nasan tunda yazo Akwai abunda ya kawo shi, kyleni da shi kawai”

Ilham ta koma dakinta tana cigaba da tunanin wani mataki Ummanta ke shirin dauka akan wannan lamarin, Itakuma me yakamata tayi? 

Wasa2 kwanan Jalal uku da dawowa amma sam Mummy bata sa Jalal a idonta ba, da kanta taje dakin Jalal amma baya nan. 

Ilham ma duk yadda taso taga Jalal bata ganshi ba, ko ina yake tafiya oho?. 

Bangaren Jalila kuwa sekuma shan gyara takeyi, basu gaya mata Jalal yace zasu koma kano ba.

Kwanan Jalal hudu a kano sannan Daddy ya dawo, koda ya dawo babu wata tarbar Arziki daya samu daga Mummy se mita da masifa, Bebi takanta ba ya cigaba da sha’anin sa, babban abunda yake kular da ita kenan, tasa shi agaba taita masifa Amma ya kyaleta yaki kulata.

Ranar da Daddy ya dawo da daddare Jalal ya shigo, ba kowa a palourn dan haka ya wuce part din Daddy, shikansa Daddy yaji dadin ganin Jalal, 

Daddy yace “Ango, Ango se wani kyau ka keyi, alamu hankalin ka a kwance” 

Jalal ya dan bata fuska yace

“Ina wani hankalina a kwance yake, Kawai su Anty sunje sun rike ta a can gurinsu ko mene amfanin hakan oho?” 

Daddy yai murmushi yace “Tunda sukayi haka Akwai dalili” 

Jalal ya dan hade fuska yace

“koma meye dalilin nasu ni munyi magana da Abee zan dakkota tazo ta tare” 

“Jalal meyasa kai haka? Zasu ga kaman bakayi musu kara ba” 

“Daddy sati guda da komawa makaranta yakamata ace ta koma itama, sannan kasan in dai da Auren nan idan nazo kano bani da masauki, bani kwanciyar hankali saboda masifar Mummy indai nazo gidan nan, nasan bata son Auren nan, nikuma inason abuna, kaga ko nazo Kano a gidana zan sauka baseta ganni ba bazan zo mata gida ba” 

Murmushi Daddy yayi yace “koma dai meye she’s your Mum, yakamata ka dinga mata uzuri sannan ka dinga hakuri da ita” 

Jalal yace 

“Daddy maganar gidan da zan zauna ne yasa nazo Kano fa” 

“to wane gidan zaka zauna, gadon kayan zaka koma kokuma yaya?” 

“No bazan koma gadon kaya ba, zamana a gidan nan zena tunamin abubuwan da suka wuce masu batamin rai” 

“to ya kake so ayi?” daddy ya tambayar yana bawa Jalal attention dinsa

“gida zan siya a tarauni, a can zan zauna in danyi nesa daku, bana son yawan fitina ko hayaniya, Gobe in Allah ya kaimu se muje ka tayani zaban gidan” 

“hmm Jalal kenan, to ai tunda bani zan zauna ba, kai da ita matar taka yakamata ku zabi gidan da kuke so” 

“Kyaleta kawai duk gidan dana zaba baza tace beyi ba” 

“to shikenan ina fatan kun daidai ta kanku babu matsala” 

“karka damu Daddy, in Allah ya kaimu gobe muje a siyi gidan, ka gayawa Abba, next week Insha Allah in basu kawo ta ba, zanje in dakko ta” 

Daddy kallon Jalal kawai yake, jalal din maganar sa yake kansa tsaye kuma hankali kwance ba wata kunya ko makamancin haka a tare da shi. 

Suna ta hirarsu ba zato ba tsammani sega Mummy ta shigo ďakin, seda ta danyi turus ta tsaya, ganin Jalal da tayi kanan kayane a jikin Jalal kaman yadda yasaba sakawa, Amma abun mamaki dogon wandone har kasa a jikinsa, da riga me dogon hannu, wuyansa babu sarka, sannan babu wannan askin banzan da yakeyi kuma ya sawa kan color duk babu, yayi kiba abunsa kuma fuskarsa ba laifi a sake yana murmushi, sabanin da da kullum fusakarsa a murtuke. 

Idan lissafinta dai2 ne kimanin watanni shida bata ganshi ba ko a waya baya kiranta, dama ina ta kai matsayin da Jalal ze aje lambarta balle ya kirata.

Jalal yace “Daddy in aka siyi gidan se a sai furnitures ma in saka, kayan kitchen ban san kansu ba maybe su Anty sa saimata, kokuma muje da ita ta siya” 

Wannan statement din data ji yafi kowanne bata mata rai, su Jalal basu san ta shigo ba, dan sun bawa kofar baya, nan Take ta shakunu ta karasa shigowa dakin fuskarta babu walwala ta zo ta tsaya. 

Jalal na ganinta ya maze ya jingina da jikin kujera ya dora kafa daya kan daya

Ta kalli Jalal tace 

“Sannu mara mutunci wanda be san ciwon kansa ba, Jalal saboda ba ka maidani komai ba tsawon watanni shida ban saka a idona ba, kuma saboda kai ba dan mutunci bane har a hada kai ai maka Aire ba tareda izinina ba, saboda munafunci baka tuntubeni ba tunda akayi Auren nan ka hada kai da dangin ubanka kayi tafiyarka inda ta zaba maka, se yau ka dawo kana zaka saimata gida da furnitures, kudin na ubanta ne? Ko shi ya tara maka? Wallahi Jalal se an kashe Auren nan, ban yadda ka zauna da yarinyar nan ba, seka saketa kuma seka baro wannan tsinan nan aikin data samo maka a lagosa, tunda ba ita ta haifamin kai ba”

cikin masifa Mummy take wannan hakilon Masifar, har Daddy ya fusata zeyi magana Jalal yace

“No Daddy yi hakuri, ban sanka da fada ba, kayi shiru kawai, bari zanje in dawo” Jalal ya mike ze fita, Mummy ta kuma fusata tace

“Nizaka mayar ‘yar Iska ina maka magana, Wallahi Jalal in baka saki yarinyar nan ba sena maka baki” cak Jalal ya tsaya ya waigo yana kallonta. 

Daddy dafe kai yayi, dan shi a rayuwarsa sam baya son tashin hankali. 

Jalal yazo gaban Mummy ya kalleta yace

“Mummy idan kikamin baki akan na wasu zaki ďora, inkin min baki baze dameni ba, tunda wanda yake dawainiya dani be ishekiba, baki da wata cikakkiyar hujja na kin Aure na, bazan saki Jalila ba saboda ina sonta, kema soyayya ce tasaki zama da mahaifina, nima na Auri wadda na rayu da sonta, baze yuwu amin Auren dole ba, tunda kema bashi aka miki ba”

“Jalal ni kake gayawa haka?” 

Kai tsaye yace

“Yau na fara gaya miki gaskiya? Bazan Auri macen da bana so ba saboda san zuciyarki, da in saki mata ta gara kimin bakin, dama can a lalace nake, in kika min baki kinga dorawa zanyi” 

Yana gama maganar ya fice. 

“Innalillahi wa inna ilaihi raji un, nashiga uku, dan dana haifa ya tsaya a gabana yana gaya min wannan maganganun, Habib Jalal ua zabi mace akaina da na haifeshi, ban taba zaton haka ba, tunanina Jalal shaye2 kawai yake, yaushe Jalal ya fara son Jalila da har yake gayamin wannan maganar akanta, tun yanzu, wallahi na tsani yarinyar nan”

Daddy yace “Khadija be kamata kiyi wannan maganar ba, bari in tuna miki wani abu, Soyayyar da nake miki tasa na zauna dake tsawon shekaru, na fifita ki fiye da Ahalina, kika rabani da kowa nawa, Ashe ba dadi, na fuskanci Soyayya bazata yiwa Jalal da wasa ba, dan haka ki shirya sa hannu ki karbi irin abunda kika aikata kema”

Mummy cigaba da rusa kuka tayi tama fadin 

“Wallahi baze yuwu ba, ni na haifi dana ba’a isa amin iko da shiba, babu wadda ta isa ta juyamin yaro, nasan wannan makircin Salma ne, zata ďau fansa a kan ďana, tana tunanin zata mallake min ďa saboda wannan banzan shirin nata? Wallahi bata isa ba” tuni Idon Mummy yayi jawur tana kuka tana masifa, Daddy ba shi da zabin da ya wuce yabar mata ďakin, dukda yadda yakejin kukan nata a zuciyarsa, Amma wannan faďan rashin gaskiyane kawai take yi.

Ilham kuwa tana kitchen tana hada abunda zata ci, sama bata san Jalal ya shigo part din ba, tana daga kai ta window taga shigar Jalal part dinsa, gabanta ne ya fadi, ya wani kara kiba, wani tunani ne yazo mata, hakan yasa ta fito da sauri ta tafi part din nasa, tana zuwa ta tarar baya palourn dan haka kai tsaye itama ta bishi bedroom din nasa, Amma tana zuwa ta tarar har ya shiga toilet, gefen gadonsa ta samu ta zauna ba tare da fargabar komai ba, tayi a kalla mintuna Ashirin sannan ya fito sanye da gajeren wando jikinsa babu riga se karamin towel yana goge ruwan jikinsa, Sam Jalal be kula da Ilham ba, yayinda Ilham ta daskare a zaune tana karewa surar Jikin Jalal kallo, 

Gaskiya Jalal ya kai a so shi koba dan dukiyar sa ba, ko ina na jikinsa kwance yake da gashi tun daga kansa har kafafunsa, dogone jikin sa a murde yake, dama ga jikinsa yana cin karfe, kallo daya zaka masa kasan namiji ne me matukar kwarjini, yana ďaga kai yayi ido hudu da Ilham zaune akan gadonsa, a fusace yace “Ke meye haka? Uban me yakawo ki dakina a daren nan? Ta shi kifita ki barmin daki” 

Mikewa Ilham tayi ta tako gaban sa ta tsaya tana kuma kare masa kallo, “Jalal dagaske kayi Aure ko?” 

“Tambayata ma kike? Ban sani ba, fita ki barmin daki” 

Towel din hannunsa ta karba, ta ajiye ta zuba masa ido, Hawaye ne ya fara bin idonta

“Jalal namaka son da ban taba yiwa wani namiji makamancin sa ba, Jalal why? Ina sonka Jalal, meyasa zaka Auri wata bani ba, Wallahi ina sonka, Jalal ka shmmace ni, ka Auri yarinyar da nafi tsana a rayuwata, Haba Jalal meyasa kamin hakan?” 

“kina son Jalal ko kina son cutar da shi? Kina sona nikuma na rayu da son yarinyar da kika fi tsana, saboda a duniya a yanzu babu wanda ya gwada min so kamar yadda tayi, I love Jalila with all my heart, ba abunda bazan sadaukar akanta ba, i am sorry, kema Allah yabaki me sonki”

Wani kululun takaici ne ya tokare kirjin Ilham, Amma ta maze, hannu ta mika kirjin Jalal zata shafa kirjinsa amma ya rike hannunta, ya girgiza mata kai, 

Ya dan lumshe ido ya bude yace

“Abunda yasa nake kara Son Jalila kenan, ba ruwanta da abunda ba nata ba, karki tsallake iyakar ki, karki taba mata miji kin san halin ta dai base na gaya miki ba, Abunda kike hari tsawon lokaci ya zama nata, a gaskiya ta miki ba dadi, ta rusa shirinki gaba ďay” ya karasa maganar yana ďanyin murmushin mugunta, sekuma ya haďe rai yace 

“malama get out from my room” 

Ilham tace “Amma Jalal” 

“ki fitar min daga ďaki malama, ko ba kya banbance abunda ya dace da wanda be dace ba? Kifita bana son ganinki” Jalal ya katseta

“Yaya Jalal…” 

“kifita nace ko in miki Illa, natsaneki bama son ganinki, ki fita ki bar min daki ko in kakkarya ki” 

Yadda yakoma yana maganar a fusace ya sa Ilham ta fita da sauri ta bar dakin. Wani dogon tsaki Jalal ya ja ya saka doguwar Jallabiya ya kwanta. 

Ilham kwana tayi tana juyi ta kasa bacci, Jalal da ba ruwansa da mata yaushe ya fara Soyayya? Har yake gaya mata yana son Jalila fiye da komai, yadda taga rana haka taga dare zuciyarta kamar zata fito,tana karajin tsanar Jalila a ranta. 

Kamar yadda suka tsara, Jalal da Daddy sukaje suka sai gida a tarauni, gidan yayi matukar kyau da tsaruwa, yanada girma sosai gidan, palour biyu, bedroom uku kowanne da toilet se kitchen biyi da store da katuwar harabar gida. 

Daddy ya samu Abba akan, an sai gidan dasu Jalal zasu zauna, Jalal ze sai furnitures, Abba yace be yadda ba shi zewa Jalila kayan daki, Jalal ba dan yaso ba ya hakura, Abba da Maama sukaje suka ga gidan sun yaba gidan sosai, Abba seda ya cikawa Jalila ko ina da kaya, gidan ta yayi kyau ya tsaru matuka. 

Sam Jalila bata san abunda ake ba, ita dai taga su Hajiya Salma sunata kara shiryata, Hajiya Salma taje ta samu Jalila a daki tace “Jalila ki ware gashinki, me kitso zatazo ayi miki kunshi da kitso, ranar Asabar zaki tare” 

Zare ido Jalila tayi tace “Wai Asabar me zuwa?” 

“Eh mana, mijinki yace; se kin tare ya gaji da wannan sintirin” 

Shiru Jalila tayi ta sunkuyar da kai, Hajiya Salma tace 

“Haba Jalila meye kuma na damuwa? Allah ya baku zaman lafiya, karki damu kinji” jinjina mata kai kawai Jalila tayi ba tareda tace komai ba. 

Yau weekends ne, Hanan sun gama cin Abincin Rana da Jawwad, tana ta zuba shagwabarta yana biye mata, dan ba karamin birge shi wannan shagwabar take ba, yace 

” Habibty Inaga ranar Saturday fa sister dinki zata tare” 

“Wai Jalila?” 

Jawwad yace

“eh ita, munyi waya da shi dazu da safe kina bacci, ya gayamin ya sai gida, an gama zuba komai ranar Saturday zata tare, inkuma sunki zeje ya dauketa ne kawai” 

Dariya Hanan ta kama yi, Jawwad yace

“ya dai, ya naga kina dariya?” 

“Akwai kura ne” 

“Kura kuma? Meyasa kikace haka?” 

“Hmm bakomai, gaskiya yakamata muje kano, zanso inyi kallon yadda wannan rayuwar masoyan zata kasance” 

Jawwad yai murmushi yace “lafiya kalau zasu zauna” 

“Hakane wuyatta su zauna guri daya, bari a jima in kirata, naga har yanzu bata da waya, se dai kabani taka in kirata” 

Jawwad yace “Shikenan naga be bata wayarba har yanzu” 

“nasan ze bata insha Allah”

Hanan ta mike ta tafi bedroom dinta. 

Jalila tarasa meya kema ta dadi, wai ita ce zata tare a gidan Jalal, a matsayin matarsa, tanata tunane2, Amal tayi sallama, Jalila ta amsa, Amal tace “Anty Jalila, Mummy tace in kawomiki phone, your sister wants to talk to you” 

Jalila a ranta tace ;kai yaran gidan nan sunfiye iyayi, ji yadda take magana kamar me koyon hausa

Jalila tasa hannu ta karbi wayar tareda cewa “Nagode” 

Wayar aka sake kira Jalila ta daga wayar tareda fadin 

“Salamu Alaikum” 

Yanayin muryarta ze gaya maka tana cikin damuwa, Hanan tace

“Amaryar Yaya Jalal, ke ko kirana ba kyayi se idan nina kiraki ko?” 

Cikin sanyin jiki Jalila tace

” kinsan bani da waya tun ranar dinner da ya karba be baniba, bana son yawan takura musu da karbar waya” 

Hanan tace “hakane ya kike ya shirye2” 

“shirye2 me?” Jalila ta tambaya 

Hanan tace 

“Ahhh Haidar yacemin ranar Saturday In Allah ya kaimu zaki tare” 

Dan karamin tsaki Jalila tayi 

“shine wani ya shirye2, ba wani shirye2 ni abun duniya ya dameni, ina tunanin irin zaman da zanyi a gidan nan” 

“meye wani abun damuwa kuma? Karki dorawa kanki ciwo mana, Allah yabaku zaman lafiya yasa kina zuwa kiyi karo da shi” 

Jalila tace “inyi karo dame?” 

“ďan baba mana, nan da wata tara muzo suna” hanan ta bata amsa

Wani uban tsaki Jalila tayi “Ke kinfiye shirme wallahi” 

“bawani shirme, Addu’a nai miki tagari” 

“rike addu’ar ki bana so, ni ba haka naje yi ba” 

Dariya Hanan ta dinga yi “Wallahi karya kike, abunda kikaje yi kenan, sekin cika masa gida da ‘ya’ ya duk shekara zaki dinga haihuwa” 

Kashe wayar Jalila tayi, tareda yin dogon tsaki, inta biyewa Hanan bata mata rai zata cigaba da yi. 

Shirye2 sunyi nisa, Hajiya Salma da Anty sun tsaya an gyara Jalila yadda yakamata, sun hada mata kayan turaruka daban2, Suka shirya mata kayanta a trolley. Ta wani bangaren Jalila tanata murna zata koma garinsu, ta cigaba da zuwa makaranta, 

Anty tace “Jalila na cika alkawarin dana taba yi miki, ga turaruka nan, in sun kare ma kiyi magana se in hado miki wasu” 

“to Anty na gode” 

Abee yayiwa Jalila nasiha sosai, tareda yi mata fatan Alkhairi, yabata kyautuka na litattafan Addini dana zamani, sekuma kyautar system yace taje taita karatu. Jalila tai tayi masa godiya. 

Hajiya Salma sunyi waya da Jalal, cewar zasu taho da Jalila gobe zasu tsaya a gidan su Jalila, sannan su kaita gurin Mummy daga nan akaita gidanta. 

Jalal yace “gaskiya bana son ku kaita gidan Mummy, dan seta bata muku rai, kawai ku kyale ta” 

“A’a Jalal baza’ayi haka ba, Mahaifiyarka ce akwai bukatar a sauke hakkinta na uwa, yakamata ta sawa Aurenka Albarka” 

Jalal yace “Shikenan yadda kuka gani, Amma ni a gurina babu bukatar hakan. 

Ilham bata taba sanin tana kaunar Jalal ba kamar yanzu, gaba daya kishi ya hanata sukuni ko Abinci bata iya ci, ita a tunanin ta tana so tayi soyayya da Jalal ne dan cika burin mahaifiyarta, Amma yanzu ta gane kaunar Jalal tayi mata illa, bata bacci sam, yadda taga rana haka taga dare, wai Jalal ke gaya mata shidin mallakin Wata mace ne, macen da ta dade tana cusa masa miyagun maganganu da cin mutunci amma saboda bashi da zuciya yake fadin shi mallakin ta ne, hawaye ne ya gangaro daga idon Ilham tace “Wallahi Jalal muddin baka Aureni ba sena fitini rayuwar Auren ka, sena uzzurawa rayuwarku, se Gidan Auren ka yazama kurku ta fishi ‘yanci, idan har kuka ji dadin Aure ba Saudatu ce ta haifeni” ta cigaba da kuka da surutai a daki. 

Jalila se murna take zata koma Kano, koba komai zata dinga zuwa makaranta ta rage kadaici, karfe goma sha daya na safe suka shirya, Anty, Hajiya Salma, Husna, da wasu daga danginsu Jalal suka taho yiwa Jalila rakiya Kano, 

Se kusan karfe hudu na yamma suka iso, Maama ta san da zuwansu dan haka ta riga ta shirya komai, har ‘yan uwanta da makwabta ta sanar, bayan sallar magariba za’a raka Jalila gidanta. 

Jalila tayi murna ganinta a gida, Abba yayi murna yadda yaga Jalila tayi kalau da ita tayi fes kaman wata matar hamshaki. Dakinsu taje komai yana nan yadda ta barshi, kewar Nana ta dinga ji a ranta, tana tuno abubuwa da dama da ya faru a wannan dakin, wasu ma farinciki wasu na bakinciki. Maama tazo ta sameta tace

“Jalila ki debi duka abunda kike so akayanki, wanda zakiyi Amfani da shi nan kusa se a tafi miki dashi” 

“to Maama zan diba Insha Allah” 

Sukaci Abinci sukayi Sallolin da ake binsu. 

Anty tace “Jalila yakamata ki shirya muje a kaiki gurin uwar mijinki, kar dare yayi sosai” 

Ras gaban Jalila ya fadi! Jikinta yafara Rawa, ta shiga duniyar tunanin wace irin karba Mummy zatayi mata. 

Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta Amsa, seda takuma wanka ta canza kaya, suka nadeta a cikin lafaya, se kamshi takeyi Maama ta kama hannunta ta kaita gurin Abba, ya dinga mata nasiha da Addu’a, Jalila se kuka take, yadda Abba yaji rabuwa da Jalila beji haka akan Nana da Jawwad ba, yana matukar tausayinta. Bayan ya gama ne Maama tayi mata ‘yan nasihohi da Addu’a, dan sosai take jin kunyar abubuwan da ta aikatawa Jalila. 

Wasu daga cikin’ yan rakiyar amarya sunyi gaba dan suje suga ďaki, Yayinda Hajiya Salma da Antyn Jalal suka nufi gidan su Jalal Da Amarya Jalila. 

Vote, Comment and

Share please 

I want comments not stickers or just thanks 

Daga alkalamin Aysher cool 

🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️

What’s app only 07063065680. 

Follow me onWatpad @Ayshercool7724 

     ……🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By

AISHA HUMAIRA

( _Daddy’s girl_) 

*PERFECT WRITER’S* 

*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ’𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼’ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

*P.W.A*✍️

PART 2 

_PAGE 5️⃣3️⃣ 106

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam. 

Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka

Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba. 

Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what’s app number dina

07063065680

Watpad @Ayshercool7724 

                _MY FIRST NOVEL _

Tunda suka doshi gidansu Jalal gaban Jalila ke wata irin mummunar faduwa ta dinga karanta duk abunda yazo bakinta, suna tun karar kofar da zata sadar da kai da cikin gidan gabanta na cigaba da faduwa kirjinta se bugawa yake da karfin gaske. 

Anty ce tafara sa hannu ta murda handle din suka shiga a babban parlour suka zaunar da Jalila, Hajiya Salma ta kira daddy a waya tasanar masa sun iso amma basu ga kowa a parlour ba, da yake daddy ya koma, dan haka ya kira Mummy a waya yace taje parlour tana da baki. 

Abun ya bata mamaki sosai, wani irin bakine haka da bazasu kirata ba, fitowa tayi ba tareda tayi tsamanni ba tayi karo dasu Hajiya Salma a zaune a palour, rabon da taga hajiya Salma tun lokacin da ta bar mata gidan, Salma tana nan da gayun ta ba kace ta haifi Mahmud ba. 

A fusace Mummy ta dube su a wulakance tace “lafiya daga ina? Mekuka zo yimin?” 

Hajiya Salma tace “kwantar da hankalinki mana Hajiya khadija, ba abun zafi bane ba, Matar danki muka kawo miki, ki musu Addu’a ki sa musu Albarka zamu kaita gidan danki” 

Wani tsinannen Kallo Mummy taiwa Hajiya Salma tace “Albarkata ake nema a wannan Auren munafuncin, da kuka haďa kai kuka aura masa yarinya ba da izinina ba, shine zakuzo wani wai im sa muku Albarka, bazasu taba samun Albarkata ba, saboda bana son yarinyar nan, na tsaneta tun kafin ta Auri ďana take juya shi, abunda takeso shi zeyi danme zan kaunace ta? Auren nan baze taba Albarka ba, kuma wallahi sena ga bayansa, senaga bayan Auren nan “

Anty tace

“Allah sarki, abunda kike gudune se ya faru, sannan Jalila taimakawa Ďanki take, kin san ba dan mutunci da girmamawa ba, Baza’a dauki nutsatsiyar yarinya abawa ďanki ba” 

“tunda ansan ba nutsatsen bane, uban meyasa a lika masa wannaan yarinyar, se a kyaleshi da halinsa in aura masa yarinyar da nake so, wallahi bazan taba son yarinyar nan ba, da nake mata kallon mutuniyar kirki amma tunda tafara bin dana nagane makira ce mara mutunci “

Rirrike Hajiya Salma Jalila tayi ta kara sautin kukanta, Hajiya Salma tace

” ko ki sota ko karki sota Allah ya riga ya haďa Auren nan, zuwa yanzu yaci ace kinyi laushi kinyi hankali amma babu alamar hakan a tare dake, Allah shaida ne ba abunda yarinyar nan ta miki da ta cancanci wannan kiyayyar da mugun bakin daga gareki” 

“kinga sauraramin bana son salon munafurci, nafada bana sonta, kuma bazasu taba ganin haske ko albarka a rayuwar Auren nan ba, kuma wallahi sena kashe Auren, babu wani alkhairi ko amfani da take da shi a gurin Jalal, wannan dunkiyar tasa kawai take kwadayi, shiyasa ta aureshi ta juyamin shi, to wallahi bata isa ba, tunda nina haifi ďana, shida abunda ya mallaka nawane, muddin ta shiga gidan Jalal tafara kirga ranakun bakinciki a rayuwar ta har seta kyalemin ďana, shegiyar yarinya mara usuli”

Tunda ake fadawa Jalila rashin mutuncin Mummy bata taba zaton ya kai haka ba, wata hira da suka tabayi da halima ta fado mata rai da halima take ce mata “Sayyada karki bari wani abu ya hadoki da matar nan dan bata da mutunci” sosai Jalila miyagun maganganun Mummy suka daki zuciyarta. 

Hajiya Salma tace “Shikenan mungode da wannan karbar da kikayi mana muda matar ďanki, Amma ki sani idan kin rabani da gidan mijina kin zauna lafiya, bazan taba bari ki lalata auren nan ba, Allah yafi ki sannan a wannan karon dai2 nake dake, Aure an riga anyi shi kuma mutuwa ce zata raba shi”

“Se ayi in gani ai” 

Anty tace “Jalila tashi mu tafi” 

Jalila ta mike wani irin jiri na kwasarta, se rarrashinta Anty take, 

Ilham ce ta shigo palourn da alama daga wani gurin take, wani kallon banza Ilham tayiwa su Hajiya Salma kafin idonta ya dira akan Jalila, dukda Jalila tana cikin lafaya, amma Jalila tayi kyau, jikinta yayi sumul sosai ga wani kamshi da dakin yake yi, hannunta ya sha kunshi ja da baki. 

Ilham na ganin ta wani azababben kishi ya taso mata, gurin Jalila ta nufa gadan2 idonta ya rufe gaba daya tace

“Wallahi bazan taba yafe miki ba, kin rabani da ďan uwana abunda na dade ina so shekara da shekaru, wallahi zakigane baki da wayo, munafuka kece me cewa babu abunda zakiyi dashi, kinsha kiransa namiji mara daraja, mara tarbiyya da yake makirace kika zagaya kika Aureshi, algunguma…. Sosai Ilham take kuka tana kokarin fizgo Jalila 

Hajiya Salma a fusace ta sa Jalila a bayanta tace “Ke lafiya meya haka?” 

“ban saniba wallahi sena yi mata rashin mutunci, seta gane ni ba kanwar lasa bace, naga ta yadda zatayi zaman Auren a kwanciyar hankali” 

Jalila tasa hannu ta ďaga lifayarta ta kalli Ilham ido duk hawaye, ga idanunta sunyi jawur, kallon da Jalila tayi mata seda gabanta ya fadi yadda taga Jalila ta hade rai tana mata wani irin kallo. 

Sunkuyar da kai Jalila tayi ta cigaba da zubda Hawaye, Jan hannun Jalila su Anty sukayi suka fice waje. 

Anty tace “Anty Salma su dangin su khadija tun asalinsu basu da mutunci, masifa acikinsu kamar barkono” 

Hajiya Salma tace “Allah dai ya kyauta, ki kwantar da hankalinki Jalila komai ze wuce Insha Allah” 

Suka sa Jalila a mota zuwa gidan ABDUL JALAL. 

Dukda kan Jalila na cikin mayafi amma gidan ya tsaru sosai, suka kaita daki suka ajiyeta, akaita mata nasihohi, daga nan suka tafi suka barta a gidan, sakkowa tayi daga kan gadon ta nemi guri ta zauna a kasa, tana tuno irin maganganun cin mutuncin da Mummy ta dingayi mata da wulakanci, take taji mugun danasanin Wannan Auren yakara rufeta, Hawaye kawai takeyi, Mummy ta riga tayi mummunan furuci akan Auren nan, dama gashi bata tabaccin shi kansa Jalal din yana sonta, ga Ilham ma miyagun maganganun da ta dinga faďa, shikenan ni kowa na raba nazama abar kyama, Allah ka yafemin in wani laifin na aikata. 

Har wajen goma na dare sannan Jalal ya shigo gidan, milk din yadine a jikinsa me laushi, da hula akansa, dakin da aka kai Jalila ya nufa dauke da ledoji a hannunsa, yana shiga ya tarar tayi zaman dirshan a kasa tanata zubar da Hawaye, dan tsayawa yayi yana kallinta dan be san ta ina ze fara ba, a hankali ya karasa gabanta, tana jinsa amma ta share ta cigaba da kukanta, ya sa hannunsa ze janye nata daga dukunkunewar da tayi a mayafi, da sauri ta janye hannunta ta ja da baya sekace taga dodo. 

“Wai kukan me kikeyi hakane? Ke kullum duk inda kika zauna sedai kiyi kuka ne?” 

Kallon shi tayi da rinannun idanuwanta cikin kuka tace “dole kace haka mana, me ya ragemun a rayuwa inji dadi banda kukan? Ka gayamin me ya ragemin? Mahaifiyarka bata sona, bata kauna ta, kaima kasan hakan amma ka Aureni, mahaifiyarka tace; bazata taba kaunata ba, seta kashe Auren nan, kasan da haka amma ka Aureni, anata kwallo da rayuwata daga nan zuwa can, dana fita daga wannan matsalar in fada wannan, zamana da kai nasan wani sabon shafin kaddarar ne, dan Allah ka sakeni in auri wanda yak sona, wanda mahaifiyarsa zatayi farinciki da shigata rayuwarsa,”

Shiru Jalal yayi ya tsura mata ido yana kokarin gano ko har cikin zuciyarta take maganar nan, mikewa yayi ya juya ya fice yabar ďakin zuciyarsa a cunkushe. 

Daya bedroom din ya nufa, yana shiga ya sauya kaya, ya ajiye wayoyinsa ya nemi guri ya kwanta, tunani daban2 ya ziyarci zuciyarsa, Kenan Mummy ciwa Jalila mutunci tayi? Shiyasa tun farko be so akaita gurin ta ba, ga shi ta bata komai, Amma ta wata fuskar Jalila tanada gaskiya, babu wanda ya tuntubeta aka yanke mata wannan hukuncin, aka daura mata Aure ba tareda Amincewarta ba, shikenan wannan zaman ze yi a rayuwar Aurensa? Zuwa yaushe Jalila zata yadda da shi a matsayin miji? Haka ya dinga tunani abun duniya yabi ya isheshi. 

Yana fita Jalila ma ta cigaba da kukan, karshe a zaune a kasan nan tayi bacci, ko kayan jikinta bata canja ba. 

Koda gari ya waye bata bi ta kansa ba, tai sallar asuba tai kwanciyar ta, ta cigaba da baccin ta, lokaci2 idan ta tuna yadda Mummy ta dinga cin mutuncin ta se taji gaba daya haushin Jalal ya kamata, dan me ze yadda da Auren ta bayan ya san maman sa bata so, gaba ďaya Mummy ta gama kwashewa Auren nan Albarka, yunwa ce ta ishi Jalila dan haka ta tashi tai brush tai wanka, ta dauki ledar da ya shigo da ita jiya, ta bude kajine a ciki gasassu, se fresh milk, ko warming dinsu batayi ba ta ci abunta ta kora da madara, ta cigaba da zaman ďaki. 

Tun ranar da’aka kawota da Jalal ya shigo bata kara ganinsa ba. A kayanta akwai tarkacen biscuit su ta cigaba da ci, kusan kwana biyar bata kuma haduwa da Jalal ba, da safe tayi wanka ta sa kaya ta fito, tana dan zazzagawa tana fitowa main palourn ta ci karo da katon hotonta da nashi, Hajiya Salma ta sa sukayi, an rubuta Happy marriage life, hoton yayi kyau sosai, ďan tabe baki tayi ta cigaba da za gayawa, gida yayi kyau masha Allah, Amma kwata2 takasa farinciki da hakan, saboda bacin rai da yake cin zuciyarta. 

Koda ta duba store Jalal ya aje komai na kayan Amfani, hatta omon wanki akwai, duk abunda yasan na amfanine kona kayan masarufi ya ajiyeshi, fitowa tayi ta fita harabar gidan tana kuma kallo, katuwar haraba ce sosai, tana zagayawa ne ta fara jin kaurin sigari, tunkarar inda take jin kaurin tayi, tana zuwa ta tarar Jalal yanata zukawa cikinsa, yana fesar da hayakin a iska, ta dade a tsaye a gurin be sani ba, kamar an taba shi kawai ya juyo, yaci karo da ita a tsaye tana kallon sa

Jikinsa yayi sanyi da irin kallon da Jalila ke masa, amma ya basar ya cigaba da shan tabarsa, juyawa tayi ta koma cikin gidan ba tareda tace masa uffan ba. 

Kusan sati biyu da tarewar Jalila amma ko maganar kirki bata haďata da Jalal, Abun ya damu Jalal matuka, be taba zaton Jalila zatayi watsi da shi haka ba, girki ma batayi, se yunwa ta addabeta zata hada cornflakes ta sha, gashi mafi yawan lokutanta tana karar dasu a kuka se bacci wani lokacin, ya damu sosai da wannan hali da takeyi. 

Ko yayi niyyar yi mata magana idan yaga fuskarta da yadda take basar da shi se jikinsa yayi sanyu. 

YauDa Asuba da Jalila ta idar da sallah tana zaune akan dadduma ya shigo dakinta, bata ce masa uffan ba, yasa hannu a Aljihu ya dakko sabuwar waya ya ajemata akan side bed, ya dakko kudi ya ajiye mata, sannan yace “ga kudin mota nan kikoma makaranta, ni zan wuce lagos” 

Dagowa tayi ta kalleshi, ta kalli inda ya aje kudin 

“wai nika dai zan dinga kwana a gidan nan? Gaskiya ni bazan iya kwana ni kadai ba tsoro nakeji” 

“to ya kikeso ayi?” ya tambayeta

“Sedai in koma gida in zauna, in dinga tafiya school din a can” 

Wani mugun kallo ya mata

“ba inda zakije, daga makaranta ban yadda kije ko ina ba” 

“to Amma nifa bazan iya kwana ni ka dai ba, inajin tsoro” 

Cikin ko in kula yace “se kisan yadda zakiyi, ni yau zan koma” ya fice ya barmata dakin

Haushine ya isheta, ta yaya zata iya kwana a gidan nan ita ka dai? Zuwa tayi tai wanka tafara shirin makaranta hankalin ta ya kai kan wayar daya ajiye mata, sabuwar wayar daya ajiye mata, dauka tayi ta kunna ta, komai nakan waccan wayar tata yana nan, da lambobinta, amma ya canza mata layi. 

Ajiye wayar tayi ta gama shirinta ta tafi makaranta. 

Tunda taje take shan tambayoyi daga gurin ‘yan ajinsu akan dagaske tayi Aure? 

Haka ta dinga basu amsa dai2 da tambayoyinsu,’ yan jin kwaf kuwa sukace tunda basuje bikinta ba zasu kawo mata ziyara har gida. 

Koda ta dawo gida ta tarar baya nan, ya tafi, da ranan ma tsoro takeji, tasaba ko yaya tana jin motsinsa, tun kan magariba ta kulle ko ina ta koma daki ta rurrufe ko ina ta sa key, Tana sallar Isha’i ko Abinci bata ciba ta haye gado ta lullube tana rarraba ido, sam takasa bacci. 

Shima sam Jalal yakasa bacci, yana ta tunanin ko yaya zatayi? Ko tayi bacci oho? Tunani yayi ko ya kirata ne, amma ya tuna a halin da suke shida ita dan haka ya fasa kiranta dan karma ta bata masa rai. 

Jalila kam bacci da kyar tayi shi, cike da tsoro, ko yaya taji faduwar abu zata firgita ta tashi. Alla2 ta dingayi gari ya waye saboda tsoro, gari na wayewa take shiryawa ta tafi school. 

Wasa2 Jalal seda yayi sati biyu bata kuma jin duriyarsa ba, gashi ita ba lambarsa ce da ita ba, inma tana da lambarsa ta kirashi tace masa me? Amma tasan shida ya canza mata waya yana da lambarta, Amma be iya kiranta yaji wani hali take ciki. 

Seta kunna karatun qur’ani a speakun palourn ta take iya bacci, yanzuma tana kudundune a gado ta dau wayarta ta kunna data, taga Hanan ta mata magana ta what’s App, chatting suka dingayi can Hanan takirata a waya suka cigaba da hira

Hanan tace “ke by now kamata yayi a ce kina tareda mijinki, Amma kina nan kina chatting” 

“ke meya hana kije ki kula da naki mijin?” Jalila ta bata amsa

Hanan tace “Wallahi ya fita siyomin cashew ne” 

“cashew kuma a daren nan?” 

“Eh mana, ba mijina bane”? 

Jalila tace “haba Hanan, ya kike garamin ďan uwane, dare fa yayi zaki tura shi siyan cashew” 

“to ya zanyi, wallahi nakasa cin Abinci ne, shi nake son sha” 

Jalila tace “hmm kodai kodai abunne?” 

Hanan tace “au to ku zamu tsaya jira, kifara saimana feeder da pampers” 

Jalila tace “wow masha Allah, Allah ya in ganta” 

Hana ta amsa da “Ameen, ke kije ki kula da mijinmi seda safe” 

Jalila tace “wai wane miji? Yana lagos fa” 

Hanan tace

“dan yana lagos bazaki kula da shiba, keep him busy, kuyita chat kina zuba masa kalamai har yayi bacci” 

Dan guntun tsaki Jalila tayi. 

Hanan tace “Jalila kaddai har yanzu ba kwa jituwa? Jalila me yasa?” 

“Hanan babu wani Alkhairi a wannan Auren namu, Hanan mahaifiyarsa tacimin mutunci fiya da yadda kike tunani, wallahi jin gidan nake kaman kurkuku” 

“Haba Jalila, to Jalal ne yayi miki? Meye laifinsa anan, wannan Auren iyaye ne suka hada shi ba Jalal ba, yakamata ki tausaya masa Jalila, ranar suna video call da Haidar ya rame sosai, wallahi ina tunanin bashida lafiya ma, sedai kinsan ba lallai ya fada ba, saboda zurfin cikinsa, in Allah ya dubi niyyarki akan sa seya temake ki, mijinki ne Aljannarki zaki nema, shi wanda kike tunanin kina so din sekiga ba shine Alkhairi ba, kiyi tunani ya zakiji idan ninakewa Haidar abunda kikewa Jalal? ” shiru Jalila tayi, Hanan tace

” yakamata kiyi tunani, Jalal mutum ne shima, wannan shareshin da kikeyi ze iya jefa shi halaka fiye da baya, kuma zakiji kunya idan dangin mahaifinsa da suka yadda dake suka gano irin zaman da kike da ďansu, ke hatta Abba bazeji dadi ba”

Haka Hanan ta cigaba da da yiwa Jalila nasiha, sukayi sallama ta kwanta, shiru tayi tana nazarin maganganun Hanan, da kyar tayi bacci tanata tunani, Hanan ta ce mata ya rame kaman bashida lafiya, Ta danyi Ajiyar zuciya, a haka har bacci yayi awon gaba da ita. 

Washegari yakama Friday, da wuri ta shirya dan ta wuce makaranta, Amma tana fitowa parlour da uwar safiyan nan kawai taga Jalal a parlour, ta tsorata sosai, shigowar dare yayi, dan haka bata san ya dawo ba, ya ďaga kai ya kalleta, ya sunkuyar da kansa ya cigaba da abunda yake, ba tareda ya kalleta ba, Jalal ya rame sosai ta bakin Hanan kaman bashida lafiya, bredi yake ci babu ko tea se lemo me sanyi da yake sha, yana ci yana bata rai, gaba daya tausayinsa ya kamata, Amma yadda yayi kaman be ganta ba yasa itama tai wuce shi a parlour tai ficewarta. 

Koda taje makaranta tunanin ne yake damunsa ya hanata sukuni, dukda yau juma’a se karfe biyar ta gama lectures. 

Da ta koma gida motarsa tana harabar gidan, da sauri ta shiga cikin gidan amma baya palour kamar yadda tasaba in ta dawo tana tarar da shi a parlour, ko baze kulata ba, kullum yana zaune a palour seta dawo yake barin palourn ya shiga wasu sabgogin, Amma yau baya nan, mazewa tayi taje ta watsa ruwa, ta shiga ayyukanta Amma hankalin ta yana kan rashin ganin gilmawar Jalal, wasa2 har dare yayi amma bata ganshi ba, ta sa kayan bacci ta kwanta taji zuciyarta takasa nutsuwa. 

Dan haka Mikewa tayi tasa hijjabinta ta nufi dakinsa, seda ta ďan ja wasu mintuna tana nazari, sannan ta murda kofar ta shiga. 

Koda ta shiga dakin warin sigari yake, Can ta hange shi akan gado daga shi se 3 quarter da vest, ya rufe ido se juyi yake akan gadon, da sauri takarasa gaban gadon tace “meyake damunka ne?” 

Bece komai ba idonsa a rufe, se juya kai yake, ya dafe kansa da hannunsa kan gadon ta hau tana magana “ka gayamin ko baka da lafiya?” 

Hannu tasa ta janye hannunsa daga kan nasa, ji tayi jikinsa ya dau zafi sosai 

“Jalal meyake damunka ne?” yanayin yadda ya bude idonsa ya kalleta ya mayar ya rufe tagane a buge yake, juyawa tayi bayan gadonsa taga guntayen sigari da ya shanye, ga dogayen kwalaban giya da ya shanye. 

Tuni idonta ya ciko da hawaye tace “giya Again, Jalal why? Meyasa haka? Kacemin zaka dena kuma kawai inga haka why Jalal?” 

Da kyar yake iya bude idonsa, sunyi jawur kaman an hura garwashi, cikin maye yake kokarin yi mata magana amma yakasa. 

Domin sauke Cikakken Littafin sai ku danna bulun Rubutun dake kasa.

👇👇👇

https://www.aihausanovels.com.ng/2022/09/abdul-jalal-chapter-15-book-1-end.html

Vote, Comment and

Share please 

I want comments not stickers or just thanks 

Daga alkalamin Aysher cool 

Back to top button